Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kamar taji abinda yace yasa ta ɗan saki jikinta

Ganin suna shirin ɗaukar hanyar office ɗinsa dake ministry of finance yasa yace "no banan zamu fara zuwa ba School ɗinsu zeeyadah zamu fara zuwa zayi mata registration, cikeda girmamawa wanda kejan motar ya amsa da to ranka ya daɗe cikin mintunan da bazasu gaza 5 ba suka iso bakin get ɗin makekiyar makaranta wadda akayi rubutu kamar haka *_AL-FALAQ INTERNATIONAL SCHOOL_* central Area. Ciki suka shiga suka faka sannan ya fito cikin takunsa na isa sa ƙasaita yana gyara zaman rigar dake jikinsa ya buɗe mata ƙofar ta fito se faman kalle-kalle takeyi ya kama hannunta suka fara takawa a hankali, yanayin yanda take tafiya yake kalli tamkar wadda ake koyawa sabida yanda takalmin ƙafarta ke wahalar da ita sunkuyawa tayi tareda cire takalmin ta ringumesu a ƙirjinta da ɗaya hannun tana jiran su tafi, kalle-kalle ya fara yana sannan ya dubeta yace "ajiye kisa . Kamar zatayi kuka ta kafeshi da ido so take tayi masa magana amma bazata iya ba don batasan me zatace masa ba.

Ganin bata da niyar maganar ne yasa ya karɓi takalmin ya ajiye mata a saitin ƙafarta yace "oya wear it. Har zata turo masa baki se kuma taga ya harareta ba shiri ta fasa. Har suka shiga principal office ɗin hannuta na cikin nasa

Nan da nan ya karantawa principal ɗin ƙudirinsa na sanyata a makarantar sosai shima yayi farin ciki da hakan tareda tambayar sunan ɗalibar, Shiru Edyan yayi yana tunanin sunan daze sanya mata a matsayin na mahaifinta amma ya rasa samun matsaya kawai seya kalli principal ɗin yace "her name is Mulaikha Edyan Edriss. Nan take kuwa akai mata rigista da wannan suna tareda bata Uniform da duk wasu abubuwan da ɗalibi ke buƙata na makaranta.

Nan take ya biya kuɗin komai sannan yay salama da principal ɗin akan gobe zata fara zuwa makaranta inda zata kasance a cikin jerin ɗalibai ƴan jss 1

Koda suka bar makarantar office ya wuce da ita sannan ya haɗa mata tea da kansa daya fahimci tanajin yunwa. Se wajen 4pm ya tashi daga office seda suka biya da Sahad store dake Garki ya jibgar mata siyayyar kayan sawa wanda duk suka kasance dogayan riguna donya fahimci sunfi mata daɗin sakawa sannan suka wuce gida.


****

Gidan Alhaji Abdulwahab kuwa wata irin rayuwa akeyi mara daɗi tamkar ba wannan Ahalin ba wanda suka saba rayuwasu cikin farin ciki da walwala ba, sosai Ummie take ɗaurewa Abie fuska ko part ɗinta ya shigo sam batabi ta kansa balle har maganar fatar baki ta haɗasu, wani irin haushinsa takeji tareda ƙunar zuciya idan ta tunada irin cin fuskar dayayi mata a rayuwa ta hanyar damƙata a hannun hukuma batareda yayi mata uziri ba ko kaɗan, yauma kamar kullum zaune take a makeken falonta suna hira da Baba Hajara Abie ya shigo perlourn, sanye take cikin wata doguwar riga milk colour wadda taji uban stons masu ɗaukar idanu gamida sheƙi, kallo ɗaya zakayi mata ka fahimci ita ɗin ma'abociyar sanya dogayen riguna ce domin kuwa sunfi komai yawa a cikin kayanta, tunda ta kalleshi so ɗaya ta ɗauke kai bata ƙarabi takansa ba waje ya nema ya zauna akan ƴan ubansun royal kujerun da sukayima parlourn ƙawanya sannan ya dubi Baba hajara yace " don Allah Baba bari nayi magana da Aishat.

