Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mugun qarfi loƙaci guda kuma ta sulale qasa jiɓirrrr kamar zubewar gini............












Chubaɗo ✍️
[3/3, 5:40 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


Page:50

*_I Dedicate this special page for you SADIYA SIDI SA'ID (SIDIYA the writer of GIDAN MISBAHU) na rantse da Allah tukuicin Qaunar da kikemin kyautar shafi guda na littafin dana sadaukar miki yayi kaɗan ya zama tukwici a garki, amma nasan Ɗan gidan gima shine ke halin girma duk inda akace akazo al'amarin ki na gado ne bana taka haye ba, na daɗe ina cin karoda mutane daban-daban a rayuwata Amma wllh ban taɓa karo da wadda ta qaunace ni bisa gaskiya da Amana kamar ke ba. I'm so proud of you malamar FARSAFA kokuma in kiraki da kwalba uwar Alkhairi Don bazance Uwar sharri ba 😂_*


*_MASU YIMIN ADDU'AR ALKHAIRI AKAN EXAM ƊIN DANAKE GABATARWA ALLAH UBANGIJI YA SAKA DA ALKHAIRI KUMA YABAR ZUMUNCI❤️_*

___✍️Sulalewar datayi zuwa qasa ne ya bawa hannunta damar danna kiran number Zainab ba tareda tasan tayi hakan ba sabida tsabar tashin han kalin data samu kanta a ciki, daga ɓangaren zainab murmushin qarfin hali ta saki kana tace "Ummien mu!!

Jin sunan data ambata ne yasa Muzaffar dake kwance bisa cinyar mom ya kaleta da idanunsa waƴanda suka canza launi sabida halinda zuciyarsa ke ciki ba tareda ya iya cewa komai ba ya miqa mata hannu alamar ta bashi wayar, ba musu ta zainab ta miqa masa ya karɓa tareda kara wayar a gefan kunnensa yace " Ummiey na!

Wani irin bugawa Qirjinta yayi da qarfin gaske a lokacin data tsinkayi amon muryarsa ta doki dodon kunnenta.

Wani irin zaro ido tayi se kawai ta saki wani irin kuka daga qasan maqoshinta tareda sanya hannunta ɗaya ta rufe bakinta gam dashi, tabbas tasan tayi kewar muryarsa kwatankwacin yanda zuciyarta ke bugawa a ko wace rama, haqiqa yau ta gama tabbatarwa da kanta cewar numfashinta gabaɗayan sa yana fita ne da sirkin ɗigon kewar muzaffar me tsananin gaske a cikinsa, haka kuma batajin cewar zata iya ɗauke kanta daga barin tunaninsa koda kuwa ace badashi zata rayuwa ba a nan gaba!!!

Ajiyar zuciya muzaffar yaɗan sauke sannan yayi murmushi mara sauti yace "Ummie kada ki damu wllh ba wani serious ciwo bane kawai rikicin Qurra ne so ki gama abinda kikeyi a nitse kafin ki dawo. Ya faɗa yana katse kiran ba tareda yaji sautin kukan nata ba ko kaɗan

Miqewa tayi jikinta a mace ta kaiwa Ummie wayarta sannan ta fito ta koma ɗaki ta kwanta sabida wani irim juya mata da kanta keyi ta wani ɓangaren kuma ji take kamar zuciyarta zata faso qirjinta ta fito.

*********

A kwana a tashi babu wuya a gurin Allah kamar yanda moddibo yayi alqawari hakan ne kuwa ya kasance, don haka tun ana gobe ɗaurin Auren Rabe da Bamanga Edyan da mom ɗinsa da kuma zeeyadah suka iso garin, tunda suka yanko hanyar Rugar zeeyadah da Mom suka cika da ɗumbin mamakin yanda jama'ar garin suke Rayuwa ba tareda fargaba ko tsoro ba, lallai bahaushe yayi gaskiya dayace "Allah ɗaya gari banban. Dukda kasancewar mom Edyan cikakkiyar Bafulatar yolo hakan be hanata shiga mamakin irin yanayin dajin da Raben ta fito ba, A haka motarsu ta iso tayi parking a gaban gidan still suna qara jinjina lamarin a ransu , Suna tsayawa ba jimawa sega motar su Abie ma ta iso tareda Driver ɗinsa da kuma wasu jibga-jibgan haɗaɗɗun jib baqaqe wuluk se baza qyallin sabunta suke suna take masa baya, sannan suka fito daga cikin motocin duk a lokaci guda.

