Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qamshi wurin Na tsuma zuciyarsa gaban wani qwarama mai ruwan garai garai qarqashin sirran bishiyiyin ayaba ga qatuwar bishiyar bangoro da wata bishiyar kashu da jijiyoyintama cikin tabkin suke ninqaya ga kukan tsuntsaye masu kama da sautin sarewa a hankali ya taka ya qarisa kan daya daga cikin kuyerun da aka jera a wurin masu dan tsawo Wanda sunfi kama Dana kwanciya 🌳
A hankili ya kwanta tare da yin wata sassanyar ajiyar zuciya gamida lumshe idanshi duk Wanda ya ganshi yasan yana cikin nishadi
Cikin yanayin tsokana Adam ya dan yafito Ahmad ya nunashi da ido yace shi dai har abada haka yake son kasan cewa ba kowa kusa dashi ya lumshe ido kome yake gani ranine.? sai Allah Ahmad ya bashi amsa yana dan murmusawa
cikin shauqi ya fara zagaya wurin yana dan ciren yayan itatuwan cikin zuciyarshi Aysha ce ke yawo phoneπŸ“±enshi ya zaro gami da kiranta bugu daya ta daga Cikin muryar tsantsar qaunar Ya Ahmad dinta take mgn jin muryarta da shauqi ya jingina jikin bishiyar 🌳 hadi da lumshe ido cikin sanyin murya yace Aysha kina ina ? .
Ta dan qara magalewa jikin innayi ta danyi ajiyar zuciya tace
Ya Ahmad gani a kan gadon innayi
Cikin sanyi ya fesa munfashi yace toh kizo lambu gani ina jiranki
Toh tace gamida da cewa ya Ahmad ta wanne gefen kake ?
Bakin gwaramannan ya bata amsa
Aiko cikin zumudi ta figi mayafinta ko Amira da Maryam bata nemaba ta fita da Sauri sauri ta nufi rafin
Ahmad ya nufi gun kenan yaci karo da hydar da sauri ya miqa mai phone enshi yana ya Ahmad Abba Na nemanka tun dazu yake kiranka layinka bai Shiga shine yace Na kawo ma
Da sauri ya kara phone en a kunne πŸ“±πŸ‘‚πŸ»cikin biyeyya ya ke mgn toh Abba ganinan zuwa ehh yanzu zanzo cikin sauri ya katse kiran ya miqawa hydar phone en ya nufi gun su Yusuf fuskarsa dauke da murmushi yace biyaye ni Abba Na kirana ZAmu tf bakin kogi gun dabbabi πŸ„πŸͺ da sauri Adam ya miqe yana muje Nima xani har sundayi nisa Ahmad ya dawo ya dan kalli Yusuf yace biyaye kai bazaka jebane ?
Kai ya gyada mai alamar bazashi ba Adam yace kai da Allah zo mu tf ai kasanshi ba zuwa zaiyiba ya fada yana hararanshi shi ko sarkin hali ko idanshi bai budeba da sauri suka tf abinsu
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
Tunda ta shigo cikin rafin sanyin iskar da qamshin furannin suke ratsata ta lumshe idanta hadi da ware hannayenta tana tfy cikin rausaya tana shaqar qamshi kai tsaye gun da ya Ahmad dinta ya gayamata ta nufa tana dan ratsewa shuke shuken har ta qarisa wajen duk idanta a rufe cikin nitsuwa take dan tsallaka kujerun a nufinta zataje bakin ruwan ta zauna aiko a hankali qafarta ta dan zame zata antaya cikin ruwan da sauri ta ja qafar baya tana shirin juyowa taji ta afka kan kujerun
Yusuf dake kwance a rigingine idanshi a rufe ba abinda yaji sai fadawar mutum a kan faffadan girjinshi cikin mmk da sauri ya ware idanshi gami da dan yunqurawa zai tashi
Ita kam tun da ta fadi cikin razana ta yunqura sai tajita jikin mutum da sauri cikin fara.a tace ya Ahmad yau kam Dana karye ta dan saki murmushi gami da dan manna fuskarta kan girjinshi ta zagaya hannuta ta bayanshi duk abinnan da take idanta a rude
Shiko cikin takaici da jin haushinta ya ware manyan idanunshi kan fuskarta cikin fushi da takaici ya danna mata tsawa keeee Baki da hankali ko jin muryar dodonta cikin tsoro ta bude idanta dan tsawace mai rikita mutum ya sakarmata har sai da cikin rafin ya dauki sautishin da sauri ta yunqura dan ta tashi bata gama firgicin tsawarba taji wani irin axabebben mari daya yarfa mata cikin jin zafi tasaki qara aiko ya miqe cikin zafin nama ya rinqa zuba mata Maruka tun tana tsaye har ta fadi qasa nanko yasa qafarsa ya rinqa bol da ita tana kuka tana wayyo Hamma Yusuf dan Allah kayi haqri wlh ban saniba ne plss Na tuba
su hydar dake can gefen bishiyoyin goiba da sauri suka nufi gun amman suna zuwa ganin Hamma Yusuf ne ke tabkarta yasa gaba daya suka tsaya hydar ya kallesu cikn jin takaicin Yusuf yace wai me ya tsaiya daku ? Rabi,u yace tab wazai qarisa wannan mugun yahada dashi shi dama in dai baiyi dukaba baya jin dadi cikin jin tausayin ta ya Shiga tsakaninsu ya sunkuya ya dagota ya dan juyo badan ya soba sai dan kar Yusuf yace ya rainashi yace dan Allah kayi haquri Hamma Yusuf
Cikin fushi da murtuqe fuska yace maza Ku bacemin da ganan aiko da sauri ya jata suka tf

