Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

look don't cry please just eat. Taɓe baki tayi tana wani mirza ido. Ganin dayay bata da niyan karɓa ne yasa ya matsa dabda ita ya fara bata abincin ta cokalin tanaci tana zubarwa a haka haraya gaba bata ya ajiye flet ɗin yace "barin je na dawo ko?

Da wani irin mugun sauri ta diro daga gadon ta riqe hannunsa gam tana hawaye a haka su mom da Dr. Suka shigo ɗakin. Bayansa ta koma da sauri tana ɓoyewa alamar batason mutane sosai

Murmushi mom tayi tana kallonta cikeda so sannan ta maida kallonta ga Edyan tace "Dr. Ya bada takaddan sallama se kuma drugs daya rubuta kuma suma mun siyo mata yanzu gida zamu wuce kawai. Murmushi kwai yayi yace "ok mom muje. Ya faɗa yana riƙe da hannunta

Har sunkai ƙofa ta fizege hannunta ta dawo ta ɗauki wannan jakar da Moddibo ya bata sannan ta dawo ta riƙe hannunsa suka fita.


Wajen shiga mota ba ƙaramar ɗirama akayi da ita ba ihu ta dinga zuba musu seda Edyan yay dagaske sannan ta yarda ta shiga suka tafi gida gabaɗaya, duk a tsorace take kallonsu kawai take itako zeeyadah gabaɗaya tausayin yarinyar ya gama cika mata zuciya.


India🇮🇳

A kwana a tashi babu wuya a gurin Allah a ɗan wannan tsukun lokacin abubuwa dayawa sun faru masu daɗi da marasa dadi, a ɓangaren Muzaffar kuwa sosai yake samun sauƙi dukda irin ɓarnar da poison ɗin yayi masa a ciki, ada sam baya iya zama amma yanzu kam yana iya zama da kansa harma yayi tafiya koda bame tsaho bace. Sosai hkaan yawa Su mom da Abie daɗi har hakan ya kasa ɓoyuwa akan fuskokinsu.


Bayan sati biyu da samun lfyar muzaffar Muhammad Karim Ahmad ya tura case ɗinsu zuwa Nigeria tun kafin su dawo ƙasar aka fara bincike akan case ɗin kasancewar Ummie ta amsa Laifinta na cewar ita ta bashi gubar da hannunta yasa al'amarin yazowa masu yanke hukuncin da sauƙi, wahe gari da sassafe jirginsu ya ɗaga zuwa Nigeria.

Sosai Ummie ta fita daga haiyacinta kamar ba ita ba, tun Doguwan rigar da aka Kamata da ita sanda abin ya faru har yanzu itace a jikinta idanunta duk sun zurma sunyi ciki tamkar bana Hajiya Aisha ba mata ƴar ƙwalisa da son kwalliya a haka aka sake jefata cikin magarƙama aka rufe.


Mom sun koma gida lfy kullum.ƙara tattalin ɗanta takeyi kasancewar Zaynab sun koma makaranta ne yasa komai yazo Musu da sauƘi, komai nasa mom ce keyi da kanta wasu lokutan abin har yana bawa Abie mamaki, Baba Hajarah ma ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba santa tayi arba da Muzaffar gabaɗaya ya rame yayi duhu kamar bashi ba, kuka ta dingayi itama daga bisani kuma ta haƙura tacigaba dayi masa addu'o'in Alkhairi da kuma na samun lfy.

Washe gari da safe mom ta kira Baba Hajara tazo ta sameta a falo tareda maryam me aikin Hajiya Aisha a zaune, da girmamawa Baba Hajara ta gaida Momy sannan ta sunkuyar da kanta

Mom ta kalleta tace "Hajara ga maryam nan zaku zauna tare kuci gaba da gudanar da hidimomin gidannan don Allah seku haɗe kanku kuma ku zauna da juna lfy.

Murmushi Baba Hajara tayi tace "to Hajiya insha Allahu. Mom ta kalli maryam tace "ki ɗauki kayanki ki bita zata nuna miki ma saukinki. Da to Maryma ta amsa sannan ta miƙe tabi bayan Baba Hajara suka nufi ɓangarensu.

