Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ture na'eema daga jikinsa hade da cewa "oh shirt"
ya Mike tsaye yanufi kofar fita da sauri kamar zai tashi sama na'eema da ke tsaye fuskarta dauke da mamaki me Amar ya tuna da shi da yahadasa masa wannan saurin haka yana fita ya hango ta jikin fila yaja yayi tsaye yasauke ajiyar zuciya ya qura mata ido ita kuma ta murguda masa baki yayi murmushi yakarasa kusa da ita cikin sanyaya murya yace baby me yahana ki shiga ciki"?
Raheela tayi rau- rau da idanu ta langwabe kai tace yaa Amar ina tsoro haduwa da yaya na'eema bansan wane irin kala maraba za tayi min ba, tsanani tausayi ta Yakama Amar yariko hannu ta yace karki damu raheela tunda nayiwa daddy alqawali zan kula da ke bana tunani akwai wani mahaluki da zai takura ki "fill free baby remember it's your hero house okey"
Raheela ta daga kai alamar ta gansu da kalaman sa with full confidence" tashiga cikin gidan na'eema fito daga kitchen hannu ta dauke da hadade tray da lemon kwali akai da kuma glass cup's" idanu ta suka hasko mata fuskar raheela da Amar sun jero hannu Amar na danke da na raheela batasan lokacin da tasaki tray hannuta cup's suka sauka bisa tiles suka tararatsi ita kuma tadafe kai hade da fadar innalillahi wa'inna illahi raji'um nashiga uku ni na'eema, wace irin masifa ce yau tasauka a gida na?
Babu shiri Amar yasaki hannu raheela yakarasa wajen na'eema yariko ta yace calm down sweetheart" da sauri ta ture shi idanu ta sun kada sunyi jajir tsanani tashin hankali ya baiyana akan fuskarta cikin sarkewa halshe tace you ask me to calm down yaa Amar as how just tell me as how"?
Ta karasa zance ta cikin daga murya da kururuwa, Amar yadafe kanshi yasoma tunani mafita cikin zafin nama na'eema ta esa wajen raheela tafisgo ta wanke ta da mari ta kuma rufe ta da duka, tana cewa wallahi raheela ko kece 'yar sarkin matsafa na duk duniya baki esa ki rabani da yaa Amar ba don haka yau sai na kashe ki in yaso nima a kashe ni, me na tare miki da za ki zabi hanyar musgunawa rayuwata ki barni na rayu da yaa Amar domin ni nafi chanchanta na kasance tare da shi ba ke ba raheela yayida raheela sai kakari mutuwa takeyi domin ba karamar shaqa na'eema tayi mata ba da gudu Amar yakaraso wajen su yadauke na'eema da wawan mari Wanda yahadasa mata sakin raheela bata shirya ba raheela ta zube kasa numfashi ta na fita guda-guda jijiyoyi kanta sun fito radau-radau kwayar idon ta sunyi jajir, Amar yadurkusa gabanta yadago kanta yadaura bisa cinyoyi shi yace........

💃Happy sallah💃

Jeeddah Aliyu🌹🌹
[06/07 10:58 am] Jeeddah aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

