Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta, cikin wannan yanayi su ka fito daga ciki'n mota raheela, na hango Amar da na'eema takara fadada murmushi'nta.....

Jeeddah Aliyu🌹🌹
[18/06 8:37 am] Jeeddah Aliyu🌹: [12:51PM, 5/31/2016] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN
'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~4⃣7⃣~

Amar ya ja ya tsaya a gaban'ta fuskar'shi a sake yace 'yan mata kaka''
Raheela tace ina kwana yaa Amar takara juyawa waje na'eema wance take ta faman watsa mata kallon banza tace ina kwana yaya na'eema"?
Mtss...Na'eema taja tsoki hade cewa da ban kwana ba kya gani munafuka kawai, ta raba gefen raheela ta wuce tana kai wa kofar da za ta shige ainihi gidan, ta labe tana leko su, raheela tasauke ajiyar zuciya cikin bacin rai wanda ita batasan lokacin da ya lullube ta ba tafara magana, kana kallo zazzafa kiyayyar da ta wanzu tsakanina da 'yar uwa ta kuma kaine sila, yaa Amar miyasa yaya na'eema takasa gano cewa duk wani furucin Ka akaina ba gaskiya bane"?
Shin in har da gaske kana sona miyasa ka aure yaya na'eema"? Batare da tajira amsa da zai bata ba tacigaba da magana hawaye na zuba akan fuskar'ta, shin ita yaya na'eema wannan bai esa hujja da za tagano cewa Kayi, amfani da kalma so akaina ne domin ka tarwatsa min farin ciki ka kuma rura wutar gaba a tsakani na da ita, na roke ka yaa Amar ka sanar'da matar ka baka sona ka tsane ni ka fada mata cewa babu wata halitta da ka tsana, ka ke nunawa zalla kiyayya iri na koda hakan zai dawo da kyakyawa alaqa da ke tsakanina da yaya na'eema, takarasa zanceta tana mai rushewa da kuka mai sautin gaske yayida hawaye da majina suka chakude akan fuskar'ta.
Tun lokacin da raheela tafara magana Amar yake kallon'ta zuciya'rshi, cike da takaici'n ashe duk wannan hauka da yakeyi akan raheela ita bata dauke shi, a matsayin SO ba kenan har yanzu raheela kallon makiyi take yi min, yasauke ajiyar zuciya wani iska mai zafin gaske yafito daga bakin'shi, zuciyar'shi na tafarfasa ya bude bakin'sa da kyar yanayi sa tamkar na mai ciwo hakora, yace duk abunda zan fada miki a yanzu bashida amfani raheela, iya abunda zan iya cewa da ke ni ba makiyi ki bane ni masoyi ki ne na hakika, nafara son'ki raheela tun ranar'da da ki ka fado duniya shin ta yaya za ki danganta hakan da kiyayya"?
Yadago fuskar'ta da ke sunkuye tana kallon kasa ya zare lollipop din da ke ciki'n bakin'ta wasu yawu masu yauki su ka lullube lollipop din, ya kuma ciro farin "handkerchief ya goge mata hawaye masu hade da majina a zuciya shi yace raheela rigima duk, wannan kuka da akeyi lollipop na makale a baki a, baiyane kuma sai, yace banaso kukan ki raheela domin yana kona mini rai nayi miki alqawali zan dai-daita tsakani ki da na'eema kinji"?
Batare da raheela ta kalle shi ba tadaga kai ta kuma juya ta nufi, gate yayida shi kuma ya bi ta da kallo, daga bisani yajuya jiki ba lakka yashiga part din iyayye shi. na'eema da ke tsaye tana kallon abinda yawakana a tsakani su ta toshe bakin'ta sakamako kuka da ya kunbuce mata, da gudu takarasa shiga gida direct falon umma hajara tafada umma hajara da ke zaune tana fama da dinbi mamaki furucin raheela, sai kawai ta ga na'eema tafado gaban'ta, tana kuka rija-rija kamar ranta zai fita.