Da sakin fuska gamida girmamawa Edyan ya isa ga Abie tareda rissinawa ya gaisheshi, fara'ar dake kan fuskar Abie ce ta qaru a lokacin dayaga Edyan ɗin sannan ya amsa masa da kulawa a haka suka antaya zuwa indasu Ummie ke tsaye suna jiran qarasowarsu.

Sosai ummie tayi farin ciki da zuwan Matar C.p ɗin don har hakan ya gaza ɓoyuwa a saman kyakkyawar fuskarta, hugging ɗin zeeyadah Ummie tayi tana Murmushi tace "bansanki ba Edyan kawai na sani shima don yana zuwa gurina ne duk sanda yaje india, nan dai sukai murmushi gabaɗayan su sannan suka antaya zuwa cikin gidan inda bukkokinsu suke.

Sosai Ummie ta taka rawar gani wajen ganin ta cikawa su Mom Edyan da Zeeyadah gabansu ta kayan qwalan da maqwalashe, kafin kace me tuni har Inna Laure ta dama musu lafiyayan Fura da kuma nono wanda yaji Uban suga, sosai Zeeyadah ya buɗe cikinta tasha furar kamar bazata dena ba sabida an jima ba'a gamu ba 😂

Se bayan ta gama cika cikinta ta kalli Ummie tace "Banga Amaryar tamu ba pls where is she?

Hararar wasa Mom ta jefa mata tace "ja'ira se yanzu zaki tambayeta tunda kinci kin qoshi ko? "no wllh mom ba haka bane tunda mukazo garin nan take raina kema ai kinsan hakan. Zeeyadah ta faɗi hakan tana dariya

Edyan ne ya shigo ɗakin ɗauke da sallama hannunsa Rike da babban kwanon sha ya kalli Ummie yace "Ummie Abie yace ki qra masa Suger a ciki. Ya faɗa yana miqa mata kwanon yana murmushi

Karɓa tayi itama tana dariyar tace "hmmmmm nikam ban taɓa ganin mutum me son suger kamar Abie ba ko tsoron shan zaqi bayayi. Ta faɗa tana karɓar kwanon tareda zuba masa suger ɗin ta miqa masa ya karɓa ya fice daga ɗakin, yana fita zeeyadah ma ta miqe tabi bayansa da sauri tace "ya Edyan wai ina ne ɗakin mulaikha ne ?

Murmushi ya sakin mata tareda nuna mata bukkar sannan yay gaba abinsa, da sauri Zeeyadah ta nufi ɗakin cikeda zumuɗin ganin mulaikhanta bakinta ɗauke da sallama ta shiga

A kwance ta sameta idanunta a lumshi bisa qaramar katifarta, da sauri zeeyadah ta isa gareta tareda faɗawa jikinta tana dariya, buɗe lumsassun idanunta Rabe tayi waƴanda sukai mata masifar nauyi akan zeeyada lokaci guda kuma ta miƙe zaune ta rungumeta, kukan data daɗe tana dannewa ne ya samu nasarar kufce mata don hkaa ta shiga rerawa a jikin Zeeyadan tamkar dama jira takeyi ta ganta

Ɗan buɗa idanunta Zeeyadah tayi cikeda damuwa ta zarota daga jikinta tana kallon fuskarta wadda ta jiqe da hawaye tace " meyasa kike kuka irin haka Mulaikha shin bakya tsoron kanki yazo yanayi miki ciwo? Koma dai wani abin ne yake damunki ne?

Hannunta tasa ta goge fuskarta sannan ta kama hannun zeeyadah tace "ina so naga Partner yanzu pls!

Wayar hannun zeeyadah ta karɓa da sauri ta shiga kiran Edyan, bugu ɗaya ya ɗauka tareda faɗin ya akai ? Duk a zatonsa zeeyadah ce

Bakinta na Rawa tace " i wanted to see you plssssssss!

