Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganina da alama darasi na yafara tasiri shiyasa nadawo na d'an k'ara tunatarda ke _are you not happy_ ??
_I'm not_ tafad'a tana murguda baki Ya mak'e kafad'a alamar ke kika sani yak'ara matsawa daf da ita har yana jin bugawar zuciyarta ya yi 'kasa da murya yace to me kike tunani"?
Wannan kuma bai shafeka ba tsakani na ne da zuciyata, na tsani shishigi da cusa kai ba kwarjini a rayuwata kai kuma ka kwarai a wannan fagge Sai kayita shshigewa mutane, ba kuma shi zai sa kasami gidin zama anan ta nuna saitin zuciyarta da yatsa.
Duk da zuciya Amar ta Sosa da jin kalamai ta amma sai yadake, kamar ba abunda ya ji, batare da yace uffan ba yajuya yashige _bedroom_ d'insa, raheela tasaki ajiyar zuciya tace amma _guy_ nan bala'i ne mutum sai kace aljani saura kiris ya halbo jirgina, k'amshi turare _pure blue_ yadaki hancinta shi yabata tabaci yadowa cikin _parlour_ da sauri ta yada kallonta a bakin k'ofa idanu ta suka hasko mata shi, cikin lallausar farar shadda tasha aiki da bak'in zare 'kafarsa sanye da _cover shoe black colour_ yana rik'e da hularsa bak'a yana gyara mata kari a zuciyata tace cab amma _Hero_ mugun d'an duniya ne ko ina yanufa da yasha wankan farar shadda"?
A baiyane kuma sai tace _iyeee d'an guyu ina kuma aka dosa da farar shadda_ ??
Harara ya watsa mata yace bansaniba
Uhm...Allah yasa wannan wanka ba don mata waje ake yi sa ba don ni bangane ba wai anyi yamma da kare.
Amar ya yi d'an bazawari murmushi had'e da cewa dad'i na da ke raheela shirme ni da nakeda zankad'ed'iya mace irinki me zai had'ani da matan waje ae ko sha'awarsu takamani saidai nadawo, gida na huce gajiya a jikinki yak'arasa magana had'e da d'aga mata gira.
Raheela ta kwa6e fuska tace tir kai kan Sam bakaji kunya furta irin wadanan magaganu.
Amar yace ke karki 6ata mini lokacin da wannan d'an banza surutu naki kamar _parrot_ Kaduna zan je ta'aziyya Allah ya yiwa iyayyen umma hajara rasuwa ga shi ke kuma kin tsare ni da surutu.
_innalillahi wa'inna illahi raji'um_ raheela tafad'a had'e da dafe 'kirji tace yaa Amar _accident_ sukayi ne"?
Ya girgiza kai had'e da cewa a'a gobara ce ta tashi tsakiyar dare su duka biyu sun kone a yanzu haka har anyi jana'izza su.
Cikin tausayawa raheela tace ashe tafiya kaduna yasamemu
Kallon sama da k'asa Amar ya yi mata ya wani ta6e baki yace....
[09/08 6:18 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA 🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

9⃣6⃣

Tafiya _Kaduna_ tasame ku, ke da wa 'yan mata kaka"?
Raheela ta turo baki tace ni da kai mana'
_Uhm....yarinya ce Allah kin tuba kare hauka ya cije ni da zan tafi da ke Kaduna_ ??
Ae ba sa6o nayi ba da za kace na tuba tak'arasa magana tana murgud'a baki
Ko kinyi sa6o ko bakiyi ba ba zan je da ke ba kwata-kwata kwana ki uku kachal a gidanan shine zan d'ebe ki zuwa _Kaduna_
Idanu ta taf da kwala tace dan Allah yaa Amar katafi da ni ae ka ga bai dace ace banje na yiwa umma ta'aziyya ba"?
