Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rauni murya tace, tabbas umma kinyi nasara datsa kaunar da ke tsakanina da na'eema, saidai kuma har abada ba za ki iya raba jini da ke gudana a jijiyoyi jikin'mu ba tun kafin na mallake hankali kaina nakeji wannan kazamar kalma daga bakin'ki amma kuma umma akwai abunda har izuwa yanzu da ki ka kasa amincewa da shi wanda har yanzu yake wahalar'da ke shine yarda da kaddara, in har baki manta ba kaka tasha fada miki cewa ni kainuwa ce dashen Allah, ba yanda za ki yi da ni dole ki rungume ta annabawa, domin da mugun alkaba'e ki yana tasiri akaina da yanzu bana numfashi a doron kasa.
Ciki'n fushi umma tace karya ki keyi shegiya 'yar gadon talla shayi a wannan karon ni ce mai nasara domin na raba ki da amar rabuwa ta har abada ki kuma saurara zuwa bala'e da ke jira ki.
Umma kenan ni yaa amar baya gabana koda ace ina sonshi zan iya sadaukar da soyayya da nakeyi masa ga na'eema ballantana banaso shi don haka ku je chan ku karata da shi.
Wannan karo na'eema ce tabata amsa ta hanyar cewa, haka za ki qare babu
Mashishini har abba yagaji da ke yasamu mai bakin uwa yabashi sadaka kuma ki bace mana da gani domin uwar'ki da ki ke takama da ita batanan sai ki koma inda ki kafito batare da raheela takara furta uffan ba tafice daga falon.
tana fita daga falon tanufi "part" din kaka tana tafiya tana kuka, amar da ke tsaye a "compound" yana waya da Dr kb yadago da sauri sakamako sautin kuka raheela da yasauka ciki'n kunne sa ya tsura mata idanu har ta kawo kusa da shi yana kallon'ta ta raba gefe'nsa ta wuce tashige "part" din kaka ya bi ta da kallo yana so ya tambaye ta, me take yiwa kuka sai kuma yaji tamkar an dinke masa baki.
Raheela na shiga falon taci karo da kaka zaune inda tabarta, gani yanda raheela take kuka yasa kaka cikin firgici tace ke lafiya kuka me ki keyi"?
Ciki'n shashekar kuka raheela tace zamewa nayi a "bathroom" din aunty amarya baki na yafashe, kaka tayi murmushi tace kai raheela yanzu don kin zame shine ki ke wannan barar baki, ni har nayi tunani ko hajara ce ta taba min ke.
raheela ta girgiza kai domin tasan matukar tafadawa kaka abunda yafaru yau mai rabata da umma hajara sai "Allah don haka sai ta yanke shawara da ta boyewa kaka asalin abunda umma da hajara su kayi mata.
kaka ta rarrashe ta har tadaina kuka saidai kuma lebe bakin'ta na sama ya kumbure.
*************************

WASHE GARI*****

Amar yasami iyayye sa da zance na'eema daddy da Abba sunyi matukar farin ciki'n don haka su ka hada dan karami'n "family meeting" a falon kaka "daddy, abba, mamee, aunty amarya da kuma umma hajara gaba daya su suna zaune bisa kujeri falon kaka, yayida amar, nazeer, Abdulhakeem, Abdulhaleem, da na'eema suna zaune kasa bisan "carpert" raheela ce kadai ke zaune bisa kujera kusa da kaka.
Daddy Yayi gyara murya yace hajja dama wani abin farin ciki ne yasamu yara nan amar da na'eema ne su ka hada kansu shine mu ga yadace a sanar'da ke saboda mu naso a hade su gaba daya har su abdul ayi biki'n kowa yahuta yajuya waje da nazeer yake zaune yace kai kadai yarage ka kawo mana wance ka keso, nazeer yayi murmushi da sauri raheela takara shigewa jikin kaka domin tasan itace zabi nazee kamar daga sama taji murya nazeer yana fadar......
