Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata taimakon gaggawa abinka da masu citta a hannu sun juma suna gudanar da aikinsu a kanta sannan Dr. Mujaheed ɗin ya fito daga ɗakin wata matashiyar nurs na biye dashi a baya.

Direct inda matashin ke zaune tareda Gurds ɗinsa Dr. Mujaheed ya nufa sannan ya kalleshi yace "muje office ba musu ya miƙe yabi bayansa seda duka ɗanyi tafi kaɗan sannan suka isa office ɗin me shegen kyau sannan suka zauna, cikeda damuwa matashin yace "ya jikin nata Dr.? Murmushi Dr. Mujaheed yayi yace "ka kwantar da hankalinka Edriss insha Allah komai zeyi daidai, ka godewa Allah ma kun kawota akan lokaci. Murmushin jin daɗi Edriss Adam yayi tareda faɗin "Alhamdulillah Dr. Wllh har hankalina ya kwanta.

Magungunan da suke buƙata ya rubuta masa tareda cewa "a halin yanzu tana buƙatar jini domin kuwa ta rasa jini dayawa, mun binkita mun gani launin jininta me wuyar samu ne kuma ya kamata a ƙara mata shi da gaggawa idan ba haka ba gaskiya something can happen to her. Da sauri Edriss yace " no Dr. You can take my own because nau'in jini na ze iya yiwa kowa

Ƙura masa manyan idanunsa Dr. Mujaheed yayi a zuciyarsa yana mamakin yanda Edriss ya damu da wannan baiwar Allah, ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "who is she to you Edriss?

Murmushin rainin hankali Edriss yayi yace "ba wannan ba tukun muje ka ɗau jini na. Ya faɗi hakan yana kallon tsakiyar ƙwayar idon Mujaheed ɗin

Basarwa yayi ya miƙe yace "bani zan ɗau jininka ba Edriss yanzu dai zan turaka inda za'a ɗauka ɗin, cikin mintunan da bazasu gaza 10 ba akayi komai aka gama se'a lokacin hankalin Edriss ya kwanta sannan ya wuce gida donya samu ya huta.


INDIA🇮🇳

dakewa Ummie tayi tana binsa da kallo tamkar wadda aka dasata a gurin, gaba ɗaya ji take komai ya tsaya mata chak har motar Asibitin ta ƙaraso ƙofar gidan still tana tsaye kan ƙafafunta, Maryam ce ta fita da hanzari tayo musu jagora zuwa cikin gidan inda muzaffar ɗin ke kwance samɓal babu alamar numfashi a taredashi, kin kimarsa sukayi suka ɗorashi bisa wani siriri gado sannan suka fito dashi Zuwa cikin motar, basu jira fitowar wani daga cikin gidan ba sukaja motar sabida ganin irin condition ɗin mara lfyn se bayan sun fita Hajiya Aisha ta zube bisa doguwar kujerar dake falon tana maida numfashi

wayar muzaffar dake kusa da System ɗin Ummie ce ta fara ƙara kasa ɗagawa ummie tayi hakanne yasa maryam ta isa ga wayar jikinta na wani irin rawa ta Amsa ba tareda ta duba sunan me kiran ba, cikin yanayi na rashin kwanciyar hankali mom tace "boy are you Ok?

Wani irin fashewa Maryam tayi da kuka nan ta shiga zaiyanawa Mom halinda muzaffar ɗin ke ciki. Wani irin Zabura mom tayi ta miƙe zaune daga kwancen da take cikin yanayi na fitar haiyaci tace "ɗan nawa ne yafi guba ??????

Abie wanda ke kwance ne ya miƙe idansa nakan Mom wadda jikinta ke wani irin rawa sabida tsabar tashin hankali, fashewa tayi da kuka tana danne ƙirjinta dake mata wani irin suya ta kalli Abie bakinta na rawa tace "kagani ko? Senayi magana sekace kishi ne ke ƙoƙarin hanani zaman Lfy da Aisha to gashi nan yau ta zubawa ɗana guba a abinci kuma ya........... Girgizata yayi da wani irin Sauri sabida ganin idanunta na ƙoƙarin rufewa take mom ta dawo daidai cikin haiyacinta tareda faɗawa jikin Abie ta saki wani irin kuka me taɓa zuciyar duk wata uwa datasan ma'anar haihuwa. A daran ranar Abie yayi hayar privet jet zuwa ƙasar India aiko kiran sallar farko suka himmata sukabar ƙasar.


