Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kin gode ko Mulaikha?

Murmushi ta sakin ma mom ɗin har seda beauty point ɗinta both side suka lotsa at the same time, juyawa mom tayi ta kalli zeeyadah tace ki ajiye wayar nan malam kuzo khitchine zamu shirya abinci na musamman Sabida yau Dadynku xe dawo. Wani uban tsalle zeeyadah ta buga tareda wirga wayar kan gado tazo ta rungume mom tana murnar tace "are you serious mom?

Ɗaga mata kai mom tayi tareda faɗin "sure darling. Sannan ta Shafi gefan fuskokinsu tace "muje ko. Tare suka fita zuwa kicin suka fara gabatar da komai cikin tsari tareda zumuɗin dawowar mijin nata ita kuma zeeyadah na farin cikin ganin Dawowar Daddyn nasu, a haka har suka gama girkin cikin nutsuwa da aminci bayan sun gama girkin a manyan kuloli na gani na faɗa mom ta kwashe abincin sannan ta kalli Rabe tace "dota kuzo kuje keda Zeeyadah part ɗin Daddy ku gyara sannan ku kwashe womers ɗin nan ku kai kan daining ɗinsa. Da to suka amsa sannan suka tafi cika umarnin mom ɗin.

Kamar yanda mom ɗin ta faɗa hakan ne kuwa ya kasance, sosai suka shiga gyaran part ɗin da dukkan ƙarfinsu tun kafin aci litinin da talata a aikin zeeyadah ta xube akan kujera tace ta gaji, murmushi Rabe tayi sannan ta ci gaba da aikin ba tareda ta huta ba seda ta gama tsaf sannan suka fito zeeyada na kuranta ta da irin zafin naman da mulaikan kedashi, itadai mulaikha murmushi kawai take har suka fice daga falon sannan suka fita

Se wajen yamma sannan jirginsu Dad ya sauka a babban birnin taraiya Abuja, gabaɗaya Ahalin na gidan Edyan ya kwasa a mota da kansa ba tareda guards ba suka tafi except Mulaikha da aka bari a gida don gudun kar dad ya ganta.

Lokacin da sukaje ba ƙaramin farin ciki dad yayi da ganinsu ba sabida yanda yay masifar kewarsu, shigewa jikinsa Zeeyadah tayi tana dariya tace "dad i miss you wllh. Murmushinsa ya faɗaɗa sannan ya kalli mom yace "murja banga mamana ba were is she?

Ɗan jim kaɗan mom tayi don wllh koze kasheta bata san inda Hajar take ba, rabonta da ita tun safe kafin ta tafi office. Murmushi ta ƙaƙalo masa tace " she's in the office...

Taɓe baki Edyan yayi a haka har motocin jami'an tsaron suka iso sannan suka ɗaukeshi tareda yi masa rakiya zuwa gida tareda iyalansa, suna isowa gida aka wangale musu Get motocin suka dinga danno kai kamar bazasi ƙare ba, dad na fitowa daga motar idanunsa suka sauka akan Rabe data leƙo ta windon falon sama. Da sauri ta saki labulan gabanta na faɗuwa.



*NEW DELHI*

Mohad moghandi special Hospital, muzaffar ne zaune bisa wani ƙayataccen ɗaki wanda aka ƙawata da kayayyakin kula da lfy iri-iri, wani ƙasaitaccen gado na hanga daga can gefe wanda moddibo ke kai idanunsa a rufe ruf, a tsakanin bakinsa kuma masuburbuɗar oxygen ce maƙale a fusƙarsa wadda take sauwaqe masa hanyar shaƙar numfashi cikin sauƙi. Ƙura masa idanu muzaffar yayi yana kallonsa cikeda zallar tausayinsa yasa hannunsa ya shafi gefan fuskarsa sannan ya fice daga ɗakin da sauri.

Direct inda aka tanada don biyan kuɗin tiyatar ya nufa batareda ɓata lokaci ba yayi musu transfer Ɗin naira million 5 ɗin da suka buƙata sannan suka bashi racit shedar ya biya yabar gurin zuwa ɗakin da yabar modɗibon, cikin mintunan da bazasu gaza goma ba aka shiga dashi tiyata room ɗin a ƙarƙashin jagrancin Dr. Rahul Gufta da teams ɗinsa.

