Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bisa gadon kaka sai faman shashekar kuka takeyi, Amar yayi tsaye a bakin kofa yana kallon'ta yayida kuka'nta ke ratsa masa zuciya" cikin tako sa na kasaita yakarasa kusa da ita ya zauna jin motsi mutum kusa da ita yasa tafara magana batare da ta juya ba a tunani ta kaka ce tashigo don ta rarrashe ta cikin murya kuka tace kaka tun ina yarinya yaa Amar ya tsane a lokacin ina tunani don ina da rigima shiyasa baya sona amma a yanzu kaka na girma na kuma daina rashin ji duk da haka yaa amar baya sona me nayi masa da ya tsanani"?
Sonta da tausayin'ta suka dira lokacin daya a cikin zuciya amar" jin shiru kaka yayi yawa yasa raheela ta juya don gani abunda kaka ta yiwa shiru "4 eye's tayi da amar da ke zaune yana kallon'ta ta galla masa harara ta kawar'da fuskarta amar yasa hannu yajuyo da fuskarta da sauri ta runtse idanu'ta"
chan kasa makoshi Amar yafara magana sai kace mai rada "am so sorry raheela kiyafe min kidaina kallo a matsayin wanda baya so kidinga yi min wanda yafi kowa so da kaunar'ki yakarasa zance sa hade da jan karan hancin'ta, raheela ta ture buge masa hannu tace ni ka kyale ni ko yanzu ka bawa yaya na'eema waya ni baka bani ba in kuma aka bani ka karbe katuwar budurwa da ni ace banida waya saidai nayi, amfani da ta kaka.
Amar yasaki baki da hanci yana kallon raheela daga bisani yace budurwa raheela yanzu kece katuwar budurwa yakarasa zance sa yana dariya.
raheela ta murguda masa baki tace ni dai za ka siya mini koh"?
Amar yayi mata kallon kasa ido hade da cewa ba yanzu ba sai kin kamalla "secondary school"
Raheela ta bata fuska kamar za tayi kuka tace ka rike kayan'ka banaso, amar ya make kafada alamar "I don't care" ya mike tsaye yasaka hannu cikin aljihu "black jeans" din da ke jikinsa yafito da dan karami'n zobe sai shaki da daukar ido yakeyi, ya riko hannu raheela ya zira mata zobe a dan yatsa ta na hagu yace raheela wannan zobe shine tsabar'ki.
Raheela ta tsurawa zobe mai dauke da zane "heart" idanu haushi da takaici suka turnuke ta tace me zanyi da wannan karfe'n"?
Amar yace waya gaya miki karfe ne"?
Raheela tace ga Abu nan yana kyali dagani sa kasan karfe ne tacire zobe ta mika masa karbe kayan'ka in baso ka keyi na jefa shi a "fish pond" din daddy kafiye su hadiye shi ta karasa magana tana murguda baki cikin zafin rai amar yafinciko hannu'ta da karfi yace.....


🖊excellent writer's🖊

jeeddah Aliyu🌹🌹
[18/06 8:33 am] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN
'YAR UWA TAA🍆🍆