{Part 2}
Goron sallah

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

5⃣5⃣

Yace am so sorry" raheela zan dauki mumuna mataki akan, wannan cin kashi da na'eema tayi miki domin ke amana ce a wurina, kiyi hankuri kitashi kinji, raheela takara fashewa da matsananci kuka tace dan Allah yaa Amar ka mayarda ni Kaduna wallahi banaso zaman gidanka domin nasan ba karamin, qalubi zan fuskanta, kafin Amar ya bata amsa na'eema ta karaf tace zai fi miki sauki ki koma Inda ki ka fito don nasha alwashi sai na kassara rayuwarki munafuka alguguma baqar makira mai buri rusa farin ciki 'yar uwa taa kaicho ki raheela da kwakwalwa ki tasa gano miki yaa Amar Mijin 'yar uwa ki ne, kuma na ran........kee na'eema ki rufe mini bakin ki tun kafin ni na qassara taki rayuwa yaa Amar ne yadaka mata tsawa dole, na'eema ta kama baki ta sai faman haki takeyi ta juya fuuu ta haura upstairs" ta nufi bedroom dinta, yayida Amar yacigaba da rarrashi raheela da kyar ya ciyo kanta tadaina kuka yacigaba da fadar tashi mu je na nuna miki room dinki, raheela ta mike tsaye Amar ya shige gaba ta Mara masa baya, saida yakaita har cikin daki sannan yajuya yafice daga dakin.
Raheela ta fada bisa gado tasaki ajiyar zuciya mai karfi, tasoma tausayi kanta saboda tasan duk lokacin da na'eema tayi nassara Kara danqa ta ba, karamin cin ubanta za tayi ba gaskiya ba zan iya cigaba da juri irin wannan wulakanci ae bani nakawo kaina gidanta ba kawo ni akayi mtsss taja dan karamin tsoki, hade da mikewa zauna ta buga dan uban tagumi ta cigaba da zance zuci ni narasa me ke damu yaya na'eema ita har yanzu nata hauka yana nuna mata yaa Amar yana sona, lalle yaya na'eema karamar kwakwalwa ce da ita ko ta manta ne ni da ita uban mu daya har take tunani akwai wata alaqa da ta danganci soyayya tsakani na da yaa Amar"?
Mtsss...takara Jan tsoki kalle yanda ta shake ni kamar za ta rabani da rai na tasaka hannuta na dama tana shafar wuyan nata, sai faman zogi da radadi yakeyi mata musanmman makogwaro ta da takeji sa yana fitarda wani zafi tamkar ta sha tafasashe ruwan zafi, kai ina raheela tafada a baiyane tsanani bacin rai ya baiyana akan fuskarta duk lokacin da yaya na'eema takara kuskure taba ni sai na shuka mata rashin mutunci don ni ba baiwa bace da za ta dinga jingata, duk ranarda nayi mata illah mijinta da kanshi zai mayarda ni inda yadauko ni tasaki murmushi jin dadi domin har ta hango kanta bisa ciyoyi kaka ta Mike da sauri tashiga "bathroom"
Na'eema na shiga dakinta ta fisgo wayarta da ke chaji ta dannawa umma hajara kira saida tayi ringing kusan sau uku tana tsinkewa sai a na hudu umma tadauko, tana karawa bisa kunne ta sautin kuka da kururuwa na'eema yadaki dodo kunne ta a firgice tafara magana ke na'eema waye ya mutu ne"?
Cikin shashekar kuka na'eema tace ba mutuwa akayi ba umma amma na rantsi da Allah gara mutuwa da wannan masifa da tasauka a gida na, wayyo umma nashiga uku na lalace watan kunyar mu da tonuwar asiri mu ya tsaya na tabbata kwano tuwo na yaqare a gidan yaa Amar cikin tsanani tashin hankali mai dauke da rudani umma hajara ta aikawa na'eema tambaya wai meke faruwa ne na'eema kiyi gagawa ki warware mini zare da abawa domin zuciyata cike take da tsantsan fargaba"?