Semuce Allah yasa ayi a sa'a Dr. Rahul Gufta.


Ako wani lokaci abubuwa da dama kan sauya manufarsu musamman ga zuciyar dake cike da zallar muradi gamida begen akan dukkan abunda take mafarkin samu tareda mallakarsa na har abada, zuwa yanzu baze iya tabbatarwa da kansa irin halin dayake ciki ba hatta jinin dake gudana a jikin kowace gaba ta jikinsa a gauraye yake da wani nau'i na musamman tareda sirki irin na zazzafar soyayya mara misaltuwa.

Amsawa ƙirjinsa yayi da sauri lokaci guda kuma wani irin tsoro ya ɗarsu a saman zuciyarsa , haka kawai seyaji jikinsa yamasa masifar sanyi wanda hakan yasa ya durƙushe a saman gwiwoyinsa tareda dafe saitin zuciyarsa dake fitarda wani irin bugu me sauti, iskar dake bakinsa ya furzar da ɗan sauran guzarin daya rage masa a nitse ya miƙe tareda jan ƙafafunsa da sukai masa wani irin Nauyi harya samu zarafin ƙarasawa bakin gadon da Moddibo ke kwance, hannunsa ya miƙa ya kamo hannun moddibon cikin nasa ya ɗamƙe tareda zaman bisa kujerar dake bakin gadon, a hankali yake iya buɗe bakinsa da nufin yayi masa magana Amma kuma seya kasa sabida yanda maganar dayake son faɗa ɗin tayi masa nauyi, ajiyar zuciya ya dinga saukewa akai akai tamkar wanda ta gwabza tsere da ingarman doki maji ƙarfi.

A tabbas a yanzu kam ya ƙara tabbatarwa da kansa cewar shiɗin baƙo ne akan lamari irin wanda ya samu kansa a ciki, haka kuma da ace yanada yanda zeyi da wannan muraɗin dake addabar zuciyarsa a kowace daƙiƙa ta Rayuwarsa tabbas daya samawa kansa mafita a kai, gabansa ne ya faɗi a karo na biyu daya tuna da batun Auren dake tsakaninta da Bawuro, cikeda zallar tashin hankali ya zare hannunsa daga cikin na moddibo idanunsa sukai wani irin ja.

Wayarsa ce ta ɗauki ruri, a hankali ya zaro wayar tareɗa zubawa screen ɗin wayan manyan idanunsa masu ɗaukar hankalin duk wani me kallonsu, sunam Ummie daya gani yana yawo a saman wayar ne yasa ya ɗaukar ba tareda yayi magana ba. "Assalamu'alaikum. Ummie ta faɗa muryarta ɗauke da Amon murmushi a cikinta .

Wata nannauyar Ajiyar zuciya Muzaffar ya saki har seda Ummie ta ɗan razana kaɗan, cikin yanayin damuwa da zallar kulawa Ummie tace "Sweetheart are you alright?

Kamar zeyi kuka yace "Ummie I'm scared I don't want to lose her!!! I feel like kamar somthing is definitely happen to her Umm..... Kasa ƙarasawa yayi sabida yanda ƙirjinsa yay masa masifar nauyi kamar ze tsage.


Miƙewa Ummie tayi daga zaunen datake sabida yanda hankalinta yay masifan tashi da yanayin muzaffar ɗin tace "look son pls relax don Allah ka nutsu karka sawa kanka damuwa ka kwantar da hankalinka zuwa lokacin dazaka dawo Nigeria insha Allah komai zeyi daidai, ka sa a ranka cewer babu bind ze faruda it se alkhiri kaji ko?

A hankali yake sauke nufshi kimanin lokaci meɗan tsayi can ƙasan maƙoshinsa yace "pls Ummie keep pray for me wllh i don't want lose her idan na rasata wani abu ze iya faruwa dan......."stop saying that son!!!! Are you in your sense? "I don't want you to say anything like that again kaji na gaya maka indai baso kake nima wani abin ya faru dani kafin kai ba. Ummie ta faɗi hakan a matiƙar harziƙe


Kamar zeyi kuka yace "I'm sorry ummie baran ƙaraba. Murmushi ta sakin masa har yana iya jiyo sautinsa tace "that's my darling son Barakhallahu'feekah, ka kula da kanka kaji ko and don't forget to pray ok? Jikinsa a mace yace "ok Ummie bye.