Baba tayi murmushi tace "to ranka ya daɗe ta faɗa tana miƙewa daƙyar sannan ta fara takawa a hankali tabar perlourn. Tana fita Abie ya miƙe daga inda yake zaune ya dawo kusa da ita tareda sauke Ajiyar zuciya yace "Aisha kowani ɗan Adam a Rayuwa ajizi ne kuma ze iya aikata badaidai ba a kowani lokaci, nasan ban kyauta miki ba ko kaɗan tunda harna kasayin uziri a gareki akan laifinda har yau zuciyata bata gama gamsuwa da cewar kekika aikata ba! Nasan zaki dinga kallona a matsayin mutum me son kansa dayawa amma kuma ta wata fuskar koda kece a matsayina abinda nayi shi zakiyi Aishatou, sannan kuma ni'a tawa wautar ba komai ne yasa na aikata haka ba face zallar sonda nakeyiwa gudan jina tareda ƙoƙarin ganin nayi masa adalci a matsayina na uba a gareshi wanda Allah ya damƙamin Amanarsa... "Hmmm Abdul kenan ni wato ba amana bace a gareka sannan kuma niba iyayene suka haifeni ba tunda har ka iya ɗaukata ka miƙani ga hannun hukumar daba ta ƙasarmu ba duk a bisa zargin na ciyar da ɗanka guba, ni'a zatona koda a labari kaji cewar ni Aisha zan iya kashe koda dabbace wllh zakayi kokwanto a kai tunda har kafi kowa sanin Halaiyata da ɗabi'una Abdul amma se gashi abin takaici harda kai aka ɗaukeni aka ɗamƙani ga hukuma suka azabtar dani duk akan laifinda bani na aikat.......... Wani irin kuka ne yaci ƙarfinta yasa dole tayi shiru ta kasa ƙarasa maganar sabida yanda kukan baƙin cikin abin ya turniƙeta.

Janyota jikinsa Abie yayi tareda haɗeta da ƙirjinsa yanajin wani irin sonta da kuma tausayinsa na ratsa matsa kowani lungu da saƙo na zuciyar sa, wani irin nauyinta da kunyarta yakeji a yanzu musamman idan ya tuna irin ɗumbin halacciɓ da Aishar tayi masa a rayuwarsa, ta sadaukar da abubuwa dayawa na rayuwarta sabida shi ciki kuwa harda gudan jinin tilon ɗanta data haifa a duniya kuma duk tayi hakanne sabidashi a kasalance ya buɗe bakinsa dayayi masa wani irin mugun nauyi yace " Don girman Allah Aisha kiyafemin abinda na aikata a gareki pls karki bari zuciyarki ta samamin wani gurbi na ɓacin rai a cikinta don girman Allah!!!!!

Tureshi tayi daga jikinta tana kuka tace "gurbi dai kace ko Abdul toka sani tun ranar daka miƙani ga hukua zuciyata tayi maka tanadin wani babban masauki zallar tsanar.......... Da sauri Abie ya yunƙura cikin zafin nama ya haɗe bakinsa da nata guri ɗaya. Duk yanda Ummie taso ta ƙwace kanta abin gagararta yayi domin kuwa Abie be mata riƙon wasa ba, nan take dattijon ya shiga sarrafa matarsa cikin salo na ƙwarewa da bajinta a fagen iya soyayyah gamida tattali ya jefa uwar gidan tasa Ummie cikin duniyar gajimaren soyayyarsa ganida begensa. Ganin ze wuce gona da iri ne yasa ta shammaceshi ta fusge jikinta tayi hanyar ɗakinta, yunƙurawa yayi ya bita tana ƙoƙarin kulle ƙofar ya tura da ƙarfin tsiya ƙofar ta buɗe bayan ya shiga ne ya murzawa ƙofar key ya janyota jikinsa yana aikin rarrashi, ganin zata bashi wahala ne yasa ya shiga aikin rarrashin ta wata hanyar daban mesa zuciya ta zagwanye sabida shauƙin so gamida zallar ƙauna mara algus a cikinta, nan dai Abie ya sami nasarar sheƙe zuciyar ummie suka faɗa duniyar Ma'aurata.

