Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuciya kawai mu je kayi "breakfast"
Ba yanda Amar ya iya dole ya hadiye 'yan kalman sa ya bi bayan ta wance tuni ta tsofa a dining area" ta ja masa kujera ya zauna sannan ta hada masa "tea ta kuma zuba masa chips" ta tura masa a gabanshi, duk da yana jin yunwa kasa sakewa ya yi ya ci abinci, yayida na'eema sai bishi da kallo ta keyi, gani ya mike yasa ita ma ta mike, ta mara masa baya a tsakiyar falon ya ja ya yi tsaye ya tattaro natsuwa da jarumta shi yace na'eema ni zan fita ko kina da bukatar wani abu ne"?
Ta girgiza kai gani taki yi masa, magana yasa karaso daf da ita yafisgo ta da karfi tafada kirjinshi yasoma rada mata kalamai masu dadi gaske sai ga na'eema ta watsake har da su kyalkyala da dariya yadago fuskarta yasake mata dafi "kiss a lips" yace sai nadawo my na'eema, saida ta wani lumshe idanu daga bisani ta bude su tace adawo lafiya yaya naa, ya juya yafice daga falon tabishi da kallon kauna.
Amar yana fita yanufi gida sakamako zuciya'rshi da ke azalzala shi da son gani raheela yadanna horn maigadi yabude masa gate yayi parking daga bisani yanufi "part din kaka...
[6:43PM, 5/26/2016] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN
'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~4⃣4⃣~

Da sallama yashiga falon saidai falon tsit yake ba kowa a ciki, kaitsaye yadoshi "bedroom" din kaka hannaye shi na zube ciki'n aljihu wando shi, ya murda handling" yashiga cikin daki hango ta ya yi kwance bisa gadon kaka tana rungume da pillow" tana sharar baccinta ciki'n kwanciyar hankali da gani yanayi ta batada matsala, a hankali yake tafiya har yakaraso kusa da ita ya tsura mata idanu, yayida zuciyar'shi ke bugawa da sauri-sauri tamkar za ta faso kirjinshi ta yi tsalle tafado kasa ya cigaba kallon kyakyawa fuskar'ta wance yakasa banbance tsakani tana bacci da tana falke wane tafi kyau yakara mayar'da gani shi, akan pillow da ta yiwa kyakyawar runguma a zuciya'rshi yace ina ma ace ni ne ki ka rungume raheela ba wannan dan banza pillow mai tauri tsiya, yakara yada gani shi akan "pink lips" din'ta wanda duk lokacin da ya kwanta bacci sai ya yi mafalki ya sumbace su nan take ya kudiri anniya sai yadan lasa su ko zai rage jin radadi da zogin da zuciya'rshi ta keyi masa akan wannan taurarowa da ta mayar da rayuwar shi tamkar ball a raga, batare da wani dogon tunani illah da hakan za ta jefa shi ba ya zauna kusa da kan'ta ya sunkuya dai-dai bakin'ta ya sumbace ta, raheela kan bacci'nta takeyi batasan waina da Amar yake toyawa a hankali yazare "pillow daga kirjin raheela saboda wani irin zazzafan kishi pillow yakama shi gani yakeyi pillow baidace da yasami mutsugunni a kirjin raheela ba, yariko hannuta ya tsurawa kunshi hannuta ido a hankali yake shafar zane kunshi da dan yatsa shi, a ciki bacci raheela ta ji ana mata tafiyar tsotsa a hannu'ta a firgice ta falka tana bude idanu taci karo da fuskar Amar yana zaune rike da hannu'ta da sauri ta fisge hannu nata ta tashi zaune tana zarar idanu, yayida Amar yacigaba da kallon'ta ciki'n sarkewa halshe tace dan Allah yaa Amar ka yi hankuri, dama ina da niyar baka wayar k.....saura kalman ta suka kargame a makoshi'nta sakamako dan yatsa shi da yadaura akan "lips din'ta yace shhhhh..tsawon dakika uku zuwa hudu su ka dauka suna kallon juna daga bisani Amar ya murtuke fuska yace ina waya ta"?