Katse wayar tayi tareda yin shiru tana nazari akan damuwar gudan jinin nata, jikinta ne yayi wani irin sanyi data tuna cewar ɗan nata baƙo ne a cikin al'amarikn daya danganci muradi me haɗe da sirki irin na soyayyah.

Hannu ta ɗaga tace"ya ubangijina ga amanar daka bani nan ta ɗan dana haifa, amatsayina na uwa kuma me rauni banida ikon dazan iya yaye masa damuwarsa komai ƙanƙantar ta sekai Ubangijina, ina roƙonka da sunaye ka tsarkaka mafiya kyawu ya Allah ka sauwaƙe masa samun cikar muradinsa cikin sauƙi ba tareda ya sha wahala kokuma ya shiga wani hali ba. Ummie Ta faɗi hakan tana share ƙwallar data zubo mata a saman fuskarta, sallamar Abie ce ta sanyata saurin goge ƙwallar da sauri sedai dukda hakan seda Abie ɗin ya gani a hanzarce ya ƙaraso kareta damuwa kwance a saman fuskarsa ya zauna daga gefanta yace "Aisha lfy kike kuka? Meya faru dake da harya sakaki zubda hawaye irin haka? Abie ya jera mata tambayoyin duk a lokaci guda.

Dakewa tayi tareda gaiyato jarumta a tareda ita tace "Abdul inajin tsoro kar yaron mu ya faɗa a cikin ramin soyayyar da balallai ya iya fitowa ba, muzaffar ya faɗa a soyayyar wata yarinya wadda ta kasance Bafulatana ce sun haɗu ne a can wata ruga dake cikin jihar taraba sakamakon taimakonsa da mahaifin ta yayi a lokacin dayake dabda rasa rayuwarsa, nan dai Ummie ta sanar da Abie kaf abinda ke faruwa ba tareda ta iya ɓoye masa koda kalma ɗaya ba, ƙuri Abie yayi mata yana kallonta tamkar ya samu Tv harta dasa aya ba tareda ya katseta ba.

Seda ta gama tsaf sannan ya dubeta yace "kina nugin ɓatan da muzaffar yayi tsahon watanni dama wasu ne suke ƙoƙarin halaka min ɗa ba tareda na sani ba kuma shima be sanar dani ba? Dafa kafaɗarsa Ummie tayi cikeda rarrashi tace "ka kwantar da hankalinka Abdul an riga da anyii handling komai ai tunda har Maryama ɗin ta shiga hannun hukuma.

Shiru yayi yana ƙara juya abin a ransa sannan ya dubeta yace "lallai be kamata mu gaza wajen samawa ɗanmu cikar muradinsa na Auren yarinyar dayake so ba Aisha, koda ace a ƙarƙashin ƙasa take bawai a Daji ba ni nan zanje na nema masa Auranta koda ace gabaɗaya abind na mallaka ze ƙare ne gaba ɗaya, tunda har kikaji ya furta miki da bakinsa cewar yanasonta I'm very sure he loves her more than our think, becouse shiɗin mutum ne me matiƙar zurfin ciki akan dukkan lamarinsa tinda har ya kasa ɓoyewa to lallai abin ba ƙarami bane sedai kawai muyi fatan dawowarsa ƙasar lfy.

Da Amin Ummie ta amsa tana me ƙara jinjina lamarin a ranta.


******

Al'amarin gidansu Edyan kuwa sosai rayuwarsu ke tafiya cikeda jin daɗi gamida walwala, lokacin da Dady ya dawo daga America yayi mamakin ganin baƙuwar fuskar dake zaune a gidansa, don haka ya buƙaci da mom ta taro masa taron Ahalin nasa gabaɗaya don yaji ba'asin komai, bayan sun hallara a babban falon na Dady sosai Mulaikha (Rabe) ta tsorata da ganin Dadyn kasancewar bata taɓa ganinsa a gidan ba se yau, ƙanƙame jikinta tayi a jikin mom kamar zata shige jikinta.

