Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gida, Suleiman ya marairaice murya yace tun yanzu _my heartbeat_ wallahi ban gaji da gani wannan _beautiful face na ki ba_ raheela tayi murmushi had'e da cewa gobe ma rana ce za ka iya dawowa, suleiman yasaki murmushi jin dad'i yace na gode da wannan damar da ki ka bani _my heartbeat_
Raheela tace _you are highly welcome_
Amar yayi sallama yashiga falon da gudu fahad da jabeer suka rungume shi _uncle oyoyo_ fuskar Amar d'auke da murmushi yace ina yaya hafsat"?
Fahad yace tana _bedroom_ bara na kira ta Amar yanemi kujera ya zauna yaya hafsat tafito tana rik'e da kausar tace barka da zuwa likita Amar yayi murmushi had'e da cewa yauwa babban yaya da fatar na same Ku lafiya"?
Lafiya qalau ya 'karfi jiki?
Jiki _Alhamdullah_ raheela tayi sallama tashigo yaya hafsat ce ta amsa mata yayida Amar ya watsa mata mugun kallo Wanda ya hadasa mata fad'uwar gaba.......

Jeeddah Aliyu🌹
[01/08 8:34 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [01/08 12:53 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

8⃣1⃣

Raheela tanemi kusa da yaya hafsat ta zauna, tayi kamar bata ga Amar ba sai fama _operating_ d'in wayar ta takeyi yaya hafsat takasa hak'uri tace raheela baki ga Amar bane"?
Na ganshi mana ae mu gaisa a 'kofar gida Amar ya bud'e baki da hanci yana kallon raheela, daga bisani ya kawarda fuskar sa ta mik'e ta nufi d'akinta Amar yabita da kallon yayida yaya hafsat take kallon shi cikin tausayawa tace Amar
Cikin tsanani jin kunya Amar yajuyo yace _Na'am_ yaya hafsat"
Na fahimci cewa raheela ita ce farin ciki ka, me zai hana kabani dama na sanarda kaka tayi magana da su Daddy, su a aura maka ita domin samu kwanciyar hankali ka tunda _addini_ bai hana ba na tabbata suma za suyi farin ciki da jin raheela za ta maye gurbi 'yar uwa taa.
Amar yasauke gwaron numfashi cikin murya mai matukar ban tausayi yafara magana, tabbas yaya hafsat ina masifar son raheela amma a yanzu na ha'kura da ita saboda banaso na zamo sila kawo sabani a zuri'ar mu ita kanta raheela bata sona _she hate me, so much_
Yaya hafsat tayi ajiyar zuciya tace raheela ba matsala bace ni nafi kallon umma hajara a matsayin babbar matsala da za ta kawo cikas tsakani ka da raheela, amma kabar komai a hannu na _I will try my best_ nagani burin ka yacika Amar yayi murmushi jin dad'i yace na gode yaya hafsat da wannan taimako naki agareni yaya hafsat tace amma da cewa kayi ka ha'kura da ita"?
Fad'a kawai nayi yaya hafsat son raheela ya riga yayi min illah, ko yanzu nan da na shigo naganta da wani shirgege 'kato baki ga yadda zuciyata ta dinga tafarfasa ba yaya hafsat ta kyakyale da dariya tace to kayi 'kok'ari ka siye zuciyata, tadaina kula shirgege 'kato
Murmushi Amar yayi yace zuciyar raheela ce tamkar dutsi shigar ta yanada matukar wahala.
