Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

      *******

Ɓangaren Edyan da abokanan tafiyarsa kowa ya isa gida lfy  haka kuma kowa da abinda zuciyarsa ke tufka masa ta ɓangaren abinda ke wakana a zukatansu,  lokacin  da Edyan ya isa gida Direct part ɗinsa ya nufa tareda faɗawa toilet ya sakarwa kansa ruwa me zafin gaske sabida gajiyar dake taredashi, ya jima a toilet ɗin sannan ya ɗaura alwala ya fito ɗaure da wani babban towel wanda ya tsaya masa iya digadigansa,  ko mai bai shafa ba ya Buɗe tangamemiyar drower ɗinsa dake manne a jikin bangon ɗakin ya fara bin side ɗin inda qananan kayansa suke, wata riga mara nauyi ya ɗakko da wandonta  mallakin companyn Pajamas ya saka sannan ya tada sallar dake kansa, yana idarwa ko tasbihi beyi ba ya miqe ya hau kan makeken gadonsa sabida wani irin bacci dake muqurqusarsa, cikin mintuna kadan bacci mai nauyi ya ɗaukeshi.

Al'amarin Muzaffar kuwa tun bayan dawowarsu gabaɗaya zuciyarsa ta gaza samun nutsuwa sabida tarin damuwar dake kwance a qasan zuciyarsa, duk hada-hadar dayakeyi daurewa kawai yakeyi yana gabatar da wasu abubuwan don haka yay wata iri Rama wadda sedata girgiza Mommy,  dukda irin damuwar dayake ciki sam be fasa gudanar da yanayin aikinsa ba don haka nasarori kullum qara samuwa suke a sanadinsa.

Zaune yake a cikin hamshaqin office ɗinsa yana matsa na'urar laptop ɗin dake gabansa, kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci he is doing something important on his system ɗin.  Ahankali take takowa cikin takunta na isa da qasaita harta samu nasarar tura qofar glass ɗin dake office ɗin, da hanzari sectary ɗinsa ya nufota yana faɗin "I'm sorry ma'am but my  boss said he don't want to see any client karnabar kowa ya shiga senan da 1 hour. tsayawa Hajar tayi jikinta duk a mace sabida tasan halinshi sarai muddin ya faɗi abu aka saɓa tofa bashida sauqi ko kaɗan ta wannan fannin.

Makeken glass ɗin dake manne a fuskarta ta zare tareda ɗaga qafafunta ta nufi gurin da aka tanada don zaman baqi masu jiran iso idan sunzo, badan ranta yaso ba ta zaro wayarta tana wani latsawa tamkar babu abinda ke damunta. Tana nan zaune Ta hangi fadilah cikin shigar wata arniyar baqar suite with street siket se faman walwalin baqi takeyi, kanta kuma ɗaure cikin rolling irin na mutanna qasar misrah a nitse take takowa cikeda nutsuwa tamkar ba stubborn Fadilah ɗinnan ba  me shigen nuna isa da kuma wulaqanci ba, Direct office ɗin ta shige hannunta ɗauke da wani file ko lura da Hajar dake zaune gurin batayi ba.

Ta jima a ciki sannan suka fito taredashi hannunsa bisa kafaɗar Fadeelah ɗin suna dariya, still tayi tana kallonsu ba tareda sun lura da ita ba fadilah ne ta kalleta lokaci guda kuma ta zaro ido tace "oh Hajar long time no see  ya kk?   Ta faɗa tareda matsawa ga Hajar ɗin wadda ta kafe Muzaffar da wani mayen kallo kamar zata cinyesa ɗanye, wani irin masifan kyau taga yayi mata a cikin Royal blue ɗin Korean suit ɗin dake jikinsa wadda tai masifan karɓar jikinsa.  A dabuce ta saki murmushi Ba tareda ta iya furtama Fadilah dake tsaye komai ba.

Kallonsa Fadilah tayi tace "Yaya lemme back to my office I have a client that are still waiting for me.  Ta faɗa tareda barin gurin tana dariyar yanda taga ya wani sauya fuska duk sabida ganin chiwebegum ɗin nasa kamar yanda take kiran Hajar ɗin dashi.