A nitse Dady yakai dubansa gareta tareda ajiye News Paper ɗin dake hannunsa sannan ya kalli mom yace "ina sauraronki meye ma'anar zaman yarinyar nan a gidan nan ? Tun kafin mom tayi magana Hajar tayi caraf tace "kaima dai Daddy ka faɗa wllh nima dawowa nayi na sameta a gidan nan, kuma wllh daddy laifin mom ne tun a lokacin da Ya Edyan yazo da ita gidannan naso su korata inda ta fito amma sukaƙi, wllh ranar har Marina Mom tayi akan wannan yarinyar da ba'asan Asalinta ta don kawai ita BAFULATANA CE.

Mari kika ce Mamana? Sure Daddy wllh marina mom tayi akanta don kawai nayi mata tsawa!

A fusace Daddy ya dubi mom yace "anya kina cikin hankalinki Murjanatu da har zaki ɗaga hannu ki mari Mamana sabida tayiwa wannan yarinyar tsawa ? Dad ya faɗa yana nuna Mulaikha dake ƙara ƙanƙame mom jikinta se uban rawa yakeyi.

Dukda cewat batajin abinda suke faɗa sosai sabida ba wani jin hausar take me tsaho ba ta fahimci cewar lallai Dady akanta yake magana.

Wata uwar tsawa daddy ya dakawa Mulaikhan (Rabe) wadda tasa ta sakin mom da sauri ta fashe da wani irin kuka tana kallon mom ɗin yace "gashi nayi mata tsawa Murjanatu nima sekizo ki mareni sabida na ɗagawa ƴar gwal murya. Ya faɗa yana wani hura hanci kamar zeyi aman wuta sabida fushi.

Sallamar Edyan ce ta katse Dady daga faɗam dayake zubawa mom kamar ya Ari baki, a rayuwar dady Allah ya jarabceshi dason Hajar tayanda har baya iya yi mata faɗa idan tayi ba daidai ba don kawai ya sanya mata sunan Mahaifiyarsa wato HAJARAH, Wannan dalilin yasa hajar takecin karanta babu babbaka

Da wani iri sauri Rabe ta miƙe ta nufi Edyan ta faɗa jikinsa tareda ƙanƙameshi ta saki wani sabon kukan daya ƙara ɗaga masa hankali, ƙoƙarin rabata da jikinsa ya farayi amma ina da sauri ta koma bayansa tareda rige gefan rigarsa jikinta na wani irin rawa kamar mazari.

Daga yanayin fuskokin iyayen nasa ya fahimci akwai abinda ke faruwa, dakewa yayi yajata tana turjewa har suka isa falon idanunsa nakan mom da idanunta suka sauya launi sabida ɓacin rai, wllh da ace ba'a gida ta haifi Hajar ba tsaf zatace canza mata ita akai, bata gama dawowa daga duniyar tunani ba ta tsinkayi muryar daddy yana faɗin "tunda abin ya zama Rashin mutunci da ɗibar albarka lallai yarinyar nan tabar min gidana yau ɗin nan base anjima ba tunda har akanta kika sanya hannu kika marar min yarinya, yanzu ke Murja don Allah ko dukanta Mamana tayi ai kya tayata bawai kisa hannu ki mareta b..... "haba daddy don Allah why are you saying that?

Baki Cp ya wangale yana kallon ɗan nasa yace " Au tambayata ma kakeyi Edriss?

"no dad kawai dai gani nai kamar ba'a kyautawa yarinyar nan ba idan aka mata haka, bama wannan ba dad mom fa ita ta haifi hajar bawai Hajar ce ta haifeta ba, shikenan kuma uwa bata da rights ɗin dazata ɗaga hannu ta mari ƴarta se'an mata kashedi don kawai abata dama ta raina mutane? Wllh dad ina jiye maka tsoron ranar daza'a koro maka hajar daga gidan miji sabida baƙin halin da kuma ƙarancin tarbiyar......... "keep quiet Edriss!!!!!! Dady ya katseshi ta hanyar daka masa wata uwar tsawa.

