Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take bedroom d’in nasa Kansa yana cigaba da sara masa. Duk ‘ko’karinsa na son furta addu’a sai dai harshensa ya ‘ki ba shi had’in Kai. Tsawon lokacin da shi kansa ba zai iya ‘kayyadewa ba yana zaune a bakin gadon sai d’aga kai yayi ya ga gari ya fara haske. Da kyar ya mi’ke ya shige toilet. Sai da ya fara sakar kan sa shower ko zaiji sau’kin rad’ad’in da kansa da zuciyarsa ta ke yi, kafin ya d’auro alwala ya fito.
Sallahr ma yayi tane kawai ba tare da nutsuwa ba al’amarin da zai tabbatar maka tabbas da sihiri. Imran mai ‘ko’karin Ibada musamman Azkar na bayan sallahr Asuba, yau shine da mi’kewa da sauri bayan ya idar da sallah. Burin sa kawai ya aiwatar da abinda zuciyarsa take so na sakin Shatu, yana ji tabbas idan ba hakan ya aikata ba zai samu lislama cikin ‘kirjinsa da kwanyar kan sa ba.

Biro kawai ya d’auko da jotter ya kuma rubuta abinda zuciyarsa ke son ya aiwatar. Ya nad’e takardar had’e da mi’kewa. Direct part d’in Shatu ya nufa.


Shatu tun da Imran ya farka itama ta farka sai dai rad’ad’in da take ji a ‘kasanta shi ya hana ta mi’kewa, har zuwa san da ya fice daga bedroom d’innata tana jinsa.
Ba ta jima sosai ba ta mi’ke da
‘Kyar don duk jikinta ya d’au tsami, sai dai ta dake ta shiga toilet d’in a hankali. Yarda ta ga yayi mata da daddaren haka itama ta had’a ruwan ta zauna a ciki. Tsawon
Mintuna sannnan tayi wanka Ta d’aura Alwala ta fito.

Tana zaune saman daddumar da carbi a hannunta kan ta akam gwiwarta. Idanununta a lumshe da alama barci take ji, amma da yake ta saba sai tayi azkar d’in dole haka ta zauna tana son ta ‘karashe ta kwanta, don bata jin ko school zata iya zuwa yau.

Motsin bud’e ‘kofar ne yasa ta d’ago idanunta suka sauka cikin nasa, Gabanta ya fad’i ganin yarda idanunsa suka nuna tsananin ‘bacin rai haka nan fuskarsa babu annuri ko mis’kala zarratin, tamkar dai fuskar mutumin da aka yiwa mutuwa mai tsananin d’aga hankali, mutuwar iyaye d’a ko miji haka fuskarsa ta nuna. Da sauri ta d’auke kai don kuwa ba zata juri kallon da taga yana antaya mata ba, sai ya tuna mata da kallon da yake mata lokutan baya da ya shud’e sai dai wannan har ya fishi muni. Zuciyarta ta shiga sa’ke-sa’ke da son hasasho mata ma’anar kallon tambayoyi barkatai ta shiga yiwa kanta ita da zuciyarta. Laifin mai nayi masa? Ko dai ya taraddani ba budurci? Da sauri ta kawar da wannan tunanin don ba zata mance zafafan kalmomi da yabo da godiya da ya dinga mata da ya sameta a cikakkiyar budurwa da ta kai mutuncinta d’akin miji. Ba wannan bane zuciyarta ta bata amsa. Bai bari ta sar’ke da wani tunanin ba ya mi’ka mata takarda, ba tare da ya jira ta bud’e ba yayi azamar barin d’akin.

Hannunta na rawa ta shiga bud’e takardar, fatan ta taga yabo da godiya kamar yarda take karantawa a littafi sai dai tuni idanunta suka ga sa’banin haka kan kace kwabo hawaye sun ji’kar takardar sharkaf, ta sake ware idanunta akan rubutun da suka koma mata dishi-dishi “Ni Imran na saki mata ta Shatu.....
Daga haka ta yarda takardar ta fara gurshe’ken kuka “Tabbas nayi ganganci Imran da na mallaka maka kaina na manta ma’kiyi baya ta’ba zama masoyi, abinda kake sha’awa a jiki na kenan kuma ka same shi, dole ka sake ni don ka sha fad’a dama abin kunya ne a ganni tare da kai ace matarka ce mai zaka yi dani? Ni Shatu ‘yar ‘kauye Shatu da na taso a daji.” Hawayen ya cigaba da gangaro mata. Tana ji zuciyarta na bugawa na tsananin ‘bacin rai da ‘kuncin zuciya.

