Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gadon cikin zafi nama ya chafko k'afar raheela yajayonta da k'arfi, yayi mata kyakyawa muhalli a k'irjinshi, nan take yalalu6o bakinta yasoma tsotsa, yanayi yana shafar lallausar fatarta, daga bisani yacire 'yar rigarta yajefa, raheela sai faman kuka takeyi abun gwani ban tausayi, _{nace Allah sarki raheela aure kenan aure yak'in mata}_
Amar kam bai fasa yunk'uri cima burinshi yakeyi, wani razanane ihu da raheela ta kurma shi ya tabbata mini da cewa _Dr Amar matawalle_ ya tsallaka _border_ sai kawai nafara jin raheela na cewa wayyo kaka Hero zai kashe ni wayyo k'afafu na Dan Allah Hero kayi hank'uri wallahi mutuwa zanyi,
Saida Amar ya tabbatar da ya kashe wutar zazzafar k'aunar raheela da ke tururin a zuciyarshi sannan ya kyalleta ya wani k'ank'anme ta yana sauke numfashi, raheela kuma sai faman shasshek'ar kuka takeyi.........

_I'm sorry masoyan mijin 'yar uwa taa yau naso na kawo muku k'arshen wannan labari saidai Allah bai nufa ba sai kuma gobe in Allah yanufi mu da kaiwa_

Jeeddah Aliyu🌹
[17/08 11:11 am] Jeeddah Aliyu🌹: [16/08 5:09 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA 🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

1⃣1⃣3⃣

```WASHE GARI```

Tun da asuba Amar yad'auki raheela yakaita _bathroom_ yacika _bathtub_ da ruwa masu d'umi yasaka _dettol_ yasakata ciki wani mahaukaci ihu ta kurma ta chukuikuiye wuyan rigar Amar tana kuka, yayin da shi kuma yake aiki rarrashinta saida ruwan suka huce yak'ara saka wasu yayi mata wanka tass, sannan yafice yabarta ta tsalkake jikinta raheela tafito d'aure da _towel_ iya cinya sai wani Jan k'afafu takeyi Amar rik'o hannuta yabata zani ta d'aura yasaka mata hijab had'e da shinfid'a mata _pray mat_ tayi sallah tana kamalla sallah ta zabga tagumi, Amar yashigo d'auke da _teacup_ ya mik'a mata mai d'auke da _tea_ mai kaurin gaske a sanyaye raheela ta k'ar6i _cup d'in_ ta fara _slipping_tana yatsinar fuska ta shanye tea d'in ta ajiye cup ta kauda fuskarta gefe Amar ya yi murmushi saboda ya fahimce raheela kunyarsa takeji yad'auke ta chak ya shinfid'e ta bisa gado ya kuma cire mata hijab sai ya ji jikinta ya yi zafi alamar zazzab'i magani yabata tasha daga bisani ta kwanta, ya rufa mata _blanket_ ya sunbace goshinta sannan yafice daga d'akin, yayin da raheela ta lumshe idanu ta, hoton abunda yafaru tsakaninta da Hero daren jiya yadawo mata a kwakwalwa take tafara jin sabon sonshi yana ratsa jini jikinta tacigaba zance zuci har bacci ya yi nasara yin awon gaba da ita.