Cikin yanayi na Wanda yarasa mafita da tudun dafawa na'eema ta kwashe abunda ya wakana ta sanarda umma, tsawon dakika uku zuwa hudu umma hajara tadauko tana nazari daga bisani ta nemo abun fada saida tasaki katuwar ajiyar zuciya mai cike da konar zuciya tace amma Allah yatsinewa hajja rahee albarka domin nasan wannan quli aikinta ne, lallai a wannan karo dole na nunawa hajja kaka kuskure ta sai na hadasa mata nadama tura raheela gidanki da tayi zan shiga na fita domin na kawo karshen numfashi raheela a doron duniya sai na zamo sila goge babi ta a duniya koda hakan zai kasance nima na rasa rayuwa ta {kaicho umma hajara jahilci yariga yayi miki kanta kin kasa gano cewa babu yi sai Allah wannan shine furucin da ni yar gidan Shehu aliyu nayi yiwa umma hajara amma kuma mu je zuwa karshen alawa kasa}
Saida umma hajara ta dasa aya a zance ta sannan na'eema tasamu damar kara tofa albarkacin bakinta umma ki taimake ni ki je wajen boka duguzuu yayi aikin da raheela zata mutu saboda ina ji a jikina wannan zuwan da raheela tayi kamar za kawo karshen zama na da yaa Amar, da sauri umma hajara ta katsi ta, ta hanyar fadar kul karna sake jin kinfadi wannan mumuna furuci, yanda raheela ta shiga rayuwa ki ta zamo sila hanaki rawar gaban hantsi nima na rusa rayuwa ta don haka ki kwatarda hankali ki kamar kinyi bako ya mutu a wannan karo raheela bazata kai labari gobe zan dira garin Kaduna kudi ne kawai suka zame mini dole na dauka daga nan sai fada boka duguzuu cikin tsanani jin dadi na'eema tace na gode umma naa shiyasa nake matukar sonki domin duk lokacin da nashiga damuwa kina nemo min mafita, umma hajara tayi dariya tace to wa nake da shi in bayan ke ae dole nayi fito na fito da makiyanki haka umma hajara da na'eema suka cigaba da kule-kule su nagani bayan raheela.
Amar yana fitowa daga dakin raheela "direct bedroom dinshi yashiga kaitsaye bathroom yadosa yasakewa jikinsa "shower" bai dauki dogon lokacin a bathroom ba yafito yashirya jikinsa da white jeans trouser" da t-shirt blue colour" sai faman zanga qamshi turare pure blue" yakeyi masallaci ya wuce yayi sallah azhar yana dawowa daga masallaci yanufi dining table yayi saving din abinci ya dauki lemo kwali na fruitta da glass cup" nufi dakin raheela.
Tabagare raheela kuma tana fitowa daga wanka ta janyo trolley dinta tafito da slick material" riga da siket tasaka sannan tayi sallah tana kamalla sallah taji hanji ta yafara kugi yunwa ga raheela batada hankuri akan yunwa dole na nemowa kaina abinda zan ci in kuma yaya na'eema tayi yunkuri tabani ni ma zan nuna mata nawa kala hauka da wannan zance zuci raheela ta mike ta nufi kofar fita karaf taci Karo da shi, da sauri ta juya ciki daki ta nemi gefen gado ta zauna yakarasa shigowa ya dire plate din hannu shi a kasa ya kura mata idanu kamar yau yafara ganinta saida ya share tsawon dakika biyar yana kallonta yayida ita kuma kanta yana sunkuye yayi gyara murya tamkar mai shirin yi kiran sallah daga bisani ya kiranta sunanta cikin sanyaya muryar mai tsanani sanyi da gardi domin raheela saida ta lumshe idanu ta raheela yakara kiran sunan nata da kyar tayi namijin kokari ta danni zuciyarta sannan ta dago dara-dara idanu ta masu masifar jifa Amar ciki yanayi na zazzafa soyayya ta tace na'am shiru Amar yayi kamar yafasa fadar abunda yayi niyar fada daga bisani ya durkusa a gabanta yace raheela bazan boye miki ba zuciya ta takasa hankuri da juriya akan sonki ina sonki raheela basan ya akayi nafada cikin soyayyar na'eema duk da na aure na'eema zuciyata takasa hankura da ke sonki a cikin jinina yake raheela na tabbata koda za'ayi nassara rabani da sonki tabbas sai an tsiyaye jini jiki na tun lokacin da yafara magana idanu raheela suke fitarda hawaye sai faman aika masa kallon tsana takeyi daga bisani tace.............