Gaba daya raheela tagama tsorata babban tashin hankali'nta bai wuce kaka tayi samako ta tafi gaisuwa rasuwa 'yar aminiyar ta da rasu ballatana ta kwace ta hannu Amar, yau na shiga uku abunda raheela tafada a baiyane, Amar ya yi murmushi, hade da cewa baki shiga uku ba da saura don sai kin nuna min inda aka rubuta "made in China" a phone dina.
raheela takara zaro dara-dara idanuta masu cike da tsoro ta kuma kwabe fuska kamar za ta fashe da kuka tace, Allah yaa Amar karya na ke yi banida qawar da take da irin phone dinka da sauri tadaga pillow tadauka waya ta mika masa, yagame wayar da hannu'ta yarike ya kalle dan yatsa ta da ke makale da zobe da yabata, yace ashe baby har yanzu zuciyata tana nan tare da ke"?
Raheela ta wangale hakora tace cab yaa Amar ae in har ka ga zobe nan yabar dan yatsana to bana numfashi, Amar ya zaro ido, raheela tacigaba da cewa tun ranar'da yaya hafsat ta gayamin diamon" ne nake tattali shi kamar tsoka daya a miya ta karasa magana tana dariya.
Amar ya dan murmusa, yace ke kan'ki "diamon ce baby dama kan'ki ki ka dinga yi min tattali ba wannan zobe ba, tabe baki ta yi hade da cewa 'hmm.
Amar yasaki hannu ta ya balle murfi wayar ya Zare sim card din shi ya rufe wayar ya mika mata yace ga wayar nan na barki miki ba don halin'ki ba in nadawo anjima zan kawo miki "SIM" cikin zumudi raheela ta karbe wayar tasoma zuba masa godiya, ya mike tsaye yace ina wannan masifafiya tsohuwa ne banji motsin ta ba tun lokacin da nashigo?
Raheela tayi murmushi hade da cewa tafita unguwa, Amar Ya tabe baki yace gaske dai naci kare na babu banbaka da tana nan da yanzu ta hanani rawar gaban hantsi, a wannan karo raheela batace da shi komai kawai tacigaba da jujuya wayar hannu'ta fuskar'ta na fitar'da annuri farin ciki gani ta shagala da kallon waya yasa yafice daga daki'n yanufi 'part din mamee.
*********************
Tabangare amarya na'eema kuma bata kara saka angonta a ido ba sai da yamma lis yadawo tana zaune falon taci kwalliya tana zuba ido ta ga inda angon nata zai bullo.
Amar ya yi sallama yashigo falon da sauri na'eema ta mike tanufi shi ta fada kirjin shi ya dan rungume ta yana shafar bayan ta yace my na'eema ya zama kadaci yaa yatafi yabarki koh"??
A shagwabe na'eema tace har da kuka na yi, Amar ya yi murmushi yace kinfiye shagwaba na'eema, miye kuma abun kuka sai kace na bata"?, takara narkewa bisa kirjin'shi tace to ba kai bane tun safe da kafita baka dawo ba sai yanzu, Amar yakara saki dan bazawari murmushi yace to sakeni na je nayi wanka lokacin sallah magarib yakaraso.
Ciki'n hanzari tasake shi tace mu je na hada maka ruwan wanka, tawuce gaba Amar ya mara mata baya kaitsaye ta wuce 'bathroom ta hada mishi ruwan wanka koda tafito tarar'da shi yatube daga shi, Sai boxers da sauri tarufe fuskarta ya tabe baki ya bi ta gefe ta yashige "bathroom na'eema ta bude fuskar'ta tafice daga daki'n zuciya ta cike tsantsan son Amar.
