Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin da hajara take cewa, kudai yi abun kunya ya da kanwa suna aure gida daya don tsabage kwadayin a mallake abin duniya dama ci rani aka zo matukar ina raye bazan zauna da sadeeya a matsayin kishiya ba.
Ke dakata 'yar gadon mugun abu to aniyar ki ta sharri tabi ki hajja Rahee ce ta daka mata tsawa, hajja tacigaba da cewa da ba'a aure ke da ana auro ki, mafi alkhairi a tare da ke ki zauna lafiya da sadeeya ko kuma kiyi waje road" don ba ki zo da "block's a gara ki ba ballatana ki nuna mana baqin mulki da lami take yiwa sambo kiyi maza ki bace mini da gani 'yar gadon rashin tarbiya da sauri hajara tafice, daga falon saboda duk iskanci'ta tana masifar tsoron hajja.
Hajja ta juya wurin Abdullah tace kai kuma tun da kace za ka iya to kuwa dole ka jajirce ka zama tsayaye namiji in ba haka ba, hajara za ta mayar'da kai shanyaye kamar yadda uwar'ta ta mayar'da ubanta, tana karasa zanceta tafice daga falon fateema da Abdullah suka cigaba da rarrashin sadeeya tun daga ranar da sadeeya tashiga gidan,abdullah a matsayin matar'shi tayi ban kwana da farin ciki da kwanciyar hankali saboda hajara ta tsare gaba ta tsare baya duk don gani ta fitar'da sadeeya daga gidan Abdullah kowa ina taji labarin sabon boka sai ta kai mishi ziyara saidai babu biyan bukata kwatsan ana cikin wannan rungutsumi sadeeya tasami ciki saura kiris hajara ta hadiye zuciya ta mutu abunda take nema shekara da shekaru bata samu ba sai gashi da shigowar sadeeya tasamu tun daga, lokacin tasha al'washi sai ta zubar'da cikin duk wurin boka da taje sai yace mata tabbas sai sadeeya ta haifi cikin nan abinda yakara daga mata hankali kenan bayan wata tara sadeeya ta haihu tasami "twins" duka maza rana da ana mutuwa adawo da sai hajara ta mutu tadawo, don tsabar bakin ciki kasa zuwa tayi taga yaran ranar suna ta zagayo, aka radawa yaran suna abdulhakeem da abdulhaleem haka rayuwa tacigaba gaba da tafiya, wasu na cikin jin dadi wasu na cikin wahala sadeeya, tana daya daga cikin mutane da ke cikin wahala, saboda batada 'yanci tafito tsakiyar gida yanzu hajara na fitowa tafara zagin'ta ta, uwa ta uba ga sadeeya ba iya ramawa takeyi ba "twins" na da shekara uku sadeeya takara haihuwa wannan karo ma "twins ta haifa kuma duk maza aka rada musu suna sadeeq da saleem.
Ranar hajara daki tashiga ta rufe kofa tadinga rusar kukan baqin ciki tana cikin wannan halin kwatsan Anty asabe ta kawo mata, ziyara gani halin da hajara take ciki yasa ta tausaya mata ko zama batayi ba, tace tashi mu tafi daga wannan lokacin kinyi ban kwana da baqin ciki...


๐Ÿ–Šexcellent writers๐Ÿ–Š

Jeeddah Aliyu๐ŸŒน
[18/06 8:29 am] Jeeddah Aliyu๐ŸŒน: ๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†MIJIN
YAR UWA TAA๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†

