Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidanan.
Abba yaja tsoki daga bisani yace ku dai kawai kun aza mata karan tsana, dalilin da yasa bataso shigowa "side" dinan ya juya wurin Raheela yace mama'naa ki dinga hankuri da su kinji koh"?
Raheela tayi murmushi, hade da cewa toh..abba ta fakace idanu mutane falon ta yiwa hajara gwalo, hajara takara harzuka ta kuma kudiri anniya ko ta wane hali sai, ta tarwatsa rayuwar raheela.
Abba yayi gyaran murya daga bisani yace dalilin da yasa na aika kiran'ku saboda ke ne na'eema kin kamalla karatu'nki lafiya kuma cikin nassara don haka nabaki wata biyu kacal, kifito da mijin aure ni da yaya mu yanke shawara a hade bikin aure ki da na su Abdul ayi a lokacin daya, shima amar da yazo "weekend" dole yafito da mata ko mu aura masa zabi mu, rass...gaban na'eema yafadi numfashi'nta yadinga fita da sauri-sauri wani masifafe gumi ya tsiyayo akan goshin'ta yasauka bisa fuskar'ta, da kyar ta tattara raguwar natsuwa ta tasoma share gumi da gefen hijab dinta, abba yacigaba da cewa lamari Amar yafara tsorata ni ace matsayin shekaru shi bashida budurwa"?
Aunty amarya tayi murmushin, tace miye abin tsoro abba na'eema"? in la'akari da miskilaci irin na amar zai yu akwai wanda yakeso fada ne kawai baiyi ba raheela tayi karaf ta karbe zance hanyar cewa abba yaa amar bakin jini ne da shi kullum fuskar'shi a hade kamar maigadin makabarta ta ya za'ayi yasami budurwa kawai ku hada shi aure da lantana mai aikin mamee za suyi matukar dacewa da juna takarasa zanceta tana washe hakora.
Abba ya kyakyace da dariya yace kai mama'naa wallahi bakida dama ke da Amar bansan ranar'da za ku shirya ba, raheela ta turo baki tace babu ranar abba saboda yaa Amar mugu ne duk lokacin yazo weekend" hankali shi ba zai kwanta ba har sai yasakani kuka nima shiyasa bana son'shi.
Abba yakara tintsirewa da dariya umma hajara sai harara take galla mata, aunty amarya kuma sai murmushin takeyi sabani na'eema da ta tsunduma a kogin tunani da neman mafita, abba ya tsagaita da dariya da yakeyi yace kamata yayi maama na hadaki aure da Amar, raheela ta zabura hade da zaro idanu kamar wanda taga abin tsoro daga bisani tace "Allah tsare gatari da sarar shuka ko da gida da mota, makka duk shekara abba za ka bani ba abinda zanyi da yaa amar nifa abba na tsani yaa amar " I hate him more than my own death"
Aunty amarya ta daka mata tsawa ta,hanyar cewa ke dallah rufewa mutane bakin'ki in aka kyale ki sai ki wuce makadi da rawa tashi ki koma inda ki kafito raheela ta mike tsaye tayi kasa da murya tace abba ni yaya nazee nakeso, kuma shi za ka aura min kaji abba"?
Abba yayi dariya yace wannan hadin shi ake kira da gwado, nazeer da raheela a matsayin mata da miji lallai za'a tafka tsiya raheela ta bata fuska cikin shagwaba tace Allah abba yaya nazee yana da hankali kuma y.....umma hajara ta katsi mata hanzari tace ke dallah kifita kibamu wuri, duk kinbi kincika mana kunne da shirme ki na banza da wofi raheela ta juya tanufi kofar fita daga falon takara juyowa karaf suka hada ido da umma hajara ta murguda mata baki umma ta zaro idanu tace raheela ni ki ke murgudawa baki"?
Da gudu raheela takarasa ficewa daga falon, "direct" ta wuce "side" din mamee...