India 🇮🇳

Hajiya Aisha da ƙyar ta iya miƙewa ta koma ɗakinta tareda zubewa a bakin gadonta zuciyarta duk a cushe, gabadaya komai ya tsaya mata tayanda takejin cewar dama hakan bata faru ba do take tayi kuka amma kuma ta kasa yin hakan, dama idan wani bala'in ya sameka hawayen ma ɗaukewa yake gabaɗaya a haka har gari ya fara haske still tana zaune batareda ta rintsa ba.

cikin ikon Allah jirginsu Abie ya sauka lfy cikin mintuna kaɗan motocin company sukazo ɗaukarsu Kasan cewar basu san Asibitin da aka kwantar da Muzaffar ɗin ba dole yasa suka ɗauki hanyar gidan Hajiya Aisha, gabaɗaya mom ta birkice tamkar wata zararriya idanunta duk sunbi sun koɗe sabida kukan data gurza, a haka motocin suka tsaya a bakin ƙofar gidan cikin jerin gwano.

kokaɗan basu jira an buɗe musu ƙofar motar ba kamar yanda suka saba mom ta ɓalle murfin motar ta diro tana huci, da wani irin sauri ta shiga gidan tana kwaɗawa Ummie kira a birkice, sautin muryarta ne yasa Hajiya Aisha tasha jinin jikinta kuma ta fito daga ɗaki jikinta a saluɓe tamkar kazar da ƙwai ya fashe ma

tana fitowa idonsu ya sarƙe cikin na juna a karon farko tun bayan shekara 35, wani irin wawan Mari mom ta ɗauke Ummie dashi har seda taga taurari tun kafin ta watsetsake ta ƙara ɗauketa da wani marin, cikin kiɗima Ummie tace "ni kika mara Saratu?

cikin fusata Mom tace "na mareki Kiyi duk abinda zakiyi, Se yau na sake tabbatar da cewar ki cikakkiyar shaiɗaniya ce Aisha kuma wllh ki kwana da sanin cewar sena hukuntaki a bisa laifinki na bawa ɗana guba wllh koda kuwa abinda na mallaka ze ƙare akan shariya dake!!!!

Abie dake tsaye yana kallonsu ji yayi duk Hajiya Aisha ta sure masa a rai a sanadin abinda ta aikatawa gudan jininsa namiji tilo tabbas baze ƙyaleta ba a wannan karon dole ne shari'a tayi aiki akanta, ya juya yana kallon jami'an tsaron dake bayansa yace "ku tafi da ita!!!

Wani irin zazzafan hawaye ne ya zubo mata daga idanunta ba tareda tayi magana ba jami'an suka tusata Station abisa yunqurinta na kisan kai..............


Har suka fita da ita bata dena kallon Abie ba lokaci guda kuma ta fashe da wani irin kuka wanda ita kaɗai tasan ma'anar abinta.





Thanks 4d love fans❤️


comment
nd
share

Sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


*_Page :24_*


*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Banyi Editing ba🙅‍♀️

_____✍️Har suka fita kuka takeyi sosai jikin Abie ya sanyi dajin sautin kukanta seda dukda hakan bayajin cewar ze iya ƙyaleta bisa yunƙurinta na kashe masa ɗa.

Tsaki Mom taja tana shirin magana sega maryam ta fito, ƙura mata iɗanu mom tayi a ranta tana tunanin inda tasan wannan fuskar Katse mata tunani maryam tayi ta hanyar cewa "Sannunku da zuwa Ranki ya daɗe nice wadda mukai magana dake ta waya ta faɗi hakan tana matse ƙwallar data zubo mata da gefan zanin Atamfar dake jikinta. Ajiyar zuciya mom itama hawaye na zubo mata tace "wani Asbiti aka kaimin ɗana ?