Amar ya ta6e baki ya yi tafiyarshi raheela ta kifa kanta a hannu kujera tana gunji kuka, har Amar ya kai bakin k'ofa sautin kukanta yadaki kunnensa, kasa jurewa yayi yadawo falon ya durk'usa gabanta yad'ago fuskarta yace kinsan duk duniya ba abunda yake k'ona mini rai irin kukanki banaso _please_ raheela kidaina yi mini hasara hawayenki tashi maza ki shirya mu tafi
Farin ciki ya lullu6e raheela ta mik'e da sauri ta nufi hanyar d'akinta tana is a bakin k'ofa Amar, ya kwada mata kira tayi tsaye chak yak'araso daf da ita yace ki tabbata kin Saka Jan baki{lipstick}
Zaro idanu tayi had'e da furta ni da zan tafi gidan mutuwa miye had'i na da Shafa Jan baki {lipstick}"?
Matukar kinaso na tafi da ke dole kibi umurni na batare da tace komai ba tashiga d'aki ta sauya kaya zuwa atamfar _super Holland_ _red &yellow colour_ anyi mata d'ikin _cut lace_ kayan sunyi masifar yi mata kyau tayafa _yellow veils_ had'e da takalmi ta _hill_ su ma _yellow colour_ tafesa turare tayi tsaye gaban _dressing mirror_ tana kallon kanta ta ga yadda tayi kyau tasaki murmushi, sai kuma ta6ata fuska sakamako tunawa da umurni yaa Amar da tayi, tad'auki _lipstick red colour_ tashafa tafice daga d'akin har yanzu yana nan tsaye inda tabarshi, ya kafe ta da idanu kamar yau ne yafara ganinta ta watsa masa harara had'e da cewa wannan kallo duk na menene"?
Amar ya lumshe idanu yace na yabawa ne kin yi matukar kyau kamar na cinye ki.
Raheela ta6ata fuska tace uhm...tace ka ji da shi a _parlour_ suka tararda lamtana tana 'yan goge-goge ta Amar yace lamtana za mu tafi Kaduna ki kula da gida insha Allahu da yamma za mu dawo, lamtana tace Allah ya dawo da ku lafiya a gaida su mami.
Raheela tace za suji
Amar yana gaba tana biye da shi har suka isa _parking space_ ya bude mota yashiga raheela aka kame _seat_ d'in gaba Amar ya yi addu'ar hawa k'arfe ya tayarda mota _Joseph_ ya bude _gate_ tun lokacin da suka d'auki hanya ba Wanda ya tankawa d'an uwansa kowane da abunda yake sak'awa a zuciyarsa a dai-dai wani k'ato shago na siyar da wayoyi {phone's} Amar ya yi _parking_ batare da kalli ta ba yace ina zuwa ya bude k'ofa yafita yayin da ita kuma tabishi da kallo har yashiga shagon tana kallonsa, tasauke gwaron numfashi cikin zuciyarta tace yanayi tafiyar _Hero_ kadai abar sha'awa ce gaskiya _Hero_ yahad'u ba k'arya sai kuma ta wani turbune fuska saidai matsala ta da shi miskilanci da shu'umaci ga shi kuma mugu, k'arar bude k'ofa yasa tajuya ga ni shi tayi rik'e da Leda fara mai d'auki da tambari shago da yashiga yana shiga mota don tsabar d'aukar magana irin na raheela tace _Hero_ ya yi banza da ita kamar baiji ta kira shi ba, yaja mota sai da ta galla masa harara sannan ta bud'e murya da k'arfi tace _Herooo_ taka wawa birki yagangara gefen titi ya yi _parking_ ya cije lebb'e sa ya na mata kallon k'asa ido kallon da raheela ta tsana kenan a kasalance ya furta _baby_ ya akayi ne"?
Wani duba tayi masa tana murmushi nan take Amar yagano wani sabon iskanci za ta guma masa yayinda shi kuma yasoma shirya mugunta da zaiyi mata yace kiyi magana mana kin wani tsaya kina murmushi munafuci.
Raheela ta turo baki had'e da cewa.....