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
Abinka da farar fata tuni fuskarta ta kumbura tayi jawur ga wani azabebben zazzabi daya rufeta tun kafinnsu isa gida jikinta sai bari yake
tab aiko Ummi kam ta hatsala fada take tamkar zata aro baki har zuwa bayan maggariba fada take sosai Nenne sai bata haquri take amma ina fada take har su Abba da Ahmad suka shigo gida yayinda bba bello da Yusuf ke binsu a baya .

Yan uwana musulmai ina barar addu,arku ga dan uwana ya Abubakar Wanda Allah ya mai rasuwa ya Allah ya jiqanshi da rahama πŸ‘πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­

By garkuwan Fulani 090,,,,,,
[4/9, 1:48 PM] β€ͺ+234 909 785 3276‬: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
MI,WASMITI.....page 9⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
πŸ™πŸ»Bayan ya bude taron da addu,a ya dan yi gyaran murya ya jinjina kanshi jikin kushin ya dan kalli illahirin Family enshi din haqiqa shi da kanshi yanajin nauyin furicin da zaiyi zuciyarshi Na samun rauni idan ya kalli idanu jikokin nashi yana samun fargaba sosai yanajin tsoron kar yau ta kasance ranar nadama ko ranar baqin ciki ko ranar daukewar farin cikin wani sashi daga cikin sashikan zuriyar tasa jikin jinjina kai ya dan dago kanshi Ya dan zuba musu ido gaba daya a hankali ya danyi gyaran murya ya bude baki cikin sanyin lafazi da taushin baki yace

Bello da kai da sauran qannan ka da matanku da qanwarku da maigidanta da dan uwana da iyayenku mata Yau gashi mu dukkanmu Allah ya kawomu wannan rana da muke fatan isar da wani alqawari da muka dauka idan Allah ya nufa yai shiru ya dan zuba musu ido
sukuma yara daga kan Adam har xuwa kan Aysha ido suka zuba musu cikin yanayi tabbayar wanne alqawarine wannan Ahmad tun wayewar garin bugun zuciyarsa ta zarce tunaninshi sai yanxu yaji abin Na sauqa shiko Adam kallon kakan nasu yayi cikin dan zaquwa yace gsky mu bama son Jan rai kana mgn kana jinkirtawa da sauri baba Umar ya daga mai hannu alamar ba batun wasa ganin haka yasa gaba daya sukayi shiru sai yusuf shi dama baiyi mgn ba asalima kanshi a sunkuye yake Aysha da ke dan manne jikin innayi ta maida kanta tai lamo yayinda Amira ke gefen Adam maryam kuma Na jikin Nenne duk suka maida hankalinsu kan Bappa yayan a hankali yaci gaba da cewa Ahmad
Bai Amsaba sai ido daya zuba mai bugun zuciyarsa Na tsananta πŸ’—Ahmad ya kuma kiransa da gyar ya iya amsawa Na,am jin yadda sautin muryar Ahmad din ta fito yasa Yusuf da Aysha dagowa a tare suna klonshi sai yanxu su duka sukaji wani baqon yanayi ya darsu kan zuqatansu sautin muryar kakan Nasu ya katse musu Al,amarin yana mai cewa Ahmad A kullum duk zuriyarmu tana alfahari da kai haqiqa Na tabbata kai mutum ne mai cikir haiba da nazartan hilin da ake ciki Ahmad ina alfahari da kai a zuriya ta Na tabbata kai dayane mai fahimtar kalemen mutum duk kaushinsu da dacinsu
Tun kana yaro baka taba kaucewa
Umurnin iyayenka ba ko yaushe kai mai biyeyyane a garemu
Baki daya shiru ya dan kumayi yayinda duk parlon sukayi sit Yanayin Ahmad kuma yafi kama da wanda tsoro ya cika zuciyarsa sukuma iyayensu gaba daya sada kansu qasa sukayi
Cikin qarfin hali yaci gaba da cewa Ahmad a yau Alfarmanka nake nema kuma da yafiyarka dani da iyayenku baki daya Ahmad muna masu tausar zuciyarka muna kuma buqatar haquri daga gareka
Cikin rashin fahimta yace bappa yaya ni kuma muryarsa har rawa take yaci gaba da cewa ya isa tunda tun forko kace iyayena toh mgna ta kare ba wani neman alfarma tsakaninmu a hankili ya daga kanshi ya kalli qanin mahaifinshi yace Abba ni dai ni din Abba me kuke buqata a gareni da har kuke ban haquri ni Ahmad danku meye rage da baku minba a duniyarnan 🌍 ya maida dubanshi gun mahaifinshi da mahaifi yarshi yace baba da Nenne kun gama min komai Nenne am Na Dade ina Neman abin da kike buqata in miki a duniyar nan da kema zakiji bakiyi asarar yaranki da suka rasuba cikin 'yaya 12 da kika aifa sai mu 3 Allah ya bar miki Nenne ni Ahmad ki gayamin meye buqatarku yaku iyayena ya qarishe mgnar
Yana mai zubda qwallah😭 ya dan kalli kakanshi yace bappa Yaya gayamin meye buqatarku ko zanji sauqin abinda ka dauramin haqiqa zuciyata ta soku πŸ’˜in dai bazaku sani Abu kai tsayeba sai kunce kuna Neman alfarma
Ahankili Abba ya daura hannushi kan tsakiyar kanshi cikin wata iriyar murya yace Ahmad Allah yamaka albarka ubangiji ya jibanci Al,amuranka
Cikin muryar kuka nenne tace Amin yusuf kam tuni zuciyarsa ta fara tafasa ganin hawayen biyayenshi Aysha ko kuka takeyi sosai innayi Na tausarta
Gyaran murya yayi yace Ahmad alfarman da muke nema a gareka batun Aurenka da Aysha sai kuna ya sunkuyar da kanshi ganin yadda gaba dayansu jikokin nasa suka zuba mai ido
Haqiqa yusuf yasan wannan zaman kalen fitinane shiyasa ya dago kai fuska a murtuqe yace dan Allah kai mgn kana gasamin zuciya da maganganunka da suke Sa dan uwana zubda qwallah

Ayijar zuciya ya danyi
Yace Ahmad batun aurenka da Aysha babushi dan ita Aysha tana da mijin 😳😳😳
Cikin razana da fargaba da bugawar zuciya ya katse shi da meyasa ? Waye mijin tadin ? A ina yake ? Hannunshi Na dafe da qirjinshi yake wadannan tabbayoyin a take sukar zuciyarsa ta tsananta wani nauyi ya danni maqoshinsa
Zufa ta fara ketomai tsoro mai tsanani ya rufeshi har cikin hanjinshi yake jin sanyi Na ratsashi
Itako Aysha tunda taja wani numfashi sai ta zama mutum mutumi a zaune sai barin da jikinta keyi cikin mmk abin yusuf yace ai wannan mgnar hogice wayeshi da za,a hana dan uwana farin cikinshi akan wani can banxa tun tana qarama yake wahala da ita wlh ni dinnan a matsayina Na yayanta ni zan aurar da ita ga dan uwana Adam ya dan kalli Bappa Yaya a fakaice yace cikin yanayin kaji tsohonnan da zance shirme ai wanan ba huruminka bane sai ka bari iayenmu suyi ikonsu a kanmu Allah sarki Ahmad duk sun rikice sabida bidar farin cikinsa dama Ku hausawa kunce nagari Na kowa
Su Usman ma duk sunyi zurui Abdul mai saurin kuka shikam da Sadiq kuka suke sosai Rabi,u kuma sai kada kanshi yake a hankali yace (nayeku Na ko jibare ) tsufa ko rikicewa ne
Baba bello ne ya dan rinqa musu fada cikin qarfin hali yana sabida me zaku samu a gaba kuna kuka ko ance muku mutuwa akayi da gyar dai suka dan tsaqaita sai yanxu Bappa Yaya yaci gaba yace Ahmad tabbayoyinka harsunmin yawa duk da dai zan amsa ma ka su yanxu wasu kuma sai wataran zakuji amsar sai batun aurenka da Aysha babu shi domin kuwa ita tana da miji
Amman duk da haka ba hanaka sure za,ayiba tunda an dakatar dakai kan Aysha haka nan kuma an mayarma ka da yar uwarka Maryam a madadinta
Sai yaxu Usman yace toh wai waye ne wannan da za,abashi Aysha a hana ya Ahmad ita ?
Yusuf ne shine mijinta shine Abokin rayuwarta shine tsohon alqawarin zuriyar nan ya basu amsa

daram duumm ras ras zuqatansu suka rinqa amsawa cikin firgici da razana ta dago kanta a take zufa ta keto mata bakinta har rawa yake tana waye kace?
dan uwanki yusuf nake nufi Adam ido ya zazzaro waje cikin dimuwa yace (hey ado andi ko a yeccata bo) kai Kasan abinda kace kuwa shiru yayi bai bashi amsaba
πŸ˜­πŸ’—πŸ˜±
Cikin dimuwa da fargaba Ahmad ya dan ja guiwarsa ya qarisa gun Abba hannushi ya daura kan guiwowinshi ya dago kanshi ya zuba mai ido cikin wani can ji da muryarsa tasamu yace Abba gskanta min furucin mahaifinku shin zancenci gsky ne ya kuma batun haramcin auren nasu Abba ko ya mantane Aysha da yusuf uwa daya uba dayane ? Abba matuqar ka gskan tamin toh nayi alqari koda zan rasa raina nane
Da sauri yusuf ya qarisa gunda yake yasa tafin hannushi ya rufe bakinshi

Toh masu karatu Ku biyoni muji wannan wanne irin rikitaccen Al,amarine wannan sarqakiya ya zata kaya

By garkuwan Fulani 85
[4/9, 2:23 PM] β€ͺ+234 909 785 3276‬: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
MI,WASMITI.....page 8⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
Da sauri Ahmad ya qarisa kan kujerar da take zaune zama yayi daf da ita yana klon fuskarta cikin yanayin damuwa da tabbaya hannushi daya yasa yana shafa fuskarta da tayi jawur yayinda ta dan manne jikinta da nashi tasa hannuta daya ta sankalo hannushi ta daura dayan kuma kan hanun nashi ta dan ranqwafar da kanta kan damtsenshi
Cikin zaquwa yace Ummi meya sameta ? Cikin fushi da jin haushi Ummi ta nuna Yusuf dake zaune can gefe kan dining table ai kasani Ahmad ba mai salon muguntar nan sai shi din shugaban mugaye ko yaushe mutum bai da aiki sai cin zali nan taci gaba da fadan kamar forko qara matsowa kusa dashi tayi cikin fada tace wlh ina gaya maka ka fita harkar yaranan idan duka kake son yi toh dole sai ka haqura sai randa ka haifi naka 'yayan amma bamu zaka yi ta dakawa yaraba daga yau sai yau ko mugun klo ka kuma yiwa yarannan ranka zai baci
Sosai Ummi take mai fada gaba daya shi kam ya gama cika yadda take mai tsababi a gaban qannenshi kanshi ya. Sunkuyar duk da hali irin Na Yusuf baison bacin ran iyayenshi baison yaga ransu Na baci a kanshi cikin yanayinshi dayafi kama da baya son mgnan ya kalli Ummi a hankali ya bude bakinshi yace dan Allah kiyi haquri Ummi daga nan bai kuma mgn ba
Ahmad kuma dake klonsu duk ya fahinci abinda ya fada da kuma abinda ke zuciyar saπŸ’›ya tabbata tsanar Aysha fadannan ya qara mai shiyasa bai fiye son ana mai fada a kan lmrin taba
Hankilin shi ya mayar kan Abba da yayi shiru ya zuba mai ido cikin ta kaici ya bude baki kamar maiyin fada sai kuma yace Yusuf am Allah ya shir yeka ya tausasa maka zcyar ka πŸ’› yasa maka qaunar yan uwanka Allah sarki Abba shi bai iya fada da mugun baki ba a rayuwarsa shiyasa komai lamarinsa yafi tfya da Ahmad
Borkono 🌢sai Baba bello gaba daya halin Yusuf halin wan mahaifinshi ya dauka bba bello shiyasa duk bala insu da masifarsu su suna shiri da juna lkta da dama ganin Abba da Ahmad suke a matsayin su kamar basu damu da raini ko wani abu ma kamanci shiba Shiyasa kuma ba komai Yusuf keyiba bba bello zai fadaba sai dai ya zuba musu ido yana dan fara,a
Bayan sun kam mala cin abinci kamar yadda suka saba in sunzo mambila duk haduwa suke a parlon aita hira
Yanzuma duk suna ta hira sai Yusuf da Adam da suka fita yayinda Ahmad kuma yau jinya yake tuquru duk ya susuce a kan abar qaunarsa itako sai zuba shogoba da sakalci take tun dazu yake ta faman lallaba mata koda tea ne ta dan Sha taqi ya dan kalleta cikin jin tausayin ta yace plss Aysha tashi ki dan Sha ko kadanne a hankali ta qara male hannushi tai rau rau da ido cikin sanyi mirya tace ya Ahmad ni ya isheni bana jin yunwa hannushi daya ta kamo ta daura kan wuyanta tace kaji jikina fa zazzabi nakeji
Jikin kam yayi zafi sosai shiyasa da sauri ya miqe ya dan debo ruwa a dan roba da dan qaramin towel a hannishi ya dawo gun ya zauna ya dan kamo hannuta ya zaunar
Daidai lkcin su Adam suka shigo Adam ya kallesu da kyau yace sannu da qoqari biyaye
Usman dake gefensu tun dazu yake binsu da ido ya dan ja tsaki ya juya kanshi yana wlh ya Ahmad yarinyar nan tama rainaka kai kuma sai wani biye mata kake Rabi.u ya dan harareta yace ai ni nafijin haushin me biye matan ai wlh ba mgnin ta sai Hamma Yusuf
Bki ta dan tura gami da dan hararsu tace ehdin
Da sauri ya dan juyo gunta gami da watsa mata harara cikin murtuqe fuska yace (hey Ummuh hado moi on qworgima hado de a tonta ta amin ) ke tashi daga nan waye Sa,anki anan da kike bamu amsa