Karka zama matsoraci Amar ni a ganina babu zuciyar da baza ka iya ratsawa don haka kayi amfani da damar ka ta d'an namiji ka mallaki zuciyar raheela shikenan yaya hafsat zan gwada amma Dan Allah kidaina barinta tana fita banaso naganta da kowa yaya hafsat ta tabe baki had'e da cewa kaji da shi.
Da Wannan zance Amar yayi sallama da yaya hafsat yawuce gidanshi katsaye _bathroom_ yanufa yasakewa jikinsa _shower_ bayan yafito daga _bathroom_ yasaka _pajamas_ yafeshe jikinsa da turare _pure blue_ ya haye gado ya lumshe idanu shi yasoma tunani irin rayuwa da yayi da na'eema _Allah sarki my na'eema kintafi a dai-dai lokacin da nakeda buri kyautata miki_ ya sauke gwaro numfashi yajuya ya janyo _pillow_ ya rungume a 'kirjishi yayida zuciyarsa take hasko masa kamanu raheela, ya mik'a hannu bisa _bedside_ yad'auki wayarsa yayi _dialling_ number raheela
Kwance take takasa baccin sai faman juyi takeyi bisa gado jin _ringing_ d'in wayarta yasa taja tsoki baiyane tace wash Suleiman yana son ya kashe ni har da dare ba zai barni na huta ba"?
Yaa Amar tafad'a had'e da zare ido me yaa Amar yake nema a wurina a dare nan"?
Tad'ago idanu ta, ta kalli _agogo 10:30pm_ yayida wayar tacigaba da _ringing_ kamar ba zata d'auka ba sai kuma ta chanza shawara tayi _picking_
A sanyaye tace _hello_ yasaki ajiyar zuciya sautin yasauka a dodo kunne raheela, batasan lokacin da ta lumshe idanu ta ba tsawon da'ki'ka uku suka d'auka ba Wanda yace komai gani shiru yayi yawa yasa raheela tace in baka abin cewa zan ajiye waya, Amar y marairaice murya kamar zai yi kuka yace _raheelaaa_ yadda yaja sunan nata ya haddasawa tsigar jikinta tashi amma tauri rai irin na raheela sai kawai ta fuske kamar bataji komai ba tace _ya akayi ne Mr hero_?
_Bakida kirki raheela ina matsayin yayanki amma bakya girmamani na share tsawon wata d'aya a Germany ina jinya baki tab'a daga waya ki, kirani ba nadawo kuma kin kasa yi mini sannu me nayi miki raheela da ki ke nuna mini zazzafa 'kiyayya_?
Ba kayi mini komai ba yaa Amar kawai dai banada ra'ayi magana da kai banaso kowace ala'ka tak'ara shiga tsakani mu ina mai baka shawara kafita hanya ta saboda na tsane ka bana sonka yaa Amar.
Da sauri Amar ya katsi wayar domin ba zai iya cigaba da juri jin mumuna kalaman raheela ba mik'e zaune yayi tagumi yasoma zance zuci ya zanyi da sonki raheela?
Ko za ki yanka ni raheela bazan daina sonki ba.
Haka Amar yacigaba da sintiri a gidan yaya hafsat da raheela taji muryar sai ta shige d'aki ta murza _key_ ba za fito ba har sai yatafi in kuma ya kira ta da waya tak'i d'agawa damuwa ta taro tayiwa Amar yawa duk yabi ya rame ko lokacin da yayi hatsari baiyi ramar da yayi a yanzu ba gani yadda yake ramewa kada ciwo zuciya ko hawan jini Yakama shi yasa yaya hafsat ta yanke shawara yiwa raheela magana raheela magana Amar ce nakeso muyi raheela ta bata fuska had'e da cewa maganar yaa Amar kuma"?
[01/08 8:34 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

