Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Cikin gurɓatcciyar hausarsa yace ka kwanta yaro dare Yana yi kuma gashi kun kwaso hanya. Yana gama faɗin Haka ya juya jikinsa a salube ya bar ɗakin yay canta bayan bukkokinsa ya fashe da wani irin kuka..............












Chubado✍️
[3/3, 5:39 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


Page :46


*_WRITING BY: CHUBAƊO_*


Not edited🙅‍♀️


_____✍️Wani irin kuka yakeyi tamkar ransa ze fita seda ya ɗau lokaci me tsayi yanayi sannan ya danni zuciyarsa yayi shiru, dafe kansa yayi da duka hannayensa biyu yana me tausayawa kansa bisa jarrabawar da Allah yayi masa gefe kuma ga iftila'in daya faɗawa iyalinsa wannan wace irin musiba ce haka ace iyalinka na ɗauke da cikin da Allah kaɗai yasan ubansa.

Maza sama da uku ace sunwa mace fyɗe at same time wa zaka nuna a matsayin uban wannan yaro?

Gabansa ne yay wata irin faɗuwa lokaci guda kuma ya dafe saitin zuciyarsa dayaji tana masa wani irin zafi, miqewa yayi daqyar ya nufi bukkarsa inda Ya sauki Edyan a ciki ya fara laluben ƴar qaramar jakar da ya shigo gidan da ita wadda ke ɗauke da magungunansa na Asbiti ya ɓalla ya afa a baka, ya jima zaune sannan ya ɗan samu relif da ace yabar wannan jakar a gidansu Muzaffar a sanadin Ganin Danejo dayayi da besan inda ze tsoma ransa ba.

Fita ya sakeyi zuwa bukkar da Laure ke ajiye shirginta ya kwanta acan ya barwa Edyan ɗakin shi kaɗai donya sake, yanajin fitar moddibo ya miƙe ya zauna tareda kunna fitilar wayarsa take hasken ya game ko wace kusurwa ta ɗakin, ajiyar zuciya ya sauke me qarfin gaske sabida wani irin ciwo dayaji haqarqarinsa na dama ya farayi sabida rashin saboda irin wannan makwancin, ɗan buɗa idanunsa yayi tareda shafa kwantacciyar sumar gefan fuskarsa sannan ya miqe ya fara zagaya ɗakin yana tunanin yanda za'ai ya iya baci akan katifar ciyawan dake ɗakin, take yaji zuciyarsa ta mugun karye wasu siraran hawayen tausayin su moddibo ya fara zubo masa

"Taya za'ai ace mutum ya iya rayuwa a cikin irin wannan Dajin?

Edyan yayiwa kansa wannan  tambayar, take wani ɓangare na zuciyarsa yace dashi "ba gashi nan su suna rayuwa a ciki ba.

Hannunsa yasa na dama ya shafe ƙwallar data zubo masa a hankali ya furta "Alhamdulillah ya Rabb dakaimin ni'imar da ba kowa kayiwa kamarta ba, na tabbata ka haɗani da mulaikha ne don kawai a sanadinta nazo naga irin rayuwar da sukeyi Don kawai na Qara imani akan Rayuwa, ya Allah ka qara mana sutura duniya da lahira don Alfarman manzon Rahama (S.A.W).    A haka Edyan yayta tufka da warwara har bacci ya fara ɗaukarsa,

Kamae wanda aka mintsina yay firgigit ya tashi sabida wani irin kukan qwaro daya addabeshi, koya ya rufe idanunsa da nufin yayi bacci seyaji ya kasa sabida qarar kukan gyaren daya cika ɗakin, wani sirin tsaki ya saki tareda miqewa ya zauna a saman katifar kamar ze saki kuka sabida takaicin kukan qwaron da kuma rashin sabo da kwanan irin wannan gurin, duk irin gajiyan dayayi kasa baccin yayi  yanda yaga rana haka yaga dare.

         Wannan shine abinda ya faru a Rugar Arɗo.

