Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da allon gadon dake ɗakin sannan ta nunata da yatsa tace " bansan wani irin baƙin haline ke bibiyar zuciyarki ba fadilah! Ke wace irin maramutunci ce da har zaki saka hannu ki shaƙi wuyan rigar yayanki wanda ya girme miki fiyeda shekaru biyar? Duk haƙuri irin nasa seda kika ƙureshi Fadilah harya ɗaga hannu ya mareki why are you Behave like that why Fadilah?

Kuka kawai takeyi hannunsa still on her own face wadda ta caɓe da ruwan hawaye gamida majina, mom batabar ɗakin ba seda tayiwa Fadilah tatas sannan ta fito zuwa downstairs inda tabar su Abie, jikin zainab a mace ta kalli Muzaffar tace "bro I'm so sorry for Fadilah's action I'm sure she will regret what she did to you soon. But kafin nan you should forgive her please kar abin ya mata yawa kaji Hayatie.

Murmushin gefan baki ya sakin mata yace "it's OK Qurrah i forgive her since ai tun kafin ma nazo gida, so karki ɓata bakinki share batun kawai

Dariya tayi shidai Abie cin Abincinsa kawai yake harya gama bece dasu ƙala ba, a haka kowa ya gama cin Abincin da abinda yake aiyanawa a ransa.

Se yamma liƙis Fadila ta fito daga ɗaki duk fiskarta ta kumbura abinka da ajebo lol, shima yunwace ta matsa mata shiyasa ma ta fito donta samawa kanta abinda zataci, Zaynab ta Samu ita kaɗai a falon se kuma Hajara me aikinsu wadda ta ɗan fara manyanta suna hira, ɗauke kanta tayi kamar bata gansu ba ta nufi khitchine tana raba ido kozata samu abinda zata zubawa ƴaƴan hanjinta, tsayawa tayi cak tanabin ko ina da kallo amma bataga wani abu dafaffe ba kwaɗawa Hajara kira ta shigayi kamar zata tashi gidan, da hanzari Hajara ta iso khitchine ɗin tana faɗin "Gani ranki shi daɗe me kike so ?

Wani kallon sheƙeƙe ta bita dashi tana wani male baki tace "ki dafanin endomie yanzu ki kawo min ɗaki, bata jira cewarta ba ta juya tabar khitchine ɗin tana wani ɗaga kai kamar zata tashi sama harta kama step zainaba tayi Saurin cewa "oh Allah ya Fadilah Ashe kuma haka abu ya faru babu ɗaɗinji, kaico amma gaskiya na jajanta miki don daga ganin fuskar nan taki ta maru ba kaɗan b.......... Tun kafin ta rufe baki Fadilah tayo kanta gadan-gadan tana huci.

Da sauri zaynab ta miƙe tayi waje da gudu tana ihu, da Abie sukaci karo yana ƙoƙarin shigowa falon kunnensa ɗauke da waya da sauri zaynab tayi bayansa tana tura baki tace "uhmm Abie kaga ya Fadilah ko?

Takaici ne ya kamashi lokaci guda kuma ya zare wayar daga kunnensa yanabinsu da kallo batareda yace dasu ƙala ba, suda kansu sukasha jinin jikinsu Jiki a mace zainab tace "we are sorry Abie baramu ƙara ba.

Raɓawa Abie yayi ta gefansu ya wuce tareda mayar da wayarsa kunnensa yaci gaba da wayanshi.