🍆🍆MIJIN 'YAR UWA
TAA🍆🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~1⃣6⃣~

Tana shiga falon mamee tafara kwada sallama sai kace bakuwa, jin ba'a amsa mata ba yasa taja tayi tsaye wani fitinane kamshi takeji yana fitowa daga "kitchen din mamee yasa babu shiri ta nufi "kitchen" din gani wanda ke ciki yasa tafara sanda tana karasawa kusa da ita tace ke a firgice lantana ta kurma ihu raheela ta tintsire da dariya tace ke dai lantana kin cika tsoro, lantana taja dan karami'n tsoki hade da cewa ke kuma kin cika daukar alhaki.
Raheela ta zaro manya idanuta tace kai'kai lantana baqi za'ayi ne"?
Lantana tace me ki ka gani ne"?
Raheela ta yatsine fuska tace naga kina soya 'yan uban kaji duk kin cika gida da kamshi, lantana ta washe hakora hade cewa kin manta gobe juma'atu babbar rana likita zai dawo"?
Raheela taja tsoki tace aiki'n banza da wofi yanzu duk 'yan uban soyayu kaji nan saboda yaa amar aka tanadi su"? Lantana tace kwarai kuwa raheela takara jan tsoki ta mika hannu cikin katuwar "food flask" din da kaji'n suke ciki tadauki cinya nan take ta cinye ta jefar'da kashi takara daukar wata cinya tace mutumi da sai gobe zai dawo shine don tsabar rawar jiki ake soya masa kaji tun yau dole gobe yaci dumame lantana tace ae likita baya cin soyayar kaza sai ta kwana raheela tabe baki tace yaa amar badai iya yi ba takara daukar cinya lantana riko hannuta tace dan Allah ki rufa min asiri kada yaya na'eema tace na cinyewa likita, kaji mtwww....raheela taja tsoki tace dallah sake ni duk yawan kaji nan ace na mutum daya ne wannan son kai har ina wallahi dole na yagi rabona na'eema ce tashigo cikin "kitchen din tace kefa raheela bakida kirki an gaya miki na banza ne da za ki yagi rabon'ki"?
Raheela tace na banza ne mana tunda ba da kudi'nki ki ka siya ba haka kawai za'a dinga kwasowa daddy kaji gona ana soyawa kato na'eema ta galla mata harara hade da cewa yaa amar ne Kato"?
Kafin raheela tabata amsa mamee tashigo, "kitchen tace wai hayaniya me nakeji haka"?
Raheela tace mamee yaya na'eema ce wai ba za ta sami naman kaza nan ba kuma ka gashi yabiya min a rai, na'eema ta zaro idanu tace Allah mamee koda nashigo "kitchen dinan da katuwar cinya a hannu'ta mamee tayi murmushin, tace yi hakuri na'eema ki kara mata kadan ki huta da fitina ta na'eema tadauko fifike ta mikawa raheela a yatsine raheela take kallon fifike'n tace Allah ya kiyaye naci fifike kaza badai naman na yaa amar ne a gaban ki za mu ci, shi tare na'eema tayi dariya tace ke da wa raheela"?
Raheela ta turo baki hade da cewa ni da yaa amar na'eema takara tintsirewa da dariya nima da zanyi farin Ciki in haka takasance mtwww...tayi tsoki ta fice daga cikin "kitchen din...


🖊excellent writer's🖊


Jeeddah Aliyu🌹🌹
[18/06 8:31 am] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN
'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~1⃣7⃣~