Take qirjinsa ya wani irin buga wanda sam be shiryawa hakan ba, a hankali ya sauke ajiyar zuciya yace "ok bt where are you nw?

Zan jiraka a bayan gida wurin shanu. Rabe ta faɗi hakan a taqaice

Katse wayar yayi tareda zubawa qasan gurin idanu sannan ya miqe ya fita yabarsu Abie da moddibo sunata hira abinsu, jikisa a saluɓe haka ya isa gurin ya sameta a tsaye ta sarqe hannayenta duka biyun a qirjinta tana jiran isowarsa.

Ya jima a tsayen sannan ya buɗe baki yace "kinaso ki faɗamin wani abun ne? Hawayene suka zubo mata sannan tasa hannunta ta goge ba tareda ta kalleshi ba tace " inaso na gaya maka abinda ya kamata ace ka sani ne patner, dukda cewar kusancinka da muzaffar ya wuce akirashi da abota sedai a kira hakan da sunan ƴan'uwantaka, partner Muzaffar yanada wata budurwa a Rayuwarsa wadda ya jima yana ɓoye abinda ke ransa tsahon lokaci.

Ɗago idanunsa yayi cikeda matiqar kaɗuwa ya dubeta yace "wannan wace irin magana ce kikeyi haka Mulaikha?

Ae haka maganar take Partner amm......." toni meyasa kike zaɓi da ki gayamin wannan wannan maganar bayan kuma shida bakinsa be taɓa gayamin ba?

Hawayen daya zubo mata ta sake gogewa tace " wasu maganganun da wanda yake qaunarka kawai zaka iyayinsu Yaya Edyan, musamman akan abinda ya shafi rayuwar ka!

Ni kawai abu ɗaya na sani shine wannan Auren daza a ɗaura min a gobe muddin na Bari akayishi shine kuskure mafi girma da zan aikata a rayuwata, wllh partner banason shi kaina gaba ɗaya ya gama kullewa banaso na aikata abinda ze taɓa kimar mahaifina!!!!!!! Ta fadi hakan tana fashewa da wani irin kuka.

Kafeta kawai da idanu Edyan yayi a ranaa kuma yana aiyana wani al'amari wanda shi kansa bazece ga matsayar daya samu a ransa ba, tabbas yasani har cikin zuciyarsa yake qaunar Rabe so me tsananin gaske, to waishin ta ina ma ya kamata ya fara ne?

A hankali yake jan qafarsa harya bar kurin ba tareda ya rarrasheta ba, guri ya samu daga can nesa da gidan ya zauna har yammacin al'muru ya fara ketowa, a hankali yaji saukar hannun mutum a saman kafaɗunsa don haka ya ɗago da sauri yana kallon wanda ya dafashin.

Moddibo ne tsaye bisa kansa yana murmushi yace "ai tun ɗazu nake cigiyar ka shine Abou muzaffar yace min kanata nan wurin. Ya faɗi hakan yana zama daga gefan Edyan ɗin, shiru ne ya ratsa gurin tsahon lokaci sannan moddibo ya dubeshi yace " na rigada na gama gane wanda Rabi'atou take Qauna. Da sauri Edyan ya ɗago yana kallonsa zeyi magana moddibo ya dakatar dashi ta hanyar cewa "Ba yanzu ba tukunna zan baka damar magana amma fa har sena gama tawa tukunna.

Wanda takeso ɗin na zauna dashi a yanzu dukda cewar shiɗin be taɓa furta abinda ke zuciyarsa akanta ga kowa ba, dukda cewar yasan hakan kurkurene me girman gaske amma kuma yake qoqarin ya aikata ɗin, nariga na gama Fahimtar komai Edriss nariga na gama gane wanda Rabi'atou take Qauna har cikin Ranta,, idan harna Aurar da ita ga wanda bataso tabbas na cutar da ita mafi girman cutarwa, nasani damace ubangiji ya bani a yau wadda zan iya gyara kuskuren danake qoqarin tabkawa a baya ta hanyar turo min kai zuwa nan, koda wasa bazance Bamanga da Rabi'atou basu dace da juna ba amma to ya muka iya da zannan abinda qaddara tazo mana dashi?

