Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunani yaudara ki zanyi kinyi kuskure raheela saboda tun kafin wadanan "ball's" din sunfara fitowa a kirji'nki nakeso'nki yanuna kirji'nta da yatsan shi, in kuma kina tunani don kyau ki nakeso'nki shima kin tafka kato kuskure saboda, akwai mata da yawa suka fiki kyau da a duniya, iya abu daya nasani raheela son'ki ina miki son da bana yiwa kaina shi ni mahaukaci ne akan son'ki don haka ina mai baki umarni ki bini a hankali domin ni mutum ne mai wuyar sha'ani zan iya ajiye son da nakeyi miki a gefe nayi miki dukan tsiya in yaso daga baya na rarrashe ki da zazzafa'r soyayya ta wannan shine salo naa sai ki kiyaye yana karasa zance'sa ya ture ta tayi tangal-tangal za ta fadi ya riko hannuta yajanyo ta da karfi saura kiriss....tafada kirjinsa sai kuma ta tsaya da kafafu'ta yasoma yi mata rikitace kallo mai cike da so da kauna na'eema da ke jingine jikin fila tayi zurun tana kallon su idanu ta na zubar'da hawaye masu masifar zafi, amar yasa hannu yarike tsinke "lollipop" din da ke bakin raheela yafisgo shi da karfi, yayida hawaye suka wankewa raheela fuska tarasa wane irin cin zarafi za ta yiwa Amar domin ta huce takaici wannan bakin ciki da yaguma mata bata ankara ba taji ya murda mata hannu runtsa idanuta tayi saida yakara mata kallon wulakanci yasake ta daga bisani yanuna mata hanya da yatsa yace oya shiga gida, ki je kiyi jinyar zuciya da gangar jikin'ki ni zan fita in nadawo zan daura miki daga inda muka tsaya kinsan ni soyayya taa mai zafi ce bana gajiya da aika sako'ni, raheela ta share hawaye da bayan hannu'ta jin takeyi kamar ta shako wuyan Amar tayi ta duka'nsa har sai masu gadi Sun kawo masa dauki saidai ina ba abunda zai yuwa bane sata lahira akawo duniya wannan shi ake kira fin karfi, gani tayi shiru sai hawaye ke zuba akan fuskar'ta yasa yadaka mata tsawa ciki'n hargowa yace dallah malama wuce ki shiga gida kinyi wani tsaye kina hawaye munafuci salon wani yaganki ace nafara cutar'ki tun kafin a daura mana aure da gudu raheela ta juya tanufi ciki'n gida na'eema nagani haka itama ta falla da gudu, Amar yabi bayan ta da kallo a baiyane yace ina son'ki baby naa" yajuya ciki'n nishadi yashiga motar'sa yaja yafice daga gidan kaitsaye ta shige "bedroom din kaka tafada bisa gado tafashe da kuka tace "I hate u yaa Amar wallahi na tsane ka ba yanda za'ayi na so ka haka kawai ina zaune lafiya da 'yar uwa taa kanaso ka haddasa gaba a tsakani mu yanzu me zai faru in yaya na'eema taji yaa Amar ni yakeso ba ita ba"?
Wani bangare na zuciyar'ta yace ke ma raheela shashasha ce ya za'ayi Amar ya so ki shin ko kin manta tun kina yarinya yaa Amar bayaso yaganki cikin farin ciki"? Yayi amfani da kalma SO" ne kawai don yasanya ki cikin 'kuncin na'eema ita ce tafi dacewa da shi domin ita yake nunawa SO sabani ke da yake nunawa baiyananiya kiyayya, lallai yaa amar dan reni "senses" ne na bugawa a jarida, amma zan nuna masa cewa kan magge yawaye......


