Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka zakaji dadi kaji matarka da wani qato tana ihu tana Kiran a taimaka Mata dadi zai kasheta dadin ubanka wannan jemammiyar fatar har wani gardi zatayi saidai santsin quruciya sakarai kawai"



Haushi ne ya cika Lameer yace “to waima labe tayi mana ne?" Da sauri Hajiya tace “Eh labe tayi tana zaman zamanta ta taso ta hauro tajiyoku kuna bawa sama hayaqi ni har kunya naji da tana fadamin yanzu ma sai kuka takeyi saika saki wannan yarinyar wai ta rabaka da ita baka ko son ganinta"🤣

Tabe baki yayi yace “tunda kin zama yar aikenta kice Mata bazan sakiba sai naji kan Bindiga a maqoshina, da jibi ma zamu wucce amma yanzu dole sai anyi suna" dakinsa ya shiga ya fito da kudi yabata yace “gashinan kikai mata suyi duk abinda ya dace"..............



Download>>> Kwarata Complete Document



Hauwah ce tace “Hajiya zanzo inga jaririn" harara ta watsa mata tace tunda uwarki ta haifa mata ai saikizo ki gani shegiya me qirar samudawa..." Daga mata hannu yayi yace “ya isa haka don Allah kada ki dorawa yarinyar nan damuwa"

Juyawa tayi tace “eh ita aita dorawa wani ai komai takeyi Kaine ka daure mata gindi da anyi mgn sai kace yarinya ce Ina wata yarinya tunda har ta iya qacen kwana ta kwana da miji" shidai bai qara cewa qala ba sai Zulaiha ce tace “don Allah Hajiya kije wannan ba girmanki bane ita wacce kuke surutun nan ma akanta in kuka nutsu zakuga ba abinda ke gabanta kenan ba"



Abulle ce ta daga Mata hannu tace “kekuma rasa kunya waye yasa dake nifa wlh kawai na tsani yarinyar nan" cafewa Hajiya tayi da cewa “ni dama bantaba son mayyar yarinyar nan ba dandai kawai Alh yafi qarfi nane qur'anin Allah da sai ya saketa"

Murmushin takaici yayi ya kalli Hauwah da itama ta kalleshi da sauri idonta ya ceko da qwallah ya kamota jikinsa ya rungumeta yana shafa bayanta yace “saidai hqr kuma ba ke Zainab wlh ki fita daga harkar matata kada kema kijawa kanki raini"



Daga haka bai qara cewa komai ba ya mayar da hankalinsa wa wasa da gashin Hauwah ita kuma tayi luf a jikinsa tana lumshe ido ganin daga ita harshi babu me kulasu ne yasasu fucewa daga part din yayi ajiyar zuciya yace.

“don Allah ki meye zasuyi miki kada ki kilasu kinga duk sun haifeki kina kulasu zaace kinyi musu rashin kunya musammam Hajiya" gyara kwanciyarta tayi a jikinsa tace “toni kuma Ina ruwana dasu nifa na fahimci ma duk danginka Aunty Zulaiha kawai ke Sona saboda haka Nima nasan zaman da zanyi dasu Allah babu ruwana da kowa sai Alhajinka sai Aunty Zulaiha kuma ko gdanku bazanke zuwa ba"



Shafa qirjinta yayi yace “amma ni ai da ruwanki dani ko?" Zabura tayi ta tashi zaune da sauri tana cije lebe tace “ai kaikam sai mun tsaya hisabi gaban Allah na muguntar da kayimin kawai dan nace maka inason baby sai kazo ka sakamin wannan abin naka har maqoshina najishi bansan sanda na mutu na dawo ba"

Sumsumsum Zulaiha ta juya ta fice musu daga parlourn ta shiga kitchen din Hauwan ta fara hada musu abincin rana tunda tasan yanda take rakin nan yana biye mata ba abin arziqi zasu tsinana ba ga kuma baqi anatayi tasani sarai duk wanda yazo barka yaji sunanan zaice zaizo bangaren amarya to ga kuma amarya ta gamu da aikin maza ko tafiyar ma ita bata gwadawa daukar abarsa yakeyi duk inda zata.