Jeeddah Aliyu 🌹
[09/08 8:53 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [09/08 7:59 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA 🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

9⃣7⃣

Na ganka da Leda shine nace _gift_ d'in amarci ne kasiyo min saboda ko 'yar kaza nan da ake siyawa amare baka siyo mini ba"?
Amar ya yi murmushi yace yanzu nan kuwa zan baki _gift_ dama kinsan nace ki Shafa _lipstick_ kinga sai na tsotsi kayana sai na baki _gift_ kazar amarci kuma tana nan tana jiranki duk ranarda kika shirye ki kai, kanki _bedroom_ d'ina za ki ci kaza sai kinture ya k'arasa magana had'e da kashe mata ido
Ras-ras gaban raheela yafad'i tasoma danasani furtawa Amar wannan tambaya kafin tadawo daga duniyar sak'e-sak'e Amar yafisgo ta ya had'e bakinshi da nata yana saida ya tsotsi _lipstick_ d'inta tass sannan yasaketa yayinda raheela ta jigina jikinta a jikin kujera tana sauke numfashi Amar yalek'a fuskarta yaga ta lumshe idanu ta, yad'auki Ledar yajefa mata a cinya ya zura hannu cikin aljihu gaban rigarsa yaciro wayarta yad'aura mata saman ledar yaja mota cikin nishad'i.
Saida raheela ta share tsawon dak'ik'a biyar sannan ta bud'e idanu ta karo na farko da raheela bataji haushi abunda, Amar ya yi mata amma tsabar tauri rai da kafiya irin na raheela sai kawai tace ni fa gaskiya yaa Amar nafara gajiya da wannan al'amari naka ta yaya kake so mayarda ni kamar _lollipop_ na fad'a maka bana sonka na tsane ka miyasa bazaka fitarda ni daga zuciyarka wallahi duk ranarda ka k'ara tsotsa mini baki sai na sharyarda kai mamaki har tagama zabga iya shegenta Amar bai dube ta ba _driving_ d'insa kawai yakeyi kuma babu alamar ya ji zafin maganarta mamaki yarufe raheela cikin zuciyarta, tace miyasa duk zafin wadannan magaganu da na furtawa _Hero_ bai nuna ya ji zafi ba"?
Ta yi shiru tana sak'e-sak'e ko ta bashi hank'uri sai kuma ta wata zuciya tace da ita kina bashi hank'uri zai fara tunani ko kinfara sonshi take raheela ta turbune fuska sai wani cika take tana batsawa har suka shiga garin Kaduna ba Wanda yak'ara kula d'an uwansa kuma raheela bata bude Leda da yabata ba kaitsaye Amar unguwar da iyayyen umma hajara suke da yake gidan yayan umma hajara Alhaji sadi ake zaman mak'ok'i saboda babu nisa tsanani sa da gidan mahaifin nasu Alhaji sambo Amar ya yi _parking_ batare da raheela ta kalle shi ba ta bude murfi mota tafita tana shiga falon gidan suka had'a ido da umma hajara cikin sanyi jiki raheela tak'arasa wurinta, tayi mata ta'aziyya a dak'ile umma hajara ta amsa raheela ta sada kai k'asa tanaso ta tambayi umma hajara mami da aunty amarya tana jin tsoro irin amsar da za tabata.
Amar ya shigo falon ya durk'usa ya yiwa umma hajara da sauran mutane falon ta'aziyya shima umma hajara ta amsa ba ya6o ba fallasa, daga bisani Amar ya mik'e yafita, don tsabar jarraba da rashin imani irin na dangin umma hajara saida suka yadawa raheela magana aunty asabe tace hajara wannan kamar amarya raheela"?
umma hajara ta kyabe baki had'e da cewa ba kama bace ita ce mai auren cin amana
Aunty asabe tace ikon Allah kwana uku da aure ace amarya tafito anyya kuwa hajara wannan 'yar taku, takai budurcinta gidan Amar"?
A tsoroce raheela tada'go idanu ta cike da kwala ta tsurawa umma hajara ido taji irin amsar da za ta bata....
