Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace mu musulmai ne mu yarda da k'addara dama duk mai rai mamaci ne Allah ya jik'ansu ya gafarta musu'
Dr Abbas yayi murmushi yace Alhaji ba Ku jira na k'arasa zance na kun yanke hukunci, daddy yace Dr ba wani zance da za ka k'arasa a gaban mu aka fita da gawar aboki hatsari su.
Dr Abbas ya Shafa sak'o sa yace Alhaji 'ya'ya Ku suna raye basu mutu ba, saidai suna ciki "critical conditions" mu samu mace tafarfad'o amma Dr Amar zuciyarsa kadai ke aiki kuma yasamu "injury's" da yawa daga ciki harda kariya a k'afarsa ta hagu da hannu sa na dama ita kuma mace tasami kariya a cinya da kuma hannuta, ga kuma "internal injury's" saboda kanta ya bugu duk da haka ita tafarfad'o mu yi mata allura bacci ne za ta farfad'o "around" 6:00pm insha Allah in tafarfad'o za Ku iya ganinta amma Dr Amar sai yadda hali yayi...
[27/07 7:31 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

7⃣6⃣

Daddy da Abba suka share gumi ciki yanayi na mutuwar jiki suka fito "office" d'in Dr Abbas da sauri mami da kaka suka had'a baki wurin tambaya Alhaji ya jikin su"?
Daddy yasauke ajiyar zuciya yace na'eema tafarfad'o sunyi mata allura bacci sai k'arfe 6:00pm zata farfad'o amma Amar ba wani kwakwara bayani akan shi, umma hajara tasaki ajiyar zuciya mai k'arfi gaske duk Wanda ke wurin saida yajuyo ya kalle ta tace Alhamdulilah"! Kaka, mami da kuma aunty amarya suka fashe da kuka, Raheela ta zube kasa da sauri Nazee ya taro ta, Raheela tafashe da kuka gwanin ban tausayi daddy da Abba suka nufi massllaci da ke cikin asibiti domin sallah azhar, Nazee ya kalle kaka yace kaka jikin raheela yayi zafi sosai da alamu zazzabi mai zafi ne yakeso yarufe ta, kafin kaka tabashi amsa umma hajara, tayi karaf tace yoo" ae dole tayi zazzabi tun da abokin shashaci ta rai a hannu Allah"
A harzuk'e kaka ta mik'e ta wankawa umma hajara mari hawaye na zuba daga idanu kaka, tace tir da halinki hajara ke kan kin zama annoba haihuwa ki batayi yiwa iyayye ki rana sun haifo masifa da bala'e rashin imani ki a baiyane yake ae ko ba komai Amar mijin 'yarki ne ki tuna da irin zalunci da Ku kayi masa, duk da haka Amar yayi biyayya da umurni mahaifi sa ya amince zai zauna da 'yarki shine yanzu ki ke binsa da mugaye kalamai to ta Allah ba taki ba insha Allah Amar zai mik'e da k'afafu sa, in yaso sai ki had'iye zuciya ki mutu don bak'i ciki umma hajara ta sunkuyarda kanta kasa tana huci aunty amarya, ta mik'e ta rik'o hannu kaka tace yi hak'uri hajja karki biye mata Ku saida hali domin ita abin kunya gaba taba shi ba baya ba, ba Amar take k'i ba Raheela ce bataso wallahi na tabbata da hajara na da yadda zatayi da yanzu tayi domin ta kawarda Raheela a doro k'asa kwana ta ne kawai ke gaba'
Kaka ta koma wurin zamanta ta zauna, Raheela tak'ara fashewa da kuka mai cin rai cikin bacin rai Nazee yaja hannuta suka fita.