Ranar gidan yini yayi da mutane shima Muneef anan ya yini dauke da boyayyen dansa yana qare masa kallo yanajin dama ace dansane na sunnah, gefe kuma yanata fakon fitowar Hauwah amma shiru gashi jiya yayan nasa yayi masa tsakani da bangarenta yace tunda tasu batazo dayaba to ya daina zuwa inda take.

Hakanan ya yini sukuku babu wani kuzari a jikinsa har zuwa yamma da ya gaji da jiran tsammani ya tafi.

Itakuwa Zulaiha tayi guri tanacan sunata hirarsu da Hauwah tanata kwasar dariya labari take bata na abinda ya hadasu da mubaraka tayi mata duka har tsautsayi yasa tace “itama saiya bata baby"



Download>>> Matar Makaho Complete Document



Dariya sosai takeyi tace “kedai bazaki rabu da quruciya ba Aunty Hauwah dake waye yace miki da sauqi ake samun baby ai san ansha wuya gurin haihuwar ma jidali ne abuda kake kusan mutuwa qafarka daya a lahira daya a duniya"

Cikin tsoro tace “nashiga uku na irin wahalar da nasha jiya kenan?" Dariya tayi tace “tabdi yarinya ai ta jiya shafar mai ce yanzu kinga kin gamashan wahalar wannan sauranki dadinsa shima kwananan Zaki fara kwasheshi anayi kina cewa ohhhhh babe qara yi da qarfi dadi Babe" kunyace ta kamata ta rufe idonta tace.



“Kayyy Allah Aunty Zulaiha babu dadi fah nikam bama zaa qara ba banaso ya riqe kayansa" murmushi tayi tace “aa baza ayi hakaba ki more amarcinki yarinya kiji dadinki da mijinki" wasu tarkace ta hada mata ta bata tace “bari na hada miki wadannan kisha Zaki dainajin zafin gurin zai washe yanzu"

Kofi ta dauko da nono a freegde ta zuba maganin a ciki ta karkada tabata tace “ki shanyeshi sannan ki sha wannan tsumin zakiji dadin jikinki sosai" shashashar ku ta bude ciki ta dirke magani tas ta koma ta zauna sukaci gaba da hirarsu.



Sai biyar mijin Zulaiha yazo ya dauketa sukayi sallama Hauwah me hannun kyauta turarukan da malamarta ta hada Mata ta bata cikin wadanda ta taho dasu sukayi sallama akan sai jibi zata dawo, sai lkcn ta samu damar sauka qasan Lameer na zaune a parlourn qasan yanata yiwa Fadwah wasa yaga fitowarta ya zuba mata ido yana mata murmushi.

Itakam qasa tayi da kanta Fadwah ta zame ta nufota ta washe baki tace “babena nayi missing naki bakije mun gaisaba yau" kwanciya yarinyar tayi a kafadarta shikuma ya janyota ta fado jikinsa ya sauke numfashi yace “kinyi kyau fiye da kullum babe sperm dina ya karbeki Allah yabani ikon bakishi kullum Allah yasa ke bazamu samu matsala dakeba"



Janyewa tayi a jikinsa ta dosana mazaunanta a kujerar tace “tabdi qatuwar matsala ma ai wlh ka dameni guduwa zanyi danma dai Aunty Zulaiha tace daga na jiya an dainajin zafi yanzu saura dadi"

Mubaraka dake zaune ta hadiyi wani baqin ciki shikuwa gogan ya sake matsowa jikinta yace “ni dama dadi naji wai ashe har ihu na rinqayi Ina Kiran dadi zai kasheni oh su gulma anyi asara kuma kinsan ashe Hajiya na taji sanda nake ihun dadi gsky Babe na keta dabance" miqewa tayi a qufule tace “eh naji Lameer ai and dade ana ruwa qasa na shanyewa ba yau ka bara zalumtata ba ba yau ka fara cin amanata ba ince har Mata kake ajiyewa a garin da kake ko an fada maka bansani bane"



Ko kallonta baiyi ba ya dauke Fadwah ya sauketa a qasa yace “jeki kwanta Luvly" miqar da Hauwah yayi yace “muje ki tayani nayi wanka muyi sallah mu dora daga inda muka tsaya"Kama hannunta yayi suka shige suka barta tsaye da sakakken baki.