Da kyar ta mi’ke ta koma bakin Gado ta zauna, tana sake saka maza a layin mutane marasa tabbas dubi dai kalaman da ya dinga gaya mata jiya dubi sakayyar kuma da yayi mata yau, sakin aure a ranar da ta kwana uku da tarewa a gidan miji ya mayar da ita ‘karamar bazawara a shekarunta da ko shekaru sha shidda bata rufa ba. Wallahi ya cuce ta kuma ba zata ta’ba yafe masa ba har gaban abada ta kuma tsane shi tsana mafi muni, da bata ta’ba yiwa wani mahaluki ba.



Shi kuwa yana komawa d’akin sa ya ji duk wani ‘bacin rai da ‘kuncin zuciya sun kau daga ransa ya lumshe idanunsa yana sakin ajiyar zuciya. Shi dama ya san ba zai ta’ba son Shatu bada jiyan ma bai san me yasa har yaje ya kusanceta ba yana kuma dana sani da ba’kin cikin aikata hakan, ya tabbatar yanzu raini zai shiga tsakaninsu ba zai kuma bar ‘kofar rainin ba. Don ko dariya ba zai yi mata ba balle ta raina shi. Mommah da ya tuna shine gaban sa ya fad’i ya sani sarai a wannan ga’bar ba zata yi masa sassauci ba, yayi zugum yana tunani zuwa lokacin da wayarsa taand hauand ringing.
Da sauri ya d’auka ganin mai nemarwa Shaheedah visar zama a turkey ne, nan yake sanar masa visa ta kammala kuma ko gobe suke so zasu iya tafiya akwai jirgi da zai tashi daga Abuja. Cikin farin ciki da son gujewa fad’an Mommah Imran yace yayi masa booking. Da sauri ya mi’ke ya shiga shirya kayansa, yau zasu wuce Abuja idan yaso gobe jirginsu ya d’aga zuwa turkey shikkenan ba shi ba fad’an Mommah.


Ita kuwa Shaheedah tana can zaune jiran tsammani tun asuba take saka ran ganin Imran sai dai bai shigo ba, hankalinta a tashe yake bata da tabbacin maganin yayi aiki ko baiyi ba. Duk da dai bata haufi game da shu’umancin Shuwa. Ko sleeping dress bata cire ba balle aje ga babin wanka, idanunnnan yayi ‘kozai-‘kozai tunda ranar ba makeup gashi na kwana ana kuka. Tana cikin wannan yanayin Imran ya shigo. Gabanta ya fad’i ganin fuskarsa a had’e ba dai abu bai tafi yarda suke so suke fata ba. Ba kamar yarda hasashenta yake ba shi Imran haushinta yake ji tunaninsa duk ita taja masa yaje ya saukewa ‘karamar yarinya bu’katarsa ta jawo masa raini, da bata kulle ‘kofa ba ai da duk hakan bata faru ba. Fuskar nan a had’e yake dubanta, ya ja tsaki ganin duk tayi Jeme-jeme da ita zai iya cewa tunda yake bai ta’ba ganinta ba makeup ba, don haka yau yaga fuskarta ta kamar an tsamo kaza a
Salu’be daga ruwan zafi. “Ki tattara duk wani komatsanki.....” da sauri ya kalleta ba tare da ya ‘karasa ba ganin ta d’ora hannu a ka tana shirin runtuma ihu ido a waje take cewa “Don Allah kayi ha’kuri.” Tsaki ya ja “meye haka? Ai ba kiga hukuncin da zan miki ba sai nan gaba kad’an wallahi don na lura kin raina ni sosai. Kiyi sauri malama kada mu rasa jirgin tafiya Abuja gobe zamu wuce turkey sai kiyi waya ki sallama da duk wanda ya dace nan da 30mint jirgin Abuja zai tashi.” Daga haka ya juya ya fice Shaheedah ta saki wata wawuyar ajiyar zuciya, idanu a lumshe take fad’in Alhamdulillah wallahi har na tsorata. Na zata saki na zai yi. Sai kuma ta fara taka rawa jin turkey zasu wuce. Murnar ta ta tsaya cak tana tunanin ina labarin sakin Shatu? Ko har ya sake tan bata sani ba? Ture zancen tayi a gefe ta tashi da azama tana tattara kayan da zata tafi dasu. Tana yi tana danna kiran Antyn ta, sai dai bata d’aga ba da alama tana can tana hidimar Dahda.