🍆🍆MIJIN 'YAR UWA
TAA🍆🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~2⃣6⃣~

Raheela tacigaba da zance zuci gani haka ba Zai fishe ta ba yasa ta share hawaye ta, bacci yayi awo gaba da ita.
Da gudu na'eema tashiga falon tafada jikin umma hajara tafashe da kuka umma tace oh ni hajara ina zan saka kaina da wannan masifa da takunno kai a gida na to kuma yanzu me faru ki ka shigo min falon da gudu kina kuka"?
Na'eema takara fashewa da wani sabon kuka tare da cewa ki dubi girma'n Allah umma ki ceto rayuwata daga afkawa halaka umma ni kadai ki ka haifa in na mutu bakida wasu 'ya'ya da za ki kalla a matsayin ke, ki ka haifa ki taimake ni umma kar narasa yaa amar wallahi umma ina sonshi ina yi masa mahaukaci SO da zuciyarta, bata iya jure ganisa da raheela umma in har narasa yaa Amar nima za ki rasa ni domin zan sha ''poison" na kashe kaina a firgice umma hajara tadago na'eema, ta wanka mata mari tace kan'ki daya na'eema da zaki kashe kan'ki akan wani banza" to ki kwatarda hankalinki domin ni uwa ce mai son farin ciki 'yarta koda ace zan dawo yawo tsirara a gari sai na kwanto miki soyayya'r amar kuma nayi alqawali sai na tarwatsa rayuwar raheela tun tayi sanadi zubar hawaye ki yadda ki kayi kuka akan Amar ita ma sai tayi kuka akansa so nake ciwo zuciya yazamo shine, ajali'nta don haka maza share hawaye ki ciki'n tsanani jin dadi na'eema ta share hawaye tace umma yanzu ya za'ayi saboda banaso na bude idanu na nagansu tare"?
Umma hajara tayi dariya mugunta tace sha kurumin'ki na'eematu boka duguzuu shine mai magani 'ya'ya iska na'eema tayi murmushi tace da kyau umma so nakeyi raheela tagano cewa tayi babba kuskure naso abunda nakeso tagano cewa ba'a tabani a kwana lafiya Umma tace to ki bude kunne ki da kyau ki saurare huduba da zanyi miki na'eema ta gyara zama tace na bude umma wani kafiri murmushi umma tayi daga bisani tace daga yau karki kuskura ki kara shiga "side" din fateema ki kuma tataro duk wani abu da ya kasance mallaki ne ki baro bangare kaaka kidawo nan da zama inaso ki daura gaba da mutane gidanan domin ba kauna sukeyi ba kuma banaso ki kara kowace irin hulda da raheela tsakani ki da ita kiyayya ce mai zafi, na'eema tace angama umma hudubar ki ta zauna a kwakwalwa ta saboda yanzu babu saura kaunar raheela a zuciyata asalima jin nakeyi kamar na daba mata wuka a kaho zuciya umma hajara tayi murmushi jin dadi tace tashi maza ki je ki tataro kayanki na'eema ta yatsine fuska tace tun yanzu umma?
Eh mana ae ba'a bori da sanyi jiki na'eema ta mike tanufi "side"din kaka....

Jeeddah Aliyu🌹🌹
[18/06 8:33 am] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN
'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~2⃣7⃣~

Kaitsaye na'eema tashiga falon kaka, gani babu kowa a ciki yasa ta wuce "bedroom" din kaka taya tayi tsaye sakamako, hango raheela kwance tana bacci taja tsoki mtsss...a baiyane tafara magana banza munafuka maciyiya amana raheela da ke ta shara baccin ta bata masan tana yi ba na'eema jin takeyi kamar tashake raheela ta mutu kowa ya huta,cikin zafin rai ta bude "wardrobe" da karfi tasoma kwaso abinda yake mallaki ta, ta jingewa kasa, yanayi ta tamkar na mai tabin hankali karar budewar "wardrobe" ne yayi sanadiyar falkawa raheela, cikin tsananin mamaki ta ke kallon na'eema, da ta iya bude bakin'ta dalilin nauyi da yayi mata ga kuma wani masifafe ciwo kai da ke barazana, tsaga mata kai tace lafiya yaya na'eema ki ke kwashe kayanki"?
Banza tayi da ita tamkar bataji tambaya da tayi mata ba tadauko katuwar "trolley" dinta tasoma dibar kayan da ta jinge kasa tana zubawa ciki'n "trolley" da sauri raheela tasauko bisa gado ta riko hannu na'eema fuskar'ta dauke da tsantsan damuwa, tace dan Allah yaya na'eema kiyi min magana me ke faruwa ne"?
Ciki'n bacin rai na'eema ta buge mata hannu tadaka mata tsawa cikin tsabar masifa da bala'e tace dallah ki saurara min haka nan ko kina tsanmani banida masaniya dangane da zago kasa'n da ki ke yi min"?
Cikin rashin fahimta inda zance'ta yadosa raheela tace ni fa yaya na'eema kina kara jefani ciki'n rudani saboda ban fahimce manufar wannan zance naki mai kama da halshen damo ba, na'eema taja tsoki kamar za ta gutsiri halshen'ta hade da cewa kada Allah yasa ki fahimta abu daya nakeso kisani raheela banza irinki bata esa tarabani da Yaa Amar domin abin abaiyane yake duk fadin matawalle family ba wanda baida masaniya ni yaa Amar yakeso ba ke inda ma wani kulle-kulle ku ka kulla ke da munafukar uwar'ki to ta Allah bataku ba, domin ni da yaa Amar mutu karaba ne takalmin kaza nan gani nan bari dukiyar uban wani tana karasa zanceta taja "trolley" din'ta da karfi tafice daga daki'n yayida tabar raheela tsaye ciki'n wani hali, hawaye na zuba akan fuskar'ta, ta durkushe a tsakiyar daki takara fashewa da sabon kuka kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa, tasoma sabbatu, buri ka yacika yaa Amar shikenan karabani da 'YAR UWA TAA" ka hadasa gaba a tsakani mu me nayi maka yaa Amar da ka zabi wannan hanyar don ka musgunawa rayuwata"?
Jin andafa kafada ta yasa tajuya gani kaka tayi tsaye fuskar'ta dauke da damuwa da sauri ta mike tsaye tafada jikin kaka tasaki kuka mai tsuma zuciya mai karatu, ciki'n sigar rarrashi kaka take bubuga bayan'ta da kyar kaka ta rarrashe ta tadaina kuka, kaka ta zaunar'da ita a gefe gado tasoma tambaya'r ta dalilin kuka'nta raheela ta kwashe iya abunda tasani tafadawa kaka kowane su yayi shiru sai kace masu nazari daga bisani kaka tayi murmushin takaici, hade da cewa babu zance yaudara a ciki'n zance da amar yafada miki da gaske ne yana sonki raheela saidai ni kaina ina mamaki wannan halaya ta Amar iya abunda nasani kowane dan-Adam yana kokari yaga ya kyautatawa abinda yakeso sabani amar da yake munanawa abinda yakeso yana farantawa abinda bayaso rai tabbas raheela" amar yana son'ki so da shi kan'shi ba zai iya misalta shi, ba a tsorace raheela tace haba kaka miyasa wannan karo ki keso ki goyi bayan yaa amar"? duk fadin gidanan ba wanda baisan yaa amar ya tsaneni baya sona wannan al'amari a baiyane yake kaka.
Kaka tace ba tsanarki yakeyi ba raheela son'ki ya ke yi wallahi amar yana tsanani son'ki soyayya'r da amar yake miki tasamo asalin tun daga ranar da ki kazo duniya ni shadace akan haka, ki yarda da ni raheela kinsan bantaba fada miki karya ba kuma kinsan ina adawa da duk wani abu da yayi yunkuri shiga tsakani ki da farin ciki ki, amma azahari gaske inaso ki da amar domin amar yar.o ne nagari kuma kowace uwa tanaso 'yarta ta aure miji nagari shiyasa nake miki sha'awa kasancewa da amar.
Raheela ta turo baki tace wallahi kaka banaso shi na tsaneni shi don haka kifada masa ya kyale ni yaje ya rungume me sonshi, kaka tayi zugun tana kallon raheela daga bisani tace dama abinda nake yiwa amar gudun kenan tsuntsu da yaja ruwa shi ruwa kan doka wannan shiri sa ne shi, kuma yasan yadda zai gyara kayansa.
Raheela ta tabe baki hade da miqewa tsaye tace dan Allah kaka kije kidawo da na'eema ki kuma fada mata cewa ni banaso yaa amar shi kadai ne yake shirme sa.
Kaka ta galla mata harara tare da cewa ae bani nakori ta ba da zanje nadawo da ita, raheela tayi kasa da murya tace dan Allah za kije ba don halina ba kaka taja tsoki mtsss....ta mike tafita tabar ma raheela daki...


🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~2⃣8⃣~

Raheela ta mara mata baya sai faman yi mata magiya takeyi ciki'n fushi kaka tace wai ke wace irin maya yarinya ce"? Wannan rashin zuciya naki yayi yawa, to ba inda zan je don ni ba shashasha bace irin'ki in har ke damu da rashin ta sai ki tatara komaitsa ki, ki koma bangare su da zama.
Raheela ta bata fuska tace Shikenan kaka ki sha zaman ki yaa amar dai ne nace banaso shi duk mai daukar zafi da ni yayitayi ni ko a jikina, tana karasa zanceta batare da tajira jin ta bakin kaka ba taficewar'ta.
"side" din mamee tanufa a falo tarar'da mamee zaune tana kallon tashar sunnah tv raheela tayi sallama mamee ta amsa mata "direct" ta zauna kusa da mamee ta dan kwato da jikinta a jikin mamee tace wash....Allah na nagaji mamee ta tabe baki tace, da ki kayi aiki me"?
Raheela ta Yatsine fuska tace aiyuka da yawa mamee ta ture tace ke dagani banaso shiririta duk wanda aure ki yana da aiki, ciki'n shagwaba raheela tace nifa mamee danki zan aura.
mamee tayi dariya hade da cewa dadi na da ke raheela rashin kunya mu ae ba mahaukata bane da za mu hada ki aure nazeer, raheela ta tunzire baki tace wai saboda me"?
Mamee tace saboda daga ke har shin din bakuda ta natsu raheela ta tintsire da dariya tace kai mamee yanzu kallon motsatsu ki keyi mana"?
Mamee tace kwarai kuwa" raheela takara tintsirewa da dariya har tana fadawa jikin mamee, sallama amar ce takatsiwa raheela dariya da takeyi ta wani bata fuska shima batare da ya kalle ta ba ya kai zaune, mamee tace kawo maka abinci ne"?
Amar ya shafi sumar kan'shi wanda ya zame mishi dabi'a daga bisani yace banaji yunwa a koshe nake.
Raheela ta mike tsaye tace mamee na tafi sai anjima, zan dawo nayi miki gyara "wardrobe" mamee taja tsoki tace nasan halin ki raheela ni da kara ganinki sai kuma gobe ko don kin fahimci nafiso naki da na na'eema, ne shiyasa ki ke mini yawo da hankali raheela tayi dariya tace Allah mamee zan dawo mamee tace adawo lafiya raheela tafice daga falon, amar da ke lumshe da idanu kamar mai bacci ya bude idanu shi, shima ya mike tsaye hade da cewa mamee inaso kiyi min dambu nama in tafi da shi, mamee ta tabe baki tace yakamata kayiwa kan'ka fada ka ajiye iyali haka nan amar dan murmusa batare da yace da mamee komai ba yafice, raheela na fita daga falon mamee tanufi "garden" ta nemi kasan "grass carpet" ta zauna har cikin zuciya'ta tanaso taje tabawa na'eema hankuri ta kuma fada mata ita bataso'n yaa amar saidai tanaji tsoro masifar umma hajara domin kuwa tono silili Za tayi mata wanda janyo kowa yagama Jin amar yace yana sonta kuma hakan zai iya kara haifar da gagarumar matsala mtss....taja tsoki yaa amar yacuce ni, ya jefani cikin damuwa ina zaman, zama na ciki'n kwanciyar hankali ni da 'YAR UWA TAA gashi ya haddasa mana gaba ko me zai faru in na'eema tafadawa umma hajara ni yaa amar yakeso ba ita ba.
Gaskiya yaa amar mugu ne duk wa shekaru nan yasan ni yakeso miyasa yake nuna min zallah kiyayya yake kuma nunawa na'eema tsantsan so"?
Tun lokacin da raheela tafada kogin tunani amar yake tsaye a bayan'ta gani ta tsunduma da yawa yasa ya karyo ganye bishiya mangwaro ya aza mata bisa wuya, a firgice ta mike tsaye tana kurma ihu Amar ya kyakyace da dariya daga bisani ya tsagaita da dariya da yakeyi yace ya akayi ne "baby naa" wannan ihu duk na menene"?
Kallon tsana raheela tafara aika masa daga bisani ta ja wani wawa tsoki tajuya da suna tafita daga "garden" din ciki'n zafin nama yariko hannuta...

Jeeddah Aliyu🌹🌹
[18/06 8:34 am] Jeeddah Aliyu🌹: [6:13PM, 5/8/2016] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN
'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~2⃣9⃣~

Batare da tajuyo ba tace dallah malam kasake min hannu, yayi murmushi yace in kinada karfi ki fisge hannu naki mana, tace kasan bazan iya ba shiyasa ka ke wannan karadi"
ya make kafada yace wai me kike nufi da ni ne uhmm"? kina gani na falon mamee ki ka tsare na biyo ki nan kuma kinaso ki kara tsarewa me hakan yake nufi"?
Raheela tace dan Allah yaa amar ka kyale ni kafita daga rayuwata iya abunda nasani ba'a soyayya dole, nace banaso bana sonka bana kaunar'ka ka kyale ni mana kaje ka rungume yaya na'eema domin itace take fama da haukan sonka, ka nisanta daga gareni in har baso ka keyi nayi maka, rashin mutuncin.
A harzuke yakara matsi hannu'ta yace ki san irin furucin da ki kefada mini domin na fahimci kinaso ki wuce makada da rawa in har akan sonki ne ashirye nake da na shanye duk wani rashin mutuncin ki, dole kafadi haka yaa amar saboda kanaso ka tarwatsa min farin ciki da jin dadi bansaba da damuwa karka kace za ka hadasa mini shiga cikin'ta, in har da gaske tun ina yarinya ka keso na miyasa ka kasa reno zuciyata da sonka"? Batare da ta jira jin ta bakin'sa ba tacigaba da cewa, sai ka zabi hanyar ka cusa mini kiyayya ka ka dinga nunawa yaya na'eema son da kulawa wanda yayi sanadi da ta afka kogin sonka, shine yanzu don bata basira za ka zo kace kana sona to ba zan boye maka ba koda za ka yanka ni bana sonka aslima ka kara daura mini tsanarka a zuciya, domin kana yunkuri, rabani da 'yar uwa ta so ka sake mini hannu tsakanina da kai kiyayya ce mai zafi.
Har ta dasa aya a zanceta Amar yana kallon ta yasauke katuwa ajiya zuciya, hade da cewa zance banza zance wofi, ita na'eema wane kare hauka ne ya cije ta da har tayi sake sona yasami muhalli a zuciyar'ta tabbas ta, tafka kuskure mafi muni a rayuwata domin ni ko a kafa aka daura min ita zan kwance na yarr saboda bana sonta ke nakeso raheela ke ce mafalki na, ke ce farin ciki'na ki tausayawa rayuwata ki bani dama zan koya miki yadda za ki soni.
Raheela tafashe da kuka cikin shashekar kuka tace wallahi bana sonka yaa amar bana kuma fatar na so ka, kayiwa rayuwata adalchi ka kyale ni karka jefa ni cikin matsala.
Tsawon lokacin suka dauka a tsaye ba wanda yakara cewa komai sai sautin kukan raheela, ne ke tashi daga bisani amar yasausauta riko da yayi mata chan kasa makoshi yafara magana ba zan iya rabuwa da ke raheela son'ki yariga yayi min illah, ki taimaki rayuwata ki aura ni zan shayar'da ke tsantsan farin ciki zan wanke duk wata kiyayya da ki keyi min na maye gurbinta da zazzafa soyayya ki yarda da ni "baby naa" ni makaho ne a son'ki.
Wani murmushi takaici raheela tayi tace miyasa yaa amar ba za amfani da kwakwalwa ka, ka fahimce cewa matukar yaya na'eema tana raye ka haramta da raheela, a tsorace ya kalle ta jikinsa sai faman rawa yakeyi kamar mazari idanu shi sun kada sunyi jajir, sai huci yakeyi kamar zaki da yakeji yunwa, Ciki'n hargowa yace baki esa ba raheela baki esa ki haramta min kan'ki akan wata banza koda ace narasa ki ba zan taba son na'eema za je na sanarda iyayye mu domin nasan su ba za su hanani ke ba,yana karasa zance'sa yayi wulgi da hannu'ta yajuya har yayi tako biyu zuwa uku raheela ta kwada masa kira ya tsaya chak da gudu takarasa gabanshi ta zube tayi "kneel down" ta daga hannaye ta tasoma roko sa cikin rauni murya, ka dubi girman Allah Yaa Amar karka sanar'da su daddy wannan zance ka bani lokacin zan rarrashi zuciyata ta amince da soyayya'rka.
Ya dan murmusa yace wannan shawara ce mai kyau amma a wuri'nki tabbas gobe in har ina numfashi kafin na koma abuja sai na sanar'da su daddy abinda ke tsakanin'mu, wani abu da bakisaniba raheela kaka tana goyon bayan aure na da ke kin ga kenan bakida wani zabi, illah ki karbi tayin soyayya ta.
Cikin konar zuciya ta mike tsaye ta ja dogon tsoki tace har abada bazan taba son
Mugu mai son datsi igiyar zumuncin irin'ka ba tajuya tashiga gida tabar amar tsaye kamar "lamination" tana shiga falo tafada jikin kaka tasaki kuka dan Allah kaka ki ce yaa amar yarabuda ni banaso shi, in har yayi sanadiyar da su daddy suka tilassa min aura shi sai yayi danasani furta kalma so akai na.
Kaka tayi murmushi tace to naji amma wannan koke-koke ya esa haka nan ki share hawaye ki ba zan taba goyon baya ayi miki aure dole ba cikin jin dadi furucin kaka raheela ta share hawaye ta.