8⃣2⃣

Kwarai kuwa maganar Amar, raheela yakamata ace zuwa yanzu kin amince da soyayya da Amar yakeyi miki,ki tausayawa d'an uwanki ki dubi yadda Amar yarame yafita haiyaci sa duk a dalilin son da yakeyi miki ina 'kule da ke duk lokacin da yazo gidanan sai ki shige d'aki ki boye kuma kinsan saboda ke yake sintiri a gidanan.
Raheela tayi shiru tana kallon yaya hafsat kamar yau ne tafara ganinta daga bisani tace haba yaya hafsat kwata-kwata _watani_ hudu da mutuwa yaya na'eema ace anfara yi mini maganar yaa Amar wannan wane irin gwad'o ne"?
Koda ace inaso yaa Amar ba zan iya aure shi ba saboda ```mijin 'yar uwa taa ``` ne nikan ba zan iya wannan abin kunya ba haka kawai ina zama-zama na yaa Amar yanaso yad'auko abunda yafi k'arfi na yanufo ni, da shi nace bana sonshi dole ne.
Yaya hafsat ta tsurawa raheela ido tana mata kallon mamaki daga bisani tace raheela kada ki jahilci abinda baki saniba addini ya halattawa Amar aure ki babu inda akayi hani da ```k'anwa bata aure mijin yaya taa ``` don haka kuskure ne ki dinga daganta hakan da _abin kunya_ raheela ta share hawaye ta, tace bazan boye miki ba yaya hafsat banaso yaa Amar kuma ina rok'o ki da ki rufe wannan zance anan banaso su ```daddy su San da wannan zance ```
Yaya hafsat tayi murmushi tace shikenan raheela insha Allahu ba zan 'kara yi miki zance Amar amma inaso kisani Amar yaso ki tun kafin kinsan ```wacece ke ``` Kuma ina da ya'kini cewa zai cigaba da sonki har karshen rayuwa sa.
Raheela ta sunkuyarda kai 'kasa tana sharar hawaye yayida yaya hafsat ta mik'e tafice daga falon tabar raheela zaune tana kuka.

_WASHE GARI_
Bayan raheela taje _school_ ta zayanewa Ayshat yadda sukayi da yaya hafsat, yanzu fisibillahi in naso yaa Amar ae ban yiwa yaya na'eema adalci ba kuma tun tana raye nayi mata alk'awali bazan tab'a son mijin ta ba shine yanzu don bata raye sai na k'arya alk'awali gaskiya ni bazan tab'a iya cin amanar yaya na'eema.
Dad'i na da ke raheela shirme wane irin cin amana ae ita na'eema tun tana raye tasan ba ita yaa Amar yake so ba ke yakeso raheela, 'kaddara ce ta had'a su kuma a yanzu mutuwa ta raba su wallahi yaa Amar yana matuk'ar bani tausayi ko jiya da yaje gida na yana yi mini _k'orafi_ akan irin wulak'anci da ki ke yi masa saida ya zubarda hawaye _kai so masifa ne_
Cikin bacin rai raheela tace dallah dakata malama ke ki ka bashi izzini yaje gidanki koh"?
Ayshat ta galla mata harara had'e da cewa gida na yaje ba gidanki ba don haka ba ruwanki kuma ina tausayi miki ranarda za ki fad'a a tarko son yaa Amar na tabbata har, hauka sai kinyi.
Raheela taja tsoki tace ni _raheela abdullah matawalle_ naso yaa Amar _god forbid_ ko a mafalki bazan tab'a son yaa Amar ba don haka ki rubuta ki ajiye duk ranarda naso yaa Amar ki sakani a gaba kiyi mini dariya iya son ranki.
Ayshat ta kyakyale da dariya tace kidaina cika baki raheela _shi so baya neman izzini shiga zuciyar d'an-Adam kawai yakeyi so cuta ne raheela in yasami muhalli a zuciya ba 'karama barna yakeyi ba_
Ina ruwa na da zaman shi cuta duk Wanda ki ka ga ya cutar shi yayi sake ni nan zuciyata a datsi take bana tunani ina cikin _jinsi_ da so yake cutarwa.
Ayshat ta tabe baki had'e da cewa chan ta matsi miki.

```BAYAN SATI D'AYA```

Raheela tadawo daga _school_ a gajiye tashiga falon ta tararda yaya hafsat da su jabeer zaune tun kafin ta zauna yaya hafsat tace ke kadai mu ke jira raheela za mu tafi Kaduna yanzu nan raheela ta zaro ido tace Kaduna kuma lafiya za mu tafi Kaduna da yamma nan"?
Lafiya qalau _family meeting_ za'ayi ba yadda raheela ta iya dole ta shirya suka d'auki hanyar Kaduna.