"ohh ai gashi nan kai naga tarbiyar a tareda kai, look I don't want to repeat my word and karka bari raina ya ɓaci maza- maza ka ɗauki yarinyar nan ta barmin gidana yanzu base anjima ba, idan yaso seka idan zaku iya kaita duk inda kukeso amma ba nan ba tunda har sabida ita Murja kike iya marin ƴata kaikuma Edriss kake jayayya dani.... "don girman Allah Dad kayi haƙuri karka yanke hukunci cikin fishi, na tabbata don baka zauna da ita bane shiyasa kake ganin kamar ita ɗin ba'abar a zauna da ita bane dad, amma wllh tafi yaya Hajar halaye masu kyau nesa ma ba kusa ba sannan kuma dad ko kaine kaga abinda yaya Hajar tayiwa baiwar Allahr nan kaida kanka zaka hukunta tat....... Haɗiye maganar Zeeyadah tayi sabida wani ɗan iskan kallo da Dad ke binta dashi

Miƙewa yayi a fusace ya kalli Edyan yace "maza ka ɗauketa ta barmin gidana yanzu base anjima ba, kuma wllh muddin bakayi abinda nace ba seƙaga fushina

Miƙewa Hajar tayi zuciyarta fessss tabi bayan dad, kokaɗanbataji komai ba akan yanayin data saka mahaifiyarta a ciki ba da ƴan uwanta.

Iya ɓacin rai ran Edyan ya gama ɓaci har wani irin ɗaci yakeji a saman maƙoshinsa, kasa cewa komai yayi yaja hannunta sukabar falon zuwa part ɗinsa suna shiga Direct bedroom Ɗinsa ya wuce still yana riƙe da hannunta, zaunar da ita yayi a bakin gadonsa se faman murza idanunta da suka koma kalar ja takeyi sabida kukan datayi, miƙewa yayi zuwa gaban drower ɗinsa ya buɗe ya ɗakko wannan jakar saƙin daya tsinceta da ita sannan ya dawo gabanta ya zauna akan dandiryan ƙasan carpet ɗin tareda zuba mata manyan tsimammun idanunsa Cikin harshen turanci ya farai mata magana donya fuskanci zuwa yanzu tafi ganeshi Sosai akan Hausa yce " tunda muka bugeki da mota naji a raina cewar tabbas akwai wani babban al'amari a tareda Rayuwarki, haka kuma daga yanayin ƙwayar idanunki na ƙara tabbatarwa da kaina cewar lallai a kwai ciwo a Rayuwarki wanda kike ɓoyewa har yanzu kin gaza sanar da kowa. Bazan tilasta ki cewar lallai sekin sanar dani labarin Rayuwarki ba Mulaikha kawai nidai inaso na taimakeki dukda cewar har ynzu bansan wacece ke ba, a shirye nake na fuskanci ko wani irin ƙalu bale a rayuwata muddin hakan zesa ki haɗu da iyayenki no matter what!!!! Ya faɗa tareda ɗora mata jakar Sakin akan ƙafafunta

Jikinta ne yay wani irin sanyi duk a sanadin kalamansa da yay amfani dasu na ƙarshe, lokaci guda taji wani abu ya tsirga mata a tsakiyar ƙirjinta a gameda Edyan ɗin a zahirin gaskiya ta daɗe da bashi wani mashahurin matsayi wanda ya zarta na musamman a cikin zuciyarta tunda Allah ya haɗata dashi a cikin littafin ƙaddarar ta, daƙyar ta iya tsayar da hawayen dake zubo mata bakinta na wani irin vibrateting tace " Sunana Rabi'atou Abubakar Moddibo ne, kuma ni haifaffiyar jihar tarabace, Mahaifina makiyayi ne na taso cikin maraicin Uwa sedai dukda hakan besa Mahaifina ya gaza nuna min ƙauna daga ɓangare biyu ba, ma'ana ya gama cike duk wani ɓangare a gareni dazesa na tuna cewar na rasa kulawar Mahaifiyata. Nan dai ta kwashe komai ta sanar da Edyan har zuwa ranar da ƙaddara rabuwa samu nasarar giftawa a tsakinin Mahaifinta.