Sosai Abie ya fahimci yayi kewar matar tasa tsahon lokaci wanda itama Ummien ta ɓangarenta kusan hakanne a haka dai al'amura suka wakana komai kuma ya tafi daidai kamar yanda yake fata. A haka dai Ummie ta daure ta kuma yafewa mijin nata don koda wasa bazata iya fushi ɗashi ba sam.


Ɓangaren Muzaffar kuwa kwance yake a ɓangarensa ko abinci ya kasa ci sabida tsabar fargabar dayake ciki komai bayajin daɗinsa don hkaa ma be nemi wani abinci ba sabida halinda yake ciki yafi gaban nan, wayarsa dake gefansa ce ta ɗauki ƙara harta katse be kalli inda wayar take ba, seda aka sake kira a karo na biyu sannan ya miƙa hannunsa ya ɗauka tareda karawa a kunnensa batareda ya kalli screen ɗin ba, Muryar Hajar ya tsinkaya ta doki dodon kunnensa tace "Hi sweetheart. Shiru yayi sabida rashin sanin makamar abinda zece mata, kamar zata mai kuka tace" sweetheart are you there? Daƙyar ya Iya buɗe bakinsa cikeda ƙosawa da maganganunta yace "yeah WhatsApp? Lushe idanunta tayi da sauri sabida wani irin daɗi dataji tace "i just call you ne dama to ask you ko kana lfy, I feel like something is definitely wrong with you sweetheart, wllh koda fitar numfashinka ce ta sauya senaji a jikina..... Ta faɗi hakan idanunta na cikowa taf da kwallah.


Shiru yayi yana sauraron ta maganganunta nayi masa yawo a tsakiyar kansa, yau a karon farko yaji cewar hajar ta samu wani ɓangare na daban a cikin ransa dukda cewa hakan ba yana nufin yana sonta bane a'a kawai dai yaji ta bala'in burgeshi ne data fahimci irin halinda yake ciki a maganarsa. Ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfin gaske yace "I'm fine Hajar is just a headache but Alhamdulillah I'm feeling better now. Zatayi magana kenan ya katseta ta hanyar cewa" i will call you tomorrow in the morning Insha'Allah. Ya katse wayar


Washe gari da safe kamar yanda ya mata alƙawari ya kirata suka ɗanyi magana sannan ya katse wajen 8am suka tafi Asbitin gabaɗayansu don Ayi musu gwajin ƙwayar halittar da alƙali ya bada Umarni (DNA TEST) tunda suka fita daga gidan ƙirjin muzaffar ke bugawa da ƙarfi hakama na Mom wadda tun a daren ranar bata rintsa ba sabida tashin hankali, daga ranar da Alƙali ya ɗage zaman shariyar zuwa yanzu duk Mom ta gama Ramewa ta fita haiyacinta kamar ba ita ba se dogon hanci wanda ya fito yay mata ƙwam a tsakiyar fuska. A haka suka isa cikin Babban General Hospital ɗin dake garin na Abuja don tabbatar da abinda sukazo neman.......





Thanks for d du'ah sisters Rabbi yabar zumunci👏



Comment
Nd
Share


Sushmah💋
[3/3, 5:37 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


*_Page:34_*


*_WRITING BY:CHUBAƊO_*


Banyi Editing ba🙅‍♀️


____✍️Jiki babu ƙwari muzaffar ya sakko daga motar hakama Ummie wadda ta kasance ita kaɗaice a motar datake babu kowa ciki se drivern dake tuƙa motar, cikin sa'a kuwa idanunta dana muzaffar suka Sarƙe cikin na juna wanda tunda ya fara mallakar hankalinsa hakan bata taɓa faruwa a tsakaninsu ba, wani irin Amo da soyayyar uwar ce kwance a tsakiyar ƙwayar idanun Ummie wanda sam hakan ya gaza ɓoyuwa.

Take jikin muzaffar ya fara barazanar rawa tamkar ana kaɗa masa gangi, wani irin baƙon yanayi yakeji a cikn jikinsa me wahalar fassarawa a gareshi wanda sam ya gaza fuskantar ma'anar wannan yanayi dayake ciki ɗin, hannunsa mom ta damƙe cikin nasa hakanne ya taka mahimmiyar yawa wajen dawo dashi cikin nutsuwarsa.