Tsoro hade da firgici suka sami mazauni akan fuskar umma, cikin sarkewa halshe tace na shiga uku ni hajara Allah yasa ba watan kunyar mu ne ya tsaya ke daina wannan kuka nake wanda bashida amfani ki warware min zare da abawa tun kafin Zuciyata, ta yi kuli-kuli kubra ta fado gabanki"?
Na'eema ta tsagaita da kuka da takeyi tace yaa Amar da raheela s....da sauri umma ta zabura ta rufe mata baki tace karki ce komai tashi mu shiga daki kada ki fada yafada kunne makiyi su yi mana gori ta riko hannaye na'eema su ka shige bedroom din'ta ta zaunarda ita a gefe gado ita ma takai zaune tace inajinki na'eema, fada mun abinda Amar da annoba su kayi miki wanda ya hadasa miki wannan kukan na bala'e.
Nan take na'eema ta kwashe abunda yake faruwa, tun daga ranar'da ta dire gidan Amar kalar wulakanci da yanka kauna, da yakeyi mata duk ta dalilin raheela tana dasa aya umma lailayo asshar ta durawa raheela, sai faman huci takeyi tabbas tsugunna bata kare ba, ya zame mini dole na koma waje boka duguzuu, ko ta wane hali sai naga bayan raheela, na'eema ta karbe zance ta hanyar cewa umma ahalin yanzu na fi so gani bayan raheela banaso na cigaba da gani raheela tana numfashi, kirka saka tausayi a zuciyar'ki so nakeyi raheela ta zama gawa ko kuma takarasa rayuwata a bola tana tsice-tsice, dole raheela ta mutu ko ta haukace umma domin shine hukunci da yafi dacewa da ita tashiga rayuwa ta da yawa, in bacci mijina yakeyi sunanta yake kira in kuma yana falke sam baya gajiya da anbato sunanta, inda kuma ya yi tarayya da ni da sunanta yake kira na, kodai boka nisanta zuciyar Amar daga kanta ko kuma ta mutu ko ta haukace, domin shine hanyar da farin ciki na zai wanzu nima, na dandani dadi da ma'aurata suke ji a gidanje aure su, takarasa zanceta hade da rushewa da wani irin rikitace kuka.
Da kyar umma tayi nasara shawo kan'ta tadaina kuka umma tace Ki kwatarda hankalinki, ki zuba ido kisha kallo za ki ga irin mumuna hukunci da zan dauka a yanda zuciyata ta cika da tsanani kiyayyar raheela ko wane irin aiki zan iya aikatawa akanta tashi maza ki bi mijin'ki ku tafi tun da kina da ni matsalar ki ta zo karshe, na'eema ta mike, tana sharar hawaye umma ta mara mata baya suna fitowa su kaci karo da Amar da aunty amarya zaune a babban falon suna fira, Amar ya gaida umma ta amsa adakile daga bisani, Amar ya mike yace aunty za mu tafi"
Aunty amarya tace to Amar Allah ya tsare ya kai ku lafiya"
Amar ne kadai ya amsa da Ameen!"
Da suka yi sallama Amar yadauki hanyar abuja zuciya'rshi cike da kunci musanman in ya tuna kalaman raheela da kuma wanda kaka tafada masa lokacin da yashiga bangare ta domin ya yi mata sallama, tafiya kurame su kayi Amar "driving kawai yakeyi hade da tunani raheela yayida na'eema ta kifa kanta tsakiyar cinyoyi ta tana tunani makomar rayuwar ta.....
[9:11PM, 5/31/2016] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~4⃣8⃣~