```KADUNA```

A lokacin da su raheela suka eso falon Daddy a cike yake da 'yan uwa suna had'a ido da Amar ta murgud'a masa baki shi kuma yayi murmushi suka bi sahu mutane falon suka nemi wuri suka zauna yayida abdul haleem yabud'e taro da _addu'a had'e yiwa marigayiya na'eema addu'a_
Daga bisani daddy yafara magana dalilin da yasa muka taro anan shine muna so gobe _jama'a_ insha Allah za mu cikawa marigayiya na'eema wasiya da tabar mana.
A zuciya raheela tace _Allah sarki yaya na'eema harda wasiya tabari_
Yayida daddy yacigaba da ce wa wasiya da na'eema tabari shine had'a Amar da raheela aure tun kafin daddy yadasa aya Amar da raheela da kuma uwar gaiyya umma hajara a lokacin d'aya suka mik'e tsaye kowane su da yanayi tashin hankali sa.....

Jeeddah Aliyu🌹
[02/08 7:32 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [02/08 11:14 am] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

8⃣3⃣

Umma hajara ta bi mutane falon da k'as'kantace kallon daga bisani tasoma tafa hannaye, tace lallai mutane gidanan kun kware a fagge na cin amana da zalunci abin kunya gaba Ku ka bashi ba baya ba to na rantsi da Allah ba zan amince kowane d'a mace ya tozartani a ido duniya ba wannan kwamacala har ina 'kanwa ta aure mijin yayarta dama ni nasan akwai mak'ark'ashiya a mutuwa na'eema haka umma hajara tacigaba da zubda ruwan rashin mutunci kowa ya zuba mata ido saida tagaji don kanta tayi shiru.
Abba ya mik'e tsaye cikin kwanciyar hankali ya nuna mata kofa da hannu shi yace tunda kin gama ae sai kifita ko"?
Umma hajara sai faman huci takeyi kamar kububuwa tace kaji tsoron Allah Abdullah kana nuna banbanci a tsakani 'ya'ya ka kafifita raheela akan saura 'ya'ya ka tun na'eema tana raye kafi son raheela akanta yanzu kuma bata raye kafito da wani sabon salon cin amana ka d'auki mijinta sukutun kabawa raheela wannan wace irin 'kiyayya ake nuna min a gidanan"?
tak'arasa zance ta had'e da rushewa da kuka Abba yafisgo hannu ta da k'arfi ya cilla ta waje yace kifita ki ba mu wuri ke kin manta da irin zalunci ke da 'yarki Ku ka yiwa Amar wallahi koda ace Amar bayaso raheela na'eema ta mutu sai na aura masa ita ballatana ita ce zabi sa kai Amar a matsayi na na mahaifi raheela na mallaka maka ita kyauta'
Raheela da tayi mutuwa tsaye hawaye kawai ke fita daga idanu ta sakamako jin furunci Abba na 'karshe yasa ta daka tsalle tayi fad'uwa 'yan bori, tace wayyo, wayyo jama'a ku taimake ni Ku kawo mini agaji zuri'ar Abdulrazaq matawalle sun had'e mini ka za su kassara rayuwa ta wallahi banaso yaa Amar, ni bazan aure ```MIJIN 'YAR UWA TAA ``` da na aure yaa Amar gara na 'kare rayuwa ta a _prison_ kai, kai ina wallahi ba zan aure yaa Amar ba ke kuma umma hajara da ki ke cewa Abba yafi sona ba gaskiya bane yafi so kowa akaina Abba ya tsane ni baya sona aunty amarya ta mik'e tsaye ta wanke raheela da mari a maimako raheela tayi shiru sai ma tak'ara 'kaimi tacigaba da zuba sai kace zautata na gwance yadda Ku ka yi mini taro dangi ku taso kuyi ta duka na sai na mutu da na aure yaa Amar.
Daddy da yaga abin na raheela yafara yawa ya mik'e ya kamota yace raheela kiyi hak'uri ki bamu had'in kai mu cikawa 'yar uwarki alk'awali da muka d'auka mata da ace Amar yana da wata illah bazan amince a aure miki shi ba, raheela tak'ara fashewa da kuka tace shikenan 'karshe na yazo ya Allah ka ji'kaina ba don na mutu ba domin na tabbata ko mutuwa nayi duk gidanan ba wanda zayi min _addu'a_ saboda ba su sona tajuya wurin kaka tace kaka kina kallo za'a had'e ni da mugu maras tausayi da imani abdulhaleem yadaka mata tsawa ke dallah ki yiwa mutane shiru In banda ```'KADDARA SO ``` me yaa Amar zayi da ke mahaukaciya kawai fitsarariya
Dallah dakata malam nazee ne ya takawa abdulhaleem birki cikin zafin rai da konar zuciya yace kadaina yi mata _shouting_ ka barta taji da zafi d'aya mana da sauri raheela tafisge daga rik'o da daddy yayi mata ta nufi wurin Nazee ta fad'a jikinsa tace dan Allah yaya nazee ka taimake ni karka bari a aure mini yaa Amar _please yaya Nazee help me I don't love him I really hate him I don't wants to be with him any more_
Hawaye suka zubo daga idanu nazee yace _calm down raheela_ da ina da yadda zanyi na rabaki da aure nan da nayi kiyi ha'kuri kawai amma wallahi ancuce ki aure dole sai kace muna 'kauye
Mami ta gallawa Nazee harara tace ka fa nazeer bakada mutunci a maimako ka rarrashe ta sai ka buge da zugata
Ni fa mami ba zugata nakeyi ba gaskiya ce nafad'a a wannan karo yaya hafsat ce ta karbe zance ta hanyar cewa dallah ka rufewa mutane baki munafuki kawai da bayaso alkhairi
Daddy yadaka masu tsawa yace miye haka banaso shashaci Abba yace kyale su kawai yaya kowa ya fad'i albarkaci bakin sa insha Allah gobe Raheela ta zama mallakin Amar
Sai lokacin kaka tayi magana tace ae tun farko laifi Amar ne da baisan yadda ake bayyana so ba barshi dai da d'an banza fad'i rai da miskilanci tsiya ni ba ruwa na chan ta matsi muku kaka tak'arasa zance ta had'e da ficewa daga falon yayida Abba da daddy suka Mara mata baya.
Raheela tajuya wurin da Amar yake zaune ya wani aza 'kafa bisa 'kafa yana tauna _chin gum_ sai faman danna waya yakeyi hankali sa kwance'
Raheela tace yaya Nazee kalli yadda wannan _wicket man_ d'in ya hard'e 'kafafu yana kallon mutane a wulaqance Allah kadai yasan irin mugun tanadi da yatanada min a ciki zuciyarsa.
Nazee yace karki damu Allah yafishi amma yadda tsofafi nan suka cika falon nan tabbas mai hanaki zama matar yaa Amar sai Allah zo muje na baki wata kyakyawa shawara da sauri Mami tace kai nazeer ka kiyayye ni wace irin shawara ce za ka bata da mu baza mu bata ba"?
Amar yaja wawa tsoki yafice zuciyarsa na tafarfasa jin yakeyi kamar ya rufe nazee da duka yana fita nazee yaja hannu raheela suka fice daga falon......
[02/08 7:31 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA 🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