Amar yana fitowa daga wanka yanufi "dressing mirror yadauki body lotions ya shafe jikin shi yakara daukar "comb ya shace sumar kan'shi, jin anfara kiran sallah da sauri yanufi wardrobe yaciro blue jeans hade da body hook" brown colour ya feshe jikin shi da turare "pure blue" yafice daga dakin gani na'eema bata ciki'n falon kaitsaye yanufi bedroom din'ta karo na farko da shiga daki'n nata, tana zaune a gefe gado ta rafka dan uban tagumi ko tunani me ta ke yi ne oho" batare da damu da yanayi da take ciki ba yace na'eema na tafi masallaci ke ma kitashi kiyi sallah, ciki'n sanyi murya tace toh adawo lafiya, yadaga mata kai yafita daga daki'n.
Kaitsaye yanufi parking space ya ja motar'shi yafice daga gidan saida ya yi sallah magariba da esha'e sannan yanufi inda zai je a baki titi ya tsaya wani shago siyarda katin waya yasiyawa raheela sim ya kuma yi mata "register' kara yiwa motar'shi key ya halba kan titi yayida zuciya'rshi tafara yi masa sake-sake shin me ke shirin faruwa da ni"?ada zuciyata raheela take so kwantsan na waye gari cikin so da kauna na'eema, nake kuma jin inda har ban aure na'eema zan iya daina numfashi yanzu kuma na aure ta amma gaba daya zuciyata takarkata akan raheela, wani abin takaici' duk lokacin da nayi arba da fuskar'ta sai naji na tsane ta, wani bangare na zuciyar'shi yace amma kuma dazu ka yi namiji kokari ta hanyar danne kiyayya da ka ke yi mata wanda sanadi hakan ne yajanyo maka farin ciki maras misaltuwa musanman in ka tuna cewa yau ka sumbace tautausan labba raheela, sai kawai ya lumshe idanu shi ya Kuma bude su yakara dankarawa mota giya zuciya'rshi cike da buri'n kara son gani raheela......

Jeeddah Aliyu🌹🌹
[18/06 8:37 am] Jeeddah Aliyu🌹: [2:11PM, 5/28/2016] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN
'YAR UWA TAA🍆🍆

💕Love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~4⃣5⃣~

Tun kafin yayi parking ya hango raheela da nazeer tsaye a "compound" ko me nazeer yake fada mata take faman kyalkyale dariya nan take ya ji wani masifafe kishi ya turnuke shi, kasa fitowa ya yi daga ciki'n mota ya tsura musu na mujiya yana kallon su.
Nazeer ya katsiwa raheela dariya da takeyi ta hanyar cewa ga "big bros chan watakila godiya ya zo ya yiwa umma na 'yarta da mallaka masa ae kuwa raheela takara kyalkyalewa da dariya nazeer ya mike mata hannu su ka tafa, da sauri Amar ya rintsi idanu shi, sakamako wani kololo da ya tokare masa makoshi,
Ringing" din wayar nazeer ce ta katsi musu dariya da su ke yi, yafito da wayar daga aljihu rigar shi ya zaro ido yace tawan zan tafi gida amarya ta taso ganina, raheela ta tabe baki hade da cewa su amarya manya da bamusan asali ugulu ba da tace daga kasar masar tafito, nazeer ya yi murmushi yace duk wannan zaurance naki na fahimce inda ya dosa kina jin haushi bahijja ta yi miki "snatching" dina.
Mtwww..raheela taja dogon tsoki daga bisani tace ina kuda balle romonsa ae ni bahijja taimako na ta yi tarabani da jangwan dama kaka tace ba mudace da juna ba shiyasa kana furta bahijja ka ke so nima son'ka yafita daga zuciyata sai daga baya nagano cewa shakuwa ce a tsakani mu ba so ba takarasa zanceta tana dariya.