Kamar zatayi kuka ta qaraso gurin da yake tsaye ta kafeshi da mayun idanunta tana kallonshi tace "kayi haquri my ster kawai bazan iya zaman jiranka har zuwa lokacin da kasawa ranka zakazo gidan mu bane,  kwanaki can da daɗewa kace  min zakazo gida muyi magana amma kum......... Kuka ta sakin masa sabida yanda takjin ciwon abin a ranta.

Ɗan wara manyan idanunta yayi sabida yanda ta mugun bashi mamaki, hannunsa yasa ya dafe kansa tareda firzar da wani irin iska mai zafi daga bakinsa yace "look Hajar I don't want any trouble plz oya tashi muje badai rashin zuwa gidanku bane kawai matsalar ?  To muje .   Ya faɗa yana nuna mata hanya

Takawa ta farayi tana share hawayen dake sakko mata suka fito farfajiyan companyn, kallonsa tayi zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyar cewa"ki shiga motarki zan biki a baya banson problem, juyawa tayi da sauri ta shiga motan ta sannan shima ya shiga nasa guards ɗinsa na take masa baya a haka har suka isa gidansu Hajar Ɗin ya ɓalle murfin motar dayake ciki ya kalli Solomon yace "ku jirani a nan base kun shigo ciki ba  nan da 5minute zan fito insha Allah.

Be jira cewarsu ba ya tura qofar get ɗin ya shiga cikin gidan, a hankali yake takawa cikin takunsa na isa da jinkai harya isa maine qofar da zata sadashi da pard ɗin Mom Edyan  ba tareda ya tsaya ga hajar wadda ta ƙwafe a guiding tana jiran ya qaraso susha hirar love ba.

A nitse ya shiga falon da sallama tareda fara qoqarin zare rufaffan takalmin fatar dake qafarsa, dakatar dashi Mom tayi ta hanyar cewa bar takalmin ka ka shigo dashi son. Ta faɗa tareda yalwata murmushin fuskarta

Cikeda kunya ya durqusa har qasa yace "mom ina yini?       "lfy lau muzaffar yau kaine a gidan namu? "ae wllh mom nine dama nazo ne nayi muku godiya bisa ɗawainiyar da kukayi da Rabi'atou.   Haɗe rai mom tayi ta sake kallonsa tace "banda abinka muzaffar Ai rabi'atou ƴa take a gurina koda ace babu alaqar jini a tsakaninka da ita, haka kuma bamuyi mata don ka gode mana ba komai mukayi mata wllh munyi mata shine don Allah badan neman jiran saka mako ba.

Shafa gefan kansa yay cikeɗa da kunya sannan yace "mom Edyan yana nan kuwa?   Ba tareda ta kalleshi ba tayi murmushi tace yana part ɗinsa be jima da dawowa daga office ba.  Zeeyadah ce ta shigo falon hannunta ɗauke da flet wanda ke ɗauke da fruite a ciki, da sakin fuska gamida girmamawa ta iso falon tana faɗin sannuda zuwa ya muzaffar  yau kaine a gidan namu?

Murmushi yayi mata wanda ya qarawa fuskarsa kyau yace "yeah.  Murmushin dake kwance kan fuskarta ta qara faɗaɗawa tace "your highly welcome.

Miqewa yayi tareda faɗin  "thank you dear  kafin yama mom sallama ya nufi part ɗin Aminin nasa Edyan, a hankali yake tafiya zuciyarsa ɗauke da wani al'amari wanda yakejin masifar nauyinsa tamkar an ɗora masa gingimemen dutse me girman gaske, ko kadan bayaso mace ta shiga tsakaninsa da Babban Amininsa shiyasa yake qoqarin ganin ya yaqi al'amarin dake ransa gameda Edyan ɗin, yana matiqar martaɓa Edyan tayanda yakejin cewar qimarsa takai ya iya sallama masa komene muddin hakan zai sanyashi farin ciki koda kuwa ace Rabi'atoun ce kuwa.