```k'arfe 11:15am```

Sai lokacin raheela ta falka, ta mik'e da kyar ta nufi d'akinta, kaitsaye _bathroom_ ta wuce tayi wanka ta zauna gaban _dressing mirror_ tayi _simple make up_ ta bude _wardrobe_ ta d'auko atamfar _super English_ _papule colour da touch's d'in orange_ tasaka tafeshe jikinta da turare masu k'amshi gaske, tana cikin d'aura d'an kwali Amar yashigo cikin tsadadiya shadda _ash colour_ gashin kansa yasha gyara sai kyalli yakeyi, ta ciki _mirror_ suka had'a ido da sauri raheela ta sada kai k'asa Amar yasaki murmushi, yak'arasa daf da ita ya rungume ta yad'aura kanshi a kafadar ta chan k'asan mak'oshi yace _Good morning my Angel_
Raheela ta rufe fuska da tafi hannuta, cikin 'yar muryata mai dad'i tace _morning Hero_
Amar yashafi wuyanta da hannu shi yace ya lafiyar jiki ina fatar babu inda yake miki ciwo"?
Turo baki tayi cikin murya shagwa6a tace cinyoyi na kadai ke min ciwo kuma bana iya tafiya da kyau tausayi ta yakama yaa Amar yace _I'm sorry baby zai daina ciwo tafiyarki zai dawo normal kinji_
raheela taga kai alama ta gansu da bayani sa yarik'o hannuta suka sauk'o _downstairs_ kaitsaye _dining table_ yanufa da ita yad'auki _plate_ ya yi _serving_ da kanshi yadinga _feeding_ d'inta har ta k'oshi sannan shu kuma yacika nasa ciki daga bisani suka nufi _parlour_ a _three star_ Amar ya zauna yajayo raheela ya manna ta a k'irjinshi yayin da ita kuma talafe kamar magge.

```kaduna```

Duk yadda 'yan uwa umma hajara suka so Abba ya hak'ura yasaka baki _police_ su bada beli su Abba ya k'i amincewa da wannan, buk'ata tasu haka suka cigaba da sintiri zuwa waje Abba da Daddy daga karshe saida suka had'a Abba da dattijai da yake jin kunya had'e da ganin girmansu sannan Abba ya amince aka sake su sadai Abba yakafa sheda duk abunda yasami danginsa su ne mutane na farko da zai fara tuhuma, a bisa wannan sharad'i Abba ya amince aka bada belinsu suna fitowa daga _police station_ babban yayasu Alhaji sadi yadakata da su ta hanyar cewa ina fatar kuna da muhalli da za Ku zauna domin ni banida matsunnguni Ku a gidana hajara da asabe suka k'asa suna rok'onshi yarufa musu asiri yace iya rufin asiri da zanyi muku kenan da nayi tsaye tsayin, daka aka fito da Ku don haka Ku Kama gaba Ku, tun dare baiyi muku ba kunemi muhalli da Ku tsugune yana gama magana yaja motarshi yayi gaba duk gidan 'yan uwa da suka dosa k'ora kare akeyi musu daga karshe sai k'onane gidan mahaifisu suka nufa, a _boys Questar's_ suka zauna shima d'akuna wuri duk su rube in ana ruwan sama a tsaye suke, kwana saboda duk rufin ya farfashe a haka suke rayuwa mai cike da matsi da 'kuncin abinci da za su ci sai in 'ya'ya asabe su aiko mata ta d'an samma umma hajara tun kafin tafiya tayi nisa asabe tafara yiwa umma hajara gori tagaji da cida k'atuwa banza don haka umma hajara taje ta nemo na kanta...
[16/08 6:09 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN YAR UWA TAA 🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

1⃣1⃣4⃣

Tun daga ranar tadaina samma umma hajara abinci, ko taci tarage saidai ta, zubar dole umma hajara tafara fita neman aikatau kada yunwa ta halak'ata, da kyar tasami aiki wanke-wanke a bakin tasha shagon wata bayarbiya mai siyarda abinci duk Wanda yaci yarage ta zube cikin Leda a haka take samu abunda taci _dama ance in za ka Gina ramin mugunta ka Gina sa gajere watakila kai ne za ka fad'a ciki duniya ta juyawa umma hajara baya tayi danasani abunda ta aikata a rayuwata_