WASHE GARI*******

Tun da misali karfe 11:00am na'eema tashiga kitchen" tafara hadawa yaa amar hadade girki, tuni kamshi yacika gida mamee tafito daga "bedroom" dinta tace kai na'eema wannan kamshi har ina tun kafin ki karasa girki nan yawu na sun fara tsinkewa, na'eema ta kyakyace da dariya mamee tacigaba da cewa na fahimce cewa kece ki ke kara shagwaba Amar shiyasa har yanzu yakasa nemawa kan'shi abokiyar zama, kodai 'yar gida za'ayi tsakani ki da Amar"?
Na'eema ta rufe fuskarta da tafin hannuta mamee tayi murmushin hade cewa dama najima ina zargin faruwa hakan, daga gani wannan shakuwar taku ke da Amar nasan akwai wani abu a kasa shi, tun lokacin da amar ya koma abuja da aiki nagano manufar ku shi, yakasa fitarda Matar aure, ke kuma kullum cikin korar samari ashe kunsan kulaliya da ku ka kulla, na'eema takara kyalkyalewa da dariya tace kai mamee ni ba abinda ke tsakanin'mu mamee ta rankawashe ta tace karya ki keyi munafuka, indai tayi tsami dole mu ji, mamee na karasa zanceta tafice daga kitchen din.
Bayan na'eema ta kamalla girki tayi wanka tana zaune gaban "dressing mirror" sai faman caba "make up" takeyi sai kace sabuwa amarya raheela da ke nade cikin "blanket" tana baccin ta falka tasauke idanuta akan na'eema, ta wani yatsine fuska ta yaye "blanket" tayi mika hade da dogowar hamma, na'eema ta mike tsaye tasoma feshe jikinta da turare "violet roses" raheela sai faman kallon'ta, takeyi daga bisani ta tabe baki tasauko bisa gado ta nufi "bathroom" har ta murda "handling" din kofa ta juya tace iska na wahalar'da mai kayan kara batare da ta jira amsa da na'eema za ta bata ba tashige "bathroom" na'eema tayi murmushin, hade da girgiza kai, ta dauki mayafinta tafice daga dakin.
Kaaka na zaune a falon hannuta rike da casbaha na'eema tafito, wani malalacin kallo kaka ta bita da shi, tace ke kuma sai ina"?
Na'eema tace ba fita zan yi ba kaka ta zaro ido tace wai na'eema yaushe zaki daina, wahalar'da kanki akan Amar"?
Banza tayi da kaka kamar bataji abinda tafada ba, sai ma wayarta tadauko tafara buga "game" kaka tayi dariyar takaici tace matukar za ki cigaba da jiran Amar to kuwa za ki tsofe a gida ne ki yiwa kan'ki fada na'eema ki dangana da wannan jarababe son amar da ki ke yi, jin abunda kaka tafada yasa tadago idanuta ciki'n sanyi murya tace bazan iya ba kaka saboda son yaa amar yariga yayi yiwa zuciyata mumuna illah.
Kaka tace yaro, yaro ne yaro man kaza, in banda ke da abinki na'eema wa kika taba gani yayi so shi kadai"?
Amar bai masan kinayi ba kibawa kan'ki lafiya ki hakura da shi "Allah zai kawo miki, wanda yafi shi,.
Na'eema ta girgiza kai tace bana tunani zan sami wanda yafi yaa amar kaka in har narasa yaa amar tabbas zan rasa rayuwata, kuma na tabbata shima yaa amar yana sona, tun kafin na mallake, hankali kaina yaa Amar yake nuna, min kauna hade da kulawa, karki manta kaka, har gobe yaa Amar yana banbantani da raheela wannan kadai ya esa ya nuna miki yana sona kuma ina ji a jikina yaa Amar yayi kusa furta mini abunda ke zuciya'rshi.
Kaka tace umhh...yayi kusa dai yafurta mata, a firgice na'eema ta jefar da wayarta bisa kujera da ke kusa da ita cikin tashin hankali, tace kaka dama yaa amar yataba fada miki akwai wace yakeso"?
Kaka tayi yiwa na'eema kallon uku saura kwabo batare da ta tanka mata ba ta mika hannu ta janyo dan karami'n "basket" mai dauke da goro ta bude ashasha ta dauko katon goro farin tass..tasaka a bakin'ta ta gutsira tacigaba da Jan casbaha.
Na'eema tasauke ajiyar zuciya tace dan Allah kaka kifada mini wacece yaa amar yakeso"?
Kafin kaka tabata amsa raheela tashigo falon kaitsaye ta nufi "two star ta zauna ta mayar'da ganinta wurin na'eema gani yadda take hada gumi yasa tace lafiya yaya na'eema badai fada ki kayi da kaka ba"?
Cikin sarkewa halshe na'eema tace a'a.
Raheela ta bata fuska tace duk lokacin da naganki cikin wannan yanayi kaka tayi magana yaa Amar, takarasa zanceta hade da Mikewa tsaye ta riko hannu na'eema tace zo mu tafi kyale kaka tana kishi ne don za ki kwance mata miji.
Raheela da na'eema suka fice daga falon sukayi "side din mamee suna cikin tafiya raheela tace yaya na'eema zan baki shawara amma takasance sirri a tsakani mu, saboda in kaka taji za ta hana ki na'eema taja birki tana kallon raheela fuskarta dauke da mamaki zance ta.....