A hankali ya murɗa babbar qofar dake falon tareda kunna kai ciki, babu kowa a falon se Tv dake ta faman aiki don haka Direct ya nufi qofar bedroom ɗinsa, da sallama ɗauke a bakinsa ya tura qofar tareda sauke manyan fararen idanunsa Akan kowace kusurwa dake cikin ɗakin, sakin qofar yayi ya Still yaci gaba da takawa zuwa cikin ɗakin harya isa bakin makeken gadon dake ɗakin ya zauna yana me zubawa qofar toilet ɗin dayaji zubar ruwa idanu.

Seda ya kwashe kimanin 3minute zaune sannan Edyan ya fito sanye cikin farar jallabiya yana sauke hannun rigar zuwa qasa da alama Alwala yayi, kafeshi da ido muzaffar yayi batareda yace dashi qala ba, murmushi Edyan yayi tareda qarasowa ga aminin nasa ya zauna daga gefansa yana me qara yalwata murmushinsa yace "anya kuwa idanuna daidai suke nuna min kokuwa dai gizo kake min?  Idan har zan iya tunawa daidai rabonda mu haɗu irin haka tun a Gyambu.  Ya faɗa yana dafa kafaɗun muzaffar ɗin wanda ke kallosa har yanzu baice qala ba

Ajiyar zuciya ya sauke me nauyin gaske sannan yace "nazo ne kawai na ganka nima sabida inaji a jikina cewar Nayi Kewarka Edyan !!!    Muzaffar ya faɗi hakan yana kallon Edyan ɗin yana murmushi shima, amma kuma a ransa yana me tausayawa Edyan ɗin sabida wata shegiyar rama dayayi wanda yake da tabbacin cewar irin damuwar dake addabarsa kullum a zuciyarsa irinta ce ke addabar Aminin nasa Shima, take wani irin tausayinsa yay masa dirar mikiya a ransa.

Seda suka ɗan taɓa hira kimanin tsahon mintuna 5 sannan nuzaffar ya miqe yana murmushin qarfin hali yace "zan wuce gida zuwa anjima mayi waya ko?

Ajiyar zuciya Edyan ɗin yaɗan sauke sannan yay murmushi cikeda qarfin hali yace "ok  thank you so much for the visit.  Kallon tsaf muzaffar yay masa sannan ya dafa kafaɗunsa lokaci guda kuma ya fice daga ɗakin cikin takunsa  harya ɓace idanun Edyan na kansa a ransa yana me tausaya masa shima.

Koda ya fita direct guiding ɗin ya nufa inda yake da tabbacin cewar Hajar na gurin tana Aikin jiransa, tunda ya nufo gurin ta kafshi da idnu tamkar zata haɗiyeshi sabida so harya samu guri ya zauna still tana kallonsa,  yana zama ya sarqe qafafunsa ɗaya kan ɗaya sannan ya dubeta a karon farko a rayuwarsa yace "Hajaaaar!

Wani irin Amsawa qirjinta yayi sabida wannan shine karon farko dataji sunanta a bakinsa, wani irin farin ciki taji yana ratsa zuciyarta nan take hawayen farin ciki ya farayi mata zarya, bakinta yana rawa ta fara magana daqyar tace "haqiqa yau itace rana ta farko a rayuwata wadda tazo min da tarin alkhairai ciki kuwa harda wannan zaman da mukai da juna dakai a yanzu, wllh Muzaffar zuciyata me rauni ce indai har akan son da take maka ne na shiryawa dukkan abunda ke shirin yimin katanga dakai Koda kuwa hakan na nufin Rasa Rayuwata ne gabaɗaya!!! Don Allah ka fahimci damuwata kada ka hukuntani da abinda bazan iya ɗauka ba plssssss.

Tunda ta fara magana ya kafeta da tsimammun idanunsa waƴanda suka tashi daga launin farare suka surka da launin ja sabida tausayinta,  a hankali ya dubeta tareda sauke numfashi yace "Haqiqa na tausaya miki Hajar kuma babu shakka kin samu nasarar dasa tausayinki a zuciya ta,  nasani jarrabawar soyayya ba qaramin Abu bane haka kuma duk mutumin daya samu kansa a ciki abu ne mawuyaci ya iya samun kwanciyar hankali harse zuwa ranar da ya samu abinda ransa ke muradi, sedai dukda hakan ina me baki haquri bisa abinda bakina ze furta miki a yanzu wllh hajar a halin yanzu sam ba relationship bane a gabana I have a lot of abubuwan dake gabana wanda sam bazan iya haɗasu da soyayyah ba, koda ace ma zanyi soyayya to zuciyata tanada wadda takeso kuma take Qauna banajin cewar zan iya son wata mace kamar yanda nake sonta! Wannan dalilin yasa bazan iya amsar soyayyarki ba koda kuwa ace na Rasa daman Auren wadda zuciyar tawa takeso.

