Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fito se baza uban ƙashi yake tamkar wanda aka tsamo daga ƙoramar ruwan turare gabaɗaya.

Duk wanda ya ganshi a wannan lokacin zeyi zaton sam ba mutumin ƙasar nigeria bane sabida yafi kamada larabawan yakin ƙasar Misrah (Egypt) shugar dake jikinsa ce kawai zatasa ka fahimci shiɗin cikakken ɗan Nigeria ne.

Yana fitowa parking lot ya nufa ya faɗa cikin wata hamshaƙiyar Bugati baƙa wuluk wadda taji uban tinted kamar bala'i ya figeta @360 se babban filin jirgin dake cikin babban birnin taraiya, yana zuwa befi saura minti biyar jirgin ya tashi ba don haka a gaggauce ya perkar motar sannan ya fito ƙarfe biyar ɗin Asuba na bugawa jirginsu ya ɗaga zuba Tarabah State.




Se muce a sauka lfy Muzaffar ✊












Sushmah💋
[3/3, 5:38 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


Page :38


*_WRITING BY: CHUBAƊO_*


Banyi Editing ba 🙅‍♀️


____✍️Cikin ikon Allah da himarsa suka iso garin Taraba lfy, sedai tunda ya shigo cikin garin taraba ƙirjinsa ke wani irin bugawa wanda shi kansa besan dalilin hakan ba, sedai yafi ta'allaƙa hakan da baƙon yanayin dayake ciki wanda Ummien sa ta fassara masa shi da suna Soyayya, ajiyar zuciya ya sauke tareda shafa kwantaccen lallausan baƙin gashin dake zagaye da kyakkyawar Fuskarsa ma'abociyar haiba da kuma kwarjini

cikin gari ya shiga zuciyarsa a cike fal da tarun abubuwa wanda yasa hakan ya haifar masa da faɗuwar gaba me tsananin gaske, guri ya nema daga geban wani babban titi ya zauna tareda dafe saitin zuciyarsa idanunsa a lumshe, ya jima a hakan sannan ya miƙe ya fara tafiya cikin takunsa na isa da ƙasaita harya isa bakin wani Babban bakin wanda akayi rubutu kamar haka ZENITH BANK.

kuɗaɗemasu yawan gaske ya cira sannan ya fito ya samu shatar wata ƙaramar motar dazata kaishi Gyambu ya shiga ciki ya zauna tareda biyan Driver kuɗinsa ya kuma buƙaci da ya kaishi wani babban super makert ɗin dazeyi siyayyar kayan Abincin, ɗaga masa kai Driver ɗin yayi cikeda girmamawa sannan yaja motar don cika umarni.

A gaban wani katafaren Super maket suka tsaya ya cikin nutsuwa ya fito jikinsa duk babu wani guzari ya shiga ciki ya fara labtar kayan abinci tun daga kan buhuhuwan shinkafa har zuwa kan catons na taliya, seda ya kashe kuɗi sosai ba ɗan kaɗan ba sannan yaje ya biya kayan aka fito masa dasu zuwa mota, taf aka cika booth na motar babu masaka tsinke har seda aka zuba wasu kayan a sit ɗin bayan motar sannan suka kama hanya don gudin karsu ɓata lokaci.

Sunyi tafiya me nisa gaske damkar zasu bar gari sannan suka iso bakin hanyar dazata kaisu cikin Rugar tasu Moddibo, tsayawa da motar Driver yayi sannan ya dubi muzaffar yace "Ranka ya daɗe ta ina kake tsammanin zamu iya ratsawa ta cikin wannan dajin ?

"sannan kuma gurin wa zakace a cikin wannan sunkurun dajin da babu wani bil'adama dake Rayuwa a cikinsa? A haka dai kayi kamada mutum me kamala kuna wanda hankalinsa yake taredashi balle ince ko matsalar ƙwaƙwalwa gareka.

Ɗan jim muzaffar yayi kamar bazece komaiba yace "kaga malam ji nake biyanka nayi? Indai har ba kyauta ka ɗakko ni ba to kayi yadda nace ɗin idan kuma kuɗinne yayi maka kaɗan seka gayamin na ƙara maka.