🍆🍆MIJIN 'YAR UWA
TAA🍆🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~1⃣8⃣~

Raheela ta lumshe idanu'ta daga bisani ta bude su cikin sanyaya murya tace me zai hana ki fadawa yaa Amar kina sonshi"?
Na'eema tayi shiru kamar me tunani daga bisani tace kina gani wannan shine kadai mafita"?
kwarai kuwa yaya na'eema saboda yaa amar shu'umi mutum ne ba kasaifai ake gane inda yadosa, ba ni anawa gani yaa amar yana son'ki kawai girman kai da miskilaci irin nashi sune suka hana shi baiyana soyayya'r da yake miki ki daure ki fada masa abinda yake zuciyar'ki.
Tsantsan farin Ciki ya maye gurbi fargaba da ke tare da na'eema ta rungume raheela tace "thanks my little sister" Shiyasa banada wata kawa da ta wuce ki raheela a duk lokacin da nashiga matsala, ke ki bani shawara mai kyau Raheela tayi murmushi hade da cewa banida kamar ki yaya na'eema shiyasa bana farin ciki matukar kina Cikin bakin ciki, kiyi min alqawali za ki baiyanawa yaa Amar sirri da ke zuciyar'ki na'eema ta share hawaye da suka zubo mata tace nayi miki alqawali "my little matukar ina numfashi yau zan yayewa yaa amar hijabi soyayya'r sa da ke lullube da ni, raheela tayi dariya tace da kyau 'yar uwa taa haka nakeso ji.
na'eema ta dan murmusa Cikin tsokana tace ina fatar ba ki manta ba yau tare da yaa amar za kiyi lunch"?
Raheela ta turo baki tace nafasa" na'eema ta tintsire da dariyar keta harda dafe ciki tace dama ba za ki iya ba cika baki ne kawai Irin naki, raheela ta ture hannu' na'eema daga riko da tayi mata tace Allah kuwa zan iya na'eema ta tsagaita da dariya takeyi tace to kiyi mana nifa har za ki ci abinci tare da yaa amar, komai ki keso matukar bai fi karfi na ba zan mallaka miki shi, a matsayin kyauta ta nuna bajinta hade da gwazo da ki kayi ta karasa zanceta cikin dariya.
Raheela ta tabe baki, tace material" din da yaa Amar ya kawo miki "last week" shi nakeso, na'eema takara kwashewa da dariya daga bisani tace dama tun ranar'da yabani shi naga kina misi-misi da kirar ido nagano cewa kina son "material din kuma na amince zan baki shi amma fa a bisa sharadi sai kinci abinci tare da yaa amar"
Raheela ta washe hakora tace shikenan za ki sha kallo yau, na'eema tace uhmm...lallai kuwa yau don jikin wata zai gaya mata kallon sai na baki mamaki raheela tayi mata da wannan "drama" suka shiga cikin gida.