Barka Ku da sallah 'yan uwa musulmi Allah ya karbi ibadamu yanuna mana badi. {Ameen}


Jeeddah Aliyu🌹🌹
[11/07 8:44 am] Jeeddah Aliyu🌹: [09/07 6:29 pm] Jeeddah aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

{Part 2}
💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

5⃣6⃣

Gaskiya yaa Amar kwakwalwa ka tana da matsala yanzu kai ko kunya bakaji ina matsayin 'yar uwar matarka amma kana furta mini irin wadanan kalamai, tir da wannan dabi'a taka irin ta karnuka kum...cikin zafin nama yakai mata wawa duka a baki Wanda yahadasa mata hadiye sauran kalaman ta, a harzuke yace don tsabar iskanci ni zaki danganta da karnuka"?
So ba karya bane raheela ina sonki kuma har abada bazan daina sonki don haka kiyi duk abunda zaki iya banza 'yar reni hankali tsanani mamaki ne yarufe raheela sai faman zarar idanu takeyi wai yaa Amar wane irin shu'umi mutum ne??
Harara galla mata yace daina kallo na in baso ki keyi na tsiyaye miki kwayar ido da sauri ta sunkuyarda kanta tana shafar labba ta, ya mike tsaye hade da daukar plate din abinci da yakawo mata, gani zai fice da abinci yasa tayi magana cikin sarkewa halshe yaa Amar yunwa nakeji fa, a fusace yajuyo yace sai ki nemo kare da zai baki abinci ta marairaice murya tace ni dai dan Allah kayi hankuri kabani abinci naci kallon uku saura kwabo ya watsa mata daga bisani yace ae nayi tsanmani a matsayin iya shegenki zaki iya jure yunwa shiru tayi takasa furta komai saida ya dama don kanshi ajiye Mata "plate" din daga bisani yajuya yafice daga dakin raheela ta raka shi da katuwar harara tadauki plate din tafara lodawa hanji ta abinci, tana ci tana zagin Amar cikin zuciyarta ta kuma kudiri aniya ko da bala'e second semester" bazata zauna a gidansa.
Amar na fita kaitsaye dakin na'eema yanufa tana kwance akan gado ta dukufa wurin nemowa kanta mafita yayi sallama yakarasa kusa da ita, a sanyaye ya kira sunanta kamar jira takeyi sai kawai tafashe da kuka da sauri Amar yadago ta ya manna ta a kirjin shi, yasoma rarrashi ta kiyi hakuri na'eema nima ba'a so raina na mare ki ba gani nayi kina kokari aikata mumuna aiki shiyasa na dauki wannan mataki amma har ciki zuciya ta banji dadi faruwa hakan ba na'eema ta share hawaye fuskarta ta zare jikinta daga nashi tace to me tazo yi a gidanan ni na tabbata zuwa raheela babu alkhairi a cikin sa domin gashinan tun ba'aje ko ina ba kafara duka na akanta don Allah yaa Amar in har da gaske kana sona kana kuma son farin cikina da kwanciyar hankali na raheela ta koma Kaduna a gobe wannan shi zai tabbatar mini da cewa babu saura son raheela a zuciyarka Wani shegen murmushi Amar yasaki duk kwarewa mai karatu da son kwan bazai iya gano me wannan murmushi na Amar yake nufi, ciki kwarewa da iya sarafa zuciyar na'eema yafara tsara ta haba my sweet na'eema ke ko ance da ke ina son wannan shashasha yarinya zaki yarda ne"??
Ae raheela "she is not my type" me zanyi da ita yarinya da Sam batada hankali ae ko daga ni sai ita mukayi saura a duniya ba abunda zanyi da ita ko yanzu da zata zauna a gidanan zata zauna ne albarkaci daddy amma ke kanki kinsan "I hate her" so kidaina tada hankalinki akan wannan kwaila yarinya tsanani ki da ita ido banaso kina shiga harkata ba ruwanki da ita a sannu zan koya mata hankali kuma daga yau matukar tana gida duk wani aiki na gidanan ita zata dinga yi ke kuma ki dinga yi min kwalliya ina kallonki ina Kara sonki ae ni 'yar aiki na kawo miki, na'eema ta kyakyale da dariya farin ciki ta qanqame Amar tace shiyasa nake matukar sonka, my hubby" Amar ya sunbace gefen wuyanta yace my na'eema yunwa nakeji mu je kibani abinci da sauri ta Mike hade da fadar yanzu yaa Amar baka ci abinci ba"??
Amar ya kashe mata ido daya yace ta yaya zan iya cin abinci gimbiya ta tana fushi da ni na'eema ta kara langwabe kai kamar qadangarwa yayida dadi yake ratsa sassa jikinta kafin tadawo da natsuwarta Amar ya sunkuce ta yanufi falon kasa da ita sai faman kyakyala dariya sukeyi suna saukowa kasa dai-dai lokacin da raheela tafito domin ta ajiye "plate" kallon daya tayi musu ta kauda fuska ta nufi "kitchen" ta ajiye plate din tafito har tayi kusan kaiwa kofar dakinta Amar ya kwada mata Kira kee raheela zo nan'
Shiru tayi zuciyarta na tafarfasa domin tasan wani wulakanci ne ya shirya mata yadaka mata tsawa cikin hargowa yace ba kiranki nakeyi ba raheela takarasa wurin shi taja tayi tsaye ta kuma sunkuyarda kanta kasa saida yagama shan qamshi sa yace abunda nakeso da ke daga yau duk wani aiki na gidanan ke zakiyi tun daga kan wake-wake, shara har izuwa kan girki ke dinga yi a firgice raheela tadago idanu ta tana qare masa kallo daga bisani ta yatsine fuska hade da tabe baki Amar yace ko bakiji abunda na fada bane da kika wani tsare da ido"?
Raheela ta murguda baki tace naji amma a cikin abubuwa uku nan da ka lissafa guda biyu kacal zan iya sai ka nemo wanda zai dinga yi ma guda daya, har ta dasa aya a zance ta Amar yana kallonta kafin yayi magana na'eema tayi karaf tace baki esa ba wallahi ae nan ba gidan kaka bane Inda ki ka saba zuba iya shege ki a kyale ki tun da ki ka zabi ki zauna a gida na dole ki bauta mini in kuma ba haka ba sai ki tattara shirgi ki, ki koma inda ki ka fito raheela tayi mata kallo ke a suwa dan wake a "hotel" tace yaya na'eema kenan kedai kina taqama da wannan kango wannan abin ne gida ta nuna falon da yatsanta takara yatsine fuska tacigaba da cewa ni bana kallon wannan abun a matsayin gida ke ya eshe ki na'eema ce tadaka mata tsawa ta mike tsaye da suna ta tunkuri wurin raheela tayi mata dukan akawo wuka Amar ne yataka mata birki ta hanya rike hannuta, yace tadawo ki zauna my na'eema ki barni da ita ae tafi kowa sani halina banida kyau bata tsokano ni ba na lakada mata duka ballatana tashiga gona ta kawai ki zuba ido ki sha kallon yanda zan girbe ta ya mike yanufi wajen da raheela take tsaye raheela nagani haka tafara ja da baya na'eema ta kyakyale da dariyar mugunta kafin yakaraso raheela ta kwasa da gudu tafada "bedroom" dinta ta murza key Amar yayi tsaye yana shafar sumar kanshi fuskar dauke da murmushi mtss.. Na'eema taja tsoki domin haushi Amar yabata sakamako murmushi da taga yanayi cikin zafin rai tanufi bedroom dinta Amar yabita da kallo ya tabe baki yadauki Key's din motarsa yafice daga gidan...
[11/07 8:42 am] Jeeddah aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

