Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yakamata sannu-sannu ana jinyarta sai ta mutu shikenan yarinya ki ci kare ki babu banbaka ba dan banza da ya esa yatuhume ki, na'eema ta kyakyale da dariya jin dadi tace da kyau umma dadi na da ke akwai "brain" kina kawo "light" Allah yabarmi ke umma naa naji dadi shinfida mulki a gidan Dr Amar matawalle
"Ameen" 'yar nan.
Da wannan bahaguwa shawara ta umma hajara, na'eema ta dogara.
Yau Sam raheela bataji dadi zuwa "school" ba sakamako rashin gani ayshat, ae kuwa nan take ta kira ta a waya taji dalilin rashin zuwanta school ayshat tayi "picking" tace "hello besty"
Raheela tace na'am gani nashigo "school banganki ba ina fatar lafiya ce ta boye ki"?
Lafiya qalau bash ne yakawo min ziyara bazata, kuma yau zai koma shiyasa nayi zama na domin yana bukata ta a kusa da shi"
Mtss...raheela taja tsoki tace me bash ya zo dauka a wurinki, ba sai weekend yake zuwa ba"?
Bara na bashi "phone sai yafada miki abunda ya zo d'auka waka a bakin mai ita tafi dadi sauraro'
Da sauri raheela tace sai anjima ta kashe waya.
A lokacin da raheela tagama d'aukar "lecture" dole tanufi gate domin samu taxi da zai kaita gida dama yaa Amar ke kawota ayshat ta mayarda ita duk "taxi" d'in da ta tara taji an zafga mata kudi tace malam tafiyar'ka mtsss....taja tsoki hade cewa duk 'yan "taxi abuja barayi ne me za'ayi da irin wannan garin mutane sai 'yar banza tsadar rayuwa, tana wannan zance wata mota ta tsaya a gabanta da sauri ta kauda fuskarta mai mota yasauke "glass" ya leqo fuskarsa yace kanwata daina kawarda fuska yaya ki ne har yanzu baki sami "taxi bane"?
Sai lokacin raheela tasaki fuska hada dan gajere murmushi domin tagano course mate d'inta ne Amar Ibrahim dalilin da yasa take kirasa da yaya naa kenan tace "eh duk wance na tsayar sai naganta da mutane {ni kuma 'yar gidan Shehu aliyu saura kiris dariya ta kunbuce min nace kutt su raheela an fara qarya}
Ayya to shigo na sauke ki mana, saida ta yatsine fuska daga bisani tace lah...yaya naa da kabarshi da sauri yace kedai shigo tsayuwa a titi ba dadi a zuciyar raheela tace da na bada wadanan manya kudi a kaini gida gwada nashiga "lift" ta balle murfi mota tashige hade da cewa na gode yaya naa
Amar Ibrahim yayi murmushi yace "you are welcome"
yana yin "parking" a kofar gida raheela ta bude kofa tafito ta dan leqa kanta cikin motar tana qara yi masa godiya sai ga motar yaa Amar ta danno kai, rass...gaban raheela yafadi sai kawai ta dake kamar bata ganshi ba yadanna "horn" Joseph ya bude masa "gate" Amar Ibrahim yaja motar sa yaqara gaba yayida raheela tayi tsayin ta a bakin gate saida ta share tsawon dakika biyar a tsaye daga bisani tashiga gida, karaf idanu ta suka sauka bisa fuskar yaa Amar da ke tsaye a "parking space" sai faman kallon agogo yakeyi hade da girgiza kafa kallo daya raheela tayi masa ta kawarda fuska a baiyane kuma sai tace "poor guy" da alama matar'sa tafita bada izzini shi ba sai ta wani tabe baki tace "very sad" amma kuma na tausaya mata domin yanda naga hero yana girgiza kafa na tabbata yau zuciyar 'yan maza a bace take kamar ance taqara juyawa sai kawai ya yafito ta da hannu zaro ido tayi ta nuna kirjinta da yatsa alamar da ita yake kuwa yadaga kai ya kuma daga yatsu sa uku, raheela taqara zare ido tace wallahi da ni yake gashi nan yace kafin ya kirga uku na zo cabdijam matukar "guy" nan yadake ni akwai bala'e a gidanan don sai nafasa masa gilashi mota, gani ya lankwashe yatsu sa biyu yadaga guda daya yasa ta kwasa da gudu takarasa wurin shi, ta ja tayi tsaye ta wani turo baki hade cewa gaskiya ni yaa Amar kadaina yi min kirge da" da yanzu ba daya ba "I'm mature" so take note"
Amar yayi shiru yana wasa da key d'in hannu shi, kamar baiji abunda tafada ba gani yanda ya yi banza da ita yasa ta bude "handbag" taciro "lollipop" ta nunawa Amar hade da daga masa gira tace makami kasan mu bama yawo babu makami sai kuma ta zaro ido tace kai ba fa bindiga nake nufi ba ina nufi "lollipop" naga har ka tsorata tabare abarta ta jefa baki tana tsotsa tana lumshe idanu daga bisani tace Allah yayi yiwa "company" wannan alawa albarka domin alawa ce mai kawarda bacin rai, duk lokacin da nake tsotsa ta sai na tsinci kaina cikin nishadi da annashuwa, tun lokacin da tafara zuba Amar yake mata kallon kasan ido, gani har izuwa yanzu baiyi magana ba yasa ta tabe baki tace ga shawara yaa Amar me zai hana ka bude "company" lollipop saboda na fahimci cewa kai mutum ne mai zafin rai sam bakada fara'a dariya wuya takeyi maka shiyasa ko kayi dariya baka kyau kana bude company lollipop za ka dawo kamar gonar auduga saboda, fara'a sai yaya na'eema tagaji da gani dariyar ka, takarasa zance ta tana washe hakora ita a dole so take taqara harzuqa shi.
Ya lashe labba sa hade da cizo su, ya bude mota yaciro "briefcase" yace karbi ki shiga min da ita cikin gida ki cewa na'eema na koma hospital" akwai abunda na manta da zan je na dauko.
Raheela ta kyakyale da dariya tace.....