```WATA UKU ```

Amar da raheela na gudanarda rayuwar su cikin so da kaunar juna, yau raheela ta tashi da zazzab'i da Amai yayin da Amar duk yarudi daga karshe ya yi mata _pregnant test_ yagano cewa tana d'auke da ciki d'an wata biyu, nan take yadinga ihu yad'auke ta chak yana juyi da ita, tun daga lokacin yak'ara bata kulawa ta musanmman cikin raheela na da wata biyar Amar ya yi mata _scanning_ yagano cewa tana d'auke da _twins_ duka maza ranar Amar har da kuka ya yi saboda farin ciki.
A hankali raheela take saukowa daga _upstairs_ sai fama tura tintsitsi cikinta takeyi Amar da ke zaune a _parlour_ hannu shi rik'e da _magazine_ yana d'agowa ya hango raheela ya mik'e da sauri yanufi wurinta yarik'o hannuta ya zaunar da ita, ya shafi kumatu ta yace sannu _baby_ raheela ta ya motsa fuska, had'e da cewa Allah hero cikin nan yana min nauyi da yawa ina zauna da kyar nake iya tashi in kuma na kwanta da kyar nake iya tashi, Amar ya yi murmushi yace _oh sorry Baby_ sai next month _EDD_ ki zai cika.
Raheela tamkar zai tayi kuka tace ni wallahi na matsu na haihu ni kadai nasan yadda nakeji akan ciki nan.
Kafin Amar yabata amsa lamtana tafito daga _kitchen_ da plate rik'e da hannuta, tayi sallama ta mik'awa raheela _plate d'in_ da sauri raheela ta k'ar6i plate tace lamtana har d'an wake ya nuna kamar kinsan yunwa nakeji.
Amar ya zaro ido yace haba lamtana banace kidaina sakawa raheela yaji da yawa a cikin abinci ba"?
Da sauri raheela ta katsi masa numfashi ta hanyar cewa gaskiya Hero kacika, k'orafi da yawa d'an wanke ba yaji ya za'ayi ya yi dad'i ci
Amar ya dungure mata kai yace, sai basir ya kamaki zai kiyi bayani, raheela tayi murmushi had'e da cewa da basir yana kamani da yanzu yadad'e da kamani.

Cikin raheela na shiga wata tara kaka ta dinga masifa da Amar dole yadawo da raheela gida kwana ta biyu a Kaduna tashi da nak'uda, kaitsaye aka nufi _hospital_ da ita mami na kiran Amar da waya ta sanar da shi raheela tana _labour_ a lokacin yana _office_ a rikice yashiga mota yanufo garin Kaduna, tun kafin Amar ya shigo garin kaduna mami tak'ara kiranshi tayi masa kyakyawa albishir raheela ta haihu lafiya an sami _twins_ farin ciki kamar ya kashe Amar yana shigowa _hospital_ d'in yanufi _room_ d'in da take cikin tsanani farin ciki ya rungume raheela yabata _hot kisses_ kaka ta galla masa harara tace kai fa Amar bakada kunya sai lokacin Amar ya lura da mutane da ke cikin d'akin...


Jeeddah Aliyu🌹
[17/08 11:12 am] Jeeddah Aliyu🌹: [16/08 7:16 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA 🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

1⃣1⃣5⃣

Ya d'an Sosa kai alamar jin kunya yanufi wurin, mami da aunty amarya da ke rik'e da baby's yafara k'ar6a na hannu aunty amarya ya yi masa, kiran sallah had'e da hud'uba, daga bisani ya tsura masa ido yaga _photocopy_ d'insa sak ya sunbace kumatu shi, ya mik'awa aunty amarya mami ta mik'awa masa na hannuta, Amar ya zaro idanu kasa boye mamaki sa ya yi yace _Allahu Akbar Allah mai iko mami kamanu yara nan irin d'aya sak_
Mami tayi murmushi tace haka ne Amar kowa abunda yake fad'a kenan Amar ya yi murmushi ya yiwa yaron h'uduba kamar yadda ya yiwa d'an uwansa.

```RANAR SUNA ```

Yara suka ci sunan Daddy da Abba akayi musu lak'abi da Arman da Aryan raheela na hango tayi tasha make up tana sanye da wani tsadad'e lashi, Ayshat da zainab amarya saboda ba'a fi watani uku da aurenta da Dr kabeer sai faman hidama sukeyi da jama'ar da suka gaiyato anyi bikin suna lafiya ank'are lafiya, yayin da maijigo da yaranta suke samu kyakyawa kulawa daga wurin kaka musanmman raheela da kaka keta faman tsinma ta da had'ad'u kayan mata.
Amar kuma sai faman sintiri yakeyi tsakani abuja da Kaduna sai da raheela tayi wata uku a lokacin yaranta sunyi kwari sannan kaka ta amince takoma gidan Amar ranar saida Hero ya suma don dad'i saboda raheela tadawo masa budurwa sak.