[8:23PM, 5/18/2016] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~3⃣8⃣~

Nima "daddy nasami wance nakeso sunanta bahijja saidai ba mu gama fahimta juna ba saboda ban fi sati daya da haduwa da ita ba.
Cabdijam tashin hankali wanda ba'a sa masa rana Cikin yanayi na tashin hankali raheela da kaka su ke kallon mutane falon, tuni jikin raheela yajike sharkaf da gumi'n yayida umma hajara tsantsan farin cikin ya baiyana akan fuskar'ta abba yace ba matsala nazeer sai kabani "address" din gidan su yarinya zan yi bincike akan'ta, ciki'n jin dadi nazeer yace toh abba.
Daddy ne yafara angara da shiru da kaka tayi yafara yawa Cikin girmamawa yace hajja kinyi shiru ba ki ce komai ba"?
Ciki'n tsanani fushi kaka tace ban amince da aure zumuncin ba don haka na soke aure tsakani amar da na'eema shi ya je yanemo matar'sa a waje ita ma taje tafara lalube mijin'ta a waje duk wanda ke Cikin falon ya girgiza da jin furucin kaka musanman amar da na'eema da kuma jahanama ga "passenger" umma hajara, Abba ne yayi yunkuri neman Karin haske daga wuri'n kaka yace hajja ba mu muka hada su ba su ne suka hada kansu kaka ta zaro idanu ta masu cike da masifa tace kai Abdullahi ka kiyaye ni banaso maganar banza duka'nku a karkashin iko na ku ke kuma ba wanda ya esa ya zantarda wani hukunci batare da amincewa ta don haka ku tashi ku bace mini da gani munafuci banza da wofi duk wani munafuki, ina sane da shi a gidanan sai nayi magani shi nace ku tashi ku fice daga falon kaka takara daka masu tsawa, da sauri mamee da aunty amarya su ka fara mikewa suka fice umma hajara ma ba'a bar'ta a baya ba ta Mara musu baya zuciyar'ta cike da haushi takaici kaka yayida "daddy da Abba suka bi ayari su abdul suka fice yazamana saura amar da na'eema da suka fita haiyyaci su sai kuma raheela da ke sharar hawaye a fakace kaka tajuya waje na'eema ciki'n hargowa tace ke tsohuwar makira me ki ke jira ne da ba ki bacewa ganina ba"?
A hargitsi na'eema ta mike tafice amar ya mike kamar ragumi, kaka ta galla masa harara hade da cewa koma ka zauna tsoho algugumi mai baki biyu, ciki'n tashin hankali raheela ta tashi tafita daga falon yayida amar ya bi ta da kallo, kai....kaka tadaka masa tace daina kallon'ta in baso ka keyi na tsiyaye maka kwayar ido munafuki kawai da sauri amar ya sunkuyarda kai falon yayi shiru na tsawon dakika biyar daga bisani kaka tasoma kare masa kallo tace amar kadago idanu ka ka kalle na da kyau domin zan fi gansuwa da amsa min tambayoyi na da za kayi ciki'n faduwar gaba amar yadago, fuskar'sa kaka tacigaba da fadar yaushe kafara son na'eema"?
Yaushe ne kuma kadaina son raheela"?
shin dama chan raheela ka ke so ko na'eema"?
Ko kuma gaba daya su ka ke so"? Kuma yazame maka dole ka amsa mini wadanan tambayoyi.
Kaitsaye amar yatsince kan'shi da fadar nafara son na'eema tun kafin ta mallaki hankali kan'ta cikin mamaki kaka ta katsi masa hanzari ta hanyar cewa na'eema ko raheela"?
Ciki'n rashin damuwa Amar yace na'eema nake nufi kaka tayi kyaci ta wani girgiza kai, amar yacigaba da fadar sai kuma amsar tambayar'ki ta biyu bantaba son raheela ba asalima na tsane ta fiye da tunani kuma kema sheda ce akan haka, kaka takara harzuka ta cika fam jira take wani mai tsantsayi yatabata ta fashe, amar yace sai kuma ams...kai saurara bana bukatar jin wata amsa daga bakin'ka, badai na'eema ka keso ba kuma baka taba son raheela ba to tashi kafita, kamar jira yakeyi ya mike yafice daga falon.
Kaka ta share gumi'n da ya wanke mata fuska tasoma zance zuci shin meke faruwa da amar da kuma wannan dan banza nazeeru tabbas nasan amar yana so raheela nazeeru ma yana sonta amma kowane su ya kasa furta hakan agare ta nan take wani irin tsoro ya lullube kaka tafara addu'a domin ita kadai ce mafita agareta har raheela tashigo kaka na duniyar tunani da karfi ta girgiza kaka tadawo haiyyaci ta Cikin sanyi murya raheela tace kaka kinga yanda yaya nazee yayi min koh"?ashe dama yana da wance yakeso yaudara ta ce kawai, yakeyi. Kaka ta girgiza kai ciki'n takaici tace ae ba ke kadai aka yaudara ba raheela nima amar ya yaudare ni raheela batasan lokacin da ta kyalkyale da dariya nan take taji bacin rai da ke ranta yafita taji zuciyata wasai kamar an wanke mata da soso ta takaita dariya da ke yi tace dama chan kece ba ki fahimci hakan ba kowa yasan tsakanina da yaa Amar kiyayya ce mai zafi yabijro da wannan zance ne don kawai yabata tsakanina da yaya na'eema kuma yayi nasara don haka ina roko ki kaka da ki danne zuciyar'ki kiyi hankuri ki amince da aure su kada ki kawo kace-nace a zuri'ar ki Yaya nazee da nakeji dan sonshi a zuciyata shima yanzu naji nadaina sonshi ki amince kawai kaka kowa rai yayi yiwa dadi bai yi kamar mai shi, ba ki zuba na mujiya ki sha kallo.
har raheela tadasa aya a zanceta kaka tana yi mata kallon mamaki kasa hankuri kaka tayi saida ta furta abunda ke ranta ashe dai raheela kinfara hankali, raheela takara kyalkyalewa da dariya kaka tana taya ta daga bisani raheela tace dama ina da hankali kaka tsabar iya shege ne kawai irin na wanda yake da goyon bayan kaka irin ki kaka takai mata duka hade da cewa ja'ira anjima zan nemo iyayye naki nafada musu na amince da aure'n ciki'n tsanani jin dadi raheela ta rungume kaka.

****************
DARE******
Da misali karfe 8:30 na dare kaka ta kira daddy da Abba ka kalle su, daya bayan daya tace na amince da aure 'ya'yanku Allah yasanya alkhairi Cikin tsananin jin dadi Abba da daddy suka ce "ameen!''
Daddy yacigaba da cewa nan da wata daya za'ayi bikin su kowane su yayi azumin da iyalinsa.
Kaka tace uhh..Allah yanuna mana yayida abba da daddy" suka cigaba da tsara yanda bikin zai kasance kaka jin su kawai takeyi gani yanda ta zuba musu na mujiya yasa suka suyi mata sai da safe....

jeeddah Aliyu🌹🌹
[18/06 8:35 am] Jeeddah Aliyu🌹: [11:45PM, 5/19/2016] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN
YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~3⃣9⃣~

Raheela cikin ''uniform'' din'ta na isalamiyya tafito daga "bedroom" din kaka saboda tun lokacin da na'eema tayi musu kaura ita ma ta tattaro shirginta tadawo daki'n kaka da zama takaraso cikin falon kaka na zaune idanuta kyan bisa akwati talabiji tana kallon manara tv" raheela tace kaka na tafi isalamiyya sai lokacin kaka ta dauke, idanu ta daga talabijin din ta kalli raheela gani tana tsotsa "lollipop" yasa kaka ta galla mata harara hade da cewa ba dai hanya za ki bi kina tsotsa duniya bisa tsinke ba"?