"Ghandy Special Hospital ne dake Ƙarshen Layin nan naryam ta faɗin hakan. Cikeda Masifa mom tace "taya za'ai kukaishi ƙaramin Asibiti a madadin kukaishi na Compay? Wll......" kinga Saratu pls ki nutsu ki dawo cikin haiyacin ki insha Allah komai zeyi daidai, Nasan Asbitin farin sani kuma sunada kayan aiki sosai karki manta nan ba Nigeria bace suna bawa Asbitocinsu dukkan abinda ya dace wanda za'a kula da marasa lfy dasu cikin ƙwarewa.

Kuka ta fashe masa dashi har suka fita daga gidan zuwa Asibiti bata dena kukan ba, a nitse Driver ɗin dake tuƙasu ya faka motar a harabar Asibitin inda aka tanada sabida hakan, Dukda cewar Asbitin ƙarami ne amma yana da kyau gamida tsari fiyeda zaton me karatu kusan gabaɗaya hankalin mom baya jikinta burinta kawai taga halinda ɗanta yake ciki.

A haka suka isa reception na Asbitin A nitse Abie ga ƙarasa gurin da wasu nurses ke zaune da alama sune cashier's na Asbitin, tambayarsu yayi inda aka kwantar da mara lfyan cikin harshen turanci matashiyar yarinyar tace "faɗi sunan mara lfyn sena duba maka. Cikin mintuna kaɗan ya gaya mata sunan take ta binciko musu ɗakin da mara lfyn yake suka nufin ɗakin

A bakin ƙofar ɗakin suka tsaya sabida hanasu shiga da akayi seta ƙofar glass ɗin dake jikin ɗakin suke hangensa, kwance yake kan gadon Asbitin an saka masa uniform me launin kalar brown, fuskarsa ɗauke taƙe da oxygen inda bakinsa kuma akai warring wani dogon five wanda ya taho tundaga cikinsa sabida poison ɗin dayaci, babu abinda ke motsi a jikinsa se iskar numfashin dake fita ta cikin na'urar oxygen ɗin da aka saka masa. Se'a lokacin idanun Abie suka sauka akan Rubutun da akai bisa jikin ƙofar glass ɗin dake jikin ɗakin kamar haka (ICU) intensive care unit. Ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfin gaske a ransa yace "lallai ɗansa yana cikin tsaka me wuya tunda har aka kawoshi cikin wannan ɗakin to abin bana wasa bane. Wani iri yakeji a zuciyarsa gameda wannan gagarumin cin Amanar da Hajiya Aisha tayi masa, meyasa zata aikatawa ɗan daya haifa irin wannan zalincin?

Kuka sosai mom take hakanne yasa Abie ya jawota jikinsa yana bubbuga bayanta, wata irin tsanar Ummie ce take ƙara ratsa duk wani lungu da saƙo na zuciyarta tareda ƙudurtawa kanta cewar wllh koda abinda ta mallaka ze ƙare setayi shariya da Hajiya Aisha tayanda nan gaba koda ɗan dabba bazata sake yunƙurin kashewa ba ballan tana ɗan mutum.

*******

ƁANGAREN HAJIYA AISHA kuwa station suka hurgata suka kulle gabaɗaya komai ya tsaya mata cak ta rasa abinda ke mata daɗi a cikin wannan duniyar, bata taɓa zaton haka daga gurin Abie ba tayi zaton cewar ɗabi'arta data ɗaɗe tana nuwa masa bazata barshi ya amince da wannan al'amarin daya faru da ita cikin sauƙi ba amma kuma se gashi shida kansa yasa ƴan sandan wata ƙasa suka kamata har cikin gidanta suka fito da ita suka kawota wannan gurin mara tsabta. Tabbas tayi data sani a rayuwarta na sanin Abie da zuriyarsa tun farko, da ace bata sanshi ba da duk hakan bata faruwa.

wani irin kukan baƙin ciki ne ya taso mata tareda data sanin Abinda ta aikata a Rayuwar ta, babban tashin hankalinta a yanzu shine taya zata iya sanar da iyayenta da ƴan uwanta halin datake ciki??????

A haka Rayuwa ta dinga tafiyar mata cikin yanayi na rashin jin daɗin Rayuwa gamida walwala.