Washe baki mutumin yayi sannan ga taka motar suka kutsa cikin dajin, ta tsakiyar labin fulani suka dinga raɓawa suna samawa kansu hanya har suka iso cikin tsakiyar rugar, suna faka motar Befi da mintuna kaɗan ba Mazan Garin suka zagaye motar hannunsu ɗauke da manyan makamai.

Sosai Drivern ya tsorata hakama muzaffar amma kumashi seya dake batareda ya nuna tsoron dake taredashi ba ya fito yana kallon screen ɗin wayarsa , cikin harshen fulatanci wanda yafi kamada na zallar ɗan koyo yace "ni baƙon Alkhairi ne a gareku bana sharri ba, hkaa kuma nazo ne don na gana da Malam moddibo.

Take yanayin fuskarsu ya sauya daga yanayin da suke ciki zuwa na tausayi suka dubeshi ba tareda sunce dashi ƙala ba suka buɗa masa hanya ya nufi ƙofar karan dake kewaye da gidan nasu Rabe ya kunna kai ciki, mata ya gani a zazzaune inda su kuma su malam iro suke ƙoƙarin fitowa da gawar moddibbo dake kwance samɓal cikin makara an lulluɓeshi da zani, har suka gama fito dashi daga cikin bukkarsa da aka shiryashi a ciki idanunsa na kansu ba tareda ya motsa ba sabida tsabar tashin hankalin dayake ciki. Bayan sun fito dashi ne muzaffar ya samu zarafin zubewa akan ƙafafunsa dirshen a ƙasa ƙirjinsa na wani irin bugawa.

Banda rawa babu abinda bakinsa keyi so yake yayi magana amma kuma ya kasa daƙyar ya iya ɗaga hannunsa yay nuni da makarar daga inda yake zaune ya buɗe bakinsa dakyar ya haɗo kalmomin dake maƙale a ƙasan maƙoshinsa yace "why Baffah ? "why are you doing this to me? "I said why!!!? Muzaffar ya faɗa da wani irin ƙarfi lokaci guda kuma ya fashe da wani irin kuka kamar mace.


Hakanne ya janyo hankalin jama'ar dake gidan zuwa gareshi gaɓaɗayansu suka kafeshi da ido suna kallonsa.

Babu wanda yace dashi ƙala sabida sam basu shaidashi ba ciki kuwa harda Inna Laure, kallonsa kawai takeyi Idanunta na zubar da Hawaye me matiƙar zafi da ciwo tambaya ɗayace take mata yawo a rai wadda ta rasa amsarta itace shin wanene wannan Matashin ?

Yanaji yana gani su Malam iro suka Raɓa ta gefansa suka fita da gawar zuwa Waje donsuyi masa sallah, ya jima a gurin zaune yana kuka har suka kabbar Sallah still yana zaune ya kasa koda motsin kirki

Shiru yayi ya zubawa ƙofar ɗakinsa idanu nan da nan ya faɗa cikin ƙoramar tunani, da wani irin mugun sauri ya tashi ya fita da gudu zuwa inda Malam iro ke gabatar da Sallar gawar yasa hannu ya fin cike zanin da aka rufeshi dasi, cikin ƙanƙanin lokaci ya saita hannunsa a daidai saitin zuciyarsa yasa hannunsa duka biyun ya fara dannawa da ƙarfi still idanunsa na zubar da hawaye.

Sallame sallar sukayi da hanzari sukayo kansa suka janyeshi daga jikin gazawa kowa na tofa albarkacin bakinsa, masuyi masa kallon mahaukaci nayi haka kuma masu magana ma nayi.

Shidai Drivern da sukazo tare kallonsa kawai yakeyi a ransa yana me tausaya masa, igiya suka samu me kaurin gaske suka ɗaure muzaffar da ita sannan aka samu akayiwa moddibo sallar


Bayan sun idar ne suka fara giji-gijin ɗaukar makarar take sukaga jikin moddibon na wani irin karkarwa, gab aɗayansu jama'ar dake gurin tserewa sukai kowannensu ya cika wandonsa da iska sabida faruwar wannan abin al'ajabi idan kuka cire Malam iro, shine kaɗai be iya barin gurin ba ya tsaya cak yanai masa addu'o'i. Shima alfarmar ilimin Addinin dayake dashi wadatacce ne ya sanyashi tsayawar batareda ya gudu ba, fuzge jikinsa muzaffar yayi da ƙarfin tsiya tareda nufo gurin da wani mugun gudu, kallon Driver ɗin da sukazo tare yayi cikin ɗaga murya yace "matso da motar mukaishi Asbiti.

