Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gama cin abinci duk inda yaso kusantar ta kin yarda tayi Wai bacci take ji badan yaso ba ya jika tea ya Sha ya kwanta,domin Fatima bata girki

Washe gari da safe ya shirya ya fito falo dama ya rigada ya Saba da rashin breakfast shiyasa be wahala da kanshi ba ya fita aiki

Yana kaiwa kowa ya mike ya gaidashi ya amsa ya shiga office

Ishaq dai na desk dinshi yayi serious Yana aiki

Sadiya ce ta kawu me coffee ta ajiye me godiya yayi mata

Tace"ishaq"

Yace"Wai miye?"

Tace"haba ishaq ka bani dama Mana ka gan nawa kala soyyaya"

Ishaq yace"aiki Nike please don't distract me"

Ta ajiye wani kula tace"ok ga abinci na kawo maka daga gida"

Yace"nagode je kiyi aikin ki zamuyi magana anjima"

Wucewa sadiya tayi badan taso ba tana wucewa ya sauke ajiyar zuciya

Coffee ya d'auka ya fara sha ya bude abincin ya gan lafiyayar jellouf ne da nama tabe baki yayi ya rufe abincin Yana Gama shan coffee ya cigaba da aikin shi"telephone din ne yayi Kara ya d'auka ok sir, s kawai yace"ya mike ya shiga office din a lokacin da suka had'a ido ji yayi Kamar ya fashe da dariya tunawa da abinda ya faru jiya Amma sai ya basar ya karasa yace"sir gani"

Aslim yace"wani time ne meeting din?"

Yace"10:30am sir"

Yace"ka gama aikin ka"

Yace"sir iam still working on that sir"

Yace"ok gobe Ina son ka gama zuwa gobe so that mu duba mu gani kafin mu had'a plan din"

Yace"ok"har zai fita,aslim yace"kasa a kawo min coffee"

Ishaq yace"ok sir"

Yana fita yaje inda zai gan sadiya amma Bata nan duk Babu kowa a wurin,kawai sai ya d'auki cup me kyau ya had'a me coffee ya aza a tray ya kawo me ya ajiye a table"

Har zai wuce ya ji yace"please use my laptop to reply the email din public procurement board

Ishaq yace"nidai na gan jaraba kamar ni kadai ne a office din"kasa-kasa yayi magana inda bazai ji ba Yana zuwa ya fara danne-danne

Ji yayi aslim yace"who made this yayi daban dana jiya"

Ishaq yace"sorry sir dana je ne ban gan kowa ba a kicin din shiyasa na had'a ma da kaina Amma in baka so Bari inje in nimo sadiya ta had'a ma"

Aslim yace"no infact I love it,gaskiya ka iya coffee waya kowa maka domin jiya banji dadin shi ba"

Ishaq yace"thank you sir kawai ginger ne nasa kila shiyasa kaji dadin shi"

Aslim yace"as from today you will be the one to make me coffee "

Ishaq yace"ok sir nayi sending email din "

Yace"ok"komawa yayi ya zauna,Ranan ishaq be je gida da wuri ba kowa ya tafi ya barshi domin Yana son ya gama aikinshi kafin gobe

Da misalin karfe 5:30 zee ta Kira ni'ima tace"kefa Nike jira mu tafi gida"

Ni'ima tace"please yanzu Zan fito bani 10minit"

Zee tace"ok"suna Gama waya Ni'ima ta mike ta fara had'a kayanta ta saka waya a aljihu godiyar Allah ta d'aya duk ta samu tayi sallolinta domin ta fita taje shagon su zee a sace

File ta kwashe ta kai store ai tana shiga kofar ya kulle da ita a ciki

Babu irin bugun da batayi ba Amma shiru ga duhun ya mamaye store room din

Bugu da take da karfinta ko security zasu jita Amma abu kamar Wasa sanda tafi minti 30 ga number zee be shiga service ma gabad'aya d'aukewa yayi dama cikin kwanakin ana fama da matsala network