Wani irin kuka ne ya kufce mata don haka ta shiga rerawa kamar bazata dena ba, koda wasa beyi yunƙurin hanata kukan ba dinya fahimci a wannan lokacin babu abinda ze sama mata nutsuwa kamar kukan, seda tayi me isarta sannan ya shig ashare mata hawayen yace " it's OK dear insha Allah I will make sure naga kin koma gaban mahaifinki lfy ba tareda wani abu ya sameki ba koda hakan yana nufin bazan dawo namu gidan da numfashi b...... Da sauri ta ɗora hannunta akan pink soft lips ɗinsa tana hawaye tace "stop saying that partner insha Allah babu abinda ze sameka sai alkhairi.

Murmushi yayi me sauti wanda ya ƙara baiyana kyawunsa sannan ya miƙe tareda janyo wata babbar trolly dake ajiye can gefe yazo gabanta ya tsaya yana kallonta ido cikin ido ba tareda ya iyafurta ko kalma ɗaya ba, itama kallonsa take a karon farko a rayuwarta dashi Wani irin abu ne ya tsirga musu a lokaci guda da sauri ta ɗauke idanunta daga kansa ƙirjinta na bugawa da ƙarfin gaske, hannunsa ta tsinkaya a daidai satin fuskarta alamar tazo su tafi ba musu ta ɗora hannunta ya Bisa tattausan hannunsa suka fara tafiya. A bakin ƙofar sukai kaciɓus da mom idanunta duk ya caɓe da hawaye da wani irin mugun sauri ta nufi Rabe ta rungumeta tana ƙara sautin kukanta.



******

NEW DELHI INDIA

Alhamdulillah anyi aiki cikin nasara da kuma sa'a, sosai jikin moddibo ke ƙara samun sauƙi tamkar bashi ba har wani irin haske ya ƙara sabida yanda yake samun kulawa daga masu alhakin akan hakan, sedai har kawo yi wannan lokacin basuyi ido hudu da Muzaffar ba, a lokacin daya farka yaga fararen fata suna kai kawo a cikin Asibitin yayi zaton mafarki yakeyi kokuma ƙiyamarsa ce ta tsaya, shiru yayi yanabin ko wace kusurwa ta ɗakin da kallo har zuwa haɗaɗɗen gadon dayake kwance a kai, shigowar Dr. Rahul Gufta ne ya ƙara firgita tunaninsa musamman dayaga kyawawan mata sanye da fararen kaya a jikinsu ya ɗauka Mala'ikun da akace suna zuwa yiwa mutum tambaya ne a cikin kabarinsa yayinda aka binne shi, da sauri ya rintse idanunsa yana yana ambatona sunayen ubangiji tareda neman sauƙi wajen amsa tambaya😂

Dubashi Dr. Rahul yayi tareda duban Nurse din dake bayansa yace "ta bashi abinci sannan yasha magani. Cikeda girmamawa ta amsa da "ok sir. Juyawa yayi yabar ɗakin yana murmushin ganin tarin cigaban da suka samu a cikin tiyatar zuciyar da sukayiwa moddibon. Da ido kawai Moddibo kebin nurse ɗin a ransa yace "kodai tashi yayi a wata duniyar ta daban Batareda ya sani ba? sedai dukda irin abubuwan dayake facing besa tunaninsa yayi ƙaura daga kan tilon ƴarsa Guda ɗaya ba wato Rabe, a kullum Be taɓa gazawa dayi mata Addu'ar alkhairi ba kullum addu'arsa shine a duk inda take ubangiji ya tsare masa ita da tsarewarsa. Wasu lokutan har kuka yakeyi idan abin ya isheshi

A haka harya kwashe satin biyu cur yana jinya a cikin babban Asibitin dake cikin Birnin New delhi ɗin ƙarƙashin kulawar Dr. Rahul Guftah sannan yasan wanda ya ɗauki nauyin aikin nasa wato Muzaffar, lokacin daya sani seda ya zubar da hawaye masu yawan gaske, da ƙyar muzaffar ya rarrasheshi yayi shiru sannan suka shiga hirar yaushe gamo.

Cikeda kunya muzaffar ya ɗago manyan idanunsa yana kallon Baffa yace "Baba ya Rabi'atou take? Lokacin danaje hankalina ya tashi ban samu zarafin haɗuwa da ita ba. Ya faɗa bakinsa na rawa cikeda tsoron karaya ce masa tayi Aure.