NIGERIA 🇳🇬

Edriss ne zaune tareda mom ɗinsa cikin danƙareren falonsu na alfarma wanda ko gidan shigaban ƙasa se haka, da damuwa kwance akan Handsome face ɗinsa yace "mom nifa hankalina sam ba'a kwance yake ba wllh inaji a jikina cewar dama banje Taraban nan ba sam wllh. Ya faɗa kamar zeyi kuka

Da kulawa matar daya kira da mom ta ɗago fararen idanunta ta kalleshi tace "why are you saying that sweetie? "mom wata yarinya muka bige a hanyar dawowan mu daga Taraba. Edriss ya faɗi hakan yana kallon tsakiyar idanun mahaifiyar tasa. Be damu da irin kallon datake binsa dashi ba yaci gaba da cewa" haka kawai naji a raina ina tausayin yarinyar mom becouse ƙarama ce sosai kuma wllh mom she's pretty.

Sosai mom Edriss ta kaɗu dajin baya nan ɗan nata da ƙyar ta iya cewa " yanzu Edriss a wannan uban dajin ta ina gida ze kasance balle har a samu yarinya har ku bige da mota?

a dake ya kalleta yace "no mom ba yarinya bace kamar kowa she's Fulani girl......

Cikeda kaduwa Mom Edriss ta kalleshi tsoro ƙarara akan fuskarta tace "Fulani girl? Ta faɗa cikin karaji.........




comment
Nd
Share




Sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


Page :25


*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

*_All Characters, place, organizations and incident of this Interesting Novel are fictitious😁, so pls my dearest sisters abinda yake me kyau a ciki to dashi zamuyi koyi bada akasin hakan ba, Allah ya bamu ikon aiki da darasin dake ciki don isar mazon Allah✊_*


___✍️ Murmushi yayi har seda fararen haƙoransa suka baiyana sannan yace "mom why are you looking so surprised?

Ajiyar zuciya mom Edriss ta saki sannan tace "no like that sweetie I'm just feel like there's definitely something behind the Fulani's girl ɗin ne thats why I look so shocked. Dariya Edriss yayi yace "pls mom ki manta da wannan maganar babu komai a tareda ita se alkhairi insha Allah wllh mom tausayin yarinyar nakeji because she's to young like Sis Zeeyadah. Ya faɗa kamar ze sakin mata kuka

Shiru Mom Edriss tayi tareda maida hankalinta ga makekiyar Tvn bangon dake manne a cikin falon, miƙewa Edriss yayi tareda faɗin pls mom ki shirya zuwa 4pm insha Allah semuje Hospital ɗin ki ganta. Ya faɗa yana kallon ƙofar falon sabida motsin dayaji a gurin

Hajar ce ta shigo cikin Shigar doguwar rigar material Baƙi wuluk wadda tai bala'in bin jikinta, sosai kayan sukai bala'in karɓar jikinta kasancewarta farar fata sedai a ɓangare na Addini sam shigar datayi bata dace da koyarwan Addinin mususulci ba, taɓe baki Edriss yayi yana kallonta yace "hey meye haka kekuma kamar wata ƴar babyn Roba?

Hararanshi tayi tareda zama a kusa da mom kamar zara shige jikinta tace "uhm ai dama kai ya Ediyan ɗinan komai sekayi magana baka gani kayi shiru. Ta faɗa tana ƙunƙuni a ranta kuma tace "baƙauye kawai. Wani shegen kallo ya watsa mata lokaci guda kuma ya saki muskilin murmushi yace "look at you don Allah tayama za'ai Zafsy ya soki (muzaffar)? Wllh mom yarinyar nan babu namijin daze sota a haka jibeta fa sekace ɗiyar mutannan gabashin Ameerica. "gaya mata dai ya Edyan kullum gani take kamar tafi kowa wayewa sabida Dady ya kaita ƙasar England tayi karatu. Zeyadah dake sakkowa daga saman sters ta faɗi hakan tana dariya, Zeeyadah ƙanwa ce ga Edriss uwa ɗaya Uba ɗaya kamar yanda hajar ma ta kasance ƙanwa a gareshi, Edriss shine babba sannan Hajar se kuma Zeeyadah wadda ta kasance Auta, mahaifinsu Alhaji Adamu babban ɗan sanda ne wanda a yanzu yake taka matsayin IG a nan ƙasarmu ta Nigeria, a kwai shaƙuwa sosai a Tsakanin Edriss da Sisters ɗinsa Hajar da kuma zeeyadah sedai shaƙuwar dake tsakanin Zeeyadah da Edriss ya shallake duk yanda me karatu ke zato da kuma tsammani, shiyasa take kiransa da Ediyan a madadin Edriss. Hakan ya samo Asaline da ƙuruciyar Zeeyadah wannan shine mafarin komai.

