Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na jima ina jira zuwa wannan rana da zan kassara rayuwarki raheela, sai yau tsohon burin na yacika akanki kafin raheela tayi yunkuri bata amsa sai kawai tafito da wata kwalba tacigaba da cewa wannan "acid" ne da shi zan lalata miki jikin'ki ta yanda babu wani da namiji da zai yi sha'awa aurenki ta yanda za ki dawo abin gudu da kyama a wurin 'ya'ya maza, da sauri raheela tafara ja da baya tana zarar idanu, umma hajara na biye da ita tana kyalkyala dariya karaf taji tayi karo da mutum a bayanta a kidime ta juya sai kawai taga na'eema a tsaye fuskar'ta tafi ta umma hajara muni saboda ita har wani huce takeyi duk da haka raheela ta kankame ta ciki'n rawar murya tace yaya na'eema don Allah ki ce umma tayi hankuri kada ta watsa mini "acid" na'eema tayi mata wani mugun kallo ta ture ta daga jikin'ta fuskar'ta babu fara'a tace umma bani kwalba hannu ki da sauri umma ta bata tana juyowa ta watsawa raheela "acid" din wani masifafe zafi ya ratsa fatar jikinta tasaki gawurtace ihu a firgice ta falka tasaka hannuta tana share gumi rass....gaban'ta yafadi sakamako gani na'eema bata bisa gadon'ta da sauri ta dira kasa jikin'ta na rawa tafita daga dakin ta nufi daki'n kaka zaune tarar'da kaka bisa "pray mat" hannu ta rike da casbaha da gudu raheela takarasa waje'nta tashige jikin'ta kaka ta shafin kan'ta tasoma karanto mata addu'a tsari, saboda ta fahimci mumuna mafalki ne tayi ba'a dauki dogon lokacin ba bacci yakara awon gaba da raheela.

WASHE GARI*********
Tun misali karfe 8:20am driver yadauki hanyar abuja da na'eema suna shiga garin abuja "direct" gidan Suwaiba da ke wuse 2 ya wuce da ita batare da bata lokaci ba yajuya kaduna domin umarni da umma hajara tabashi kenan, ko hutawa na'eema batayi ba aunty Suwaiba tace tashi ku tafi ga Ramlat nan ta raka ki "hospital" din da yake aiki na'eema tabata fuska tace aunty bari na huta mana Suwaiba ta wulga mata harara hade da cewa ke fa sokowa mai nema baya hutu har sai yacima abinda yake nema tashi maza kutafi na'eema ta mike tsaye hade da saba "handbag" din'ta Ramlat ce ke driving" na'eema na zaune kusa da ita zuciya'rta cike da fargaba irin tarba da za ta samu daga wurin uban gaiya amar kaitsaye Ramlat tadanna hanci motarta a"Alliance hospital" da ke Garki inda amar yake aiki ta nufi "parking space tayi "parking" lokaci daya suka fito daga ciki'n mota Ramlat ta kalle na'eema tace kinsan "office" dinsa kuwa"?
Na'eema ta girgiza hade da cewa bansaniba, Ramlat tace "okey ba matsala bari mu tambaya kaitsaye suka nufi ciki'n "reception" gaban na'eema na duka tara-tara waje wasu nurse da ke zaune suka nufa Ramlat tace tayi musu sallama daga bisani tace dan Allah "office" din Dr Amar m. Mawatalle mu ke nema Saida suka kare musu kallo sannan daya daga ciki'n su tace "steered" za ku bi wannan hanyar za ku ga "stairs" sai ku haura za ku ga hanya ta rabo kashe biyu dama da hagu to dama za ku bi "office" na uku shine office dinshi kuma za ku ga sunan Shi a jikin "office" din Ramlat ce tayi mata godiya suka bi hanya da ta nuna musu suna esa bakin office" din suka ja birki sakamako tsayarda su da "messenger" yayi yace akwai "patients" a ciki sai ku jira har tafito dole suka koma gefe suka tsaya "tsawon 10 minutes suka dauka a tsaye daga bisani "patients" din da ke ciki yafito, da sauri na'eema ta zuge zip din bag" dinta tafito da turare boka ta shafa a jikin'ta, da sauri hankali "messenger" yadawo kansu yasoma yi musu kallo tuhuma Ramlat ta fisgo hannu na'eema suka fada ciki'n "office" din.....