๐Ÿ’•love story 2016๐Ÿ’•

Na Hauwa Shehu Aliyu๐ŸŒน

~9โƒฃ~

Hajara ta share hawaye fuskarta ta dauki mayafi da jikka suka fice daga, gidan drivern Anty asabe sai faman sharara gudu yakeyi kamar wanda zai bar duniya tuni sun fita daga cikin garin kaduna yana dauki hanyar Niger state" saida yayi kusan shiga garin minna sai kuma ya yanke wata hanya wanda babu kwata akanta sai jar kasa, haka ratsa daji daga karshe yasami wata 'yar karamar rugga fulani yayi, parking" saboda babu hanyar da mota za tabi zuwa gidan bokan suka fito daga cikin Mota suka soma tafiya da kafa, driven yana gaba suna biye da shi saida sukayi tafiya mai nisa gaske tun nesa suka hangi gidan boka duguzuu zana ce kewaye da gidan sai kayan tsafi da ke daure jikin zanar bukoki ne guda biyu a cikin gidan,Komai girman jikin mutum ba zai iya shiga cikin bukar ta tsaye dole, sai ka duqa saboda kankata kofar babban tashin hankali na farko da za ka fara fuskanta daga jefar kafar ka tsakiyar gidan boka duguzuu, shine wari ,wani masifafe wari na fitar hankali gidan yakeyi hajara ta toshe hanci ta da sauri anty asabe ta buge hannu'ta tace kinga hajara ki rufawa kan'ki asiri ki kuma rufa mini ni da nayi sanadiyar zuwan ki gidanan, karki kuskure ki qara toshe hancin'ki saboda abinda boka duguzuu yatsana kenan in kuma ki ka bari yaganki zai mayar'da ke abar kwatance hajara tafara tsorata da jin furucin Anty asabe.
Drivern anty asabe yace hajiya ni zan tsaya daga nan sai ku karasa cikin,bukar Anty asabe ta wuce gaba hajara ta mara mata baya suna karasawa bakin kofar suka ji wani irin masifafe wari yana musu barka da zuwa Anty asabe tace "ahuuwanku" gafara dai boka duguzuu dan hasarariya wata mushirika dariya suka fara ji tana fitowa daga cikin bukar gaba daya dajin yasoma amsa amon dariyar tasa, tsawon lokacin yadauka yana kwasan dariya daga bisani yace barka ku da zuwa 'ya'ya hasarari barka ku da zuwa abokan zuwa jahanama, barka ku da zuwa fadar boka duguzuu dan asarariya ku shi ku da kafar hagu a lokacin daya fargaba hade da firgicin suka ziyarce hajara jikin'ta yafara rawa Anty asabe nagani haka tariko hannuta suka, fada cikin bukar zaune yake gaban wata katuwar tukunyar tsafi baki wulik da shi fuskar'shi tamkar ta gwaggo biri idanu shi, jajir masu kama da garwashin wuta ga shi da kiba ciki sa kamar na mai cikin wata tara yana daure da walki na fatar damisa cikin sa, sai walkiya yakeyi kamar wanda yashafa mangyada ya zaro kafirai idanusa yadakawa hajara tsawa cikin muryar'sa mai kama da kukan jaki yace ke zauna da sauri hajara tadawo haiyyaci'nta cikin rawar jiki ta kai zaune....


๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†MIJIN YAR UWA๐Ÿ†๐Ÿ†
TAA๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†

๐Ÿ’•love story 2016๐Ÿ’•

Na Hauwa Shehu Aliyu๐ŸŒน

~1โƒฃ0โƒฃ~

Boka duguzuu dan asarariya ya watsawa mata mugaye idanusa ya bude bakin'sa mai kama da na alade yace meke tafe da ku mata masu neman biyan bukata"?
Cikin rawar murya hajara tace boka dama kishiya ta ce ta, takura ni ta hanani rawar gaban hantsi sai zazzaga 'ya'ya takeyi ni ko bata wata bantaba yi ba a taimaka boka a rufe mata mahaifa tadaina haihuwa in kuma da akwai wani taimako da za'a bani nima nasami nawa iri a taimaka min ni dai burina in haihu.