Cikin dan jin haushi da tsanarsa ta miqe tana klon Ahmad hannuta ya kamo ya ranqwafar da ita yace biyaye (anon on wari tawi amin hado mai ko ?) Ku kukaxo kuka samemi a nan din ko ?_toh dan haka kuyi gaba ..
Dry Adam yayi yaja hannun Yusuf yace (en dillu) mu tafi suka tafi suma su Usman tfya part ensu sukayi
Shiko sai da ya samu ta danyi bacci ya zame hannushi ya dan gyara mata gashin kanta ya dan shafa kan kuncinta da yasha maruka yayi jawur ya dan kalli Ummi da Nenne da suke dan hirarsu qasa qasa yace Ummi tayi bacci ya dan qarisa gun Nenne yace Nenne am (sai fajira ) good Night Nenne Na ya juya ya tf Murmushi tayi tana jin dadin yadda dan nata gudan jininta yake gwada mata qauna sosai
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
Yau Sunday kuma yaune zasu Koma cikin taraba su baba Umar kuma gobe zasu nufi Yola tun wayewar garin ranan Bappa Yaya da yaranshi da matanshi da qaninshi gaba dayansu suke babban parlonshi suna ta tattaunawa
Su Nenne kuma Suna ta shirinsu yayinda su hydar da Usman suka tfi cikin rafi Adam kuma da Amira gidan kawun amiran suka tf sai Ahmad dake kula da Aysha Suna parlon su Ummi nata xirga zirgansu a hankili ta kirashi
Ya Ahmad cikin kulawa yace Na,am Aysha meke faruwa ?
Ta da sunkuyar da kanta tace ya Ahmad wai pisa bilillahi me nayiwa Hamma Yusuf ne ya tsaneni haka ?har baya iya boye qiyeyyata kowa Na sona Amman bandashi meyasa ne
Murmushi ya danyi mai dan sauti yace Aysha ina kika tabajin dan uwa ya tsani yar uwansa biyaye yana sonki shi dai kawai haka halinshi yake yana da mishkilanci kuma baison raini
Da sauri ta kallishi gamida sake hannishi ya Ahmad kenan ni Na rainashi ne ? Dry ya danyi ta kuma dan kauda kanta ta dan tura baki tace wlh ai dama Na ganeka ya Ahmad wlh kafi son Hamma Yusuf a kaina kai akan kowama ko yayi laifi baka gani kuma ka sani sarai ( o kallu do ) shi mugune bai da tausayi
Shirun da taji yayine yasa ta dago ta kalleshi ita ya zubawa ido cikin wani yanayi duk yanayinshi ya sauya a hankali yake dan girgiza kanshi ya maida bayanshi ya jingina jikin kjra ya dan lumshe idanunshi da sukayi jaa cikin sanyin murya yace
Yusuf da Ahmad da Adam wasu abune guda 3 da Allah ya halitta wadanda suka kasance tamkar hanta da jini a jikin juna farin cikin daya cikin mu 3 dinnan ya wada cemu yayinda bakin cikin daya zai mana illah a zuqatan mu πŸ’˜ baki daya rayuwarmu zata kasance ne tamkar taurarin nan guda 3 da suke nuna alamun lkci Aysha ina son yan uwana bana taba jurar baqar mgn a kansu haqiqa ina son yusuf amma duk da hakan shi yafi sona yusuf da Adam jinina ne ya dan tsaya ya bude idanshi ya zuba matasu itama din gaba daya shi ta warema NATA idan da sukafi kama Dana maijin bacci a zahiri ta ga gskyar abin da yake fada a kwayar idanshi a hankili ta nuna kanta tace ya Ahmad harni bankai Hamma Yusuf a zuciyar kaba ? kai ya girgiza yaci gaba da cewa shi Yusuf da Adam jininane su ke kuma bugugun zuciya tace πŸ’—πŸ’˜ tabbas in babuke toh ba Ahmad cikn wani irin sauti yace Aeeeshahhh ni da kaina bansan wane irin so nake miki ba Aysha sonki a zuciyata babban sukane πŸ’˜ Na tabba ta in ance babu ke a a cikinta to bani a duniya 🌍 jawota yayi ya manna kanta kan girjinshi yace kinji bugun zcyta toh duk numfashin da zan shaqa a duniya da qaunarki nake shqarsa a hankali tayi sassanyar ajiyar zucya tace ya Ahmad har abada ZAMU kasance tare
A haka sukayi ta jaddawa juna son da qaunat da sukewa junansu har su yusuf da Adam dasu hydar suka dawo