                    *******

Ɓangaren su muzaffar kuwa basu shigo cikin Gyambu ba se wajen qarfe 11:00pm na dare,  direct wani babban hotel suka nufa muzaffar yay musu booking ɗakuna guda biyu Ummie tareda Zainab shi kuma nasu shida Abie

Bayan kowa ya nufi ɗakin baccin nasu ne Muzaffar ya buɗe ƙofar ɗakinsu ya fito zuwa inda nasu Ummie yake, a zaune ya sameta bisa saman dadduma da Alama sallar ishsha'i ta gama gabatarwa, tsayawa yayi daga bakin qofar yana kallon yanda damuwa ke baiyane qarara a saman fuskarta take wani irin tausayinta ya gama cika zuciyarsa, a  salube ya tako zuwa gareta ya zauna daga gefanta tareda kamo hannayenta cikin nasa yana ɗan mammatsaya cikin sugar rarrashi yace "Ummie nasan yanda kikeji a ranki sam ba abubane me sauki da mutum ze iya handling dinshi cikin sauqi, bt dukda hakan ya kamata ace kin qarama kanki qarfin gwiwa akan jarrabawar datazo miki a rayuwa, don Allah ki ragewa kanki damuwa sabida kar wani abun ya sameki na tabbata Baffa ze fahimceki kuma delensa ya karɓe yunda keɗin jininsa ce no matter what,  koda ace sular rabuwa bata gifta a tsakaninki dashi ba dole wata sekun rabu tunda tun ran gini ran zane Allah ya rubuta muku hakan a zannan qaddarar ku.

Ajiyar zuciya muzaffar ya sauke me qarfun gaske sannan yaci gaba da cewa " ummie qaddara ba abarda ɗan adam zeyi shawara a kanta bace, rubutu ne tun daga mafari kafin ayi halitta don haka babu yadda muka iya dole tsarin Allah shine a saman komai indai har baffa ɗan uwanki ne na haqiqa wllh zeyi miki uziri akan dukkan abinda zaki faɗa masa, don haka ki dena sa damuwa a ranki insha Allah everything is going to be alright kinji Ummie na?

Muzaffar ya faɗa yana jawota jikinsa yay hugging ɗinta with so much love between son to his mother.

Kuka Ummie keyi qasa-qasa tareda miqa godiyarta ga Allah daya bata ɗa irin muzaffar wanda yafi darajar kilo giram 70 na zinare a idanunta.

Ya jima tareda ita sannan ya miqe yay mata sallama zuwa ɗakinsu, bisa ga mamakinsa a zaune ya samu Abie shima ya kasa rintsawa duk a dalilin damuwar da Aisharsa ke ciki, zama muzaffar yayi daga gefan abie ba tareda ya kalleshi ba yace " Abie wani al'amari ne a rayuwar Ummie wanda har yake sanyata zubar hawaye irin haka?

Kallonsa Abie yayi da sauri lokaci guda kuma yay qasa da idanunsa yace "koma menene zakaji komai da zarar mun isa ga moddibo.    Abie na gama faɗin haka ya haye gadon yaja ɓargo ya rufe jikinsa dukda cewar idanunsa a soye suke babu alamar bacci a cikinsu.

(o'o see love don Allah, wllh duk duniyar nan babu abinda yafi samun miji na gari ni'ima da kwanciyar hankali, so pls my dearest sisters wake up and keep praying for miji na gari, wllh idam kika saki vaki kina bacci cikin dare ba tareda kin miqe kin roqi miji na gari  ba your life is in danger malama, becouse duk duniyar nan babu abinda yakai samun miji na gari daɗi.  ya Allah ka zaɓawa ƴan matan mu da mazajen mu mata na gari tareda zuriya ɗaiyiba ))

Washe gari tun 7:00am suka haɗa komai nasu suka kama hanyar rugar Arɗo,  tun daga irin jejin da suke ratsawa ta ciki suna tafiya zuciyar Abie ta fara tsinkewa, babban abinda ya ɗaure masa kai shine taya za'ai ace mutum me rai ya rayu a cikin wannan qungurmin dajin?

Haka muzaffar ya dinga ratsawa ta cikin labi (hanyar shanu) harya isa cikin rugar,  motar daya hanga a tsaye ce tasa ya qara qaimi don ganin ya isa kusa da motar.