Aslim ne ya shigo company sanadiyan mantuwa da yayi security ya gani a kasa suna hiransu suna ganinshi suka mike suna tambayarshi ko lafiya yace"kalau Abu zai d'auka,d'aya daga cikinsu ya biyoshi sai yace"ah'ah Yi zaman ka"

Komawa yayi ya zauna,shiko ya haura 3rd floor yana haurawa ya shiga office dinshi ya d'auki abinda zai d'auka ya fito ji yayi ana buga kofa da karfin

Karasawa yayi Yana cewa who is there"

Budewa yayi Amma be gan kowa ba hakan yasa ya shiga yana haska wuta kamar kofar jira yake ya Kara kullewa da sauri ya juya ishaq ya mike cikin tashin hankali da tsoro ya Karasa da gudu ya

Maman nur
9/10/20, 6:32 AM - Ummi Tandama: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*NI'IMATULAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

Wanan littafin na kudi ne 300 me bukatar karantasa har karshen a tura naira d'ari uku ta wanan asusun banki Aisha Mohammed 0092544083
Access bank ko Kuma Kati mtn vtu ta wanan layin 08148088368 me niman Karin bayani sai a min magana ta wanan layin 09090112846 sai na ji ku

*Last free page*

πŸ…Ώ3️⃣0️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Rungumeshi ishaq yayi jiki na rawa duk ya daburce"

Jin ishaq jikinshi yasa Aslim yin shiru na d'an lokaci domin wani yanayi yake ji na daban,jin shiru yasa ishaq janye jikin shi yace"sorry sir wallahi na zo ajiye file kawai sai door din ya kulle wallahi na fi 40minit a ciki"

Kallonshi aslim keyi a duhu hakan yasa ishaq juyawa da wuri yace"sir p
kofar ya Kara rufewa kuma dama kofar nada matsala tun last week manager yace zai kira me gyra in kofar ya kulle sai an bude ta waje"

Tsaki Aslim yayi yace"that is my problem with securities door suna da wuyan sha'ani"

Karasawa yayi ya fara kokarin budewa Amma Taki buduwa

Shima bugawa yakeyi Amma shiru shi kanshi yasan masu gadi bazasu tab'a jinsu ba domin duk Suna can waje gajiya yayi ya koma ya zauna ya bar ishaq Yana bugawa

Gajiya yayi yace"yanzu sir ya zamuyi kuma ba service"

Aslim yace"I guess a nan zamu kwana har zuwa gobe"

Ishaq yace"what? sir Yan gidan mu will be worried and I can't reach them please sir ka taimaka"

Aslim ya gyra Zama yace"ishaq what do you want me to do iam as worried as you are but I can't help it domin ko ya Zamuyi kofar nan bazata tab'a budewa ba Kuma duk inda akayi akwai wanda ya tab'a kokarin shiga ne ba sani ba,just seat and relax

Ishaq a ranshi yace"how can I relax when iam in trouble in na cigaba da wanan zufa this fake bears zai fita,and zaka gane ni macece bana Miji ba"

Ji yayi yace"why not ka cire suit din you are sweating"

Ishaq yace"no never mind sir I will coup"

Shi dama cikin jeans da polo yake domin har yaje gida yayi wanka ya dawo ne ya d'auki wani file yayi aikin a gida"

Zama ishaq yayi sai shafa gemu yake ganin abin ya fara b'anb'arewa"

A ranshi yace"innalillahir wa Inna illahi raji'un ya rabbi ka taimakeni"

BΓ yan wasu mintuna sai ga cockroach a wajen kafarshi a
da sauri ya mike yaje ya rungumeshi yace"sir cockroach ka taimakeni"

Aslim ya fashe da dariya ganin fa da gaske tsoron yake har jikinshi na rawa"

Yace"ishaq wanan wani irin tsoro ne Kamar ba namiji a why ishaq jibi fa har maganarka ya canza zuwa na Mata saboda tsoro"

Sai a sanan ishaq ya gane ya kwabsa ya canja murya yace"please sir ka koreshi wallahi tsoro Nike ji"