```BAYAN SHEKARA BIYAR```

Raheela ta cikawa Daddy burinsa ta zama cikkakiya likitan mata, yayin da Daddy da Abba suka ware billiyoyi kudi suka Gina katafare _hospital_ mai suna *Abdulrazaq matawalle memorial hospital* domin tunawa da mahaifin su inda Amar da raheela suka tattaro komatsa suka dawo Kaduna da zama saboda kula da hospital d'insu yayin da suka tare a tafatsitsi gidansu da yaya su guda uku saboda a lokacin raheela tak'ara haihuwa 'ya mace mai sunan na'eema suna kiranta da Ainaan burin Amar yacika ya mallaki raheela rayuwa suke gudanarwa cikin kwaciyar hankali da kaunar juna.

Raheela na zaune gaban _dressing mirror_ tana make up Amar yashigo yana sanya da _English wear's_ harara ya galla Mata daga bisani yace wai ke duk lokacin da za mu fita sai kin 6atawa mutane lokacin, raheela ta yi murmushi had'e da mik'ewa tsaye ta d'auke _handbag_ da _veil_ d'inta tace mutafi sarkin k'orafi har ta juya Amar yafisgo ta da k'arfi ya tsotsa _lipstick_ d'in bakinta, sannan yasaketa raheela ta kai masa duka da _handbag_ cikin shagwaba tace haba Hero kai kenan kullum sai ka tsotsi min _lipstick_ Amar ya rungumo ta suka nufi k'ofar fita yace _sorry babynaa duk lokacin da naga lips d'inki da lipstick banida kwaciyar hankali har sai na tsotsa shi_
Raheela tayi murmushi had'e da cewa ni ma shiyasa akoda yaushe nake shafawa saboda nasan _my super Hero_ yana matuk'ar sonshi
Dad'i ya lullube Amar yace ina sonki raheela kuma har abada kece taurarowa da ke haska zuciyata.
Suna k'arasa shiga _parlour_ yaransu da ke zaune suna jiran fitowarsu a lokacin d'aya suka mik'e Ainaan yarinya 'yar shekara biyu tanufi wurin Amar da gudu da sauri yasake raheela yad'auketa yace _oh my angel I miss you_
Ainaan ta kyalkyale da dariya cikin 'yar muryarta ta yara tace Daddy yoyipop{lollipop}
Amar yajuya ya kalli raheela suka kyalkyawa da dariya Aryan yace Daddy karka 6ata saboda ko yanzu guda, uku tashanye Amar ya yi murmushi ya shafi kan Aryan suka fice daga gidan.....
[17/08 8:05 am] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA 🍆🍆