Tunda Abie ya dawo daga india be samu ya zauna ba sabida ciku2 shariyarsu da Ummie, so yake ayi abin bisa sirri don bayaso kimarsa ta taɓu a idanun al'uma dakuma na ƴan jarida kasancewarsa babban mutum kuma wanda ƙasa kejidashi. Be wani sha wahala ba me shariya ya amince da batunsa na mayar da shari'ar tasu ta sirri because this is the only thing dayake ganin ze iyayiwa ummie a rayuwarta don bayaso ta wulaƙanta a idon duniya har yanzu yana ƙaunarta a cikin zuciyarsa ƙauna me tarin yawa bata wasa ba.


Washe gari Ya kama litinin ne kuma a ranar shariyar zata fara, Mom ce ta fito cikin shigarta na alfarmar a nitse ta gama sakkowa daga sters ɗin sannan ta samu Fadilah a falo tana kallon news.

Da kulawa mom ta kalleta tace "dota idan kin tashi kije ki duba yayanki sannan kisa Hajara ta dafa masa abu meɗan ruwa2 wanda zeji daɗin ci seki kai masa kinji ko?

Fadilah tayi musmushi tace "ok mom sekin dawo Abie ya shigo tun ɗazo da alama keyake jira. Shafa kanta mom tayi tareda sumbatarta sannan ta fice a hanya sukaci karo da Baba Hajara ta dawo daga rabawa masu gadi da masu yankan flowers abinci.

Cikeda girmamawa suka gaisa sannan tace "to semun dawo Hajara. Da murmushi a akan fuskar baba hajara tace "hajiya yau kece da fitar sassafe?


Tsayawa mom tayi cak sannan ta juyo da murmushi tace "wllh fitar ta dole ce kotu zamu kinsan mun shigar da ƙara akan Aisha.


Take gaban Baba Hajara ya buga da ƙarfi tanaji tana gani a haka mom tayi gaba ta barta zuciyarta na dukan tara2.








Thanks 4d love sisters naga addu'o'inku Allah yabar zumunci👏




Comment
Nd
Share



Sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


*_Page :27_*


*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

BANYI EDITING BA🙅‍♀️


____✍️Wata irin zuface ta shiga yankowa Baba hajara tamkar an kunna fanfo da ƙyar ta iya ƙarasawa ɗakinsu tana ɗingisawa sabida ƙafar dake ɗan mata ciwo ta zauna daga gefan katifarta kasancewar ita nata katifan a ƙasa yake sabida yanayin jikinta, duk sanyin Ac n dake ɗakin nemassa tayi ta rasa sabida tsabar rashin kwanciyar hankali, maryam ce ta shigo hannunta ɗauke da faranti ta takeshi da soyayyoyar shinkafa wadda taji uban kayan lambu se baza ƙamshi takeyi, harta zauna tana kallon baba sabida yanda taganta duk ta fita haiyacinta.

Ajiye Abincin tayi tareda matsowa gareta tace "Baba lfy kuwa nagani haka duk kin fita haiyacinki?

Hawayen da suka samu zarafin zubo mata Baba ta goge sannan ta kalli maryam tace "wai nikam meyake shirin faruwa a gidannan ne tsawon shekaru ina cikinsa bantaɓa cin karoda abinda ya ɗagamin hankali kamar wannan ba, wllh maryamu inajiyewa kaina tsoron abinda zeje yazo a cikin wannan iyalin danake kallo tamkar nawa!!

Yanzu Hajiya Saratu take sanar dani cewar wai kotu zata tafi da sassafen nan haka kawai sena samu kaina da rashin kwanciyar hankali duk a dalilin jin hakan.