[09/08 8:50 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA 🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

9⃣8⃣

Umma hajara ta yatsine fuska kamar gwaggo biri tace wane irin budurci"?
Ae tun a waje Amar yakawar mata da budurci babu abinda batasaniba domin ko zaman da tayi gidansa, a lokacin da na'eema tana Raye ba abinda suke aikatawa sai masha'a wannan tsinaniya da kike gani tuni Amar yagama kwalkwale ta ya tsotsi ta ya gama kwashe albarkatu jikinta.
Aunty asabe ta wani zaro idanu na munafuci da kilinbibi tace biri ya yi kama da mutum shiyasa aure da kwana uku tafito don ta nunawa duniya tagama sani dad'i da d'and'ano d'a namiji.
Wata mata da takasa kunne tana sauraro abunda ke wakana, tayi karaf tace gata yarinya k'arama ace kinsan d'a namiji tir da ke iyayyenki sunyi hasara haihuwa ana magana kina fik'i-fik'i da idanu 'yar banza mai idanu kamar fitila _vespa_
Umma hajara tace wannan tsohuwar kilak'i ce yarinya wannan k'ato da ki ka ga tafiya shine aboki lalatar ta tsabar yasan dad'inta ya kashe 'yar uwa ta ya aure ta.
Aunty asabe tace kice ```mijin 'yar uwa taa ``` ta aura kwarai kuwa umma hajara tafad'a tacigaba da cewa bak'ar algguma
shegiya tsananiya sai na zama ajalinki tashi
Ki ba mu wuri sai faman wari k'ato ki keyi Raheela ta fashe da matsanacin kuka, mai matukar cin rai ta tashi tsaye da jiri na d'ibar ta tanufi k'ofar fita saura mutane da ke cikin falon da basuji abunda ke faruwa ba sai faman bata hak'uri sukeyi a tunani su kukan mutuwa takeyi Amar na zaune ya hango raheela tafito tana kuka, tashiga mota hankalinsa yayi masifar tashi da sauri ya mik'e yanufi mota takifa kanta tsakiyar cinyoyinta tana gunji kuka, cikin sark'ewar halshe Amar yace.....

Jeeddah Aliyu🌹
[11/08 6:53 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [11/08 8:23 am] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA 🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

9⃣9⃣

Meke faruwa ne Raheela kike kuka"?
Tacigaba da rusa kukanta mai cike da bacin rai da k'onar zuciya tamkar, bataji tambayar da ya yi mata ba.
Cike da sanyi jiki had'e da alhini sanadi kukanta ya jawo ta cikin jikinsa, cikin sigar rarrashi yake magana _please raheela talk me_ miye musanbabi kuka ki"?
Nan ma raheela bata tanka ba saida tad'ago rinannun idanu ta ta dubi Amar tak'ara rushewa da kuka'
Amar yakara rud'ewa yace haba raheela na tambaya ki kin kasa bud'e baki ki bani, kuma kink'i daina kuka yakikeso nayi da rayuwata"?
Na tsani kukanki raheela yana jefa ni a yanayi na tashin hankali, na rok'e ki da ki share hawayenki saboda zubar su tamkar ana zubawa zuciyata tafasashe ruwan zafi ne.
Kuka yaci k'arfi raheela da kyar ta sarafa halshenta tace _please yaa Amar mu bar gidanan banaso na sake bud'e idanuwa na naganni a cikin sa
Mamaki ne ya sark'e Amar har yahadasa masa zaro idanu batare da yace komai ba yabi umarni ta ta hanyar fisga mota aguje, _driving_ yakeyi amma hankalinsa na kan raheela domin har yanzu kuka takeyi yana _parking_ raheela ta balle murfi mota, tafita da gudu tanufi _part_ d'in kaka, yayinda Amar ya yi mutuwar tsaye daga bisani ya Mara mata baya, kaka na kishigide a _parlour_ ta tana tauna goro raheela ta shigo aguje tafad'a jikinta tasaki mai k'arfin gaske dama ga raheela ta kware da kukan yankar kauna musanmman da taji a jikin kaka ae kuwa kaka ta rud'e matuk'a tace na shiga uku me zan gani haka raheela daga ina ki ke kardai wannan d'an banzan, narka ki yakeyi don wallahi Amar ba tausayi ne da shi ba.