Gani shiru nasu ya yi yawa yasa Amar ya kunna tape yasaka kira'a al'qur'ani mai girma ya kuma jefa lollipop" din da ya karba daga hannu raheela cikin baki'nshi yana tsotsa a hankali, abunda yakara jefa na'eema ciki gagarumi tashi hankali, saboda ta ga lokacin da Amar yaciro "lollipop din daga bakin raheela, ta ja tsoki mtwww...ta kuma galla masa harara yayida Amar "driving kawai yakeyi bai ma san tana yi ba.

Raheela na fita, ta nufi gidan su zainab a bakin gate din gidan taci karo da Zainab, kallo daya Zainab ta yi mata tagano cewa ta ci kuka me ke damu ki raheela naga kamar kiyi kuka"?
Raheela tasauke ajiyar tace bari kawai zainab ina gani kamar hero yana da matsala a "brain din'shi Zainab ta kyalkyale da dariya tace, laifi me ya yi miki ne ko dukanki ya yi saboda nasan duka ki ba ya yi yiwa "hero wuya"?
Mtsww...raheela ta ja tsoki hade da cewa, da yake ni jaka sa ce dole yadake ni, ke matsala ki kenan ba ki iya shan labari ba, raheela takarasa zanceta tana murguda baki.
Zainab takara kyalkyalewa da dariya tace fada tsakani ki da hero raheela ba ya qarewa, raheela ta tabe baki tace, umhh...nan take ta kwashe abunda yafaru tsakani ta da yaa Amar tafadawa zainab, saida suka share tsawo dakika uku zuwa biyar sannan Zainab tace, ni fa tuni nagano cewa hero yana sonki raheela, musanman wasu lukuta ina lura da irin yanayi kallo da yake miki da fitinanu idanu shi nagane kallon SO" ne.
Har Zainab takarasa magana raheela take mata kallo uku saura kwabo daga bisani tace kema bakida hankali Zainab ko kin manta tun ina yarinya yaa Amar yake nuna mini zazzafa kiyayya, ke ma da ki ke qawata ya sha siya miki abu ni yahana ni ko nayi ko banyi ba yaa Amar sai yanemo laifi yadaura min don kawai yadake ni babu komai tsakanina da yaa Amar daga duka sai hantara ko yanzu ya furta yana sona ne don yarabani da farin ciki ya kuma datsi kyakyawa dangantaka da ke tsakanina da yaya na'eema kuma ya yi nasara.
Zainab tace ke ce ki ke kallon hakan a matsayin kiyayya.
Raheela takara harzuka cike da jin haushi furucin Zainab tace to ya eshe ki haka banaso ki Kara cewa komai, Zainab tayi murmushi tace shikenan nayi shiru da wannan zance suka karasa islamiyya.

************************

ABUJA********

Tun daga lokacin da su Amar su ka esa garin abuja, ya nunawa na'eema bedroom din'ta bata kara sanya shi a idanu'ta ba, gani yunwa za tayi mata lahani yasa ta yanke shawara shiga kitchen ta nemawa kan'ta abunda za ta ci tadafa indomie ta dan tsakura sama-sama ta kuna kayan kallo ko za su rage mata zaman kadaici da takeyi Sai misali karfe 10:08 na dare Amar yadawo yashigo falo hannu shi rike da leda mai dauke da take away" ya mikawa na'eema ya nufi upstairs inda badroom din'shi yake har yafara haura stairs na'eema tadakatarda shi ta hanyar cewa, ka tsaya mu ci abinci saboda ni yunwa nakeji, batare da yajuyo ba yace ki ci kawai naki ne ni naci nawa, yana karasa zance'sa da dan gudu sa ya hura stairs" din.
na'eema tasauke ajiyar zuciya, hade da bin shi da kallo daga bisani tanufi kitchen ta dauko "plate ta juye abinci ta cika tumbi ta tana karasa cin abincin ta nufi bedroom din'ta tasakewa jikinta "shower ta shafe jikin'ta da lotion ta dan shafa powder" da lips clove" ta dauko wata fitinaniya night gown pink & white colour" ta kawata jikin'ta da ita turare kuma ita kan'ta batasan adadi da tafesa, ta dauko wani chingum" ta jefa shi ciki'n bakin'ta ta nufi bedroom din Amar ta murda handling tashiga dakin yana tsaye gaban mirror yana fesa turare tashigo kallo daya ya yi mata yadauke kai sakamako wani yanayi da yafada, tanemi gefen gado ta zauna tana tauna chingum tana lumshe idanu da yake chingum din yana kara motsa sha'awa ciki'n dakika biyar zuwa bakwai tasoma fita daga haiyyaci ta Amar karasa bisa gado ya kwanta da sauri na'eema tafada kan'shi tasaki kuka makirci me nayi maka yaa Amar, da ka ke fushi da ni tun da mu ka shigo garin abuja kafita bakadawo ba sai yanzu"?
Kamshi turare ta ya hadasawa Amar jin tsanani sha'awar ta nan take ya lalube bakin'ta yasoma aika mata da sakoni masu tsanani zafi tuni na'eema takara didicewa, da kyar Amar ya iya mika hannu shi yakashe bed side lamp" ranar na'eema ta taki sa'a Amar ya rinjaye zuciya'rshi bai kirata da suna raheela ba, hakan ne yasanya na'eema farin ciki maras misaltuwa, don haka ta ji kamar ace dare shine first night" din'ta.

WASHE GARI******
A garin kaduna kuwa tun da sanyi safiya umma hajara ta dauki hanyar kauye da boka duguzuu yake, umma zaune a gaban kwaya tsafi boka duguzuu, tana Kallon shi, yana ta faman tsoki burutsu, daga bisani ya kece da kazamar dariya ya zaro jajaye idanu shi masu matukar ban tsoro da firgitarwa ya kuma bude bakin'sa mai tsanani wari hade da hamami kamar moshi jaki yace........

Jeeddah Aliyu🌹🌹
[18/06 8:37 am] Jeeddah Aliyu🌹: [2:12PM, 6/3/2016] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN
'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~4⃣9⃣~

Keee" wace irin sakarai ce shashasha ya za'ayi aljana inna ta wahala ta nemowa 'yarki gurbi a ciki'n zuciyar Amar amma ki ka yi sake da laya da mu ka baki har kaka raheela ta yi nasara kona ta bakisan cewa wannan laya ita ce za ta hadasa kiyayyar ta zuciyar Amar, sauki ki daya asiri da aka yiwa amar yaso na'eema bai karye ba da, sunan yar'ki wulakantata,domin wulakanci da za ta gani sai yafi wannan, karbi ya mika mata wata batta mai lullube da fatar maciji, yace wannan sunan shi, manta kowa, matsi akeyi da shi daga zarar Amar ya yi tarayya da yar ki shikenan ba zai kara tunani kowace 'ya mace sai yar'ki hatta da mahaifiyar'shi zai manta da ita{wa'iyazubillah Allah yashiga tsakani mu da bin tafarki shedan} amma ina gargadi ki da babbar murya ka da ki sake Amar da raheela su kwana daki daya matukar, hakan tafaru asiri ki zai tona.
Tun lokacin da boka duguzuu yafara zuba umma ta ke masa kallon hadari kaji gani ya yi shiru ya kuma tsare ta da tula-tula idanu shi, yasa tace haba boka ko da yaushe, gargadi akan kalma daya ne kada na saki Amar da raheela su kwana daki daya me zai sa su kwana daki daya sai kace 'ya'ya hasarari"? Duk banaso raheela ban ki ace tadawo magajiya karuwai, amma bana tunani za ta iya aikata masha'a don haka kadaina wannan gargadi naka maras ma'ana balle fa'eda, umma karasa zance'ta hade da ya motsa fuska.
Cikin zafin rai hade konar zuciya boka duguzuu yadaka mata tsawa, kee bakar ja'ira ni za ki yiwa bakada ko kin manta da baza ta ki ke rawa in ki ka kaini bango na juya miki baya hatta, da uwar'ki mai datti dan kwali wance ko wanke baki batayi sai bala'e da masifa ta sun shafe ta har ni za ki kalla ki ce wai su ba 'ya'ya hasarari ba ne in har su ba 'ya'ya hasarari ba ne ae ke da 'yar ki 'ya'ya harasa ne duk mutumi da shedan ya kadawa gangar sa dole don ubansa yadaka rawa a fada boka duguzuu mai aljana inna da aljana barahaza, don haka ki kiyaye ni tashi maza ki bace mini da gani,tun kafin na chanza shawara nayi miki wanka alkaba'u.
Ae kuwa umma naji boka duguzuu ya abace wanka alkaba'u ta mike da sauri jikin'ta na bari ta zazzage masa Jakarta har ta juya sai kuma ta dan dakata a bakin kofar bukka tace boka ya zance haukata, raheela"?boka duguzuu ya galla mata harara ya ce babu shi domin kin riga kin bata rawarki da tsalle, sai ki je ki yi amfani da iya abunda ki ka samu daga gareni, dole ta fice domin tana tsoro fushin dan asarariya a zuciyar'ta tace shege duguzuu bakin al'muri mai siffar 'yan wuta yanzu duk wani buri da na zo da shi akan raheela yatashi a banza, amma ba komai ae sannu-sannu bata hana zuwa saidai ajima ba'a kai ba da.
daga fadar boka duguzuu umma hajara ta zarce garin abuja kaitsaye gidan Suwaiba ta yada zango, bayan sun gama gaisawa da suwaiba nan umma tafara bata labari dalili zuwan ta Abuja, suwaiba ta yi ihu hade da shewa su ka tafa ita da umma daga bisani, suwaiba tace shawara da zan baki kada ki sake ki je gidan yanzu domin Amar zai iya dasa aya tambaya akanki, mafi al'khairi a tare da ke, ki bani guzuri'n ni zan karasa saura aiki, umma hajara ta yi murmushi ta zuge katuwar handbag dinta tafito da guzuri boka ta miqawa, suwaiba tace ki tabbata wannan saqo ya esa hannu na'eema yau dinan domin kinsan ba'a bori da sanyi jiki, Suwaiba ta kyabe baki, tace Ramlat na dawowa daga "school zan danka mata shi, ta kai mata da haka umma hajara tajuyo garin kaduna.
Raheela da kaka na zaune a falon yayida raheela take ta faman buga "game na zuuma a wayarta, kaka tace, wai raheela ba za ki ajiye wannan 'yar banza wayar nan ki dauki littafi ki, ki yi karatu, salon kuma gobe ki eshe ni da surutu kinada jarabawa bakiyi karatu ba.
Raheela ta turo baki hade da cewa ke dai kaka na fahimci kin kula kyakyawa kiyayya da wannan waya, nima ba don son da nakeyi mata ba da tuni na mayar wa yaa Amar da tsiyar'sa, kaka ta tabe baki tace anyi ba'ayi ba daukar makaho hoto, raheela ta kyalkyale da dariya daga bisani tace in banda wauta me zai kai makaho daukar photo"?
Kaka tayi murmushi, batare da takara furta uffan Ba tacigaba da kallo da ta ke yi, gani haka yasa raheela tacigaba, da fadar duk lokacin da na tuna yaya na'eema na fushi da ni banaji dadi, kuma na tabbata wani abu da na'eema ta ke yi min kai gani kasan saka ta akayi saboda ba hali ta bane, shiyasa har abada ba zan daina yiwa yaa Amar tofi Allah ya esa domin shine silar kawo sabani tsakani na da ita raheela ta karasa zanceta tana mai zubarda hawaye.
Kaka taja tsoki mtwww...hade da cewa kuruci dangin hauka lalle raheela kurciya na damu ki wannan shi, ake kira rashin sani yafi dare duhu, kafin ki yiwa Amar Allah esa kifara daga kan na'eema da uwar'ta hajara domin su ne bakake munufukai, marasa tsoro Allah" ae ni kallo su kawai nakeyi jira nake naga iya gudun ruwan su don haka tsakani ki da Amar ido banaso nakara ji kiyi mishi Allah ya esa.
Raheela tasauke numfashi cike da rashin sani inda kaka ta dosa tace, ni fa kaka ban fahimce ki ba"?
Kaka dan murmusa tace a hali'n yanzu ba za ki fahimce ni ba raheela amma lokaci na zuwa, da za ki fahimce inda na dosa don haka mu ajiye wannan zance ki tashi ki je debo abinci ki ci banaso zama da yunwa, raheela ta mike tsaye ta nufi kitchen zuciyar'ta cike da wasiwasi abunda kaka take nufi da wadanan kalamai nata masu kama da halshen damo.

ABUJA************
Ramlat ta danno hanci mota ta a farfajiya gidan Dr Amar matawalle, ta nufi parking space" ta yi parking tafito daga ciki'n Mota tana sanye da wani tsadade leshi wanda akayi wulakantace dinki, ba mayafi a jikinta sai wata katuwar "handbag" rike da hannu'ta na hagu, har tajuya za ta shiga cikin gida taji anyi horn" da sauri ta mayar'da hankali ta bakin "gate" gani wanda ke Cikin motar yasa taja tayi tsaye har yakaraso sai wani murmushin yaudara ta ke yi Amar yafito daga cikin motar'sa yana rike da briefcase" kallo daya ya yi mata yadauke fuska cikin kwarewa da bariki Ramlat tace barka da zuwa Dr"
Ya yatsine fuska amsa a dakile yauwa, ya yi sauri yashige cikin gida, yayida Ramlat ta bi shi da mayatace kallo daga bisani ta juya ciki'n mugun nufi tashiga gida.
Kaitsaye Amar ya zarce bedroom" dinshi hakan ne ya bawa Ramlat damar zaiyanewa na'eema yanda za tayi amfani da guzuri, boka duguzuu ciki'n tsanani jin dadi na'eema tace lokaci ya yi da nima zan shana a gidan aure na tabbas raheela tashiga rayuwa ta da yawa shiyasa ni ma banida buri da wuce naga bayan'ta, Ramlat ta tabe baki tace ni dai tashi ki kawo min ruwa nasha, ciki'n zumudi na'eema ta mike ta ajiye phone" din'ta bisa kujera da tashi akai tashiga kitchen da sauri Ramlat ta mika hannu tadauki wayar, tashiga "contact" tafito da ta, ta daga handbag tadauki wata number" ta mayar'da wayar inda tadauko ta, na'eema tashigo da tray" a hannuta ta ajiye shi bisa "stool" ta tsiyaya lemo a cup" ta miqawa Ramlat, a yatsine Ramlat ta karba ta dan kurba sau biyu ta ajiye ta kuma mike tsaye, tace ni zan wuce saboda naga Dr yadawo na'eema ta yi murmushi tace na gode Ramlat ki gaida aunty, za taji Ramlat tafada kaitsaye yayida na'eema ta nufi bedroom din Amar zuciyar'ta fal farin ciki.

*****BAYAN SATI BIYU*****

Tsafi gaskiya mai shi domin yanzu na'eema ta mallake Amar sai abunda tafada, tuni Amar ya manta da wacece raheela ko sunanta bayaso ji, hankali na'eema ya kwanta tana cin duniyarta da tsinke, Amar yana matukar sonta kamar ya yi haukata yayida ita kuma take mishi biyayya hade kissa da kisisina saidai su ka share wata biyu sannan su ka waiwaye garin kaduna, kwana daya su kayi tak su ka juyo birnin tarayya na'eema ta yi matukar jin dadi saboda har su ka dawo Amar bai hadu da raheela ba.......
[6:14PM, 6/3/2016] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~5⃣0⃣~