*6:00pm*
Kamar yadda Dr Abbas yad'afa 6:00pm na bugawa na'eema tafarfad'o, gaba d'aya su daddy suka zagaye ta sunayi mata sannu saboda zafin ciwo da kyar take amsawa ta juya wurin daddy muryar ta na fita a hankali tace daddy ina yaa Amar"?
Daddy yakasa bata amsa saida Abba ya ari bakin sa yaci masa albasa yace Amar na nan na'eema jikinsa da sauki, tayi shiru tana kallon mutane d'akin daga bisani tace Abba ina umma taa da Raheela"?
Da sauri umma hajara tace gani nan na'eema tak'araso kusa da ita na'eema tacigaba da cewa Dan Allah umma kiyi hak'uri kiyafe min umma hajara ta share hawaye tace na yafe miki na'eema Allah yatashi kafad'a ki'
"Ameen" umma tajuya wurin da Raheela take tsaye ta jingina jikinta da bango tace zo nan Lil sis" Raheela tak'arasa wurinta na'eema ta rik'o hannuta tace Raheela kiyafe mini abinda nayi miki ki kuma rok'a mini yaa Amar ya yafe mini nasan na cutarda Ku amma a yanzu nayi nadama, kiyi mini alk'awali ko bayan raina za ki kulla min da umma taa saboda umma batada kowa sai niya, banaso tayi kukan rashi ni ki maye mata gurbi na raheela tafashe da matsanaci kuka tace nayi miki al'kawali yaya na'eema zan kula da umma tamkar yadda zan kula da mahaifiya ta.
Na'eema ta k'ara juyawa wurin umma hajara tace umma ga raheela nan kiyi mini alk'awali za ki d'auke ta tamkar yani umma Raheela na sona tana son farin ciki na Dan Allah umma ki so ta kidaina nuna mata k'iyayya kinji umma naa"?
Na ji na'eema nayi miki alk'awali zan so Raheela tamkar 'yar da na Haifa Allah yabaki lafiya"
Na'eema tajuya wurin su mami tace kaka, mami aunty amarya Ku yafe mini gaba d'aya suka fashe da kuka kowane yana fad'ar na yafe miki Allah ya baki lafiya"
Dr Abbas ne yashigo yace wannan wane irin abu ne za ku saka maras lafiya a gaba kuna kuka"?
Dan Allah Ku fita a lokacin d'aya su mami suka fice yayi saura daga daddy sai Abba suka rage har sun juya na'eema ta kira su tace daddy da Abba dan girman Allah kuyi mini alk'awali bayan raina za Ku aurawa yaa Amar, raheela saboda ita ce farin ciki sa.
Daddy da Abba suka goge gumi had'e da kallon junan su na'eema ta katsi masu hamzari ta hanyar cigaba da rok'o su daddy yace mu yi miki alk'awali na'eema kuma insha Allahu za mu kasance musu cika miki alk'awali daga nan Dr Abbas ya gargad'a su daddy waje na'eema ta bi su da kallo idanu ta na zubarda hawaye.
Tun da misali k'arfe 11:00pm jikin na'eema yayi tsanani sai Amai jini takeyi kusan likitoci hud'u ne akanta da misali k'arfe *5:00am* na asuba na'eema tace ga garin Ku rai yayi halinsa rai bak'o duniya *innalillahi wa'inna illahi raji'um*
*k'ulli nafsi za'ikatil mauti*
*Duk mai rai mamaci ne Na'eema ta tafi tabar duniya ko me zai faru in umma hajara taji mutuwar Na'eema*?

Jeeddah Aliyu🌹
[30/07 8:50 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [29/07 1:06 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

7⃣7⃣

Dr Abbas yafito daga d'akin da na'eema take, yana share gumi da farin _handkerchief_ da sauri daddy yanufi wurin shi Dr ya jikin nata"?
Dr Abbas yayi shiru daga bisani yace _I'm sorry 2 said_ na'eema ta rigamu gidan gaskiya
_innalillahi wa'inna illahi raji'um_ kalma da daddy yake ta mai-maitawa Abba yak'araso wurin daddy yadafa kafad'ar sa yace Allah da yabamu na'eema shi ya k'arbi abar sa kuma yafi mu sonta a yanzu tsakani mu da ita sai addu'a _Allah ya jik'anta ya gafarta mata zunubai ta Allah ya kyautata makwacinta_ daddy yasauke numfashi yace *Ameen*.
Daddy da Abba suka nufi _reception_ inda kaka da umma hajara suke dama su kadai suka kwana a _hospital_ d'in cikin sanyi murya Abba yace hajja Allah ya k'arbi ran na'eema, yanzu nan za'a fito da gawar ta.
Kaka tasaki kalma shahada yayida umma hajara ta kwatsama ihu, tafara zanga sambatu _wayyo ni Allah mutuwa mai yanka 'kauna shikenan sun kashe min ita wayyo ni na'eema karki tafi ki barni ke kadai na mallaka, na shiga uku na lalace wallahi ita kenan gareni_ Abba ne yayi k'arfi halin rik'o umma hajara yace kiyi takwali hajara Allah da yabaki na'eema shi, ya k'arbi abar sa halin yanzu na'eema tafi bu'katar addu'a ki fiye da wannan kukan da ki ke yi mata umma hajara ta'kara fashewa da sabon kuka had'e da chakume rigar Abba, duk yadda Abba yaso tadaina kuka abin yaci turu sai kawai yasaka mata ido saboda abin kuka ne yasame ta dole tayi kuka.
Ba'a d'auki dogon lokacin ba aka fito da gawar na'eema aka sakata cikin _ambulance_ kaitsaye aka nufi gida da ita yayida Amar baisan duniyar da yake ba saboda har yanzu yana ciki _coma_ in kadebi zuciya sa babu abinda yake motsi a jikinsa hatta da numfashi sa ta _oxygen_ yake fita lokacin da aka eso da gawar na'eema, raheela soma tayi da kyar aka samu ta farfad'o sai faman kuka takeyi gaba d'aya gidan ya kachame da ihu had'e da kukan mata raheela na kwance a jikin kaka idanu ta jajir kamar mai ciwo ido _Apollo_ muryar ta duk ta dishe saboda kuka, tace shikenan kaka yaya na'eema ta tafi ta barmu kaka tace duk mai rai mamaci ne raheela kowa lokacin sa yake jira kiyi mata addu'a shine zai nuna cewa 'kaunarta'
Raheela ta fashe da kuka abin gwanin ban tausayi, cikin muryar kuka tace _ya Allah kayi mata rahama ka had'a ta da haske kabari kabata iko amsa tambayoyi cikin sauki_ kaka ta goge hawaye had'e da cewa *Ameen*
Misali 'karfe *10:00am* akayi _jana'izza_ na'eema aka kata gidanta na gaskiya umma hajara tana gani anfita da gawar na'eema ta yanke jiki tafad'i saida aka shek'a mata robar ruwan _faro_ biyu sannan tadawo haiyaci ta ranar umma hajara 'yar 'karamar hauka tayi.
Sai da yamma raheela tasamu ta bud'e wayar ta, ta kira Ayshat _ringing_ d'aya zuwa biyu ta d'auka raheela lafiya ki ke tun jiya nake kiran wayar ki arufe naje gidanku maigadi yace kun fita Ku duka"?
Raheela ta sauke ajiyar zuciya daga bisani ta 'korowa Ayshat abunda ke faruwa Ayshat ta rud'e sosai, daga bisani tace _Allah yajik'an na'eema yasa ta huta shi kuma yaa Amar Allah yabashi lafiya_
*Ameen* _besty_ na gode Allah yabada lada.
Ayashat tacigaba da cewa insha Allah gobe zan zo nayi wa su umma _ta'aziyya_ to besty sai kin zo sukayi sallama raheela ta kashe waya.

*BAYAN KWANA UKU*

A yau ne na'eema ta cika kwana uku da rasuwa akayi addu'a uku 'yan uwa na nesa da na kusa suka watsi gidan yayi saura daga umma hajara sai 'yan uwa ta na jini da yake aunty amarya a _hospital_ take yini kwana kadai yake dawowa da ita gida kaka da mami kuma suna _part_ d'in su wannan ne yabawa umma hajara furtawa 'yan uwa ta abunda ke ci mata tuwo a kwarya ta kalle aunty Asabe idanu ta na tsiyaya hawaye tace........
[30/07 8:49 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

7⃣8⃣

Burin Amar da raheela ya cika sun rabani da na'eema, dakata hajara aunty asabe ce ta katsi ta haba hajara kada mutuwa na'eema ta zauta ki mana ta yaya za ki danganta mutuwar na'eema da Amar da raheela bayan kowa yasan _accident_ sukayi har yanzu Amar yana ciki halin 'kila wa 'kala.
Umma hajara ta fayyace majina da gefen hijab d'inta, ta kwashe labari yadda akayi Amar ya aure na'eema har izuwa abunda yafaru ta sanarda 'yan uwa ta aunty asabe tayi salati had'e da tafa hannaye daga bisani tace lallai hajara kinyi sake, d'an zaki ya girma ke wayagaya miki ana dogaro da aikin boka d'aya ae ba lalle bane koda yaushe aikin boka duguzuu yake tasiri, shikenan kinyi tutar babu baki ga tsuntsu baki ga tarko 'yar da ki ke tunani in ubanta ya mutu ki gaji dukiya ta mutu a yanzu bakida martaba a gidanan kodai ki tashi tsaye chak kiyi tsayin daka kiyi amfani da damarki tayi miki amfani ko kuma ki zauna garin kallon ruwa k'wado yayi miki 'kafa ta'karasa magana had'e da kyabe baki.
Suwaiba ta karbe zance ta hanyar cewa ae kema aunty hajara da laifi ki duk abunda za kayi duniya karka nemi ka salwata rayuwa wani da tun farko kince asaka asirin a tsohon kabari da yanzu raheela ta haukace, don haka qaiqayi ne ya komawa mashek'iya a maimako raheela ta mutu sai 'yar ki na'eema ta mutu da za ki d'auki shawara ta da nace ki zubarda makamai ki kada garin gyaran gira arasa ido domin naga alama a wannan tafiyar bakida Sa'a.
Tun lokacin da tafara magana hajara da asabe suke aika mata mugun kallo, aunty asabe tace ke suwaiba duk wannan kwana-kwana da ki keyi kifito filin kifad'a mana cewa kina baki cikin da hajara ba wai ki ce ta zubarda makamai ba ko don bakece aka cuta ba"?
Don na fad'a mata gaskiya shine za ki danganta ni da 'yar bak'i ciki to ni bana mata bak'i ciki ina dai tausayi muguwa hanya da ki ke yun'kuri jefa ki.
Umma hajara ta zuburo tamkar za ta daki suwaiba tace lalle suwaiba bakya 'kauna ta in har ke ba za ki tayani d'aukar famsa abunda akayi min to ki zuba ido kisha kallo ba ruwanki.
Haka aunty asabe tacigaba da zuga umma hajara yayida umma ta hau ta zaune bisa ga gurguwa shawara da tabata.

Dr Abbas na zaune a office d'in sa daddy da Abba suna zaune yana musu bayani dangane da ciwo Amar gaskiya Alhaji da za Ku d'auki shawara ta da nace kunfita da Amar kasar waje domin anan bamuda wasu kwarari kayan aiki yau kwana sa biyar kenan ko d'an yatsa sa bai motsi ba hatta da numfashi ta _oxygen_ yake shak'ar sa ga kuma kariya 'kafa da hannu.
Daddy yasauke ajiyar zuciya yace Dr kana gani wane kasa yadace mu fita da shi"?
_Germany_ ita ce da yadace Ku kai shi _Co's_ suna da likitoci kwararu daddy yace mu gode sosai likita.

_BAYAN KWANA BIYU_

Bayan kwana biyu aka wuce da Amar _Germany_
Raheela na kwance a falon kaka kallon d'aya za ka yi mata ka gano rama da tayi yaya hafsat ce tashigo ta d'an zaro ido had'e da cewa wai raheela har yanzu kina nan a kwance baki shirya ba"?
Raheela ta mik'e zaune tace na shirya yaya hafsat kawai na d'an kwanta ne kafin _driver_ yazo
_okay_ kifito da kayan naki ga _driver_ nan yazo raheela ta mik'e ta shiga d'aki tafito da _trolley_ d'in ta kaka na biye da ita kaka tace Dan Allah hafsat ki saka ido akan raheela tun lokacin da akayi rasuwa nan bataso cin abincin
Yaya hafsat ta yi murmushi tace zan kula da ita _insha Allahu_ kaka da haka sukayi sallama da sauran jama'a gidan suka d'auki hanyar _Abuja_
Tun lokacin da raheela ta koma _school_ ta dawo _so silent_ duk da yaya hafsat tana kula da ita sosai.

*GERMANY*

A _Germany_ kuma Satin Amar d'aya yafarfad'o har yana iya magana, yana dawowa haiyaci shi ya tambayi na'eema Abba ya kalle shi cikin tausayi yace na'eema ta ji sauki Amar ya lumshe idanu shi saida ya share tsawon wata d'aya a _Germany_ sannan suka dawo gida _Nigeria_ a lokacin yana iya tafiya da 'kafafu sa.

_BAYAN 1 HOURS_

Bayan awa d'aya da dira Amar _Nigeria_ yana zaune a falon daddy yace daddy tun lokacin da nadawo banga na'eema ba ko batasan nadawo bane"?
Daddy yayi shiru yakasa bashi amsa Amar yace daddy kayi baka bani amsa ba"?
Tun lokacin da ina _Germany_ in na tuna da na'eema sai na tsinci kaina da fad'uwar gaba Dan Allah daddy kafad'a mini ina na'eema"?
Har daddy ya bude baki yabashi amsa sai ga Abba da umma hajara sun shigo, umma hajara ta tabe baki tace banga amfani boye masa da Ku keyi ba domin ba shi zai sanya 'yata tadawo duniya ba kai Amar duk wani boye-boye ya'kare na'eema ta mutu.
A lokaci d'aya tsnanani tsoro had'e da tashin hankali suka ziyaraci Amar wani mashahuri gumi ya lullube shi numfashi sa yafara Kai da kawo daga bisani numfashi nasa ya tsaya chak ya sulale 'kasa a _some_.......

Jeeddah Aliyu🌹
[01/08 9:38 am] Jeeddah Aliyu🌹: [31/07 5:17 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

7⃣9⃣

Da sauri Daddy yad'ago shi yana girgiza shi, had'e da kiran sunan shi, mami ta mi'ke da gudu tashiga _kitchen_ ta d'auko robar ruwan _Mr. V_ mai matu'kar sanyi ta mi'kawa Abba ya kwarawa Amar nan take Amar yasaki katuwar ajiyar zuciya, yasoma kallon mutane falon daga bisani yafashe da kuka cikin murya kuka yace _Allah sarki na'eema kin tafi a lokacin da nakeda 'kudiri nuna miki tsantsan 'kulawa kin tafi a lokacin da nasha alwashi danne zuciya ta, da tacigaba da zama da ke har 'karshen rayuwa ta "Allah yagarfata miki na'eema yasa kin huta_ yana k'arasa magana had'e da fashe da wani Sabon kuka Abba ya rungume shi yana bubuga bayan sa cikin sigar rarrashi yace hakuri za kayi Amar _duk mai rai mamaci ne tsakani mu da na'eema sai addu'a_ Abba ya taya shi mik'ewa yaraka shi d'akin shi yace ka kwanta ka huta Amar karka saka damuwa a ranka ko don yanayi jikin ka Amar yad'aga kan shi ha'de da cewa na gode Abba.
Umma hajara nagani Abba yafita da Amar sai tasami damar yada maganganu maras asali balle kan gado bakinta na fitarda kunfa bala'i da masifa don tsabar mugunta an kashe mini 'ya, to wallahi ahir d'in Ku ashirye nake duk Wanda yakeda sa hannu a mutuwa ta.
A fusace mami ta mik'e ta nuna umma hajara da yatsa tace na fahimci cewa hajara bakida hankali in banda hauka da dabbaci irin naki waye ya kashe miki 'ya anan"?
Amar shine ya kashe na'eema saboda baya sonta ya tsane ta, shiyasa ya kifarda mota 'yata ta mutu.
Daddy da Mami suka d'auki kalma shahada mami tace anyya hajara za ki ga Annabi kuwa"?
Tsabar jahilci da rashin takwali yana 'kokari jefa ki mahalaka, in banda jahilci kina _musulma_ amma ace bakisan da cewa Allah {S.W.T} shi yake rayawa kuma shi yake kashewa tir da wannan da'ki'kici naki yi maza kifita ki bamu wuri tun kafin nayi miki abinda baki tab'a tunani ba Allah yashirye ki yasa ki gane gaskiya.
Umma hajara taja tsoki had'e da cewa za ka Ku ga abinda zai biyo baya tafice daga falon
Mami tace mu ga alkhairi ta koma ta zauna tajuya wurin Daddy da ke dafe da goshi tace Alhaji kana ji abunda wannan jarabanbiya matar tafito da shi"?
Daddy yasauke numfashi yace naji fateema ha'kuri za kiyi kidaina biye mata watakila zafin mutuwar na'eema ne yatab'a ta mami ta tabe baki had'e da cewa Allah ya kyauta.

_ABUJA_

Raheela da Ayshat sun fito daga _lecture_ wayar raheela tayi _ringing_ tafito da ita daga _handbag_ gani Wanda yakira yasa ta ja tsoki had'e da bata fuska kamar za tayi kuka, Ayshat ta kalle tace miye haka kin wani 'bata fuska sai kace wance tasha mad'aci"?
Bari kawai _besty_ na had'u da 'karfe 'kafa gaba d'aya _guy_ nan ya takurani ya hanani sukuni _I don't known what's to do_
Ayshat ta kyakyale da dariya tace kina nufi suleiman"?
Shine _besty_ so yake da k'arfi da yaji ya cusa mini sonshi'
Yatsine fuska Ayshat tayi daga bisani tace nifa banga illah Suleiman ba'
Nima bance miki yanada illah ba kawai dai yayi min girma Ayshat tak'ara kyakyalewa da dariya tace kin shiga uku raheela mutum yana haukan sonki ke kuma kina masa sharri.
Raheela tayi dariya tace Suleiman yafiye naci, ko don wannan naci nasa dole na saurare shi.

_WANENE SULEIMAN_??
Suleiman haifafe garin katsina ne shekuru sa na haihuwa ba za su haura 37 ba ma'akaci banki ne unguwar su d'aya da yaya hafsat gidaje biyu ne a tsakanin s tun lokacin da ya 'kyala ido akan raheela yanace mata shi dole sonta yakeyi tun raheela bata kulashi har tadawo tana saurare shi.

_KADUNA_

Bayan sati biyu da dawowar Amar daga _Germany_ ya ji sauki sosai,don haka yau yahad'a kayan shi zai koma _Abuja_ zaune yake a falon kaka yace kaka na zo ne nayi miki sallama zan koma a bakin aikina.
Kaka tace to Amar Allah yakai ka lafiya ka kula da tu'ki karkayi mugun gudu nan da ka keyi Amar yayi murmushi, kaka tace bara na kawo maka sak'on raheela ras gabanshi yafad'i tun dawowar shi yakeso ya tambayi raheela sakamako rashin ganinta da yayi amma yana tsoro amsar da za'a bashi....
[01/08 9:36 am] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