Dama can drivern ya gama sauke kayan da suka lodo na abinci hakanne ya basu damar saka moddibon a ciki sannan muzaffar ya shiga baya tareda moddibo shikuma malam Iro ya zauna a mazaunin gaba shi kuma Drivern yaja motar da gudun gaske suka nufi cikin garin Gyambu don nema masa taimakon gaggawa daga likitoci.






Comment
Nd
Share


Don't forget to vote on whatpad.







Sushmah 💋
[3/3, 5:38 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


Page : 39


*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Banyi Editing ba🙅‍♀️


____✍️Direct Babban Asibitin dake cikin garin na Gyambu suka wuce dashi cikin ikon Allah a ɗan ƙanƙanin lokaci manyan liƙitocin dake on duty a ranar suka rufu a kansa, sun jima suna kokawa da numfashinsa sannan suka samu nasarar daidaituwarsa, bayan 2hours likitan daya jagoranci lamarin mara lfiyar ya fito sanye da farar labcord ɗinsa wanda gefanta duk yay stain da jini, wata irin zuface kwance a saman goshin likitan alamar sun wahala sosai wajan shawa kan matsalar, a nitse yake takowa cikeda nutsuwa harya ƙaraso inda su Muzaffar da Malam iro ke zaune damuwa fal a saman fuskokinsa ya tsaya ba tareda ya iya furta musu ko kalma guda ba.

Nurse ɗin dake bayan likitance ta maida kallonta ga Muzaffar tareda kafeshi da mayun idanunta kamar zata cinyeshi ɗanye, ganin sam basu lura da tsaiwarsu bane a gurin sabida ruɗun da suke ciki Nurse ɗin tai gyaran murya cikeda gwalangwaso irin na ƴan duniya tace " Ranka ya daɗe Dr. Na magana.

A hanzarce muzaffar ya ɗago manyan fararen Eye ball ɗinsa ya saukesu kan Likitan cikeda damuwa yace "Dr. How is he pls?

Ajiyar zujiya Likitan ya sauke tareda nazartar yanayin muzaffar ɗin sannan yay murmushi yace "is ok dear he is fine Alhamdulillah ya fita daga Haɗari, sannan a kwai mahimman abubuwan daya kamata mu tattauna dakai akan conditon ɗin mara lfyn, muje office . Yana gama faɗin hakan yay gaba su kuma suka mara masa baya

A tsayawa yayi a jikin wata ƙofa wadda akayi rubutu da nau'in bakin ink kamar haka Dr. Fauwaz Qaribullah. Wannan ne ya basu tabbacin cewa lallai nan ɗin shine office ɗin nasa.

A nitse suka shiga office ɗin gabaɗayansu ciki kuwa harda Dr. Fauwaz ɗin zama yayi sannan suma suka yauna tareda fuskantarsa alamar a ƙage suke suji bayanin daze musu ɗin, murmushi yayi kaɗan sannan ya gyara zaman lab courd ɗin dake jikinsa yace "im sorry to say but gaskiya he is in critical condition abu mafi girma ma shine zuciyarsa ta riga ta harbu sakamakon wani tdiro daya bito masa a tsakiyar zuciyar tasa, magana ta gaskiya a yanzu se'an masa Aiki don rabashi da wannan abin cikin sauri a hakan ma idan anyi babu tabbacin cewar ze tashi. Ya faɗa yana kallon tsakiyar ƙwayar idanun Muzaffar wanda tashin hankali mara misaltuwa ya baiyana akan fuskarsa.

Cikeda damuwa kamar ze fashe da kuka yace "pls Dr. Babu wani abu dazaka iya taimaka mana dashi akan condition ɗin nasa? Ɗan jim kaɗan Dr. Fauwaz yayi yace " munada hanya gudaɗaya wanda nake ganin a kwai yuwuwar a dace. Da sauri muzaffar yace "inajinka Dr.