A hka suka shiga cikin farfajiyar inda ake gudanar da DNA test ɗin jinin mom aka fara ɗauka sannan aka ɗauki na Ummie da kuma na muzaffar, kasancewar a kwai cigaba yanzu ba kamar da ba cikin Awa ɗaya akai komai aka gama har fitowar sakamakon duka, karɓa sukayi sannan suka fita zuwa motocinsu Ba tareda Ummie ta sake kallon indasu mom da Abie ɗin ke tsaye ba, a yanzu damuwarta ɗayace shine tasan halinda gudan jininta yake ciki wanda sam yaƙi yarda ya haɗa idanunsa da ita tun bayan fitowarsu daga lab ɗin.

Motocin suka buɗe kowa ya shiga sannan suka ɗun guma zuwa faɗar alƙali don yake hukuncin daya dace ba tareda an zalinci koɗaya daga cikinsu ba.

Bayan sun isa Inda za'a yanke hukuncin addu'a alƙali ya fara buɗewa da ita sananna ya bada umarni ga magatakardansa daya karɓo sakamakon Asibitin dake hannun security ɗin da aka haɗasu dashi don gudun ruɗani sannan ya kaimasa shi kuma ya miƙawa likitan dake zaune can daga gefan hannun daman Alƙalin donya tabbatar musu da abinda sakamakon yazo dashi, karɓa likitan yayi tareda warware takardan cikin nutsuwa Seda ya kama nazartar takardun sannan ya dubi alƙali cikeda nutsuwa yace " Sakamokon ƙwayar Halittar farko wanda ke ɗauke da sunan Aisha Muhammad Lamiɗo wanda binciken ƙwayar halitarta ya nuna cewar lallai tanada kamanceceniyar halittar jini da wasu nau'ika wanda yay daidai da ƙwayar halittar Muzaffar Abdulwahab Abdullah saɓanin yanda sakamakon Saratu Ahmadu Bello ya bayar sam babu kamanceceniyar halitta ta jini kota wani abu a tsakaninta da Muzaffar ɗin.

A zabure mom ta tashi lokaci guda kuma ta zube akan ƙafafunta ta fashe da wani irin kuka me masifar ban tausayi, daga yanda take kukan kaɗai zaka fahimci cewar tana cikin gagarumin bala'i mara misaltuwa. Sosai take wani irin kuka kamar zata shiɗe da wani irin hanzari kamar an mintsineta ta miƙe ta isa gaban Muzaffar ta zauna tana gunjin kuka tace "shikenan ya tabbata kaiɗin Ba ɗana bane Muzaffar?!! Mom ta jefo masa tambayar yayinda idanunta ke zubar da hawayen tausayin kanta da kuma makomarta.

Toshe mata baki muzaffar yayi da sauri idanunsa a cike tab da ƙwalla shima yace "don't say that Mom. Kema mahaifiyata ce tunda kece kika raineni tun ina cikin tsuma kuma kikaci gaba da wahala dani tun daga yarinta na har zuwa girma na, duk wata wahala da uwa keji a lokacinda take rainon ɗanta kinsha dani mom haka kuma Allah shikaɗai ne masani aka lokutan dana dinga hanaki bacci sabida kukana tun ina jariri harna mallakin hankalina. A cikin jerin nauyin larurar rainon da duw wata uwa keyida ɗanta kinyi dani cikina ne kawai baki ɗauka ba tareda ciwon naƙudar haihuta, don haka wllh kema uwace a gareni mom don Allah karki sake bari bakinki ya furta cewar keɗin ba mahaifiyata bace!!!!!! Ya faɗa yana sakin wani irin marayan kuka me matiƙar taɓa zuciya.


Duk ilahirin jama'ar dake falon kuka suke na tausayin Rayukan guda biyu idan ka cire alƙali tareda muƙarrabansa, ita kanta Ummie kukan take tareda jin wani irin tausayin abokiyar zaman nata Saratu na ratsa duk wata gaɓa ta jikinta.

Baba Hajara ma kukan takyi saɓanin maryamu da idanunta ke soye tanabin kowa da kallo.