8⃣0⃣

Har kaka tafito daga d'aki baisaniba ya zurfafa a tunani haske zuciyarsa raheela, saida kaka ta kira sunanshi da k'arfi sannan yadawo daga dukiya da yalula cikin tausayawa kaka tace Amar yakamata ka rage tunani a matsayin ka na likita kasan irin illah da yake haifarwa
Amar yad'an Sosa kai yace na gode da wannan shawara taki kaka, ina sak'o yake"?
Kaka ta mik'e masa katuwar leda bak'a da sauri Amar yatoshe hanci had'e da cewa wari daddawa nakeji kaka me raheela za tayi da _daddawa_?
Kaka ta galla masa harara tace to miye kuma na toshe hanci?
Banaso wari daddawa kaka'
Kana nufi kenan ba za ka, kai mata _sak'o_ ba"?
Leda _daddawa da garin kuka_ na hafsat ne ledar aya mai sikari da garin d'an wake da kuma yaji na raheela ne kasan raheela na matukar son 'dan wake'
Amar ya tabe baki yace kaka kina sagarta raheela da yawa har wani _aya mai sikari_ ki keyi Mata
Kaka tace ina ruwanka kadai sak'o ne na baka in kuma ba za kai mata ba ka bani kayana
Amar ya mik'e yace ni na tafi kaka saboda na fahimci so ki keyi mu yi fad'a kafin na tafi ni kuma banaso yin fad'a da ke'
Kaka tayi murmushi ta bishi da _addu'ar fatan alkhairi_

_ABUJA_

Raheela na zaune a falon tana kallo jabeer _first born_ d'in yaya hafsat yashigo ya zauna kusa da ita yayi 'kasa da murya yace aunty raheela _uncle Suleiman_ ya zo raheela tayi murmushi had'e da cewa _okay_ kace ina zuwa tashiga d'akin da ya kasance nata tayi _simple make up_ tafesa turare _eternity for women_ tafice zuwa _compound_ tun kafin tak'araso yafara wanke ta da murmushi, barka da fitowa _my heartbeat_
Yauwa ina wuni"?
Lafiya amma ba qalau _my heartbeat_
Raheela ta d'an zaro ido tace me ke faruwa ne suleiman"?
Ya lumshe idanu raheela duk lokacin da ki ka kirani da suleiman sai naji wani sabon, shauk'i sonki yana 'kara samu masauki a cikin zuciyata ina sonki raheela amma ke Sam bakida damu da ni ba
Raheela tayi murmushi tace dad'i da kai kenan a _suleiman_ kullum 'korafi ka guda d'aya ne ban damu da kai ba da bakada muhalli a zuciyata da ba zan dinga sauraro ka ba'
_suleiman_ ya washe hak'ora kamar gonar auduga, yace in kuwa haka ne _my heartbeat_ ki amince iyayye na suje gidanku domin asan da zamana.
Raheela tayi dariya had'e da cewa suleiman zumudi duka-duka wata d'aya kachal da had'uwar mu komai zumudi ka, ka jira har mu gama fahimtar juna koh"?
Wane irin fahimta raheela"?
Ni fa na fahimce ki sai in kece baki fahimce ni ba in har ba so ki ke nayi miki kuka ba raheela ki bani wannan damar _please_ yadda yayi magana ya ba raheela dariya batasan lokacin da ta kyakyale da dariya ba da yake _suleiman_ shashasha ne akan mace kawai sai yataya raheela dariya.
Dai-dai lokacin da _Dr Amar matawalle_ yadanno hanci motarsa a farfajiya gidan yaya hafsat tuni idanu sa sun hasko masa raheela wani irin masifafe 'kishinta ya lullube shi, a zuciyarsa yace wane 'kato banza ne raheela take tare da shi"?
Mtwww.... yaja tsoki lalle yarinya tasamu sake a gidanan shiyasa ta kafa samsani fira da katti da wannan zance zuci yayi _parking_ yafito daga mota ko kallon wurin da suke tsaye baiyi ba kaitsaye yashige cikin gida.
Raheela ta katsi da dariya da takeyi ta bishi da kallon mamaki yaushe wannan mugu yadawo ne?
Amma wannan _brother_ d'in ki ne koh"?
Kafin taba Suleiman amsa saida ta yatsine fuska daga bisani tace ni ban had'a komai da shi ba
Suleiman ya kyakyale da dariya yace kai _my heartbeat_ yanzu duk wannan kama da ki ka yi da shi za ki ce baki had'a komai da shi ba kallon d'aya za'ayi mishi a gano cewa yayanki ne don kunyi masifar kama saidai kinfi shi kyau.
Raheela tayi dariya tace to na gode zan shiga

Please Login or Register in order to submit comment