Jeeddah Aliyu🌹
[23/07 4:30 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [23/07 3:08 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

6⃣7⃣

BAYAN SATI BIYU******

Raheela na kwance a bedroom d'inta wayar ta yayi "ringing" ta yatsine fuska tayi "picking" kasalance tace "hello" jin muryar da batayi zato ba yasa ta mik'e zaune tace yaya hafsat saukar yaushe"? a bangare daya aka amsa da cewa jiya da yamma Amar bai fada miki nadawo ba"?
Tak'ara yatsine fuska hade da cewa wannan uban 'yan miskilaci ne zai fada mini kin dawo ae ba zai fada ba, yaya hafsat tayi dariya tace yaushe za ki zo gida na"?
Cikin zumudi raheela tace gobe daga "school" zan wuce gidanki, da an kwana biyu zan tattaro shirgi na nadawo gidanki da zama ni dama zaman gidanan ya eshe ni gida sai kace "prison"
Yaya hafsat ta kyakyale da dariya daga bisani tace raheela 'yan mata kaka har yanzu baki daina rigima ba koh"?
Nadaina yaya hafsat saidai in an tsokano ni, nakan d'an taba kad'an'
Dariya yaya hafsat tayi sosai daga bisani tace sai kin zo ta kashe waya.
Wani, wawan tsalle raheela tadaka a tsakiyar gado tace karshen zama na gidanan, yazo fuskar ta dauke da farin ciki tanufi "kitchen" tun kafin takarasa shiga kitchen d'in ta tsakayi na'eema ciki, har tayi niyar ta koma falon ta jira har tafito sannan tashiga sai kuma ta tuna da irin matsanaciya yunwa da takeji kawai, sai tafada kitchen d'in.
Jin motsi mutum yasa na'eema ta juyo gani raheela ce sai wani yatsine fuska kamar taga kashi, cikin rashin damuwa da irin kallon da takeyi mata tanufi locker ta bude tafito da kwalin comflask" karaf idanu na'eema suka sauka bisa d'an yatsata da hamzari ta rik'o hannu raheela a firgici raheela take kallon ta a tunani ta ko za ta zanga mata mari ne domin yadda ta danke hannu nata, cikin kad'uwa na'eema tace raheela ina ki ka sami wannan zobe"?
Raheela tasaki ajiyar zuciya saboda batayi tsanmani wannan ne dalilin da yasa na'eema tayi mata wannan mahaukaci rik'o ta fisge hannuta da k'arfi tace dallah malama sakeni, don kinga zobe a hannu na "so what's"
A fusace na'eema tace dole na tambaye ki inda ki ka sami da wannan zobe domin na mijina ne'
Hmm..su miji manya to mijin naki ne yabani
Na'eema tayi shiru zuciyata na tafarfasa jin takeyi kamar tadauki wuk'a ta dabawa raheela a k'aho zuciya, tana tsaye har raheela tagama abunda ta zo yi a "kitchen" tayi tafiyarta, tabarta tsaye tana jinyar dafi da tasake mata tamkar kazar da kwai yafashewa a ciki haka na'eema taja kafafuta tafita daga kitchen d'in tanufi d'akinta.