Zama tayi a kujerar dabas tana kallon jaririn hannunta tsoronta na qaruwa tunda ta haihu bayan daukar da yayiwa yaron a asibiti baiko qara kallonsa ba ko dazu data miqa masashi cewa yayi ta kwantar dashi, tsoronta yana qara nunkuwa a ranta tace “kardai fah ya fahimci wani abu"



Download>>> Bankada Complete Document



Shima a bangarensa ya kasa nutsuwa zuciyarsa cike take da tunane tunane tana ayyana masa abubuwa da yasa game da matar tasa da dan da ta haifa masa ya rasa meye yasa daya kalli yaron gabansa ke faduwa, ya rasa meye yasa bayajin digon son yaron a cikin zuciyarsa kamar yanda yakejin na Fadwah.

Zubewa yayi a gadon yana saqale da babensa yace “ki kwantarmin da hankali Babe bansan meye yake damuna ba na tashi da farin ciki ya rikide ya koma damuwar da bansan meye asalinta ba" shafa qirjinsa tayi a hankali tace “could down babe dama wani lkcn ana samun haka fah"



Bakinsa ya dora saman chest dinta yayi kissing nata yace “yaushe Zaki bani babyn da zanyi farin cikin zuwansa duniya inason ranar da zanganki da cikina kina zama da yan dabaru, a lkcn ne zan kaiki rugarku su Baffa suganki da jinin Kado a cikinki naga yaya zasuyi da ikon buwayi"

Shiru tayi ta lafe a jikinsa tace “inason ganin Gwaggona nasan itama tanason ganina" numfashi ya sauke yace “kin tabbata?" Daga masa kai tayi yace “ok zakije very soon amma sai mun dawo daga U.S.A da naso barinki anan zuciyata taqi nutsuwa gara duk inda nake mu kasance tare"



Miqewa yayi ya fara rage kayan jikinsa ya rage dagashi sai boxes ya kashe musu hasken dakin ya kunna lamp ya shige bargon tare da janyota jikinsa ta fara zillewa yace “don Allah kada kiyimin haka nayi miki qoqari 8 mouths kina hutawarki haba Hauwah"

Kuka ta saka masa tace “zafi fah har yanzu nakeji a gurin kuma gurin kamar ciwo dazu da naje zanyi fitsari..." Kwantar da ita kawai yayi a jikinsa yace “ok shikenan yi baccinki kawai" yanajinta tana sauke ajiyar zuciya har bacci ya dauketa yayi musu addu'a yaja musu bargo"



Shikam ba bacci yayi ba saboda wata muguwar sha'awa dake cinsa mararsa tanayi masa ciwo sosai maganin da yasha daren jiya bai sakesa ba har yanzu daqyar a daddafe asuba tayi yanayin sallah ya dawo ya rinqa lallabata da kalamai yana fada mata bazataji zafin ba.

Daqyar yayi nasarar shawo kanta ta yarda jikinta na rawa ya fara romance nata bai dauki wani lkc ba yaga ta sakar masa jiki har tana tayashi yaji dadin hakan sosai shima ya rinqa kunnata saidai ya tabbatar yakaita qarshe sannan ya fara shigarta da dabara da farko bataji zafin ba saida ya saita kansa a ciki ta qanqameshi cikin rawar jiki tace “wai.... wayyoh Lameer zaz...zafi wayyohhh Allah na........"



Download>>> Fahimta Fuska Complete Document



A hankali ya rinqa bi da ita har ta haqura ta sallama masa yaji dadinsa yadda ya kamata cikin ransa yanajin dama wannan farin cikin ya dore musu shida babensa, itakam bayan ya zare jikinsa daga nata kwanciya tayi luf a jikinsa tana mayar da numfashi yanata zuba mata ruwan albarka.

Sun huta sosai sannan ya dauketa sukayo wanka ya rinqa lallabata saboda shikam yana tsoron ta botsare masa musammam yanzu da gdan nasu yake a cike da baqi, da dabara ya jata yana janta da hira har ta saki jiki sosai dashi suka shiga kitchen suka samawa kansu abinda zasuci.



Amma fah raki yananan tunda halittane shine yake daqusheta da yaji tace “washhh" sai yace “idan kika cika qorafi komawa zanyi nafiso ki horu sosai" hakanan takeyin Shiru bacci ya dauketa a jikinsa ya dauketa cak yakaita dakinta ya kwantar da ita ya shiga nasan ya gyara ya sake cire bedsheet din da suka bata.

Da kansa ya wankeshi yanajin nishadi da soyayyarta na qaruwa a zuciyarsa ko Ina saida ya gyara Mata ya shirya ya fita zuwa qasan lkcn takwas da kwata gaisawa sukayi da kakar mubaraka da taketa binsa da kallon mamaki.



Shafa kansa yayi yace “ban fito da wuri ba Kaka inada mara lfy ne yar uwartata itama ba lfy ta isheta ba shiyasa ban samu fitowa da wuri ba" itadai tsohuwa batace komai ba saboda ba huruminta bane dama Mubaraka ce ta dameta da mitar yanacan yana shan soyayya da matarsa ya manta dasu.

Shassheqar kukan da Lameer yaji a can qarshen gadon yasashi juyawa ya kalleta ya haura gadon ya karbi Muftahu a hannunta ya zuba masa ido gabansa na faduwa yace “bansan meye yake damunki ba kinsa kishi a ranki wanda idan kikayi wasa zai zama sanadin rabaki da duk wani walwala naki"



Ajiyar zuciya tayi tace “dama dolene kake daukata mahaukaciya mana dolene kake daukata bansan abinda nakeyi ba"

Shidai bai bari mgnr tayi qarfi ba ya tashi ya fice yace “zance gurin wani me magani a Doguwa don Allah ki kula da Hauwah yarinya ce Koda yake nasan Zulaiha ma zatazo.

Ficewa yayi ya sake komawa bangaren Hauwah ya zauna a gefenta ya kamo hannunta yace “zanje Doguwa insha Allahu bazan dadeba magani zan karbo gurin wani mutum da Salees ya samomin lbrnsa, bata jaba tayi masa addu'ar dawowa lfy yayi kissing nata ya fice yana daga mata hannu.



Daqyar ta tashi saboda ciwon da jikinta yakeyi ta dan gyara parlourn sama sama duk da dama ya riga ya gyara ta dauki mayafinta ta yafa ta sauka qasan a wahalce tayi saa sun dawo parlourn qasa ta zauna suka gaisa da kaka Fadwah ta taho gurinta.

Daukarta tayi ta dubi Mubaraka ta gaisheta daqyar ta amsa ta miqa hannu zata dauki jaririn tayi saurin riqe abinta tace “ah haba yarinya ki jira lkcnki yazo kema ki dauki naki ai naga ya dage so yake sai yayi miki cikin Koda yake na gaba ai yariga yayi gaba banza dake"



Itadai jiddah bata iya kulata ba saboda zazzabin da takeji a jikinta sunanan zaune zaman kurame sai Hauwah da Kaka suke Dan taba Hira lkc zuwa lkc Kaka tana mamakin mugun halin jikar tata ita bataga laifin namiji ba idan yanada halin ajiye mace sama da daya ba don ya ajiye amma Mubaraka ta dauki qunci ta dorawa kanta.

Sai wajen 11:00am Hajiya ta iso gdan ita da autanta tunda taji tsayawar motarsu gabanta ya fadi, hakadai ta zauna har suka iso anata gaisawa shikuwa hankalinsa yanakan matar yayan nasa da kullum yake kwana da tunaninta.



Download>>> Kwana 24 Complete Document



Zamewa Hauwah tayi daga kujerar ta gaida Hajiya ta kalleta a qasqance tace “me kuma wannan takeyi anan?" Tabe baki Mubaraka tayi tace “uhm inaji zaman sa ido tazo" dariya Hajiya tayi Zainab tace “lallai fah sa ido to atashi abamu guri tunda ba fadar tsoho bace.