💕love story 2016💕



{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

1⃣1⃣6⃣

Raheela na _driving_ yayin da Amar ke ta faman yiwa Ainaan wasa _traffic light_ ya tsayar da su gungu almajirai suka lullube titi suna bara raheela ta bud'e _handbag_ d'inta ta Ciro _N500_ ta zuge glass da sunan tabada sadaka karaf idanu ta suka sauka bisa ga wata mata gurguwa zaune cikin keken guragu ta tsura mata ido yayin da hawaye ke fita daga idanu matar ganita ya yi masifar firgita raheela, har takasa mik'a sadaka da tayi niyar bata a dai-dai lokacin aka basu hannu cikin mutuwar jiki raheela ta ja mota cikin zuciyarta tace tabbas wannan matar tayi kama da umma hajara in har ita ce to ya akayi ta zama gurguwa"?
Nan take raheela ta tuna da wasiyya da na'eema tabar mata _Dan Allah raheela kiyi mini alqawali ko bayan raina za ki kula mini da umma naa saboda batada kowa sai ni_
Ras gaban raheela yafad'i duk sanyi ac da ke cikin motar ita zufa takeyi, yayin da Amar bai San abunda ke faruwa da ita saboda ya shagala da yiwa Ainaan wasa, nan take raheela tayi yuton ta koma inda suka fito,da sauri Arman yace _mommy_ mu fasa zuwa gidan kaka ne na ga kin koma baya"?
Sai lokacin Amar yad'ago kanshi ya k'urawa raheela ido ya ga tana ta faman gumi, kafin yayi magana ta gangara gefen titi tayi _parking_ tafice da sauri tanufi gungu almajirai saidai kash duk iya dube-dube raheela bataga matar ba a firgice Amar yarik'o, ta yace lafiya raheela wai me ke damuki ne"?
Wallahi ita ce yaa Amar Dan Allah ka tayani nemanta na cika alqawali da na d'aukawa yaya na'eema.
Amar yak'ara firgita cikin rawar murya yace wace na'eema kuma"?
Cikin murya kuka raheela tabashi labari abunda tagani, da kuma alqawali da tayi wa na'eema
Amar yasaki ajiyar zuciya yace daina kuka raheela insha Allah za mu nemo ta duk inda take, nan take Amar ya yi ma sauran almajirai kwatace gurguwa matar, ko sun santa sukace ta wuce gida tana kuka su ma basusan abunda take yiwa kuka kwatace
gidanta su yiwa Amar, raheela tafashe da matsanaci kuka tace wallahi yaa Amar umma hajara ce ga shinan sun fad'i sunan mahaifinta, da yake daga inda suke babu nisa da gidan sai kawai suka nufi gidan suna shiga suka tararda ita a bakin ru6abe gate din gidan tana kuka asabe na bisa kanta tana zazzaga mata masifa.
Ita kanta asabe ta girgiza da gani Amar da raheela, umma hajara tana gani su tak'ara fashewa da kuka tana rik'o su gafara, raheela ta d'urkusa a gaban umma hajara tace na yafe miki umma, amma ya akayi kika rasa k'afafu ki"?
cikin shasshekar kuka umma hajara tafara basu labarinta, kamar yadda na fad'a muku kullum sai nafita aikatau wanke-wanke nake samu abunda naci, kamar yadda nasaba fita na nufi bakin tasha ina cikin aikina sai kawai nafara jin ihu da kururuwa maman sunday cikin shagonta,tana fitowa tarufe ni da duka wai nayi mata sata kudin duka na takeyi ta ko ina, daga k'arshe ta yi mini kuran kare batare da nasan hawa balle sauka sai faman kuka nakeyi dama almajirai da ke zama bakin shago suna jin haushina sabod in ci abinci an rage d'auka ni nake hana su na juyewa na zo da shi gida, dama irin wannan ranar suke jira ae kuwa suka rufeni da duka suna mini ihun barauniya gani za su halakani yasa na kwasa da gudu idanu na sun rufe muradina na tsirar da na raina ashe bala'i na gaba yana jirana, bansan cewa na hau kan titi ba sai jin nayi mota tayi mini kwasan karan mahaukaciya ta watsar, yayin da wata mota tabi bisa k'afafu na ni dai ban k'ara sani inda nake ba, sai tsintar kaina nayi bisa gadon asibiti koda na shafa k'afafuna sai naji su lullube cikin bandeji ashe sanadiyar take