A hankali sautin kukanta ke tashi cikin wani irin yanayi na zallar tausayin kanta da makomarta tace " sonda nake maka a cikin jinina yake yawo banajin cewar haquri ze iya wadatar da zuciyata harya sa na iya cireka a raina, amma don Allah shin zaka iya sanar dani dalilin dayasa bazaka iya karɓan soyayya na ba?

Murmushi ya saki wanda ke baiyana zallar tausayawarsa gareta sam bayaso yay hurting ɗinta daqyar ya iya buɗe bakinsa yace " sabida baki dace da irin tsarin matar da zuciyata keso ba Hajar!! addinin mu ya horar damu cewar idan zamuyi aure to mu zaɓama ƴaƴan mu uwa ta gari bawai kuma ina nufin keɗin ba mace ta gari bace a'a hajar sam ba haka nake nufi ba, kawai dai bazan iya zamada matar data maida rayuwarta irinta turawa ba kamar dai yanda kike a yanzu, wllh da ace qanwarki zeeyadah ce ke sona kamar yanda kike sona tabbas zan iya Aurenta kuma na zauna da ita badan komai ba kodan sabida kyawawan halayenta......... Yana kaiwa nan ya miqe idanunta sun sauya kala sabida yanda yake tausaya mata bisa dakon soyayyarsa data daɗe tanayi tsahon lokaci.


A haka yabar gurin ko waiwayonta beyi ba. Zubewa Hajar tayi a gurin lokaci guda kuma ta saki wani irin kuka mecin rai gaamida zallar tausayin makomar rayuwarta.

Yana zuwa ya shiga mota Solomon sukaja motar sukabar harabar qofar gidan.


Tun bayan dawowarsu daga Gyambu muzaffar ya tattara lamarinta ya ajiye a gefe tareda maida dukkan hankalinsa ga aikinsa, sosai yake wata irin rama sabida yanda abin ke cinsa a rai fiyeda duk zaton mai karatu amma tsabaragen kafiya da taurin zuciya ya hanashi samarwa zuciyarsa abinda takeso. A haka rayuwa ta dinga tafiyar masa da daɗi babu daɗi still yaqi koma mata kamar yanda take mafarki a kowace wayewar garin safiya.


Kamar yanda Ummie ta sanar da Moddibo cewar zata sake dawowa bayan sati ɗaya hakan kuwa akayi, tun ana washe garin ranar dazata tafi Gyambun ta kammala shirya duk kayayyakin dazatayi musu tsaraba dashi, zaune take a tsakiyar falonta ta miƙe ƙafafunta tana duba kayayyakin da Abie ya shigo dasu wanda zatayi musu tsaraba dashi, Baba Hajara ce ta shigo falon hannunta ɗauke da wani ƙaranin bokitin roba cike taf da dambun naman kaza, inda ɗaya hannun nata kuma take ɗauke da farantin silver cike taf da kwaɗon zogale wanda yaji uban quli-quli da tumatur, fuskarta ɗauke da murmushi ta qaraso inda Ummie ke zaune ta miqa mata farantin zogalen tace "Ranki ya daɗe ga zogalen an kammala haɗawa.

Da mamaki Ummie ta ɗago tana kallon baban hajaran sannan tace "haba baba don Allah ? So nawa zan gaya miki cewar ki ɗena ɗorawa kanki hidimata tunda kema kanki ba lafiyarce ta isheki ba?