*GYAMBU TARABA STATE*

Zuwa yanzu Raɓe ta gama fitar da ran cewar Muzaffar ze dawo gareta kamar yanda ya alƙawaranta mata hakan, tafi danganta hakan da cewar ya daɗe da mantawa da ita ma, moddibo ne zaune kan tabarmar kaba yanashan Dawo inna laure ta fito ta zauna daga gefansa suna ɗan taɓa hira kamar daga sama sukaji Tashin harbin bunduga dabda bijirowar almuru, da wani irin mugun sauri Rabe dake bakin murhu ta miƙe tana raba idanu sabida tsabar tashin hankalin data samu kanta a ciki, fuzgar hannunta moddibo yayi yana suka shige bukkarsa a matiƙar kiɗime wata ƙatuwar Boronsa ya ɗaukko a rataye ya sakaƙala mata ita a kafaɗarta lokaci guda kuma ya kama kafaɗunta da duka hannayensa biyu yana kallonta idanunsa cike tab da ƙwalla yace "da alama mafarkin dana jima inayi dab yake da tabbatuwa Rabi'atou tabbas mafarkin bayin Allah gaskiya ne mafarkin annabawan Allah kuma wahayi ne, tabbas abinda ubangi ke nuna min ta hanyar mafarki na shine ke shirin faruwa babu shakka ranar Rabuwata dake yazo Rabi'atou! Rabuwarmu tazo a cikin yanayin da gabaɗayanmu bazamu so hakan ba sedai babu yadda muka iya da abinda ubangiji ya tsara mana, banida yadda na iya dole ne nayi duk me yuwuwa a matsayina na mahaifinki naga cewar kin tsira daga wannan babbar masifar data tunkaro mu a yau kodan gudun kar tarihi ya maimaita kansa.

"amma baba meyasa se kalmar rabuwace zata fito daga bakinka a lokacin danafi kowa buƙatarka? Wllh baba tunani na ya gaza kamar yanda shekaruna suka gaza wajen fahimtar kalmar da kake nanata min ta Rabuwa..... Don Allah baba kada ka bari bakinka ya sake furta wannan kalmar tabbas zuciyata da gangar jikina bazasu taɓa iya fahimtar abinda kakeso su fahimta ba Baba!!!!!? Ta faɗi hakan tana wani irin rushewa da kuka a jikinsa.

Sautin kuwar jama'ar dake rugar kawai kakeji tareda ƙara kusantowar ƙarar harbin bindigar wajen bukkokinsu, fusgeta Modibbo yayi daga jikinsa lokaci guda kuma ya daka mata tsawa yace "lallai ya zama wajibi ki saurareni a matsayina na mahaifinki, idan har Allah ya hukunta cewar zamu sake haɗuwa tabbas zamu haɗu amma kuma idan Allah ya raba ganawa a tsakanin mu lallai ki kasance me kare martabar mutuncin ki har zuwa muhalin daya dace, sannan idan ƙaddara ta sake haɗaki da Muzaffar lallai ki gaya masa cewar idan da hali to ya cika alƙawarin daya ɗaukarmin a kanki, idan kuma ƙaddara bata haɗaku ba lallai karki kuskura ki ƙara tako ƙafarki cikin Gyambu har rayuwarki ta ƙare a inda kikaj........! Ya faɗi hakan wani irin kuka yana taso masa.

Wani irin tausayinta yakeji sedai vayajin cewar ze iya barinta a taredashi a wannan halin sabida sam baze juri ganin mutuwarta a gaban idanunsa ba, ya sani cewar abu ne mawuyaci mace ta rayu a inda bata babu wani nata kuma ta rayu ciki salama kokuma cikin Aminci batareda ta lalace ba, sedai babu yadda ya iya dole hakan shine mafita a garesu gabaɗaya. Ɗaga hannunsa yayi sama yana kuka yace "ya ubangiji na ga Amanar daka bani nna ta ƴar dana haifa, ya Rabbissamawati wal'ardi ka kulamin da ita a duk halinda zata samu kanta a ciki, ya Allah kada ka barta da iyawarta ka Iya mata da iyawarka ya Allah!

zata sake magana kenan ya dakatar da ita ta hanyar jan hannunta suka fito daga bukkar yana share hawayensa.

Koda suka fito basu cimma inna laure a tsakar gidan ba hakanne yasa moddibo leƙawa ɗakinta don ya tabbatar da tana ciki kokuma ta tsere, can ya hangeta ta haye kan katifar ciyawarta jikinta banda rawa babu abinda yakeyi, takawa yayi da sauri ya fuzgota tana tirjewa a haka ya janyota suka fito, gabaɗaya babu abinda ke tashi a rugar face sautin harɓin bindigar da ƴan fashin ke amfani da ita, baka ganin komai se ƙurar jar ƙasar dake tashi a gurin hakanne ya haifar hargitsewar dabbobinsu, hatta shanunsu duk sun kwance sun fazama cikin daji a gigice.