Misali karfe 3:20pm raheela na zaune a "parking space"bisa farar kujerar roba Jin da tayi anyi "horn" yasa ta mayar'da hankali'nta bakin "gate" maigadi ya bude gate wata tsadadiyar mota ce kirar "Lexus 2016 model" black colour" sai shaki takeyi, tadanno kai da sauri raheela ta finciko dan kwali'n kanta ta lullube fuskar'ta ta wani langwabe, sai kayi tunani baccin takeyi yaa amar yayi "parking din Motar'shi daga bisani yafito yana sanya da "dark blue din "coat" idanu shi na rufe da farin gilashi ya bude "seat din baya yafito da "briefcase dinshi ya rataya bisa kafada karaf idanu shi suka sauka bisa raheela da ke lullube kallo daya yayi mata yagano ko wacece tabe baki yayi batare da ya tanka mata ba yaraba ta gefenta ya wuce har yayi tako uku yajuyo da sauri ya nufi wurinta, yayi tsaye yana kare mata kallo raheela da ke kallon'shi ta cikin dan kwali'nta tasaki murmushin samun nassara.
Mtsww.....yaa amar yaja tsoki yadaka mata tsawa yace ke...a firgice ta cire dan kwali'n da ta rufe fuskarta da shi, me ki keyi anan"?
Sannu da zuwa yaa Amar"
Yaa Amar ya bude baki yana kallon'ta kasa hankuri yayi yace babbar magana lallai raheela kinfara hankali, raheela tayi murmushi hade da cewa dama chan ina da hankali kaine baka lura da hakan ba.
Yaa Amar yakara tabe baki yace uhmm...wannan daba da ki ka kafa anan ta menene ina fatar ba wani sharri ki ke yunkuri kulawa ba"?
Raheela ta girgiza kai kamar mumina tace banida lafiya"
Me ke damun'ki"?
Ciwon kai da jiri"
Yaa Amar yayi murmushi hade da cewa don bakida lafiya shine ki zo nan ki zauna" tashi ki shiga cikin gida babu musu raheela ta mike tsaye.
Har sunyi kusan shiga cikin gida yakara watsa mata tambaya kin sha magani"?
Girgiza kai tayi, ya bata fuska yace miyasa"?
Tace banaso magani ya galla mata harara hade da mika mata "keys din dakin'shi yace kije dakina ki jira ni dole kisha magani ko nayi miki allura, cikin sarkewa halshe raheela tace yaa amar banaso allura amma zan sha magani, batare da ya tanka mata ba yakara mika mata "briefcase dinshi ya shige cikin gida.
Raheela ta bude falon yaa amar tashiga tayi kwanciyar'ta bisa "three star" ta juya wurin "food flasks din na'eema ta jera ta wani ja tsoki tace kalle duk yawan "food flasks" dinan antanade su ne don mutum daya kai amma yaya na'eema wahalaliya ce.
Shigowar yaa amar ce ta katsiwa Raheela tsoki burutsu da take yi, kaitsaye yanufi "bedroom dinshi bai wani jima ba yafito da "panadol extra a hannu'shi ya mikawa raheela ta karba ya cire "coat dinshi ya ajiye bisa hannu kujera yayi yakara cire "white shirt ya yarage daga shi sai "white vest" ya nufi "fridge ya bude yadauko robar ruwan "eva yakara mikawa raheela da ke ta faman aikin kallon'shi..