Nazee yabata fuska musanman da ya hango gaskiya abunda raheela tafada cikin kwayar ido ta ciki'n sanyi murya yace sai anjima raheela saboda nafara gajiya da wadanan munana kalaman naki, raheela tace saidai da safe domin na tabbata in har ka shiga gida bahijja ba za ta kara bari kafito shikenan yaya nazee ka zama mijin tace a fusace nazee ya kai mata duka ta goce bai same ta,
tabangare Amar kuwa ji yake yi kamar ya balle murfi Mota ya fito yahade nazeer da raheela ya yi musu shegen duka, nazee ya kalli raheela da ke nesa da shi tana masa dariya ya galla mata harara yajuya yanufi "parking space" Amar yana gani nazee yadoso inda yake sai yakara murtuke fuska kamar tsoho soja sai faman hura hanci yakeyi, Nazee yakaraso ya leka ciki'n motar yace akayi ne bross"?
Sai da Amar yagama shan kamshi sa, a dakile yace ina son gani wance yarinyar ne yanuna raheela da baki, nazee ya yi murmushi hade da cewa okey bara na kira maka ita batare da yajira jin ta bakin Amar ba, ya daga murya Da karfi ya kwadawa raheela kira wance sauri kiris tashige part din kaka kee! raheela ki zo yaa Amar yana kiranki raheela ta tsaya chak daga bisani ta nufi parking space" Nazee yace bross ni zan ware da kyar Amar ya iya bude baki yace ka gaida gida domin jin yakeyi kamar ya shako kwalar rigar, Nazee yace banaso nakara gani ka tare da raheela domin tawa ce ni kadai sai dai kash ba zai iya ba Nazee yace gida zai ji yajuya yashige motar'shi yafice daga gidan.
hakan ne yaba Amar damar kifa kan'shi bisa sitari yasoma tunani wannan masifar da yake yunkuri afkawa ciki domin ko a gari shegu bai taba gani an hada ya da kanwa ba, wannan shi ake kira gaba kura baya siyaki, raheela takaraso tadafa murfi mota tace ina wuni yaa Amar"
Firgigit ya yi yadago sexy eye's din'shi ya kalle ta kawar'da fuska cikin sanyayar muryar shi yace lafiya qalau"
Ina phone din naki nasaka miki sim"?
Cikin zumudi hade da rawar jiki raheela ta tura hannu'ta ciki zani ta tafito da wayar ta miqawa Amar''
Zaro idanu ya yi yace kee har yanzu baki daina wannan shashanci naki na boye abun ciki'n "pant wai yaushe za Ki yi hankali raheela"?
Raheela tarufe fuskarta da tafuka hannaye ta ciki'n tsanani jin kunya, tace kai yaa Amar dan Allah kidinga tauna magana kafin kafade ta.
Amar ya yatsine fuska yace naki na tauna din ae hali'n ki ne nafada ba zan iya tunani adadi yaran da ki ka yiwa kwace kina boye, cikin pants" dinki.
Raheela tayi narai-narai da idanu kamar za ta fashe da kuka tace abunda yawuce yaa Amar kadaina tadashi wannan abun da ka ke fada tun na yarinta ne kuma ae cikin zani na ne nasakade wayar.
Ya mika mata waya yace ni dai karbi wayarki banaso dogon surutu kuma ina gargadi ki da karki sake ki bawa kowane gardi number ki duk ranar'da nayi checking" din contact naki naga number gardi sai nafasa waya'r nan na kuma kar'ya miki hannu.
Cikin sanyi jiki raheela ta mika hannu ta karbi wayar tace na gode yaa Amar Allah yasaka da alkhairi"
Amar yace bana bukatar godiyar ki kawai ki kiyaye umarni da na baki.
Raheela taro baki hade da cewa ni me zai hadani da number gardi"?
