Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da zuwa mata masu neman biya bukata barka da zuwa fada boka duguzuu dan asarariya, me ke tafe da ku"?
Umma hajara ta karkace kai tafara korowa boka bayani kamar haka Allah ya taimaki dan asarariya aljana inna ta dafe maka wannan da ka ke gani 'yatace sunan ta na'eema akwai wanda takeso saidai bata gabansa domin 'yar uwa ta da suke uba daya yakeso, shine mu ka zo a taimaka mata yaro yasota in ta kuma wanchan 'yar kishiya tawa ka hada ta da baqin jini ko kare banaso ya kusance ta da suna aure so nake tadawo tamkar mujiya a ciki'n tsuntsaye tadawo abun gudu ga samari boka duguzuu ya hagame katon bakinsa mai kama da tsohuwar salaga yana dariya, sai kuma ya koma yare sa da shi kadai yasan abunda yake fada kudaje nata shawagi a bakin'sa daga bisani tsit kamar ruwa yacinye shi, ya daga hannu'shi sama sai ga bakar leda akan tafin hannu'shi ya ajiye leda a gabansa, ciki'n muryar'sa mai kama da kukan Injimi markade yadakawa na'eema tsawa ke yarinya lallai kina da sa'a, a rayuwarki domin, inna tayi miki alqawali za ta nemo miki soyayya'r amar a tsorace na'eema take kallon shi jin ya anbace suna amar al'hali su basu fada masa suna sa ba boka duguzuu yacigaba da cewa ki kwatarda hankalinki nan da dan kankani lokacin za ki aure Amar ya kwance baqar leda da Ke gabansa yaciro laya karbi wannan ya miqawa na'eema hannu'ta na rawa ta karba yace wannan ki jefa ta cikin tsohuwar rijiya wannan kuma ki sakawa raheela cikin matashi da take kwanciya sai kuma wannan turare ki shafa a jikin kayan ki, sai kije wurin amar da ya shaki kamshi sa za rikice a son'ki zai rasa kwanciyar hankali har sai ya aure ki kuma zai tsani raheela tsana Mai tsanani gaske, abu daya zai warware wannan aikin shine in har ki kayi sake amar da raheela suka kwana a daki daya daga lokacin zai daina son'ki zai kuma tsane ki fiye da tsanarda yayi yiwa Raheela sai ki kiyaye na'eema tasauke ajiyar zuciya, umma ta zuge "zip" din "handbag" dinta ta fito da duk kudi'n da ke ciki ta zube su a gaban boka domin tasan wannan shine ka'ida sa tayi godiya suka fito daga bukkar kowane su ya jike da gumi suka dauki hanyar komawa gida zukata su cike da farin ciki don gani burin su zai cika.
Raheela da Lantana na fitowa daga falon kaka, lantana ta mika mata sakon amar gashi likita yace a baki mtss......raheela taja tsoki tace dama kira da ki kace mamee nayi min kenan"?
Lantana tayi murmushi, tace shine cikin zafin rai raheela ta fisgi takarda daga hannu lantana ta warware tafara karantawa kamar haka:-banaso ki dauki maganar kaka da mahimmanci cos" zuciyata tariga tayi zurfi a son'ki a dalilin baci rai da ki ka hadasa min yasa na wuce abuja batare da nayi ma kaka sallama ba ki kula min da kanki domin kinfi komai mahimmanci a wurina.
"urs husband 2 b insha Allah Dr Amar matawalle.
Raheela taja dogon tsoki ta cukuikuiye takarda ta jefa cikin flowers......