Tun lokacin da tafara magana boka duguzuu yake kallon ta gani ta dasa aya a zanceta yasa bude katon bakin'sa wani kafiri wari mai kama da mushi kare ya buge fuskar Hajara yace
angama bukatar'ki za ta biya aljana barahazaa" za ta biya miki bukatar'ki yadaga hannu'shi sama yasoma surutu da wani yare, shi kan'shi in aka tsure shi, ba zai iya fassara abunda yake cewa ba sai ga wata 'yar tukunya laka tafado cikin tafin hannu shi ya mikawa hajara yace kije ki binne ta kada ki bari wani, ido yagane ki kuma karki binne ta inda za'a iya hako ta indan ki kayi haka har abada sadeeya ba za ta kara haihuwa ba amma kuma duk ranar'da aka hako ta zan sadaukar da mahaifa ki ga aljani qudulu.
Jikin hajara yafara rawa boka duguzuu yakara dauko wata robar mai dauke da wasu ruwa yace wannan kuma ki shanye da kin shanye su za ki Sami ciki ki zube duk, kudin da ke cikin jikkar ki hajara ta zuge "zip" din "handbag" dinta tafito da dubu dari biyu ta ajiyewa boka duguzuu cikin hargowa boka duguzuu yace ke baqar ja'ira sauran dubu dari da ki ka bari cikin jikkar ubanki za ki siyawa goro da su"? Maza ki ajiye min kudina ku bace min da gani da sauri hajara ta ajiye ragowar kudin suka fice daga cikin bukar.

Duk yadda boka ya umurce hajara tayi ta aiwatar bayan wata uku sai ga hajara da ciki "woho-woho" hajara tamkar za tayi hauka sai takara bude shafi na iskanci tana yiwa sadeeya habaici bayan wata tara ta haife 'ya mace saidai hajara ba haka taso ba saboda namiji taso ta haifa, ranar suna aka radawa "baby suna Na'eema.....


๐Ÿ–Šexcellent writer's๐Ÿ–Š


Jeeddah Aliyu๐ŸŒน๐ŸŒน
[18/06 8:29 am] Jeeddah Aliyu๐ŸŒน: ๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†MIJIN YAR UWA TAA๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†

๐Ÿ’•love story 2016๐Ÿ’•

Na Hauwa Shehu Aliyu๐ŸŒน

~1โƒฃ1โƒฃ~

Hajara sai farin ciki takeyi sakamako gani sadeeya ta, share shekara takwas bata kara haihuwa ba, Amar da Na'eema sun shaku da junan su amar yana matukar sonta a, lokacin akayi auren hafsat kwatsan sai ga ciki ya baiyana a jikin sadeeya abinda yayi matukar girgiza hajara ta banzama wurin boka duguzuu, tun dawowar ta daga wurin boka duguzuu take kukan baqin ciki saboda boka yace aiki da yayi mata ya lalace kuma aljani dugulu ya cinye mahaifarta, duk yanda hajara taso ta zubar'da ciki sadeeya saidai "Allah bai nufi ciki da zubewa ba saida cikin sadeeya yayi watani goma chib sannan ta haifi 'yar ta kyakyawar gaske tun ranar suna aka radawa baby suna Raheela hajja Rahee na tsananin son raheela tun tana jinjira, bacci kadai ke raba ta da Raheela lokacin da raheela ta esa yaye hajja Rahee ta yaye ta tun daga lokacin rikon ta yakoma wurin ta dalili dayasa raheela ta tashi a sagarce, ta kuma hinjire bataji magana kowa, bata tsoron ko ta kwana balle ta tashi duk inda ake neman fitsarariya yarinya in aka kawo wurin Raheela dole a shafa fatiha lokacin da raheela ta kai shekara 13 a duniya tsiwa da fitsarar ta suka kara baiyana, tun daga yanayi maganar'ta za ka gano lallai wannan goyon kaka ce nazeer da na'eema suna matukar son raheela duk abinda za tayi sam basa gani laifin ta, saidai ma su goya mata baya raheela sai sheka iya shegen takeyi kuma ba wanda ya esa yayi mata magana hajja kaaka ta wanke masa allon sa wannan yakara ba raheela dama tacigaba da tsula tsiya son ranta raheela ,na cikin ganiyar sheka iya shege'nta yaa Amar yadira kasar 9ja wanda ya share tsawon shekaru bakwai a kasar Germany" yana karatun "medicine" dawowar Amar su mamee suka sami sauki iya shegen'ta saboda Amar lakada mata dan banza duka yakeyi, wannan yajanyo kiyayya zazzafa tsananin su, Amar ya tsani raheela haka ita ma ta tsane shi matukar Amar ya hadu da raheela sai ya dake ta.....

๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†MIJIN YAR UWA
TAA๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†

๐Ÿ’•love story2016๐Ÿ’•

Na Hauwa Shehu Aliyu๐ŸŒน

~1โƒฃ2โƒฃ~

AMDAWO LABARI*******

Raheela zaune tasaka "plate din abincin gaba tana kuka har wani shure-shure kafafu takeyi kaaka tana gefen tana sallah cikin shashekar kuka raheela tace na rantse yau ba zan ci abinci nan shine don tsohon wulakanci irin na umma hajara za ta saka kifi a miya bayan tasan banaso kifi kaaka ki gama sallah muje tafadi dalili da yasa tayi amfani da kifi Amar da ke tsaye bakin kofa yana kallon iskanci da raheela takeyi yaja tsoki yakarasa shiga dakin yasake mata rankwashi aka a firgice tadago idanuta tana kallon Amar tana shafa kan'ta yasaka kafar'sa yayi "ball" da ita goshin'ta yabuge gefen gado wani masifafe ihu na azaba tasaki ya rufe ta da duka sai ihu kiran sunan kaaka takeyi.
Kaaka na sallame sallah ko addu'a batayi ba ta mike tanufi Amar da ke ta faman jifgar raheela tasoma kachaniyar kwatar raheela daga hannu shi, gani yaki yasaketa yasa kaaka ta gantsara masa cizo a hannu ae kuwa ba shari yasaki raheela yasoma yarfe hannu'shi yana kallon fuskar kaaka, yace kaaka yanzu don nadake wannan fitinaniyar shine za ki cije ni"?
Kaaka ta galla masa harara tace matukar baka daina sauke hannu ka akan Raheela abinda yafi cizo ma zan iya aikata maka kai kenan kullum cikin dukan yarinya haka ko dazu kafasa mata baki, wannan ae zalunci ne da mugunta in har karfi ka ke takama da shi kaje waje kanemi tsara ka amar ya tabe baki, daga bisani yace ina tausaya miki kaaka lokacin da za ki fara karatun littafin danasani akan wannan turba ta sagarci da tabarbarewar tarbiya da ki ke doura Raheela akai 'ke kenan kullum cikin haushi da hayagaga akan wannan gantalalleliya yarinya cikin zafin zuciya kaaka tace yanzu don iskanci da wulakanci irin naka, amar za ka dubi tsabar ido na kace ina haushi ni kare ce da dinga haushi"?
wannan shine, kashedi na karshe da zan kara yi ma akan Raheela ba ruwanka da abinda takeyi saboda ba'a karkashen ikon ka take ba Amar yaja tsoki cikin konar zuciya yafice, daga dakin kaaka tabishi da zagi daga bisani ta koma wurin Raheela da ke durkushe tana shashekar kuka.....



๐Ÿ–Šexcellent writer's๐Ÿ–Š


Jeeddah Aliyu๐ŸŒน๐ŸŒน
[18/06 8:29 am] Jeeddah Aliyu๐ŸŒน: ๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†MIJIN
YAR UWA TAA๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†