Parking yayi a saitin motar yana qare mata kallo harya fito daga cikin tasu motar, zaro idanu yayi lokacin da idanunsa sukai tozali da bayan motar da kuma sunan dake manne a saman lambar motar me ɗauke da harufa guda biyu kamar haka......................






Comment
Nd
Share

Don't forget to vote on whatpad




Chubaɗo✍️
[3/3, 5:39 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


Page :47


*_WRITING BY: CHUBAƊO_*



*_Miɗoyatta himɓe jeɗo tokka'am bomiɗotora Allah barkiɗinamon thnks so much for the love 👏_*

Yau dai kam Na saka fulatanci a wannan page ɗin sosai sedai ayi haquri dani 😂


BANYI EDITING BA🙅‍♀️

____✍️Da mamaki kwance saman fuskarsa ya isa jikin motar wanda zuciyarda ta gama aiyana masa ta Edyan ce, ya jima yana nanata harufan sunan dake saman jikin lambar motar kamar me koyon karatu, tambayan dake addabarsa a wannan lokacin itace "shin me Edyan keyi a nan kuma meya kawoshi?

"muje mana ka tsaya kana kallon mata.

Abie ya katse masa tunani wannan hakan yay daidai da fitowar Moddibo da kuma Edyan daga gidan, da sauri Ummie ta nufi inda moddibon ke tsaye wanda yanayinsa ya mukun sauyawa daga ganinta cikeɗa ɓacin rai yace "* _ta'awara kumbi'am danejo, miɗa mimeta milara ma hotoha aburti_* ( karki matso kusa dani Danejo banason na qara ganinki a rayuwata ki koma inda kika fito) ya faɗa yana nunata da yatsa cikin ɓacin rai.

Wani irin zubewa Umnue tayi bisa qafafunta tareda haɗa hannayenta duka biyu cikin harshen fulatanci tace " Hamma useli waɗɗu munyal na'aibiyamma nonnon Allah arti bindi plss. (don Allah yaya kayi haquri ba laifina bane haka Allah ya rubuta a qarqashin qaddarar mu).

Cikeda fushi gamida ɓacin rai moddibo ya nunata yace "An'asamte abiya miwaɗa munyal Danejo? (yanzuke bakiji kunyar kallona kice min nayi haquri ba Daneji?)

Gabaɗaya gurin zuba musu ido akayi ciki kuwa harda Edyan wanda kansa ya mugun gama ɗaurewa da maganganunsu, daga Abie har Muzaffar babu wanda yay qoqarin dakatar da wani a tsakaninsu sedai dukansu sunajin zafin zubar hawayen Ummien, musamman muzaffar da har yanayinsa ya fara canzawa din haka da sauri ya isa inda Ummien ke zube tana kuka shima ya zube nasa gwiwoyin tareda haɗa hannayensa guri guda alamar roqo yace "bansan wani laifi Mahaifiyata ta aikata maka ba Baffa amma dukda hakan a matsayina na ɗa a gareta ina roqa mata alfarmar yafiya a gareka don girman Allah ka yafe mata ba tareda kayi tunani akan irin girman laifin data aikata maka ba, kada ka manta baffa komai na rayuwa yana tafiya ne da zannan qaddara kuma idan har ubangiji ya rubuta hakan to babu shakka se'abin ya tabbata don haka nake roqonka arziqi don girman Allah ka yafe mata kodan darajarmu nida mahaifina!!!!!!


Muzaffar ya faɗa wasu zafafan hawaye na zubo masa Sabida jinɓzafin zubar hawayen mahaifiyar tasa dayakejin zubarsu tamkar zubar tafasasshiyan dalma asaman zuciyasa.