A WASHE GARI******

Daga "school" raheela ta zarce gidan hafsat ta shantak'e tayi zamanta har 10:00pm ta buga raheela tafito daga bedroom d'in yaya hafsat hannuta dauke da karamar 'yar yaya hafsat mai suna kausar tace yaya hafsat ni gaskiya tafiya zanyi kinga har 10:00pm ta buga ba zai yu na kwana anan saboda ban zo da kaya ba kuma gobe ina da "lecture"
Hafsat ta ja d'an k'arami tsoki tace ko yanzu na kira wayar Abban fahad "still" wayar shi a kashe
Raheela tabata fuska kamar za ta fashe da kuka, tace to yaya hafsat ki bari na hau "taxi"
Hafsat ta zaro ido hade da cewa ba zan sake ki a dare nan ki hau "taxi" bara na kira Amar ya zo yadauke ki'
Raheela tayi murmushin yak'e domin tasan mayuwaci abu ne yaa Amar ya zo yasauke ta
Amar da na'eema na zaune a falon Amar yana duba wasu "file's" na'eema kuma na kallo "ringing" d'in wayar Amar ne yasa yadago daga abunda yakeyi, yadauki wayar gani suna yaya hafsat yana yawo a "screen" yasa yayi saurin "received"
Muryar hafsat ce takarade masa kunne Amar don Allah ka zo ka dauki raheela'
Yatsine fuska yayi daga bisani yace ni driver" ta ne da zan zo na d'auke ta ae ba da izzini na ta wanke kafa ta je gidanki'
Yaya hafsat tayi murmushi tace don ni za ka zo ba don halinta ba "please Amar ka taimaka kayi min wannan "favour"
Amar ya tabe baki yace naji gani nan zuwa batare da yajira jin ta bakin hafsat ba ya kashe waya, duk abunda yake fada bisa kunne na'eema saboda takasa ta tsare sai wani zarar idanu takeyi Amar ajiye "file" d'in ke rik'e da shi ya mik'e tsaye yanufi inda yake ajiye key's d'in mota yadauka na'eema ta mik'e a fusace tace yaa Amar wannan wane irin raini hankali ne"?
Tsanani mamaki ne yarufe Amar kafin yabata, amsa tacigaba da fadar.....
[23/07 4:29 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