Sakin baki maryam tayi tana kallon baba harta gama magana sannan tace "Baba karkice min bakuda labari akan abinda ya faru bayan zuwan ƙaramin megida ƙasar india? To idan kuwa har Hajiya bata sanar daku ba tabbas kirkinta da kuma sanin yakamatanta ya wuce duk yanda ake zatonsa.

idan har zan iya tinawa daidai Baba yau shekarata Talatin ina tareda Hajiya Aisha inai mata aiki tun tana ƙasar nan har Allah ya ɗagata daga nan muka koma India tare ban taba samunta da wani hali na rashin kirki ba kokuma kyautatawa ba komai ƙanƙantarsa, haka kuma duk wanda Allah ya haɗata zama dashi tanayin iya ƙoƙarin wajen kyautata masa koda kuwa maƙiyinta ne shi, Amma abin mamaki se gashi an kama Hajiya Aisha dumu2 da zubawa ƙaramin megida guba a cikin abincinsa da kuma abin shansa, ni kaina na girgiza a lokacin da abin ya faru harnake ganin kamar sharri akayi mata badan ina gurin abin ya faru ba wllh zance ɗora mata kawai akayi Baba.

Amma se gashi ta faɗa da bakinta cewar itace ta zuba masa guba don kawai ta kawo ƙarshen nunfashinsa wannan shine maƙasudin baiyanar mugun halinta a gaban kowa, nafi zargin cewar don kawai bata samu haihuwa da Alhaji bane shiyasa ta gammaci data kashe musu ɗa donta huce haushin wannan zafin. Maryam ta faɗa hawaye na zubo mata

Shiru Baba tayi tana kallonta haka kawai setaji sam zuciyarta ta kasa yarda da wannan laifin da ake zargin Hajiya Aisha dashi, wllh ko a gaban uban waye zata iya shedar ta kan cewar bazata taɓa iya aikata wannan gagarumin laifin ba koda kuwa ga dabba ne ba mutum ba, a hakan kuma wai muzaffar gaskiya itakam tana tantama akai koma menene zata zauna da Alhaji tasan se sanar da ita gaskiyar lamarin kuma tasan ze saurareta tunda uwa ya ɗauketa ba ƴar aikin gidansa ba.

Murmushi Baba Hajara tayi tana kallon maryam tace " wllh maryam kin ban mamaki da har kika bari zuciyarki ta iya faɗawa cikin zargin matar data shekara Talatin tana tallafawa Rayuwarki ta ɓangarori da dama batareda ta nuna gajiyawarta ba koda so ɗaya, nayi mamaki sosai da kika iya yarda da wannan zargin a lokacin da aka baiyanashi kunnuwanki sukajishi tabbas kinji kunya maryamu. Baba ta faɗi hakan tana bin maryam da wani irin kallo wanda yasa taji ta muzanta.

Wani irin sanyi jikin maryamu yayi sabida kalaman da baba ta faɗa to amma ya zatayi dole ne ta faɗi abinda idanunta suka gane mata a wannan rana, don Hajiya Aisha ta taimka mata a rayuwa hakan baya nufin zata iya zuba idanu ta kalleta a yayinda tayi yunƙurin kashe ɗan mijin kishiyarta Hajiya Saratu.

a haka hirar tasu ta tashi jikin kowa babu ƙwari, suna nan zaune Fadilah ta shigo ɗakin kunnenta ɗauke da waya ta kalli Baba tace "mom tace ki dafawa Muzaffar farfesun kifi da kuma abinci meɗan ruwa2, and then zaki iya haɗa masa da wani abin meɗan daɗi haka. Ta faɗa tana kallon Baban tana wani yatsin fuska

Murmushi Baba tayi sannan ta miƙe tace "zama be kamani ba miji nacan ciki babu komai bari inje na sama masa abu meɗan galmi-galmi ya samu ya tauna. Ta faɗa tana miƙewa da salati ɗauke a bakinta tayi kicin tahau hidimar girkawa muzaffar abinda zeci.

Bata wani ɗauki lokaci ba ta kallama komai se baza ƙamshi farfesun kifin yakeyi tamkar ba tsohuwace ta girkashi ba, sosai baba ta ƙware a fagen dafa abinci shiyasa tai fice a cikin gidan musamman a gurin Muzaffar indai ba ita ta girka abinci ba to wllh lami ne a gurinsa shiyasa yake sonta sosai.


Da yammaci wajen ƙarfe 5pm Muzaffar dake tafiya a duke sabida yanayin condition ɗin dayake ciki ya isa katafaren garden ɗinsu wanda aka ƙawata da duk wani abu na jin daɗin Rayuwa da ɗebe keywa ya zauna akan ɗaya daga cikin fararan kujerun da akayiwa ado da jajayen duwatsu masu matiƙar sheƙi da ɗaukar ido dake maƙotaka da katafaren swimming ɗin dake gurin, gefe kuma wasu fulawoyi ne masu fitarda wani irin nau'in ƙamshi wanda yafi kamada na musamman gamida sanya nutsuwar zuciya.

Miƙe dogayen ƙafafuwansa yayi kan kujerar tareda ɗora zara2 dogayen yatsunsa a saman ƙirjinsa tareda lumshe tsumammun idanunsa yay shiru yana nazari akan jarrabawar data sameshi a ƴan kwanakin nan, kokaɗan bayaso a sanadinsa Abie ya rabu da matar daya daɗe yana tareda ita morethen 35years don kawai tayi yunƙurin kasheshi, komadai menene a shekarun baya ta wahalta masa a lokacin dayake yaro da ƙarfin jikinta dakuma bakin aljihunta dole tunda ta aikata hakan tanada wani ɓoyyayan dalilinta dayasa ta aikata hakan. Wani siririn tsaki yaja a lokacin daya tuna maganar kotun dazasu sake shiga sati me zuwa wanda daga shine Hajiya Aisha zata fuskanci hukunci, gyara zaman kansa yayi bisa lallausan hannun kujerar dayake kai a haka daddaɗan yanayin dake gurin ya fara tasiri a jikin kowace gaɓa ta jikinsa lokaci guda hakan ya zama tamkar wata ilhama ne dake jan zuciyarsa zuwaga Fulani girl ɗinsa,

lumshe manyan idanunsa yayi tareda buɗesu lokaci guda akan korayen tsirran da suka ƙawata gurin ya saki wani kyakkyawan murmushi wanda hakan yasa dimples ɗinsa both side suka lotsa a tare. A hankali can ƙasan maƙoshinsa yace "i miss you babe I miss everything about you my poor babe . Ya faɗa yana gyara zaman hannayensa dake zube saman ƙirjinsa.


wata danƙareriyar jeep ce ƙirar ford ta sulalo cikin harabar gidan Maroon colour wadda taji uban tinted da gani kasan duk wanda ya kasance mamallakin wannan mota to la shakka hannunsa ya cuɗi gadon bayansa, a nutse motar tai parking sannan ta ɓalle murfin motar ta sanyo ƙafarta waje wadda ke cikin wani haɗaɗɗen takalmi baƙi wuluk me bala'in tsini dashi se walwali yake sabida stones ɗin da akai masa ado dasu masu matiƙar haske da ɗaukar idanu,

Hajar ce the IG doughter ta sakko cikin wata shainaɗaniyar shiga ta ban mamaki tamkar wadda zata zaɓen sarauniyar kyau komai na jikinta baƙi ne hakanne ya bawa hasken fatarta damar baiyana a sarari, sosai doguwar rigar me fasalin fitet gown ta amshi jikinta tareda matse ta sosai tayanda duk wata halitta ta jikinta ta baiyana, a yangance take tafiya tana zuba yauƙi tana ƙoƙarin shiga falon gidan sukaci karoda Baba Hajara wadda ke ɗauke da babban flet a hannunta ta shiryawa ɗan gaban goshin nata Abinci zata kai masa, da fara'ar da bata kai zuciya ba Hajar tace "let me help you Old woman. Ba musu ta miƙa mata farantin tana kallonta bakinta a sake, murmushi ta sakin mata tace "yana ina na kai masa don nasan wannan abincin da ganinsa na mijin Hajar ne ko tsohuwa?

gyaɗa mata kai tayi tareda nuna mata hanyar garden batareda tayi magana ba don ita har ga Allah lamarin yarinyar nan yana masifar bata tsoro, "wannan wani irin lalacewar zamani ne ni Hajara?


Ko a jikin hajar sam bata damu da irin kallon da Tsohuwar kebinta dashi ba tai hanyar inda ta nuna mata tana wani juya mazaunai a haka ta isa garden ɗin ta sameshi idanunsa a lumshe, Ajiye flet ɗin tayi sannan ta sunkuya dabda fuskarsa tana wani bin fuskarsa da kallo kamar zata cinyeshi ɗanye, saukar numfashinta da nata ne suka haifar da sarƙewar numfashi a tsakaninsu take shauƙinso ya fara fuzgar Hajar ta fara ƙoƙarin kaiwa jajayen laɓɓansa farmaki hakan yasashi buɗe idanu da sauri ya saukesu bisa beauty face ɗinta.

jada baya tayi da sauri sabida wani bala'in kwarjini dayayi mata, kallon tsaf yayi mata kimanin 5second sannan ya miƙe yabar mata gurin yana riƙe da cikinsa, gabaɗaya ji yake dama ya kwasawa ƴar banza mari kozata fita daga sabgarsa wannan wani irin bala'i ne haka ?

shidai kam Allah ya jarabce shi da jarababbiyar yarinya wadda idan har beyi da gaske ba tsaf zata iya jefashi a masifa watarana.

Fashewa da kuka Hajar tayi a gurin sabida takaicin abinda yayi mata amma sabida naci irin nata haka ta miƙe tabi bayansa still tana kukan...


*_GYAMBU TARABA STATE_*

Tunda wannan mummunan al'amari ya faru da inna laure gabaɗaya duniya ta juya mata baya duk tabi ta rame ta koɗe kamar ba ita ba, yawan masifar nan ma duk ta dena kullum bata da aiki se kuka yau kimanin wata guda kenan da faruwar lamarin amma sam ta kasa mantawa da komai, duk sanda ta tuna ji take tamkar a lokacin abin ke faruwa da ita haƙika Fyaɗe babbar masiface me zaman kanta kuma duk wadda akayiwa shi an gama kashe mata rayuwa na har Abada!!!!

yauma kamar kullum Moddibo dake tsaye jikin ƙofar ɗakinta ya ɗaga labulan buhun yana kallonta kukan takeyi duk yanda yaso ya shareta kasaw yayi dole tasa ya shiga ɗakin ya zauna daga gefan katifar ciyarwar dake ɗakin ya dubeta ya dinga bata baki harya samu tayi shiru, sosai ya dinga zuba mata nasiha a kan yarda da ƙaddara da kuma haƙuri babu abinda take se kuka tareda nadamar bijirewa umarninsa datayi a baya, tabbas da bata biyewa son zuciyarta ba wata ƙila da yanzu ta tsira da sauran mutuncinta. Shidai moddibo miƙewa kawai yayi yabar mata ɗakin don tunda abin ya faru yaji gabaɗaya Laure ta gama sire masa, bayajin ze iya zaman Aure da ita kokaɗan sedai ze mata alfarma guda ɗaya ya cigaba da zama da ita batareda wani abu ya gifta a tsakaninsu ba, idan ta amince da hakan to shikenan zeci gabada zama da ita a haka tunda duk wanda ya rufa Asirin ƴar wani To Allah xe rufa nasa ..... Badan haka ba wllh da tabbas ya gama zama da Laure har Abadah


*_ABUJA_*

Koda suka dawo daga Asbiti basu Samu Hajar a gida ba wannan dalilin yasa sam batasan da zuwan Rabe gidan ba, Tanacan tana neman soyayyar muzaffar a gidansu