Dr. Yace "ina ganin yanzu zamuyi muku transfer xuwa wani babban Asibiti dake yola im sure of that Idankunje zaku dace. Dakatar dashi muzaffar yayi ta hanyar cewa no Dr. Ka bari kawai nidai alfarma ɗaya nakeso kamin shine ka haɗamin manyan likitocin da sukasan aikinsu wa ƴanda kuma zasu iya taimaka masa kafin zuwa gobe inyaso semu fita dashi india akan batun aikin yanzu bari nayi waya ai mana booking jirgi semu wuce Abuja gabaɗaya kafin goben.

Da wannan batun suka samu matsaya, bayan sun fita daga office ɗin Dr. Fauwaz Malam iro ya kalli Muzaffar yace "yaro taya zan iya yarda dakai kan cewar bazaka cutar da Moddibo ba idan har ka tafi dashi? Hannunsa muzaffa ya kama cikin nasa yace "a halin yanzu bazan iya furta maka komai ba Malam amma abinda na sani shine wajibi ne in biya Baffa alkhairin dayayi min koda kuwa hakan yana nufin gabaɗaya dukiyata zata ƙare ne, ya taimakeni a lokacin danake buƙatar taimako shin laifine dan nima nayi yunƙurin ceton tasa Rayuwar alhalin kuma inada damar yin hakan malam?

Da sauri ya ɗaga masa kai alamar aa bakayi laifi ba, kuɗi masu yawa muzaffar ya zaro ya miƙawa malam yace "don Allah malam ga wannan kuɗin ka kula da duk wata buƙata ta iyalan Moddibo sannan kayi musu dukkan abinda sukeso, kuma ka shaida musu cewar insha Allah Baffa ze samu lafiya har ya dawo musu da ƙafafunsa da izinin Allah, sannan idan ka koma gida ka gayawa Rabi'atou cewar ina gaisheta kuma nan bada jimawa ba zan dawo gareta . Ya faɗi maganar tareda baiyana zallar soyayyarsa gareta

kallon tsaf malm Iro yay masa da dukkan alamu besan abinda ke faruwa a cikin Rayuwar Rabe ba, wata irin zazxafar ƙwallar tausayinsa ce ta zubowa malam iro lokaci guda kuma ya juya yabar harabar Asibitin, tabbas yanzu kam ya shaida wannan matashi babu shakka shine wanda ya zauna dasu har kimanin watanni huɗu a taredasu. Komadai menene yanada yaqinin cewar baze taɓa cutar da Moddibon ba.

tun kafin muzaffar subar gyambu ya ɗaga waya ya kira PA ɗinsa Mubaraq Nuhu yace yayi masa booking ɗin private jet zuwa ƙasar india, cikeda girmamawa ya amsa masa tareda katse kiran, kamar yanda ya buƙata hakanne ya kasance gurin Dr. Fauwaz ɗin shida kansa ya haɗashi da ƙwararrun likitoci tareda mara lafiyan jirginsu ya ɗaga se birnin taraiya.

koda suka iso a ɗaya daga cikin gidajen ma'aikatansu ya sauki likitocin tareda duk wani abu dazasu buƙata sabida mara lfyan dukda cewar basa tsammanin faruwar wani abu mara daɗi a taredashi, shiko daga nan gida ya wuce Direct part ɗinsa ya nufa ya watsa ruwa sannan ya shiga part ɗin mom ya shaida mata cewar zeyi tafiya zuwa india, sosai suka dinga zuba masa adɗu'a ba tareda sun damu da tambayarsa dalilin yin tafiyar tasa ba tunda dama can sunsan yakanje ɗin musamman idan yanada meeting da abikanan kasuwancinsa, ya ɗan jima a nan suna hira sannan ya miƙe zuwa part ɗin Ummie da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga falon wanda keda zuba uban ƙamshin turaren wuta, babu kowa a falon se Baba Hajarah wadda ke kallon film ɗin hausa a tashar Tauraruwa, zama yayi a kusada ita tareda sanya kansa bisa kafaɗunta yace " Me ran Ƙarfe ya kike?