8⃣4⃣

Suna fitowa suka hango Amar cikin mota zai fita raheela ta bi motar da kallon takaici, kaitsaye _part_ d'in kaka suka shiga raheela tafad'a jikin kaka tafashe da kuka tace Dan Allah karki bari a had'ani da yaa Amar wallahi banaso shi na tsane shi kaka tace haba raheela miyasa bakida han'kuri da yafiya"?
Amar d'an uwanki ne yana matukar sonki na tabbata wata rana za ki gano alkhairi da yake tartare da Amar
Raheela ta zare jikinta daga jikin kaka a zuciyata tace ita ma wannan Tsoho tana bayan yaa Amar, ta mik'e tsaye ta kalli kaka tayi murmushi ta kuma share hawaye ta tace shikenan kaka a yanzu banida mafita ina kallo zan kasance matar yaa Amar to amma kuma ba komai ni nasan yadda zanyi don na k'arawa zaman aure mu armashi abin mamaki ni da yaa Amar za mu rayu a gida d'aya kuma a matsayin ma'aurata ta 'karasa magana had'e da kyakyalewa da dariya ta juya tashiga _bedroom_ Nazee yayi tsalle ya haye kujera ya zaro ido yace anyya kaka raheela bata zare ba kuwa"?
Kaka ta watsa masa mugun kallo in har ta zare ae da 'kari sa hannu ka domin Kaine munafuki da yake 'kara zugata.
Haba kaka ya za'ayi acuci yarinya sannan kuma kuce ba za'a tausaya mata ba'
Ba Wanda ya cuci raheela sai anan gaba za Ku gano cewa gata akayi mata
Aure Dole ba gata bane kaka da gata ne ke me yahana ayi miki naga kema aure soyayya ki kayi sai raheela ce za Ku yiwa dole don kawai ku farantawa yaa Amar rai'
Lallai nazeeru wuyan ka yayi kauri ya isa yanka har ni za ka kalle kace nayi aure _soyayya_ ?
_Eh nafada aure soyayya ki kayi ae ba karya na fad'a ba ke ni daga yau mu raba jam'iyya ni da ke_
Kaka tayi murmushi tace ae kuwa da na huta da halinka tashi maza kafita mini daga falon kuma daga yau karna 'kara gani 'kafarka anan.
Matukar raheela tana _side_ d'inan kindinga gani 'kafata kenan.
Ja'iri banza marar zuciya tsanani dad'ewa raheela a gidanan gobe saidai in bin ta za kayi gidan aure ta
Nazee ya mik'e tsaye yace ni banida lokacin cigaba da sauraro wannan surutu naki na fita amma fa anjima zan dawo ki ajiye min fura kaka ta bishi da harara.
Raheela na shiga d'aki tafad'a bisa gado tafashe da matsanaci kuka shikenan yanzu naci amana yaya na'eema na kuma k'arya alk'awali da na d'aukar mata, oh ni raheela naga takaina zan aure ```MIJIN 'YAR UWA TAA ``` amma kuma sun ce addini bai hana ba to amma ```ana bari Halak don kunya ``` da sauri ta d'auko wayarta ta kira ayshat ta zaiyane mata abunda ke faruwa tun kafin ta dasa aya Ayshat ta kurma ihu da sauri raheela ta cire wayar daga kunne ta wannan banza tanaso tafasa mini dodo kunne mtss ta jefarda waya tacigaba da shshekar kuka.
Amar yana fita gidan sa yanufa zuciyarsa cike da tsan-tsa farin ciki marar misaltuwa yad'aga hannu sama yace _Allah na gode maka da kanufi ni da samu farin ciki na Allah ka k'arawa Annabi Wasila da fadila_
Mutum na farko da yafara kira shine Dr kabeer ya sanarda shi abin farin ciki da yasame shi cikin tsanani jin dad'i Dr kabeer yace _congrats_ aboki na burin ka yacika nasamu taurarowa ka ina tayaka murna Allah yabaku zama lafiya ya kad'e fitina a tsakani ku.
_Ameen kb na gode da wannan addu'a_ suna gama waya Dr kabeer ya dinga turawa _friends_ d'in su _text_ na d'auri aure.
Umma hajara na zaune a falonta tana waya da aunty asabe na Shiga uku aunty asabe watan kunya ta yatsaya Amar zai aure shegiya yarinya nan da tsana da bana fatar na cigaba da bude ido ina ganita.
Shikenan kashi ki yabushe hajara mafita d'aya ta rage miki ki tashi tsaye ki shiga ki fita ki hanawa raheela zaman lafiya a gidan Amar.
Wallahi ashirye nake aunty asabe ko zan rasa rai na sai na tarwatsa rayuwa raheela
Rai kuma hajara, me kuma ya kawo zance rasa rai"?
Ranar biyan bukata aunty asabe rai ba'a bakin komai yake ba a yadda nakeji zuciya ta in har buk'ata ta za ta biya komai zan iya aikatawa.
Ke fa sokuwa ce hajara in kin rasa ranki ubanwa zai cigaba daga inda ki ka tsaye"?
Ki budewa kunne ki da kyau saurare ni ki shirye akwai wani hatsabibin boka a gari _Enugu_ aikin sa na matukar tasiri, shikenan aunty asabe ki shirya rana assabar mu kai masa ziyara.

```WASHE GARI ```

Tun da misali k'arfe _9:00am_ yaya hafsat tad'auki raheela suka tafi gidanta inda Hajiya Zaituna mai gyara amare tafara gyara raheela da misali k'arfe 11:09am Ayshat da zainab da wasu daga cikin 'kawaye raheela da zainab ta gaiyato suka fara cika gidan yaya hafsat kallo d'aya za ka yiwa amarya kagano bata farin ciki da wannan aure.
Da misali k'arfe _2:30pm_ aka d'aura aure ```Amar Muhammad matawalle da Raheela Abdullah matawalle ``` a bisa sadaki naira dubu _hamsi_ lakadan ba ajalan ba yayida ango Amar yasha farar shadda d'iki babbar Riga kansa d'auke da bak'ar hula kunbe sai faman gaisawa da mutane yake yi kana kallon fuskarsa za ka hango tsan-tsa farin ciki da yake tartare da shi....

Jeeddah Aliyu🌹
[04/08 7:19 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [04/08 1:20 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

8⃣5⃣

Da misali k'arfe _4:30pm_ akayi kamu raheela tayi matukar kyau, Ayshat da zainab sai faman tsokana ta sukeyi bayan antashi daga kamu ne bahijja matar Nazee ta rik'o hannu raheela tace zo mu je yayanki naso ganin ki Nazee na zaune a cikin motarsa bahijja tak'araso da raheela ta d'an kwakwasa _glass_ d'in mota had'e da cewa _honey_ kafito ga ta na kawo ma Nazee yafito daga cikin mota fuskarsa d'auke da tsantsan farin ciki yace _congratulation my sister_ ina taya ki murna ganin wannan rana mai d'ibin albarka Allah yabaku zaman lafiya da ha'kuri zama da juna wallahi raheela yau ina cikin tsanani farin ciki marar misaltuwa, na gani wannan rana da burin yaa Amar yacika na mallaka ki a matsayin matar aure sa tun daga ranarda na fahimce cewa yaa Amar yana sonki nake addu'a Allah ubangiji ya mallaka masa ke sai gashi yau Allah{s.w.t} ya nuna mini wannan rana ina rok'oki raheela ki taimaka ki bude k'ofar zuciyarki ki samawa yaa Amar fili wallahi _guy_ nan yana matukar sonki fiye da tunani ki.
A hankali tad'ago idanu ta da ke tsiyaya hawaye tana kallo Nazee daga bisani tace dama yaya Nazee baka tare da ni kai ma kana farin ciki da auren ```MIJIN 'YAR UWA TAA ``` da nayi"?
Duk wani masoyi ki raheela zai yi farin ciki da aure ki da yaa Amar ni dai rok'o na gareki ki kwantarda hankali ki shi ```SO``` a hankali yake Shiga zuciyar dan Adam a sannu za ki waye gari ciki soyayya yaa Amar kinsan _guy_ bashida sauki a fagge soyayya haka

Please Login or Register in order to submit comment