💕￿love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~￿2⃣1⃣￿~

Yace bakida hankali raheela zuciya'r tawa za ki jefawa kifiye"?
Raheela ta tabe, baki tace zobe karfe ne zuciyar'ka"?
Matsi mata baki yayi tasaki 'karar azaba hade da cewa washhh.....Yaa Amar da zafi yasaka hannusa sa na dama yadago fuskarta yanuna mata Dan yatsa shi, na hagu idanu'ta suka sauka bisa zobe da ke hannu shi "exactly" irin na hannuta banbanci kawai nashi yafi nata girma ta dan zaro ido tace Yaa Amar wannan wane irin zobe ne yafiye kyali da yawa"?
Amar yayi murmushi, yafi fuskarta da dan yatsa sa Yace zobe alqawali ne raheela daga yau, ba za mu Kara fada ba zan mu kasance a tare har karshen rayuwa'r mu.
Raheela ta turo baki tace me wannan zance naka yake nufi yaa amar"?
Amar ya tabe baki yace oho"
Tace to sake ni naji kaka tafara kira na watakila akwai abunda takeso nayi mata, a maimakon yasake ta sai yakara matsi mata baki, ta runtse idanu tace in baka sakeni ba zan kira maka kaka, amar yayi murmushi yace Ki kira'ta mana an gaya miki ina tsoro'nta ne" raheela ta bude idanuta tace ni dai kasake ni please"
Zan sakeki amma sai kinyi min alqawali, ba za ki jefar'da wannan zobe ba nayi maka alqawali yaa Amar zan cigaba da kasancewa da wannan zobe'n karfe har karshen rayuwa'ta, amar yayi murmushi hade da cewa "thanks my raheela yasake ta da gudu tafita daga dakin amar ya shafi sumar kanshi yace ina son'ki raheela "I can't do without you" raheela nashiga falon" kaka tadago tana kallon'ta da sauri raheela ta kawar'da fuskarta kaka tayi murmushi, amar yafito daga cikin dakin hannaye sa zube cikin aljihu wando sa shima da kallo kaka ta bishi shi, gani kallon da takeyi masa yayi yawa yasa yace kaka in akwai fura a dama mini zan sha ajima batare yajira amsa da kaka za ta bashi ba fice daga falon.

{DARE}********

Da misali karfe 8:30pm Raheela na zaune a falon kaka tana kallon tashar Zee world na'eema tashigo babu walwala akan fuskar'ta ta nemi kujera ta zauna raheela tayi mata kallo daya ta kauda fuska yayida na'eema tasauke ajiyar zuciya tace raheela" shiru tayi kamar ba zata amsa ba daga bisani tace na'am"
na'eema tacigaba da cewa ina cikin matsala narasa yadda zan tunkari yaa amar na fada masa ina sonshi wallahi kunya nakeyi kuma ina jin tsoro kada yace akwai wace yakeso inda haka ta kasance ina zan saka kaina raheelat"?
Tun lokacin da fara dogon sharhi ta raheela ta tsura zuba mata na mujiya gani ta dasa aya a zanceta yasa raheela ta gyara zama ta kuma yi, kasa da murya kamar munafuka tace ki natsu yaya na'eema ki nemowa kan'ki abunda ki keso in ki ka kuskure yaa Amar ya kubuce miki bana tunani zai dawo gareki.
Na'eema takara shiga cikin rudani hade da neman mafita, tace raheela ko za ki fada masa"?
Da karfi raheela tace ni kuma"? Ina wallahi ba zan fada ba so ki keyi ya yanka ni"? kedai da Allah yadaurawa jarabar sonshi ke ce za ki fada masa da bakin'ki ae waka a bakin mai ita tafi dadi ni kan baza'aji mutuwa sarki a bakina kawai malama kije yanzu yana "side dinshi ki fallasa masa sirrin zuciyar'ki.
Na'eema ta dafe kirjinta da ke barazana tunkudo zuciyarta waje tace " I can't raheela ba zan iya ba ki nemo min wata hanya amma ba da wannan.
Mtsss...raheela taja tsoki tace saboda me da bazaki gaya masa ba"?
Cikin raunin murya na'eema tace "cos am so scare"
Raheela ta tabe tace wannan "scared" din shine zai yi miki katanga karfe da yaa Amar ki dage kiyi fito na fito da shi ki yake shi, yabarki ki kai ga masoyinki.
Na'eema tace yanzu mecece mafita"?
Raheela tayi shiru kamar mai tunani daga bisani tace mafita guda daya ce......