Cikin jeji moddibo ya nausa dasu banda gudu babu abinda sukeyi a haka har suka fara nisa da rugar, fusge hannunta Laure tayi daga cikin na modibbo tace "Sakarni Moddibo wllh ban ƙara ko taku guda daga nan, kana nufin haka zamubar dukiyarmu da kuma ƴan uwanmu ɓarayi na kashesu kamar tsintsaye?

Hawaye ne ya zubo masa a lokacin daya tina Wasiyar mahaifinsa na cewar" a duk sanda masifa ta afka muku modibbo da zarar ka samu nasarar fita daga gurin da masifar ke faruwa kaida iyalanka koda wasa karka bar ɗayansu ya koma inda abin ke faruwa idan kuwa har hakan ta faru lallai ɗayanku ze mutu idan kuwa har ba'a mutu ba to zaku tabka babbar Asara cikin biyu za'ai ɗaya.

Fashewa yayi da kuka ya janyo Rabe yana kuka ya Rungumeta lokaci guda kuma ya zare jikinsa daga nata yace "lallai kiyi nisa da wannan jihar tamu nisa me tsahon gaske sannan ki sanya a ranki cewar idan da rabo wata rana zamu sake haɗuwa. Juyawa yayi da sauri zebi bayan Laure da hanzari ta riƙe hannunsa tana kuka tace "kayimin alƙawarin cewar zaka jirani har lokacin da ƙaddarar data rabamu zata dawo dani babana. Zeyi magana ta dakatar dashi tace " nidai kayimin alƙawarin cewar zaka jirani har lokacin da zan dawo gareka a raye batare da kabari muwa ta riske ka ba.

Gabaɗayansu kuka sukeyi me taɓa zuciyar duk wani me imani, da sauri ya ɗaga mata kai yace "nayi miki alƙawari ƴata tabbas zan jiraki har zuwa ranar da ƙaddara zata dawo min dake. Yana faɗin haka ta saki hannunsa tana kuka ta juya ba tareda ta sake juyowa ba ta nausa cikin jeji batareda sanin inda ta nufa ba.

Zubewa yayi a ƙasa ya fara sharɓar kuka musamman daya tuna alƙawarin daya ɗaukarwa ɗiyarsa wadda be taɓa gaya mata abinda yake ba gaskiya ba daga bakinsa, se gashi yau an wayi gari yayi mata alƙwarin da baze iya cika matashi ba.

Ya jima yana kukan sannan ya miƙe yabi bayan laure yana me ƙara jaddada Amanar Rabi'atou ga ubangijinsa....





*Chai nasha ƙorafi mara adadi dik akan wannan littafi 😂*


*Yasin idan banga ruwan comment ba se bayan sati biyu zaku sake ganina koma na ajiye alqalamin gabaɗaya Huta roro waken gixo yaqi ƴaƴa🤷‍♀️*


Comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:35 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


*_Page :20_*


*_WRITING BY: CHUBAƊO_*


____✍️ Da kallo kawai hajar tabishi tana me tausayin kanta a nan gaba, Allah ne kawai shedarta akan irin son datakema wannan bawan Allahn tun daga ranar data fara ganinsa zuciyarta ta amsa, batajin cewar zata jurar rashinsa koda na kimanin ƙwayar zarra ne.

Share hawayen dake xubo mata tayi sannan ta ƙara gyara zamanta akan kujerar datake kai, a yau dai kam ta lasarwa kanta takobin cewar bazata taɓa barin falon nan ba harse taji matsayinta a gurin Muzaffar koda hakan ze zama wani abu me zaman kansa ne a tsakaninsu. Tambaya ɗaya ce taƙe mata yawo a zuciyarta shine wacece wannan Fulani girl ɗin da cikamakin Rayuwarta yake Ambaton sunanta haka a gabanta batareda shakka ba?