Dariya aslim yayi yace"ok"koma gefe

Rakub'ewa tayi gefe jiki na rawa har ya Kori cocroach din

Dariya yayi yace"honestly ishaq ban tab'a ganin namiji that is scared of cocroach ba sai Kai Haka kake da tsoro"

Ishaq yace"sir tun ina yaro Nike tsoron cocroaches shiyasa ma yan gidan mu ke ce min namiji dole saboda Ina da tsoro gashi wasu na cewa features dina kamar na mata

Dariya ya kyakyale dashi yace"namijin dole?is that your name at home'

Ishaq yace"sir miye na dariya please bana son kowa yasan Ina da tsoro let it be our little secret if not my girlfriend zata min dariya"

Aslim yace"so you have a girlfriend tell me about her"

Ishaq ya zauna a ranshi yace"ni na gan ta kaina yau kofar nan ya bude kafin bears din nan ya cire"

A fili yace"sir please ka duba wayar ka ko akwai service"

Yace"ai na duba I think Babu service ne a store room din nan but gist me about your girlfriend kafin allah ya turo Wanda zai bude mu let while away time"

Tace"sir karfe nawa?"

Yace"7:15pm"

Zaro Ido yayi yace"sir my mum will be worried na sani"

Aslim yace"as big as you are kaifa namiji ne meyasa zata damu akan grown up man like you?a man that has a girlfriend"

Ishaq cikin kosawa yace"my mum loves me a lot kuma ni kadai gareta in ba aiki ba bata bari inje ko Ina"

Yace"zancen fa wa ke zuwa ma?"

Ishaq yace"ai during lunch nike zuwa in ganta itace wacce ke Zama a store din dake opposite din mu"

Yace"you mean the sales girl?'

Yace"yes sir"

Aslim yace"but meyasa kake Bari tana harka da anyhow friends?"

Ishaq ya gyra Zama yace"I don't understand"

Aslim yace"no I don't mean to interfere but akwai wata kawarta da Bata da kamun Kai which I don't think ya kamata suyi ta harka kartayi currupting dinta"

Ishaq yayi wani dariya yace"you mean Ni'ima?"

Yace"I don't know her name but be kamata suyi ta yawu tare ba"

Ishaq yace"nasan ma Ni'ima ce wata me son kudi ko?"

Yace"eh"

Yace"is not her fault that she loves money what do you expect in yariya bata da responsible father,a gidansu yara sun fi arba'in domin babanta aure saki yakeyi and baya ciyar dasu shiyasa take son kudi and ita kadai suka haifa tare suka taso da zee so it will be difficult to separate them"

Aslim yace"I see, it will be easy to decieve her"

Ishaq yace"kana magana ne"

Yace"no"

______________

A gida ko hankalin ummi ya tashi sosai ta rasa inda zata sa kanta domin da safe Ni'ima ta tabbatar mata zata dawo da wuri da shiyasa ma ta lallab'a tayi shinkafa da Miya Amma shiru

Hijabi tasa ta tafi gidansu zee,zee na ganinta ta duka ta gaisheta ta amsa,gaisawa sukayi da mahaifiyar zee

Ummi tace"zainab Dan Allah akwai inda Ni'ima tace'miki zata je ne?"

Zee ta zaro Ido tace"kina nufin har yanzu Bata dawo ba?8:12pm fa yanzu"

Ummi tace"toh ni Ni'ima bata tab'a min Haka ba,Bata kawai shida a waje ba"ta Kare cikin damuwa"

Zee tace"nifa na kirata da na jita shiru tace"in Bata minti goma zata fito toh har 6:30 shiru sai Kuma abbana ya fara Kira shiyasa na dawo"

Ummi ta zauna akasa tace"Allah dai yasa lafiya"

Ganin ta damu yasa zee shigar d'akin ta Kai minti biyar sai gata ta fito tana murmushi da be Kai zuci ba tace"ummi karki damu yanzu ta turo min sako Wai sun tsaya meeting Kuma ance su kashe waya shiyasa Amma da sun gama zata dawo"