Harara ya galla mata yace dan banza rawa kan'ki ne zai hadaki da number" in kuma hakan tafaru kinsan abinda zai biyo baya, har raheela ta bude baki za tayi magana yadaga mata hannu hade da cewa oya shiga gida banaso surutu, har raheela tajuya ta yi tako biyu zuwa uku taja tayi tsaye ta mayar'da ganinta waje Amar tace yaa Amar baka saka min number ka ba"?
Amar ya yi dan bazawari murmushi yace zan kira ki sai ki yi serving tace toh..na gode ka gaida yaya na'eema ta juya tashige bangare kaka.
Amar yaja mota yanufi gidan'shi zuciya'rshi cike da dinbi tunani yakamata nadaina yaudara kaina nagano cewa raheela ta yi min nisa, ba zan taba samunta ba, dole na hankura da ke raheela don haka mafi alkhairi a tare da ni in tattara komaitsa na koma abuja watakila in na nisance ki zuciyata ta rungume kaddara, da wannan tunani ya esa gidan'shi.
A falon yatarar'da ita tasha ado ciki'n wasu hadadu sleeping dress" riga da wando fuskar'ta shinfide da damuwa, tana gani yashigo tasauke ajiyar zuciya tace sannu da zuwa"
Yauwa" iya abunda yafada kenan yanufi bedroom dinshi da sauri na'eema ta mara masa baya kaitsaye yanufi toilet ya yi wanka yana fitowa ya ci karo da ita zaune a gefen gado, yabude wardrobe yaciro pajamas yasaka yafashe jikin shi da turare "suphoria men" ya haye gado ya yi kwanciya shi na'eema tace yaa Amar ba ka ci abinci ba kuma naga ka kwanta,
Amar yace na koshi na'eema in kina ji bacci ki zo ki kwanta, ba yanda na'eema ta iya dole ta raba gefen shi ta kwanta, kowane su ya yi shiru yana tunani daga bisani na'eema ta yi namiji kokari, ta rungumo bayan Amar tasoma shaqar Qamshi shi, cikin zafin rai da daga murya sai kace commander" sojoji Amar yace stop it's na'eema I don't want's any disturb right now so leave me alone"
A tsorace na'eema take kallon shi hawaye na kwarara akan fuskar'ta cikin shashekar kuka da ke baiyanar da bakin ciki da takaici tace nashiga uku ni na'eema wannan wane irin tasko ne nake gani, tsakani jiya da yau naga wulakanci maras adadi daga gareka yaa Amar, kuma nasan kana wulakanta ni ne duk saboda raheela to kasani yaa Amar, yanda Annabi ya haramta da wuta haka kaima ka haramta da raheela, kuma na kudurci aniya sai na ja dogon layi mai tsayin gaske tsakaninka da raheela koda hakan zai kasance bugun numfashi na a duniya tana karasa zanceta tafice da gudu Daga daki'n.
Amar yaja tsoki yace kan'ki akeji mahaukaciya banza jarababiya haka kawai za ta hanani bacci ya gyara pillow ya yi kwanciyar shi.

**********************

WASHE GARI****
Da misali karfe 8:30am Amar yafito daga dakin'shi yasha kwalliya cikin wata dakakiya shadda galila dark blue colour" wance tafito da sahirtace kyaun shi sumar kan'shi tasha gyara tayi luf-luf da ita sai kyalli ta ke yi ga wani uban Qamshi da yake zubawa, yafito ango sak amma kuma ango da bai da moriya cikin tako sa na kasaita yanufi falo yayida na'eema da ke zaune tadago ta kalli shi take tsananin soshi yakara mamaye zuciyar'ta batasan lokacin da tace ina kwana yaya"?
Kallon kasan ido yayi mata wanda hakan yakara jefa ta ciki'n wani yanayi yace lafiya qalau ki je ki hada kayanki za mu tafi abuja yanzu nan.
Na'eema ta zaro ido tace lafiya kuwa yaa Amar"?
Kinga malama in kina da ra'ayi zuwa ki je ki hado kayan'ki da sauri na'eema ta mike tanufi ciki'n dakin'ta.....