🍆🍆MIJIN 'YAR UWA
TAA🍆🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~2⃣2⃣~

Mafita guda daya ce ina zuwa raheela ta mike tsaye ta nufi wurin "fridge" ta bude ta dauko "jug" mai dauke da fura ta mikawa na'eema tace kafin kaka tafita tace na, kaiwa yaa amar fura don haka kije ki kai masa kuma karki kuskure kidawo batare da kin furta masa kalma so" na'eema ta karbi "jug" din fura ciki'n sanyi jiki ta juya har tayi tako biyu zuwa uku taji murya raheela na kirata taja tayi tsaye raheela tace "oll d best" batare da na'eema tace komai ba tajuya raheela nagani tafita tasauke ajiyar zuciya, sai kuma ta tsince kan'ta cikin yanayi na faduwa gaba dafe kirji'nta tafara furta "innalillahi wa'inna illaihi raji'um"!
Kaitsaye na'eema ta doshi dakin amar gaban'ta na dukan tara-tara har ta rike "handling ta bude kofa sai taji sauti muryoyin, mutane sai kawai tafasa budewa a zuciyar'ta tace yaa amar bashi kadai bane to ya zanyi da sakon da ke cikin zuciya taa"?
Kamar daga sama taji murya wani daga cikin falon yace haba amar "how long" za ka dauka kana cigaba da "hiding feelings" dinka akan raheela"?
Ras-ras-ras sautin da kafita daga kirjin na'eema kenan ta durkushe kasa tasaki kuka mai tsuma zuciya, murya amar taji yana cewa uhmm...kb kenan karka damu ko na furtawa raheela kalma so ko ban furta ba "she is mine & no body can't snatch her from me"
Na'eema ta toshe bakin'ta da tafin hannuta don kada su ji sautin kuka'nta.
Mtsww....kb yaja tsoki yace wallahi ina tausayawa wannan abari yahuce naka saboda na tabbata shi ke kawo rabon wani, amar ya galla masa harara hade da cewa raheela tawa ce ni kadai matukar ina raye babu wani mahaluki da ya esa ya hau karaga'r mulki zuciyar'ta sai ni Amar matawalle saboda ni nafi cancanta da na mulke zuciyar'ta da gangar jikin'ta yana karasa zance'sa ya fisge sigari da ke hannu kb yayi mata kyakyawar zuqa kb ya zaro ido yace amar kaida ka ke mini fada Shan sigari yau kaine da sha"?
Amar ya yatsine fuska yace dole ce takama.
Na'eema ta mike da kyar jiri na kwasar'ta da gudu ta nufi "side" dinsu tafada falon umma hajara tana kuka a firgice umma ta mike tsaye tace ke lafiya me ki ke yiwa kuka"?
Batare da Na'eema tabawa umma amsar tambayarta ba takara kwasawa da gudu tayi ciki'n "bedroom din umma cikin yanayi na tashin hankali umma hajara ta mara mata baya kwance tarar'da na'eema bisa gado tana kuka tamkar ranta zai fita umma takarasa wurin ta tadagota cikin rawar murya umma tace lafiya na'eema me ki ke yiwa kuka"?
Da kyar na'eema ta iya bude bakin'ta tace umma narasa farin ciki'na shikenan umma, narasa yaa amar rashi na har abada cikin rashin fahimta inda ta dosa umma tace bangane abinda ki ke nufi ba na'eema"?
Na'eema tace umma yaa amar ashe basona yakeyi ba raheela ce zabin zuciyarsa ki taimake ni umma kar narasa shi,domin rashin shi agareni ba karamar masifa zai sanya ni a ciki wallahi za ki iya rasani.....


🖊excellent writer's🖊

Jeeddah Aliyu🌹🌹
[18/06 8:33 am] Jeeddah Aliyu🌹: ￿￿￿￿🍆🍆🍆🍆MIJIN
'YAR UWA TAA🍆🍆￿

￿💕love story 2016💕￿

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~￿2⃣3⃣￿~

Umma hajara tadaka mata tsawa hade da cewa ke banaso shashanci banza da wofi yanzu ki rasa wanda zaki, kwalafa ranki akan'shi sai jini'n buzaye jinin da duk duniya na fi tsana to inda ma mafalki ki keyi ki falka saboda bazata sabu ba wai bindiga a ruwa, Ko kin manta da alqawali da nayiwa suraj dan gidan anty asabe na bashi ke"?
Na'eema takara fashewa da kuka tace wallahi umma banaso yaya suraj asalima na tsane shi, tsana mai tsananin gaske, umma taja tsoki tace lallai za'ayi bala'e a gidanan don bazan taba amincewa ki aure Amar saboda mahaifiyar'sa itace tushe rusa mini farin ciki'na don haka bazaki aure dan'ta ba kuma karki kuskura nakara jin kin furta kalmar "SO akan Amar sai na zube miki hakora, umma nakarasa zanceta taja dogon tsoki tafice daga dakin, yayida na'eema tacigaba da shashekar kuka'nta.
Amar da kb suna fitowa sukaci karo da "jug" din fura ajiye a bakin kofa rass...gaban amar yafadi yadafe kirji cikin yanayi na wanda yashiga firgici yaci na shiga uku, kb kalli nan yanunawa kb "jug" da hannu'shi kb ya tabe baki yace wannan ae jug" ne, Amar yasauke ajiyar zuciya daga bisani yace shikenan raheela tagama sanin sirrin zuciya ta shine ta ajiye min fura anan, cikin tsananin Jin dadi kb yace "Alhamdulillah" abinda nake mafalki yafaru shine yau yafaru, kaga malam ka kwatarda hankali'nka Allah ne yakawo maka sauki kawai yanzu ka je ka kara siye zuciya'rta da zazzafa kalaman soyayya, masu ratsa jinin jiki" ka rikita mata "brain" abokina ta hanyar dada' kalamanka amar ya kyalkyale da dariya yace kai kb bakada kyau an gaya maka ni irinka ne da zan je gaban mace ina zuba ko mace ma karamar yarinya irin raheela ae sai ta rena ni, mtsss...kb yaja tsoki yace chan ta matsi maka watakila wannan girman kai naka shine sanadi da za ka rasa raheela, har amar yayi yunkuri yabawa kb amsa kb yadakatar'da shi ta hanyar cewa sai da safe amar sauri nakeyi na bar madam ita kadai yafada ciki'n motar'sa yaja yafice daga gidan.
Amar yayi yana tunani mafita tabbas abinda kb yafada gaskiya ne yakamata nakara jadadawa raheela son" da nakeyi mata saboda boyo da nakeyi mata a yanzu bashida amfani, ya kalli agogo da ke daure a hannu'shi kirar "Rolex" yaga karfe 10:30pm tayi yaja dan karami'n tsoki saboda yasan a irin wannan lokacin kaka ta rufe kofar'ta ba yanda ya iya dole yadauki "jug" din fura shi yashige falonshi zuciyarsa cike da son da kaunar raheela.