Mama tace"alhamdullilah"

Ummi tace"toh Bari in koma gida"komawa tayi zee ko d'aki ta shige ta dinga trying number ta be shiga tace"Allah dai yasa ba Kamata akayi ba

Abu dai kamar Wasa har 11:30pm

____________

Babu abinda Aslim yakeyi sai kyakyale dariya yace"are you serious?kana nufin irin mutane Nan na existing a duniya"

Yace"iam darm serious,she was like ishaq meyasa zaka min haka why wulakanci Babu kyau fa?"ta Kare cikin muryar maza"

Niko nace"I don't want to betray you zee is the only one I love"

Aslim yace"and what her reaction when you said that"

Ishaq yace"she hug me and started crying,begging me to love her"

Aslim yace"are you serious Ashe Kai na Mata ne"

Ishaq yace"sir Kai fa, do you have a girlfriend?"

Murmushi yayi yace"not at all,ko Zaka bani cikin masu sonka?"

Ishaq ya zaro Ido yace"ai bazasu so ka ba,su dai ishaq kawai suke so"

Aslim ya mike yace"ni bansan irin gadin da security din Nan suke ba ya kamata a ce sun zo tunda motata na waje da basu gan fitowa na ba ya kamata su biyo ni Amma suna ta hiransu yanzu fa is to 12 Bari in buga kofar kuma"

Zuwa yayi ya fara buga kofa ai sai ga fake bears din ishaq ya fadi,lalube ya farayi tana sauri kafin ya juyo,ji tayi ya juyo yace"I guess a Nan zamu kwana"

Da sauri Ishaq ya juya baya ya samu ya d'auki bears din amma mayarwa zaiyi

Wutar Aslim ke haskawa har ya karaso yace"ishaq ya kamata ka cire wanan rigar ka Sha iska"

Ishaq dai yana kokarin mayarwa ai juyo dashi Aslim yayi zai haska me wuta a fuska har ishaq ya runtse Ido zuciyarshi na mugun bugawa sai ya ji yace"wayar ma ta mutu ara min taka"

Wani wawan ajiyar zuciya ya sauke sanan yayi sauri ya maida bears din amma be Kama sosai ba

Zaiyi magana sai yaji Kamar motsi da gudu ishaq ya fara kwankwasawa cikin ikon Allah sai ga security ya bude kofar

Yace"ya Haka Kuma"

Aslim yace"meyasa da Baku gan fitowa na ba Baku biyo ba"

Security yace"Babu wanda ya lura da motar ka sai yanzu shine nace Bari in zo in duba ko lafiya shi oga ishaq dama babu Wanda yasan Yana ciki"

Aslim yace"Amma a matsayin ku na masu gadi ya kamata kuyi ta zagaye office ba ku zauna Kuna hira ba"

Security yace"sorry sir "

Aslim yace"ishaq let pray kafin mu tafi gida"

Ishaq a ranshi yace"you fool ya zanyi inyi sallah ba hijab"a fili yace"ah'ah in naje gida zanyi"

Yace"ok then muje in sauke ka a gida"

A mota ko Aslim sai dariya yakeyi yace"ishaq you are funny and fun to be with"

Ishaq yace"thank you sir"

A junction ishaq yace"saukeni a Nan"

Aslim yace"no gida zan Kai ka in Yi magana da mama in fad'a mata abinda ya faru kartama fad'a"

Ishaq yace"no zatayi min fada please saukeni anan"

Yace"ok if you insist,gobe ba sai ka zo da wuri ba"

Yace"ok sir"

Yace"Amma duk anguwanku d'aya da ni'imar ko?na gan this is the same spot da na so bige ta"

Yace"eh mu makota ne"

Jan motar yayi ishaq ya ruga da gudu bΓ yan ya cire fake bears din matsalanshi d'aya Kar ummi ta ganshi cikin kayan maza"

A kofar gida ya tsaya yana Kiran ummi yace"Yana waje Domin har an kulle kofa"

Yana tsaye ya hango saude da mijin makociyarsu ya rokota matarshi tayi tafiya d'auke Kai yayi sai Suka Fara kame-kame"

Ummi ce ta fito ta bude kofa tana kallon ni'ima da har ta cire razor cut din ya rage ta babu ko d'an kwali

Matsawa tayi ta shiga suna kaiwa d'aki ummi tace"daga Ina kike Kuma Ina hijabin ki?meyasa Kikayi shigar maza?*

Rasa me zata ce tayi,a fusace ummi tace"ba da KE nikeyi ba?"