Jikin Hauwah yayi matuqar sanyi ta miqe a gajiye idanunta ya ciko da qwallah ta nufi qofar da zata shigar da ita bangarenta sukaja tsaki a tare tare da qwashewa da dariya Hajiya tace “don Allah jibi yanda take tafiya a wani tattale wai ita miji ya kwanta da ita ko uban waye baiji abinda tajiba"



Duk da haushinta da muneef yakeji Saida yaji babu dadi akan abinda akayi Mata yace “haba Hajiya kullum sai ki rinqa abu kamar wata yarinya wannan bafa girmanki bane zaki zubarwa da kanki mutunci ne a banza kisa yarinya qarama ta rainaki inama ruwanki da tsakaninta da mijinta ne wai don Allah"

Daquwa ta watsa masa tace “kaima saina sallama mata tunda duk sallamammu na haifawa duniya nifa kawai tsanar yarinyar nan a jinina take bazan taba sonta ba har abada"



Itakuwa Jiddoh dakinta ta shiga ta fada saman gadon ta fashe da kuka sosai kalaman na surukarta suka kashe Mata jiki ta rasa meye yasa kullum Hajiyan Lameer bata fadan alkhairi akanta kullum cikin jifanta da mugayen kalamai take.

Yini tayi surr a kwance zazzabinta ya tsananta har wajen magrib tana kwance, daqyar ta iya miqewa tayi sallah sannan ta dawo parlourn ta kwanta ta rufe jikinta da hijjab dinta tanajin sanyi yana ratsata bude qofarsa taji ta sauke numfashi tare da dagowa ya tako da sauri yace “lfy meye kuma Babe?" Fashewa tayi da kuka tace “tun tunda ka tafi kaina da cikina yake ciwo inajin kamar zan mutu"



A gigice yace “amma bakida lfy gidan nan cike da dangina a rasa wanda zai kirani ya fadamin" fita yayi yana masifa ya sauka qasan ransa bai taba baci irin na yau ba ya rinqa qwala musu kira yana bala'i fadi yake “saboda tsabar an rainani an mayar dani dan iska ban isa na kafa doka a gdana a bita ba to wlh anyi kadan ayimin wannan iskancin a gdana, itama fa matatace kuma sonta nake fiye da yanda kuke zato da kowa zan iya keta riga akan lamarin daya shafi Hauwah tsabar wulaqanci jiya batada lfy bata fito ba kun rinqa kirana Kuna fadamin matata munafuka ce taqi fitowa cikin dangina ayi Hira da ita, yau taji dama dama ta fito kun koreta har kuna caccaba mata magana, kuma a rasa wanda zai bita yaganemin lfyrta hardake Hajiya bayan kinsan yarinyar nan amanace a gurina to wlh bazan dauki wannan iskancin ba daga yau kada wanda ya qara takomin gidana tunda zuwa kuke domin ku rabamin kan matana kun zabi wacce kukeso a ciki, saboda haka ku dauketa ku tafi da ita bana buqata wannan din da bakwaso ni ita nakeso"



Duk wani wanda yake gurin saida cikinsa ya karta lallai ran maza ya baci yau ankai Lameer bango, miqewa sukayi sumsum suka fara ficewa bai jima ba ya dawo da gudu gudu ya haura saman ya daukota cak sai rawar sanyi takeyi ya fito da ita yasata a mota hajiya tabisa jikin motar ta Kira sunansa yayi saurin daga mata hannu yace “kiyi hqr Hajiya wlh bazan saurareki ba kece kike sabbabamin duk wani Abu da yake damuna a matsayinki na uwa kin dauki lalurata abar yayatawa a duniya kamar kaina aka fara nasani bantaba cemiki komai ba sannan kin fifita matar da take qarqashin ikona ni danki fiye dani still kina daure Mata gindi abinda takeso shi takeyi kin nuna mata banada wata daraja a gurinta haka qanne na saboda haka ki dauketa ku tafi da ita wlh a yau dai bazata kwana a gidana ba kiyi Mata daki a gidanki ki kula da ita samada wacce nakeyi mata" yana gama fadin haka ya figi motarsa a guje ya fice daga gdan...........