Shatu ta dad’e a zaune ta rasa abin yi ita ba waya ba balle ta kira Mommah. Gaba d’aya jin ta take kamar mara lafiya, da kuma zata iya dama da fita zata yi tada shiga motar haya to sam ba zata iya tafiya ba. A hakan dai ta lalla’ba ta tattare iya abinda zata iya zuciyarta na tururi, ta fara tunanin ashe haka mata suke ji idan aka ce an sake su. Tabbas abin da ciwo ba kad’an ba wallahi ta tausaya musu ta kuma tausayawa kan ta.
Tana ganin takwas tayi ta shige toilet don tayi alwalar sallahr walaha kamar yarda Mommah ta koyar da ita.


Dai-dai lokacin shi kuma Imran ya fito daga part d’insa d’auke da trolley d’insa guda biyu. Cikin shigarsa ta kullum ta yard d’inkin African Attire. Da sauri ya isa sashen Shaheedah ta gama shirinta tsaf sai zanga ‘kamshi take, tayi kyau kuma sosai kamar ba ita ya tarar wata iri d’azun ba. Murmushi ta sakar masa tana bashi side hug “Haba my Habibi afuwa mana kada mu shiga flight kana had’e min rai a zata auren dole aka yi mana.” Bai yi mata magana ba yaja trolley d’inta d’aya ya fice. Don haka dole ta bi bayansa da sauri tana kulle part d’inta. Har ya wuce part d’in Shatu sai ya jiyo ya kalli ‘kofar sai kuma ya saki tsaki, ya juya da sauri, yaa jin tsanarta na sake shiga zuciyarsa.


Sun shiga mota kenan ya gaya kiran Mommah ya sake shigowa wayarsa a karo na biyar, gaban sa ya sake fad’uwa duk da ya tabbatar har zuwa lokacin bata san da sakin ba, don ya san Shatun ba ta da waya. Hakan yasa dole ya d’aga kiran, murya ‘kasa yada gaisheta “Sannu isashshe kaga damar d’aga wayar kenan? Allah yasa dai ka kai min yarinya makaranta.” Da sauri yace “ Bata je ba.” Mommah cikin zafin rai tace “Saboda me?” Imran ya d’an ‘bata fuska kafin yace “Ba ta da lafiya ni kuma tafiya ta kama ni, dama ina shirin bugowa na sanar miki mun wuce da Shaheedah ita kuma a tura driver ya d’aukota kiyi ha’kuri Mommah.” Ya fad’a murya a sanyaye had’e da sauri switching wayar off, yaja motar da sauri. Da motar zai wuce airport sai ya yiwa Ammar waya yazo ya d’auki motar.

Mommah sakar baki tayi tana kallon wayar cikin tsananin takaicin Imran d’in Shatu bata da lafiya shi kuma shi da matar sa ta Gold tafiya ta kama su, bai kuma yi hankalin yada kawo min Shatu gida
ba saboda bai damu da ita ba cabd’i ai kuwa ido na idon Imran wallahi sai ya gane kuren sa.” (Allah sarki Mommah baki san ma mai gaba d’ayan Imran yayi ba.)


Ran ta a ‘bace ta ‘kwalawa Nahna kira, su suna nan basu tafi ba sai wani satin. Da sauri Nahna ta shiga. Key kawai Mommah ta mi’ka mata “kije gidan Imran ki taho da Shatu bata da lafiya.” Ganin ranta a ‘bace yasa Nahna bata ce komai ba taand kar’ba ta wuce.



Tana isa mai gadi yawas bud’e mata, ta ci sa’a ‘kofar main entrance d’in gidan ba a rufe take ba da Shatu ba zata ji bugun ba. A ‘kuryar d’aki tais sameta tana karatun suratul mulk da alamar sallahr walaha ta idar. Don sun mayar da ita kamar compulsory in dai kai jinin Hajiya Mama ne. Shatu ta sakar mata murmushin da zamu iya kiransa na ya’ke kafin tace sannu da zuwa Anty Nahna, idanunta na zubar da hawaye duk da ‘ko’karin ‘boyesu da take. Nahna cikin tausayinta ta zauna a gefenta tana dafa ta “wani ciwo nea yasa idanunki suka yi haka Shatu kin gasan idon ki kuwa?” Shatu ta lumshe idanunta tana jin azabar suyar da zuciyarta take kafin tace.....

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-29


Elegant Online Writers.....
“Wani ciwo ne yasa idanunki suka yi haka Shatu? Kin ga kuwa idanunki?” Nahna ta sake maimaita mata tambayar a karo na biyu, ganin Shatun ta runtse idanunta tana kwararar hawaye Ta ‘ki magana. Hankalin Nahna a tashe ta dafa ta “kiyi magana nace mai ya same ki?” “Wani abu yayi miki?” Girgiza kai tayi ta mi’ke, gaban dressing mirror taje ta d’auko ba’kar takardar sakin ta mi’ka mata, sannan ta sake zubewa a gabanta tana kuka.
Hankalin Nahna ne yayi bala’in tashi, a wani irin yanayi na fad’uwar gaba ta bud’e takardar, idanunta suka hasasho mata abinda zuciyarta take hange, ta san tabbas ba zai wuce hakan ba. “Na saki Mata ta Shatu saki d’aya.” Rintse takardar tayi a hannunta, ita kanta zuciyarta suya take hawaye na zuba a kwarmin idon ta. Tabbas Imran bai kyauta ba, ya bar musu abin fad’a a cikin dangi bata san kuma ya mutane za su kalli abin ba. Tausayin Mommah ya kama ta,mace mai son zumunci Allah ya bata d’a da ya taso da soyayyarta da son zumunci,sai dai gaba d’aya rashin tsoron Allah yasa an birkita mata shi. Kamar ba Imran d’in ta Na da ba,da ba ta saka kara ya tsallake. Ganin kukan da Shatu take, hakan yasa tayi saurin share hawayenta ta rungumeta “Kiyi ha’kuri Shatu Na san mutuwar aure da ciwo amma ina son ki d’auki hakan a matsayin ‘kaddara, haka dama Allah ya tsara I ya ‘kayyadaddun kwanakin da za kiyi da auren Imran kenan, wani mahalu’ki bai isa ya juya hakan ba, hakan kuma ba yana nufin gushewar farin cikinkiba
insha Allah soon Allah zai kawo miki madadinsa ai ba shine autan maza ba. yanzu ki tashi mu tafi kuma don Allah bana son ki nunawa Mommah damuwa balle ki ‘kara sanya ta a wani yanayi, ki daure ki ‘karfafa mata gwiwa. Ko kina son wani ciwon ya kama ta?” Da sauri Shatu ta girgiza kai “Yauwa to ki nuna mata bakomai bana son ganin hawayennan a fuskarki.” Da sauri ta goge ta mi’ke ta bi bayan Nahna da sauri, tana jin abinda ya cunkushe mata a ‘kirji yana raguwa kad’an-kad’an.

Har suka shiga Mota Nahna bata sake cewa komai ba, da alama bata ta’ba shiga ‘bacin rai kamar irin na yanzu ba.
Shatu ta juya ta yiwa gidan kallon ‘karshe a matsayinta na matar aure a gidan,tuni zuciyarta ta sake karyewa ko bakomai wallahi ta tabbatarwa zuciyarta tana son Imran, amma ko son sa zai yi ajalinta a yanzu kam ta cire shi fit daga ranta. Bata muradinsa a rayuwarta kamar yarda ya tozar ta ta iya tozarci.


Suna yin parking Nahna ta sake kallonta tace “ki tabbata al’kawarin da kika d’aukar min kin cika shi kada ki sanya Mommah ‘bacin rai.” Shatu ta d’aga kai, har a zuciyarta tana fatan ta iya danne ‘bacin ran ta amma gani take abin da kamar wuya. Kafad’ar Mommah nanne wajen da take sauke duk wani ‘bacin ranta burinta yanzu ta jita jikin Mommah tana sauke mata damiyoyinta. Ta kuma sanar da ita Imran ya ‘kwace mata budurcinta sannan ya dan’kara mata saki. Amma anya kuwa zata Iya? Zuciyarta ta tambayeta da sauri ta girgiza kai “No I can’t ai da kunya wallahi ba zan iya ba.”
Suna bud’e ‘kofar main parlourn, da Anty Amarya suka fara had’a ido tana zaune ta d’ora ‘kafa d’aya kan d’aya. Nahna ta ja hannun Shatu da take ‘k’karin gaishe ta suka wuce part d’in Mommah. Anty Amarya tsaki ta ja.
Sai dai tayi farin cikin ganin Shatun don ‘kila ha’karsu ce ta cimma ruwa kamar yarda suke fata.


A zaune suka samu Mommah ran ta duk a ‘bace tun ma ba ta ji maganar sakin ba, wannan ‘bacin ran na tafiyar da yayi ya barta ne ba ta da lafiya alhali sarai ya sani. Shatu na ganinta ta ji zuciyarta ta narke duk ‘ko’karin da take na son cikawa Anty Nahna al’kawarinta hakan ya gaza cimma faruwa, tuni ta fad’a jikin Mommahn ta saki kuka mai ratsa zuciyar mai sauraro. Momma ranta a ‘bace ta shiga shafa bayanta. Cikin muryar lallashi ta fara mata magana “kiyi ha’kuri Shatu bai kyauta ba, kuma ni da ya sanar dani baki da lafiya da tuni ban tura an d’aukoki ba, tun da ni na damu dake.” Nahna ji tayi ita ma zuciyarta ta karye da sauri ta sunkuyar da kanta. Hawaye wani na bin Wani. Sai a lokacin Mommah ta lura da Nahna da take hawaye, tun kafin ta kai ga tambayarta menene? Gabanta ya yanke ya fad’i, dama dauriya take gaba d’aya ranar bata jin dad’in yanayin jikinta. Da sauri tace “Wai menene kun bar ni a cikin duhu.” Nahna a hankali ta mi’ke tare da mi’kawa Hafsa takardar, sam ba zata iya tsayawa ba, ba zata iya jure ganin Yanayin Mommah a lokacin da ta ankare da abinda yake cikin takardar ba. Tana mi’ka mata ta fice da Sauri. Hafsa ma gabanta ne ya fara dukan uku-uku hannunta na rawa ta fara ‘ko’karin mi’kawa Mommah takardar, sai dai cak da Mommah tayi bata kar’bi takardar ba yasa Hafsa kai idon ta kan Mommah, sai lokacin ta lura Mommahn a tsaye idanunta suke cak, yanayin da yake nuna ta shiga shock sosai. Da sauri Hafsa ta mi’ke tana girgizata, sai a Lokacin Mommah Ta saki ajiyar zuciya ta runtse idanunta kawai ba tare da ta ce komai ba, ko ba a fad’a ba ta san meye a cikin takardar ba ta bu’katar ‘karin bayani. Imran ya kasa bin umarninta ya saki Shatu. Ba tare da ta karanta takardar ba tace “Saki nawa ne?” Hafsa tace “‘Daya ne Mommah amma please kada ki d’aga hankalinki.” Ganin shirun da Mommah tayi yawa yasa Hafsa d’aukan wayar ta ta kira Dahda sannan ta kira Hajiya Mama duk ta sanar dasu halin da ake ciki. Hajiya Mama sakin ajiyar zuciya tayi kafin tace “Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna, ina Addar ta ku?” Hafsa cikin sauri ta kama Mommah da take shirin zubewa ‘kasa, vedio call ta shiga ta kira Hajiya Mama. Hajiya