murmushi tayi tace "ina lfy ƙaramin me gida ya naganka haka nan kamar bakajin daɗin? Uhmm lfy na ƙalau wllh kawai dai na gaji ne sosai gashi kuma zanje india gobe insha Allah inada meeting. Jinjina kai tayi tace "to Allah ya kaiku lfy ya tsare hanya ɗan albarka. Da amin ya amsa mata yace "ummie fa? "Yanzu ta shiga ciki

miƙewa yayi ya nufi bedroom ɗin Ummien , a kwance ya sameta saman doguwar kujerar dake ɗakin Direct nufarta yayi yay hugging ɗinta tareda faɗin i miss u My. "katse wayar tayi ta dubeshi tace "ya dai na ganka haka kamar kana cikin damuwa? "no lfy lau Ummie kawai dai kewanki nake tunanin zanyi sabida gobe zan wuce india inada meeting da wasu sababbin masu hannun jari a companyn mu.

nan ma Addu'ah tayita mishi kusan a tare sukai Diner sannan ya fice ya koma part ɗinsa tareda sanya ran cewa insha Allah kafin Abi ya dawo daga kano yabar ƙasar tun kafin ya ɓaro jirginsa...


A gurguje pls

cikin ikon Allah kuwa washe gari da sassafe jirginsu ya ɗaga zuwa Qasar india. Semuce A sauka lfy C.E.O


*_ƁANGAREN GIDAN ME GIRMA C.P KUWA_*


Edyan ne zaune bisa makeken ƙayataccen falons wanda aka ƙawata da ababan jin daɗi na duniya gamida ƙawata guri, kallo ɗaya zakayiwa falon ka fahimci shiɗin bame yasanson shirgi bane ba, sanye yake da farar T-shirt gamida wando treequater wanda ya kasance baƙi wuluk dashi, ƙafafunsa zube kan table ɗin glass ɗin dake ajiye kusa dashi idanunsa a lumshe, turo ƙofar falon tayi tareda ɗan tsayawa kaɗan tana bin ko ina na falon da kallo hannunta ɗauke da littafin da biro kamar zata fashe da kuka, a hankali idanunta suka sauka akan Hansome face ɗinsa ma'abociyar kwarjini gamida Haiba, kafeshi tai da manyan idanunta karona Farko a Rayuwarta dataji tunanin muzaffar ya faɗo mata a cikin zuciya da kuma gangar jikinta Gabaɗaya, takure jikinta tayi guri guda lokaci guda kuma taji sanyin Ac ɗin dake falon yana nema yayiwa duk wata gaɓa dake jikinta illah.

Wani irin daskararren hawayene me cikeda ɗaci gamida Zallar muradi mara misaltuwa ne ya fara kwaranya a kan kyakkyawar fuskarta, sakin littafin tayi ya faɗi a saman haɗaɗɗen kafent ɗin daya zagaye falon ta ko' ina tareda sanya hannunta ta ƙanƙame jikinta gaba ɗaya.

Faɗuwar littafince ta janyo hankalin Edyan zuwa gareta, a hankali ya buɗe limsassun idanunsa masu cikeda da alamar bacci ya daukesu tar a kanta. Ganin hawayen dake zuba a saman fuskarta ne yasa ya mike da hanzari ya isa gareta tareda dafa kafaɗunta duka biyu yace "what's wrong dear? Ya faɗa cikeda zallar nuna damuwarsa gareta.

Kasa amsa masa tai illa ƙara matse jikinta da ta sakeyi guri guda tamkar wadda aka jefa a cikin ƙorar ƙanƙara, lumshe idanunsa yayi ya sake buɗesu akan beauty face ɗinta yace "wllh da kinsan yanda nakeji idan naga hawayenki da bazaki taɓayin shi'awar ki zubar dasu haka a banza ba, zuciyata da duk wata gabar da jijiyoyin jinina kebi sukan ɗauki wani irin zafi wanda ya zarce na tafasashiyan dalma a duk lokacin dana ganki kina kuka, kodan sabida yanda zuciyata ke zafi meyasa koda so ɗaya ne bazaki hana kanki kuka ba Mulaikha?