Bayan lafawar komai ne alƙali ya tabbatar da hukunci cewar Muzaffar ɗan Aisha ne ba ɗan Saratu ba kamar yanda duniya ta ɗauka, a karon farko a rayiwar Fadilah taji cewar dama ace Muzaffar yayanta ne kamar yanda take kallonta a shekarun baya lallai a yau kam ta fahimci wani abou a tareda ɗan uwan nata, ba komai ta fahimta ba illa zallar ma'anarsa da kuma irin kulawar daya dinga bata don ganin ta zama mutuniyar kirki wadda zata sanya mahaifansu Alfahari kamar ƙanwarta zainab. Ta daɗe tana kokwanto akan wasu ɗabi'un nasa dayake nunawa ga duk wanda Allah ya haɗashi zama ɗashi, mutum ne shi very friendly and social Ashe duk wannan ɗabi'un nasa gado yayi daga mahaifiyarsa. Wani irin kuka ne ya kufcewa Fadilah tareda dana sanin abubuwan data dinga aikata masa don kawai taga ta daƙile tauraronsa a idon duniya


Gyaran murya Alƙali yayi tareda gyara glashin dake idanunsa ya kalli Ummie yace "a lokacin da kika kammala dafa Abincin da kika sauki Muzaffar dashi shin kin matsa daga kicin ɗin ko daidai da second ɗaya?

Da sauri Ummie ta kalleshi se kuma tayi shiru tareda kallo gefe guda alamar tanason ta samu damar tunawa cikin sauƙi, da sauri ta kalli Alƙali tace " Ban motsa naje ko ina ba seda a lokacin danagama kwashe abincin a cikin wormers nasa Maryamu ta kwashe taje ta jera kulolin akan daining ta faɗa tana kallon Maryamu wadda wani irin gumi ya fara yanko mata.......






Comment
Nd
Share








Sushmah💋
[3/3, 5:37 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


Page :35


*_WRITING BY: CHUBAƊO_*


___Kafeta da ido Alƙali yayi take Maryamu ta ida fita cikin duk wata nutsuwarta can kuma seta fashe da kuka tana kallon Alƙali tace "Ranka ya daɗe don girman Allah kaimin Rai karka hukuntani da abinda bazan iya jurewa ba wllh tsautsayi ne yasa na aikata hakan. Maryamu ta faɗi hakan tana kafeshi ida ƙananun idanunta se kuma can ta bushe da dariya hartana neman shiɗewa tace "Haka kakeso kaji nace ko Alƙali?

Wani ɗan iskan murmushi ta saki sannan ta tacigaba da cewa"wannan kukan dakaga inayi bana komai bane face na zalar baƙin ciki da namar cewar haƙata bata cimma ga ruwa ba tunda har ban samu nasarar dazanga bayan Aisha ba sabida tsabar tsanar danayi mata, a Rayuwata idan akwai wanda na tsana fiyeda mutuwata to wllh Aisha ce dukda kasancewarta mutuniyar kirki hakan besa na taɓajin ƙaunarta a raina koɗa kimanin girman ƙwayar zarra ba. Naso ace na samu nasarar kashe muzaffar kodan a yankewa Aisha hukuncin Kisa ta hanyar Rataya kokuma a jefata cikin babbar kurkun da zata haɗu da bala'in dazefi ƙarfinta a ƙarshe harma ya zama ajalinta amma kuma kash se gashi ta fita cikin sauƙi daga cikin ramin muguntar dana gina mata.

Gabaɗaya falon kallonta akeyi especially Ummie da idanunta suka firfito sabida tsabar mamakin kalaman na maryamu, wani irin ƙululun abu ne ya taso mata ya tsaya mata a maƙoshinta sabida yanda yawun bakinta ya ƙafe daƙyar ta iya haɗo kalaman da suka rage mata akan harshenta tace "Maryamu me nayi miki kekuwa a Rayuwa da har zakiyi min irin wannan gagarumar tsanar?

Murmushi maryamu ta saki wanda iyakarsa laɓɓanta wanda yafi kamada na zallar tsana mara tushe balle makama tace "wllh bakiyi min komai ba Aisha Hasalima se alkhairi da kikayi min a Rayuwa tareda duk wani ma dake kusa dani, kawai dai laifinki ɗayane a gurina shina na tsaneki kuma bana ƙaunarki wannan kawai shine dalilina kuma wllh na ƙudurtawa zuciyata cewar muddin ina numfashi a doron ƙasa tofa senaga bayan.....