Zuciyata tana gayamin cewar kaine mutumin dayafi dacewa daya mallaki Rabi'atou. Da sauri Edyan ya kama hannun moddibo lokaci guda kuma ya maida kallonsa ga fuskarsa yace "aa baba sam be kamata kayi haka ba, kamata yayi ka zauna da Rabi'atou kaji ra'ayinta akan Aurensu da bamanga muddin ta nuna batason haka toseka sake bata wata damar a karo na biyu inyaso seta gaya maka waye zaɓin ranta da bakinta!!

Da hka hirar tasu ta dasa Aya.

Ɓangaren su Mom Edyan da Ummie kuwa sosai suka kacame da hidimar dafe-dafe da kuma sarrafa wasu abubuwan daza'a gabatar na al'adah, sosai mata suka cika gidan anata shewa da kuma aikace-aikace kafin kuma gari ya waye a shaida ɗaurin Aure. Bayan sallar Isha su Abie da Edyan da kuma gurds ɗinsa suka yada zango a farfajiyar qofar gidan kafin lokacin kwanciya yayi, miƙewa moddibo yayi ya nufi bukkar Rabe da sallama ɗauke a bakinsa ya ɗaga labulan dake saqale jikin bukkar, zaune suke ita da zeeyadah tanata faman bata labarin school Rabe nata murmushi a haka ya qasa shigowa ɗakin, cikeda girmamawa Zeeyadah ta gaisheshi sannan ta miqe a nitse tabar ɗakin don ko ba'a faɗa mata ba tasan magana zayi da ita wadda take buqatar sirri.

Zeeyadah na fita ya nemi guri ya zauna daga ɗan gefanta kaɗan yana kallonta kimanin wasu mintuna Sannan yay ajiyar numfashi yace" idan kinada matsala da wannan auren sam karki ɓoye min kawai ki sanar dani insha Allah zaki sameni a matsayin uba me adalci a gareki.

Matsowa tayi tareda kwantar da kanta bisa kafaɗunsa tace " aa baba sam banida matsala da Auren bamanga sabida ya cancanci mallakata tsahon lokaci, don haka kawai a ɗaura wllh har cikin raina na amince da hakan!!!!

Ta faɗa tana kallonsa tareda qoqarin mayar da kwallar dake qoqarin zubo mata, ko kaɗan bataso ta nuna gazawarta kodan sabida ta tsirar da kimar mahaifinta a idanun jama'ar garinsu, badan haka ba tabbas bataga dalilin dazesa tabar zaɓin ranta ta ɗau wani ba.

Duk yanda moddibo yaso ya gano abinda take ɓoyewa a ranta ta hanyar kallon idanunta sam ya kasa gano komai dole ya tabbatarwa da kansa cewar lallai har cikin ranta takeson Auren Bamangan. Ƙarfe tara na dare dedai Kakar Rabe wadda ta haifi mahaifiyarta sukazo daga Yolah tareda qannen mahaifiyarta guda biyu, sosai sukai farin cikin da zuwan nasu misamman ma Rabe wadda har hakan ya gaza ɓoyuwa a tareda ita a haka dai gidan ya dinga kacamewa da abikanan Arziqi tamkar a lokaci za'a ɗaura mata Auren.

****

Washe gari tunda sanyin safiya jama'ar Rugar Arɗo suka gama hallara a bakin qofar gidan moddibo wanda aka shimfiɗa manyan tabarmin kaba fa farfajiyar, Abie ne ya fito sanye cikin wata rantsatsiyar gizna fara fat da ita wadda taji uban aiki irina manyan masu kuɗin dake matiqar jida kansu, kallo ɗaya zakayiwa Abie ka fahimci zallar kar da suke da muzaffar tamkar Abie yayi kaki, bayansa kuma moddibo ne shima sanye cikin wata hamshaqiyar gizna farar tas da ita wadda tabawa kyawunsa damar fitowa abinka da bafulatanin Asali wanda yay gadon kyau ba taka haye ba lol😂