Mamar tayi mata umarni ta saka wa Mommahn wayar a kunne. Da sauri ta kara mata. Muryarta cikin nutsuwa ta fara mata magana “Rashin yarda da ‘kaddara a lokacin da ta sameka alamune na tawayar wani sashe daga cikin imanin mutum, idan masifa ta sameka kuma cewa aka yi kace Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna. Don haka ina umaratar ki da ki fad’a yanzunnan.”cikin rawar murya alamar kuka yana son cin ‘karfinta ta furta Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna Hajiya Mama Imran ya cuc...” cikin daka tsawa Hajiya Mama tace “akul kada na soma ji kada na soma jin kin yi masa baki ko kin fad’i mummunar kalma a kansa, duk uwa ta gari bata furuci akan d’anta a lokacin da ranta yake ‘bace, an fiso kiyi shiru ko kiyi musu addu’ar shiriya idan Imran ya lalace sai kin fi kowa shiga tashin hankali a rayuwa don haka tsakaninki dashi addu’a. Aure dai Allah ne yake ‘kaddarashi haka nan saki shi yake zartar dashi da so ko ba so duk wannan a hannun rabbul izzati yake, babu wani mahaluki da zai aikata abu face dama yana rubuce a cikin Kundin ‘kaddararsa, don haka ki yawaita yi masa addu’a da fatan Allah yasa hakan ya zame musu alheri gaba d’ayansu dama Allah (s.w.a)ya fad’a zaka ga kana tsananin son abu a zuciyarka baka san sharri bane a wajenka, kamar yarda zaka ‘ki abu tsananin ‘kiyayya ba ka san alheri bane a wajenka shi yasa a koda yaushe ake son mi’ka lamari ga ubangiji fiye da za’bin rai ko son zuciya.” Zuciyar Mommah ta d’an huce daga kumburin fushin da take sai dai hakan bai hana ta furta “Hajiya Mama a karo na ba adadi mutanennan suna samun nasara a kaina wannan karan ma sune da nasara a kaina. Ni na tabbata ba haka suka bar Imran ba.” Cikin tsananin fushi Hajiya Mama tace “Baki yarda da abinda nace miki ba kenan? Baki yarda Allah ke hukuntawa ba saboda kin saka a ranki zasu iya yi miki abinda Allah bai miki ba, ki cire wannan tunanin a ranki ki kama Allah, duk abinda ya samu bawa ko zai sameshi daga gareshi yake, idan ma su d’inne to muje a cewar sun ci Nasara a duniya to ki kwana da sanin cewa fad’uwa da madawwamiyar asara ta tabbata a garesu ranar al’kiyama. Bana son ki sanya damuwa a ranki har tayi tasiri a lafiyarki. Kiyi ha’kuri mai ha’kuri yana tare da samu, ita kanta ‘yar taki idan ta ganki cikin damuwa zaki raunatar da zuciyarta, alhali ke ake so ki ‘karfafa mata gwiwa.”

Sosai zuciyar Mommah tayi sanyi daga tu’ku’kin ba’kin cikin da take, tabbas duk wanda ya rasa mahaifiya yayi kuka. Ta d’aga mata kai alamar ta aminta da duk abinda tace “Yauwa Allah yayi miki albarka ki tashi kiyi sallah kiyi addu’a Allah yasa mu dace. Su Nahna kuma suyi shirin tahowa don sun kusa komawa makaranta.” Mommah tace “To insha Allah.” Ta fad’a tana sakin ajiyar zuciya bayan ta kashe wayar, tabbas ta samu rangwame sosai kashi talatin cikin d’ari tuni ya zagwanye ta d’ora hannunta bayan Shatu da take kwance lamo a jikinta. Ta windownta ta ga alamar giftawar mutum ta tabbatar la’be aka yi mata. Ta saki murmushi a zuciyarta tace kuyi murna kuyi farin ciki a karo na barkatai burinku ya sake cika.