k'afafu na da mota tayi sun dameji ta yadda ba za su k'ara amfanata ba shiyasa likitoci suka gutsire su, a lokacin dangina suka k'ara nisanta ta asabe ce kadai ke jinya ta ita ma don nazami mata dole, saida na share tsawon wata uku ina jinya daga bisani aka sallame ni, ashe lokacin zan fara tsintar mumuna aikin da na aikata a baya domin sai na share kwana uku ko ruwa bansaka a bakina, da kyar nasamu yaya sadi ya siya min keke tun lokacin nafara fita bara domin ita kadai ce hanyar da tarage mini da zan iya samu abinci haka na dinga yi bara wata rana hakanan nake dawo ban samo ko kwadala ba wani lokacin kuma in asabe na ji mugunta sai kawai ta rufeni da duka tanayi tana zagina wai nice silar jefata cikin wannan hali da ta ciki rayuwa tayi mini 'kunci duniya ta juyan baya k'afafu da nake sintiri da su a gidanje bokaye da 'yan tsinbo na waye gari banida su nayi nadama abunda na aikata raheela Ku dubi girman Allah Ku yafemin ko zan samu sausauci, wannan masifar da na ke ciki umma hajara tana tak'arasa maganarta tafashe da kuka.
Daga Amar har raheela sunyi matuk'ar tausaya mata, yayin da raheela tarik'o hannuta idanu ta na zubarda hawaye tace na yafemiki umma, na kuma d'auki alqawali zan iganta rayuwarki zan baki duk wata kulawa da 'ya take bawa mahaifiyarta domin na cika tsohon alqawali da na d'aukawa yaya na'eema kuka umma hajara takeyi tamkar ranta zai fita, yayin da raheela ke ta fama rarrashinta ki kwatarda hankali ki umma ina tare da ke yanzu nan zan tafi da ke zan nema miki kyakyawan muhalli kema ki rayu kamar kowa.
Amar yaciro waya daga aljihu rigarsa ya kira _driver_ gidansa ya yi masa kwatance gidan da suke, bayan kamar mintuna 15 sai ga _driver_ ya zo suka kama umma hajara daga ita har keke ta suka saka su cikin mota, aunty asabe na gefe ta rakube tana kuka mai cike da nadama, raheela ta juya wurinta tace aunty asabe ki zo ki shiga mota mu tafi dama duk abunda umma hajara ta aikata da sa hannuki a yanzu ma da duniya ta juya muku baya Ku na tare don haka, umma hajara ba za ta tafi tabarki cikin wannan hali kun nufi rayuwata da ta zuri'ata da mumuna nufi ni kuma yau zan nufe Ku da kyakyawan nufi asabe ta rushe da kuka ta zube gaban raheela tana rik'o ta gafara, raheela ta kauda fuska ta tuna ada yadda aunty asabe take gudar katuwa mazaunata kadai abun kallo ne, yau tadawo 'yar firit da ita kamar mai cutar 'kanjamau duk wahala da rashin kayakyawan muhalli ya tsiyaye manya duwawu nan.
Kaitsaye _Abdulrazaq matawalle memorial hospital_ driver yanufa da ita domin umarni da Dr Amar yabashi kenan sai a washe gari Dr Amar ya debi jini umma hajara akayi mata _blood test_ nan take suka gano cewa tana d'auke da cutar ciwon sugar{diabetes} shiyasa da aka yanke k'afafuta, tun daga lokacin Dr Amar shi da Dr raheela matawalle suke kula da umma hajara har tasami sauki, ranarda suka sallama ta kaitsaye wani _plat House_ mai matuk'ar kyau suka nufa da ita Amar yaciro takardu gidan ya mik'awa umma hajara yace umma wannan takardu gidanki ne da raheela ta siya miki ae kuwa, umma hajara tafashe da matsananci kuka tace kaichona yarinya da nayi yunk'uri gani bayanta yau ita ce ta Ingata rayuwata raheela ta share mata hawaye tace kidaina wannan kukan da kuma tunawa da abunda yawuce washe gari raheela tasa driver yad'auko umma hajara da aunty asabe ya kaisu _matawalle family House_ ta tara iyayyeta maza da mata ta rok'awa umma hajara gafara kowane su ya girgiza da gani yadda umma hajara tadawo gurguwa daga bisani suka ce sun yafe mata kuma sun yabawa raheela had'e da sa mata albarka, na cika alqawali 'yar uwa ta da tayi......