A ƙalla ba ƙasaru ba Hajar seda ta shafe Awanni uku chur zaune a falon batareda uban gaiyar yasan da ita a gurin ba har yayi baccinsa ya tashi kana yayi wanka ya canza kaya zuwa launin ƙananan , Black jeans with Sky blue T-shirt Sosai kayan ya karɓi jikinsa tamkar dama danshi akayisu, komai nasa tsaf-tsaf dashi shiyasa yake classy guy. silifas ya ɗauko a cikin shoe rack ɗinsa me launin baƙi ƙirar companyn Batozy ya sanya a ƙafarsa, hakanne ya sake fito da ainihin kalar hasken fatar jikinsa gaba ɗaya, a nitse yake takawa harya fito daga Bedroom ɗin ya ƙaraso cikin falon tsayawa yayi chak yana kallon hajar wadda ke bacci da mamaki kwance akan fuskarsa yace "ya salam what kind of lady is this?

Haɗe rai yayi sosai tareda bugawa gefan kujerar firgigit Hajar ta tashi tana kallonsa, ƙura mata idanu yayi with serious face yace "me kikeyi har yanzu baki tafi gida ba?

"taya zan tafi bayan har yanzu bansan matsayina a gareka ba? Hajar ta faɗi hakan idanunta na shirin kawo ƙwalla.

"look hajar ya kamata ace zuwa yanzu kin fahimci manufa ta, ni gabaɗaya yanzu babu soyayyah a tsarina a zatona ya kamata ace zuwa yanzu kin daɗe da cireni a ranki tunda na gaya miki abinda ya kamata ace kin gane kokuwa?. Ya faɗi hakan yana kallon tsakiyar idonta

Kuka Hjaar ta fashe masa dashi al'amarin daya ƙara ɗaga masa hankali kenan, a rayuwarsa ya tsani kukan mace ballantana kuma ace shine silar yin kukan nata da sauri yace "its ok hajar pls stop crying yanzu kije gida insha Allah idna na dawo daga india satin gaba me zuwa zanzo gidanku se muyi magana ok? Da sauri ta ɗaga masa kai tana share hawayen dake idonta ta miƙe tsaye, kusan a tare suka fito daga part ɗinsa har suka iso maine falon Momy

Waya suka samu Momy nayi tana ganinsu ta katse kiran tace "bari zamuyi magana zuwa gobe. Daga hakan ta katse kiran tana binsu da kallo

Sunkuyar dakai hajar tayi cikeda jin kunyar Momyn tace "mom zan wuce gida. Kallon tsaf mom tayi mata sannan ta ɗaga mata kai tace "kigaida mamanki. Bata ƙra cewa komai ba ta nufi daining batareda tace da muzaffar ƙala ba, sosai yasha jinin jikinsa da irin kallon tuhumar da Momy ke binsa dashi yace "mom pls me namiki?

Tsayawa tayi ba tareda ta juyo ba tace "Au tambayata ma kakeyi donka rainani? Me wannan yarinyar takeyi a part ɗinka har tsahon wannan awannin kuna tare?

Da sauri yace "Mom!!!! Are you suspecting me for doing something with her?

Ba tareda ta kalleshi ba tace "no at all but bari Abie ya dawo dolene a tsayar da maganar Aurenka koma da wace yarinya ne sabida ni bazan ɗauki iskancin nan a gidana ba, and let me tell you something muzaffar wllh dole ne kayi Aure idan har baka son ganin ɓacin raina. Damn sauri yace "mom Aure Kuma? But senake ganin...... "ya isheni haka nan malam ka wuce kawai ka bani guri.

Jikinsa a mace yabar falon ransa a matiƙar ɓace, yana fita harabar gidan ya nufi mota ze shiga da sauri Selomon ya nufoshi ze buɗe masa ƙofa ya dakatar dashi yace "ban key yau ni kaɗai zan fita. Ba mutsu ya miƙa masa keyn ya shiga motar ya buga mata key ya fuce daga gidan gaba ɗaya, tabas dole ne ya zauna da Abie tun kafin mom ta rigashi yin hakan yasan dole Abie ze fahimce shi becouse baze masa dole akan abinda bayaso ba ko kaɗan, tsaki yaɗan ja kaɗan lokacin da Hajar ta faɗo masa a rai yace "komai ya faru itace silah.

Murmushin mugunta yayi daya tuna zainab, tabbas yasan itace ta haɗa masa komai tunda ai seda ya gaya mata cewar karta faɗawa hajar yana gida amma kuma seda ta gaya mata, dole ne ya hukunta ta akan hakan.


*_GYAMBU TARABA STATE_*

Duk yanda Laure ke tsammanin bala'in dake faruwa a garin Ashe abin ya wuce zatonta da kuma tunaninta, amma sam dukda hakan batayi tunanin komawa da baya ba still hankalinta na kan dukiyar da moddibo ya jima yana tarawa, bata dire ko ina ba se ɗakin moddibo nan ta fara birkita ɗakin ɗakin ta ko'ina tana neman jakar saƙin dayake zuba kuɗaɗensa masu nauyin gaske, gaba ɗaya ta gama burkita ko ina duk yanda taso ganin jakar amma sam abin ya faskara dole yasa ta dakata da bin ciken jakar ta tsaya cak tana tunani, tabbas ɗazu da suna gudu taga jakar a bayan Rabe kenan hakan yana nufin duka kuɗaɗen moddibo ya baiwa ƴarsa ta gudu dasu?

kurma ihu tayi kamar wata mahaukaciya sannan ta fito daga bukkar tana me nadamar dawowar datayi, lallai dole ne tabi bayan Rabe ta tayi mata shegen duka sannan kum ata ƙwace jakar inyaso ta shiga duniya daganan ta buɗe sabuwar Rayuwa. Juyawa tayi da nufin barin gurin kamar daga sama taga manyan ƙarti majiya ƙarfi sun kewayeta ko wannansa riƙe da bundiga ƙirar Ak47 suna kallonta, nan take hanjin cikinta suka yamutse.

bata ƙara sarewa ba seda taga su malam Iro duk an ɗaɗɗauresu jini na zuba daga gefan cikinsa, ananne fa ta ƙara furgicewa kuma ta fashe da kuka moddibo dake zaune bisa gwiwoyinsa duk an tamkeshi da igiya kansa na zubar da jini ya ɗago idanunsa da ƙyar jirin jini na ɗibarsa ya zuba mata idanu cikin yanayi irin na fitar haiyaci, nan take laure ta ɗora hannu bisa kanta ta kurma wani uban ihu.

Ɗaya daga cikin ƴan fashin ne ya ɗaga hannu ya zabga mata wani lafiyayyen mari ne shiga nan take Laure ta tsuke bakinta tana wani zare idanu, babban cikinsu ne ya kalli wanda ya mareta yace dashu "kai Sage maza jefamin ita a ɗaki zan ɗan rage zafi da ita.

Gabanta ne yay masifar faɗu lokaci guda kuma ta zuɓe a ƙasa tana roƙonsu kan cewar su rufa mata Asiri karsu keta mata haddi, wani marin ya sake watsa mata take gefan bakinta ya fashe ya fara jini tanaji tana gani wannan ƙaton ya hurgata cikin ɗakin moddibo ogansu yayi mata fyɗe a gaban idon mutannan dake gurin. Wani irin kuka laure keyi sabida baƙin cikin data samu kanta a ciki bayan ya samu nutsuwa da itane ya fito waje yana gyara zaman wandon dake jikinsa ya kalli yaransa yace "idan dame buƙata a cikinku seya antaya shima yay mata juyen baƙin mansa.

Jiki na rawa Sage yace "oga zan ɗan kwashi romon nima. Dariya suka fashe da ita sannan Sage ya antaya ciki shima ya huce takaicinsa a kan Inna Laure a taƙaice dai seda mutum huɗu sukaiwa Inna Laure Fyaɗe tanaji kuma tana gani babu yadda ta iya.

a wannan rana Laure tayi kukan da batasan Adadinsa ba haka kuma tayi dana sani mara misaltuwa a Rayuwarta , nan take nadamar Rayuwa tayi mata dirar mikiya a lokacinda komai ya lalace mata.

*_ƁANGAREN RABE KUWA_* Jingina tayi da wannan bishiyar dake gefanta tareda zubawa Sarautar Allah idanu, wani irin kuka ne ya taso mata a lokacin data tunada halinda tabar Ahalinta a ciki babban abinda yake ƙara ɗaga mata hankali shine rayuwar da zatayi a nan gaba tareda mutanan da bata taɓa saninsu ba. Seda tayi kuka me isarta sannan ta miƙe ta gyara zaman jakar dake kafaɗarta wanda moddibo ya bata sannan taci gaba da tafiya tana kukan, seda tayi tafiya me nisan gaske sannan ta fito titi

bin ko ina take da kallo lokaci guda kuma zallar mamaki ya baiyana ƙarara akan fuskarta, sun kuyawa tayi tana shafa titin da yatsun hannunta a ɗan tsorace da sauri ta janye hannunta tareɗa ja da baya kaɗan still her eyes on the titin, mamaki takeyi shin menene wannan abin haka?

a iya Rayuwarta bata taɓa fito titi ba shiyasa ganinsa a yau ya zame mata tamkar sabon abu ne a gareta, tana nan tsaye taki gaba taki baya kawai ba zato ba tsammanin wata haɗaɗɗiyar motar ƙirar ford ta sako kai, da wani irin mugun gudu Rabe ta kwasa tana ihu tayi cikin Dajin sabida ganin motar datayi, gabaɗaya a zatonta wata halittar ce me matiƙar tsoratarwa

Seda ta tabbatar motar ta wuce sannan ta fito hannunta ƙanƙame da jakar Saƙin nan dai da Mahaifinta ya bata, kamar me koyar tafiya haka ta dinga taka titin don gani take a kowani lokaci ze iya ɓurmawa da ita (Allah sarki iyayena fulani😂)

Ruwan sama ne ya kece dole yasa ta nemi wata Bishiyar ta haye samanta ta lafe tayi shiru, a hankali Ruwan ke sauka a saman kanta yana kwaranyowa ta saman gashinta zuwa gangar jikinta, lumshe manyan idanunta tayi tareda faɗawa cikin duniyar tunanin makomar Rayuwarta.......

*_ABUJA NIGERIA_*

Se wajen 8:pm sannan muzaffar ya dawo gida Direct falon Abie ya nufa sedai yana shiga falon yaga mom a gefan Abie ɗin, gabansa ne ya faɗi amma kuma seya dake yayi murmushi ya ƙarasa cikin falon da Sallama, da sakin fuska with so much love for his son Abie yace "come near me my Qurratu ain. Da sauri ya isa gareshi ya zauna daga ƙasan ƙafafun Abie ɗin tareda kwa tar da kansa a saman ƙafafunsa, murmushi kawai mom tayi ta ɗauke kanta a lokacin da kiran waya ya shigo mata , kallon Abie tayi taga hankaƙinsa gabaɗaya yana kan ɗansa hakan yasa tayi murmushi ta niƙe ta fita tareda kara wayar a kunnenta, sosai hakan yayiwa Muzaffar daɗi don haka ya miƙe ya koma kan kujeran kusa da Abie tareda kama hannunsa cikin nasa ya damƙesu guri guda yace "Abie I feel like I'm a lucky son that I have you as a father, Abie ka cikemin gurbin komai danake buƙata a rayuwata but I don't know why I feel like I'm miss something in my life Abie, har yanzu kuma na kasa gane menene wannan abin dana rasa ɗin!!

Murmushi Abie yayi me cikeda dattako sannan yace " so tari a rayuwa mukayi kewar abubuwa dayawa a cikin Rayuwarmu musamman ma ace waƴanda muke ƙauna. Ƙauna kuma Abie? Muzaffar ya faɗi hakan cikeda rashin gamsuwa

Murmushi Abie ya sakeyi a karo na biyu yace " amatsayina na Abokinka ba mahaifi ba ina me baka shawaran cewa ka koma ka saurari zuciyarka yayinda ka keɓance kanka kaikaɗai to a nan ne zaka fahimci cewar lallai abinda na Sanar dakai gameda feelings ɗinka to soyayya ce a hakan ma me ƙarfin gaske, from this moment I'm going to be precious About what I say.

"Abie what are you trying to say wai? Muzaffar ya faɗi hakan yayinda ya ƙara kafe Abie da dara-daran idanunsa

murmushi Abie ya sakeyi a karona uku sannan yaci gaba da cewa "Think carefully Son. Whoever it Is, or whatever situation it is that's Love my Son.

wani irin zaro idanu muzaffar yayi tamkar wanda aka gaya masa wani babban tashi hankali ya kalli Abie tareda sauke Ajiyar zuciya yace "yanzun kam na fahimci abinda kake nufi Abie but why nakejin sauyi a cikin Rayuwata daga shekarun baya zuwa yanzun?

nikam tabbas inaji a jikina cewar tamkar a kwai wani Abou me mahimmanci wanda ya zarta Kalmar so a rayuwata dana rasashi Abie, pls meneɓe shi?

Kallon tsaf Abie kebin muzaffar ɗin dashi sannan ya miƙe yace "naga alamaɗ idan har na biye maka to zamu shekara dakai a nan batareda ka gaji ta jefomin sinƙi-sinƙin tambayoyinka ba, oya tashi ka tafi gobe to 6:am insha Allah jirginku ze ɗaga zuwa india.

Langaɓar dakai muzaffar yayi yace "no Abie nidai vanason tafiya a privet jet ɗin company nafiso na tafi a nomal jirgi kamar kow....... Kallon da Abie ya watsa masa ne yasashi haɗiye maganar dayay niyar faɗa. Miƙewa yayi tareda baya Abie side hugg sannan ya fice daga falon zuwa ɓangaren sa, kasancewar yayi sallar isshansa a inda yaje yasa ya fara rage kayansa sannan ya faɗa toilet, wanka yayi ya fito tareda shiryawa cikin lausasan kayan baccinsa yabi lafiyar gado

Washe gari tun sassafe ya tashi ya shirya cikin wata Arniyar Korean suits ƴar gaske me azabar kyau baƙa wuluk da itase ɗaukar idanu takeyi sannan ya tsaya a gaban mudubin dake ɗakin ya gyara gashin kansa me laushin gaske da santsi tamkar na jinsin fararen fata, a wannan lokacin kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci cewar yafi kamata larabawan yankin ƙasar misirah, ni kaina a yau seda na rola muzaffar fiyeda zaton me karatu domin kuwa ya haɗu iya haɗuwa.

Ƙafarsa sanye take cikin wani dakakken takalmin fata ƙirar Compayn Kang gi boam dake yanki Korea ta kudu. Da alama komai na muzaffar daga ƙasar akai odarsu

a nitse ya fito daga

Part ɗinsa cikin takunsa na isa da ƙasaita ya nufi falon mom, be sameta a falon ba se Fadilah dake zaune cikin kayan baccinta me launin kalar milk tana kallin news a Tv, wuceta yayi ba tareda ya kalleta ba ya haura upstairs Don because he don't have her time at all ya tsani mutum mara respect ko kaɗan shiyasa ma ya fita sabganta.

Ƙofan ɗakin mom ya ƙwanƙwasa seda ta bashi izinin shiga sannan ya kunna kai cikin bedroom ɗin da sallama a zaune ya sameta a gefan rantsatsen makeken gadonta tana jiran ya karaso, gefanta ta nuna masa alamar ya ƙaraso ya zauna ba musu yayi yanda ta umarceshin

Ɗan jim tayi kaɗan sannan ta dubeshi cikeda damuwa tace "harka shirya kenan se tafiya? Da kulawa ya kalleta yace "ae mom na gaba zan wuce ɗin Kenan . Gefan fuskarsa ta ɗan shafa kaɗan sannan tace "Allah ubangiji ya bada sa'a yasa kuma kaje lafy ka dawo mana lfy. Da amin ya amsa mata sannan ya miƙe yace bye mom.

Harya

Please Login or Register in order to submit comment