Gabaɗaya kallonsu mutanan dake tsaye a qofar gidan sukayi kunsan mutanan mu da kallo idan sukaga baqon abu lol 😂

Kasa cewa qala modɗibo yayi sabida masifan kunyar muzaffar ɗin dayakeji, badan darajarsa ba wllh ko kallon ummien bazeyi ba haka kawai yakejin kimar yaron a idanunsa ta yanda yakejin zai iya sadaukar masa da komai nasa Muddin mallakinsa ne. Juyawa yayi ya shige gidan ba tareda ya iya sake futa koda kallama guda ba

Matsowa Edyan yayi inda Abie ke tsaye tareda ɗan rissinawa ya gaidashi, da sakin fuska Abie ya amsa masa tareda dafa kafaɗunsa yace "ai tun jiya nake jarraba number Cp amma na kasa samunsa.

Edyan yayi murmushi yace "he's fine Abie, be jima da dawowa ba ai. Ya faɗa yana kallon Ummie wadda ta miqe da sauri tabi bayan moddibo

Qarasawa gurin yayi yana kallon muzaffar wanda shima ɗin ita yake kallo jikinsa a matiqar mace ya sauke kallonsa ga barin Ummie sannan ya dubi Edyan da mamaki kwance a kan handsome face ɗinsa yace "meya kawoka nan kuma dude?

Yatsina fuska Edyan yayi yace "i bring my baby to meet with her parents ne thats why I'm here. Ya faɗa with so much emotion on his face.

Take hanjin cikin muzaffar suka wani irin juya a lokaci guda nan da nan zuciyarsa ta wani irin buga da qarfi amma kuma seya dake ya saki wani ɗan banzan murmushi wanda ya ɓoye weakness dinsa yace "waw thats nice dude.

"Kaifa meya kawoku ? Edyan ya faɗi hakan yana tsareshi da manyan idanunsa.

Ɗan jim kaɗan muzaffar yayi kamar bazeyi magana ba ya ɗan saci kallon cikin mota yaga still zainab na bacci sannan yace "is just a family issues. Taɓe baki Edyan yayi yace "ok tashi mu shiga ciki

Miqewa yayi daga tsugunnen dayake ya koma mota ya tada zainab sannan suka shiga cikin gidan gabaɗayansu kowa da abinda yake saqawa a zuciyarsa.

Suna shiga direct ɗakin moddibo sukaiwa kansu masauki dukda cewar moddibon be wani sake dasu ba amma yayi qoqari sosai wajen danne zuciyarsa akan abinda qanwar tasa ta aikata masa. Bayan sun zauna ne modɗibo yasa Rabi'atou ta kawo musu tafasashshen madara da kuma damammiyar dawo wadda taji uban kayan qamshi irin na Asalin fulani.

Ƙura mata idanu Ummie tayi tana kallonta lokaci guda kuma ta saki wani tattausan murmushi wanda ya baiyana ainihin kyanta da kuma irin kamar da suke da moddibo. Itama Rabi'atoun kallonta takeyi sannan ta durqusa ta gaishesu dukda cewar batasan daga nahiyar da duke ba, kokaɗn hankalinta bekai ga muzaffar wanda ke zaune a kusada Edyan ba hakan yasa ta miqe ta fara qoqarin fita

Daqyar ya iya bude bakinsa sabida wani masifan kyau dayaga ta qara masa a sanadin canjin data samu yace "uhm you don't know how to great right?

Tsayawa tayi cak ba tareda ta samu zarafin juyowa ba sabida tsabar ruɗun data shiga a sakamakon jin muryar mutumin da kullum zuciyarta ke bugawa dason sake jin sautin muryarsa a rayuwarta, da ɗan sauran qarfin daya rage mata ta tattara ta juyo a hankali take idanunsu ya sarqe cikin na juna,

Gabaɗayansu zuciyarsu bugawa take kusan duk a lokaci guda haka kuma kowa da abinda yake saqawa a ransa gameda abokin gamin nasa. Sauke idanunta tayi da sauri kamar me koyon magana tace "g..ood morning! Sam bata tsaya sauraron respond ɗinsa ba ta fice daga ɗakin zuciyarta na bugawa.

Ɗakin da bata taɓa zaton zata iya sake shigarsa ba ta nufa sabida tsabar ruɗanin dake tareda ita, a hankali tasa hannunta ta ɗaga labulan buhun dake jikin bukkar tareda kunna kai ciki still tayi tana kallon Inna Laure dake zaune dirshen da uban ciki qafafunta duk sun kumbura.

Wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyarta take shauqin da murna suka yaye mata hujabin tsoron lauren data daɗe tanaji ta nufeta da wani irin excitement on her face ta rungumeta, ko babu komai itama zata haifa mata qanin daze dinga ɗebe mata kewar kaɗaicin data taso a cikinsa.

Duk yanda taso ta Ta kali fuskar inna Lauren sam abin be yuwu mata ba dole ta haqura ta fara qoqarin matsa mata qafar yanda zata ɗanji dama-dama

A ɓangaren zuciyar Laure nadamace zallarta dukda cewar bata fito mata da hakan a fili ba, gabaɗaya kunyar yarinyar takeji musamman idan ta tuna irin zaluncin data dingai mata a rayuwa ba tareda haqqinta ba, tayi mata alkaba'i me tarin yawa wanda bakinta baze iya qayadewa ba se gashi tun ba'aje ko ina ba Allah ya mayar matada mugun nifinta a kanta, hawayene suka zubo mata amma kuma setai saurin sa hannunta ta goge gudunɓkar Rabi'atoun ta gani.

A haka har aka kwashe lokaci meɗan tsayi suna tare tana matsa mata qafar.

A ɗakin moddibo kuwa shirun ne ya fara gundurar kowa amma banda Ummie wadda ke zaune jefi-jefi takan ɗaga idanunta ta kalli yayan nata. Abie ne ya katse shirun ta hanyar cewa "salati goma ga manzon Allah (S.A.W) nan take kowa ya amsa aka shiga jerawa manzon Rahama salati bayan sun kammala Abie ya ɗaga kansa ya kalli modɗibo yace "da farko dai ina mai baka haquri bisa abinda ke tsakaninka da Aisha bawai a matsayin suruki ba a'a ina magana ne a matsayina na Abdulwahab Abdalla kuma ubaga ɗanda Aisha ta haifa, haqiqa Aisha tayi kuskure musamman data gaza haquri ta zauna tareda danginta sakamakon iftila'in daya faɗa mata, gabaɗayan mu dagani harkai babu wanda ze iya misalta irin ciwon da zuciyar Aisha ke ciki tunda gabadayan maza ne ba mata ba amma kuma dazamu ɗora kanmu a matsayinta na tabbata hukuncin data zartarwa rayuwarta muma irinsa zamu yanke kokuma akasin hakan, banaso ka kalli aisha a matsayin mace mara tausayi kokuma adalci sabida sam siffarta ba haka take.

A iya zaman danai da ita kimnain shekaru talatin da biyar na karanci halaiyarta ta yanda ko ina naje zan bada labarin wacece ita.

"amma kuma ai hakan be hanata iya guduwa tabar Ahalinta ba duk sabida wani dalilinta mara tushe!!!!! Moddibo ya faɗi hakan ransa a matiqar ɓace. abie zeyi magana Moddibo ya kalli su muzaffar da Edyan se kuma zainab dke zaune suna raba idanu yace "maza ku tashu ku bamu guri zamuyi magana.

Ba musu gabaɗayansu suka miƙe suka fita kamar yanda modɗibon ya buqata sannan ya dubi Abie yaci gabada cewa "duk na saurari batunka nima yanzu zakaji abinda na riqa a matsayin hujja dukda cewar ba lallai Danejo ta sanar dakai ba, kamar yanda ka faɗa a maganganunka na baya tabbas ni kaina mai iya bada shaida fiyeda yanda ka bayar ne akan Danejo sabida tun batasan kanta ba nake rainonta da hannayena, nasha haqura da abubuwa da dama a rayuwarta don kawai na inganta Rayuwarta to amma meye laifina don kawai qaddara ta Fyaɗe ta faɗawa rayuwarta shikenan seta gudu ta barni ba tareda ta sanar dani inda zataje ba har tsahon shekara 35?

A matsayinka na uba wanda keda ƴaƴa mata ka ɗora maganata akan mizani shin wani irin hukunci zaka yankewa Aisha a lokaciɓ da qaddara ta sake haɗaka da ita?