Kafeshi tai da manyan idanunta tana me nazari akan maganarsa, daga irin kallon da take masa kaɗai zaka fahimci cewa sarai ta fahimci inda kalamansa suka dosa, amma kuma da ace shima ze san irin halinda take ciki a wannan lokaci tabbas dayayi mata uziri koda kaɗan ne, a irin yanda taƙeji a nata ran idan aka misalta da nasa wllh tata azabar ta zarce tasa. Wasu sababbin hawaye ne suka shiga sakko mata babu ƙaƙƙautawa lumshe lumsassun idanunsa Edyan yayi tareda miƙar da ita tsaye lokaci guda kuma a karo na farko a Rayuwarsa ya janyota jikinsa yay hugging ɗinta with so much love and caring. Gabaɗayansu wani baƙon yanayi suka samu kansu a ciki me matiƙar wahalar fassarawa sedai dukda hakan batayi yunƙurin zare jikinta daga nasa ba sema ƙara fashewa datai da wani sabon kukan wanda ita kanta batasan na menene ba.

Bubbuga bayanta ya dingayi a hankali ba tareda yayi ƙoƙarin hanata yin kukan ba, all he know is to let her cry and cry at least she will get some peace of mind akan abinda takeji dukda cewar be san meyeshi ba because har yanzu didn't tell him anything about her story shi kuma sam be tambayeta ba, abu ɗaya kawai ya sani shine a kwai ciwo a cikin Rayuwarta wanda take buƙatar koda so ɗaya ne abarta tai kuka koda kaɗan ne wata ƙila ciwon dake ranta ze rage raɗaɗi.

Seda tai me isarta sannan tayi shiru a hankali ta zare jikinta daga nasa ta kalleshi da idanunta da suka rine zuwa launin na wadda tayi kuka tace "bro Assigment pls.

Hannunta ya kama zuwa tdakiyar falon ya zaunar da ita akan lallausan kafet ɗin yace "bring the book let me see. Ɗan jim kaɗan tayi sabida yanda turancin nasa yaɗanyiwa fahimtarta nauri se kuma ta kalleshi tace "Noi?

Dariya ya sakin mata har seda kyawawan white teeth ɗinsa suka baiyana yace "nace muga littafin naki ?. Turo baki tayi a ranta tace "oh wai maganar ma baza'ayita yanda mutum ze gane cikin sauƙi ba. Hannunsa yasa yaja siririn dogon hancinta har seda ta ɗan saki ƙara sannan ya fara nuna mata yanda zatayi tayi ta fitar da answer ɗin, tunda suka fara taketa faman tura baki ita a dole wai ya takura mata. Bayan sun gama ne ta tattara book ɗin da biro ɗin ta fice daga falon babu ko thanks.

Dariya kawai yayi a ransa yana ƙarajin yarinyar a ransa sosai, haka kawai yakejin daɗin zama da ita sabida yanda wasu abubuwan nata ke yawan bashi dariya, duk daɗewarta a gidan besa ta manta wasu ɗabi'un nata dake nuna ainihin daga ina ta fito ba, a zahiri idan ka kalleta haka zakayi tsammanin itaɗin wayayyiyar mace ce Saɓanin idan tayi magana kokuma ta tafko maka wani shirmen nata me cike da zallar gidadanci, dariyace ta kufce masa daya tuna lokacin daya sameta a zaune dafi'an a saman daining tayi dare-ɗare tana shafa butter a jikinta. A hankali ya saki wani ƙaya taccen murmushi tareda Furta " Funny girl. A haka dai rayuwa ta dinga tafiya a tsakanin su cikeda zallar kulawa gamida nuna mata duk wata soyayya dazata sa ta manta abinda ke Ranta wanda kullum take aikin mafarkinsa.

Zeeyadah ce zaune a gefan gadonsu Rabe kuma tana kwance ta zubama saman ɗakin idanu tana aikin tunani, a hankali taji sallamar mom da hanzari ta miƙe tana mata murmushi alamar ta saba da ita sosai, cikin harshen fulatanci mom tace "dota bazakizo ki rungumeni ba kodai bakiyi kewata bane 2days? Tun kafin ta rufe bakinta ta tafi da gudu ta faɗa jikinta tana ɓoye fuskarta a jikin mom ɗin.

