Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗiyarsa dabe san irin halinda take ciki ba, ta wani ɓangaren kuma tausayin halinda zuciyar muzaffar ke ciki.


Jinginar da kansa yayi sosai a jikin filo ɗin dake bayansa abubuwa dayawa nayi masa yawo saman zuciyarsa, sama ya ɗaga idanunsa hawayen dake maƙale cikin ƙwayar idonsa suka tsananta zuba yace "Ya Haiyyu ya Qaiyyum Allah gani a gareka ina me miƙa matsalolina gareka tareda sanya yaƙinin cewar kaikadai ne me yaye damuwa kuma ka maye gurbinta da farin ciki, ya Ubangiji ka yayemin baƙin cikin da zuciyata ke ciki sannan ka bani mafita akan dukkan lamarina tareda sauran al'umar musulmi gabaɗaya🤲.

Shirune ya biyo baya kimanin tsahon lokaci bayan ya kammala Addu'ar hakanne ya bashi damar faɗawa a cikin tunani me zurfin gaske dangane da narkakkiyar sosayayyar dake kwance a tsakiyar idanun muzaffar, haka kawai yakeji a ransa cewar duk inda cancantar samun nagartaccen namiji me narkata take to tabbas Muzaffar ɗin yana da ita, sedai dukda hakan bayajin cewar ze iya damƙa masa hannun ɗiyarsa a matsayin mata gareshi harse in Bawuro ne dakansa yace ya janye alƙawarin Auren dake tsakaninsa da ita shine ze iya Bashi Aurenta ba tareda haufi kokaɗan ba. Ajiyar zuciya ya sauke me nauyin gaske wanda hakan yasa yaji ƙirjinsa saitin gurin da akayi masa tiyatar nayi masa xafi, a haka Doctor Rahul Guftah ya shigo ya sameshi nan ma seda suka sake dogon bincike akan gurin da suka yanka ɗin sannan ya bada umarnin da nurse ɗin dake bayansa ta bashi maganin daya ɗorashi akai bayan ya tabbatar da cewar babu wata matsala a tareda moddibon sannan ya fita daga ɗakin yana mamakin Rashin ƙan jikin da moddibo baya dashi, mostly duk wanda akayiwa irin wannan tiyatar seya shafe kimanin watanni yana jinya kafin ya warke amma kuma shi befi wata dayi ba amma gurin harya haɗe.

*******

Bayan Muzaffar yabar Asibitin Direct haɗaɗɗen Gidan da Ummie ta zauna ya nufa ba tareda ya jira Guard ɗinsa sun buɗe masa ƙofa ba ya fito yay cikin gidan idanunsa sun sauya kala daga farare zuwa nau'in jah, gabaɗaya jininsa tafasa yake sakamakon wutar muradin dake ruruwa a cikin ko wace gaɓa ta jikinsa, tsayawa yayi cak a lokacin daya isa tsakiyar kantameman falon dake cikin gidan ƙofar part ɗin Ummie ya ƙurawa idanu lokaci guda kuma zuciyarsa ta fara masa sanyi, A hankali yake jin zafinda zuciyarsa ke masa yana yaye takawa ya dingayi a hankali cikin salonsa na hamshaƙin ƙaƙƙarfan namiji harya isa jikin ƙofar part ɗin Ummien ya murɗa da ɗan sauran ƙarfin daya rage masa.

A hankali ya shiga madaidaicin palon da aka ƙawatashi da madaidaitan kujeru masu matiƙar tsari gamida ɗaukar idanu, bin ko ina yake da kallo har idanunsa suka sauka akan wata System ƙirar Companyn I phone, haka kawai seyaji zuciyarsa ta alaƙantu akanta ba shiri ya isa ga System ɗin ya ɗauka tareda da zubewa akan lallausan Kafet ɗin daya mamaye falon ya buɗe System ɗin yana bin pic ɗin dake malale akan icon ɗin system ɗin wanda yakeda tabbacin cewa Hotonsa ne a lokacin da Abie ya haɗa masa bikin Birthday ɗin cika shekara goma a duniya. Shafa icon ɗin system ɗin yayi lokaci guda kuma ya saki wani lallausan murmushi daya ƙara baiyana ainihin kyawunsa.

Wata folder ya gani A kan icon ɗin an Rubuta QURRATU'AIN a jiki da sauri ya danna Enter take folɗer ɗin ta buɗe, hotunansa ya dinga gani bila'adadin wasu tun yana jariri ɗanye goyo wasu kuma ya fara takawa gasunan dai barkatai, wani ɗan rubutu ne yaja hankalinsa a ƙasan wani hotonsa lokacin daya kammala karatun Degree ɗinsa. Ga rubutun kamar haka👇

"Ko wace uwa takanyi alfahari da duk wata ingantacciyar rayuwar ɗa ɗanta ya samu, sedai ni ba kamar ko wace uwa nake fa balle harna na nuna alfaharina a wannan ranar data zamo ta musamman a gareka Yarona, sedai dukda hakan bazan taɓa gazawaba wajen faɗa maka cewar ina matiƙar alfahari dakai ba Muzaffar Abdulwahab Abdullah sabida kaikaɗai ne duniya ta!!!!

Zuciyarsa ce ta karye a lokacin daya gama karanta wannan rubutu da ummien tayi a hankali wasu siraran hawaye suka shiga sakko masa wani rauna nannen murmushi ne yayi Escaping cute read lips ɗinsa muryarsa na rawa yace "I'm proud of you to Ummie to have you as a mother. A haka ya dinga bin pics ɗin yana kallo wasu yayi dariya wasu kuma yayi kuka a haka yaji zuciyanshi tayi masa sanyi harya manta da muradin daya shigo dashi a maƙale cikin zuciyansa.


A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah yau moddibo ya shafe watanni Uku cur a Asibitin dake babban birnin na india wato mumbai bayan doguwar jinyar dayayi, kallo ɗaya zaka masa kaga yanda yay wani irin fresh dashi kaman bashi ba, gashin kansa ya ƙara fitowa yayi wani irin baƙi se sheƙi yakeyi dukda furfuran dake tsakiyar kansa be hana fitoda duhun da gashin yayi ba, inda wanda yasanshi a baya zega moddibo wllh seya rantse wani balaraban yankin ƙasar Misira ne yazo. Yau Ta kama litinin ce wanda yay daidai da 28/12/ 2019 a yau moddibbo ya karɓi sallama daga babban Asibitin koyarwan dake Mumbai, sosai hakan ya masa daɗi don haka basu wani ɓata lokaci ba Muzaffar yasa a fara yi musu booking ɗin privet jet wanda zasu koma Nigeria.

Bayan ya gama wayar ne kiran Abie ya shigo cikeda so Muzaffar ya ɗaga tareda marairaicewa kamar Abie ɗin na ganinsa yace "im so sorry for the confusion Abie nasan zuwa yanzu ka gama ganoni kan cewan ba wani meeting danazoyi India but insha Allah I will explain everything to you my darling Abie don Allah kada kayi fushi dani kaji?

Ajiyar zuciya Abie ya saki har seda mom dake gefansa ta kalleshi sannan yace "is ok son ai Vicram ya sanar dani dukkan abinda kayimik ƙaryan akai but make sure gobe ku dawo gida tunda an sallameku sannan kuma seka shiya abinda zaka gayawa mon ɗinka idan ka dawo domin kuwa she's angry with you. Ya faɗa tareda katse wayar.

Dan zaro ido Muzaffar yayi suna haɗa ido da Moddibbo ya sakin masa cute murmushinsa me ƙara mishi kyau, a daran ranar muzaffar yasa aka kaisu wani haɗaɗɗen super maket ya narkarwa moddibo siyayya kamar me, har seda ya taka masa birki sannan ya dena ɓarna da kuɗin wani zoɓe ya gani na zinare wanda ya masifan ɗaukan hankalinsa take ya isa ga zoben yana kallonsa cikeda birgewa, kallon matar dake gurin yayi yace ta naɗe masa zoɓen yanaso ze siya sannan ya kuma nuna mata wasu zobunan guda uku suma duk na zinare ne yace ta naɗe masa su, sannan ya biya kudin duka kayan aka kai musu mota sukabar harabar gurin.

A daidai danjar dake tsakanin inda super maket ɗin yake ya hangi wani tsohon ba'indiye yana saida wasu duwatsu masu shegen kyau gamida ɗaukan hankali, a nitse ya balle murfin motar ya fita ba tareda yace da moddibo ƙala ba ya nufi gurin mutumin dayaga wasu maza da mata duk sun zagayeshi shima ya tsaya yana kallon wasu abin hannu da aka haɗasu guri guda da alama na mace ne da kuma namiji.

Yana tsaiwa a gurin dattijon ba'indiyan ya kalleshi cikin harshen turanci yace "take a look It's an eternal bracelet that will tie the fate of two together forever, so you have to buy it

Tsohon ya ƙare maganar yana murmushin dake baiyana yaƙininsa gameda wannan warwaraye guda biyu.

Ɗan buɗa manyan idnunsa muzaffar yayi yace "eternal bracelet?

Tosohon ya ɗaga kai yace "sure if you share this with your lover, even if you to break up each of you will go round and round until the two of you meet again.


Shiru yayi yana kallonsa kimani mintuna biyu sannan yace a naɗe masa yanaso. Jikin dattijon har rawa yakeyi Ya naɗe masa ya miƙa masa shikuma ya biyashi kuɗin ya tafi. A haka suka ƙarasa gida suna ɗan taɓa hira da moddibon


Washe gari suna idarda sallan Asuba kiran Abie ya shigo wayansa , basu jima suna magana ba ya shaidawa Abie ɗin jirginsu na gabda tashi zuwa Nigeria sannan ya katse wayan da murmushi kwance a saman handsome face ɗinsa around 6:00am jirginsu ya muzaffar da malam Moddibo ya ɗaga zuwa ƙasarsu ta aihuwa.

Semuce a sauka lfy C.E.O of zafar ENTERPRISES ✈️


********

Ƙanƙameta Mom tayi jikinta duk a sanyaye a hankali Edyan ya kama hannunta cikin nasa still Rabi'atou na jikinta yace "mom kin sani sanin kanki muddin Daddy ya yanke hukunci akan abu no body can change his mind sedai Allah kawai, don haka ki dena kuka insha Allah yau base anjima ba I will take to her to her parents I will make sure bata wulaƙanta ba so don't worry mom Allah is with us.

Ajiyar zuciya ta sauke tareda jin gamsuwar cewa ɗanta zeyi abinda ya dace dukda cewa mijinta be bashi goyon baya akan hakan ba, kasa magana tayi illah zare jikinta datayi daga na Rabi'atoun ta juya da sauri tabar falon tana sharar ƙwalla.

Ita kanta Rabi'atoun kukan take a haka Edyan yaja hannunta suka fita daga ɗakin tana waiwayen part ɗin mom ko zataga zeeyadah, da gudu zeeyadah ta fito daga part ɗin daddy ta nufota tareda rungumeta kusan a tare suka fashe da kuka sabida tsabar sabon dake tsakaninsu da juna. Seda sukai me isarsu sannan yajata suka isa gaban motarshi, da hanzari guards ɗinsa suka nufoshi da nufin buɗe masa ƙofa ya dakatar dasu dole yasa sukaja gefe suna kallonsa, ƙatuwan jakan yasa a buth ɗin motar sannan ya buɗe gidan gaba ya sakata ya rufe a nitse yake takawa harya kai side ɗin driver ya buɗe motar yana ƙoƙarin shiga zeeyadah ƙwalla masa kira tace " Ya Edyan Allah ya kiyaye hanya but make sure you take good care of her pls!!!!. Ta faɗa tana fashewa da wani sabon kukan.

Ɗaga mata kai yayi lokaci guda kuma ya shiga motar ya mata key sukabar gidan ransa na mishi zafi, seda sukai tafiya me nisa sannan ya dubeta ciken sanyi murya yace "zaki iya gane hanyar Gidanku ko?

Ɗaga masa kai tayi muryanta na rawa tace "sure.

Da wani irin mugun gudu ya kwashi motar sika kama hanaya.


((tofa wannan shi ake kirada saɓani me wuyar sani, to se muce a sauka lfy Mulaikhan Edyan😊))


*******

Cikin ikon Allah da hikimarsa mutanan India suka iso Nigeria lfy, tun kafin jirginsu ya iso garin na Abuja Abie ya turo Guards ɗin muzaffar ɗin da wasu danƙara-danƙaran Expensive motaci ƙirar companyn Ford's masu shegan kyau suka iso suna jiran saukar jirgin.

Jirgijn na sauka seda suka shafe kimanin 15 munites sannan matattakalar jikin jirgin ta fito, a hankali muzaffar dake sanye cikin wata shaiɗaniyar baƙar suite wuluk da ita wadda ta mugun karɓan jikinsa kamar dinshi akayita, sosai fuskanshi tayi wani irin haske sabida ramar dake taredashi, yanayin yanda read lips ɗinsa ya wani irin tattare kaman ya shafa Janbaki ba ƙaramin kyau hakan ya ƙarama fuskan nashi ba. Bayansa kuma moddibo ne biye dashi sanye ciki wata farar jallabiya mallakin companyn Emraty Fara tass da ita, kallo daya zakayi masa kaga zallar kamalar dayake da ita.

A haka suka Ƙaraso gaban motocin guards suka buɗe musu ƙofa bayan sun zuba kayansu a booth ɗin motar sannan sukaja motocin cikin jerin gwanonda suka saba gwanin ban shi'awa.

Tunda suka shiga motar zuciyar moddibo ke cike taf da mamakin matsayi da kuma gata irin na Muzaffar take yaji zuciyarsa ta amsa duk a lokaci guda.......





Comment
And
Share




Sushmah✍️
[3/3, 5:38 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


*_WRITING BY:CHUBAƊO_*


NOT EDITED


____✍️ Cikin nutsuwa motocin ke tafiya har suka samu nasarar isowa cikin Maitama, duk inda motocin suka sulala Sedai kawai kaga moddibo na baza idanu yana kallon ƙuduran Allah da kuma hikimarsa, a ransa kuma yana me girmama ƙwarewar maginan da sukai gine-ginan dake cikin garin a iya tsahon Rayuwarsa yayi yawo sosai tundaga kansu ƙasar Niger dadai sauransu amma betaɓa cin karoda guri mekyau irin Abuja ba kodan a daji ya sabayin Rayuwa oho🤷‍♀️

A haka suka iso ƙofar kantamemen gidan Me kamada aljannar duniya babu abinda ya ɗaurema Moddibo kai irin ganin yanda Get ɗin ya buɗe kansa da kansa ba tareda kowa ya taɓashi ba nan take yaji wani irin tsoro ya tsigawa zuciyarsa da gangan jikinsa, Haka suka kunna kai zuwa cikin gidan kallo ɗaya zakayiwa Muzaffar ka fahimci yana cikin Farin ciki dukda irin damuwar dake kwance a cikin ransa sam hakan be hanashi baiyana farin cikin ganin Ahalinsa ba.

Hannun Moddibo ya kama ya riƙe cikin nasa musamman daya Fahimci yanayinsa ya sauya daga wanda suka baro airport dashi suwa wani, Ajiyar zuciya ya sauke sannan yay murmushi yace "pls baffa feels free with us don Allah we are all family kasa a ranka nan ma gidanka kazo. Ya faɗa yana matsa hannun Baffan cikin nashi

Gabaɗaya Ahalin gidan suna farfajiyan gidan suna jiran fitowansu Except Ummie dake khitchine tana shiyawa ɗan nata girki na musamman don tarbarsa.

A wannan rana babu wanda beyi farin ciki da dawowar muzaffar ɗin ba, bayan sun iso sun huta ne muzaffar ke sanar da Abie irin karamcin da moddibo yayi masa a lokacin dayake dabda rasa Rayuwarsa, sosai Abie ya nuna jin daɗinsa tareda sanyawa a ɗauki modɗibo a kaishi masauki na musamman wanda aka qawata da karan alatu na jin daɗin rayuwa iri-iri.

Tabbas moddibo ya fahimci cewar muzaffar ba mutum bane gamagari kamar sauran yara ba, yaro neshi ɗan gata kuma ɗan asali da ga mutane masu tarin ɗukiya a haka ya kwana ya hantse a cikin wannan aljannar duniyar, sedai dukda hakan zuciyarsa naga tunanin ƴarsa guda ɗaya tillo wato Rabe.



Moddibo ne zaune qasan Makeken kafet ɗin dake hamshaqin falom yana daure boronsa (jaka) da alama shirin tafiya gda yake, muzaffar ne ya shigo dakin da murmushi Kwance a kan Kyakkyawar fiskarsa yace " baba. se kuma yayi shiru da sauri ya qaraso Cikin falon inda moddibon ke zaune yana ɗaure jakar kayan da suka dawo dashi daga india, cike da damuwa Ya kalleshi kaman ze sakin masa kuka yace " baba badai har ka fara shirin tafiya ba?

Murmushi moddibo yayi irin nasu na dattijawan qwarai yace "to yaro me kuma zan tsaya jira? Tunda Allah ya amince maka ka zama silar ceton Rayuwata me kuma zan zauna jira wanda ya wuce in koma ga iyalina?

Shiru Muzaffar yayi a ransa yanajin kewar moddibon ta fara addabarsa tun kafin ma ya tafi, a hankali ya buɗe jajayan laɓɓansa zeyi magana middibo ya rigashi ta hanyar cewa "zuwa yanzu Nasan Gabaɗaya jama'ar garinmu da kuma iyalina sam basa cikin kwanciyar hankali duk sabida tunanin irin halinda nake ciki Musamman ma Laure nasan Setafi kowa damuwa, da Ace ma Rabi'atou na tana tana gida tashin hankalin dazata shiyaga seyafi na kowa sabida ban taba tafiya me Nisan Irin wannan shafe watanni bana tareda ita ba, sbda tinanin Irin halinda zata shiga idan bana nan ɗin, Se gashi kuma yanzu babbar ƙaddarar Rabuwa ta gifta a tsakanin mu ba tareda mun shiryawa hakan b.......!

Wasu siraran Hawayene suka zubo masa dole ya kasa qarasa maganar yay shiru, Sunkuyawa muzaffar yayi tareda dafa kafaɗunda cikeda zallan kulawa yace "kayi haquri baffa amma komai muqaddari ne daga Allah kamar yanda qaddara tayi nasarar rabaku da ita isha Allah wannan qaddarar ce zata sake zama silar haɗuwarku, jikina yana bani cewar a duk inda Rabi'atou take sam bata cikin yanayi na rashin daɗi sabida muddin hawayenta suka zuba to wllh senaji haka a cikin jinin jikina so Dont worry Baffa insha Allah komai ze wuce.

Kasaƙe Moddibo yayi yana kallonsa a ransa yana girmama lamari irinna muzaffar ɗin, sam bashida yanayin izzar Da yaran Da iyayensu suka tara musu dukiya suke da ita, Muzaffar he's a nice person and social komai nasa da sauqi yake ɗaukarsa tamkar ba magajin attajirin Mamallakin companonin nan Ba Alhaji Abdulwab Abdullah ba.

Kafaɗarsa moddibo ya dafa still yana hawaye yace "Allah ya albarkaci Rayuwarka yaro haqiqa iyayenka sunyi sa'ar haihuwa da suka haifi ɗa kamar ka.

Murmushi kawai muzaffar yayi ba tareda yace komai ba, ajiyar zuciya yaɗan sauke sannan yace "da inada ikon hanaka tafiya wllh Baffa danayi hakan amma kum...... "Kada ka Damu yaro ai yanzu mun riga mun zama ahalin juna don haka babu me iya yanke wannan alaqar.

Kamar muzaffar zeyi kuka yace "yaushe ne tafiyar taka Baffa?

"Gobe da ikon Allah zan kama hanyar gda Tunda Allah ya azitani da lfyar dana daɗe bani da ita Wanda ta kasance kaine silar samuwarta. ya Qarashe maganar da murmushi a Kan fiskarsa

Murmushi muzaffar yayi Yace "don Allah baffa ka dena cewa hka nimafa ka ceci tawa rayuwar don haka nizan gode maka kuma har duniya ta gushe bazan taɓa dena godewa likitan gargajiya irin Baffa na ba. Ya faɗI hakan yayinda yake faɗaɗa murmushinsa gareshi.

sosai moddibo yaji Daɗin maganar muzaffar Ɗin , nan dai ya shiga yi masa nasihu masu Matiqar shiga jiki, sosai
Jikin muzaffar Yayi sanyi sbda nasihun da moddibon yayi masa, a ransa seyaji dama moddibo ya zauna tare dashi haka kawai dattijon ya gama shiga ransa,
Jiki ba qwari muzaffar ya miqe sbda jin kiran sallar ishsha'i, be cewa moddibo komaiba ya nufi hanyar fita Daga falon zuciyarsa a matiqar dagule.

Murmushi moddibo ya kuma yi A karona biyi sbda ya fahimci muzaffar Ɗin fishi yayi sbda yace ze tafi gobe,
Miqewa yayi shima suka nufi masallacin tare, daidai lokacin da Ummie ta loqo ta windown falon ta Don ganin fitarsu sedai sam bataga fuskokinsu ba se bayan su Data hanga sannan ta koma taci gaba da jera abinci akan dining.

Koda aka idar Da sallan muzaffar ya Dade yana addu'oinsa sannan suka shafa suka fito gaba daya,
Dai dai lokacin da Abie ma ya fito, kusan a tare suka jera suna tafe suna hira anan muzaffar ke shaidawa Dady tafiyar moddibo, sosai Abie ma yaji ba dadi sbda yanda ya saba dashi a kwana dayan da sukayi a gida kamar sun shekara da sanin juna, Shi kansa Abie ɗin yana buqatar ace sun samu lokaci da moddibo Donsi tattauna sosai akan wasu abubuwan na daban waƴanda suka shafi rayuwar Moddibon da kuma abubuwan dake faruwa a cikin garuruwansu na fasa qwaurin da ƴan bindiga daɗi suke musu ta hanyar yiwa yaransu qanana fyɗe kuma su qwace musu dukiyoyinsu, kodan darajar ceton Rayuwar ɗansa tilo dayayi shikuma dalilin wannan ya qudurtama kansa cewar tabbas seya taimaka musu koda kuwa hakan yana nufin ze rasa wani ɓangare na dukiyarsa ne gabaɗaya.

Har a cikin Ran Abie yaji cewar yana matiqar qaunar Moddibo sabida Yamada sauri saboda mutane Kuma ga kirki, gashi da haquri da sanin ya kamata shiyasa yake da dadin mu'amala Ta kowani fanni,
Indai ya zauna dakai koda na wuni daya ne to Se Zuciyarka ta qaunace shi Koda baka shiryawa hakan ba Sbda dattijon a kwai shiga rai,
Suna shiga Falon da aka saukeshi Abie Ya kalli moddibo yace" tunda gobe zaka tafi don Allah Meze hana Kazo Muje bangarena Muci abincin dare tare Dakai?

Shiru moddibo Yayi kamar bazece komai ba sannan ya ɗago yace "ina me baka haquri akan wannan al'amari dakazo min dashi wllh bazan iya zuwa ba idan naje tamkar ka takurani ne.

Duk yanda Abie yayi dashi amma sam yaqi amincewa Dole ya haqura badan yaso ba yayiwa moddibo seda safe, sannan ya wuce bangaren Ummie.

fita Muzaffar yayi dan dakko musu abinci a bangaren Ummien sa , be jima ba ya dawo dauke da manyan food flasks guda biyu se Zaynab dake Biyeda bayan sa hannunta dauke da flat da spoons ajiyewa tayi sannan ta koma ta daukko wani Babban flet Wanda ke dauke da kosilo Wanda yaji Uban qwai da bama ansa wata fara leda an rufe farantin da ita ta yanda kana Iya ganin abinda ke cikin flet din, da sallama ta shigo ta ajiye sannan ta gaida moddibo cike da girmamawa. da kulawa ya amsa mata tareda sakin fuskarsa dukda irin halinda zuciyarsa take ciki na kewar ɗiyarsa, Jikinsa a mace ya tambayar ta sunan ta murmushi tayi sannan tace "Sunana Zaynab.

Murmushi moddibo yayi sannan yace" Ashe mata tace da kanta. dukansu suka sa dariya sannan ta miqe tayi musu saida safe ta wuce bangaren su A ranta tana mamakin kyau da cikar zati irin na moddibo.


Zaune suke kan dining suna cin abinci Abie yake sanar da Ummie Batun tafiyar moddibo da safe idan Allah ya kaimu, Shiru tayi tana kallon Abie ɗin ba tareda ta iya furta koda kalma guda ba Lokaci guda kuma yanayinta ya sauya,

A hankali tace" daga zuwansa har ze koma se kace ana korar sa?

Murmushi Abie yayi sannan yace "wllh nima haka nace dashi amma fir yaqi yarda ya qara kwana ki Kidan sabida batun lfyarsa ma.

Dik wannan hiran da suke itada Abie qarfin hali kawai take Haka kawai setaji wani iri haka a jikinta sabida mutumin yayi mata abinda bazata taɓa mantawa dashi ba a Rayuwarta.

Abie ne ya katseta ta hanyar sanar da ita yayi kewarta,
Murmushi Ummie tayi sannan tace " Abou muzaffar kenan sekace wasu yara?

Dariya yayi sannan yace " au yara ne kawai suke da hurumin yin soyayyah?

Bata CE masa komaiba dan ta fahimci Neman magana kawai yakeyi Da ita,
A hankali ta ajiye cokalin dake hannunta ta miqe a taqaice tace seda safe.
Sam beyi qoqarin hanata tafiya ba sbda ya fahimci yanayinta ya canza tunda ya ambaci Tafiyar moddibbo.
Abinda ya qara daure masa kai shine meyasa Ta canza lokaci guda haka?

A hankali ya rintse idanunsa, sbda baya son abinda ze batawa matar tasa rai Koda kuwa menene shi, a daddafe ya kammala cin abinci, ya miqe ya nufi bedroom din shima a zaune ya sameta da alama daga toilet ta fito, kana kallon ta zakasan tana cikin damuwa, bece mata komai ba ya shiga toilet yayi brush sannan yayi wanka yafito, beyi mamakin ganin ta ajiye masa jallabiya ba sbda hakan al'adarta ce, murmushi yayi sannan ya sanya Jallabiyar a jikin sa.

yana gama sawa Ya haye gado abinsa bece mata komaiba yaja bargon Dake gefanta da nufin ya kwanta, donya qudurtama kansa cewar baze taɓa tambayarta dalilin sauyawarta ba sabida ita kanta tasan hakan na mugun ɗaga masa hankali shiyasa ma tayi.

Da kanta ta fahimci Tayiwa megidan nata laifi dan hka ta bude baki tace "don Allah kayi haquri bani da yanda zanyi ne dolece tasa,
Sanin kanka ne kasan bazan taba mantawa da irin binda wannan baƙon mutumin yayiwa ɗana ba, sannan kuma taya kake tsammanin zan iya jure ganin halinda ɗanmu yake ciki a sanadin soyayyar yarinyar da bamuda tabbacin sanin inda take a halin yanzu?

"meyasa bazakayi amfaninda damarka ta mahaifi ka nema masa aurenta ga mahaifinta kafin ya tafi ba?

"Haba Aisha so nwa kikeso muyi maganar nan ne sabida Allah? Nayi magana da bawan Allahn nan ya cemiɓ a kwai maganar Auren wani akan yarinyar shikenan kuma sena matsa masa akai don kawai inada kuɗi kuma inason ɗana?

Kuri tayi masa da ido se kawai ta fashe Masa da kuka.
Sosai Take kukan wanda ita kanta Bazata iya cewa ga dalilin Yin kukan Nata ba. Ganin abin nata bame qarewa bane yasa me Gidan nata ya Jawota jikinsa yana me bibbiga

Please Login or Register in order to submit comment