Shiru Abie yayi zuciyarsa cikeda zallar tausayin modɗibo he wish to see his sister kamar yanda modɗibo yaga tasa qanwar wadda tun bayan rasuwar mahaifinsu da aka musu rabon gado ba jimawa mijinta ya ɗauketa sukabar garin ba tareda ya sanar dashi ba, tunda suka tafi har yau be qarajin duriyarsu yayi neman harya gaji duk kuɗinsa da kuma shahararsa har yau babu wani labari akan Balaraba qanwarsa. Nan take Abie ya fashe da kukan tausayin kansa

Seda yay me isarsa sannan ya ɗaga kai ya kalli moddibo yace "ina roqonka Arziqi ɗon Allah ka yafe mata wllh da kasan irin wahalar da Aisha tasha akan tunaninka na tabbata zaka yafe mata ba tareda ka tsaya dogon nazari ba, tundaga lokacin dana tsinci Aisha a bakin hanya babu numfashi a jikinta har zuwa lokacin dana fara soyayya da ita har mukai Aure Aisha bata taɓa samun kwanciyar hankalin manta ka ba, haka kuma munje numan yafi a qirga amma kuma bamu sameku ba se bukkokinku da aka sakawa wuta suka qone, dukda haka Aisha bata yanke qauna ba kuma bata fasa zuwa numan ba akan kozata samu labarin inda kuka koma.

A qarshe da abin yayi tsamari ɗaukarta nayi kacokan na maida ita india da zama kozata rage yawan damuwar dake ranta. A qarshe kuma ina me maka wasilci kan cewar Allah ma munayi masa laifi kuma ya yafe mana ba tareda ya duba girman laifin da muka aikata masa ba.....

Hawayen dake idanunsa Moddibo ya share sannan ya kalli ummie dake zaune tanata gurzar kuka a karon farko tun shigowarta ɗakin yace" na yafe miki Danejo Allah ubangiji ya yafe mana gabaɗaya 😭

Zabura tayi ta riqe qafafunsa tace "nagode Hamma Allah ya qara girma.


A haka kowannensu zuciyasa ta cika da farin ciki mara misaltuwa, fitowa Abie yay daga bukkar bisaga mamakinsa muzaffar na kan wani dutse wanda ke facing ɗin ɗakin moddibon daga ɗan nesa, fara'ar kan fuskar Abie ce ta bashi tabbacin cewar baffan ya yafewa mahaifiyar tasa. Misalta irin farin cikin da muzaffar ke ciki abu ne da baze yuwu ba don haka suka rungume juna da Abie shikuma Edyan yanata baza uban murmushi wanda ke nuna farin cikinsa ga abokin nasa.

Tun'a safiyar ranar labari ya gama karaɗe rugagen dake maqotaka datasu moddibo kan cewar Danejo da Rabe sun dawo harda ɗanta saurayi ma da kuma mijinta, don haka akwai taron al'ada wanda za'a habatarwa da Danejo da kuma ɗanta wanda ba'ayi mata ba tun shekarun baya *_(niko nace kuji bidi'a don Allah 🤣)_*

Kafin kace me jama'a kowa ya fara halarta zuwa bikin Al'adar Auren danejo da kuma mijinta.

Bayan Azahar aka kawo kayan sakin da Ummie da Abie zasu saka wanda ya kasance launin blue da yallow a cikin wasu qwarya guda biyu kowada nasa se kuma takalman roba suma guda biyu da kuma lulluɓi, su muzaffar da Edyan ma sam ba'a barsu a baya ba sedai su nasu kayan na farin saqi ne kamar na sauran ƴan gaiya, bayan anyi sallar la'asar ne Bulo handi tazi tasa Ummie ta sanya kayan saqin da aka kawoma ummien sannan ta umarceta dataje ta taimakwa mai gidan nata ya shirya tunda tasan yanda ake komai. Ba musu ta fita daga fakin zuwa inda Abie yake

Seda ta tabbatar ta taimaka masa ya gama saka komai na biki al'adar sannan ta ɗakko cinkon saqaqqiyar igiyar kaban dake gefe ta rataya masa suka fito tare, a waje suka cimma su muzaffar da edyan da zainab suma sun shiya cikin farin saqin suna jiram fitowarsu.