Saukar wani lafiyayyen mari Maryamu taji a saman fuskarta wanda yasa ba shiri ta haɗiye maganar datake faɗa tareda zubawa wanda ya wanke mata fuska da marin, tun kafin ta ida ƙare mata kallo ta sake ɗauketa da wani hamshaƙin marin wanda yasa kunnuwanta suka toshe kimanin wasu mintuna sannan ta nunata da yatsa tace "Amma kedai wannan mata anyi cikakkiyar shaiɗaniya kuma butulu mara tabbas, lallai keta musammance a cikin jami'ar bada horo ta musamman tareda ƙwarewa a fanin Butulci da kuma cin amana, koda yake banyi mamaki ba idan akace gabaɗaya shekarun nan naki sun zama na banza shiyasa tunda idanuna suka sauka a kanki naji cewa har cikin zuciyata bana ƙaunarki ashe abinda ban saniba shine keɗin gabaɗayanki tamkar tauraruwa me jela kike wadda ganinki sam ba alkhairi bane.!!! Fadilah ta faɗi hakan tana wani irin huci kamar zata cinye Maryamu ɗanya.

Itadai mom gabaɗaya bin Maryamu take da kallo yayinda hawayen idanunta suka tsaya cak lallai yau kam ta yarda da cewar inda ranka kasha kallo a duniya, lallai duk tsiyarka a doron ƙasa to wllh a kwai mafiyinka a komai walau alkhairi ko sharri mom bata samu zarafin magana ba Alƙali ta buga gudumar tabbatar da hukuncinsa don kowa ya nutsu kuma ya bada hankalinsa don sauraron hukuncin daze yakewa maryamun

Alƙali ya nisa yace "bisa dubada hujjoji tareda iƙirarin da maryamu tayi na yunƙurin kashe muzaffar Abdulwahab Abdullah tareda iƙirarin cewar Setaga bayan Aisha Muhammad Lamiɗo don haka wannan kotu me alfarma ta yankewa Maryamu hukuncin life in prison har ƙarshen Rayuwarta kamae yanda hukuncin yazo a cikin littafin kunɗin tsarin hukuncin mulkin Nigeria. Ya faɗa tareda buga wannan guduma sannan ya bada umarni da akama Maryamu doka ta fara aiki akanta daga wannan rana

Wani Uban ihu Maryamu ta zunduma tareda fuzgar biron dake gaban aljiun Rugarsa tayi kan Ummie gadan-gadan har tana haɗa hanya sabida muguwar zuciya, da wani irin mugun zafin nama Muzaffar ya ture Ummie gefe Tayi baza zata Faɗi Abie ya tareda da hanzari ta faɗa jikinsa hakanne yayi daidai da saukar biron da Maryamu tai niyar cakawa Ummie a gefan hannunsa na dama take jini ya ɓalle ya fara zuba, kamata sukai da ƙarfin tsiya sukai waje da ita inda motar tafiya prison ɗin take cikin muntuna da bazasu gaza 10 ba sukabar harabar kotun da ita se Babbar Prison ɗin da ake adana manyan shahararun ƴan ta'adda waƴanda aka yankewa hukuncin kisa dake babban birnin na taraiya Abuja.

Da hanzari Ummie ta fuzge jikinta daga na Abie ta nufi muzaffar tareda sanya hannunta ta danne inda jinin ke zuba hawaye na sakko mata, yau a karon farko a Rayuwarta hannunta ya taɓa jikin Gudan jininta muzaffar tun bayaɓ shekara 35 a lokacin yana jariri, wani irin Abu ne me kamada nau'i shaƙuwa gamida zallar ƙauna da soyayyar ɗada Uwarsa tana Ratsa duk wata gaba ta jinin dake gudana a jikinsu, tabbas a yau ya gamsu da cewar Ummie itace Mahaifiyarsa because he feel something about her as a mother saɓanin mom dabe taɓa jin irin wannna shauƙin a tareda ita ba, Ashe dama wannan nutsuwra dake ratsashi a wannan lokacin a sanadin taɓashin da Ummie tayi shine abinda ya rasa a rayuwarsa tsahon shekara 35?