🖊excellent writer's🖊

Jeeddah Aliyu🌹🌹
[18/06 8:32 am] Jeeddah Aliyu🌹: ￿￿￿￿🍆🍆🍆🍆MIJIN
'YAR UWA TAA🍆🍆￿￿

￿💕love story 2016￿💕

Na Hauwa Shehu Aliyu￿🌹

~￿1⃣9⃣￿~

Raheela ta karbi robar ruwan ta ajiye bisa "stool" yaa amar ya zaro mata idanu yace, miye na ajiye ruwa kina nufi bazaki sha magani ba"?
Ta turo dan karami'n bakin'ta,cikin shagwaba tace ni yunwa nakeji"
Yaa amar yayi shiru yana mata kallon kasan ido shi kadai yasan abinda yakeji game da raheela anyya kuwa zan iya cigaba da boyewa raheela tsantsan so da nakeyi mata har sai ta cika 18yrs"? tambayar da amar yake yiwa zuciya'rshi kenan.
Raheela ta murguda baki hade da cewa ni dai yaa amar kadaina yi min, irin wannan kallon" Amar yayi murmushi'n har saida kumatu sa suka lotsa{dimple} tsananin kyau da kwarjini sa suka baiyana ya shafi sumar kanshi ya nufi wurin Raheela da sauri ta kawarda fuskarta, ya durkusawa gaban'ta yayi tagumi yana kallon'ta fuskar'shi dauke da tsadade murmushi'n raheela na juyo suka hada ido yadaga mata gira da sauri raheela ta janye kafafu'ta ta aja su bisa kujera da take zaune, ta rungume hannaye ta bisa kirji'nta yanayi ta tamkar na mai jin sanyi.
Amar yayi kasa da murya yace miyasa ki ke son zama da yunwa raheela"?
Raheela ta runtsa idanuta sakamako wani masifafe sanyi da ke ratsa "bones" din'ta jikin'ta na "shaking kamar wanda "shocking yaja da kyar ta iya bude baki tace miyar kifi akayi ni kuma banaso kifi gani yadda take magana idanuta a rufe yasa yakara cewa to ki bude idanu ki mana kin wani rufe idanu sai kace kinga "horror" ta girgiza kai hade da cewa ba zan iya ba tsoro nakeji"
Amar ya hade fuska yace ki bude idanu ki ko na kwawada miki mari babu shiri raheela ta bude idanuta, ta sauke su bisa fuskar'sa yayida shi kuma ya lumshe nasa daga bisani ya bude su ya mike tsaye, hade da cewa sauko kasa na zuba miki abinci, wani shegen dadi yarufe ta dama abinda takeji jira kenan da sauri ta zauna bisa "center carpet"
Amar ya zuba mata "jallof din shinkafa wanda taji 'yan ciki da "carrot da cabbage" ya zuba mata "pepper chickens" a sama ya tura mata "plate gaban'ta raheela ta yatsine fuska tace ba zan iya cinye shi ni kadai saidai mu ci tare batare yace komai ba ya dauki "spoon" yafara cin abinci gani haka yasa ita ma tafara ci suna cin abinci yana wanke'ta da murmushi, ta ajiye "spoon ta wani bata fuska yaa amar yace lafiya ki ka ajiye spoon"?
Raheela ta murguda baki hade tace ba kai bane ke sanya ni Jin sanyi, amar ya zaro idanu fuskar'sa dauke da dinbi mamaki yace kamar ya ina sa ki jin sanyi"?
Cikin rashin damuwa raheela tace wannan kallon da ka ke yi min, sai kace kana gaban "girl friend dinka tsananin tsoro da firgici suka lullube yaa amar bai ankara ba ya hadiye loma da yasaka a baki ae kuwa ta sarke shi yafara tari babu kau-kautawa idanushi suka kada sukayi jajir, sai faman sannu raheela takeyi masa.
Na'eema tayi sallama tashigo falon hannu'ta rike da "jug idanuta suka hasko mata amar na tari raheela na durkushe gabansa tana mishi sannnu da sauri takaraso ta ajiye "jug din hannu'ta ta dauki
robar ruwa ta balle murfi ta mikawa Amar ya karba yakafa kai yashanye ruwan tass yajefar da roba ya sauke ajiyar zuciya ya jingina bayan sa a jikin kujera ya lumshe idanu.
na'eema ta watsawa raheela harara tace ke wace irin mutum ce"? kina kallon yana tari ko ki bashi ruwa sai wani banza sannu da ki ke masa, raheela tayi Shiru tana kallon na'eema da ke durkushe gaban amar tana masa magana sannu yaa amar a garin yaya ka kware haka"?