WASHE GARI********

Amar zaune a falon kaka raheela na gefe zaune ta sunkuyarda kai kasa kamar munafuka, kaka ta ajiye casbaha hannu'ta tace Amar dalilin da yasa nace ka zo ada ban so na shiga wannan al'amari naku ba saboda ba tun yau ba nayi ta yima kukan faruwa hakan da yake kai ba'a chanza maka ra'ayi ga duk abunda kasa gaba to gashi abinda ka janyowa kanka nafi kowa farin Ciki in aura yakasance a tsakani ku amma bana goyon abinda Zai bata zumuncin don haka tunda raheela tace bata sonka ka hakura da ita ka aure na'eema kuma karka kuskure ka sanar'da iyayye ku wannan zance cikin tsananin tashin hankali yadago yana kallon kaka daga bisani ya mike tsaye yace kaka banaso na'eema kuma har abada ba zan taba son ta"raheela ita ce wanda zuciya ta takeso matukar narasa ta saidai na mutu banyi aure ba yana karasa magana yafice daga falon kaka tafara kwala masa kira amar"amar kadawo nace bangama fadar abinda nakeso fada ba ko yajuyowa bai yi ba ballatana kaka tasa rai zai amsa mata kira da takeyi masa, kaitsaye yanufi "bedroom" dinshi yadauki "briefcase" dinsa da keys din mota da na dakinsa yarufe kofar dakin nasa ya wuce "part" din mamee a gaugauce yayi mata sallama, mamee tace lafiya amar irin wannan sauri haka kai da kace sai da yamma za ka koma"?
Mamee a "hospital" ake nema na urgently" saboda za mu tafi wata "seminar" da kungiya "who ta shirya a lagos mamee ta washe hakora tace kayi kokari kafin kadawo ka je "company" ka gano mini wannan sarkin shiririta baso zaman sa lagos nakeyi ba alhaji ne kawai ya matsa.
Amar yayi murmushin yake yace mamee ae yana tare da su abdul za su bashi kulawa, so kidaina damu kanki, ni zan tafi "mamee tace Allah ya tsare ya kai ka lafiya bada mugun gudu, amar yayi murmushi hade da cewa "ameen yafice a "compound" din gidan yaci karo da Lantana mai aiki'n mamee ta runsuna ta gaida shi tace likita ba dai tafiya za kayi ba gashi ba'a kamalla maka dambu nama ka ba"?
Sauri nakeyi lantana sai in nadawo next week"sai ayi min wani mu je wurin mota na baki sako ki kai ma raheela......
[8:59PM, 5/8/2016] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~3⃣0⃣~

Ya bude mota yadauko biro da takarda yayi rubutu akai ya miqawa lantana yace gashi ki kai mata amma karki bari kaka tagani, lantana ta karbi takarda daga hannu'shi, tace Allah ya tsare hanya yace ameen ya shiga mota yaja yafice lantana tajuya tashiga "part" din kaka raheela da kaka na zaune inda amar yabarsu tashiga da sallama kaka ta amsa mata, ta nemi wuri ta zauna raheela tace ke kuma daga ina naga kina wani misimisi da baki sai kace munafuka"?
Lantana tayi murmushin tace mamee ce ta aiko ni wuri'nki tace tana kiranki raheela ta zaro idanu hade da cewa lafiya take nema na?
Yoo ni ina zan sani kawai tace mu zo tare, raheela ta bata fuska tace naji sai ki tashi mu tafi suka mike tsaye a lokacin daya suka fita daga falon.

"PART DIN UMMA HAJARA**********

A part din umma hajara kuma na'eema da umma sun gama shiri su na zuwa, waje boka duguzuu na'eema tadauki "handbag" dinta tace umma dan Allah kiyi sauri banaso yaa Amar ya koma abuja batare da ya furta mini kalma so, umma taja tsoki tace ke ni banaso gaugawa domin aikin shedan ce, na'eema ta turo baki da misali karfe 11:15pm suka dauki hanyar kauye da boka duguzuu yake sai misali karfe 2:09 na rana suka esa na'eema sai korafi nisa wurin takeyi inda suka saba "parking duk lokacin da suka kawowa boka duguzuu ziyara ana na'eema tayi parking" su karasa da kafa tun kafin su shiga bukka boka duguzuu umma hajara ta fadawa na'eema sharuda boka, da yake yau sun tarar'da layi saida sukayi jira na tsawon mintuna 30 babu zance sallah azahar daga bisani layi yazo kansu suka shiga boka duguzuu yakare musu kallo ya kece da kafira dariya, yace barka

Please Login or Register in order to submit comment