A haka suka fito suka zazzauna bisa tabarmin inda Jama'ar ke zaune, can na hangi Oga Edyan ya ɗau harami shima cikin wata shadda irinta mutanam sinigal brown wadda tayi masifar masa kyau, sedai fuskarsa sam babu yalwar murmushi kamar yanda ya saba. Nan moddibo ya shiga gaisawa da abokan arziqi har ya kammala amma shiru babu labarin Isowar iyayen Ango, tun anasa ran isowarsu har mutane suka fara cire rai da zuwan nasu nafa aka fara tsegumi qana nan maganganu suka fara tashi, can kamar daga sama aka jiyo muryar Hashimu Maroqi yana faɗin "Sanarwa daga bakin uban Ango Jauro ibrahimu Bawuro cewar sun janyen batun Auren Ɗansu Bamaga da kuma Rabi'atou ɗiyaga Moddibo ɗan lamidon Arɗo bisa wani babban dalili da basu baiyana ba, fatan malam moddibo ze gafarce su.

Take gaban moddibo yay wata irin faɗuwa lokaci guda kuma idanunsa suka ciko da qwallar baqin ciki, yanzu shikenan Bamanga ya gama yiwa Rayuwar ɗiyarsa illah sabida a tsarin al'adarsu muddin wata matsala ta gifta a ranar ɗaurin Aurenki har takai ga an fasa ɗaura auren tofa har Abada bazaki taɓa yin aure ba a haka zaki zauna har mutuwarki ta riskeki.

Kamar daga sama Ya tsikayi muryar Edyan a saman kunnensa yana faɗin , dama can Mulaikha ba sa'ar Aurensa bace don haka ka koma ka sanar da qananan mutanen da Suka turoka cewar a yau base anjima ba za'a shaida ɗaurin Auren Rabi'atou da wanda ya dace da ita.

Edyan ya faɗi hakan yana me zaro bandir ɗin ƴam dubu-dubu Guda biyu daga aljihunsa ya ajiye a gaban moddibo yace "Baba ina me nemawa kaina Aurenta idan har zaka bani, lokaci guda kuma Abie ya matso dabda moddibo yace "ni nan zan zame masa wakili daze karɓa masa Aurnta, cin qanqanin lokaci moddibo ya ɗago manyan idanunsa yana kallon Abie cikin wani irin yanayi wanda yafi kamada na zallar kaɗuwa yace"................







Sushmah ✍️
[3/3, 5:40 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


Page :51


*_WRITING BY: CHUBAƊO_*


____✍️"taya hakan zata kasance kuma Abdulwahab? Murmushi abie ya saki irin nasu na dattijawa yace "karka damu Moddibo sam be kamata mutanan da aka tara sabida ɗaurin Auren nan a bari su watse haka nan ba, ɗan jim yayi kaɗan sannan ya maida kallonsa ga Edyan Yay masa murmushi se kuma ya kalli moddibo da malam iro wanda sukai shiru suna nazarin abin a ransu, cikin mintunan da bazasu gaza 5 ba jama'ar dake gurin suka shaiɗa ɗaurin Aurn Rabe da wani daban saɓanin Bamanga wanda iyayensa suka janye Auren sabida wani dalili nasu na daban wanda har yanzu basu firta ba.

Nan da nan aka shiga raba Goron ɗaurin Aure da kuma manyan alawori masu tsadar gaske kamar dama an shiryawa abin, zanso team Edyan kuga yanda ango Edris yake washw baki tamkar wanda akaiwa bisharada gidan Aljanna, a haka taro ya watse kowa yana sambarka tun a yammacin Ranar iyayen Amarya da kuma gwaggwanninta sukai shiga kimtsa amarya sabida gabatar da bikin al'ada kamar yanda suka saba, sedai duk yanda Edyan yaso ya haɗu da ita sam abin ya gagara sabida an riga an keɓanceta za'a gabatar mata da abinda suke kira da biddom, idan akace biddom ana nufin wankan amaryar da fulanin daji keyiwar ɗiyarsu ne da zallar madarar shanu gamida wani sinadari na musamman wanda ya kasance sirrin su ne musamman ta ɓangaren mallakar miji da kuma inganta rayuwar Aurataiyarsu.

A lokacin dasu Ummie da mom sukaji da wanda aka ɗaura Auren sosai abin ya girgizasu musamman ma Ummie, ita kuwa mom Edyan sosai hakan yayi mata daɗi tamkar dama abinda take burin ya kasance ɗin kenan, a haka suka gabatar da bikin al'adar jikin Ummie a matiqar sanyaye don harga Allah tana matiqar tausayawa muzaffar Ɗinta, to amma yata iya tunda haka zanan qaddara yazo masa dashi.


A gurguje pls

Bayan an kammala bikin al'adar sosai Zeeyadah ta kaɗu da yanayin da Rabe ke ciki sabida zallar damuwar dake cinta a ranta, gaba ɗaya duk ta gama ramewa a tsaye amma sabida tsabar qarfin hali irin nata taqi bari wani yasan halinda zuciyarta take ciki, babban abinda ke qara ɗaga mata hankali shine ta ina zata fara rayuwar da Bamanga a matsayin mijin Aurenta? Sabida harga Allah bata san abinda ke faruwa da lamarin Aurenta ba, Yafendunta Bintu ce ta shigo ɗakin da aka gama kafata da murmushi akan fuskarta tace " Baddo.

Kuka Rabe ta sakin mata lokaci guda kuma ta faɗa jikinta tana rerawa, kaf cikinsu babu wanda yay yunqurin hanata kokuma rarrashinta badan komai ba sedan ta samu peace of mind, seda tai me isarta sannan tasa tafukan hannunta tana share hawayen kamar ba itace ta gama gurzar kuka a jikin Yafendu Bintu ba, Inna Laure ce ta shigo ɗakin tana jan qafa da qyar hannunta ɗauke da wata qaramar qwarya wadda akai mata jiqo na musamman ta miƙawa yafendu Binto tace " maza ki bata ta shanye zuwa anjima Ammi Ruqatu zata kawo ɗayan se'a jiqa kafin wayewar garin gobe masu ɗaukar Amarya suzo.

Murmushin Yafendu Bintu tayi tace "Ae lallai Laure kin dage sekin haɗa ƴar nan taki Allah dai ya saka miki da alkhairi bisa ɗawainiyar da kikayi, Allah kuma ya rabaki da cikin jikinki lfy.

Kasa magana Inna laure tayi sabida wata qwalla data taso ta kwanta a saman qwayar idaninta, nan da nan ciwon dake cinta a ranta ya dawo mata sabo fill a lokacin data tuna cikin su waye a jikinta , da hanzari ta juya ta fice tana me zubarda kwallar baƙin ciki da nadama.

A haka dai abubuwa suka dunga tafiya masu daɗi da marasa daɗi Har garin Allah ya waye Kusan a tare su mom suka fara shirin komawa Abuja, gabaɗaya bakin Edyan ya gaza rufuwa sabidaTarin farin cikin Da yake ciki

Qarfe shidan safe daidai Aka kimtsata cikin wani Blue ɗin saqi wanda yay masifar karɓar jikinta, gabaɗaya fuskarta an zane mata ita da wani farin fenti gamida ratsin yallow, kallo ɗaya zakai mata ka tabbatarwa da kanka cewar kaka cikakkiyar Asalin BAFULATANAR DAJI wadda ta amsa sunanta ƴar fillon gaske babu sirki. Ɗakin Moddibo aka fara kaita, nan ya shiga yi mata nasiha me ratsa jiki wadda a zuciyarta takejinta tamkar nasihar bankwana yake mata, sosai take kuka daga cikin mayafin saqin da aka rufe mata kanta dashi, ba zato ba tsammani ta miqe ta isa ga mahaifin nata ta rungumeshi tamau tana gurzar kuka kamar bazata dena ba. Daqyar suka ɓanɓareta suka fita da ita zuwa bukkar inna Laure, nan ma ba qaramin kuka Rabe tayi ba hakama Ɓangaren Lauren Itama, nan dai laure ta roqi yafiyar mahainiyar Allah Rabe, duk yanda taso ta miqe ta isa gareta kasawa tayi sabida nauyin cikin dake jikinta, har gabanta Rabe ta isa ta durqusa daidai yanda zata iya rungumarta tace "dukda cewar kin raine ni bada soyayya ba wllh kodedai da rana ɗaya bantaɓa jin cewar na tsaneki ba, komai ya fito daga bakinki akaina idan kika furtashi ban taɓa sashi a raina ba balle harya dameni sabida nasan komai na duniya yanada limit, don haka kisa a ranki cewar kema matsayin uwa kike a gareni na yafe Miki har Abadah!!!!!!

Ta faɗa tana fashewa da kuka.


Gaba ɗaya Laure ta kasa magana sabida kukan datakeyi a haka aka fita da Rabe zuwaga kakarta wato Mahaifiyar Babar ta, nan ma nasiha sosai Gwaggoji tayi mata me ratsa jiki akan Rayuwar duniya da kuma mutanan dazatai Rayuwa dasu waƴanda suka kasance a kwai banbanci me tarin yawa a ɗabi'unsu da kuma irin nata, nan dai Rabe ta Fahimci Auren waye a kanta.

Ko kaɗan batai baqin ciki dajin wanda ta Aura ba abu ɗaya kawai ta sani shine komai Muqaddari ne daga Allah, haka kuma ba komai muke so a rayuwa muke samu ba. Duk inda miji na gari me tattalin matarsa yakai wllh tasan Edyan ya wuce haka shiyasa bazata taɓa baƙin ciki da Aurensa ba indai har ta cika ƴar Halak kuma wadda tasan halacci.

Duk irin sabon dake tsakanin moddibo da ɗiyarsa sam hakan besa ya zubar da hawaye ba don haka har suka fito da Abie idanunsa rass kamar baya kewarta, hannun Abie ya kama yana kallon tsakiyar idanunsa yace "zan roqeka wata alfarma Alhaji tareda yaqini da sanya ran cewar zakayi min ita.

Da kulawa Abie ke kallonsa yace "kafi qarfin haka a gurina wllh kawai ka faɗi me kakeso wllh zanyi maka shi.

Murmushi moddibo yayi wanda ya baiyana dattijantakarsa yace "so nake da zarar kun isa inda zakuje don Allah karkubar Rabi'atou ta kwana a wani gida wanda bana mijinta ba.

Da kulawa Abie yace "insha Allah zan cika maka wannan alqawari naka kuma nida kaina zan kaita har ɗakinta ba tareda na fari an tsaya gabatar da wata bidi'a ba.


A haka ummie ta fito jiki a mace sukai sallama da kowa dake gurin suka shiga motocinsu, a wannan halin babu abinda Ummie ke tunani kamar gudan jinin ɗanta Muzaffar wanda tasan wajibi ne ya shiga gagarumin tashin hankali idan har ya samu wannan labarin marar daɗin ji a kunne.

A haka suka isah Airport, bayan zuwansu da minti 15 jirginsu ya ɗaga zuwa birnin taraiya, jirginsu na sauka iyalan C.p suka tarar da manyan motoci na jiran isowarsu, nan dai sukai Sallama da Mom Edyan da Ummie kowa yayta kansa akan cewar insha Allah qarfe 4pm zasuzo ɗaukar amaryarsu. Sam ba haka Edyan yaso ba yaso ace yay gabada matarsa amma kuma sam besamu damar hakan ba.


*****

Ɓangaren Muzaffar kuwa tun bayan lafawar da ciwon da kansa ke masa ya koma bakin aikinsa, duk irn zafinda zuciyarsa keyi sam hakan besa ya baiyanawa Mom da Fadilah Damuwarsa ba, Baba Hajara ce kawai tasan Halinda yake ciki sabida irin sonda take masa, dukda kasancewarta me aiki a gidansu shi sam ba'a hakan yake kallonta ba kallon kakarsa yake mata kuma wadda yake Qauna.


Zaune yake a Office se faman danna system yake amma sam hankalinsa baya taredashi, haka kawai yakejin gabansa na faɗuwa wanda gabaɗaya ya rasa dalilin hakan, a haka ya mike jikinsa a mukun mace yabar office ɗin zuwa gida.


Ɓan garen Edyan kuwa yana zuwa gida wani sabon uban wanka ya ɗauka cikin wata

Please Login or Register in order to submit comment