Raheela ta kyalkyale da dariya tace kai wallahi kaka kina da abin dariya, "lollipop" ake cewa ba duniya bisa tsinke ba'' kaka ta tabe baki tace duk daya ne raheela ta juya nufi kofar fita tana fadar sai nadawo kaka tace in ki ka kuskura ki ka bi hanya kina tsotsa duniya bisa tsinke nan ni da ke.
Takara kyalkyalewa da dariya tace da na kai "gate" zan cire na yarr kaka tace da yafi miki, raheela na fitowa ta hango yaa amar a bakin kofar dakinsa yana waya kallo daya tayi masa ta kawar'da fuskarta a zuciyata tace shi wannan mutumi bashida aiki'n yi sai waya sai kace tsohuwar karuwa, da wannan zance zuci ta nufi "gate" tana kai wa gate" ta yiwa "lollipop" din bakin'ta tauna daya ta jefar'da tsinke ta bude kofa tafita.
Waya amar yakeyi amma gaba daya hankali'nsa yana wuri'n raheela a zuciya'rsa yace ita wannan ko me takeji a cikin "lollipop" !oho" yana ciki'n waya ya hango na'eema ta nufo waje'n sa fuskar'ta dauke da murmushi shima ya mayar mata martani, tun kafin takaraso ya katsi waya'r da yakeyi.
Ciki'n shagwaba tace yaa amar laifi me nayi da yau duk baka nemi ganina ba"?
Ko bakayi farin ciki da amincewa da kaka tayi na aure mu"?
Ya dan murmusa ciki'n yanayi na wanda bayaso yawan surutu yace wadanan tambayoyi duk a lokacin daya na'eema wane daga ciki zan fara amsa miki"?
Tayi wani fari da ido tamkar na wance akayiwa gyaran idanu, ita a dole sai ta burge amar tace gaba daya za ka amsa mun.
Ya tabe baki yace uhmm...na'eema kenan mu ajiye zance wadanan tambayoyi naki a gefe ki fara amsa mini nawa tambaya miyasa baki tafi isalamiyya ba"?
Na'eema ta yatsine fuska hade da cewa ni da zanyi aure me zan je dauka a isalamiyya.
Kallon mamaki amar yakeyi mata daga bisani yace wannan ba dalili bane na'eema" aure da sai nan da wata daya za'ayi ba zai zama dalili'n da zai hanaki zuwa isalamiyya ba.
Na'eema takara yatsine fuska har da wani turo baki tace banyi ra'ayi zuwa ba, amar ya tsura mata idanu daga bisani yace shikenan yanzu ina ki ka nufa"?
Ta wani langwabe kai tace zuwa nayi mu fara tsara yanda biki'n mu zai gudana, amar ya gyara tsayuwa sa yace inajinki dama cewa nayi ka tura mini kudi ta "account" dina "next week" mu tafi "Dubai" ni da umma da kuma aunty Suwaiba mu hado kayan lefe na.
Har ta dasa aya a zanceta Amar yana kallon'ta yayi dan bazawari murmushi yace ba matsala amma ki bari sai nafadawa mamee da kuma aunty amarya in har sun amince da hakan ko nawa ki ke da bukata zan tura miki.
Wani katon haushi ya turnuke na'eema sakamako sunan aunty amarya da amar ya kira da kyar tayi "controlling" baci'n ranta tasaki murmushin yake tace amma yaa amar miye fa'eda fadawa aunty amarya"?
Amar ya dubi agogon hannu sa yaga har 6:30 tayi a zuciya'rsa yace me ya tsayarda raheela har yanzu batadawo ba"?
Wani bangare na zuciyar'sa yace kai amar ina ruwan'ka da ita, kamar daga sama yaji muryar na'eema tana cewa yaa kayi shiru baka ce da ni komai ba"?
Ya lumshe idanu shi daga bisani ya bude su yace "please na'eema we'll talk about it later okey"
Na'eema tace amma kum....da sauri ya katsita ta hanyar cewa lokacin sallah yayi ki shiga gida
Batare da yajira jin ta bakinta ba yanufi "gate" yayida na'eema tabi bayan shi da kallon mamaki.
kaitaye amar yanufi masallaci yayi sallah magarib, liman yana sallamewa ko addu'a amar baiyi ba yafito daga masallaci'n sakamako wani zafi da yake ji zuciyar'sa nayi yanufi bakin titi shagon sayar'da kayan masarufi yashiga ciki'n sakin fuska mai shago ya gaida shi daga bisani yace me za'a kawo yallabai"?
Kawai amar ya tsince kan'shi da fadar sigari nakeso mai shago yace wace iri yallabai'"?
Amar yayi shiru saboda shi dama ba shan ta yakeyi ba sai in tayi masa dadi ko kuma in yana ciki'n damuwa da ya dan busa ta sai yaji sauki damuwar'sa in kanada "oris" kabani kwali'n daya ka kuma hada mini da "lighter"
Mai shago yace toh..yallabai shikenan za'a kawo"?
Kamar daga sama amar ya tsince kan'shi da cewa ka hado mini da "lollipop"
Toh..yallabai "cartoon" za'a kawo ko kuma jakka"?
Kaitsaye amar yace "cartoon" saboda yafara gajiya da tambayoyi mai shago.
Gani mai shago yajuya ciki'n shagon yasa Amar ya mayar'da hankali'nsa waje'n titi raheela ya hango ita da kawar'ta zainab za su tsallako titi hakan ne yabashi damar karewa raheela, kallo yayida kasan zuciyar'sa yake bugawa da sauri da sauri yana kuma jin wani abu yana masa yawo a jini sa murya mai shago ce ta dawo da shi daga natsuwa shi yafito da kudi daga aljihu wando "jeans" din da ke jikinsa ya mikawa mai shago kudi ya karbe kayansa yajuya.
Da sauri zainab ta zugure raheela tace ke nayi miki farin gani takarasa magana tana dariya.
Raheela tayi murmushi hade da cewa wa ki ka gane mun 'yar uwa"?
Cikin dariya Zainab tace "Hero"
Mtwww....amma Zainab ke banza ce wallahi ki karasa abunda idanu ki za su hasko miki sai yaa amar, zainab ta kyalkyale da dariya tace wai raheela yaushe za ku daina 'Yar tsama da ke da "hero"?
Ba rana "because I hate him"
Ni da za ki dauki shawara na da nace da ya aure yaya na'eema ki hada 'yan komaitsa ki a "Ghana most go" ki tare gidanshi kina musu wanke-wanke da shara.
Har Zainab ta dasa aya raheela na watsa mata harara daga bisni tace "god forbid" koda zan yi shara da wanke-wanke ba dai a gidan "hero" ba.
Amar tafiya kawai yakeyi da gangar jikinsa amma zuciyar'sa bata tare da shi jin yakeyi kamar yajuya yakara kallon fuskar raheela sai kuma yaji wata sabuwar tsanarta na kara shiga'rsa da sauri ya tura kofa yashige cikin gida "cos bayaso kara gani fuskar raheela saboda tana jefa sa cikin yanayi na kila-wa-kala.
Raheela ta tura zainab cikin gida'nsu da yake tsakani gidan su zainab da na su raheela gidaje uku ne yaraba su "oya shiga gida kice kuma ina gaida mama.
Zainab tana dariya tace yau kawata har da kora na"?
"Eh na kore ki din" saboda na fahimci rashin kirki yanaso motsawa.
Zainab tace "Allah ya huci zuciyar raheela ta yaa amar "d real hero"
Raheela taja tsoki hade da cewa Allah ya esa tsakanina da ke kuma daga yau muraba hanya da ke tana karasa zanceta tajuya fuuu..alamar tayi fushi zainab tafara kwalla mata kira raheela"raheela " please I'm sorry daina tsaya na fada miki wata magana mai dadi" gani Zainab ta biyo ta yasa ta kwasa da gudu tana kai wa kofar gida ta ban'ki "gate" tashiga gida, amar da ke tsaye a kofar dakinsa yana jiran tsanmani yadago a firgice yana kallon raheela maigadi da ke zaune bisa farar kujerar roba yace sannu da dawowa katafila sarkin aiki ki tausayawa wannan kofar mana kalle yanda tadawo duk ta dalilin ban'ka da ki keyi mata na tabbata wannan "gate" ko shekara ba zatayi ba alhaji zai chanza ta saboda gaba daya kin fitar'da ita daga haiyyaci ta.
Raheela ta ya motsa fuska tace banaso sharri baba duk mutane, da ke shigowa gidanan ta sama suke shigowa ni kadai ce nake bi ta gate"?
Maigadi, yace ke kadai ce dai mai shigowa da gudun bala'e sai kace kura ta ya biyo ki.
Wani kallo raheela ta watsawa maigadi ta juya ta shige "part" din kaka batare da ta Kalli amar da ke tsaye yana tunani mafita....
[4:36PM, 5/20/2016] Jeeddah Aliyu🌹: ￿￿🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆🍆￿￿￿

￿💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~￿4⃣0⃣~

Sai da yadauki tsawon 10 minutes" a tsaye daga bisani ya yankewa kan'shi shawara da za ta fisheshi, "part" din kaka ya nufa cikin yanayi na mutumi da ke ciki'n tsantsan damuwa yayi sallama.
Sani daraja da sallama take da yasa kaka ta amsa masa a dakile kaitsaye yanufi kujera da ke "facing din kaka ya zauna ya wani murtuke fuska, ita ma kaka ta kwabe ta ta fuska jin takeyi kamar ta rufe amar da duka sakamako dan banza haushi da yake bata.
Raheela tafito daga "bedroom ta sauya kaya zuwa "gown ta "slink material" kan'ta babu dan kwali'n tana gani amar saida gaban'ta yafadi kawai ta fuske takarasa shigowa ciki'n falon, tace da shi ina wuni yaa amar"?
Saida ya gama shan kamshi sa ya amsa mata chan kasan makoshi "lafiya qalau" daga haka raheela ta juya waje kaka tace kaka ina ki ka ajiye min 'yar karamar jakkar nan da nake saka "comb's" dina a ciki"?
Ki duba ciki "drawer" gefen gado har raheela ta juya amar yace ke in da akwai fura ki kawo min kuma kisaka kankara a ciki
raheela tajuyo tana masa kallon mamaki sakamako gani yanda ya wani lafe jikin kujera kamar ba shi bane yayi magana, a fusace kaka tace taki ta kawo maka fura ae ba ajiye ta kayi ba in har kanaso fura kaje ka bude "fridge" da kan'ka kadauka munafuki kawai mai baki biyu.
Amar ya juya ya, kalleta ya ga yanda take huci kamar za ta rufe shi da duka ya yi murmushi sannan ya fara magana "haba kaka duk wannan bacin rai na menene tsakani jiya da yau narasa gane kan'ki"?
Ae kuwa kaka takara fusata ciki'n takaici tace kai abdulrazaq kafita daga ido na, na rufe ko ubanka bai esa ya rena mini hankali ballatana kai haihuwa jiya.
Amar ya zaro idanu hade da rike baki Yace cabdijam!" lalle abin yau babban ne da baki'nki kaka ki ke, fadar abdulrazaq, kaka ta yi doguwar ajiyar zuciya kamar za ta hadiye zuciyar'ta saboda takaici'n amar" tace nace abdulrazaq uba na ne da zan ji shakku fadar sunan"?
Uhhm...Allah yabaki na mai bara ni fura na zo sha ba neman masifa ba, yajuya wurin raheela, da ke tsaye tana kallon'su ya doka mata tsawa ke dallah wuce ki je ki kawo mun aike da na yi miki tun kafin jikin'ki yafada miki''
a razane raheela tafada "kitchen" kaka ta galla masa harara hade da cewa maras zuciya kawai, amar ya tabe baki ya Mike tsaye hannaye shi, zube ciki'n aljihu wando sa, ya nufi kusa da inda kaka take zaune ya dan rankwafa kamar mai rada yace "SO tsuntsu ne kaka a yanzu tsuntsun son raheela yatashi daga kan'ta ya koma kan na'eema don haka kidaina wannan masifa taki saboda ba shi zai sa nadaina son na'eema ba ko kin manta lokacin da kambu sarauta zuciya'ta yake hannu ta wulakanci da tadinga yi min nima yanzu nasami mai sona ita ma ta je ta nemi mai sonta.
Ciki'n zafin rai kaka takai masa duka tasami shi a kafada, da sauri ta yarfe hannuta amar ya kyalkyale da dariya Keta yace, kai wannan tsohuwa akwai ki da rigima za ki kar'ya hannu ki a banza Ki janyowa 'ya'yanki aiki.
Ran kaka yakara baci masifa da bala'e ta suka kara motsawa, dai-dai lokacin da raheela tafito da ''jug a hannu ta amar ya juya waje ta yace Ke"! Ki kai min dakina kuma ki ka bari nariga ki fita falon nan sai nafasa miki baki, yana karasa zance'sa yafice.
raheela tayi narai-narai da ido kamar za ta fasa kuka tace kaka dan Allah ki shiga tsakani na da wannan baqin azzalumi, kaka ta gyara zama tace jeki ki kai masa furar in har ya cika tantiri ya tabaki yaga yankar kauna gangariya.
Ciki'n sanyi jiki raheela tafita saboda ita kam yanzu tafara tsorata da lamari yaa amar tana zuwa bakin kofar dakinsa taja tayi tsaye tana tunani yanda za tayi tashiga, dakin nasa, kamar daga sama taji murya'rsa yana fadar wai uban me ki ke jira a bakin kofa"?
a firgice tafada ciki'n daki'n jikin'ta na rawa sai kace mazari ta dire masa "jug din fura bisa "stool shi kuma sai faman harara ta yakeyi har tajuya ta nufi kofa yace ke"! Zo nan da sauri raheela tadawo yanuna mata kwali'n da ke ajiye kusa da kafafu sa ciki'n esa da takama yace dauka ki tafi da shi, jikin'ta na rawa tadauki kwali'n yaa amar wa zan kaiwa"?
Harara ya balla mata duk fadin gidanan wa ke shan "lollipop"?
Ni"! Tafada a takaice' saida ya wani ya motsa fuska yace to na ki ne kuma duk ranar'da nakara gani ki ba dan kwali' sai na yanke wannan gashi da ki ke yi wa mutane yanga da shi "understood"? a tsorace ta daga kai, oya fita ki bani wuri da sauri tafice har tana tuntube da takalmin shi ya bi ta da kallo mai cike da wuyar fassarawa.

**************************


SAURA SATI UKU*******

A wannan lokacin biki ya rage saura sati uku, alhaji Abdullah matawalle zaune ciki'n falon shi, raheela na zaune kusa da shi, sai faman buga "game" takeyi da waya'r abba nata, umma hajara tashigo fuskar'ta a murtuke na'eema na bayan'ta saida ta gallawa raheela harara, sannan ta nemi wuri ta zauna na'eema ta zauna kusa da ita ba su fi dakika biyar da zama aunty amarya tashigo ita ma wuri ta nema ta dosana duwawu ta, alhaji Abdullah ya yi gyaran murya yace dalilin da yasa na tara ku a nan inaso naji abunda ku ke da bukata na biki"?
Karaf umma tace ni babbar damuwa ta bai wuce har aure yarage saura sati uku amma har yanzu amar bai kawo lefe ba, tun lokacin da tafara magana abba yake watsa mata mugun kallo daga bisani yace ke fa hajara bakida hankali, yanzu don tsabar wauta irin naki amar ne zai kawo kayan lefe a gidanan kenan ba aure zumuncin za'ayi masa ba umma ta zaro idanu tace kutt..ae kuwa ba zata sabu ba bindinga a

Please Login or Register in order to submit comment