{ina busy datz why ku ka daina gani "post din mijin yar uwa taa but insha Allah gobe zan kara wani post. thanks}


Jeeddah Aliyu🌹🌹
[18/06 8:35 am] Jeeddah Aliyu🌹: [12:26, 5/16/2016] Jeeddah Aliyu🌹: ￿￿￿￿🍆🍆MIJIN
'YAR UWA TAA🍆🍆🍆

￿💕love story 2016💕￿

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹￿

~￿￿3⃣5⃣~

Karaf idanu amar suka sauka bisa fuskar na'eema ciki'n baci rai ya mike tsaye yace "what's heel u are doing in my office na'ee....a hanzarce ya hadiye saura kalaman sa, sakamako tsarawa da kan'shi yayi da sauri yadafe kan shi ya koma ya zauna, ya tsurawa na'eema ido yayida ita kuma tana tsaye tana aika masa kallon kauna sai da tabbata amar yagama zuke Qamshi turare boka ta juya tafita da sauri Ramlat ta Mara mata baya amar da ke zaune ciki'n bako yanayi sai kawai ya tsince kan'shi da miqewa ya bi bayan'su{tsafi gaskiya mai shi} kallo daya za yiwa amar kagano baya ciki'n haiyyaci sa, gani yanda yafito a gigice yasanya "messenger" mikewa yace "doctor" lafiya nagan'ka a firgice"?
Ciki'n sauri amar yawuce shi batare da yabashi amsa ba tun kafin yakarasa fita daga "reception" a kofar glass" ya tsinkaye shigar su na'eema cikin mota bai kara shiga tashin hankali ba saida yaga Ramlat tafigi mota ta nufi "gate" din fita daga "hospital" din ya bi motar da kallo yajuya da sauri cikin yanayi tafiyar masu karfi yakoma "office" din'shi kawai ya tsince kan'shi da hada komaitsa shi yafito "messenger" da ke tsaye cikin tsantsan mamaki, gani Dr Amar cikin wani yanayi da ya zame masa baqo bai gama mamaki sa ba sai gani shi, yayi yafito, da "briefcase" dinshi a rataye bisa kafada sa alama da ke nuna yatashi daga aiki kenan, amar bai damu da yanayi kallo da "messenger" yakeyi masa ba yaciro "key's" daga aljihu "coat" din da ke jikinsa yacilla masa hade da cewa ka rufe mini kofa ni zan fita, yana karasa zancesa yajuya da sauri yanufi "parking space" yashiga motar'sa yafice daga "hospital"din "direct" gidan'shi yanufa yana shiga falon ya jefar'da "briefcase" hade da wayoyi sa bisa kujera ya kuma cire "coat" ita ma ya jefar'da ita saida yadawo daga shi sai "white vest" sai kuma wando da ke jikinsa, jin yayi makoshi sa yabushe "fridge" yanufa yabude yadauko gwagwani "coke" ya balle kaifa kai saida, shanye ta tass sannan ya ajiye gwagwani'n akan "fridge" shiru yayi tafara nazari abunda yake ji game da na'eema a hankali ''brain" din'shi tafara aiki nan take yafara aikawa kan'shi tambayoyi marasa amsa shin me ke faruwa da ni"?
Miyasa nakeji wani "feeling" akan na'eema"?
Me na'eema ta zo yi abuja me kuma yakawo ta office dina"?
Miyasa tun lokacin da ta tafi nake son Kara ganinta"?
!oh god what's d wrong with me" kamar wanda aka mintsina yajuya yanufi "bedroom" yana shiga yawuce "bathroom" yasakewa kan'shi "shower" tsawon lokacin yadauka ruwa na zuba a jikinsa daga bisani ya kashe, "shower" yanufi wuri'n ajiye "towel" wayam ba towel" ko daya mtsss....yaja dan karami'n tsoki ciki'n rashin damuwa ya kwashi wando sa hade da farar "vest" dinsa yafito haka nan dama wannan na daya daga ciki'n al'ada amar duk lokacin da yayi wanka da yagama "using" da "towel sai yayi "flinging da shi tsakiyar daki in kuma yakara shiga wanka yafito da wani duk lokacin da yayi amfani da "towel" kasala mayar'da shi "bathroom" yakeji shiyasa, "bathroom" din shi za ka tarar'da "towel's" sun fi goma saboda baya iya mayar'da su mazauni su kaitsaye yanufi "wardrobe" yabude yafito "black jeans" da "red shirt" yasaka yanufi katon "dressing mirror" mai dauke da tarin "turaruka birjik yadauki turare "intense man" yafashe jikinsa daga bisani ya zura kafar'sa ciki'n "red boot" ya koma falo yafada bisa kujera hade da dafe kan'shi da yayi masa nauyi kamar an doura masa buhu'n "cement" zuciyar'sa tacigaba da zaiyano masa siffar na'eema, wani irin masifafe sonta yafara shawagi da sama zuciyar'sa yayida kasa'n zuciyarsa ke ta faman azalzala shi da son raheela, ya runtsi idanu shi da karfi nan take wani sashe na zuciyar'sa ya tilassa masa ta hanyar cewa lalle ya zame maka dole kanemi na'eema domin itace magani wannan damuwa taka, batare da yajira shawara daya'n sashe na zuciyarsa ya mike zubur yadauki daya daga cikin "phones" dinsa da ya watsar bisa kujera ya danno "number" na'eema.
Tun lokacin da su na'eema suka koma gidan Aunty suwaiba su ka zube a, falon suna koro mata bayani abunda ya wakana tsakani su da amar muryar na'eema ce, takarade falon wato aunty sai yanzu nagano fa'eda da amfani da bokaye su ke da, kinga yanda yaa amar ya zuburo da sunan ya wanke min allo'na yana shaqar turare boka sai kawai yayi laushi har fa gudu sa yabiyo mu, tana karasa zanceta suka kyalkyale da dariya Suwaiba tace ae ni tun lokacin da aunty asabe ta hadani da boka duguzuu nadaina bin kowane boka in bashiba saboda aikinsa tamkar yanka wuka yake sha yanzu magani yanzu Ramlat da ke danna wayarta, sai Lokacin ta tsoma bakin'ta Cikin firar tasu domin ita kadai tasan yanayi da ta tsince zuciyar'ta ciki gaskiya momy da na'eema ba 'yar uwa ta bace da abunda zai hanani gwada tawa bajinta saboda "guy" ya hadu ba karya babban abinda yatafi da imani na "eye's" din'shi domin ko ciki'n bil'adam masu halitta irin na "eye's ball's" din'shi qalilan ne.
Tun lokacin da Ramlat tafara zuzuta kyawo halitta amar kishi ya turnuke na'eema sai faman balla mata harara takeyi ciki'n fushi da daci rai ta bude baki za tayi magana waya'rta ta, katsi mata hanzari ta hanyar yin "ringing" da sauri ta zuge "zip" din "handbag" din'ta tafito da waya gani suna amar na yawo akan "screen yasa ta zunduma ihu hade da cewa wayyo dadi aunty Suwaiba yaa amar ne ya kira da sauri aunty Suwaiba tace maza ki daga mu ji abunda ya zo da shi na'eema ta yatsine fuska tace ba zan daga ba sai naja masa "class" aunty Suwaiba taja tsoki mtwww..tace ae yanzu bakida wani aji na'eema domin aiki'n asiri ne yake sarafa miki amar don haka karkiyi wasa da dama'rki ae kuwa da sauri na'eema tayi "receiving" ta aza waya'r bisa kunne ta kashe murya kamar Tsohuwa karuwa "hello yaa amar"
Amar da ke kishigide da sauri yakoma zaune uhh...na'eema ya za ki yi min haka"?
Me nayi maka yaa amar"?
Hamm....yasauke ajiyar zuciya daga bisani ya tsince kan'shi da cewa kin tafi da zuciyata na'eema tun lokacin da idanu na suka hasko kyakyawar surar ki na nemi natsuwa da kwanciyar hankali na, narasa ki taimake dan uwa'nki domin a hali'n yanzu bana bukatar gani komai sai ke.
ciki'n hanzari na'eema ta mike tayi hanyar fita daga falon, ciki'n tsanani jin dadi tace nima ina bukata gani ka yaa Amar domin zuciyata cike take da so da kauna'rka amar yashafi sumar kan'shi yace kina ina yanzu zan zo saboda ina bukatar lokaci na warware miki dinbi son'ki da ke zuciyata"?
Ina gidan Aunty Suwaiba kanwar umma a "wuse 2 house No.6 shikenan gani nan zuwa yana karasa zance'sa yakashe waya yadauki "car key's" din shi yafice yashiga motar'sa kirar "Mercedes benz c-class" yafisge ta da karfi yanufi "gate" da gudu maigadi yafito daga dakin'shi ya bude masa "gate.
***********************
KADUNA******

Tun da asuba da raheela tayi sallah ta koma bacci bata tashi ba sai misali
karfe 8:02am, da sauri tafada "bathroom" tayi wanka agaugauce tasanya "uniform" ta dauki "school bag" din'ta tafito a falon tarar'da kaka tana saurare BBC" a 'yar karamar "radio ta raheela ta turo baki tace haba kaka shine baki tashe ni ba gashi har nayi kusan yin latti, kaka tayi murmushi hade da cewa sau nawa ina tayarda ke kina komawa bacci, raheela ta zaro ido tace shikenan bani kudi'na na "breakfast" nayi gaba kaka tace ki je daki ki dauka mana da gudu raheela takoma daki ta kuma tadawo da gudu tace nadauki 500 amma zan dawo miki da chanji Kafin kaka tabata amsa har takarasa fita daga falon bata ankara ba taji tayi karo da mutum, tana dago idanu'ta taci karo da nazeer tasaki ihu hade da cewa "oh shirt" nazeer yace "oh No" suka hada baki suka ce "oh yes" nazeer ya mika mata hannu suka tafa raheela tace yaya nazee yaukar yaushe yace da yamma amma na Lula ciki'n gari ban diro gidanan ba sai da tsakiyar dare raheela ta zaro ido hade da cewa guduwa kayi kenan"?
Nazee yayi wani yarfe hannu yace kin ji ki da wani wai guduwa abu sai, kace dan "boarding school" raheela ta kyalkyale da dariya tace amma dai batare da izzini abba ko daddy kadawo ba"?
Nazee ya tabe baki yace da izzini su nazo me zai sa nayi shigo gidanmu da tsakiyar dare ke bari na takaita miki labari ko su yaya Abdul basu san nayo kd ba.
Raheela takara zaro idanu tace cab lalle yau da kai da daddy nazee ya yatsine fuska, hade da cewa share kawai tawan nima irin na yaa Amar zanyi bazan iya cigaba da aiki a karkashin "company" raheela tace uhh..kaji da shi ni dai mutafi ka kaini "school" bisa "bike" dinka
nazee ya galla mata harara yace tun da ga "driver" ki yadawo ba to ba inda zan je a shagwabe raheela tace "please nawan wallahi yau test" nakeda kuma gashi nayi latti nazee yace mu tafi na sauke ki sarkin naci....

🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~3⃣6⃣~

Amar na esa gidan Aunty suwaiba yayi "parking" a waje "gate" ya kira na'eema yace yana kofar gida ciki'n zumudi, na'eema tadauki mayafi'nta takara feshe jikinta da hadin turare boka, sai wani bahago kallo Ramlat take aika mata duk da na'eema taga yanayi Kallon da Ramlat take watsa mata sai tayi kamar bata ganta ba tanufi kofar fita tana wani, rausaya direct" waje motar'sa tanufa tun lokacin tafito amar yake faman kallon'ta yana kuma mamaki yanda ciki'n Dan kankani lokaci sonta yayi tasiri a Cikin zuciyar'sa tana karasowa ta bude kofar mota tashiga kamshi turare ta yabugi kofufi'n hanci sa, ya lumshe idanu daga bisani yabude Su ya watsa su bisa, fuskar'ta yayida na'eema ta rikice domin idanu amar suna daya daga ciki'n halitta shi, da ke tafiya da imani 'yan mata tace ina kwana yaa amar"?
Hamm..,yasauke ajiyar zuciya hade da cewa kwana kuma na'eema ko dai bacci ki ke ji"?
Ta wani rausayar'da kai cikin sigar kissa da kisisina tace a'a amar yadago mata hannu shi yace ki kalle agogo ki ga karfe nawa, yanzu ta tsurawa agogo nashi kirar "Rolex" idanu a baiyane tace 1:11p.m amar yayi shiru yana nazari abunda zai furta sai dai bashida zabi da yawuce ya furta domin jin yakeyi in har bai furta hakan ba ruhi sa zai iya fita daga gangar jikinsa don haka ya yiwa kan'sa kiyamullaili ta hanyar cewa na'eema gani nazo gare ki yau ba'a matsayin dan uwa ba nazo gare ki ne a matsayin masoyi na'eema ina son'ki kuma in har kin amince ina son mu raya suna ma'aki {s.w.a}.
na'eema tasaki wani mushiriki murmushi na jin dadi tace na amince da kai yaa Amar dama Chan na jima jirgin son'ka yana yawo da ni kai ne ka so ka watsa mini kasa a ido, akan raheela, rass...gaban amar yafadi sakamako sunan raheela da na'eema ta kira sai kawai yatsince kan'shi cikin wani yanayi mai wuyar fassara, da kyar ya iya bude bakin'sa yace ki ajiye zance raheela a gefe "cos yanzu ke ce a gadon mulki zuciya'ta dadi yakara kashe na'eema haka su ka cigaba da fallasa asiri zuciya'rsu tsawo sati daya tayi a abuja babu abunda takeyi sai soyewa da amar.

******************

KARSHEN TIKA TIKA TIK***

Kamar yanda amar yasaba zuwa kaduna duk karshen mako hakan ce tafaru kasancewa yau juma'a karfe 12:03pm yatashi daga "office" direct gidan'shi da ke maitama ya wuce ya watsa ruwa ya chanza kayan zuwa wata tsadadiyar farar shadda galila yasaka bakar hula kubbe takalmin kafar'sa ma black" ne sai yafito tamkar sabon ango ga jikinsa na fitarda kamshi turare "natural vitality" kaitsaye yanufi "wuse 2" bai wani jima da tsayuwa ba na'eema tafito janye da 'yar karamar "trolley" din'ta da sauri amar ya balle murfi Mota yadunfare ta fuskar'sa dauke da murmushi ita ma ta mayar masa da martani hada su fari da ido ya karbi "trolley" din ya jefa a "seat" din baya ya kuma bude mata kofa tashiga ya zagaya yatayarda mota suka dauki hanyar kaduna tafiya ce akayi mai cike da firar so da kauna shiyasa suka dauki dogon lokacin kafin su eso garin kaduna, amar yadanna "horn" maigadi ya bude musu "gate" yanufi "parking" yayi parking" su ka fito daga ciki'n mota'r yayida amar ya kafe na'eema da fitinanu idanu shi, yace "sweety" ga mu a gida "Allah ya kawo mu lafiya da fatar in kinga umma ba za ki manta ni na'eema ta kada kwayar idon'ta tace matukar zan mantawa da kaina to zan iya mantawa da kai, yanzu ma don ya zama dole na shiga ciki don taga shedar nadawo lafiya ina esa mata da sakon aunty Suwaiba zan fito mu cigaba da firar mu mai sanya ni nishadi, ciki'n jin dadi amar yace shiyasa nake kara son'ki "sweety naa" bari nima na shiga na gaida mamee da kuma kaka.
Rass-rass gaban na'eema yafadi saboda tasan matukar yashiga "part" din kaka dole sai yahadu da raheela ita kuma abinda batason faruwa shi kenan saboda tagani kamar amar in yahadu da raheela asiri zai daina aiki akan'shi tafin da amar yayi mata akan fuskar shi yayi sanadiyar dawowa da ita ciki'n natsuwa ta tunani me ki ke yi "sweety naa"? tambaya da amar ya watsa mata kenan ciki'n yanayi na kwarewa da yaudara tace banaso dai-dai da "seconds" daya ka yi min na nisanta da kai yaa amar don haka ka sanar'da daddy zance aure mu kafin ka koma kaduna.
Amar ya dan murmusa yace angama sahiba taa da haka suka rabu ita ta nufi "part" din umma shi kuma yanufi "part din mamee.

********************

Da misali karfe 3:15pm achaba yasauke raheela a kofar gida yayi dai-dai da lokacin da amar yafito da motar'sa zai fita unguwa, karaf idanu shi suka sauka bisa fuskar raheela da ke sanye da "uniform" tana kachaniya fitowa da kudi daga aljihu wando ta tafito da naira dari ta mikawa dan achaba tace bani chanji cikin tsananin mamaki dan achaba yake kallon'ta yace wane irin chanji kuma, malama"?
Raheela ta galla masa harara tace chanji da kasani ko kana nufi bakasan chaji ba"?
Dan achaba yace "eh lallai yarinya kin zo da reni hankali na dauko ki tun daga "salvation" ki bani naira sannan kuma kice nabaki chanji dallah malama ki cika min kudi na raheela ta murtuke fuska tace kai kadaina yi min "shouting" ba fa abun hawa ne ba mu da a gidan'mu kawai nayi ra'ayi hawa achaba don haka kabani chanji na baka kudinka, tun lokacin da amar yaganta tasauka bisa achaba yayi "parking" yana kallon abunda ke faruwa tsakaninta da dan achaba cikin fushi da dacin rai ya balle murfi Mota yanufi waje ta fuskar'sa dauke da tsantsan kiyayya ta.....

Jeeddah Aliyu🌹🌹
[18/06 8:35 am] Jeeddah Aliyu🌹: [6:07PM, 5/18/2016] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN
'YAR UWA TAA🍆🍆