Kusan a tare suka nufo inda ake gudanar da shagalin bikin al'adar daga muzaffar har Edyan seda abin ya nemi ya basu tsoro musamman yanda sukaga an gangama uban itace uwa naci gefe kuma nawa saniya guda ne a banqare ana gasashi gabaɗaya fuskokin mutanna dake gurin duk an fenteta da uban farin fenti da yellow irindai kwalliyar fulanin jeji, har aka kabbara kiran sallar magrib ba'a fara shagalinba har seda kowa yay sallar magrib tukunna

Sosai abin ya burge zainab don haka ta fito da wayarta tana ɗaukar vedio tun daga zuwansu Abie har kujerar da suka zauna seda ta dauka a vedion , kafin kace me tuni shagali ya kankama abin babu kama hannun yaro sannan Rabe suka qaraso gurin itada ruqatu da kuma Modɗibo, gabaɗyansu tsareta sukai da ido daga muzaffar ɗin har Edyan ɗin, nan take zuciyar muzaffar ta fara aiyana masa kan cewar yaje gareta.

Yana shirin miqewa Edyan ya rigashi miqewa ya nufeta fuskarsa ɗaukeda wani hamshaqin murmushi tareda fito da wayarsa ya fara ɗaukarta hotuna tana dariya, yana zuwa kusa da ita yace "looking so Masha Allah partner. Washe haqora tayi tace "thank you partner and you too.

Matsawa yayi dab da ita yace "can I snap a picture with you babe?

Why not. Ta faɗa tana gyara tsaiwanta sosai kusa dashi


Duk abinda suke idanun muzaffar na kansu babu abinda zuciyarsa keyi banda tafasa, a fusace ya miqe daga inda yake zaune ya nufi inda suke ɗaukar hoton har idanunsa nayi masa sabida ɓacin rai............ Hannunsa yaji an riqe ta baya don haka ya tsaya chak jikinsa na wani irin rawa yana juyawa yaga zainab ce ba shiri yay hugging ɗinta still jikinsa na rawa, a tsorace take binsa da kallo Cikeda tsoro ta zare jikinta daga nasa tace "what's wrong bro? talk to me pls.









Comment
Nd
Share


Dont forget to vote on whatpad.




Chubaɗo
[3/3, 5:40 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


Page :48


*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

*ɗan tsokaci a gameda masu cewa ya kamata ace muzaffar yasan dalilin dayasa mahaifiyarsa tabar Rugarsu zuwa wani guri na daban, ina so kuyi aiki da basirar da Allah ya baku a matsayinku na ƴan Adam masu tunani, inaso ku ɗora kanku a matsayin da Muzaffar kekai shin ya zakuji idan akace yau wani ɗan fashi ya hauro gidanka kuma yayiwa mahaifiyarka Fyaɗe? Na tabbata da ace hakan ta faru gara ace ƴan fashi sun shigo gidan ka sun kashe mahaifiyarka se hankalin ka yafi kwanciya da ace wani ɗan iskan banza ya ketwa mahaifiyarka alfarmarta, bawai ban karɓi qorafinku bane a'a kawai dai inaso ku ɗora lamarin a mizanin dedaito da hankali ne👏*

BANYI EDITING BA🙅‍♀️

_____✍️A ɗan wannan taqin abubuwa dadama sun faru masu daɗi da kuma marasa daɗi, lokacin da zuciyarta ta gama tabbatar mata da cewar lallai muzaffar ya tafi  a irin yanayin data gama tabbatarma da kanta cewar baze sake waiwayarta ba se kawai ta sake fashewa da wani irin kuka wanda it kaɗai tasan ma'anar abinta,  haqiqa ita kanta tasan bata kyauta masa ba musamman data nuna masa halin ko'in kula a lokacin datasan yana matiqar buqatar hakan, to Amma yata iya bazata iya barin Edyan ba sabida ya haskaka rayuwarta ta ɓangarori da dama. Don haka kowa yanada mahaimmancinsa a idanunta da kuma zuciyarta.

     

Please Login or Register in order to submit comment