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

Banyan sunyi sallan LA,asar duk suka hallara a parlon da shirinsu Na tfy kamar yadda suka saba komai Na zuriyarsu a daidai wanan lkcin suke tsara komai da duk wani hukunci ko umurni da zasu bayar a zuriyar tasu toh hakama yanxu duk sun nitsu dan jin ta bakin Bappa yayan
Nima kaina Aysha Ali Garkuwa Na nitsu sosai dan Na tabbata yanxune ZAmU ciga cikin lbr

By garkuwan Fulani 97 πŸ“±
[4/9, 2:23 PM] β€ͺ+234 909 785 3276‬: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
MI,WASMITI....page πŸ”Ÿ Na Aysha Ali Garkuwa
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

Hannushi Na kan bakinshi ya dago kanshi ya rinqa girgiza mai kai da zuba mai manyan idanunshi da suka qanqance sukayi jawur
Shi kuma sai dafe hannushi yayi a qahon qrjinshi a hankali ya ciro hannushi daya ya zame hannun yusuf daga rufe mai baki da yayi ido yusuf din ya zuba mai cikin jin ta kaici yace haba biyaye meye amfanin furucinnan ina tunanin ka ya tfi me amfanin yarintarka shin kai yarda kayi da ( talol ) tasuniyar Bappa Yaya ya za ayi kwanyarka Na aiki kake bin shirmen qoqolwar tsohon da ya gama birkicewa kai ka gaskanta zancenshi ya dan dakata ya dan kalli iyayenshi cikin yanayin bada shawara da dan rusuna kai yace bba bello tun tini nake CE muku ku rinqa kula da yanayin zantu kan mahaifinku amma sai kuke ganin Sherri nake mishi to ai yau kunji kun kuma gani kuma ya muku ta yadda dole ku yarda tabbas ni nasan tsufa ta birkita tunaninshi zancen gsky ku kaishi likitan sakatiri ya dubashi............
Baba Hamisu ya daga mai hannu da sauri yayinda yake mai donqolo yace kai yusuf ya isa haka mahaifin namu a gabanmu kake cewa ya zauce
Kai ya daga ya kalli baba bello ya kirashi cikin Neman qarin bayani yace wai baba ku kun yarda lfyarsa lau kun kuwa ji abinda yace ko a lbrin films da novels kun taba jin inda yan uwa uwa daya uba daya sukayi aure kun tabaji ?
Ya qarishe mgn cikin tabbaya yaci gaba da cewa toh haqiqa wannan al.amari yana Neman wani duhu da zai kawo cikin wannan zuriya tamu
Abba ne ya dakatar dashi da cewa ba kai muke sauraro ba kuma ba hukuncinka muke jiraba dole tsarin mahaifinmu xamu bi
Cikin sauri Usman yace Abba koda ya sabawa sheriyarmu ta musulunci ?
Baba bello ne ya katseshi ba tare da ya bari Abba ya bashi amsaba
Shikam Ahmad tamkar robot ya zama

Cikin yanayin jimami Abba ya dafa kafadar Ahmad ya dan sun kuyo ya kalleshi cikin sanyin jiki da murya yace eh Ahmad Aysha tana da miji kuma yusuf shine mijinta kai kuma a madadin family enmu gaba daya ina mai baka hqri ha kazalika ni Na zabarma matar aurenka Ahmad Na zabama Maryam yar uwarka mu kuma yar qanwarmu
Ido kawai ya zuba musu sai duk mai mgn ya bishi da ido ya rasa me qoqolwarsa ke tunawa ya manta meye farin cikin rayuwa ga wani azabebben nauyi da ya tokari qahon qirjinshi da maqoshisa tunani yake ko mafarkine
abba ne ya kuma katseshi da kiranshi cikin yanayin Neman alfarma
Ahmad

Please Login or Register in order to submit comment