Jeeddah Aliyu🌹
[17/08 11:31 am] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA 🍆🍆

💕love story 2016💕

{ part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

1⃣1⃣7⃣

Raheela na zaune a _parlourn kaka_ tana murzawa kaka magani a k'afa Amar ya shigo d'auke da Ainaan yayin da Aryan da Arman suna biye da shi Ainaan takama zillo wai ya ajiyeta yana sauketa, ta falla da gudu ta haye cinyoyi kaka, tace kaka aya mai sikari kaka ta shafi kanta had'e da cewa na'eema kin biyo halin raheela da son zak'i mtss Amar ya ja tsoki cike da jin haushi yace ba dole ba ae duk d'an da kika rena kaka dole yasha zak'i ni kam ba zan yarda ba ki lalata mini yarinya kamar yadda kika lalata raheela yak'arasa magana had'e da shure k'afar raheela.
Kaka ta galla masa harara tace to shak'iyi ka zo kayi mini shak'iyanci da kasaba, raheela ta kyalkyale da dariya tace wai sai yaushe Hero da kaka za su daina fad'a"?
Amar ya yi murmushi ya d'an shafi sumar kanshi yace ba rana saboda ba za ta daina yi mini shishigi, a cikin al'amura na.
Kaka tabe baki tace tashi maza raheela d'auki mayafiki ki ja wannan fitanane miji naki Ku barmin gida raheela ta yi murmushi had'e da mik'ewa tace kaka yau har da Koran mu akeyi"?
Ba ke na kora ba wannan miji naki na kora, Amar ya tabe baki yajuya wurin _twins_ yace _come on boy's let's go Home"_ wannan _old woman tagaji da mu_
Arman ya mik'e da gudu ya boye bayan kujera, Aryan kamar zai yi kuka yace _please Daddy ka barmu anan mu kwana wurin kaka saboda gobe ba school tatsuniya takeyi mana mai dad'i gaske irin wance take yiwa mommy a lokacin da take little like baby Ainaan_
Harara raheela ta watsa masa had'e da cewa kai banaso iskanci, Amar ya kyalkyale da dariya kaka na tayashi cikin shagwa6a raheela, tace _please kaka kidaina basu irin wannan labari ae sai su raina ni_
Kaka tace to naji sai da safe raheela ta rik'o hannu Amar tace ka ga Hero zo mu tafi wannan tsohuwar tadaina yayinmu, suka fice daga _parlour_ yaran su suka bisu da cewa _Good night Dad Good night mom_
Amar ne ya amsa musu cikin d'aga murya _Good night kid's_
Suna isa gida Amar yad'auki raheela chak sai faman kyalkyala dariya Sukeyi yadire ta bisa _3 star_ ya chafki bakinta yadinga tsotsa daga bisani yasaketa raheela na dariya tace kai Hero kai fa baka tsofa a wannan shekaru yakamata karage wannan abin Amar yajuyo ta ya matsita a k'irjinshi yace soyayya bata tsofa raheela kamar yadda sonki baya tsofa a cikin zuciyata ina godiya ga Allah {s,w,t} da ya mallaka min ke a matsayin matata ina sonki raheela kece farin cikina kwaciyar hankalina ina alfahari da ke matata.
Raheela tak'ara rungume shi tace, bana bakin ciki k'arya alqawali yaya na'eema na son mijinta da nayi domin na cika mata guda d'aya na kula da umma hajara ada wauta had'e da kurciya suka yasa nace banaso ```mijin 'yar uwa taa ``` amma a yanzu na fahince cewa in har babu shi rayuwata ba za ta ta6a inganta ba nima ina sonka Hero kuma zan cigaba da sonka har izuwa k'arshen numfashi na.
_Ni kuma 'yar gidan Shehu Aliyu nace Allah sarki soyayya ba abunda yakai ki dad'i da gard'i_
A tsorace suka saki junan su suka kuma mik'e tsaye cikin rawar murya raheela tace Aunty Jeeddah yaushe kika shigo gidanan ne"? shine ko sallama babu kika

Please Login or Register in order to submit comment