A kwana a tashi asara mai rai gashi har raheela ta kamalla "secondary school" a lokacin ta cika 18 yrs a duniya duk wani alama na budurci yakara baiyana a jikin'ta tsanani kyaun ta yakara fitowa, tana kwance a falon kaka tana karanta hausa novel a phone dinta, ta shagala da abunda takeyi sam bataji shigowa mutum a falon ba sai jin tayi a fisge waya daga hannu ta, a firgice ta mike zaune idanuta su ka sauka bisa fuskar nazeer ta galla masa harara tace miye haka"?
Nazeer ya yi murmushi yace kina jin dadi ki tawan tun lokacin da ki ka gama secondary school" bakida aiki yi sai danna waya, raheela ta tabe baki tace to miye matsalar ka da hakan"?
Nazeer yace babu, amma ina tausayawa wannan waya, raheela ta yi murmushi tace ni dai dan Allah bani phone dina, nazeer ya mika mata wayar yanemi daya daga ciki'n kujeri falon ya zauna yace ina kaka"?
Raheela tace tana daki, Nazeer yace ina zance mu ya kwana"?
Raheela ta murtuke fuska cikin tsiwa tace bansaniba ni fa banaso damuwa akan wane dalili za ka zabi kadinga takurawa rayuwata, da chan kasan kana sona miyasa ka aure bahijja"?
Kafita daga hanya ta ko na hadaka da kaka tana karasa zanceta ta mike fuuu..tashige dakin kaka tabar nazeer zaune dafe da kai, tana shiga daki'n tafada bisa gado kaka da ke zaune bisa "pray mat" tadago ta kalle raheela tace ke kuma me da wa"?
Raheela ta turo baki tace umhh..gani tayi shiru yasa kaka ta kyale ta.

*****ABUJA*****

Kasancewa yau juma'a Dr Amar yana saurin tashi daga "hospital" tun around 12:30pm ya nufi gida a falon yatarar'da matar gidan taci 'yar uban make up" ta yi matukar kyau tana gani shi, ta mike ciki'n shagwaba tafada bisa kirjin'shi shi kuma ya rungume ta yana shafar bayan'ta yace kinyi matukar kyau my wife"
Na'eema ta kada kwayar idon'ta tace thanks hubby" yana rike da hannu'ta suka haura "stairs zuwa bedroom dinshi, yashiga wanka yayida na'eema ta bude wardrobe" tafito masa da farar shada sai daukar ido takeyi, Amar da ke bathroom yana wanka ya ji gaba daya ya yi garin kaduna, don haka a gaugauce ya cucuda jikin shi ya karewa bathroom din kallo bai sami "towel" din zai daurewa ba, yaja dan karami'n tsoki yafito daga bathroom din haka nan, na'eema da ke tsaye tana goge masa black sandal din'shi tadago idanuta gani Amar yafito ba kaya a jiki shi yasa ta kyalkyale da dariya, Amar ya galla mata harara yadauki "towel" din da yayi amfani da shi, da safe da ke ajiye a gefen gado'nsa yayida na'eema ta tsagaita da dariya da takeyi tace hubby yaushe za ka daina wannan dabi'a ta ka tafitowa "narked" daga bathroom"?
Amar yaja tsoki mtwww..yace ba rana saboda Allah ya hadani da lazy wife" wance bataso aiki, na'eema tace to ae bani nake hanaka mayar'da towel" inda kadauke shi ba, Amar ya zura kayanshi yafesa turare "fragrance world" yajuya wurin na'eema yace ni zan tafi masallacin ki shirya da nadawo za mu wuce kaduna, na'eema ta zaro idanu tace lafiya me za mu je yi a kaduna"?
Weekend" za mu yi Amar yabata amsa kaitsaye.
Bata fuska tayi kamar za ta fashe da kuka tace haba hubby wannan wace irin bakatatan ba sanarwa gaskiya ni ban shirriyawa zuwa kaduna yanzu ba saboda gobe ne za'ayi birthday party" din Ramlat kuma kasan a gidanan za'ayi don haka za ka iya tafiya kai kadai, batare da Amar ya furta komai ba yajuya yafice daga daki'n.
Misali karfe 2:03pm Amar yadawo daga masallacin yahada komaitsa shi yadauki hanyar kaduna.

*****KADUNA******

Alhaji Muhammad

Please Login or Register in order to submit comment