๐Ÿ’•love story 2016๐Ÿ’•

Na Hauwa Shehu Aliyu๐ŸŒน

~1โƒฃ3โƒฃ~

Kaaka ta dagota tace maza share hawaye ki, Allah sai yasaka miki ita kuma hajara za ta hadu da fushi na don sai naci mutunci ta sai, tafada min dalili da yasa tasanya kifi a miya bayan tasan bakyaso raheela ta turo baki tace, kaaka wallahi na tsani yaa amar da umm Hajara da zan sami aron bindiga da sai na halbe su.
Na'eema tayi sallama takarasa shigowa cikin dakin fuskar ta dauke da
Murmushi, tace laifi me yaa Amar da umma'naa sukayi da raheela za ta halbe su"?
raheela ta murguda baki tace saboda duk gidanan su kadai ne suke duka na, na'eema tayi dariya tace "Allah ya huce zuciyar raheela ta hajja kaaka masu yi ba'a fadi hankaka maida 'da wani naki turnuku fada ibilissai yaro bai gani ba balle raba" kaaka tayi karaf takarasawa na'eema ta hanyar cewa wane shi, dan ubansa kuma kijawa hajara kunne hawaiyar'ta taki yaye rama ta naga alamar tanaso nayi mata kidin zari irin wanda tun lokacin da lami ta haife ta ba'a taba yi mata irin sa ba.
Na'eema ta bata fuska tace haba kaaka wannan wane irin yanka kauna ne"? Ae ko don albarkaci na yaci ace kin ragawa umma" ni kenan kullum manne a dakin'ki kina ci mini fuska ta hanyar zagin mahaifiya taa.
Kaaka ta galla mata harara tace dama barewa ba za tayi gudu ba 'da ta yayi rerafe raheela da gidan ubanta amma, masifa da bala'e da kuma mugun alkaba'e da hajara takeyi mata yasa tadaina shiga bangare ku.
Na'eema ta cire hijab dinta ta nufi "bathroom" tana cewa ae sai kiyi ni ba zan iya wannan tashin hankali ba ke kenan kullum cikin masifa bakin'ki ko ciwo ba yayi.
Kaaka tace masifa na chan tare da hajara kuma, yadda bataso haka za tacigaba da gani saidai hasada da baqin cikin raheela su zama ajali'nta a shagwabe raheela ta riko hannu kaaka tace kiyi shiru haka nan kaaka kaina yafara ciwo da sauri kaaka ta riko kan'ta tafara yi mata tofi..

WASHE GARI******

Da yamma Amar Yana zaune bisa farar kujerar roba a "compound" din gida hannu shi, rike da "newspaper" ta dailytrust" yana dubawa da karfi yaji an bude kofar shigowa cikin gidan yadago idanushi ya mayarda hankali shi a bakin "gate" raheela ya gani taja birki sai faman haki takeyi, ga wata uwar damara da taci da hijab din'ta kanta babu dan kwali'n jela gashinta sai reto takeyi a bayan'ta amar ya yafito ta da hannu'shi nan take tafara bubuga kafafu a kasa yatsu shi uku yadaga mata alamar in ya kirga uku bata zo ba tasan sauran, da gudu takarasa wurin sa ta marairaice murya kamar mutuniyar kirki tace dan Allah yaa Amar kayi hakuri na rantsi ba wanda na tsokana, kayi hakuri karka dake ni kalli baki na da goshi na duka da kayi min jiya ne ko warke, banyi ba.
Wani mugun kallo yaa Amar ya watsa mata ya kuma daka mata tsawa ta hanyar, cewa "shut up stupid girl"?
Da sauri Raheela ta rufe bakin'ta da tafin hannuta sai wani zare idanu takeyi yakara daka mata tsawa yace oya kiyi "kneel down" raheela ta zube gaban shi yaa Amar ya tsura, mata idanu da sauri Raheela ta kawar'da fuskarta tace ni kadaina kallo na da idanu ka na "horrors" Ko so ka keyi nayi mafalki ka takarasa magana hade da murguda baki.
Yaa Amar yayi shiru kamar mai nazari daga bisani yace raheela yanzu don bakida kunya za Ki danganta ni da "horror"?
Turo baki tayi tace to ae ni yaa Amar ba karya nafada ba kowa "eye's ball" dinshi " black ne amma banda kai. Yaa amar ya galla mata harara yace ke munafuka nawa wane irin colour ne?
Yatsine fuska tayi daga bisani tace "sky blue" yaa amar yayi murmushi, yace umhh..
Da sauri Raheela tace yaa Amar daga kan'ka sama kagani zaro idanu yayi yace me zan gani"?
Tace kadaga zan nuna maka "something very important" yaa Amar ya yatsine fuska yace in nadaga banga komai ba sai na fanfalla miki mari yakarasa zance sa hade da daga kai sama raheela tace yaa amar kaga yanda giragizai suke "sky blue" haka ma "eye's ball" dinka yake wani wawa tsoki yaa amar yaja ya sake mata rankwashi a gigice raheela ta dafe kai, yace ina dan kwali'n ki"?da kyar tace yana ciki yace kodai kin jefar da shi wurin dambe"?
Ta girgiza kai yace tashi ki bace min da gani ta mike tsaye tanufi bangare su "direct" bedroom din Anty amarya ta wuce da yake haka suke kiran sadeeya jin karar ruwa a "bathroom" yasa tayi kwanciyar ta bisa gado Anty amarya na fitowa daga "bathroom" tayi 4 eye's da raheela ta murtuke fuska tace ke lafiya me yashigo da ke nan"?
Raheela ta mike zaune tace zuwa nayi naganki, Anty amarya ta galla mata harara tace kidai zo daukar magana wurin hajara raheela ta girgiza kai hade da cewa ni ba wuri'nta na zo ba Anty amarya ta tabe baki tace banaso fitina raheela nasan halinki sarai baza ki fita bangare nan ba batare da kin tsokani hajara ba don haka, tashi ki koma bangare ku raheela ta fashe da kuka cikin shashekar kuka tace me, nayi miki Anty amarya duk lokacin da nazo wuri'nki kidinga korata sai kace bake ki ka haife ni ba batare da ta jira amsar da Anty amarya za ta bata ba ta fice daga dakin a babba falon gidan taci karo da umma hajara zaune ko kallota raheela, bata yi ba kaitsaye ta nufi kofar fita hajara ta bushe da dariya tace yau kuma waya taba uwar rigimamu take kuka harda su majina a fuska"?
Raheela taja birki hade da juyawa ta watsawa hajara harara ta kuma ja mata tsoki tace ba'a saniba, hajara tace to gantalalleliya 'yar gadon mugun abun fitsara za kiyi min"
Raheela ta murguda baki tace eh' anyi miki fitsara kiyi duk abunda za ki iya hajara tace watakila sata ki kayi, akayi miki duka shine ki ke kuka raheela tace "Allah ya esa ban yafe miki ba tunda ki ka yi min sharri sata, hajara tace ae raheela sata gadon ta ki kayi waye bai san buzaye da sata kamar gafiya.
Raheela takara harzuka da jin furucin umma hajara tace ke ma ae kina sata don kin taba yiwa Abba naa sata har kaaka tace wurin bokaye za ki kai kudi Allah yatoni asiri ki......


๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†MIJIN YAR UWA TAA๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†

๐Ÿ’•love story 2016๐Ÿ’•

Na Hauwa Shehu Aliyu๐ŸŒน

~1โƒฃ4โƒฃ~

Hajara tayi kukan kura ta nufi raheela da gudu raheela takarasa ficewa daga falon, hajara tafara zage-zage kamar mahaukaciya, shegiya tabataciya, yarinya haka zaki qare a gantale matukar ina numfashi a doron duniya bake ba aure sai na mayar'da ke abar kwatance, Anty amarya da ke sallah ta sallame tasoma lazimi daga bisani tadaga hannaye ta sama tasoma nemawa 'yarta kariya daga ubangiji talikai.

Raheela na fitowa taci karo da nazeer ihu tasaki tana shafar goshin'ta da ya buge kan nazeer.
Nazeer yadago yace "oh shirt" raheela tace "oh no" suka kara hada baki sukace "oh yes" hannu yabata suka tafa dama wannan shine dabi'ar su da kyar nazeer da raheela su hadu basuyi wannan abun ba nazeer yace haba tawan wai sai yaushe za kiyi hankali kidaina wannan gudun naki na fanfalaqi"?
Raheela ta harara shi tace sai ranar'da kayi hankali nima zan yi saboda ni da kai jirgi daya ya kwaso mu nazeer yace karya ne, wallahi nafiki hankali da natsuwa raheela tace mu je a tambaye kaaka tafadi wanda yafi hankali tsakani ni da kai, nazeer ya kyakyace da dariya yace, wayo ki keso kiyi min koh"? Saboda kinsan kaka za ta goyi bayan'ki raheela tayi murmushi, tace ba wani wayo kawai dai nafika hankali da wannan dogon sarhi suka karasa bangare kaaka.

Haka rayuwar raheela tacigaba da tafiya a karkace duk lokacin da daddy yayi yiwa kaka, magana akan tadaina shagwaba raheela sai ta aza kuka wannan yasa "daddy yadaina magana dama shi, abba abdullah ba magana yake yi ba yaa Amar ne kadai yake da jarunta dukan raheela a zaune lafiya tun kaka na kai kara shi wurin mamee har tagaji tadaina saidai duk lokacin da yadaki raheela tayi mishi Allah ya esa.


BAYAN SHEKARA UKU*****

Raheela an zama 'yan mata hankali da natsuwa sun yafara shigarta a lokacin tana shekarar karshe a secondary school" na'eema kuma ta kamalla "degree dinta..


๐Ÿ–Šexcellent writer's๐Ÿ–Š

Jeeddah Aliyu๐ŸŒน๐ŸŒน
[18/06 8:29 am] Jeeddah Aliyu๐ŸŒน: ๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†๐Ÿ†MIJIN
'YAR UWA TAA๐Ÿ†๐Ÿ†

๐Ÿ’•love story 2016๐Ÿ’•

Na Hauwa Shehu Aliyu๐ŸŒน

~1โƒฃ5โƒฃ~

Note:- sharhi akan masu yada maganganu akaina kuna cewa buk din MIJIN YAYA TAA babu komai cikin sa sai batsa da badala to kusani ba ni nake rubuta shi ba, suna buk din'mu ne yazo daya Shiyasa na chanzawa nawa suna zuwa MIJIN 'YAR UWA TAA ynz kuma yarage naku sai kuje ku zagi NBABA MADA saboda shine yake rubuta mijin yaya ta mai batsa kuma kusani duk wanda, yakira baby amrah ya zagi ta shi da Allah kuma bata yafe ba sai Allah yayi mata mumuna sakayya akan'shi masoya na da suka dinga kare ni na gode Allah yasaka da alkhairi makiyya na da suka dinga zagi na da yada maganganu marasa kyau akaina kuma na gode Allah yasaka da alkhairi.
Lurv u oll my fans๐Ÿ˜


Alhaji Abdullah zaune a falon shi, umma hajara na gefen sa ta wani hakince ita a dole ga uwargida anty amarya tana zaune bisa "one star" da ke facing" dinsu raheela da na'eema suka shigo suna rike da hannu juna kaitsaye raheela ta nufi wurin alhaji Abdullah cikin shagwaba ta zauna bisa hannu kujerar da yake zaune a kai hannu ta rike da "Swรฉet din lollipop" tana tsotsa sai kace 'yar yaye umma hajara ta watsa mata harara hade da cewa to fitsarariya uwar 'yan fitsara ke kinfin karfin zama kasa ne"?
Raheela ta yatsine fuska tacigaba da tsotsan "lollipop dinta tana kada kai alamar rashin mutuncin'ta nason motsawa, aunty amarya tadaka mata tsawa tace ke bada ke ake magana ba da ki ka wani shantake"? Maza ki sauko kasa raheela ta turo baki ta zauna kasa alhaji abdullah yayi murmushin, yace banaso kuna takurawa mama'naa ku bar'ta tayi abunda takeso kurciya ce kawai take damunta wata rana kamar batayi ba.
Umma hajara tasaki kalma shahada harda su tafa hannu tace kai abdullahi ka ji tsoron "Allah yanzu wannan katuwar baliga za ka danganta, ta da kurciya Allah na tuba wannan da a kauye take har ta wuce muzalin aure.
Raheela ta kyabe baki tace kai umma harda su kalma shahada sai kace kinga macijin, kuma ki daina kiran suna abba na bakatatan ba ko dan lakabi umma hajara ta galla mata harara kamar kwayar idon'ta yafado kasa tace to iyani mai dan doro shi uban naki baiyi korafi akaina ba sai ke shugaba ta marasa kunya gani yadda umma ta zakalkale tana kunfar baki yasa abba yataka mata birki ta hanyar cewa kefa hajara bakida ta natsuwa miye na biyewa Maama kina tada jijiyoyi wuya da 'yar cikin'ki wannan ae hauka ne.
Aunty amarya tace amma abban na'eema ita ma kan'ta maama ba kanwa lasa bace a wasu lokuta itace ummul-aba'esi tsokano fitina a

Please Login or Register in order to submit comment