6⃣8⃣

Wannan ae salon cin amana ne to wallahi" wallahi" matukar ka d'auki kafa ka je d'aukar raheela ni kuma sai na zantarda hukunci mafi muni akanka, domin nagaji da cin amana ta da ka keyi, har zobe ka je aka k'era maka mai Zane "heart" kasaka daya a hannu ka kasaka mata daya to kayi a banza saboda nariga na zana layi mai tsayi a tsakani Ku saidai S0 raheela ya zama ajalin ka amma bazaka taba samu ta a matsayin matar aure ka, ni d'inan da baka so nice abokiyar rayuwar ka ta har abada, shashasha kawai mai kwakwalwa tumakai Wanda baya gudun abin kunya mtss..taja tsoki ta haura "upstairs" da gudu tabar Amar tsaye kamar bishiya kwa-kwa ya sauke gwaro numfashi tsanani tsoron Allah ya kama shi, wai ni na'eema za ta wanke wa allo tabbas na'eema ta shuka mini rashin mutunci na nuna a gidan talabiji na BBC world"
Ya kad'a kai yafice "driving" yakeyi amma ji yake kamar zuciyar'shi za tayi tsalle tafaso kirji shi tafito a haka yak'arasa gidan yaya hafsat, yana yi "parking" akafara yayafi dama garin yadau hadari a kasalance ya kira wayar yaya hafsat yace ki ce da ita tafito ya kashe, yaya hafsat tajuya wajen da raheela take zaune sai taga tadaura kanta a hannu kujera tana bacci, ta d'an bubuge ta, tashi tana bude idanu ta tace yaa Amar ya zo ne"?
Yaya hafsat tadaga mata kai da sauri ta d'auki "handbag" d'inta tace sai da safe yaya hafsat tafita da gudu, tun daga nesa Amar ya hango ta ya girgiza kai ko yaushe raheela za ta girma tadaina gudu oho"
Ta bude kofa tashiga tun kafi ta rufe kofa yafisgi mota da k'arfi gaske, raheela ta murguda baki suna fita unguwar su yaya hafsat aka sake da ruwa da k'arfi don haka Amar yak'ara "speed" dama gashi gwani ne a fagge gudu da mota, cikin 20 minutes" suka eso gida yayi "parking" daf da kofar shiga babban falon suka fito da gudu raheela tanufi kofa tana murda "handle" taji kofa gam Amar yakaraso yadaka mata tsawa yace kofar ma baza ki iya budewa sai na bude miki"?
Har raheela ta bude baki ta bashi amsa yak'ara daka mata tsawa ta hanyar cewa, dallah bani wuri ta matsa masa yana Kama "handle" yana murdawa ya ji kofa a rufe ruff'
Raheela ta kyakyale da dariya, wani mugun kallo ya watsa mata Wanda yayi sanadi da ta hadiye saura dariyar ta, yasoma "knocking" tun yanayi a sannu har yadawo yi da k'arfi daga karshe yadawo kwadawa na'eema kira, a hankali "window" ya bude na'eema ta lek'o kanta ta da sauri Amar yace na'eema wannan wane irin dabbanci ne da za ki rufe mana kofa kenan duk "knocking" d'in da nakeyi kina jina koh"?
Saida tak'are musu wulaqantace kallo sannan tace, na rufe kofa kayi duk abunda za ka yi, gantalalu kawai, maciya amana sai kuma inda Ku ka saba zuwa kuna iskanci Ku, Ku kwana a chan.
Wata irin zufa ce ta k'aryo wa Amar cikin sark'ewa halshe yace me ki ke nufi da na'eema"?
Duk abunda na ke nufi kasani munafuki mai bak'ar fuska'
Raheela kam mutuwar tsaye tayi yayida hawaye suka wanke mata, fuska cikin rawar murya tace haba yaya na'eema me mu kayi miki da ki ka zabi kiyi mana wannan mumuna k'azafi"?
Na'eema tadaka mata tsawa ta kuma nuna ta da yatsa, tace ke k'arama karuwa rufe min baki ba da ke nake magana ba'
Raheela ta kurma ihu tace yaya na'eema ni ki kira da karuwa kin manta ko ni wacece agareki"?
Mtsss... Na'eema taja tsoki cikin zafin rai Amar yanufi window" yace ke na'eema yau na fahimce cewa wani Sabon hauka ki ke ji to zan sauke miki shi ki zo ki bude mini kofa'
Na'eema ta kwabe fuska tace ba zan bude ba yau saidai ko kwana a waje amma ba dai a cikin gidanan ba 'yan iska kawai jarababu karaf ta rufe window" tayi tafiyarta.
Raheela ta durkushe tana rusar
Amar ya shure kofa da kafar shi, yasaki razanane ihu sakamako wani zafi da ya ziyarci kafar sa.
Gani ruwa suna k'ara k'arfi yasa ya kalli raheela yace ke tashi mu tafi
Tadago idanu ta da su ka kad'a sukayi jajir batare da tace komai ba tabi bayan shi ya bude mota yashiga ita ma tashiga a tunani ta fita zai yi sai taga yanufi "parking space" yayi parking yad'aura kanshi bisa "steering" raheela kuma tasaka kanta tsakiyar cinyoyi ta tacigaba da shashek'ar kuka....


Jeeddah Aliyu🌹
[23/07 8:33 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [23/07 6:46 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

6⃣9⃣

Tsawon lokacin suka d'auka a haka babu mai rarrashi wani, ga kuma ruwan da ake zangawa kamar da baki k'warya kamar daga sama raheela ta ji Amar ya bude kofa yafita tabishi da kallo, yanufi bakin "gate" d'akin Joseph yayi knocking" tana kallo Joseph yafito sukayi magana, yakoma d'akin shi, yayida Amar yajuyo bayan kamar dakika biyu zuwa uku sai ga joseph yak'ara fitowa hannu shi rik'e da "umbrella" yakare ruwa.
Raheela tasauke numfashi, a zuciyata tace ko amfani me Joseph zai yi mana"?
Amar yana k'arasowa yace ke fito'
Cikin sanyi jiki raheela tafito, tabi bayan Amar ita dai fatan ta, taga wayewar gari lafiya tattara kayanta tabar musu gida tunda har na'eema tafara yi mata k'azafin zina kaitsaye "guest room" suka nufa Joseph ya bude kofa Amar ya masa godiya, yana shiga raheela ta rufa masa baya ta nemi daya daga cikin kujeri falon ta k'ame Amar yanufi "bedroom" yasaka key yabude kofa saidai kofar tak'i budewa, tsawon lokacin yad'auka yana fama da kofar ta bude amma tak'i cikin tsanani jin haushi da takaici yadawo ya zauna yadafe kanshi da ke barazana tsagewa gida biyu, a fakace raheela take galla masa harara saboda tafi jin haushi sa akan na'eema mtss...ta ja tsoki tafito da wayar ta, ta duba tym" rass gabanta yafadi sakamako gani 12:44am a zuciyata tace na shiga uku ba dai nufi yaa Amar anan za mu kwana ba, kai ina ba zata sabu ba bindiga a ruwa na kwana d'aki daya da yaa Amar kenan zargi yaya na'eema zai tabbata akan mu.
Da sauri tadago tace yakamata ka koma wurin matarka kada zargin ta yak'ara tasiri akan mu, domin banga amfani zaman ka anan ba'
A fusace yace in ki ka k'ara yi mini magana sai na fasa miki baki ko na tilassa ki kwana anan"?
Kinga malama tun kafin nakasa "controlled" temper" na ki tashi kifita, jikinta na b'ari tanufi kofa saboda tayi masifa tsorata da shi ta bude kofa tafita, wata irin tsawa mai hade da walk'iya akayi raheela batasan lokacin da tattara siket d'inta ta kwasa da gudu ta koma inda tafito kallon d'aya Amar yayi mata kawarda fuska, ta lallaba ta nemi bayan kujeri ta rukube, a hankali tafara gyangyadi daga bisani ta kwanta k'asa bacci yayi awo gaba da ita, Amar ko ta kanta baiyi ba yacigaba da zance, zuci kamar ni na'eema zata wulaqanta"? tabbas na'eema tayi min abunda ba'a tab'ayi mini a tarihi rayuwa ta, wane irin jahilci ne ke damu na'eema da har yarufe mata ido take mana zargi zina"?
Tsawon rayuwa ta bantaba kallon, wata 'ya mace naji ina sha'awa aikata zina da ita ballatana raheela da nakeso kamar numfashi na, ko a yanzu da na rasata rashi na har abada bantaba kallon ta, naji ina sha'awa aikata zina da ita, tabbas na'eema batayi mana adalci ba miyasa ta danganta mu da mumuna kalma mai matuk'ar zafi da dafi irin wannan"?
Har k'arfe 3:35am Amar yana zaune ya buga d'an uban tagumi, sai faman tufk'a da warwara yakeyi daga bisani yadan kishigide da haka shima shugaba b'arayi na duk duniya ya sace shi.
Kiran sallah da ke fita daga wayar Amar ne yayi sanadiyar falkawa Amar, a firgici ya tashi zaune yadafe k'ok'o kanshi nan take majigi kwakwalwa shi, yafara tariyo masa abunda yafaru da shi a watani baya, Amar ya kurma ihu hade da furta "oh no"
Kamar a mafalki raheela taji ihun Amar a tsoroce ta, tashi zaune da rerafe ta k'araso gaban shi jikinta na rawa tace yaa Amar lafiya"?
Wani mashahuri tsoro ne yak'ara lullube raheela Wanda yahaddasa mata zama babu shiri ba komai bane illah kukan da Amar yakeyi tamkar k'arami yaro, raheela tak'ara shiga rud'ani sakamako gani Amar ya durkushe k'asa yana kuka har da su shasheka abunda raheela a tarihi rayuwata bata tab'a gani ba babban mutum yana kuka ko babban shu'umi, hatsabibi, kuma miskili irin Amar tabbas k'azafi da na'eema tayi musu yataba shi.
Gani yadda yake kuka yayi masifar bata tausayi karo na farko da raheela ta ji tausayi Amar ya ziyarce ta, ta matsa kusa da shi, tace don girman Allah yaa Amar kadaina kuka kowa yasan kai ba d'an iska bane, sharri ne kawai irin na yaya na'eema nasan dalilin da yasa tafadi haka saboda bataso zama na a gidanan, insha Allah gari yana k'arasa wayewa zan tattara kayana na bar mata gidanta domin banaso na zama silar rusa zaman auren Ku.
Har raheela tadasa aya a zance ta Amar bai fasa kuka da yakeyi ba, ita ma batasan lokacin da tafashe da kuka ba sai ga Amar da raheela na kuka ba mai rarrashi wani.....
[23/07 8:32 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

7⃣0⃣

Ba ka ji komai sai sautin kukan su da yakarade falon, raheela ta rik'o hannu Amar ta matsi cikin nata tace "for god sake" yaa Amar kayi hakuri kadaina kuka nan komai yayi zafi magani sa "Allah duk abunda mutum yayi don kanshi Amar yasauke ajiyar zuciya mai k'arfi gaske wata iska mai zafi tafito daga bakin shi tasauka a fuskar raheela ya zare hannu shi daga nata ya mik'e yafice, raheela ta bishi da kallon tausayi bayan fitar shi da kamar mintuna uku sai gashi yadawo ruwa da tagani a k'afafu shi yasa tagano alwala ya yi, tana kallon shi har ya kamalla sallah, da yake ita tana fashin sallah tsawon lokacin yad'auka yana addu'a hawaye na zuba daga fuskar sa, raheela tak'ara fad'awa a zango tunani to wai me ke faruwa da yaa Amar ne, kamar Wanda aka mintsina taga, mik'e yana huci yanufi kofa yanayi sa tamkar na mayunwaci zaki da yafito farauta, a firgici raheela tad'auki "handbag" d'inta tabi bayan shi hade da k'walla masa kira yaa Amar ina za ka tafi"?
Ko juyowa baiyi ba ballatana tasa ran zai amsa mata gani yanufi cikin gida tasaki ajiyar zuciya, tafiya yakeyi amma ita da gudu take bin shi duk da haka takasa cinmasa hanyar "garden" yanufa ita dai raheela na biye da shi a maimako yashiga "garden" saida taga yabi wani d'an k'arami "corridor" wata kofa ta "glass" ya bude yashiga, a zuciyar raheela tace cab" dama da kofa a wurinan duk tsawon zama na a gidanan bansaniba"?
Suna shiga ciki taci karo da tari "gym's machine's" a zube tace umh...ashe nan ne guy" nan yake barje gumi sa"?
Suna wuce takarce k'arafai yak'ara bude wata kofa "exactly" irin ta farko raheela ta zaro ido sakamako gani wani had'ade falon kamar kana kasar nasara, kutt dama akwai irin wannan falon a gidanan bansaniba"? tana cikin kashe kwarkwata idanu ta, ta hango Amar yanufi wata kofa nan take tagano hanyar da za tabi tashiga d'akinta da sauri kuwa tanufi d'akin nata saboda gari ya waye tass"
Amar yana bude kofa ya hango na'eema nade cikin "blanket" tana sharar baccinta cikin kwaciyar hankali yayi wani kukan kura chafko kafafu ta ya cillo ta k'asa kanta yadagi "bedside" tasaki razananiya k'ara yarufe ta da duka tamkar zai rabata da ranta cikin konar zuciya yace, kifad'a mini yadda ki kayi ki ka aure ni"?
Duk tsanani zafin dukan da tasha bai hana mata tunawa da kashadi boka duguzuu kada Ku sake su kwana a d'aki d'aya duk ranarda suka kwana a d'aki d'aya asiri zai k'arye, na'eema tace wayyo Allah na asiri na yatonu dan Allah yaa Amar kayi hakuri wallahi ina sonka bazan iya rayuwa ba kai, tsanani takaici ne yarufe Amar baisan lokacin da yanushi bakinta jini yasoma zuba kamar anbude famfo kin cuce ni na'eema kinyi sanadi rabani da farin ciki na Allah ya esa tsakanina da ke da kyar na'eema ta mik'e ta arce na kare shima ya Mara mata baya tun kafin tak'arasa sauka daga "upstairs" ya cima tun daga sama yake yana jingar ta har suka sauko k'asa raheela da ke had'a kayanta taji ihun na'eema yacika gida da gudu tafito, ta hango Amar yana ta faman "ball" da na'eema gaba d'aya fuskarta tarine da jini a gigice ta esa wurin Amar ta chakume shi, tace kan'ka d'aya kuwa yaa Amar kashe ta za kayi"?
A harzuk'e yace ko na kashe ta bazan huce takaici da bakin ciki abunda ta haddasa min, raheela wannan da ki ke gani muguwa ce azzaluma ce batada imani ta rabani da ke bayan tasan ke ce farin ciki na shikenan na'eema kin wargaza min rayuwa kin rusa duk wani gini na rayuwa ta, domin raheela ita ce rayuwa ta yana karasa zance sa ya zube k'asa yafashe da matsananci kuka raheela tafara ja da baya tsawon rayuwa ta batada amincewa da Amar yana sonta sai yau saida takai karshen bango ta sulele k'asa ta zauna tajuya ta kalli Amar yana durkushe yana kuka ta juya wajen na'eema tana kwance a k'asa ta rusar kuka baki da hancinta na zubarda jini, raheela tafashe da kuka tace me ke shirin faruwa da mu"?
Wane irin sabon al'amari ne yake yunk'uri kunno kai a zuri'ar mu"?
Amar yad'ago jajaye idanu shi yanuna na'eema da yatsa yace na rantsi yadda narasa raheela ke ma kin rasa ni har abada saboda bantaba jin na

Please Login or Register in order to submit comment