Amar ya bude jajaye idanusa ya mike tsaye yace zan shiga wanka za ku iya tafiya yajuya yashige "bedroom" da sauri raheela ta mike tanufi kofar fita,na'eema tabi ta da kallon mamaki Daga bisani ita ma ta mara mata baya.
"direct" raheela ta wuce "side" din kaka zaune ta tararda kaka tana kallon tashar sunnah tv ta zauna kusa da ita kaka tace ayawo kajin birni daga ina ki ke"?
Raheela ta yatsine fuska batare da taba kaka amsa ba ta kwanta tayi matsahi da cinyoyi kaka, ita ma kaka bata ni ta kan'ta ba Saboda tasan hali'n mutuniyar'ta ta.
na'eema ce tashigo fuskarta a hade tanemi kujera ta zauna, kaka kalle ta ta watsar tacigaba da kallon raheela ta mika hannu tadauki goro kaka tana ci yaa amar yayi sallama yashigo kaka ta amsa masa hade da cewa likita bokan turai saukar yaushe"?
Amar yayi murmushi yace tsohuwa mai ran karfe, kinci lokacin'ki kin ci namu na jikoki ki" kaka to shakiyi kafara koh"?
Yaa Amar ya mikaqawa na'eema farar leda yace kanwa taa ga tsaraba'rki cikin jin dadi na'eema ta bude ledar zaro idanu tayi sakamako dalleliya waya da taciro cikin kwali'nta.
Na'eema ta washe hakora tace na gode Yaa amar Allah yasaka da alheri" amar yace "ameen kanwataa yajuya wurin raheela da ke ta faman tauna goro da karfi sai wani "kas"kas"kas takeyi yadaka mata tsawa ta hanyar cewa ke bana hanaki cin goro ba"?
raheela tacigaba da cin goro ta kamar bataji abinda yafada ba" cikin bacin rai yace da ke nake magana raheela ki ajiye goro nan tun kafin ranki yabaci.
Raheela ta tunzire baki ta jefar da goron da ke hannu'ta Amar yace ki tofar da na bakinki, hawaye na zuba akan fuskar'ta ta tofar da goro'n"
na'eema tace kaka kin ga sabuwar wayar ta kaka ta kyabe baki tace nagani Allah yasa ki more na'eema ta mike cikin murna da jin dadi tace bari naje na gwadawa su umma batare da tajira amsa da kaka za ta bata tafita.
Raheela ta mike da gudu tashige cikin "bedroom din kaka yaa amar yabita da kallo kamar daga sama yaji muryar kaka tana cewa kana bani mamaki amar wannan so ne ko ki kai kenan kullum cikin musgunawa raheela kana farantawa na'eema rai bakajin tsoro kiyayya da raheela takeyi maka tayi tasiri a zuciyarta"? Yayida kaka tacigaba da cewa a yanzu raheela ta mallake hankali kanta tana iya banbanci tsakani so da ki ina ji maka tsoro kada kwaba ka tayi ruwa.
Amar yayi murmushi yace karki damu kaka saura lokacin dan kakani na sanar'da raheela sirri zuciyata,
mtsww....kaka taja tsoki tace yanzu meye amfani abunda kayi"?
Cikin rashin damuwa Amar yace na me"?
Kaka tace na siyawa na'eema waya ita kuma ka ki siyo mata, amar yayi murmushi yace wannan ae ba bako bane a wuri'nta saboda ba yau nafara siyawa na'eema abu ban siya mata ba don haka banga abin tashin hankali a ciki'n sa ba.
Kaka ta girgiza kai alamar tana tausayawa wannan shirme na amar tace, yanzu kafiso kaga raheela tana kuka koh"? Kuma Kaine sanadi hanata rike waya
Amar yace Kaka raheela bataji magana don nace tadaina ci goro shine tayi fushi harda shigewa daki"
Kaka tayi murmushi tace ba shine dalilin fushi'nta ba amar yace to me take yiwa fushi kaka"?
Kaka tace dakin bako ka ne da bazaka shiga ka tambaye ta ba" amar yayi murmushi ya mike tsaye yanufi dakin kaka...


🍆🍆MIJIN 'YAR UWA
TAA🍆🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~2⃣0⃣~

Kwance take tayi rigigine

Please Login or Register in order to submit comment