Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

TO ALL MUSLIMS UMMAH!!!*


*_O'o naji qorqfinku mabiya wannan littafi har seda na godema Allah 😄 Don haka qorafinku ya karɓu isha Allah zan cigaba da rubuta muku wannan littafi koda ba kullum zan dinga baku update ba, motsi yafi laɓewa inji ƴan magana lol. Ngde sosai da nuna qaunarku a gareni sonso fisabilillah❤️_*


___✍️Zaune yake cikin hamshaƙin office ɗinshi wanda aka ƙawatashi da abubuwa na musamman wa ƴanda suke tafiya da zamani idanunsa sanye cikin wani bakin glass mallakin compayn prada, gabaɗaya ya maida hnkalinsa kan system ɗin dake gabansa tsaki yaɗan ja kaɗan tareda zare baƙin glass ɗin daya rufe idanunsa dashi donya tabbatar da abinda idanun nasa suka gane masa, wara manyan idanunsa yayi kaɗan yana kallon yanayin sababbin tsare-tsaren da aka samu a cikin ɗan tsukun lokacin daya rasa a cikin Rayuwarsa na ɓatansa, lokaci guda ya miƙe yana wani cizon jan lips ɗinsa na ƙasa ya nufi office ɗin Accounter Salahudden, duk inda yabi kallonsa kawai ma'aikatan keyi tareda risinawa suna kwasar gaisuwar a gareshi faɗaɗa murmushin yaƙen dake kan fuskarsa yayi tareda amsa musu gaisuwar da sakin fuska a haka har ya isa office ɗin Accounter Salahuddeen ɗin.

Tun kafin ya iso office ɗin Salahudden ke kallonsa ta glass ɗin dake zagaye da ko ina na office ɗin, Ɗaure fuska Muzaffar yayi sannan ya tura ƙofar ya shiga cikin takunsa me ɗauke da sirrin kwarjinin dake taredashi, Direct gaban table ɗin dake jibge da uban files gamida system ɗin dake gaban Salahuɗden ya nufa idanunsa na cikim nasa.

Da sauri Salahudden ya miƙe yana murmushi yace "Ran C.e.o ya daɗe yau kaine da kanka a cikin office ɗina aida bakazo da kanka ba ka turo an kira maka ni inyaso ni sena kawo kaina gareka Allah ya taimakeka.

Taɓe baki Muzaffar yayi yana kallonsa a ransa yana me jinjinawa ƙwarewar Salahudden a wajen iya kafcen dramar wasan kwaikwayo yace "Accounter a ƙa'idar wannan Companyn tun kafin haihuwata zuwa yanzu ba'a taɓa fitar da kuɗi komai ƙanƙantarsa batareda an shigar da hujjar abinda akayi dasu a rubuce ba a matsayin sheda. meyasa ka fitar da kuɗi kimanin naira million 60 batareda sani na ba ?

Zaro ido Salahuddeen yayi yana kallonsa da manyan idanunsa lokaci guda kuma wani irin gumi ya shiga keto masa tamkar an sheƙa masa ruwa a daburce yace "Ammm.....Ae.....dadd..dama..inaso...uuhmm "ka dakatar da wannan dramar da kake ƙoƙarin shiryawa a gabana Salahuddeen!!!!!. Muzaffar ya katseshi ta hanyar daka masa wata uwar tsawa cikin ɓacin rai yace "zaka gayamin dalilin fitar kuɗin ne kokuwa sena sa an Rubuta maka takaddar Sallaman ka daga aiki gaba ɗaya?

Miƙewa Salahudden yayi da sauri ya zagayo inda muzaffar ɗin ke tsaye yace "aa don Allah C.e.o karkayi min haka na roƙeƙa wllh ba laifina bane fin ƙarfina akayi dole yasa na taimaka mata muka fitar da kuɗin ba tareda saninka ba, idan har ka koreni wllh kayiwa rayuwata illa ta ɓangarori da dama pls kayi haƙuri ka yafe min wllh zan maka bayanin yanda akai komai ya faru!