Amar da ke tsaye a bakin k'ofa yayi karaf yace da yake ni ne mareni ki karkataciya kuuka mai dad'i hawa duk wata shara da ki ka kwaso kaina kike juyewa, to a wannan karo bani bane asalima bansan dalili kukanta ba sai ki tambaye ta tafad'a miki ke da kike da tausayi shugaba ta kungiyar talafawa marayu.
Harara kaka ta galla masa girar idonta ta mik'e tayi cirk'o-cirk'o tsan-tsan masifa da bala'i da aka jima ba'a ta6a ba ya motsa tace ta yaya ya za Ku tare sannan kace bagada masaniya akan kukanta ko kuma so ka keyi ka raina mini hankali"?
Kinga kaka karki sauke kwadon masifa da bala'i ki akaina yadda ki ke jin zafi da rad'ad'i kukanta nima haka nakeji
K'arya ka keyi Amar kasan dalilin kukanta kawai dai ba zaka fa'da ba saboda kasan ka zalunce ta.
_how many time kaka I told you I don't known anything about her cry_ ki tambaye ta da kanki _maybe_ ke ta fad'a miki.
A hazuk'e kaka tace kai Amar ka kiyayeni, shine ka juye baki kana turanci ka na banza da wofi to magafok yaci uwarsa
Amar ya rufe baki had'e da zaro ido yana kallon kaka, tun lokacin da aka fara buga wuta tsakani Amar da kaka raheela tadaina kuka tana sauraro su, gani za ta kwa6e musu yasa tace ni fa kaka, ba abunda yaa Amar ya yi min kuma baisan dalili kuka na ba.
_thank God_ Amar yafad'a had'ewa da zaunawa yace yanzu sai kifad'a mana dalilin kukanki, raheela ta sada kai k'asa ta fed'e musu daga biri har wutsiya ae kuwa kaka tasoma zazzga tijara da yanka kauna saida tagaji don kanta tayi shiru Amar kan dafe goshinsa ya yi ya kasa cewa komai daga bisani yad'ago yace Dan Allah kaka karki yiwa umma hajara magana, saboda irin wannan babbar magana za ta iya haddasa fitina musanman in Abba ya ji domin zai iya d'auka mumuna mataki akanta.
kaka tace me zai sa nayi mata magana ae duk abunda mutum ya yi don kansa jahilci ne yake dawainiy da ita har yanzu watan nadama ta ne bai tsaya ba amma a juri zuwa da tulu rafi waya zai fashe.
Amar ya yi murmushi had'e da cewa, tashi mu tafi _part_ d'in su mami mu gaida su daga nan mu wuce kinga mu bar lamtana ita kadai
Raheela ta narke fuska kamar za tayi kuka, da sauri kaka tace tashi Ku tafi 'yar albarka raheela ta mik'e tana murmushi, Amar kuma ya tabe baki kaka tace ina zuwa bara d'auko miki aya cikin zumudi raheela tace aya mai sikari kaka"?
Kaka tace eh!
Har kaka tadawo Amar yana aikawa raheela harara ita kuma tana murgud'a masa baki, kaka ta mik'awa raheela leda aya suka fice, kaitsaye part" d'in mami suka fara shiga mami tayi matuk'ar farin ciki gani su tak'ara yi musu nasiha dangane da zaman aure daga bisani sukayi mata sallama suka shiga part" d'in aunty amarya, sun tararda da ita zaune a _parlour_ da gudu raheela tafad'a jikinta, aunty amarya ta tureta had'e da daka mata tsawa ke miye haka"?
Wai yaushe za kiyi hankali maama ki gano cewa girma yakamaki kidaina wannan shashaci naki?
Raheela ta turo baki Amar ya gaida aunty amarya ta amsa cikin sakin fuska, raheela tace gaskiya ni banta6a gani _last born_ mai bak'in jini iri na abunda ki keyi min aunty ko su yaya Abdul da suke _first born_ bakiyi musu haka nan tak'arasa magana hawaye na zuba daga idanu ta, aunty amarya tayi murmushi had'e da jawo ta a jikinta tace !haba raheela kaka miye kuma abin kuka"?
Cikin sigar shagwaba raheela tak'ara narkewa ajikin aunty amarya
Yatsine fuska Amar ya yi had'e da mik'ewa tsaye yace to sarki shagwaba sai ki tashi mu tafi, ba yadda raheela dole ta mik'e suna shiga mota raheela ta d'auki leda da Amar yabata had'e da cewa bara naga miye a cikin wannan Leda da aka yiwa kirari da _gift_ d'in amarci in naga ba wani abin a zo a gani bane a fuska zan jefawa mutum kayansa.
Sau d'aya Amar ya dube ta ya kauda fuska.......
[11/08 11:51 am] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA 🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

1⃣0⃣0⃣

Raheela na bud'e Leda taci k'aro da tsaleliyar waya {phone} mai matukar kyau da tsada ta kurma ihu farin ciki ya lullube ta batasan lokacin da ta rungume Amar mahaukaci birki da Amar yataka yasa raheela ta dawo natsuwarta, inda Allah ya taimaka basu hau kan titi da sun had'a d'an 'karami accident{hatsari} Amar Yasauke gwaron numfashi yarike kunne raheela ya murd'e yace ke so kike mu yi accident {hatsari} koh"?
Kallon mamaki ta watsa masa daga bisani tace don nayi ihun farin ciki shi ne zai sa mu yi accident"?
_uhm_ tsanani dad'in wannan _hot hug_ da kika bani shine ya kusan haddasa mana _accident_ bakiji wani irin masifafe _shock_ da ya ratsa jinina saura kiris nasaki _steering_
Ta dage gira sama ta yatsine fuska tace, gaskiya yaa Amar kai maye mata ne kawai na d'an rungume ka sai ka susuce, ni fa ba da wata manufa nayi ba nayi ne don na nuna maka farin cikin siya min waya{phone} da akayi.
Amar ya lumshe ido yace raheela kenan mata ababe so ne duk wanda yace miki bayaso mata k'arya yakeyi don bai samu bane, ballatana ni da nakeda _fresh & sexy girl_ irinki ni da za ki taimaka ki k'ara min guda d'aya ni kuma nayi miki alk'awali zan siya miki _lollipop_
Ta zaro ido fuskarta ta baiyanar da tsoronta a fili daga bisani tace me zan k'ara maka"?
Yayi k'asa da murya yana wani lum-lumshe idanu yace _hot hug_ kafin raheela ta bashi amsa ya manna ta a k'irjinsa ya rungumeta tsam a jikinsa yana shinshina had'e da shak'ar k'amshi sai wani sauke zazzafa numfashi yakeyi, tuni yafara fita hayyacinsa raheela ta tak'ark'are ta damkara masa cizo a wuya baisan lokacin ya saketa ba yasaki ihun azaba, yayinda raheela tasoma kiciniyar mayarda _zip_ d'in rigarta saida Amar yad'auki tsawon _5 minutes_ yana jinyar wuyansa daga bisani yasake mata rankwashi yace mayya kawai wance bataso farin cikin mijinta, in ba dole ba me zanyi da mace irinki k'irji a bushe kamar kilishi tab'a ki kawai nakeyi ba abunda nakeji mata-maza kawai.
Ta juya a fusace ta dube shi ta nuna shi da yatsa idanu ta sun kad'a sunyi jajir tace k'arya kake yi yaa Amar ka kira ni da suna mata-maza da bakaji komai da baka dinga tab'ani ba, kuma wallahi sai kayi nadama kira na da wannan sunan.