Edyan ne ya shigo ɗakin hannunsa ɗauke da wani kwali ya kalleta yace "Mulaikha come with me I want to show you something special that I Bay it for you I'm sure you will love it. Da hanzari ta saki mom tabi bayansa ba tareda ta lura da irin kallon dasu mom ɗin kebinta dashi ba, a falo sukaci karoda Hajar tana ƙoƙarin shigowa falon da sauri ta ɗaga fararen idanunta tareda washe mata baki tace "welcome beck sister. Hararanta tayi ba tareda ta kulata ba ta wuce tana jan tsaki

Shidai Edyan sam bebi takan wata Hajar ba ya buɗe kwalin ya fito da wani takalimi ƙirar toms me masifar kyau gamida tsada, ƙurawa takalmin idanu tayi kinta a buɗe tamkar taga ktafaren abin al'ajabi, ƙafarta ya jawo ya fara ƙoƙarin saka mata takalmin tayi saurin janyewa tareda fuzge takalmin daga hannusa tana dariya tace "wannan ai ba takalmi bane mudubi ne patner. Ta faɗa tana ƙalla idanunta ta cikin babban ston ɗin dake saman toms ɗin wanda keta baza uban kyalli tamkar ɗanyen daimond 💎

Baki ya saki yana kallonta kamar ya samu tv wani irin masifan burgeshi yaji tayi shiyasa ma ya shagala da kallonta, batareda ya shirya fuskanta abinda zeje yazo ba daga can ƙasan maƙoshinsa yace "I love you Mulaikha i really Love you with all my heart !!

Dakin baki tayi tareda maida kallonta gareshu ta wani irin kafeshi da wani irin mayan kallo wanda har seda yaji jikinsa yayi sanyi, ta ɓangarenta kuma haka kawai taji a ranta cewar kalmar daya faɗa ɗin tayi madifar jan hankalinta becouse ta taɓa jinta a kwanakin baya da daɗewa, seɗai dukda hakan sam bata san me kalmar take nufi ba.

Murmushi yayi tareda Sumbatar gefan kumatunta ya fice daga falon ba tareda ya waiwayo ba, yana dabda fita daga ƙofar falon ya tsinkayi muryarta tace "thank you partner. Be juyo ba ya fice gabaɗaya

Daki ta koma da kwalin takalmin a hannunta ta tarar da zeeyadah na zaine a bakin gado tana amsa waya, itadai bataji ƙarshen maganar da zeeyadah keyi ba taji tace "I love you too dear.

Kafeta tayi da idaninta sannan ta ajiye takalmin a tsakiyar ɗakin ta nufi zeeyadah tareda ɗora hannunta a daman kafaɗunta tace "pls me wannan kalmar take nufi? Cikeda rashin fahimta tace "wani kalma kuma Mulaikha?

"i love you ? Ta faɗa with so much courage. Kallonta kawai Zeeyadah tayi da mamaki kwance a saman fuskarta tace "who told you so mulaikha? Ba tareda ta kalleta ba tace "pa....... Momce ta shigo ɗakin hakanne yasa bata ƙarasa maganar ba ta nufi mom da sauri tareda ɗaukan takalmin tana dariya ta nufi mom ɗin dashi tana nuna mata.......





comment
Nd
Share


Don't forget to vote on whatpad







Sushmah💋
[3/3, 5:38 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


Page : 40-41


*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

*Duk wata Qaddarar dake ɗauke da zallar soyayya gamida muradi me ƙarfin gaske Kan zamewa zuciya Kamar gyambo me matiƙar zafi gamida Ciwo musamman Idan Zanan ƙaddarar rabuwa ya gifta atsakanin masoyan😢.*


*Banyi Editing ba kuyi haquri da typing error*

____✍️Sosai mom ta nuna mata jin daɗinta akan takalmin da Edyan ɗin ya siya mata musamman dataga yanada Mulaikhan ta nuna jin daɗinta sosai akai, kallonta mom tayi cikin ido tace " kince mishi

Please Login or Register in order to submit comment