[9:37PM, 5/28/2016] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN
'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~4⃣6⃣~

Ko da tafito yafice daga falon hakan ya tabbatar
Mata da yafita dole ta rufe kofufi gidan, daga bisani ta ja katuwar "trolley" dinta ta nufi compound din gidan a parking space" ta tsinkaye shi tsaye takarasa waje shi, ya karbi "trolley ya jefa a seat din baya yajuya ya zauna a "driver seat" yayida na'eema kuma take zaune a gefen shi, ya yi addu'a ya ja mota ya tsaya bakin "gate ya yi sallama da maigadi sannan yakarasa ficewa daga gidan.
*********************
Raheela ta fito daga daki hannu'ta rike da jakkar littafai ta na islamiyya tashigo falo ta kalli kaka da ke zaune da casbaha hannu tace kaka zan tafi isalamiyya.
kaka tadago ta kalle ta, tace "oh Allah gagara misali wai raheela yaushe za ki natsu ne"?
Raheela ta turo baki Ciki'n shagwaba tace me nayi"?
Kaka tace ba kiyi karin kumallo ba kin dauke duniya bisa tsinke kina tsotsa ni narasa munafuki da yasiya miki kattan na duniya bisa tsinke nan baki da aiki sai na tsotsi-tsotsi duk inda ki ka ga dama sai ki jefar min da tsinke, ke ko tsoro bakyaji kada basir yakama ki ga kuma wannan munafuka waya da wannan gantalale yaro yabaki nace ki mayar masa da tsiyar sa amma ki kayi kunne uwar shegu da ni.
Har kaka ta dasa aya a zanceta raheela tana Kallon ta, daga bisani tafara magana kamar za tayi kuka haba! Kaka wannan fada duk akan waya ne"? To ni dai gaskiya Saidai ki yi hankuri ina son waya ta takarasa magana tana murguda baki.
Kaka tace shikenan tun ke ba'a fada miki ki ji ae sai ki tayi, indai Amar ne ina nan zan ji labari ta matsi muku.
Raheela tayi murmushi tace kaka kenan mugun fata da ki keyi mana kenan"? To insha Allah ba za ta matsi mana ba.
Umhh...Allah yasa domin Amar shu'umi ne na karshe, ko uwar da ta haife shi bata gane inda yadosa ballatana ke karan kada miya.
Oh! Ni raheela kaka ba dai korafi da sa eye's ba na fahimci tun daga ranar'da yaa Amar ya yi miki PDP ki daura mishi karan tsana takarasa zanceta tana dariya.
Ae kuwa kaka takara harzuka tace ya dai yiwa kan'shi PDP domin na tabbata indai rai da rabo wata rana za ta bare mishi da kan'shi, zai nemi ni.
Toh...ae shikenan sai ki jira in zo sai kifada masa ni miye nawa a ciki"?
Akwai domin ke ce mai kunne qashi da ki ke kula shi, raheela ta zaro ido hade da cewa cab yau tsohuwa nan masifa safe ta keji sai ki jira mai tsautsayi da zai fado falonki, sai ki wanke masa allo shi son ranki, ni kan kinga tafiya ta, tajuya tafice daga falon cikin daga murya kaka tace ki tabbata kin cire tsinke nan daga bakin ki kafin kifita gidanan.
Raheela tace kullum haka ki ke fada, sai kace an gaya miki da shi nake fita.
Kaitsaye part din iyayye ta ta nufa, a dining area tarar'da su zaune bisa dining table" ta runsuna ta gaida abban taa tajuya ta gaida aunty amarya, yayida ko kallo umma hajara bata esheta ba, ta nufi kujera da alhaji Abdullah yake zaune, aunty amarya tadaka mata tsawa cikin bacin rai tace, kan'ki daya kuwa raheela baki ga hajara bane da ba za ki gaida ta"?
Raheela ta turo baki kamar za tayi kuka tajuya waje umma tace yakike"?
A harzuke umma hajara tace ni za ki kalla raheela ki ce da ni ya nake don tsabar rashin tarbiya, su iyayye ki ae ba haka ki ka gaida su ko don ni kin rena ni.
Aunty amarya ta gallawa raheela harara tace ki gaida ta ko na kwada miki mari gani yanda aunty amarya ta zaburo mata yasa ta boye bayan Abba, yayida abba abinci shi kawai yake ci tamkar bai ga abunda yake faruwa ba, hannu shi yasa yajanyo raheela yace zauna kiyi breakfast mama naa, raheela ta bata fuska tace sai nadawo daga islamiyya zan ci Abba.
Aunty amarya tace amma alhaji yakamata kadinga tsawatawa maama akan irin wannan rashin kunya da takeyi.
Alhaji Abdullah ya ajiye fork din da ke hannu shi yace duk abunda maama ta ke yiwa hajara bana gani laifi ta saboda hajara ce tafara nuna mata baiyananiya kiyayya sai kace da ita ta ke kishi a yanda na fahimce hajara kiyayya da take nunawa maama,
ko ke da ki ke matsayin na kishiya ta bata nuna miki irin ta me maama ta tare mata ne"?
Umma hajara tace raheela bata esa ta tare mini komai a gidanan, ita da babu duk daya suke a wuri'na takarsa zanceta tana huci.
alhaji Abdullah ya yi murmushi ya kalle raheela cikin kulawa yace tashi ki tafi isalamiyya mama na kada kiyi latti hasada ga mai rabo taki, raheela ta mike tsaye taciro waya daga aljihu wando uniform din'ta ta mikewa abba tace abba kalli waya na da yaa Amar yabani, saura kiris umma hajara ta hadiye fork din hannu'ta ta zaro turu-turu idanuta da suka baiyanar da tsanani tashin hankali da ta afka ciki kamar daga sama ta ji murya abba yana cewa iyee lallai yaa Amar ya burge ki mama irin wannan waya mai tsada haka cikin zumudi raheela tace abba ya sunanta ne"?abba yace iPhone6 ce raheela ta daka tsalle ciki'n jin dadi tace abba nima na karo wulakanci kenan"?
Abba ya yi dariya yace sosai ma kuwa, raheela tace abba ka yi "checking din account balance dina abba ya yi yanda raheela ta umurce shi yakara sakin dariya hade da cewa "ten thousand" nagani"
raheela takara wangale baki tace yaa Amar ne yasaka min abba kayi min serving number ka, abba yana murmushi ya yi mata serving din number ya kuma mika mata wayar.
Tun lokacin da raheela ta anbace sunan Amar umma hajara tashiga tashin hankali maras misaltuwa a yanda boka duguzuu yace da su da zarar asiri yakama Amar zai tsani raheela hatta kashi sai yafita daraja da kima a waje shi, amma kuma gashi raheela ta zo da wani sabon bidi'a wai Amar yabata waya lallai ya zame mini dole na koma waje boka duguzuu, murya raheela ce ta katsi mata tunani, da takeyi abba na tafi, yayida umma hajara ta bi raheela da mugun kallo, kamar wance aka cewa tajuyo raheela tajuya, karaf idanu ta su ka hango mata kallon tsana da umma take mata, raheela ta yi murmushi hade da yi mata gwalo, domin duk duniya ba abunda umma hajara ta tsana irin raheela ta yi mata gwalo abun yana kona mata rai da za ta sami sarari, da ba abunda zai hanata gutsirewa raheela halshe.
Fitowar raheela daga ciki'n gida yayi dai-dai da parking din motar Amar tun daga nesa ya hango ta numfashi'n sa yafara kai da kawo, na'eema kuma ta murtuke fuska tamkar wance ta hango wani bala'e yana tunkaro

Please Login or Register in order to submit comment