Janyo Ummie yayi da hanzari ya Rugumeta lokaci guda kuma ya saki kuka tareda kwantar da kansa a kafaɗunta ya shiga rera sabon kuka tamkar wani ƙaramin yaro, shafa bayansa kawai Ummie takeyi itama hawaye nayi mata Ambaliya a saman Fuskarta

Gabaɗaya falon ficewa sukai duk girmansa ya kasance daga Muzaffar se Ummie kuka kawai yakeyi tana shafa bayansa ba tareda ta dakatar dashiba sabida a wannan lokacin babu abinda yake buƙata sama da hakan da ƙyar ya iya buɗe bakinsa muryarsa na Cracking yace "Ummie why? Why Ummi....... Gabaɗaya yama kasa magana sabida tsabar yanda kukan yaci ƙarfinsa, still she's tapping his shoulder hawayenta na ƙara tsananta zubowa


Ummie ƙara rungume ɗannata tayi cike da so ganida zallar ƙauna,
Seda suka dauki lokaci me tsayi a haka babu Wanda ya samu zarafin magana

Duk abinda ke faruwa a tsakanin Ummie da ɗan nata Fadilah na zaune na kallonsu itama tana hawaye sabida tsabar yanda suka bala'in bata tausayi it almost 35 years Rabonda yaji ɗumin jikin mahaifiyarsa, A hankali Fadilah ta sakko ƙasa daidai inda ƙafafun Muzaffar batareda tayi magana ba ta wani irin fashe da kuka tareda ficewa daga falon da saurinta, wani irin kunyar Muzaffar takeji bisaga abubuwa na rashin kunya da ƙiyayyar data dinga nuna masa mara tushe takeji se'a yanzu ta fahimci cewar Ashe ba tsanarsa tayi ba kawai dai kishi takeyi dashi akan abinda take ganin nata ne ba nasa ba wanda tafi dan ganta hakan da ƙuruciya gamida wauta, harta kai ƙofar fita daga falon se kuma ta tsaya Chak lokaci guda kuma ta juyo tana kallonsu tace " haƙiƙa ina me jajanta muku akan abinda ya Sameku dakai da Ummie yaya Muzaffar Haka kuma ina me yi maka addu'ar alkhairi a koda yaushe sbda kai ɗin ɗan uwa na ne guda ɗaya tilo, wanda kaf duniyar nan bamuda kamar ka nasani wata rana dole Kaine zaka zama uba a garemu gaba ɗaya, tunda Uwata ta haifeni ban taɓa jin kunya irinta yauba danake tsaye a gabanka nake kuka yaya muzaffar! Yaudai kam na yarda da maganganunka da kake gayamin kullum cewar idan har ban gyara wasu abubuwan na Rayuwata ba tabbas wata rana zanyi nadama to yaudai kam da alama wannan ranar ce tazo min tunda har na fahimci kuskurena tun kafin lokaci ya ƙuremin.

A madadin Mahifiyata dani kaina Don Allah Ina me roƙon ku afuwa dakai da Ummie akan abinda muka aikata muku don Allah yaya muzaffar ka yafe mana plsss. Ta faɗa tana zubewa akan gwiwoyinta still tana maganar tana hawaye.

A hankali ta ɗaga jajayen idanunta ta kalli Ummie tace " haƙiƙa kin cika Uwa wadda ta cancanci da a yaba mata, tunda har kika Iya sadaukar da ɗanki guda ɗaya tilo dan kawai ki sanya mikinki farin cikin wllh dik inda uwa ta gari Takai to kinkai a kiraki da wannan suna Ummie, naso ace ina ɗaya daga cikin waƴanda suka fito daga cikin cikinki tabbas danayi alfahari dake a matsayin Uwa.
Tana kaiwa nan ta miƙe ta fice daga fallon tana me zubar da hawaye

A wannan rana muzaffar kwanan farin ciki Yayi, hakama Ummie da Abie ta ɓangaren Mom ma kusan hakane ko babu komai yanzu tayi karatun tanutsu da al'amarin Rayuwar duniya, haka kuma ta fahimci cewar lallai Aisha ta musamman ce tunda a

Please Login or Register in order to submit comment