Nidai don Allah baba karki sake bawa kanki aiki da sunan zaki wahalta min don girman Allah. Ummie ta faɗi hakan yayinda take kallon baba hajarar wadda keta faman murmushi

Cikeda dattako Baba Hajara tace "haba Ranki ya daɗe ai wannan sam ba aiki bane me wahala da har zaki damu kanki don kawai nayi miki shi, don haka sam ki dena damun kanki akai ne jikina ya daɗe da warwarewa. Zatayi magana kenan Muzaffar da Fadilah sika shugo falon bakinsu ɗauke da sallama yana gaba Fadilah na binsa a baya a haka suka shigo tsakiyar falon idanunsu duk akan farantin dake gaban ummie cikeda uban zogale wanda aka baɗeshi da quli gamida tumatur me yawan gaske, zama suka sannan Fadilah ta gaida Ummie tana dariya tace "Ummie muqaddiman naku kukeyi kenan keda Baba Hajara akan aiki ko?

Da sakin fuska tace kin ganta nan wllh Fadilah kullum senayi fama da ita akan magana ɗaya dai amma taki ta bari miqewa baba hajara tayi tareda miqawa muzaffar bokitin dambun naman datayi masa don tasan yana sonsa sosai, faɗaɗa murmushinsa yayi tareda karɓan bokitin yace "kai lallai matar nan kin iya kula da mijinki yanda ya kamata. Ya faɗa yana ɗiban dambun yakai bakinsa

Dariya sukai gabaɗaya sannan Ummie ta miqe ta wuce ɗakinta, sun jima suna aiki a system tareda Fadilah se wajen dabda magrib suka gama aikin tsaɓ sannan kowa ya koma ɓangarensu.

Washe gari gabaɗayansu Ahalin gidan suka raka Ummie airport ciki kuwa harda Mom da baba Hajara da kuma zainab, har seda sukaga tashin jirginsu sannan suka koma gida ita kuma Ummie jirginsu ya nufi birnin na Yola.



******

Gyambu (taraba state)

Jirginsu na sauka wasu lafiyayyun motoci guda uku baqaqe wuluk sukazo ɗaukarta cikin qanqanin lokaci Ummie ta fito cikin shigar doguwan riga me shegen kyau, take guards ɗin suka buɗe mata motar dake tsakiya ta shiga ta zauna sannan suka ɗauki hanyar gyambu.

Sosai moddibo yay farin cikin da zuwan ummien har hakan ya gaza ɓoyuwa a kan fuskarsa, don haka ya shiga hada-hadan haɗa mata duk wasu abubuwa dayasan tana masifan sonsu tun tana qarama.

Sosai Ummie kejan Rave a jikinta don haka yarinyar ta ɗan saki jiki da ita ko babu komai ganinta na rage mata kewar Abin Qaunarta muzaffar. A haka rayuwa ta dinga tafiya kullum zuciyarta na azabtuwa da kewar zaratan mazajen datai rayuwa dasu kuma har zuciyarta ta afka a qoramar saboda su.

Sosai ummie kejin daɗin zaman garin hkaa kuma wata irin shaquwa ta musamman na qara giftawa a tsakanin Moddibo da kuma qanwar tasa, wannan dalilin yasa ta qara tabbatarwa da kanta cewar maganar bahaushe gaskiya ne dayake cewa "kowa yabar gida tofa gida ya barshi. Sosai take kula da yanayin cikin laure wanda yay masifar girma don haka ummie ta dubeta da kulawa tace " Amma laure wannan cikin naki kun taɓa zuwa Asbiti akan batun awo kuwa? Ni watansa nawa ne ma tukun na?




Jikinta a mace laure ta kalli ummie tace..........









Sushmah ✍️
[3/3, 5:40 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


Page :49


*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Banyi Editing ba🙅‍♀️

____Jikinta a mace tace "ai kinsan yanayin yanda muke rayuwa A nan Danejo don haka ban fahimci abinda kike kira da wannan sunan ba.

Murmushi kawai Ummie tayi a ranta tana taya ɗan uwan nata samun haihuwa a karona biyu, addu'arta ɗaya ce Allah yasa Laure ta haifa masa zaratan maza guda Biyu kodan ƴaƴansu su samu yawaitar ƴan uwa ba kamarsu ba da suka kasance su uku rak a gaban iyayensu. A haka moddibo ya shigo gidan ya samesu fuskarsa ɗauke da murmushi yaja ɗaya daga cikin kujerar tsugunon dake gefan ummie ya zauna hannunsa dauke da baƙar leda meɗan girma kaɗan Gamida qatuwar qwarya wadda aka rufeta faifai.