A WASHE GARI********
Raheela na kwance a falon kaka tana tunani dalilin da yasa na'eema bata kwana a "side" din kaka ba Amar yayi sallama yashigo hannusa dauke da "jug" fuskar raheela dauke da murmushi ta amsa hade da cewa ina kwana yaa Amar"?
Amar ya murtuke fuska sai kace tsohon soja yaja birki a bakin kofar shigowa yace ke zo nan ciki'n sanyi jiki raheela ta mike ta nufi wurinsa gaban'ta sai faduwa yakeyi a zuciyar amar yace kai kaga yarinya tun ma kafin na furta kalma SO" a gaban'ta tafara rena ni mtssss....shine matsala soyayya da kanana yara raheela ce ta katsi masa zance zuci sa ta hanyar cewa yaa Amar gani.
Kallon uku saura kwabo yayi mata daga bisani yace uban me ki ke yiwa dariya"?
Gani yadda ya murtuke fuska, yabawa raheela dariya batasan lokacin da ta kwashe da dariya ba amar yakara harzuka yadaka mata tsawa yace abin ki iskanci ne koh Raheela"?
Da sauri ta hadiye dariya'rta ta hanyar toshe bakinta da tafin hannuta" Amar yacigaba da cewa don tsabar iskanci shine jiya kika yi min labe ki kaji abinda nake fada bayan kingama mini labe a maimakon ki shiga ki kai min fura ta sai ki ka ajiye a bakin kofa koh"?
Raheela ta zaro manya idanuta hade da girgiza kai tace yaa Amar b...... yadaka mata tsawa shiru banaso jin komai daga bakin'ki yakara matsowa daf da ita har sunaji bugun zuciya'r junan'su yayi kasa da murya yace duk abinda ki kaji a dare jiya a dakina gaskiya ne raheela babu karya a ciki, yakarasa magana hade da daga mata gira, raheela ta turo baki tace nifa yaa Amar ba abunda naji ehee"
Ya galla mata harara yace karya ki keyi munafuka in bakiji firar da mukeyi ni da kb miyasa ki ka kasa shiga ki kai mun fura sai ki ajiye a bakin kofa"?
Raheela ta murguda baki tace haka kawai"
Amar yace haka kawai ki ka ce"?
Raheela ta zaburo baki tace eh" haka kawai, amar yayi murmushi mugunta yace "good" ya bude murfi "jug" din ya juye mata ragowar fura da ke ciki'n a jikin'ta yakara tanke fuska yace na baki na baki "ten minutes" kije kiyi wanka ki samini a "parking space" zan daura miki karatu daga inda ki ka tsaya da jin firar mu ta jiya ya kuma saka dan yatsa sa ya lakato fura da ke bisa kumatu ta ya lashe yace "just ten minutes" yajuya yafice daga falon raheela tafashe da kuka gashi kaka batanan ballatana ta tare mata wannan wulakanci'n na amar haka ta juya tashiga "bathroom" tana kuka.
Wanka takeyi amma tana tunani wace irin fira ce yaa Amar sukeyi da na'eema tayi labe tanaji"?
To ko shine dalilin da yasanya yaya na'eema bata kwana a side nan ba"?
Cab ae kuwa dole yaa Amar ya saurare ni na wanke kaina ta hanyar fada masa bani bace da wadanan tunane-tunane raheela ta gama wanka ta dauro "towel batare da tayi "make up" ba tasaka riga da siket na "blue lace mai touch din pink tafasa turare "pink heart" ta yane kanta da dan karami'n "veils shima pink duk da batayi "make up" ba tayi matukar kyau na ban mamaki har ta juya za ta fice daga dakin karaf idanu'ta suka sauka bisa "side bed drawer" ta bude tadauki "lollipop" dinta guda daya ta bare ta jefa ciki'n baki tana tafiya tana tunani yadda za ta wanke kanta wurin yaa Amar......

￿￿🍆🍆MIJIN 'YAR UWA
TAA🍆🍆🍆￿￿

￿💕love story 2016💕

Na Hauwa shehu Aliyu🌹

~￿2⃣4⃣￿~

Amar da ke zaune bisa boot" din mota ya tsurawa raheela idanu tsananin sonta na kara samu muhali a zuciyar'sa ya lumshe idanu shi.
raheela tacigaba da zance zuci ta hanyar cewa na shiga uku yaya na'eema kin daza min masifa kalli yadda "guy" nan yasha "omo ba shakka yau sai naci dan kare duka a wurinsa.
Raheela na karasawa "parking space" daga nesa da shi taja tayi tsaye, amar yayi mata wani mugun kallo wanda yayi sanadiyar da hanji cikin'ta ya murda da Sauri takarasa gabanshi tsura mata idanu yayi yana mata shu'umin kallo wanda yasanya raheela shiga ciki'n bakon yanayi wani rikitace sanyi ya ratsa kassa jikinta tamkar sanyi hunturu yayida tsigar jikin'ta ta, tashi zuciyata na bugawa da sauri-sauri Amar yasaki murmushi samu nassara saboda yasan 'yar karamar kwakwalwa raheela tadauki sakon da ya tura mata, tuni jikin raheela ya mutu takasa sarafa kan'ta" Amar yacire "lollipop" din bakin'ta yajefa a nasa baki yana tsotsa yabar raheela sake da baki tana masa kallon kana rikita ni fa suna hada ido yakashe mata ido hade da cewa yadai da sauri ta sunkuyarda kan'ta kasa Amar ya kira sunanta Chan kasan makoshi, da kyar ta kalli shi, gani har yanzu "sexy eye's" dinsa suna kafe akan fuskar'ta yasa ta murguda masa baki tare da cewa yaa Amarrr...yadda ta kira sunan shi yasa Amar yaji yarrrr....yana yawo a gangar jikinsa nan take yakara jin wani sabon sonta yana kwarara a zuciyar'sa kamar daga sama yaji muryar raheela cikin shagwaba tana cewa ni daina yi min wannan kallon naka na "magic" Amar ya dan murmusa tare da cewa yau kuma nan ki ka koma"? kin gama kira na da mai idanu "horror" raheela ta turo baki tace to ae gaskiya na fada kuma sai na fadawa kaka wulakanci da kayi min.
Amar ya tabe baki yace ke fa bakyaso, a zauna lafiya yaushe nayi miki wulakanci"?
Raheela tace wanke ni da fura dakayi batare da nayi, maka laifi komai ba" Amar yayi murmushi'n yace mari naso na wanke ki da shi sai ki ka ci sa'a "jug din fura yana hannu na da in na wanke ki da Mari sai hakora ki sun fita, raheela ta zaro idanu tace cab mari fa"?
Ya galla mata harara tare da cewa ko kin wuce mari ne"?
Raheela tayi fari da idanu tace "Nop" ko duka na za ka iya Amar yace miyasa jiya ki kayi min labe"?
Raheela tace ni fa daina cewa nayi maka labe, Amar yayi murmushi'n tare da cewa nadaina yaya raheela" jin suna da ya kirata da shi, yasa ta kyalkyale da dariya tace ka rufa min asiri yaa Amar wannan sunan yafi karfin shekaru na, Amar ya shafi sumar kanshi yace raheela kinsan me SO yake nufi"?
Raheela tayi murmushin tace wannan Wace irin tambaya ce yaa Amar"?
Amar ya hade fuska yace na tsani nayi tambaya a mayar mun da tambaya a maimakon amsa "so take note" raheela tayi shiru tana kallon'shi ya zaro idanu yace ki bani amsa mana raheela ta rausayarda kai tamkar za tayi kuka, tace yaa Amar "SO" sai kuma tayi shiru kamar mai nazari gani haka yasa Amar yace kince SO kiyi shiru ko kina nazari ne"?
Cike da shagwaba raheela tace, "SO wata halinta ce da ke shiga jikin dan-adam batare da sani sa ba '"SO baya neman izzini a lokacin da zai sami muhalli a zuciyar dan-adam cuta ta SO batada magani illah samu amincewa zuciya'r da ka ke SO" tun lokacin da tafara magana Amar yake kallon dan karami'n bakin'ta mai dauke da "pink lips" tana dasa aya a zanceta Amar yadauki tafi raf-raf-raf yaciro lollipop" din da yake tsotsa yasaka mata a baki dai-dai lokaci'n da na'eema tafito a "compound" din gidan karaf idanu'ta suka hasko mata amar yana sanyawa raheela "lollipop" a baki runtsa idanuta tayi hawaye na zuba akan fuskar'ta amar yace baby sha lollipop" kafin nayo miki "special shopping" saboda kin gama tafiya da zuciyata raheela ta kyakyace da dariya, amar yace dole kiyi dariya "baby domin kin sanyaya zuciyar da ke muradin ki kafin nayi miki fashi'n baqi fada mun inda ki ka samu wadanan zazzafa kalamai"?
Raheela ta turo baki tace a hausa Novels"
Amar ya zaro idanu hade da cewa eh" lallai kam yarinya kinyi nisa ni ina nan ina miki kallon karamar yarinya ashe kin wuce da sani na maganar kb ta tabbata mudi'n na tsaya wasa zan rasa ki, jikin raheela yayi sanyi sakamako jin kalamai amar masu halshen damo, Amar yayi gyaran murya ya murtuke fuska yace raheela ki natsu ki bude kunne ki da kyau yau zan baiyana miki sirri'n zuciyata, tuni jikin'ta yafara jikewa da gumi zuciyar'ta tashiga wasiwasi me yaa Amar yake nufi, yayida Amar yacigaba da cewa tun ranar'da ki ka zo duniya banida wani mafalki da ya wuce naki raheela, zuciyar'ta ta kamo da tsananin son'ki tun lokacin da bakisan miye duniya ba wani irin yanayi raheela tashiga mai wuyar fassarawa nan take ta nemi natsuwa'rta tarasa hakan ne yabawa Amar damar Cigaba da tona asirin zuciya'rsa, ke ce farin ciki'na raheela gaba daya rayuwa ta na tsara ta ne tare da ke, bantaba kallon wata 'ya mace da sunan SO sai akanki raheela, kuma bana bukatar jin amsa kin amince ko baki amince ba daga bakin'ki saboda zuciyata ta tabbatar min da kema kina sona, don haka kifara shirye-shirye biki saboda aure nakeso nan da dan kankani lokacin inaso afara kirana da "daddy yakarasa magana hade da daga mata gira.
Raheela tasauke katuwar ajiyar zuciya ta kuma share gumi'n da ke fuskar'ta da mayafinta, tayi zurun tana kallon Amar zuciyar'ta tamkar zata fado kasa don tsanani tsoro da rudani da tashiga wai ita yaa Amar yakeso anya kuwa Wannan lamari na yaa Amar akwai kamshin gaskiya a cikin'sa"?
Mutumi da yafi kowa tsanata yau shine tsaye a gabana yana furta mini kalma'r SO" in har da gaske ne yaa Amar yana sona to yaya na'eema fa"?
Kai ba zai yu ba ni ba sakarai bace da zan amince da makiyina a matsayin masoyina kuma ba zan iya taba cin amanar 'yar Uwa taa gani shiru nata yafara yawa yasa Amar ya kira sunanta Chan kasan makoshi'nsa raheela wani irin "shock" taji amma sai tadake tayi wani dagowa tana masa kallon sama da kasa tana yatsinar fuska daga bisani ta kyakyace da dariya tace......

🖊excellent writer's🖊


Jeeddah Aliyu🌹🌹
[18/06 8:33 am] Jeeddah Aliyu🌹: ￿￿🍆🍆🍆🍆MIJIN
'YAR UWA TAA🍆🍆￿

￿💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~￿2⃣5⃣￿~

Tace lallai yaa Amar ka haukace, kai yanzu don bakada kunya za ka dubi tsabar ido na kace kana sona ae ni ko maza suka kare a duniya ba abinda zanyi da kai, kalle ka fa wani jingege da kai, in kamanta yaa Amar na tuna maka ka sha fada mini cewa ka tsaneni bakaso na don tsabar kwarewa da iya yadaura da son bata zumuncin shine za kace kana sona to ni banaso'nka kuma na tsane ka, tun lokacin da tafara wankewa Amar allo'nsa yake kallon'ta batare da yayi yunkuri katsita ba saida tagaji don kan'ta tayi Shiru tana sauke numfashi'n Amar yadiro daga sama "boot" din mota fuskar sa tayi jajir don tsabar fushin ciki'n zafin nama yadanko hannu raheela ya dago habarta da hannu sa guda, ya tsura mata idanu, ciki'n sarkewa halshe raheela tace miye haka yaa Amar? wannan ae hauka ne kasake ni karka ji min ciwo
Amar yakara zaro idanu yace duk duniya ba abunda na tsana irin rashin kunya, don nace ina son'ki bashi zai baki dama ki renani ba ni mutum ne mai matukar son girma, kinga kuwa dole ki girmama ni kuma dole ki soni, ke ba ma abin alfahari ne a wurin'ki a matsayin, da nakeda shi na bude baki nace ina so'nki "who do u think u are"? Ya sauke gwaron numfashi yasake habarta ya matsi "lips" dinta batare da yajira jin ta bakin raheela ba yacigaba da zazzaga mata masifa mai cike da gargadi, in har kina

Please Login or Register in order to submit comment