{Part 2}
💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

5⃣7⃣

Raheela na rufe kofa tayi kwanciya ta tadauko wayarta ta kira kaka, raheela naji muryar kaka tasaki ajiyar zuciya cikin shagwaba tace kaka nayi kewarki kaka tace nima haka raheela wannan boko banyi min adalci da ya nisanta ni da ke raheela tayi dariya tace to ya za'ayi kaka tunda daddy yanace akan sai nayi karatu anan kawai ki tayani da addu'a kaka tace addu'a inayi raheela saidai nakara bisa ga wance nakeyi miki Allah yayi miki albarka ya tsare min ke "ameen kaka raheela tafada hade da share hawaye fuskarta kaka tace ina fatar mutane gidan basa takura miki"??
Raheela tayi murmushi tace kaka kenan ko kwana daya banyi ba ta yaya za'a takura min"?
kaka ta kyabe baki tace halin mutane gidan nasani daga maigidan har matar gidan basuda kirki duk Wanda yataba ki, ki kirani a waya ki ga yanda zan cin mutunci mutum, raheela tayi dariya tace ba Wanda zai taba ni kaka ni da nazo karatu Ina ruwa na da shiga sabgar mutane gida kawai abunda nazoyi shi zanyi, kaka tace da kyau 'yar albarka ki kula da kanki kinji"?
To kaka ki gaida gida"
Gida zai ji"
raheela ta kashe wayarta kamar jira akeyi tagama waya da kaka "call ya shigo gani sunan da ke kai kawo bisa "screen" yahadasa mata faduwa gaba me wannan dan duniya yake nema a wurina"? mtss... Bazan dauka ba ballatana har yasami damar fada mini maganar banza yayida wayar tacigaba da "ringing" raheela ta ya mutsa fuska tamkar za ta fashe da kuka a baiyane tace gaskiya yaa Amar tsoho maye ne ko akan wane dalili zai dameni da kira"?
Mtsss... Dan reni wayo kawai bara na dauka naji da wane sabon iskaci yazo min da shi danna received" a fusace tace "hellloo"
Amar take kwance a falon Dr kabeer yace "what's my baby doing"?
Raheela ta zaro idanu tace bansaniba, Amar yasaki mushiriki murmushi yace ina fatar ba wani laifi nayi da ya hadasawa baby naa fushi da ni"??
Saura kiris raheela ta kurma ihu domin ita yafara fin karfinta duk haka sai ta zabi hanyar zazzaga masa rashin mutunci lamba daya ko Allah zai sa ya harzuka yafita hanyarta, wai ka yaa Amar wane irin banza ne maras zuciya"? kaifa mijin 'yar uwa taa ne in har kai baka gudun abin kunya ni ina gudun sa, Amar ya zaro ido tamkar yana gaban raheela cikin zafi rai hade da konar zuciya yace raheela ni za ki kira da banza"??
Eh" na kira ka din tunda nake bantaba gani banza irin ka mai budurwa zuciya shu'umanci ka na banza ne tunda a gaba yaya na'eema bazaka iya furta mini Kalmar so wannan shi ya tabbatar mini da cewa kai nusari ne kuma duk rana da ka kuskura ka kara furta mini wannan shirme naka sai na fadawa daddy domin yanzu na fahimci kadaina tsoron kaka, mtss shashasha kawai batare da ta jira jin abunda zai fada ba ta kashe wayarta, Amar ya kurawa waya ido sai faman huci yakeyi, Dr kabeer yafito daga kitchen hannu shi rike da lemon kwali da cup's gani yanda Amar yake huci yasa ya jefa masa tambaya ta hanyar fadar kai kuma kai da wa irin wannan huci haka"??
A fusace Amar ya mika hannu bisa "stool yadauki kwali sigari ya zaro guda daya yacila mata wuta cikin konar zuciya yake zukarta yayida Dr kabeer yake aikin kallo shi, saida ya zuke sigari tass ya jefa "filter cikin ashtray" yadafe kanshi hade da sauke ajiyar zuciya, Dr kabeer yakara jefa masa tambaya wai meke faruwa ne da wa ka ke waya ne"??
Cikin sanyi murya Amar yace raheela ce kb da raheela nake waya me nayiwa raheela ta tsaneni"??
Cikin dinbi mamaki Dr kabeer yafurta sunanta raheela cabdijam dama har yanzu Amar son raheela yana tare da kai"??
Amar ya yatsine fuska yace kwarai kuwa kb har gobe ina son raheela"
Amma kasan wannan kuskure ne koh"?
I known kb but nima bansan me ke damu na zuciyata tazamo bana iya sarafa ta itace take sarafa ni wasu lokuta zan ji na tsani raheela tsana mai tsanani gaske a wani lokacin kuma sai naji duk duniya ba mace da nakeso irin ta I don't known what's wrong with me" Amar yakarasa zance sa hawaye suka wanke masa fuska abinda yakara jefa Dr kabeer cikin firgici kenan da sauri ya zauna kusa da Amar cikin sigar rarrashi yace kadaina kuka Amar nasan daci da zafi da so yakeda shi, amma na tambaye ka mana"?
Amar yadaga masa kai, Dr kabeer yacigaba da cewa Amar kadaina son na'eema ne sannan kuma kanada labari cewa babu aure tsakani ka da raheela"??
Amar yasaki ajiyar zuciya hade cewa kb ina matukar son na'eema babu abunda ya sauya daga dinbi soyayya da nakeyi mata, ina sane da cewa raheela ta haramta a gareni ae ni ba jahili bane nasan abunda nakeyi"
Harara Dr kabeer ya watsa masa cikin baci rai yace in har kai ba jahili bane to kai kursugumi dan iska ne tayaya zaka bari shedan yayi tasiri a zuciyarka ka hade soyayya'r ya da qanwa wannan ae ganganci ne kayi kokari ka rarrashi zuciyarka ta hakura da soyayya raheela gudun tafka abin kunya.
Har Dr kabeer yadasa aya a sharhi sa Amar yana kallon shi saida ya share tsawon dakika biyar yana kallon Dr kabeer daga bisani yace bazan iya daina son raheela saboda son ta yariga yazame mini jini jiki na kawai zanyi kokari nadanne duk wani " feeling's da nakeji akanta koda hakan yanufi ni zan rasa nawa kwanciyar hankali zan tattara duk wata soyayya da nake yiwa raheela nadawo mata yaa Amar din da tasani a bayan zan dawo mata mugu maras tausayi amma ba wai don na daina sonta ba.
Mtss... Dr kabeer yaja tsoki hade da cewa chan ta matsi maka ita dai bata kallo ka a matsayin masoyi saidai Mijin 'yar uwar taa don haka iska ne kawai yake wahalarda mai kayan kara"
Amar yayi miqa hade da cewa kb kenan bakasan so bane shiyasa amma da kasan dadi da radadi so da ka tausaya min
Kb ya tabe baki yace "please mu ajiye zance raheela a gefe mu yi zance da ke gaban mu.
Ta bangare raheela kuma tana ajiye waya tafashe da kuka tafara zance zuci na Shiga uku ni raheela wannan wace irin masifa ce yaa Amar yake yunkuri jefa ni a ciki"??
Takara fashewa da kuka cikin shashekar kuka tafara magana kamar wata zarara wallahi na tsane ka yaa Amar kuma har abada bazan taba sonka, tsanani na da kai kiyayya ce kuma duk ranarda ka kara furta mini kalma son

Please Login or Register in order to submit comment