Ni'ima tace"Dan Allah kiyi hakuri ummi wallahi.."

Wanka mata Mari ummi tayi tace"tube kayan ki"kallon ummi tayi cikin tashin hankali ta fashe da kuka tace"ummi wallahi ni ban bin maza"a fusace ummi tace"zaki tube ko sai ranki ya b'ace?"

Ni'ima na kuka ta tube kayan ta kwanta ummi ta saka mata hanun Ihu tayi sai ta wurga Mata zani rai b'ace ni'ima ta tashi taje ta d'auro alwala tana kuka bata yarda ta kalli ummi ba"

Ummi da jikinta yayi sanyi ta zauna bakin gado tana kallo yar'tata harta idar da sallah

Ummi tace"Ni'ima Ina takura Miki ko?"

Ni'ima ta fashe da kuka tace"ummi har yanzu baki yarda Dani ba abin na damuna ni bana bin maza"

Ummi ta mike ta zubo mata abinci tace"gata Nikeyi Miki ko bana Raye wata rana Zaki gode min"

Ni'ima taki amsa tace"na koshi"

Ummi tace"in baki ci abincinan ba yanzu Zaki gan b'acin Raina"

Ni'ima tace"toh muci nasan kema Baki ci ba"

A tare suka ci bayan sun Gama Ni'ima ta kwanta bacci yayi awon gaba da ita"

__________
Aslim na zuwa ya tarar Fatima tayi bacci ko ta kanta be bi ba yaje d'akinshi yayi sallah ya kwanta Aslim ne ya fad'o me a Rai da labaran daya bashi sai kawai yayi murmushi yace"funny guy"kwanciya yayi sai kawai ya tuno da inda ya kankameshi daya gan cocroach murmushi yayi yace"silly guy"

(Niko nace tohfa)

BΓ yan sati d'aya sosai ishaq ya maida hankali akan plan dinsu kuma sun Zama friends da Aslim domin a cewar aslim yana sashi nishad'i

Yau dai da asuba ta fito zata je aiki tana sauri a junction dinsu ta hango motar Aslim murmushi tayi ta karasa kusa dashi ta buga glass din sai ya sauke Yana ganin Ni'ima ce ya hade rai"

Fuskar tausayi tayi ta duka har kasa tace"Ina yini sir"

Da mamaki yace"lafiya Lau"

Tace"sir dama Ina ta niman ka in baka hakuri akan abubuwa da nayi maka wallahi sharrin shadaine da Kuma bukatar kudin Amma insha Allah Zan biya ka dubu goma Sha biyu ko??wallahi a lokacin ummi ta ce ba lafiya shiyasa Amma Zan biya"

Aslim a ranshi yace"this is my chance"a fili yace"not at all dear na baki"

Murmushi tayi tace"toh nagode"

Har zata wuce yace"please mu Zama friends Mana"

Tace"ok ba damuwa,amma me kake zuwa Yi a unguwan mu kullum Haka"

Yace"Ina da abokine ishaq"

Ni"I'ma tace"Allah sarki ai saurayin kawata ne,dazu ma ya wuce aiki"

Aslim yace"ok Ashe ya wuce ok then"

Jan mota yayi ni'ima ta fashe da dariya tace"fool"

Keke ta tare ya sauketa gaban shagon su zee a guje ta shige ciki ta canza kaya,ya shirya sak domin ya siya sabon saje

Fitowa yayi Yana gyra neck tile,turus yayi sakamakon ganin Aslim da yayi tsaye yana magana da zee,murmushi yayi yace"sir meka zo yi a Nan?"