Kamar yarda tayi hasashe kuwa Zainab ce jikin windown ta kuma ji duk abinda yake wanka na, don tsananin farin ciki har rawa da juyi tayi a cikin parlournta burinta ya cika wannan karon ma suke da nasara. A fili ta furta haba Dijah muje zuwa ni daku d’an halak ka fasa in dai ina da Shuwa ai na tabbata bani ba kuka. Yarda na zauna da ba’kin cikin ki shekara da shekaru kema yanzu zaki fara d’and’ana nawa. Don Imran dai haihuwarsa kawai kika yi sai na dawo ni nake iko dashi kamar ra’kumi da akala.
Ta sake lalubar numberr Shuwa wannan karan ma dai switch off da alama har zuwa lokacin bata isa wajen mutumin ba. Tsaki ta ja labari take son bata amma ba dama. Ta juya akalar kirannata a layin Shaheedah ita ma still switch off. Kawai sai ta dangwarar da wayar tana sakin dariya.sai muce Allah ya shirya.


Dahda kuwa hankalinsa a tashe ya baro office ya taho gidan jin wannan tashin hankali, shi kansa ya tausayawa Dijah a yanayin da ya ganta. Sam Imran bai kyauta ba wallahi gashi yayi ta kiran wayarsa a kashe burinsa dama yaji idan da damar sulhuntawa a sulhunta tun kafin labari ya baza dangi. Shi kansa yaga wautar Imran da ya saki Shatu yarinya son kowa ‘kin wanda ya rasa. Rashin samun wayar yasa ya taho gidan jikinsa a salu’be.

A parlour ya tarar dasu kan kujera, har Shatu da take kwance kanta a saman cinyar Mommahn, ita kad’ai ta san azabar da take cinta a ‘kar’kashinta sai dai ba damar furtawa. Ina kunya ba zata barta furtawar ba don haka take ta nu’ku-nu’ku da abinta, su kuma zatonsu duk damuwar sakin da aka yi mata ce. Dahda yayi sallama ya shigo wanda ya sa Shatu saurin mi’kewa, Dahda ya kai dubansa kanta tausayinta gaba d’aya ya sake rufeshi. Ta gaida shi ya amsa cikin kulawa. Tare da shiga ciki yana duban Mommah “Muje ina son ganin Ki.” Mommah ta mi’ke ta bi bayansa bayan ya shige bedroom d’inta. Tana shiga ta saki ‘yan ragowar hawayen da take ta ‘ko’karin dannewa. “Kaji abinda d’anka yayi min ko?” Dahda ya saki d’an murmushin da bai kai zuci ba. “Shine abinda yasa kike ‘bata ranki a banza, shin sakin ba d’aya bane? Idan kuwa haka ne ai Kin ga za’a iya mayar da auren kafin ma wani yaji.” Wani kallo Mommah tayi masa kafin ta saki murmushi mai ciwo tace “Ai Dahda ko Imran ne autan maza a duniya Shatu ba zata sake komawa aurensa ba, anyi an gama kenan wallahi.” Dahda ya girgiza kai “kada kice haka Dija na ba’a yiwa aure wannan cin alwashin baki san abinda Allah zai zaratar ana gaba ba.” Ranta ne ya sake ‘baci “Don Allah Dahda mu bar wannan maganar ni ko zancen Imran ma a yanzu bana son ji, aure kuma tsakaninsa da Shatu ko bayan raina na haramta masa shi har abada kuwa, kuma daga yanzu na kulle wannan chapterr Shatu karatu zata cigaba da yi har zuwa sanda zata siyawa kanta ‘kima da mutunci a gurin kowa, a daina kallonta a matsayin fulanin daji bagidajiya har ayi mata sakin wula’kanci, farin ciki na d’aya da bai riga ya d’ebe mata albarkatun jiki ba, bai kuma kawar mata da budurci ba da ya cuce ni

1 Comments On ME ZANYI DA ITA
avatar
hafsat-bello

12 months ago

Reply

Complete

Please Login or Register in order to submit comment