Yana fita asibitin su Salees ya nufa yakaita aka shiga da ita aka fara bata taimakon gaggawa cikin ikon Allah ta fara samun sauqi ranar anan suka kwana yana jinyarta tun a daren ya gama shirya musu komawarsu Lagos saboda ya fahimci sai yayi da gaske akan lamarin Mubaraka da Hajiyarsa.

Washegari sai goma aka sallameta suka tafi gida dayake sunsan tujararsa idan aka kaishi qarshe bai tarar da kowa ba hakan ya bashi damar sakewa sosai da matarsa ya rinqa bata kulawa sai washegari da yaga taji sauki sannan suka wucce Lagos.



Tunda suka koma Lagos yake riritata babu abinda ya sake shiga tsakaninsu yana maganinsa a hankali saida sukayi sati biyu sannan ya sake nemanta da kukanta da komai haka ya rinqa lallabata suka raya daren bai wani dadeba kamar karonsu na farko dana biyu gaba daya baifi minti uku ba yayi release.

Baiso hakan ba amma hakan ma yaji dadi sosai yana ganin alamun nasara haka rayuwar taci gaba da tafiya a hankali Hauwah ta fara sabawa da yanayin mijinta itama bata wani damu ba idan yazo miji idan baizoba salamun sukanyi sati biyu uku har wata wani abu bai shiga tsakaninsu ba duk ranar da zai nemeta kuwa to yini yakeyi a kwance da zazzabi da ciwon mara.



Download>>> Yar Harka Complete Document



Shekararsu daya da rabi da aure soyayya babu irin wacce bata gani a gurinsa duk wani burinsa akan iyalansa yake, zuwa lkcn daqyar Alhajinsu yasa ya komar da Mubaraka dakinta hakan yasa ta dan nutsu bata nuna zafin kishinta akan Hauwah.

Ko dawowa sukayi bata fiye shiga harkarta ba saidai habaici da take jefar mawa da Hauwan ita kuma wata nutsuwa ta shigeta bata biyewa suyi saidai tayi murmushi, Abu daya da yake damunta shine gorin da dangin mijin sukeyi Mata wai baayi kyau ayi yado ba.



Akwai lkcn da ya matsa mata sukaje gaida Hajiya ya shiga gurin Alhnsa yabarsu itama Hajiya ta tashi ta shiga kitchen saboda ita har cikin ranta bata qaunad Hauwah hakan yabawa Muneef dake zaune a gefe damar tasowa ita bata ankara dashi ba ta miqe ta cire hijjab dinta ta ajiye ta fara gogewa Hajiya kayan da take gogewa ta tashi.

Batayi aune ba saijin hannu tayi a saman qirjinta da suka qara cika suke daukar ido, bin hannun tayi da kallo gabanta ya bada wani rass ganin farar fata sabanin ta mijinta chocolate, hannunta tasa ta janye hannunsa da sauri.



Miqewa tayi shima ya miqe kafin yayi aune ta daukeshi da mari bai dago ba ta sake sauke masa wani a daya kuncin jikinta na rawa ta nunashi da yatsa daidai lkcn da Hajiya take fitowa tace “Allah ya isa tsakanina dakai dan iska fasiqi maci aman....."

Itama Marin taji an dauketa dashi daya sanyata faduwa cikin bala'i Hajiya tace “lallai kinzo birni kinci shinkafa kinsha madara har dana Zaki mara ki kalla a gabana kicewa fasiqi ubanki yayi miki...." Dagowa tayi ta zari dankwalinta daya fadi tace “au yanzu Hajiya bakiga abinda yayimin ba saini kikaga abinda nayi masa wannan zindiqin fasiqin har dane da zaayi alfahari dash....."



Dauketa taji an sakeyi da mari tana dagowa taga Muneef dinne, hannunta ta dora akanta ta rusa ihu tace “Allah ya isana wlh bazan yafe muku ba" fitowar Lameer da Alh tayi daidai da miqewarta ta zari hijjab dinta tana kuka mecin rai.