Da kulawa Ummie ta dubeshi cikin harshen fulatanci tace "sannuda isowa hamma.

Murmushin dake kwance a saman fuskarsa ya qara yalwatawa ya dubeta yace " yauwa Danejo maza tashi ki ɗakko min ƙwarya kizo mu kasa wannan goron ɗaurin Auren. Bakinta sake ta dubeshi fuskarta ɗaukeda mamaki tace "Goron ɗaurin Aure kuma Hamma?

Bece mata qala ba illah Ajiye qwaryar dake hannunsa da yayi wadda ke ɗauke da farin saqi tass a cikinta gamida mayafinsa se kuma takalmin roba guda biyu a gaban Ummie kana ya sauke ajiyar zuciya yace "Danejo ga kaYan tsaida maganar Auren Rabi'atou nan iyayen BAMANGA sun kawo yanzunan.

Kafeshi da idanu Ummie tayi gabanta na dukan tara-tara, abu ɗaya ne ke dabaibaye da zuciyarta shine tausayin Muzaffar wanda tasan ba lallai bane ya iya jure rashin Rabe a taredashi ba. Amma kuma a zahiri se Ummie tayi murmushin irin na ɓoye damuwar nan sannan tace "masha Allah ubangiji ya sanya alkhairi ya kumasa ayi damu, amma Hamma wata nawa kasanya musu kafin Auren?

A taqaice Moddibo yace "sam ba watanni nasaka ba Danejo kwana biyu kawai na saka jibi-jibin nan zan ɗaura mata Aure. Yana kaiwa nan ya miqe yabar gurin ba tareda ya damu da irin kallom mamakin da ummie da Inna Laure kebinsa dashi ba yay gaba abinsa

Rabe dake tsaye jikin ƙofar karan dake jingine da ɗakinta sam batasan sanda ta sulale akan qafafunta zuciyarta na bugawa da mugun qarfi ba, Allah ya sani sam bazata iya hana zuciyarta abinda takeso a wannan gabar ba ko kaɗan, sedai tasan koda giyar wake tasha sam bazata iya bijirewa mahafinta akan muradinsa na Aurar da ita ga Bamanga ba,

Komai da mafarinsa tasani sanin kanta Bamanga ba shine zaɓin Zuciyarta ba to amma idan harta bijirewa wannan Auren tamkar ta kunyata mahaifinta ne, Aure ta da Bamanga tamkar igiyar kabar da aka daɗe ana tufkata ne tunkafin tasan kanta, ma'ana dai Aurene da iyayensu sukai alqawarin faurawa tun a ranar da aka haifeta don haka dole ne tayi haquri da Bamanga a matsayin mijinda Qaddara ta zaɓa mata shi.

Daga Ummie har Inna laure babu wanda ya tanka akan lamarin hukuncin da Moddibon ya zartar, dole tasa suka amince da hukuncinsa dukda cewar a zukatansu sunada ja akan abinda yake shirin zartarwa akan Raben.

Tun daga Ranar Rabe ta ɗaura da zubar da hawaye gamida tilastawa kanta faɗawa a qoramar tunanin zaratan mazan da suka shigo rayuwarta a baya, sosai ta rame tayi wani irin duhu duk a kwana ɗaya kachal tamkar ba ita ba, ko abinci se Ummie ta matsa mata kana take iya cinsa shima ba wani sosai take cin ba.

Tun'a daran jajiberen Aurenta da Bamanga Rabe ta gama saddaqarwa da kanta cewar tabbas tayi rashi a rayuwarta irin rashinda bazata taɓa mayarda kamarsa ba, a hankali take ɗaga qafarta harta iso bakin qofar bukkar da mamie ke kwana, sunkuyawa tayi kana ta shiga cikin bukkar bakinta ɗauke da sallama, a zaune ta samu Ummie wadda keshan fura se faman murmushi takeyi da alama video call takeyi itada su Zainab da kuma Abie. Tana ganin shigowarta Ummie ta kashe wayar tareda maida hankalinta ga Rabe tace " Dota na Amarya shigo mana kika tsaya kamar kuwa kinsan yanzu nake shirin nabiki ɗaki akan maganar shirin bikin sekuma gashi kinzo da kanki, yau insha Allah Adda Maryamu da yafendunki Gwaggoji duk yau zasu iso insha Allah daga yolah.

Kanta a qasa tayi murmushi kawai ba tareda ta iya furta koda kalma guda ba, ko babu komai har a ranta ta ɗanji sanyi dajin batun zuwan qanwar Mahaifiyarta da kuma kakarta wadda ta haifi Mahaufiyarta wadda sike kirada (gwaggoji) ko babu komai tasan zata ragewa kanta damuwa muddin ta tattauna matsalarta da wani

Kanta a qasa tana wasa da yatsun hannunta tace "Ummie ki bani aron wayarki zan kirasu mom.

Shiru Ummie tayi a ranta tana mamakin yanda yarinyar kejin nauyinta sannan tayi murmushi ta miqa mata wayar Ta karɓa tabar ɗakin tanajin wani irin sanyi na ratsa zuciyarta, tana fita ɗakinta ta koma tareda buɗe qatuwar jakar da Edyan ya lafto mata uwar siyayya lokacin daze dawo da ita gida tayi lokaci guda kuma ta zaro wani qaramin card, qurama card ɗin idanu tayi zuciyarta na wani irin racing sannan ta shiga danna numbers ɗin jikin katin a jikin wayar sannan ta kara a kunnenta tareda lumshe idanunta tana jiran ya ɗauka.

Can ɓangaren wanda ta kira ɗin zaune yake cikin katafaren ofinshinsa wanda aka qawata da kayan alatu na morewa rayuwa ya ɗora dogaren santala-santalan qafafunsa duka biyun a saman table ɗin dake gabansa, a hankali ya ɗaga hannunsa na dama yana me sassautawa kansa necktie ɗin dake ɗaure a wuyansa.

Qarar wayarsa ce ta katseshi wadda ke ajiye bisa gefansa a nitse yakai hannunsa ya ɗauka tareda zubawa number dake kiran nasa tsimammun idanunsa kamar baze ɗauka ba se kuma can ya ɗaga tareda karawa a kunnensa yay shiru ba tareda yace qala ba.


Daga ɓangarenta Ajiyar zuciya ta sauke me qarfin gaske sannan ta buɗe bakinta wanda yayi mata nauyi tace "yaya Edyan nice mulaikha c.....!!! Se kuma ta fashe mishi da wani irin kuka wanda yasa ba shiri Edyan ya miƙe tsaye cikin kiɗima gamida tsagwaron tashin hankali yana faɗin "meya faru dake mulaikha ? Meyasa kike kuka irin haka?

Edyan ya jefa mata waƴannan tambayoyin duk a lokaci guda, daqyar ta iya buɗe bakinta tace "don Allah partner kazo I wanted to see you tomorrow plss.........!

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya gyara zamansa kamar tana gabansa yace "look mulaikha don Allah ki ɗena kuka kinji babe, kin sani banason kukan ki sabida it really hurts me so please don't cry again OK?

Ɗaga masa kanta tayi kamar yana gabanta lokaci kuda kuma tace "uhm. Murmushi yay kaɗan sannan yace"not hmmm mulaikha na just promise me cewan bazaki sake kuka irin haka ba kinji?

Bakinta ta buɗe a hankali tace "i promise!

"yauwa that's my girl bye. Ya faɗa yana me katse kiran ba tareda ya tsaya jin abinda zatace ba.

Ƙurawa wayar manyan idanunta tayi tana kallon wayar kamar bazata dena ba, tana riqe da wayar wani sabon kiran ya shigo wayar Ummie da sauri ta ɗauka ta kara a kunnenta sabida duk a zatonta Edyan ɗinne ya sake kiranta a karona biyu.

Daga ɗaya bangaren zainab tace "Ummie gaskiya ya kamata ki dawo haka nan wllh sabida bro Qurraty bashida lfy jiya ko office bai samu yaje ba, pls Ummie don Allah ki dawo koke ze iya sanar dake abinda ke damunsa.

Sakin wayar Rabe tayi sabida tsabar bugawar da zuciyarta dayi da

Please Login or Register in order to submit comment