A ɗakin zeeyadah aka sauketa sannan mom tabada Umarnin zeeyadah ta tsefe mata wannan gashin nata Dayaci uban datti a gyara mata amma fir Rabe taƙi yarda se zuba ihu takeyi dataga Zeeyada na neman takura mata ne yasa ta fusge jikinta ta koma gefan Edyan ta zauna tana matsar ƙwalla dole tasa zeeyadah ta ƙyaleta, Dariya Edyan Yayi sannan ya kalli zeeyadah yace "bani abin tsifa gashin. Ba musu ta miƙa masa ya kama doguwar jelar Ƙatuwar kalban yana tsefewa A hankali tamkar wanda ke koyon tsifan, yamutsa fuska ta farayi alamar tanajin zafi zata tashi taga ya haɗe rai dole yasa ta sunkuyar dakai tana wasa da yatsun hannunta a haka harya gama warware mata kasancewar guda biyu ne dama Kalban, nan da nan gashin ya baje a gadon bayanta tareda rufe mata fuskarta daga mom har zeeyadah seda yanayin gashin nata ya basu mamaki, ranar momce da kanta ta wanke mata gashin tass a toilet ɗin zeeyadah nan ma ba ƙaramin danbarwa sukasha da ita ba sannan aka gama, Bayan an gama wankin kan ne mom tayi mata wanka Tas ta wanketa se zuba ihu takeyi Sedai duk uban ihun datake zubawa be hana mom saɓeta ba, Towel tasa babba ta ɗaura Mata tareda busar mata da gashin tas wanda ya ƙara wani mugun baƙi da santsi sannan suka fito mom tace "zeeyada ta bata kayan bacci ta saka .

Doguwar riga ta ɗakko mata me ƙaranin hannu daƙyar ta yarda ta nuna mata tasa amma sam taƙi yarda a kama gashin dole suka ƙyaleta se uban kuka take zuba musu, tana fitowa falo ta faɗa jikin Edyan ta fara Wani sabon kukan hular hannun zeeyadah ya karɓa ya saka mata dukda haka gashin be rufe duka ba se faman sauke ajiyar zuciya takeyi.

A haka sukai diner Tana manne a jikinsa harta fara bacci sannan ya mike Tareda zare Jikinsa daga nata zebar falon da sauri itama ta miƙe zata bishi Duk irin baccin dake idonta tsayawa yayi cak yana kallenta bece komai kawai ya nufi ɗakin zeeyadah tana biye dashi har suka shige mom da Zeeyadah na kallon ikon Allah.

Zeeyadah data sake baki tana kallonsu ta kalli mom tace "momcy wllh nikam tausayi take bani bata iya hausa ba gashi kuma ƙaddara ta kutso mata da silar rabuwa da iyayenta mom, na tabbata yanzu iyayenta hankalinsu A tashe yake sabida ɓatanta.

Shiru mom tayi itama tana kallonta ita kanta tunanin dayake mata yawo kenan a saman zuciyarta, insha Allahu itakuwa zata taimakawa wannan yarinya har zuwa ranar dazasu maidata gaban iyayenta don ita harga Allah takejin yarinyar a cikin ranta musumman idan tana kallonta.

Duna shiga ya nuna mata mata gado yace "hau ki kwanta kasa yi masa musu tayi ta hau gadon still tana kallonsa Wani bala'in laushi taji wanda bata taɓa jin irinsa ba a Rayuwarta da wani irin mugun sauri ta saukko tana ihu zata shige jikinsa ya dakatar da ita. Yana kallon tsakiyar ƙwayar idanunta ya sake ce mata hau ki kwanta nan ma ba ƙaramar wahala ta bashi ba sannan ta hau ta kwanta, seda ya tabbatar da bacci ya ɗauketa sannan ya fita daga ɗakin yana murmushi.









Comment
Nd
Share



sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️


*_Page :28_*


*_WRITING BY: CHUBAƊO_*


Banyi Editing ba

✍️___inda yabarsu mom da zeeyadah a nan ya dawo ya samesu komawa yay ya zauna sannan suka kalli juna gabaɗayansu suka fashe da dariya, momce ta kalleshi tace "wllh Edyan a kwai aiki agaban mu babba ma kuwa becouse yarinyar nan daga ganin ta da kuma yanayinta cikakkiyar Asalin Bafulatanar Dake Rayuwa a cikin daji ce. Ajiyar zuciya yaɗan sauke sannan ya kalli mom yace "ni kaina mom na lura da hakan duba da yanda take yawan janyewa daga mutane tareda nuna tsoronta ƙarara ga wasu abubuwan tabbas bata taɓa ganinsu ba kuma batasan da dasu ba. Anyway we have to help her with everything dazata buqata a Rayuwa Especially knowledge.