💕Love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~3⃣7⃣~

Tun kafin amar yakarasa waje su yaji muryar dan achaba yana fadar ke karki nemi ki kure mini maleji, nayi miki rashin mutunci kuma da Ki ke zance abun hawa, to uban wa yahana ki hawa abunda ku ke da, shi sai ki ka buge da hawa achaba dagani yanayi Zubi ki na 'yan aiki ne.
Raheela ta zaro idanu hade da dakawa dan achaba tsawa kai mallam karka saki ka zage ni, kuma kudi'n ba zan ba yarba in kana da karfi ka kwata, kafin dan achaba yabata amsa amar yakaraso batare da ya kalli gefen da raheela ta ke ba yaciro 1000" ya mikawa dan achaba yayida raheela ta kawar'da fuskarta taki kallon sa da sauri dan achaba ya karbe kudi amar yajuya cikin salon tafiyar sa ta kasaita, dan achaba yace yallabai chanji ka, batare da yajuyo ba yace na barmaka raheela tabi amar da kallon mamaki, a zuciya ta tace me wannan mutumi yake nufi ne naga Sai wani shan Qamshi yakeyi"?
ta tabe baki takara da cewa Chan ta matsi maka ta juya wurin dan achaba ta balla masa harara hade da cewa dallah malam ka ja rukubabe mashin dinka ka bar mana kofar gida dan achaba ya kyalkyale da dariya yace yanzu nan 'yan mata kiyi sa'a wannan balarabe yaya naki mai kama da ke saidai yafi ki hankali da natsuwa ya biyani kudi na da na gwada miki rashin mutunci mai "remote" bai jira jin ta baki raheela ba yaja babur dinsa yayi gaba.
Raheela ta turo karamar kofa tashiga ciki'n gida da shigar'ta falon kaka ta jefar'da "school bag" bisa kujera tacire rigar "uniform" ta jefar tayi saura daga ita sai "vest" kaka dai na zaune tana kallon'ta da gudu tashiga "kitchen" sai ga ta da "plate" din abinci tana tafiya tana ci kaka ta girgiza kai tace wai raheela yaushe za kiyi hankali"? ta turo baki tace me nayi"?
Kalli yanda ki ke cin abinci a tsaye kuma nasha yi miki fada kidaina wannan gudun naki na wahalar'da jini jiki amma kin ki dainawa, ta tabe baki tace shegiyar na debo kaka bakiji yanda hanji na yake tsuwa ba kaka tace ko yau kenan ba kiyi "breakfast" ba"?
Raheela ta washe hakora hade da zaunawa kusa da kaka tace kaka bana fada
Miki tara kudi nakeyi ba in lantana za ta tafi kauye na bata tasiyo mini awakai nayi kiyo, kisan tace awakai akwai arha a kauye'n su kudin da na tara za su iya siy......ke dallah dakata kaka ta taka mata birki tace miyasa bakida ta natsu raheela"? Ke kenan kullum da sabon iya shegen da za ki bullo da shi, ina murna kinfara hankali ashe sabuwar hauka nan tafe wance taci uban ta da.
Raheela ta bata fuska ta ajiye "plate" kasa tace na fahimci tun lokacin da nace banaso yaa amar ki ka dauki zafi da ni shin kaka ko kindaina sona ne"? takarasa magana'rta kamar za tayi kuka kaka tayi murmushi tace raheela sarkin rigima yau kuma rigimar akaina tasauka, ki ajiye magana'r amar a gefe saboda tuni na rufe shafi'n ta ina ki kin ga wurin ajiye awakai a gidanan'"?
Ciki zumudi raheela tace a bayan gida mana kuma ba wanda zai ce komai in har ki ka ce ke ce ki ka siya min.
Kaka taja tsoki hade da cewa banaso zance banza raheela, in karki kuskure ki kara yi min zance awakai nan sai na saba miki.
Raheela ta turo baki ta mike tsam ta tsallake "plate" din abinci tafice daga falon ta nufi "part" din'su tana shiga babba falon ta tarar'da umma hajara da na'eema a zaune suna kule-kulen makircin su dadi ya lullube raheela sakamako gani na'eema da sauri ta nufi kujera da na'eema da ke zaune tace lah''! Yaya na'eema yaushe Ki kadawo"?
Ke miye haka wannan ae dabbanci ne da dakikanci miye hadi na da ke da za ki watsa mini wannan tambaya"? na'eema takarasa zanceta hade da ture raheela tafadi kasa bakin'ta ya bugi "stool" yashe sai jini ke zuba tasaka hannuta tadafe bakin nata a tsorace tadago tafara aikawa na'eema kallon mamaki, takara sauke ganinta bisa fuskar umma taga umma na murmushin mugunta, takara dawowa da ganinta wurin na'eema, kafin tayi wani yunkuri na'eema tacigaba da cewa wannan soman tabi ne ki ka fara gani mudi'n baki fita hanyar yaa amar sai na kassara ki domin amar nawa ne ni kadai.
Raheela tasaki murmushin takaici tace haba!'' yaya na'eema yanzu akan da' namiji ki ka zabi ki watsar'da kaunar da mu ke yiwa junan mu"?
Kwarai kuwa domin nafi kaunar shi akanki nafi so na rayu da shi akanki, ke yanzu ba komai bace a wuri'na face makiyiya na'eema na dinga aya a zanceta umma hajara tafara zazzaga nata, ina gargadi Ki da babba murya ki fita hanyar amar da na'eema, in kuma ki ka ki za ki sha dibin mamaki domin rayuwarki za tadawo tamkar ta alade.
Da kyar raheela ta mike tsaye idanu'ta su ka cika da kwalla, ta kalli umma hajara ciki'n

Please Login or Register in order to submit comment