Itadai Mom Edriss jinsu kawai takeyi amma hankalinta naga wannan yarinyar da ɗanta ya kira da fulani girl. Haka kawai takejin zuciyarta na rawa gabaɗaya ta rasa makama babbaɓ burinta shine tayi ido huɗu da wannan yarinyar kota samu nutsuwar zuciya.


*****

India 🇮🇳

Bayan Abie sunbar Asbitin da muzaffar ɗin ke kwance basu dire ko ina ba se magarƙamar da aka sanƙame Ummie a ciki, nan take bada ɓata lokaci ba ya nemi da a tura case ɗin babban ofishin jakadancin Nigeria dake ƙasar indian kasancewarsu ba ƴan ƙasa ba. Be wani sha wahala ba suka amince da hakan tareda tura case ɗin can kamar yanda Abie ya buƙata

Muhammad Kareem Ahmad shine wanda case ɗin Ummie bisa yunƙurin kisan muzaffar ya faɗo hannunsa, gyara zaman farin glashin dake manne a idanunsa yayi tareda gyara zamansa bisa hamshaƙiyar lallausar kujerar dake cikin katafaren office ɗin sannan ya dubi Abie yace" ina evidance ɗin da Asibiti suka baku wanda ya tabbatar da cewa Guba yaron yaci?

Miƙa hannu Abie yayi ya karɓi takardun dake hannun Mom wadda tunda sukabar Asbitin take kuka ya mikawa Muhammad kareem Ahmad su, ƙurawa takardun idanu yayi yanabin komai daki-daki cikeda sanin kan aikinsa kimanin wani lokaci me tsayi sannan ya dubi Abie cikin ido yace

"haƙiƙa wannan al'amarin zan iya cewa a kwai tarin sarƙaƙiya a cikinsa wanda idan bamu maida hankali ba zamu iya zartar da hukunci ba'a muhallin daya dace ba Alhaji Abdulwahab, dole ne mu zarfafa buncike har mu gano gaskiyar lamarin nan, a sakamakon da likitocin Asibitin da yaron yake kwance suka bayar ya nuna cewar gubar bata daɗe a cikin jikinsa ba ta fita sannan kuma iskar daya shaƙa kafin yaci abincin ita kanta a gurɓace take don haka dole ne mu ƙara samun cikakken bayani akan wannan case ɗin na Hajiya Aisha.

A wannan takin ita kaɗaice zata iya fitar damu daga shakku. Ya faɗi hakan yana kallon wani matashin saurayi yace "kace musu su shigo da me laifin nan zata amsa min wasu tambayoyi dazanyi mata. Juyawa matashin yayi a hanzarce ya fice cikin ƴan mintunan da bazasu gaza 2ba aka shigo da hajiya Aisha hannunta ɗaure cikin ankwa idanunta duk sun jeme sabida kuka, kallo ɗaya zakayi mata ka fahimci cewar bata cikin nutsuwarta ko kaɗan...

wani irin kallon tsana mom take binta dashi har Ummie n ta zauna a kujerar da aka nuna mata, tunda ta shiga bata ɗaga kanta ba don batasan da idon da zata kalli Abie ba

Kallon tsaf Muhammad kareem Ahmad yakebin Ummie dashi cikeda son tabbatar da abinda yake tunani a kanta dannan yace "Hajiya Aisha shin zaki ya baiyana mana abinda ya faru a wannan ranar da kika ciyarda ɗan mijinki guba a cikin abinci?

cikeda dakewar zuciya tace "Ae zan iya tunawa ranka ya daɗe, a wannan ranar da kaina na dafa abincin dazan saukeshi dashi bayan na kammala dafawa na jera a kan daining ina jiran isowarsa na buɗe kular Abincin danasan yafi so na zuba masa guba a ciki tayanda zeci ya mut....... Wani irin Kuka ne ya taso mata dole yasa tayi shiru da maganar ta shiga rusar kuka. Wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ne ya tasowa Abie a lokacin dayake kallonta cike da tsana yace "Muhammad don Allah Zan roƙeka alfarma a karona farko ina roƙonka don girman Allah ka tura case ɗinnan gida Nigeria ta yanda za'a hukunta wannan baiwar Allah butulu da tushe.

shiru Muhammad yayi bakajin sautin komai sena kukan Mom, cikin muryar kuka mom tace don Allah ka taimaka mana Ranka ya daɗe plssssss. Mom taja plss ɗin kamar zata shiɗe

Kamar bazece komai ba ya kalli Abie yace "naji duk batunku sedai bazamu amince ba harse munga yanayin jikin yaron, bazeyu ku tafi ba harse ranar da yaron ya dawo cikin haiyacinsa ta hakane kawai zamu iya tura ƙararku zuwa gida Nigeria Inyaso sesuku shiga kotu........

Godiya mom ta dingayi masa sannan suka masa sallama itakuma hajiya Aisha aksake maida ita magarƙama aka kulle.

Ko kaɗan bata dana sani aka abinda ta aikata gani take abinda tayi shine daidai, dukda cewar a tsare take a hannun hukuma wllh seta koyawa Hajiya saratu hankali tayanda zata sanyata cikin baƙin ciki fiyeda zato koda kuwa za'a yanke mata hukuncin kisa ne gabaɗaya. Ta ƙare maganar tana murmushi wanda yafi kamada na takaici

*_GHANDY HOSPITAL 🏥_*

Dr. Varun ne bisa kan muzaffar hannunsa ɗauke da wata ƙaramar na'ura wadda ya saitata bisa kan cikinsa, gefansa



*Kuyi haquri don Allah da wannan ban samun time ne, da kuji ni shiru gwara na baku update koda kaɗan ne. Thanks 4d lover sisters🥰*



comment
Nd
Share


sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


*_Page :26_*


*_DUK ABINDA ALLAH YA BUƊE BABU WANDA YA ISA YA RUFESHI, HAKA KUMA DUK ABINDA ALLAH YA RUFE BABU WANDA YA ISA YA BUƊESHI. AL'AMARIN ALLAH HAKA YAKE 🤷‍♀️_*

*_Ya ubangiji kayi min tsari da duk wanda ke neman ɗaga min hankali mace ko namiji a duniyar yanar gizo🤲, ya ubangiji ka gina min katangar ƙarfe a tsakanina dasu Allah idan ni ban sansu Allah kasansu ya ubangiji kai mana maganinsu don isar manzon Allah SAW🤲_*

*_Masu cewa chubaɗo tace Karku fasa cewa nace kuyita faɗa daga nan har mahadi ya baiyana, ku aiki ya kama tunda gabaɗayan ku babu me wuta bare aljanna da sannu kuma zamu haɗe a madakata✊._*


*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Banyi Editing ba🙅‍♀️

___✍️Gefansa kuma wata matashiyar yarinya ce riƙe da faranti silver irin wanda malaman lfy ke amfani dashi, abubuwa ne akan farantin dayawa waƴanda suka danganci ɓangare irin na ciwon muzaffar ɗin.

Bayan ya gama scanning cikin nasa ne ya gano cewar a kwai inda gubar ta fara yi masa illa ta ɓangaren liver ɗinsa, nan take ya bada umarnin a turashi zuwa ɗakin tiyata don a tari matsalar dawuri idan bahaka ba tsab ze iya rasa rayuwarsa, a gaggauce aka turashi zuwa ɗakin tiyatar cikin mintunan da bazasu gaza 30ba suka kammala cikin ƙwarewa da kuma yarda dakansu a fagen aikin sannan suka maidashi zuwa ɗaki na musamman.

A haka rayuwa taita tafi still babu wani canji a tareda muzaffar ɗin

Nigeria🇳🇬

Edriss ne sanye cikin ƙananan kaya black jeans with write T-shirt gashin kansa duk ya baje harta bayan wuyansa hannunsa ɗauke da mukullin mota ya kalli mom wadda ke gyara zaman mayafin dake jikinta yace "mom amma dai bada waƴan nan yaran zamu tafi Hospital ɗin ba? Ya faɗa yana kallon su Hajar da zeeyadah.

Taɓe baki mom tayi tace "why are you asking me Bayan gasu nan duk da bakinsu? Male baki yayi irin na ajeboters ɗinnan sannan ya fara ƙoƙarin fita daga falon da sauri Zeeyadah tace "pls ya Edyan don Allah zan biku.

Juyowa yayi yana kallonta kimanin wasu mintoci sannan ya sakin mata murmushi yace "ok amma da sharaɗi babu yawan surutu kinji ko? Da sauri tayi nodding kanta alamar ta yarda da sharaɗinsa.

Mom na miƙewa Zeeyadah ma ta miƙe tana gyara rolling ɗin kanta sannan ta kalli Hajar tace "Aunty ke zaman gida ya kama mukam kinga tafiyar mu. Wata uwar harara ta watsa mata sannan tace "dama ai sedai ke ɗin tunda kece uwar neman gindin zama da cusa kai. Hajar ta faɗa tana jan wani uban tsaki

Tun kafin ta ƙara wata magana mom tace "wllh Hajar zakici Uwarki dani a falon nan tunda ke rashin kunyar taki kullum ƙara yawa takeyi a madadin ta ragu, to wllh nida kaina zan sauke miki duk abinda yake kanki. Mom ta faɗi hakan yana zuba uban huji gwalo zeeyadah tayi mata sannan taja hannun mom sukai gaba abinsu.

A harabar gidan suka samu Edyan yana ganinsu ya nufi wata zabgegiyar Renge Rover ɗinsa baƙa wuluk da ita se faman ɗaukar idanu takeyi da hanzari guards ɗinsa suma suka fara ƙoƙarin tada motocinsu dole hakan yasa Edyan ya fito ya kallesu yace "no base kun bini ba zanje ni kaɗai Hospital zanje. Cikeda girmamawa ɗaya daga cikin guards ɗin yace "amma ranka shi daɗe Me girma IG fa yayi mana kashedi akan barinka kai kaɗai ka fit........."tunda ni jariri ne ko ? Edyan ya faɗi hakan with so much angry.

A ladafce suka haɗa baki suna faɗin we are sorry sir. Tsaki yaja sannan ya buɗewa mom back seat na motar sannan ta shiga ya rufe zeeyadah kuma ta kame a front seat, harya shiga motar be ce da kowa ƙala ba a haka yaja motar suka fice daga gidan gabaɗaya Zuwa Asbitin, cikin min tunan da bazasu gaza 15ba suka iso babban madaidaicin private hospital ɗin wanda aka qawata da kayan qawa iri-iri tamkar ba Asibiti ba. A notse ya faka motar cikeda ƙwarewa sannan ya fito ya zagayo ya buɗewa mom side ɗinta ta fito tana murmushi sannan ya rufe motar.

Sakkowa zeeyadah tayi tabi bayansu suka ƙarasa cikin harabar Asibitin, Direct office ɗin Dr. Mujaheed suka nufa, bayan sun shiga da sallama Edyan ya miƙa masa hannu suka gaisa sannan suka gaisa da mom da zeeyadah, nan Edyan yake tambayarda yame jiki?

Ɗan murmushi Dr. Mujaheed yayi sannan yace "jikinta da sauƙi sedai tun jiya data farka take mana kuka kuma taƙi bari kowa yazo kusa da ita munyi2 taci abinci amma taƙi sam. Cikeda damuwa Edyan yace "kana nufin har yanzu babu abinda tasa a cikinta se kuka datakeyi?

Dr. Mujaheed yace "sure.

Da sauri Edyan ya miƙe ya bar office ɗin ya nufi ɗakin da aka kwantar da itan, Da sallama ɗauke a

Please Login or Register in order to submit comment