Ɗaga kai Mom tayi Alamar gamsuwa da maganganunsa tace "but sweetie what about her parents da kuma danginta? Sam be kamata ace daga ka bige musu yarinya ka ɗakkota ka daga garinsu ka kawota nan ba Edyan I'm sure of duk inda iyayen yarin nan suke wllh nasan hankalinsu baze taɓa kwanciya ba, don haka duk yanda za'ayi ka samu idan ta ƙara samun sauƙi ka mayar musu da yarinya inda haɗarin motar ya faru na tabbata bazata kasa tuna inda gidansu yake ba.

Kallon mom zeeyadah tayi da sauri idanunta na shirin zubar da hawaye tace "pls mom let her to stay with us for a long while before she gets to her on parents pls mom, indai har ba itace da kanta tace zata tafi ba don Allah karki sake cewa ya mayar da ita pls wllh daga lokacin dana fara kallon ƙwayar idonta na fahimci there's something behind her mom is either good or bad Allah shikaɗai yasani but pls mom let her to stay Don Manzon Allah. Ta faɗa tana fashewa da kuka

Gabaɗayansu kallonta suke shi kansa Edyan bayaso yayi jayayya da ita ne amma a zahiri sam bayaso ya mayar da yarinyar, haka kawai yaji ubangiji yasa masa wani irin tausayinta wanda shi kansa besan daga ina hakan ke fitowa ba a yanzubashida burin daya wuci yaga rayuwar yarinyar ta inganta ta yanda bayaso yaga ta rasa wani abu a cikin Rayuwarta, kowace daƙiƙa idan ya kalleta burukansa akanta ƙara yawa suke nason ganin tazama kamar kowa. Hajar ce ta shigo falon hannunta ɗauke da mukullin motanta tana bada step tamkar me koyon tafiya, da kallo mamaki mom tabita sannan ta maida kallonta ga Agogo tace " ke daga ina kike at this time eh?

Dukansu kafeta sukai da ido suna jiran suji me zatace . Turo baki tayi tareda jan kujerar daining ɗin tace "gidansu Fadilah naje karɓan wani abou a gurinta and kum....."abunda ubanki ya Ajiye a gidan kikaje karɓa ko? Mom ta katseta cikin fishi sannan taci gaba da cewa "waike mara hankalin inace Hajar? Don uwarki an gaya miki nan ƙasar india ne da mace ke zuwa neman Aure gidansu saurayi?

Murmushi Edyan yayi wanda yake baiyana takaicinsa akan ɗabi'ar ƙanwar tasa yace "ai ko a indian ma mom namiji shike fara zuwa da danginsa suga yarinyar kafin daga bisani ta biya sadaki a ɗaura musu Aure, kinga kenan ko'a nan matan indiawan da addini be ishesu ba sunfi Hajar hankali da kuma mutunta kansu, na rantse da Allah mom koda ace nine Muzaffar bazan taɓa Auren wannan mahaukaciyar wadda batasan ciwon kanta ba as uwar ƴaƴana ba. Ya faɗa cikin ɗaga murya alamar ta gama bashi haushi

Ƙus tayi taƙi magana sabida tasan tanayin magana zeci ubanta a falon yasa ta sunkuyar dakai tana hawaye, itadai zeeyadah kallonta kawai takeyi tana mamakin wannan ɗabi'ar ta ƴar uwar tata, miƙewa yayi yabar falon zeeyadah ma ta kama hanyar ɗakinta ya kasance daga mom se ita, hakanne ya bata dama yimata faɗa sosai sannan ta miƙe ta barta a gurin tana kuka.

******

Ɓangaren muzaffar kuwa sosai yake samun sauƙi don yanzu yana iya miƙewa yayi tafiya kamar yanda yake da, sedai ramar dake tare dashi komai yanzu bayajin daɗinsa ko kaɗan musamman idan ya zauna shikaɗai bashida wani aiki wanda ya wuce na tunani, gabaɗaya duniyar ta fice masa a kai sabida yanda mutannan cikinta suke sam wasunsu basuda imani sukan iya aikata komai akan abin duniya, abu ɗayane yake

Please Login or Register in order to submit comment