Jeeddah Aliyu🌹🌹
[18/06 8:35 am] Jeeddah Aliyu🌹: [2:35PM, 5/9/2016] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN
'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~3⃣1⃣~

Lantana ta zaro ido hade da cewa haba uwa dakina wulakanci ba bu kyau, raheela ta yatsine fuska tace indai akan yaa amar ne wulakanci yanzu nafara sheka shi, amma Uwa dakina sai naga kamar hakan baidace ba ko ba komai likita dan uwa'nki ne don yana dan uwa'na shi zai sa na soshi"? Banaso yaa amar lantana saboda haka mu rufe "chapter" shi domin cigaba da zance'sa zai iya janyo baqin jini sa ya shafe ki, lantana takara zaro idanu tace Allah yabaki hankuri uwar dakina batare da raheela takara furta uffan ba ta riko hannu lantana tace zo muje "part" din mamee mu yi fira lantana ta tabe baki.
A gajiye na'eema tayi parking din mota a lokacin daya suka balle kofar mota'r suka fito na'eema na jan kafa suka karasa cikin gida a "bedroom" din umma suka yadda zango umma hajara ta mayar'da ganinta wurin na'eema tace kin ga yanzu mu jefa daya'r laya a rijiya sauran aikin yarage gareki na'eema tayi murmushin mugunta tace anjima da dare zan je "part din kaka na cika saura aikin sai kuma yaa amar har dakinsa, zan kai masa ziyara umma hajara ta tintsire da dariya tace da kyau 'yar albarka sai yanzu nasan nayi kyakyawa haihuwa na'eema tace ae umma kyauwo 'ya tagaji uwarta sai yanzu nagano hali'n mutane gidanan da ki keyi min kashedi akai dama kamar jira umma takeyi ta wani gyara zama ta budewa na'eema sabon shafi na tugu da kisisina daga karshe suka fito babba falon inda aunty amarya take zaune hannu'ta rike da hisnul-muslim tana dubuwa, suka fara aika mata wulakantace kallo ciki'n sanyi jikin aunty amarya tadago idanu'ta mamaki ta yakaru sakamako gani na'eema na harara ta, kasa hankuri tayi tace lafiya ku ka tsaya min akai musanman ke na'eema naga kin zo min da wani bakon al'amari saboda ita wannan in da sabo na saba da halinta"? Ta nuna umma hajara da baki cikin hargowa umma hajara tace ke sadeeya hawainiya ki ta kiyaye rama ta domin ni kurugu ce mugun kifi duk uba da yaci tuwo da ni miya yasha aunty amarya tayi murmushi hade da cewa iko Allah yau kuma haukan ya motsa to sai kiyi da wani domin ni tun da kurciya ta banyi wannan hali'n dabbobi ba, ballatana yanzu da na ajiye iyali" na'eema tayi karaf ta karbe zance ta hanyar cewa ga ki nan katuwar dabba mai abun kunya to ki jawa shegiyar 'yar ki da ta za me miki annoba kunne ta fita gonata domin bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane, tsantsan mamaki yarufe aunty amarya wai na'eema ce ta ke gaya mata haka shin me ke faruwa"?
Maganar umma hajara ne ya katsiwa aunty amarya, zance zuci da takeyi in kuma taki zan jagorance tabarbarewa rayuwata domin zan mayar'da ita abun kwatance a gari in kunne yaji gangar jiki ta tsira.
A harzuke aunty amarya ta mike tsaye tace, ba tun yau ba ki ke da wannan mumuna kudiri a ranki nagani kin tarwatsa rayuwa raheela to ta Allah ba taki ba "Allah ba zai baki sa'a ba bakar anniyar'ki kan'ki za ta koma, ke kuma na'eema wannan hanyar da ta daura ki akai ba hanyar kwarai bace domin tana so ta gurbata miki ingantaciya tarbiya da kaka tabaki, na'eema tayi mata kallon uku saura kwabo tace mahaifiya tace duk yadda taga dama tajuya akala rayuwa ta kuma duk ranar'da raheela takara yi wa umma rashin kunya,sai na rama mata akanki ke in takama ko dukanki zan iya domin anjima ana ruwa kasa tana shanyewa raheela ta jima tana ci wa mahaifiya ta mutuncin nima lokaci yayi da zan dauki famsa.
Umma hajara tace da kyau iri albarka fada mata ba ita kadai ta iya haihuwa ba nima na haifa "aunty amarya tayi murmushin tare da cewa, duk rashin kunya da raheela ta ke yiwa mahaifiya ki bata taba zagin ta ba don haka kada ki sake kurciya ta dibe ki, ki zage ni domin hakan shi zai zame miki kuskure na karshe da za ki aikata a rayuwarki.
Cikin fitsara mai cike da rashin kunya na'eema tace an zagi ki din munaf.....saura kalaman ta suka kargame a makoshi ta sakamako wawa mari da aunty amarya ta wanka mata, saida jin ta yadauke na wance gadi'n umma hajara tayi wani kukan kura tayi ciki'n aunty amarya, kamar za ta hadiye ta sai kuma taja tayi tsaye tana wani yarfe hannaye hade da durawa aunty amarya ashar gani zagin munisa yayi yawa yasa aunty amarya tashige dakinta, dole umma taja hannu na'eema suka koma inda suka fito umma hajara ta sauke ajiyar zuciya tace barni da shegiya kisan mumuke zan yi mata sai ta gwamace kida da karatu tashi maza kije dakin amar ki duba in yana nan kidawo ki shafa turare boka duguzuu, so nakeyi nafara cin uban mutane gidanan daya bayan daya na'eema tayi murmushin jin dadi ta mike tsaye tafita...
[9:09PM, 5/9/2016] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~3⃣2⃣~

Kaitsaye ta doshe kofar dakin amar ta murda handling" taji kofar a rufe tayi shiru tana nazari ina amar yashiga ne ko yana "part" din kaka ba dan ranta yaso ba ta koma "part" dinsu domin tana tsoro shiga part" din kaka saboda tasan kaka na jiraye da ita a falon tarar'da umma tana cin abinci umma ta kalle ta ciki'n kulawa tace ya akayi ne"?
Na'eema ta ya motsa fuska tace bayanan umma ta tabe baki tare da cewa shine ki kadawo maimako ki shiga "part" din fateema watakila yana chan ki san shi, da shegen nacin uwa sai kace shi kadai ne da.
Da sauri na'eema takara miqewa tsaye, tafita daga falon da sallama tashiga falon mamee da raheela na ta faman kyalkyale dariya sakamako labari da Lantana take basu domin lantana gwanace a fagge ba da dariya, mamee ta katsi dariya da takeyi ta amsawa na'eema sallama takaraso ta gaida umma ta kuma watsawa raheela mugun kallo, mamee tace ina ki ka shiga ne na'eema"?
Na'eema tayi murmushi tace na raka umma unguwa ne sai yanzu mu ka dawo tacigaba da cewa mamee ina yaa Amar naje daki'n shi naganshi a rufe"?
Mamee tace amar ya tsofa a abuja saboda nasan shi da shagen gudu tsiya, na'eema tayi shiru yayida zufa ya keto kan fuskar'ta da kyar tasamu tayi "controlling" din kan'ta tayi wani dan maraye murmushi mai kama da yake, karaf suka hada ido da raheela ta wani galla mata harara ta mike tsaye tace mamee ni zan tafi batare da tajira amsa da mamee za ta bata tafita da sauri raheela, da mamee da kuma 'yar araka yarima asha kida wato lantana suka bi bayan na'eema da kallo kowane su da abunda yake sakawa a ciki'n zuciyarsa na'eema na shiga part din su tafashe da kuka tana zuwa tafada jikin umma hajara ciki'n yanayi na tashin hankali umma tadago ta tace to akoke sarki kuka me kuma, yafaru"?
Ciki'n rashin mafita na'eema tace umma yaa amar ya koma abuja, shikenan narasa shi, da sauri umma tarufe mata baki tace maza ki tofe mugun yawu ko ta wane hali sai kin aure amar saboda haka gobe za ki dauki hanyar abuja domin aiwatarda shiri mu, na'eema ta zaro idanu tace haba umma wane irin zance ne kina nufi naje gidan yaa amar"?
Umma tayi shu'umi murmushi tace gidan Suwaiba za ki yadda zango daga nan kanemi "hospital" din da yake aiki, ki bade shi da kamshi turare boka duguzuu, sai ki koma gidan Suwaiba ki jira sakamako domin banaso kidawo batare da maganar aure ba na'eema ta share hawaye ta tasaki murmushin samu nassara tace amma umma ke bala'e ce "brain" dinki na kawo "light" lallai ya zame mini dole gobe na dauki hanyar abuja.

DARE*******

Da misali karfe 8:30pm na dare raheela da kaka na zaune a falon kaka na Jan casbaha raheela kuma na dubu "book's" din'ta saboda gobe "monday tana da "test" na physics" wayar kaka da ke ajiye bisa hannu kujera tayi "ringing" kaka ta miqa hannuta bisa kujera tadauki wayar taddana kore madani ta kara a kunne ta tace "Assalamu alaikum" amar da ke kwance bisa "three star" a hadade falon shi da ke abuja yasaki murmushi yace "Wa'alaikum sallam" ya tsohuwa mai rai karfe ina fatar kina Cikin koshin lafiya"?
Kaka tayi murmushin hade da cewa shakiyi banza ae ni banyi tsanmani magana za ta kara hada ni da kai ba, amar ya shafi murdadiya sumar'sa ya dan murmusa har "dimple" dinsa ya lotsa yace mai nema baya fushi kaka tun da ina son 'yar jikalle ki dole na shanye wulakanci ki.
Kaka tayi 'yar bazawara dariya tace tanan kuma ka bullo to dadi abin bani na kai zomo ba rataya aka bani, amar ya tabe baki yace ke ji da wannan zaurance naki ni dai bata waya naji sanyayiya muryar'ta mai sanyaya mini zuciya ko nasami sukuni, kaka taja tsoki tace ba zan bayarba amar yayi kasa da murya cikin sigar rarrashi yace haba kaka ki taimaka min mana baki ga yadda nayi "missing" din'ta ji nakeyi kamar na zama tsuntsu na zo naga "beautiful face" din'ta.
Kaka tace chan ta matsi maka kai da turanci ka domin ni bana fahimta abunda ka ke fada, Amar ya kyakyace da dariya daga bisani yace to bata waya in nagama soyewa da ita za ta fassara miki, abunda nake nufi "kaka takara kyabe baki tace kaji da shi, ta ciro wayar daga kunne ta tace ke raheela zo ki karbi waya ana so magana da ke ciki'n zumudi raheela ta taso ta karbe waya daga hannu kaka batare da ta duba sunan mai kiran nata ba domin tasan nazee ne kadai mai kiran'ta da wayar kaka ta aza wayar, bisa kunne ta tace "hellooo...nawan...

Jeeddah Aliyu🌹🌹
[18/06 8:35 am] Jeeddah Aliyu🌹: [12:51PM, 5/13/2016] Jeeddah Aliyu🌹: [8:41PM, 5/11/2016] Jeeddah Aliyu🌹: ￿￿￿￿🍆🍆🍆🍆MIJIN
'YAR UWA TAA🍆🍆￿

￿💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~3⃣3⃣~

Muryar'ta, ta daki dodo kunne amar ya wani lumshe idanu yace yaushe na zama naki"?
Rass...gaban'ta yafadi sakamako jin murya da batayi zato da tsanmani kara jin ta ba da sauri ta sauke waya daga kunne ta, ta tsurawa suna shi da ke bisa "screen" idanu daga bisani ta maida waya'r bisa kunne ta, tace lafiya malam kace kaka tabani waya"??
Amar yayi murmushi hade da gyara kwanciyar shi, yace lafiya'r kenan "baby naa" dama so nakeyi nace miki na eso lafiya
Mtss....taja tsoki tace to ni ina ruwa kaga malam kadaina yaudara kan'ka akaina domin ni bana son'ka kuma banaso kowace hulda ta hadani da kai, ran amar in yayi dubu yabaci sakamako jin furucin, raheela yasauke zazzafa ajiyar zuciya yace son'ki yariga yashiga zuciyata raheela duk bugu daya na zuciya ta hade yake da kwayar son'ki "I'm madly in love with you baby" ina roko ki da ki tausayawa rayuwata ki aure ni nayi, alqawali zan baki kulawa ta musanman wanda za yi sanadi da sona zai sami mutsugunni a zuciyar'ki.
Ummh....dadi na kai yaa amar rashin fahimta da yare hausa fa nakeyi maka magana, nace banayi" banayi" yaa amar nace bana sonka tun da ba'a tare muka zo duniya ba don me da ba za ka kyale ni ba, so ba'a dole ka hakura ka nemi mai sonka.
Runtsi idanu shi wasu hawaye masu masifar zafi da radadi suka zubo a gefen idanu shi suka sauka bisa wuya sa, yayida wani mashin yadaki zuciyar'sa da sauri yasaka hannu shi na hagu yadafe saitin da zuciyarsa,take tsananin son raheela yakara ratsa gangar jikinsa, da kyar ya tattaro sauran natsuwa sa ya kuma hada da Kafin hali'n domin shi kadai yasan hali'n da ya afka a ciki muryarsa na rawa yafara magana ina son'ki raheela amma zan bawa zuciyata hankuri ta hakura da ke amma kisani duk abunda yasame ni kece sila karo na farko da raheela ta ji tausayin amar yakamata, ta juya taga ko wane irin kallo kaka take aika mata saidai kash kaka bata wajen domin tun lokacin tabata waya tashige "bedroom" dinta tayi kasa da murya ciki'n tausasa halshe tace kayi hankuri yaa amar banaso kashiga wani hali a dalilina duk abunda nake fada maka har ciki zuciyata haka ne matukar yaya na'eema na numfashi a doron duniya na haramta a gare ka don haka ka rarrashi zuciyar'ka ta amince da yaya na'ee......"shut up" raheela yadaka mata mahaukaciya tsawa wanda ta hadasawa dodo kunne ta daukar zafi da sauri tasauke wayar daga kunne ta tasaka ta a "loudspeaker" yacigaba da magana cikin bacin rai da konar zuciya da alama ran 'yan maza yabaci kada Allah yasa ki soni raheela ni kuma nayi wa kaina alqawali kasancewa tare da ke domin ina sonki sannan kuma ko ta halin 'ka'ka sai na aure ki bakida mijin da yawuce ni amar matawalle.
Batasan lokacin da tafashe da kuka ba domin lamari amar yafara bata tsoro mutum sai kace mahaukaci bana son'ka"bana sonka yaa amar kuma har abada bazan taba son'ka ba.
Yayi murmushi takaici yace ba ki esa ba raheela wallahi baki esa kisa na zubar da hawaye na a banza yanda nayi kuka akan sonki dole ke ma sai kin zubarda hawaye ,akan sona koda ace banyi nassarawa aure ki ba sai nayi nassrawa cusa miki zazzafa soyayya ta yana karasa zance'sa ya katsi waya'r.
Raheela tayi jefa da 'yar Nokia kaka ta bugi bango ta rabu gida biyu takarkare iya karfin'ta ta kwatsama ihu wayyo na shiga uku yaa amar zai kashe ni da gudu kaka fito daga dakin'ta har tayi tuntube saura kiris tafadi ta nufi wurin raheela da ke ta faman taratsin kuka Mai hade da ihu yau tsohon iskanci ta na da ya motsa a rikice kaka tariko ta, ta kuma girgiza ta da karfi'n gaske amma hakan baisa raheela tafasa abunda takeyi ba sai ma yakara mata karfin guiwa ta bude sabon babi na bori da hargowa na rantsa bana sonka yaa amar kuma kai baka esa kasani na so ka ba mugu kawai baqin azzulumi, na gwamace Jini jikina ya tsiyaye da zuciyata ta so ka, gani haukar ba mai karewa bace yasa kaka tarufe mata baki da tafin hannuta tace ke banaso shashanci banza da wofi kina hauka ne"? da za ki dinga yi min wannan kururuwa a gida, ture hannu kaka tayi daga bakin'ta tace ki yiwa Allah da manzon'sa kaka ki shiga tsakani na da yaa amar haka kawai ina Cikin kwanciyar hankali banida matsala asalima bansan miye damuwa ba saboda bantaba shiga cikin ta ba gashi yana yunkuri katsi mini jin dadi hade da farin ciki'na.
Kaka tayi shiru tana nazari magana raheela daga bisani tace shikenan zan sam abin yi tashi ki je kwanta, raheela ta mike hade da kwashe "book's" din'ta na'eema da ke labe a bakin kofa tana saurare abunda ke wakana ta yaye "curtain" tashigo da 'yar siririya sallama kaka da raheela suka tsura mata na mujiya, daga bisani kaka ta balla mata harara tace me yashigo da ke bangare na"?
Na'eema takara sunkuyarda kanta kasa tayi shiru, kaka tacigaba da fadar burin'ki ya cika na'eema raheela tace bataso amar, amma abunda ba ki saniba yanda raheela ta haramtawa kan'ta Amar haka shima amar ya haramta gare ki, ba tun yau nasha zaunar'da ke na gargade ki akan ki fitar'da soyayya amar daga ranki domin nasan akwai wace da ke zuciyar'sa amma da yake, ke mai naci tsiya ce ki kayi kunne uwar shegu da magana ta yanzu sai ki je ki zuba ruwa a kasa ki sha saboda raheela bataso amar kuma har abada ba zan taba amincewa ayi mata aure dole don haka ga ki ga amar dabara taragewa mai shiga rijiya, kaka na karasa maganar ta tashige dakin'ta ta bar raheela da na'eema a tsaye raheela ta kawo karshen shiru nasu ta hanyar cewa, ki yi hankuri yaya na'eema komai yayi farko yana da karshe nayi miki alqawali koda baki cikin, duniya na haramta ga yaa amar don haka ki kwatarda hankalinki dole yaa amar ya aure ki. Na'eema tayi murmushin mugunta tace na gode "my lovely sister" ta riko hannu raheela suka karasa "bedroom" dinsu suna shiga raheela ta ajiye "books dinta bisa "bedside drawer" tace yaya na'eema zan shiga wanka na'eema tadaga mata kai zuciyata cike da mugun nufi akan raheela tana gani tashiga "bathroom" ta mike da sauri ta nufi gadon raheela ta cusa layya ciki'n "pillow" ta ta ajiye pillow" ta kuma bisa nata gado, ta runtsi idanu'ta kamar tafara bacci nan take tafara hango kan'ta kwance bisa kirji yaa amar yana shayar'da ita ni'emataciya soyayya......
[8:30PM, 5/13/2016] Jeeddah Aliyu🌹: ￿￿🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆🍆￿￿￿

￿💕Love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~￿3⃣4⃣￿~

Raheela na fitowa daga "bathroom" ta nufi "wardrobe" tafito da "sleeping dress" dinta sai Lokacin idanuta suka, sauka bisa fuskar na'eema da ke baccin karya, ta dan murmusa hade da cewa yaya na'eema badai har kinyi bacci ba"?
Banza tayi da ita kamar da gaske din tayi bacci raheela ta sanya 'yar karamar "night gown" dinta "light blue" ta shafe jikin'ta da hadadiya humra kasancewa'r hakan ya zame mata jiki bata iya kwanciyar batare da ta wadata jikin'ta da Qamshi, na'eema da ke kallon'ta ta kasa ido a zuciyar'ta tace shegiya mai kama da karuwa ke ba Matar aure ba, amma kullum sai kin bade jiki da humra, duk lokacin da aikin boka yayi tasiri akanki za ki yi bayani da laranci, raheela tana gama abinda takeyi ta nufi gadon na'eema ta zauna kusa da ita tasoma bubuga mata hannu hade da kira sunanta yaya na'eema kitashi mu yi magana, ciki'n dacin rai ta tashi zaune tana wani yatsine fuska, a sanyaye raheela tafara magana yaya na'eema karki saka damuwa akanki domin inaji a jikina yaa amar yayi kusan zama mallaki'n ki na'eema tayi murmushin takaici tace raheela kenan wannan hasashe ne kawai ki keyi yaa amar ya sona ke yakeso don haka na hakura da shi, saboda ba zan iya cigaba da son namiji'n da ya ke son kanwa ta.
Da sauri raheela tariko hannuta tana girgiza kai karki ki ce haka yaya na'eema nasan kinaso yaa amar so mai tsananin gaske bai kamata kiyi saurin "give up" a lokacin da yaa Amar ya fahimce ba zai taba samu na dole ya hakura ya karbi tayin soyayya ki.
Na'eema tace kidaina wahalar'da yawun bakin'ki saboda na riga na fitar'da sonshi a zuciya'ta, raheela tayi murmushi jin dadi tace da kyau yaya na'eema taa dama Chan banaso ki aure shi, saboda bashida kirki kuma ga shi mugu, na'eema tayi murmushin yake hade da cewa ki je ki kwanta raheela dare yayi sosai kuma gobe "monday" kina zuwa "school" raheela ta mike ta nufi gadon'ta zuciyar'ta fass..sakamako ta shirya da 'YAR UWA TAA batare da wani tunani ba ta gyara "pillow" ta kwanta, na'eema nagani ta kwanta bisan "pillow" tasaki ajiyar zuciya dadi ya lullube ta nan take taji zuciyata wasai sai takeji kamar ta gama auren amar.
Raheela na kwantawa bacci yayi awo gaba da ita dama akwai gajiya a jikin'ta don haka baccinta take shara ciki'n kwanciyar hankali.

ABUJA*******
Amar kwance bisa gadon sa abin duniya ya sha masa kai sai faman juyi yakeyi da "frame" mai dauke da "pic " din raheela yakara matsi "frame" din bisa kirjinsa tun lokacin da yayi waya da raheela yanemi natsu sa yarasa tabbas ina son raheela kuma ba zan iya rayuwa babu ita kuma sani da nayiwa iyayye mu ba za su amince da auren dole ba, to yanzu ina mafita"? Ya watsawa zuciyar'sa tambaya, dayan bangare na zuciyar'sa yace amar ka hakura da raheela domin ba rabo ka bace, a baiyane yace "No ba zan iya ba "cos raheela ta zama jini jikina bugun zuciya'ta haske idaniya ta "she is my whole life I can't do without her" ya runtsi idanu shi jin yakeyi tamkar yafashe da kuka sakamako zafi da radadi son raheela da ke yawon a sassa jikinsa, nan take yasoma danasani nunawa raheela kiyayya a maimako so duk yadafe kanshi da ke sarawa tamkar ana buga masa kuduma, ina sonki raheela zan iya aikata komai don na mallake ki, haka amar yacigaba da tsoki burutsu sa har barawo ya sace shi bai sami mafita ba.

KADUNA********
Tana zaune Cikin "garden" hannu ta rike da "lollipop" tana tsotsa kamar wanda aka zungura ta juya tana kallon kofar shigowa ciki'n "garden" din umma hajara tagani tsaye fuskar'ta babu annuri, suna hada ido ta watsa mata harara ita ma raheela batayi kasa da guiwa ba ta murguda mata baki, ciki'n zalla zalunci hade da mugun nufi ta nufi waje raheela tace

Please Login or Register in order to submit comment