Nufota yayi da sauri ya riqota cikin tashin hankali yace “menene me sukayi miki" fadawa tayi jikinsa ta rushe da kuka me tsuma zuciya tana girgiza kai tana cewa dashi “mu tafi babe mu tafi bazan qara zuwa gidannan ba har abada wlh na tsaneshi na tsani Muneef Allah ya isana ya cuceni"



Dagota yayi cikin tashin hankali yace “me yayi miki Hauwah fadamin meye ya hadaku?" Ita dama ba isasshiyar lfy ba dan ta kusa sati tana fama da zazzabin dare da amai, nandanan numfashinta ya fara daukewa, hankalinsa fa ya tashi yayi qasa da ita yana jijjigata yana Kiran sunanta.

Itama Hajiya tsuru tayi gabanta yana faduwa don batasan asalin rigimar ba taka haye tayi shikuwa Alh kafe Muneef da ido, miqewa Lameer yayi gashin jikinsa duk sun miqe saboda tashin hankali idonsa ya kada yayi jajir ya kalli Muneef da Hajiya ya girgiza kai ya dauki matarsa ya fice da sauri.



Download>>> Maraicin Nawaff Complete Document



Asibiti yakaita suka fara bata kulawa sannan suka binciketa gwajin farko sakamako ya fito tana dauke da ciki na sati bakwai, farin ciki kamar anyi masa albishir da Aljannah nandanan ya nemi damuwarsa ya rasa abinda ya dade yana addu'ar zuwansa yazo ji yakeyi kamar baa taba samun ciki a gdansa ba.

Sai Tara na dare ta farfado Koda ta farfado da kukan ta tashi tanajan zuciya ya matsa da sauri yace “don Allah ki fadamin menene Babe wlh kinsayani cikin damuwa me Muneef yayi miki?" Kukanta ta qarawa qarfi tace “nidai kawai ka mayar dani gurin iyayena na gaji Babe nagaji da zama da zuri'ar da basa qaunata meye laifina meye aibina da mahaifiyarka bata sona laifin me nayi Mata?"...........……….



Duk yanda yaso tayi masa bayani taqi sai kuka kawai da takeyi da yayi Mata mgn hakanan ya qyaleta suka oma gda yaci gaba da tattalin ta duk wani motsinsa akan idonta baya sakaci da duk wani abu daya shafeta qauna yakewa cikin na musamman.

A wannan tsakanin ne tafiya ta taso masa zuwa Germany lkcn tana tsakiyar laulayi yaso tafiya da ita amma tayi fur tace ita bazataba ya mayar da ita kano, dolensa badon yasoba ya kawota Kano kwana biyun da yayi a part din Mubaraka ne itakam zaman doya da manja akeyi ita dashi tunda ta lura da samuwar cikin na Hauwah ta dauki kishin duniya ta dorawa cikin.



Ranar da ya bar dakinta ranar ya tafi amma saida ya nemowa Hauwah wata dattijuwa da zatake kula da ita saboda tsaro, farin ciki gurin Muneef kam baa cewa komai kura ta mutu ya huta gda ya dawo nashi.

A ranar itama Mubaraka bata kwana a gdanba gdan wani Alhnta ta kwana ta zubewa Nanny din yaran su a cewarta bikin qawarta akeyi, itadai Hauwah tana samanta tana fama da kanta bata sanin wainar da ake toyawa sosai.



A hankali ta fara fahimtar wani abu wata rana ta sauko daga saman wajen biyar na safe daga ita sai rigar bacci tunda ta fito ya kafeta da ido tare da qara lafewa a kujerar da yake kwance, itakam batama lura dashi ba ta wucce ta shiga kitchen din da niyyar dauko fresh milk saboda tashin da tayi taji cikinta kamar anyi mata yasa.

Kitchen din ta shiga hakan ya bashi damar miqewa zumbur yabi bayanta batayi aune ba kawai saijin mutum tayi a bayanta ya dora hannunsa a saman weast dinta, zabura tayi tayi baya tare da qwallah qara yayi saurin rufe mata baki ta hannunsa tare da murdawa qofar key.



Jikinta tsuma yakeyi tanaja da baya da sauri shikuma yana binta har takai qarshen kitchen din, yana wani murmushi yana lasar lebe ta wawuro wata shafceciyar wuqa tayi kansa yaja baya da

1 Comments On MATAR HARIJI
avatar
ashiru-3

11 months ago

Reply

.

Please Login or Register in order to submit comment