Ya kalle ta ya kawar da kai yayinda ya ja mota yana dariya k'asa-k'asa abunda yak'ara k'ula da raheela kenan tace kaga malam kayi dariyarka iya son ranka nima lokacina na zuwa _I will take my revenge_
Amar ya kyakyale da dariya har yana dukan _steering_ daga bisani ya tsagaita da dariya da yakeyi yace _you are such a fool raheela_ ba abunda za ki iya raheela tayi shiru tana tunani lallai sai na nunawa yaa Amar ni cikkiya mace ce ba mata-maza ba sai na haddasa masa rashin baccin da ciwo kai ta juya ta dube shi tana wani cize lebb'e tayi murmushi kawai da wannan _drama_ suka shiga garin _abuja_
Da yake kowane su yadebo gajiya suna Shiga cikin gida kowane yanufi _room_ d'insa.

```BAYAN SATI D'AYA ```

kasancewa yau _weekend_ ne Amar bai cika fita ba sai in fitar ta zama dole, yana zaune a _downstairs parlour_ yana sanye da wando _three quarter_ da Riga marar hannu {armless}ta d'an yi _tight_ d'insh hannu shi rike da _newspaper_ ta _daily trust_ yana dubawa lokaci-lokaci yakan mik'a hannu shi, bisa _stool_ d'in da ke gabansa yad'auki gwagwani _Amstel Malta_ yana _sipping_ 'kamshi turareta ya sauka a hancinsa ya lumshe idanu, cikin zuciyarsa yace wannan 'yar Bana bakwai sai yanzu tagama dama tashi"?
Ya juya dube ta tasha kwaliyya cikin _English wear's_ wando _skintight blue colour_ da _top whites colour_ a gabanta a rubuta _Hot_ da _blue colour_ rubutu a lokacin gud'a Amar ya hadiye yawu had'e da sauke sanyaya ajiyar zuciya domin wanka raheela yagama tafiya da imani shi da sauri yad'auke idanu shi daga kanta.
A hankali tak'araso wajensa tayi tsaye tana kallon sa batare da ya dube ta ba yace wannan wane irin sabon fi'eli ne kin wani tsaya min akai"?
Tasaki murmushi mai sauti tace to bara na dawo gabanka, tadawo gabanshi yayinda numfashin Amar yafara fita da sauri -sauri tsanani sha'awarta ta kamashi....

Jeeddah Aliyu🌹
[11/08 6:54 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [11/08 3:50 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA 🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

1⃣0⃣1⃣

Har Amar ya mik'a hannu ya yi mata kamu kazar kuku sai kuma yadakata sakamako sautin kukan, lamtana da ya karad'e _parlour_ a tsorace suka nufe ta Kowane su yana tambayar ba'asi kuka nata da kyar ta bude baki tace yanzu nan yayana ya kirani a waya yace inna ta batada lafiya sosai shine nace bara na fad'a muku ina so in tafi k'auye yanzu nan saboda bansan wane hali take ciki ba.
_subhanalillah_ Amar da raheela suka fad'a a lokacin d'aya Amar yace Allah yabata lafiya yasa kaffara ce Raheela ta amsa da _Ameen_ Amar yacigaba da fad'ar ki je ki had'o kayanki mu kai ki _motor park_ {tashar mota} ke kuma raheela ki je chanza kaya tuni lamtana tanufi d'akinta yayinda raheela ta juya a sanyaye, zuciyarta cike da tausayi lamtana.
A maimako raheela ta chanza kaya sai kawai tasaka _after dress_ tad'auki _phone's_ d'inta tafito, lamtana na tsaye tana sharar hawaye raheela tace kidaina kuka lamtana insha Allahu inna za ta sami lafiya lamtana ta d'aga kai Amar yafito hannu shi rik'e da _car Key's_ suka fice, motar da Daddy ya ba raheela ita suka shiga, bayan su ajiye ta a _motor park_ Amar yafito da kud'i 'yan _0ne thousand_ na _20 thousands_ yabata yace ga wannan ki siyawa inna magani yak'ara Ciro _five thousands_ yace wannan kiyi kud'in mota Allah

Please Login or Register in order to submit comment