Aslim ya hade rai yace"na Kama ka yau na Kama ka red handed"

Ishaq ya had'iye wani miyau,zee zatayi magana yace"Yi min shiru I didn't expect this from you inda kike sa hijab ban tab'a tunanin Zaki shigar da namiji ciki ba"

Ajiyar zuciya ishaq ya sauke yace"sir I can explain"

Juyawa yayi ba tare daya amsa soda drinks dinshi ba ya wuce ciki"

Zee tace"yanzu ya zakiyi?"

Dariya ishaq yayi yace"zargi yake ko matse ki nikeyi ciki tunda ya ganni na fito Ina gyra necktie"

Zee tace"ya zakiyi yanzu?"

Ishaq yace"Raina me hankali zanyi"

Binshi ishaq yayi ko daya ya shiga office ya tarar already Yana cikin office dinshi had'a Ido sukayi sai Aslim ya hade rai ya d'auke kanshi,ishaq ya zauna ya fara aikinshi

Da misalin karfe 10:30 ishaq yayi natsu Yana aikinshi sai ga Fatima ta shigo building din da warmer na abinci me kyau,karasawa tayi desk din ishaq hakan yasa ishaq ya d'ago Kai daga kallon computer da yikeyi ya kalleta

Fatima na had'a ido da ishaq tace"Mashaallah ka gan namiji Mai kyaun Mata"

Ishaq yace"how may I help you"

Fatima tace"handsome ya sunanka?"

Ishaq yace"ishaq"

Tace"you are handsome please ko zaka bani number ka muyi ta gaisawa?"

Ishaq a ranshi yace"toh fa"

A fili yace"ok'

Tace"please sir Aslim na zo Nima"

Ishaq yace"ya shiga meeting sai 12:pm zai fito"

Tace'ok gashi In ya fito ka ce me Fatima ce zan ma kirashi"

Har ta juya zata wuce ta dawo tace"the number"

Ishaq ya Bata number sanda ta kira ta gan waya yayi ringing a desk dinshi sanan ta wuce"

Tana fita tayi dialling number salma,Salma na d'agawa tace"Salma guess what yau na gan namiji da ya birgeni a rayuwa Baki ganshi ba kyaun mata gareshi wallahi yau for the first time naji Ina son namiji and he is Young bazai wuci 25-26 to 27 ba,eh yanzu gani nan zuwa"

Sai misalin karfe 12;30 Aslim ya fito a meeting ko kallon inda ishaq yake beyi ba ya shige ciki office dinshi

Ishaq ya d'auki warmer din ya bishi office yace"sir wata Wai Fatima ta kawo ma abinci"

Ba tare da ya kalleshi ba yace ajiye,ajiyewa yayi yace"sir is not what you think"

Aslim yace"meyasa kullum kake zuwa shagon ku kebe a cikin changing room da yariya I even saw you yesterday"

Ishaq yace"sir is not what you think"

Aslim yace"don't try to decieve that girl just because she loves you,please don't take advantage of that poor girl"

Ishaq yace"sir what are you insinuating?kana zargin Zina nikeyi da yar mutane?"

Aslim yace"in bashi ba me kake zuwa Yi kullum Kuma yau na Kama ka kana fitowa harda gyra necktie"

Ishaq yace"sir ni ba mazinaci bane I have respect for women,how can you think of that?"

Aslim yace"can you swear baka tab'a taba ta ba?"

Ishaq yace"not at all"

Aslim yace"you mean baka tab'a kissing dinta ba?"