Kallon sheƙeƙe yakebin Salahudden ɗin dashi lokaci guda kuma yace "wannan matsalarka ce kiada kuka aikata tare da wanda yafi ƙarfin naka oya tashi ka bani cikakkun bayanai akan fitar kuɗin da kuma sunan uban wanda yasaka kuka fitar da kuɗin. Jikinsa na rawa ya juya ya fara neman takardun kasancewar abin be wani daɗe ba yasa ya binkitosu cikin sauƙi ya miƙa masa, karɓa yayi ya fara dubawa take sunan Md Fadilah Abdulwahab ya baiyana a jikin takardan ƙuru-ƙuru a matsayin wadda aka haɗa hannu da ita wajen fitar da kuɗin

Wani shaiɗanin murmushi ne yay escaping red lips ɗinsa ya kalli Accounter yace "karka taɓa tsammanin cewar zan ƙyaleka ban hukuntaka ba akn abinda kuka aikata kaida Md ba Salahudden, it possible hukuncin dana yanke mata kaima shi zan zartar akanka ba tareda na banbanta hakan ba tunda har ka iya biye mata kuka haɗa hannu wajen gudanar da zanbo cikin Aminci A cikin wannan Company, dole ne ku karɓi hukunci. Ya faɗi hakan yana wani datse lips ɗinsa da white tooth ɗinsa da suka ƙara ƙawata kyakkyawar fuskarsa

Juyawa yayi ya fice tareda takardun a hannunsa ranshi a ɓace. Dole ne ya ɗauki mataki akan Fadilah a wannan karon don baze ci gaba da zuba mata idanu tana aikata duk abinda taga dama ba becouse this time ta fara wuce iyakarta.

Be dire ko ina ba se Office ɗinshi tareda zuɓe takardun a saman table ɗinsa sannan ya zauna ya jawo system ɗinshi zuwa gabansa ya fara daddannawa, cikin mintunan da bazasu gaza 4 ba ya kammala rubuta gajeran saƙon da yake rubutawa tareda turashi ta wani Email Address sannan ya miƙe ya fice tareda rufe System ɗin. Tun kafin ya fito saƙon korar Fadilah Abdulwahab Abdullah ya cika Companyn abinka da zamani na kimiya


Fadilah dake zaune cikin office ɗinta tana gudanar da Aiyukanta ne ta ɗago ta zubawa wayarta idanu sabida ƙarar saƙon daya shigo mata a wannan lokacin, tsaki taja me sauti sannan ta jawo wayar ta buɗe saƙon tan akarantawa take idanunta suka firfito sabida tashin hankalin data samu kanta a ciki, wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ne ya turniƙeta nan take wata sabuwar wutar tsanar muzaffar ta fara kwaranya a saman zuciyarta. Miƙewa tayi a hasale ta nufi ƙofar fita daga office ɗin tana huci tamkar zata tashi sama, Direct office ɗin Abie ta nufa ƙwalla kwance a tsakiyar ƙwayar idanunta

Duk inda ta nufa sedai kaga ana juyawa ana kallonta masu yi mata dariya a ɓoye nayi masu jajanta mata ma nayi, wannan baƙin cikin ne yasa tana shiga office ɗin Abie ta fashe da kukan baƙin ciki da takaici a lokacin dataga kujerar zaman Abie ɗin babu kowa a kai hakanne ya bata tabbacin cewar Ya tafi gida, kife kanta tayi akan gwiwarta ta shiga gurzar kuka bisa wannan abin kunyar da muzaffar ya jawo mata a idon mutanan dake ƙasanta.

Zuciya ce ta kwasheta ta fito daga office ɗin har idanunta na Rufewa sabida fishi da ɓacin Rai ta nufi ƙofar fita daga companyn da wani irin mugun gudu ta ƙarasa fitowa a lokacin data hangi Muzaffar na ƙoƙarin shiga mota gurds ɗinsa na tsaye alamar gida Zashi

Kamar ƙiftawar idanu se gata a gabansa lokaci guda kuma ta damƙi wuyan Korean suits ɗin dake jikinsa ta fara ƙoƙarin fito dashi tana binsa da kallon tsana.

Wani irin ɓacin rai ne ya tasowa Muzaffar lokaci guda ya fito daga motar tareda watsa mata wasu lafiyayyun maruka a fuskarta, lokaci guda kuma yasa ƙafa tokareta take tayi baya lu zata faɗi ya riƙeta da sauri yana huci yace "komai yazo ƙarshe fadilah tunda kikasa yau na dora hannuna a jikinki. Wai shin ke wace irin yarinya ce? Wllh da ace ba'a gida Momy ta haifeki ba zance sam keba jinin mu bace sabida baƙin Halinki, karki bari ki kaini bango Fadilah nayi abinda ze janyo wani sabon al'amarin a tsakanina dake so you have to respect your self.

Ya faɗa yayin da yake tureta daga jikinsa cikin fushi

Kifewa tayi a gurin tana kuka shikuma ya rufe motar suka bar harabar companyn zuwa gida, ta jima tana kuka a gurin sannan ta miƙe ta nufi motarta ta shiga gurds ɗin mutum biyu na take mata baya a motarsu suka nufi gida zuciyarta na suya .

Ɓangaren Muzaffar kuwa sosai yakejin haushin kansa da har ya iya ɗaga hannu ya doki ƙanwarsa wadda suka fito ciki ɗaya sabida wani ƙaramin laifi data aikata masa na kama masa wuyan riga a cikkn jama'a nan take yaji wani irin tausayinta na kwaranyowa daga ƙasan zuciyarsa, a haka suka kai gida Ransa duk babu daɗi, Direct part ɗinsa ya wuce sabida be shirya yin magana da kowa ba sabida yanda Fadilah ta ɓata masa mood ɗinsa na yau.

Bayan dawowarsa da minti goma sega Fadilah ma ta dawo, buɗe motar tayi ta fita tana kuka batareda ta jira gurds ɗinta sin buɗe mata ba kamar yanda ta saba ba, cikin gidan ta nufa da cogalelen takalminta tana kuka a haka ta shiga falon ko Sallama babu, gabaɗayansu ido suka zuba mata daga Momy har Abie zainab kuwa baki ta saki da hanci tana kwasar kallo sabida a iya zaman da sukayi tare kafin ta tafi India bata taɓa ganin Fadilah tana kuka irin haka ba se yau itako meya sameta haka?

Bata kulawa kowa ba ta kwasa da gudu ta nufi Upstairs tana ƙara sautin kukanta Al'amarin daya ƙara ɗagawa su Abie hankali kenan sukabi bayanta, duk yanda sukaso su cimma Fadilah abin ya faskara tana shiga ɗakinta ta murza key ta faɗa gado ta shiga rusa wani sabon kukan baƙin cikin, duk irin rarrashi da ban bakin dasu Abie keyi kanta buɗe musu ƙofar fur Fadilah taƙi buɗewa dole yasa suka haƙura suka barta.

*******

*Gyambu Taraba state*

Zuwa yanzu kam moddibo ya gama sarewa da lamarin Rabe sabida yanda yarinyar ta rame kuma ta fita haiyacinta, bata da aiki se kuka da keɓe kanta daga shiga cikin mutane wannan al'amarin ne yake ƙara ɗaga masa hankali, ko abincin kirki bata iya ci yau tunda sanyi safiya take fama da wani irin ciwon ƙirji me matiƙar zafi, buguda ƙari ga wani irin nauyi da saitin zuciyarta keyi mata.

Kokaɗan bataso ta nuna gazawarta a idon Mahaifinta wadda yanke kallonta a matsayin sanyin idaniya a gareshi, tasan dolene idan ya fahimci irin halinda take ciki beze taɓa samun kwanciyar hankali ba shiyasa ta zaɓida ta boye masa lalurarta, kwance take kan katifar ciyawarta idnunta na kallon saman bukkar dake ɗakin wasu zafafan hawayene suka shiga zubo mata a lokacin data tuna abinda ya faru a tsakaninta da Muzaffar ranar da suka tafi kiwo na ƙarshe dashi.

*Flash back*

tunda suka tafi kiwo bashi da aikin daya wuce kallonta haka kawai yaji cewar yana shi'awar kallon nata dik inda tabi idanunsa na kanta tamkar baze dena kallonta ba, ita kuwa sabgar gabanta kawai take ba tareda ta lura da irin kallon dayake binta dashi ba tana ɗagowa a karon farko idanunsu ya sarƙe cikin na juna
A hankali ta buɗe baki tace" Hamma zafar meyasa kake yawan kallona a ƴan kwanakin nan?

Murmushi yayi sannan yace"sabda zanyi missing naki.

Sosai take kallon sa tace " meye kuma mushin ke nufi?.

Dariyace ta kamashi amma kuma ya danne yace "kalmar tana nufin zanyi kewarki ne to.

Wata irin Dariya ce ta kamata sosai irin wadda bata tabayin kamarta ba a gabansa ba a Iya zaman da yayi tareda dasu, daƙar ta iya saita kanta ta dena dariyar tana kallonsa tace "amma Kaɗo ka iya tsiya Aradu.

Tunda ta fara dariyar yake kallonta kamar zeyi kuka yace, meyasa kik dariya irin haka bakisan yawan dariya yana gusar da imani ba?

Murmushi tayi tace abinda ka faɗa ne ya bani dariya, Aradu senaji Kalmar taban tamin daban a shikin kaina.

Hade rai yayi yace " to kada ki sake min irin wannan dariyar bana so, kinji yanda kika tsorata ni kuwa?
Sunkuyar dakai tayi sannan ta riƙe kunnuwanta guda biyun kamar yanda yakeyi mata idan ya ɓata mata rai kamar zatayi kuka ta tsuguna ƙasa tace "waɗu munyal Hamma zafar badan ƙara ba!

Dariya ta bashi sosai dan haka yay murmushi tare da Jan kumatunta yace "uhm that's my Fulani girl shikenan na haƙura amma kaɗan.
Dariya sukayi gaba ɗayansu dukansu, a haka wannan Ranar ta kasance daban a garesu koma a kirata da Rana ta musamman a gareta.

A zaman datayi dashi kullum ƙara samun kusanci yake da zuciyarta batareda ita kanta tasan hakan ba, wasu Zafafan hawayene suka shiga zubo mata yayi data farka daga duniya tunanin data Afka akan matashin ɗan kasuwar mejida kuɗi da ƙwalisa wanda a gurinta ya kasance tamkar wani mutum na daban wanda take kallo tamkar wani waliyi a birnin zuciyarta Saɓanin shida ya mance da batun wata fulani girl dake Rayuwa a wani ƙaramin daji wanda sam be gina masa wani muhali a cikin filin zuciyasa daze iya tunawa nan kusa ba.

Zuwa yanzu kam ta sare kan cewar Zafar baze taɓa cika alƙawarinsa gareta ba na cewar ze dawo gareta komai daran daɗewa koda kuwa ba nan kusa bane yau gashi ya kwarari kusan shekara da tafiya ba tareda ya juyo gareta ba. Burinta a yanzu shine Allah yasa a duk inda Hamma zafar yake ya kasance a cikin Farin ciki da ingantacciyar rayuwa koda ace baze ƙara tunata a cikin Rayuwarsa ba har Abada zata cigaba dayi masa kyakkyawan fata har zuwa ranar da Ranta zebar jikinta.

*Abujah*

Tunda ya dawo ya kasa gudanar da komai sabida ɓacin ran daya dawo dashi daga office, ajiyar zuciya ya sauke me nauyin gaske sannan ya miƙe ya faɗa toilet donyin wanka be jima ba ya fito ɗaure da towel ɗaya a ƙungunsa ƙarami kuma bisa wuyansa, goge jikinsa yayi tsaf batareda ya shafa maiba ya buɗe tafkekiyar drower ɗinsa dake manne a jikin katafaren bangon dake ɗakin ya fito da wasu ƙananan kaya marasa nauyi ya sanya a jikinsa, tareda yin cumming lallausar Sumar dake kansa ya fita harabar gidan.

Da Zainab yaci karo tana mishi murmushi tace "bro Anul Abie da momy ne sukace y nazo na dubaka ko lfy sunji ka dawo amma bakazo kayi lunch ba. Dafa kafaɗanta yayi suka fara tafiya tare har suka isa maine falo ɗin Momy suna ɗan taɓa hira sannan yace "Cutie zee jeki haɗamin ouds pls banson cin komai yau

Da kalli Momy ta bishi wanda yafi kamada na mamaki tace "Son a kwai abinda ke damunka kenan tunda naji kace Zainab ta haɗa maka ouds meyake damunka?

Ajiyar zuciya ya ɗan sauke kaɗan sannan yaja ɗaya daga cikin kujerun dake zagaye da daining ɗin yace "Mom ba wani babban al'amari bane fa. Haɗe rai tayi tana kallonsa da sauri ya janye idinsa ya kalli Abie yace "pls Abie kace mom ta bar yimin irin wannan kallon don Allah wllh xan faɗa muku komai.

Murmushi abie yayi me cikeda dattako sannan yace "to naji gaya mana meke faruwa. Ɗan jim yayi sannan ya shiga sanar da Abie kaf abinda ya faru a tsakaninsa da Fadilah ba tareda ya rage komai ba. Ƙura masa ido mom tayi bakinta a buɗe sabida tsabar mamaki...........






Sushmah💋
[3/3, 5:35 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


*_Page :19_*

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Not Edited
____✍️nausawa tayi cikin jejin babu abinda takeyi se kuka sabida rabuwar datayi da mahaifinta, jefa ƙafarta kawai takeyi batareda tasan inda take jefata ba ga dare daya farayi, babu komai cikin dajin face kukan gyare da kuma na tsintsaye kasancewarta Bafulatanar Daji hakan besa taji tsoro ba becouse dama a cikin dabbobin ta tashi kuma take rayuwa so babu wani baƙon Abu a gareta , babbn abinda zuciyarta ta yarda dashi shine there's nothing can happen to her because her father prayer is still by her side, da wannan tunanin kawai tke tafe zuciyarta nayi mata zafi.

Ta sani sarai cewar ita kaɗaice ta ragewa mahaifinta a halin yanzu haka kuma ƙaunar dayake mata me girma ce, batajin ze iya sadaukar da wannan babbar ƙaunar dayake mata a banza becouse ruwa baya tsami banza inji ƴan magana. Dole yanada dalilinsa me ƙarfin gaske da har yasa yashi rabuwa da ita a wannan lokacin. Ƙirjinta ne ya amsa da sauri lokaci guda kuma ta zuɓe akan gwiwoyinta tareda ɗora hannunta na dama a saitin zuciyarta, rarrafawa tayi tareda gyara zaman wannna jakar saƙin da moddibo ya rataya mata a kafaɗarta batareda ta bari jakar ta faɗi ba, a haka ta jingina bayanta da wata ƙatuwar bishiya tana maida numfashi.

*_ABIJA NIGERIA_*

yau tunda sanyi safiya Muzaffar ya gama shirinsa cikin wata Ash ɗin Korean suits iya gwiwa kasancewar garin da ɗan sanyi sosai, tsaye yake jikin makeken Dressing mirror ɗin dake manne jikin bangon ɗakin yana gyara zaman agogon rolex ɗin dake hannunsa, ƙurawa kansa idanu yayi kamar meson gano wani abu a tattareda kansa, lumshe idanunsa yayi sannan ya buɗe wanda hakan yayi daidai da saukar idanunsa kan tabon ciwon da lallausan gashin kansa ya fara rufewa, hanunsa yakai gurin ya janye lumsasshen gashin kansa yana kallon tabon lokaci guda ya dafe kansa yace "ya Rabbi!!

Juyawa yayi da sauri ya fita daga bedroom ɗin nasa zuwa falo, koda ya fito falon ma tsayawa yayi cak becouse ya kasa tuna actual abinda ya fito dashi daga ɗakin, zibewa yayi akan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun royal chairs ɗin sukayiwa falon ƙawanya.

Wayarsa ce ta ɗauki ruri yana dubawa yaga sunan Abie yana yawo akan screen na wayar, ajiyar zuciya ya sauke meɗan nauyi sannan ya answer call ɗin Abie yace "son gobe ne fa meeting ɗin daza'a gabatar a India ya kamata ka fara shiri akan tafiya zuwa gobe da yardan ubangiji lallai ya kamata ace kana guri za'ayi komai becouse hajiya Aisha she's not feeling fine.

"insha Allah zanyi ƙoƙarin yin hakan Abie and then you should send me her number so that na kirata na dubata. "Ok son i will send it for you. Abie ya faɗi hakan yayinda yake katse kiran

Ajiye wayar shima muzaffar yayi haka kawai seya samu kansa dajin wani baƙon yanayi wanda ya kasa misaltashi, ajiyar zuciya ya sauke a karo na biyu a lokacin da Babban Amininsa Edress Adam ya faɗo masa a rai, wayar dake gefansa ya zaro lokaci guda kuma ya fara ƙoƙarin lalibo number ɗin Edrees ɗin tareda kira, harya katse amma Edress sam be ɗaga ba har seda ya sake kiransa a karo na biyu sannan ya ɗauka tareda faɗin "shugaban masu kirki WhatsApp?

Tsaki muzaffar yaja kaɗan sannan yace "fine ya kk?. " I'm fine and you? Edrees ya faɗi hakan yana wani male baki kamar an masa dole. A daƙile muzaffar yace "ban sani ba ɗan renin sens you but you know what?

Edrees dake zaune a madaidaicin falonsa ɗauke da remot a hannunsa yace " how could I know bayan bkaa gayamin ba? Kaga malam forget about what I did to you pls let's talk. Muzaffar ya faɗi hakan yana gyara zamansa akan sofa ɗin dayakd zaune.

naji and I don't want to talk to you right now because you baka neman mutum se matsalanka ya taso, don haka yanzu ni kuma banida time ɗinka malm idan ka matsu da magana dani seka jirani har ranar sazan dawo Abuja becouse I'm not in Abuja yanzu. Jan numfashi Muzaffar yayi sannan yay murmushi yace "ok ba damuwa nikam gibr zan wuce india maybe next time. Ya faɗa yana katse kiran da murmushi sosai a saman face ɗinshi.

zaiynab ce ta shigo falon sanye jikin doguwan riga milk colour ta yafa mayafin bisa kanta tace "Hayatie kazo inji Mom da alama you have a visitor. Ɗan buɗa lumsassun idanunsa yayi sosai yace "who? Zainab na dariya tace "uhmmmm i think is the IG Doughter. Taɓe baki yayi yace "kuma se akace miki wurina tazo ko? Da sauri Zainab tace "sure becouse tana zuwa kaikaɗai ta tambaya kuma senake gankn kam......."its ok Qurrah tell her that bana nan na fita kinji. Muzaffar ya katseta ta hanyar faɗar hakan.

fita zainab tayi tana dariya a maine parlour ɗin ta samu Hajar Abdullah suna ɗan taɓa hira da Mom tace "yace na gaya miki ki sameshi a part ɗinsa he's to busy for doing something. Murmushi Hajar tayi wanda ya ƙara mata kyau sannan ta niƙe ta nufi ɓangaren muzaffar ɗin, a nitse ta murɗa handile na ƙofar falon tareda sallama ta shiga ciki wanda hakan yayi daidai da miƙewarsa yana buɗe boturan gaban Korean suits ɗin dake jikinsa, juyowa yayi yana kallon bakin ƙofar take ya tsaya cak yana kallonta with surprise on his handsome face. Tunanin daya fara zuwa masa kai shine taya akai yarinyar nan tasan hanyar part ɗinshi?

Takowa ta farayi a hankali harta iso tsakiyar falon da murmushi akan fuskarta tace " fatan na sameka lfy? Ɗan jim yayi yana kallonta sannan yace "fine and you?

murmushi kawai tayi tace "fine kwana biyu. Ta faɗa tana ƙoƙarin zama da sauri ya dakatar da ita yace "no base kin zauna ba don fita zanyi inada aiki a office. Ya faɗi hakan yana sauya yanayin fuskarsa zuwa wani yanayi na daban. Kamar zatayi kuka tace "muzaffar meye laifina don kawai inason ka? Shin koda so ɗaya ka taɓa tunani akan cewar yanakeji a gameda kai?

Ajiyar zuciya ta sauke kaɗan yayinda idanunta suka ciko da ƙwalla tace "bazanga laifinka ba kokaɗan tunda har tsarinka ne a haka na rashin bawa mace damarta acikin Rayuwarka amma inaso ka tunada Abu guda ɗaya cewar, duk mutumin daya nuna maka kulawa a rayuwa kuma har ya iya sadaukar da lokacinsa a kanka dukdan ya samu kusanci dakai tofa wannan mutumin ba abin yarwa bane balle har ka jinginar dashi kimanin tsahon lokaci ba tareda ka tuna dashi ba.......... All i know is I love you Zafar Abdulwahab!!!

Ƙirjinsa ne ya buga da ƙarfi a lokacin da kalamanta na ƙarshe suka sauka a cikin kunnuwansa, lokaci guda ya dafe kansa da hannayensa duka wani irin baƙon yanayi ne ya samu gurbi da matsuguni a cikin zuciyarsa zama yayi jagwab akan kujera yana sauke numfashi, A hankali siraran laɓɓansa suka motsa cikin Husky voice ɗinsa yace "Im so sorry Fulani girl ban kasance me cika alƙawari a gareki ba i'm sorry for what I did to you my dearest Fulani's girl insha Allah I wll be back for you just for you soon!!

Ƙura masa ido Hajar tayi tana kallonsa hawaye cike tab da idanunta tace "who is that Fulani girl pls I want to know something about her who is she? Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta lokaci guda kuma ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa har ya buɗe ya shike Hajar nabinsa da kallo tana me tausayin kanta akan son mutumin da bata taɓa samun kulawa daga gareshiba koda so ɗaya.






*_Thanks for the love and support sisters about this novel BAFULATANA ❤️_*


comment
nd
share

Sushmah💋
[3/3, 5:35 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


*_Page :18_*


*_WRITING BY: CHUBAƊO_*


___✍️Daga irin kallon da momy take masa Abie ya Fahimci irin zallar mamakin dake kwance a saman fuskarta, a fusace momy ta kalleshi tace "amma kaidai wllh anyi sakarai tunda har ka barta baka karya mata ƙafafu ba, ni wllh Abie lamarin yarinyar nan ya fara ɗagamin hankali musamman ma ɗabi'unta, wllh da ace ba'a gida na haifeta ba tsaf zance canzamin ita akai wannan wace irin jarrabar rayuwace ne?

Dakatar da ita Abie yayi ta hanyar ɗaga mata hannu yace "look malama karki ɓatamin zuriya ta hanyar jifan ɗiyata da miyagun maganganu a madadin kiyi mata Addu'ah, karfa ki manta fushin iyaye tareda kalamansu akansu yanada matiƙar kaifi arayuwar ƴaƴasu don haka karki sake furta komai akanta muddin ba alkhairi bane. Insha Allah komai zeyi daidai watarana zata canza halinta daga baƙi xuwa maikyau

Jiki a mace mom ta miƙe ta nufi upstairs ɗakin Fadilah ranta amatiƙar ɓace tura ƙofar tayi tareda tsayawa a bakin ƙofar tana bin kowace kusurwa dake ɗakin da kallo.

Zaune ta hangeta ta haɗe kai da gwiwa zaune dirshen kan makeken lallausan kafet ɗin dake ɗakin fuskarta duk ta caɓe da hawaye, ƙarasawa mom tayi tana binta da wani ɗan iskan kallo wanda yasa hanjin cikin Fadilah motsawa, wani sabon marin mom ta ɗauketa dashi wanda yasa har seda kanta ya bugu

Please Login or Register in order to submit comment