Kafeshi d ido modɗibo yayi take wata sabuwae ƙwalla ta zubo masa cikeda karayar zuciya ya shiga sanarwa da muzaffar ɗin abinda ya faru. Wata irin zabuwa muzaffar yayi jikinsa na wani irin rawa kamar mazari , bakinsa na rawa yace " k...kkkk....kana nufin Matar tawa ce ba'asan inda take ba?

Ya faɗa yanayinsa na ƙara sauyawa kamar wani bugagge

Kallon da moddibo ke masa ne yasashi haɗiye maganar dake maƙale a maƙoshinsa.






Comment
Nd
Share



Don't forget to vote on whatpad 🥰



Sushmah✍️[3/3, 5:38 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


Page :42


*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

*_Allah yayiwa Mahaifin Mamana Rasuwa a jiya 5/12/2020 ina roqonku arziqi don Allah ku sanyashi a cikin addu'oinku ubangiji yay masa Rahama tareda sauran musulmai baki ɗaya Amin😭_*

Banyi Editing ba kuyi haquri👏

____✍️ Daga irin kallon dayake binsa dashi ne yasa moddibo ya fahimci irin zallar soyayya tareda muradin dake cinsa a zuciyarsa tabbas wannan ƙaunar dake gudana a jinin muzaffar ba ƙarama bace ta zarta duk wani hasashensa, amma kuma a zahiri seya basar tamkar be fahimci komai a tareda yanayin nasa ba kokuma inda ya dosa ba, ya jima yana kallonsa daga bisani kuma ya kauda kansa gefe zuciyarsa na bugawa da ƙarfin gaske

rintse idanunsa muzaffar yayi da ƙarfi lokaci guda kuma ƙijinsa ya shiga bigawa da wani irin ƙarfi ji yake tamkar ana janye masa jini da ruwan dake gudana a duk wata gaɓa ta jikinta, se'a yanzu yakejin cewar tabbas be kyautawa kansa ba da har ya kasa fahimtar ma'anar abinda ke gudana a cikin ransa seda lokaci ya ƙure masa, dafe kansa yayi da dika hannayensa biyu tareda zubewa akan wata lallausar kujera dake gefansa.

Wata irin zuface take keto masa dukkuwa da irin sanyin Ac ɗin dake ɗakin, kallonsa kawai moddibo keyi a ransa yana mɗe tausaya masa duk a sanadin halinda zuciyar Muzaffar ɗin ke ciki, tabbas baya buƙatar ƙarin bayani akan irin son da muzaffar ɗin keyiwa ɗiyarsa domin kuwa duk amsar dayake son tabbatarwa da kanso ƙwayar idon muzaffar ɗin ta gama nunawa.

Ajiyar zuciya kawai yake saukewa Akai-akai tamkar wanda ya gwabza tsere da ingarman doki maji ƙarfi, lokaci-lokaci yakan dunƙuƙe hannunsa ya daki ɗaya tafin hannun nasa dashi, miƙewa yayi da nufiknbarin ɗakin da sauri se kuma ya tsaya cak ba tareda ya juyo ba yace "tabbas zan sauke nauyin dana ɗaukarwa kaina bawai a matsayin babban yaya kawai ba Baffa, zanyi hakanne ta wata fuskar daban a matsayin Jajirtaccen masoyi wanda zuciyarsa ke cike taf da zallar ƙauna me haɗe da sirkin muradi a cikinta, zan hakanne tareda yaƙinin sauke nauyina a matsayin mijin Aure ga Rabi'atou!!!!!

Ya faɗu hakan tareda ficewa daga ɗakin cikin wani irin saurin da tunda yake betaɓa sanin yanadashi ba a Rayuwarsa, da ido kawai Moddibo ya bishi harya ɓacewa ganinsa a ransa kuma yana jinjina irin girma da tasirin muradin dake gudana a cikin jinin muzaffar ɗin wanda abu ne mawuyaci zuciyar dake ɗauke da wannan nauyin ta samawa kanta hutu koda na sakan guda ne.

Tausayinsa ne yay masa dirar mikiya lokaci guda kuma ya sanya hannunsa ya share hawayen daya zubo masa na tausayin rayuka biyu, ta wani ɓangaren

Please Login or Register in order to submit comment