Ishaq yace"eh toh muna d'an tab'a kiss and hugs but not sex"

A fusace Aslim yace"you mean matse Yar mutane kakeyi karamin yaro da Kai sai shegen jaraba"

Shima ishaq a fusace yace"and what is your business in my personal relationship?in badan Kai namiji bane da sai in ce kishi kake,ai kiss and hugs is common in relationships why are you even bothered tunda. ba sister ka bace"

Aslim ya sake baki Yana kallonshi shi kadai yasan inda yake ji

Ishaq ya rike Kai yace"iam sorry sir for shouting at you is just that you are interfering too much and I don't like it"

Aslim yace"just because i cared and want the best for you,you think I am interfering ishaq you are too young for all this,and na d'auke ka a matsayin kanina please ishaq becarefull"

Ishaq dake me wani kallo domin lamarin ogan nashi ya fara bashi tsoro kodai gay ne shi

Yace"sir zan wuce Ina da aiki yi"

Har zai fita ya ji yace"get me coffee"

Ishaq yace"Zan fad'awa sadiya"

Aslim yace"no do it yourself"

A wunin ranan ishaq be Kara yarda yaje office din ba shiko Aslim abin ya tsaya me a Rai sai juya kalman kishi yakeyi

Koda Suka tashi nacewa Aslim yayi shi zai Kai ishaq gida

Ishaq yace"tare fa muka saba wucewa da zainab"

Be jira amsarshi ba ya wuce yana fitowa sai wani mutumi ya tareshi manager nice builder suna cikin magana sai ga Aslim ya fito a mota kallo d'aya yayi musu ya d'auke Kai"

Bayan kwana uku Ni'ima ne a cikin motar Aslim tace"da gaske kake zaka aureni Kuma kana sona?"

Yace"eh Kuma bana son ya wuce sati biyu Ina sonki"

Ni'ima ta rufe fuska tace"Nima Haka"

Aslim yace"muje inyiwa baba magana"

Ni'ima tace"toh har gaban gidansu ta kaishi tana murna ko ba komai su talatu zasu mutu da bakin ciki"

Baba na ganin Mai kudi ya sunguna har kasa ya gaishe shi hakan ya bawa Aslim kunya shima ya sunguna

Baba yace"ai ni'ima yariyar kirki ce ga iya girki"

Aslim a ranshi yace"kwad'ayi ne dasu"

Yace"baba dama niman izini na zo Ina son in turo magabata na"

Baba yace"toh ba damuwa,Aslim be bar wurin ba sanda ya direwa Abba dubu d'ari"

Kwanciya ne Abba ya rage beyi ba

Cikin kwana uku Aslim ya tura fake relatives da ya biya Suka zo niman auren Ni'ima inda akasa biki Nan da sati biyu

Duk inda ummi taso ayi bincike abin gagara yayi,su talatu da saude ko hassada zai kashesu

Ana bikin su saura sati d'aya Ishaq ne zaune a office yana aiki

Aslim ya fito yace"muje hope you are ready for the presentation?"

Ishaq yace"yes sir"

Manager yace"ok muje sir"

Suna fitowa domin a public procurement zasuyi meeting din meeting din da in sunyi sa'a zasu samu contract din da yayi Worthing billions of naira

Bayan kowa ya zauna nice builders ne Suka Fara presentation abin mamaki abinda su Aslim zasuyi presentating shi sukayi exactly

Kallon tuhuma Aslim yayiwa ishaq,domin ya gansu tare ranan kenan ishaq ne ya sayar musu dashi

Manager ya kalli Aslim dake zufa ganin duk wahalan da Suka sha ya tashi a tutar Babu"

A Haka har company hudu sukayi Sanan aka fito break sai 3:pm za a dawo

Suna fitowa ishaq yace"sir what is happening"

A fusace ya damko shi yace"I think I should be asking you that"

Zaiyi magana ya finciko shi ya kaishi mota ya tura shi ciki sai office dinshi a fusace ya turashi ya Fadi kasa

Ishaq yace"sir me nayi?"

Yace"nawa Suka biya ka?"

Ishaq ya gyra rigar shi idonshi tab da hawaye yace "....


Toh my people free page ya Kare me son karantawa har karshen sai a hanzarta biyan 300 ta wanan asusun banki Aisha Mohammed 0092544083 vip 500 watoh masu son a tura musu p'c kenan ko katin MTN ta wanan layin 08148088368
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment