Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaisuwa mana ,ina kwana

naki na amsa ,tunda saida na roka ,yamaida kallanshi ga meimah ,yace pls meimah ,ki bani aron kanwarki ,xata dan tayani Aiki ,Indai ba abinda xata miki


Meimah tace "babu abinda xatamun ,saidai xaku barni cikin kadaici ,

Murmushi yai ,yace "Ai ba matsala ,in kin gama abinda kike kya taho ,Ki tambayi offis ina xa'a nuna miki ,

Tom ,shikenan kuje ,meimei ,sai na taho ,

batai magana ba ,ta Mike ,tabi bayanshi ,byan ya fita ,


yana gaba ,tana bunshi a baya ,tana karewa bayanshi kallo ,cikakken namiji ,tunda ga sama har kasa ,mai kyan haiba ,tafiyarshi ma kadai ,taisa ,ta sace xuciyar mace ,ko batai shiri ba ,tana wannan sake saken har suka karasa offis in ,

sanyin kamshin air freshner mai dadi da tafi da xuciyane mai kuma kwantar da hankali,ya bugi hancinta ,wata iriyar nutsuwa taji ta shigeta ,sbd shigowa ,hadadden offis din da ya ratsu iya ratsuwa ,

Watsa idanuwanshi yai a kanta ,ya nuna mata kujera ,yace xauna meimei ,

Xama tai akan kujerar mai tsabagen laushi ,ya juyo mata computer saitinta ,ya ajiye mata wasu takaddu ,yace "typing insu xakimin ",
kana ya koma kan kujerarshi dake saitinta ya xauna ,

Tunda ta dukufa ,ta fara aikinta ,shikuma ya xuba mata idanuwa yake kallanta ,wanda hakan ya faranta xuciya da ruhinsa ,
indai ta dago sai sun hada ido ,kuma hakan baya sashi janye idonshi daga kanta ,ita kuma saidai tadinga jin wani yar xuciyarta na bugawa ,

sai da taci karfin aikin ,kana ta dago ,cikin shagwaba ,tana matsa hannunta tace "wash "

Wani irin kallo maheer ,ya jefeta dashi ,kana cikin wata iriyar murya dashi kadai yasan halin da yake ciki ,yace sannu kin gaji ko ?
ta dan lumshe idonta ,tace uhmmm ,
cikin rudewa yace "muga hannun "
ya kawo hannunshi yana kokarin kama hannunta ,da sauri ta janye tana jifanshi da wani irin kallo ,shima kallanta yake ,wanda ya nuna gaba dayansu,sun shiga mayen SO ,

karar xa'a bude kofane ,yasasu dawowa daga duniyar da suka tafi ,da sauri maheer ya tashi daga tsugunan da yake ,

Meimah ce ta shigo ,murmushi maheer yayi mata ,itama ta sakar masa murmushi ,
yace yauwa meimah ,Amshi meimei ta gaji wai ,

Karasowa ciki tai ,tana bari naga aikin da tayi ya gajiyar daita ,dan nasan ragwantar sis ,
takai karshen maganar ,yayin da take dubawa ,

Maheer yace "kin tabbatar meimei ba raguwa bace ba ko?

Murmushi tai ,tace "Ai dama tsokanarta nake ko sis?

Murmushi meimei ,tai ,ta tashi daga kujerar ,tace xauna tukun kedai Ki fara ,

ta koma kan kujerar da ke gefenta ta xauna ,suna dan taba hira tsakanin Su uku jefi-jefi ,Amma yawancin maganar maheer sai ya ambaci *meimei*...........





E.W.F
[11:15pm, 9/9/2017] YAR GATAN HUDAH: ♠♣🖤♣♠♣
*BABBAR CUTA*
♠♣🖤♣♠♣

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM♻

( *GORON SALLAH*)



Writing by ;♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*

~this page dedicated to shugaba jagaba hakima tauraruwar pure moment ,FATTY AXLAND ,da dukkanin membre in pure moment of life writers,Ana tare irin har abada dinnan~😘

*81-85*
cikin wata guda ,maheer da meimei sunyi shakuwa mai tsanani ,indai bata da Aiki to tana offis inshi ,duk randa bata xoba ,to shi xai jemata ,gaba dayansu xuciya da ruhinsu Sun makanto à kaunar juna ,irin sosai da sosai dinnan ,
Xuciyoyinsu Sun Aminta ,idan basa tare baxasu iya rayuwa ba ,

duk kaucewa soyayyarshi da meimei take ,saida ta tsunduma tsundum ,Amma tanaji À ranta xata bar soyayyarshi à ranta ,indai har bai furta mata ba ,koda yama furta mata ,baxata Amince ba ,sbda irin tarin kaunarsa da take gani à idon YAR UWARTA ,hakanne yasa wani lokacin take lallasar xuciyarta ,

À randa daddyn maheer ya dawo ,da daddare xuwaira ke samunshi da maganar nana da maheer ,kan cewa kaunar juna suke ,me xai hana à hadasu aure kawai ,
sai yace mata ,ta bari ya fara tuntubar maheer din yaji ,

bai tashi yima maheer magana ba ,sai da yasha ganinsa yana shiga offis in meimah ,sai abun ya daure masa kai ,shikwa maheer sinturin da yake offis in meimah ,meimei ce ya kwana biyu bai gani ba ,in yaje offis inta kuma bai samunta ,itakwa tana ganinshi ,boye mishi take ,sbd à duk sanda xata ganshi soyayyarshi ruruwa take kamar garwashi à xuciyarta ,shiyasa take so ,ta karfi da yaji ta yakice soyayyarshi ,


suna xaune à falon daddyn nashi ,suna hira ,ya sako mishi xancen ,
yace Auntynka tamun maganar wai kuna son juna kaida Nana ?
fuskarshi ce ta canja kala ,alamun ranshi ya baci ,yace daddy ni Sam bansan da xancenba ,

daddy ,yace "Toh maheer shekarunka sunja ,kana bukatar iyali ,domin shine cikar mutumcinka ,ban tabama xancenba ,Amma yau nama ,sbd n'a gaji da xubama ido ,dan haka yau munyi magana da hjya harisah(mami),sbd n'a lura kana soyayya da yarinyarta ,dan haka n'a sanar mata ,gobe xaka fara xuwa gunta cen gida ,ku fahimci juna ,dan ba lokaci xa'à jaba ,

Murmushi ne ya subucewa maheer ,danshi à tunaninsa meimei daddynshi ke nufi ,danshi har ga Allah bai kawo meimah daddynshi ke nufi ba ,dan à yanxu yama manta daita ,dadi ya baibaye XUCIYA DA RUHINSA ,domin ya kusa samun SANYIN IDANIYARSHI ,

ganin murmushi à fuskar yaron nashi ,ya tabbatar mishi lallai yana san meima,


****

Kwance take bisa gadonta ,tunaninshi ya cika mata RUHI ,saiga meimah kan gadon kamar an jefota ,
cikin farin ciki da annushuwa tace "sis albishirinki ,
cikin dashe kyawawan hakoranta masu kyau tace "GORO "
Maheer n'a sona ,gobe xai fara xuwa guna xance ,mami da daddynshi Sun gama magana ,💃🏼baxa'à dau lokaci mai tsaho ba ,

À take bugawar xuciyarta da daukewar numfashi ya sameta ,kwalla ta ciko mata ido ,bata iya daurewa ba ,saida hawaye ya xubo mata fuska ,

take annnurin da ke fuskar meima ya dauke ,ta girgixata ,sis lfyrki kuwa ,kinji me nace miki ?

Murmushin yake mai kama da kuka meimei tai ,tace n'a jiki sis ,n'a tayaki farin ciki ,Allah ya yaye miki kuncin da ke damunki ,nikwa nasan nawa dashi xan koma ga mahalliccina ,ta share kwalla ,

cikin nuna damuwa ,meimah tace "wani kunci ne ke damunki sis ban sani ba ?"

kar ki takurani sai kinji sis ,dan n'a riga n'a barwa XUCIYA DA RUHINA sirrinshi ,

shiru gaba dayansu sukai n'a yan sakanni ,dan meimei ta kawar da abinda xai xowa meima à rai ,sai ta Mike ta nufi gun kayansu tace ,
"Sis bari n'a xaba miki kayan da xakisa tun yanxu ,kuma da kaina xan dandasa miki kwalliyar da maheer in ya gani xai shiga rattabo miki kalaman love mai ratsa xuciya ,"

Murmushi meimah tai ,tace kamar kinsan abinda ke raina 🤣

sis kenan ,im so happy da jin daddadan labarinnan ,dan haka xan nuna miki farin cikina ,ni xan shiryaki ,yadda maheer yana ganinki xai gigice,

dariya sukai à tare suka tafa .





****
Washe gari ta kama saturday ,tun safe meimei da meimah suke shirin tarbar maheer ,xuwa yamma gidan nan ya dumame da kamshin soye -soye ,
Sun gama shiri tsaf ,n'a komai da komai ,
Xuwa karfe 06:00pm maheer ya dira à gidan ,sanye yake cikin shadda dakakkkiya mai dan ubansun kyau ,ruwan makuba ,An mata Aiki copy in xare ,hula takalmi ago go duk ya sanya copy ,yayi matukar kyau ,sai xuba kamshi yake ,xuciyar nan tashi kar ,yau xai bayyanawa meimeinshi kalmar SO,

An mishi masauki A falon da Abba ke saukar baki ,

yana xaune shiru ,yana ta jiran tauraruwar xuciyar tasa ,saiga meimah ta shigo ,cikin doguwar rigar codless ,fitet gouwn ,kalar light blue ,mayafi,yari da sarka,takalmi agogo ,ta sanya dark blue ,tayi kyau sosai da sosai ,sai kamshi take baxawa ,

xama meimah tai kan kujera ,kana tace ,barr barka da yamma ,

cikin dauriya ,da halin da yashiga yace "barkanki dai meimah ya gida ?

lfy qalau ,kaxo lafiya?

lfya qalau ,

Tun daga haka dukkaninsu sukai shiru ,shi maheer yana jiran ta tashi ta tafi ,yayin daita kuma meimah take jira taji yafara xubo mata kalamai masu ratsa xuciya,

shiru kake ji falon tsit ,maheer sai danne danne yake cikin wayarsa ,

Meimei ce ta shigo dauke da tire à hannunta ,sanye take cikin doguwar riga yar kanti ,red colour ,ta yafa mayafin rigar ,fuskarta ba kwalliya ,dan ko kwallli babu à cikinsa ,Amma duk da haka tayi kyau ainun ,

Kamshin turaranta yaji ,ya dago da kanshi ,yabita da kalllo har ta ajiye tiren dake hannunta ,

murmushin karfin hali tai ,tace "barr ina wuni?

idaniyanshi à kanta yake amsa mata ,lfya qalau meimei ,ya gida?


lpy qalau ,barr banda San wahalarmun da sis ,da kana santa kaki sanar mata ,Allah ne ya taimakeka da ba'ai maka shigar sauri ba ko sis ,

Murmushin yake meimah tai ,sbda ganin yadda maheer ya shagala da kallon meimei ,dan da alama baima saurari abinda take cewa ba ,tace sis jeki ciki kawai ,

juyawa meimei tai xata bar falon ,maheer ya taso yana kiranta ,meimei ina xaki tafi ki barni ,byan gurinki naxo ,

cikin dauriya meimei tace gurina kuma ,,gurindai sis ,bata jira me xaice ba cikin sarsarfa tabar falon ,

Xuface ta lulube maheer ,to me ke faruwa ,daukar wayarshi yai da key in mota da ke kan kujera ya fice ,

Meima shashshekar kuka take ,daga gun da take à xaune ,
Mikewa tai ta nufi daki da gudu ,kan gado ta fada tahau rusa kuka ,

Meimei kwa kichen dinsu ta nufa ,tasha kukanta ,sbda gudun kar meimah taxo ta tadda ita ,

sai da meimei ta gama kukanta ,ta gyara fuskart,ta nufi daki ,ta tadda meimah n'a tikar kuka ,

dagowa tai ta kalli meimei tace sisi tsakaninki da Allah babu komai tsakaninki da maheer?

cikin sanyin murya meimei tace ,wlh babu komai tsakanina dashi ,sai mutumci ,

Kwanciya kawai meimah tai à ranta tace koma mene ne xai fasu........








E.W.F
[3:54pm, 9/10/2017] YAR GATAN HUDAH: ♠♣🖤♣♠♣
*BABBAR CUTA*
♠♣🖤♣♠♣

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM♻

( *GORON SALLAH*)



Writing by ;♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*

~This page dedicated to maryam À Abubakar ,Rabbi ya baki lafiya ingantacciya ,mai dorewa ,tare da alummar musulmi Ameen ,muna sanki irin har à XUCIYA DA RUHI DINNAN~😘



*86-90*
kasancewar ana ta kiraye -kirayen sallah ,saida maheer ya tsaya yai sallah à masallaci ,sai yadan ji xuciyarshi ta samu nutsuwa kadan ,kana yashiga gida ,

gun dad inshi ya fara xuwa ya sameshi yana xaune ,yana jan carbi ,guri ya samu à gefensa ya xauna,

shafa kanshi Abba yadingayi ,yace yarona me ya faru ,naga fuskarka ta canja?

Sunkui da kai yai ,yace dad gun wa ka turani ne?

dad ,yace Wannan wata iriyar tambyace ,da wacce kake so ,byan haka ma ,Ai yarta budurwa daya n'a sani à gidan meimah ,

dad su biyune ,da meimah da meimei ,nikuma dad meimei nake soh nasha ita kake nufi ,saida naje naga sabanin haka ,

Wani irin su biyu kuma ,kar ka maidani wanda baisan abinda yake ba ,

Wlh dad yaranta biyune ,

fuskar dad cike da mamaki ,yace mikomun wayata ,mikewa yai yaje ya xarota daga cagi ya kawo masa ,

Numb mami ya nemo ya danna mata kira ,

Mami da ke xaune à falo ,kan meimah n'a kan cinyarta ,kasancewar Abba baya gari ,wayarta dake kusa daita tadau kuwa ,da hanxari ta dau wayar ,ganin me kiran nata ,

byan Sun gaisa ,daddy yace "wata magana naji gun maheer ,wai yaranki biyune ,meye gaskiyar lamarin ?"

mami cikin fushi tace ,"Ni yarinyata dayace meimah ,sai kannanta ,kanana twinc,

dad yace ,toshi yace "meimei yake so ,ba meimah ba ,

Mami jitai gabanta yayi rararas ,tace "meimei Ai ba ya"ta bace ,byan hakama An riga an bada ita "

Wannan magana à kunnen meimei ta sauka ,taxo shigewa ,taje kichen domin samun abinda xata ci ,maganar an bada ita ,bata daga mata hankali ba ,kamar Yadda taji tace "meimei ai ba yata bace ,hawaye suka fara sintiri à kumatunta ,tun tana boye sautin kukan nata ,har ya fito fili ,

Juyowa mami tai tana kallanta ,byan ta idda wayar ,

tsugunawa meimei tai ,tace mami n'a rokeki ki sanar dani mahaifiyata ,ina San jin dadin uwa ,kamar yadda kowa yake ji ,

cikin rashin nuna damuwa mami tace "ko baki rokeni ba ,xan sanar dake ,Amma saidai ki sani ,babu ke bajin dadin uwa har abada ,

À gigice meimei ta dago ta kalleta ,
Mami taci gaba ,bakin cikin da mahaifinki da mahaifiyarki suka sakani ,ni kadai nasan irin axabarshi ,banda mahaifiyata ,da baxaki taso ki tadda kanki cikin gidannan ba ,da saidai kiyi rayuwa gidan marayu ,kamar yadda uwarki ta taso anan ,sbd mahaifiyata ta bani Amanarki shiyasa n'a barki anan gidan ,
Amma duk sailin da naganki ,ina jin takaici ,inajin n'a tsaneki ,tsanar da naiwa mahaifiyarki à lokaci daya ,ita ta juyo kanki ,
ta share kwalla ,sannan ta bata labarin abinda ta sani ,dangane da mahaifinta da mahaifiyarta ,

Kuka meimei take kamar xa'à dauki ranta ,bare da taji mahaifanta Sun rasu ,da take kwadayin samun soyayya gurinsu ,kuka take wiwi ,ji take kamar yanxu ne mahaifan nata suka rasu ,
tashi tai ta nufi daki da gudu ,

Mami ta juyo ga meimah da itama take kukan rashin mahaifinta ,tace mata share hawayenki mu fuskanci matsala ta gaba ,maheer yace ba ke yake soba ,meimei yake so ,garin ya har yasan meimei?

meimah tace ,tana yawan xuwa offis ina shiyasa yasanta ,

Baxaki hankali ba ,har yanxu meimah ,tun yaushe n'a takareki ,da karki sake taje miki offis saboda gudun haka ,dan duk inda shegiyar yarcan ta shiga sai an sota ,

cikin sanyin murya meimah tace mami ai hakan À JININTA YAKE ,dan haka ni n'a hakura da son maheer ,n'a bar mata ,tunda ita yake so bani ba ,

tsawa mami ta daka mata ,da tasata dinke bakinta ,mikewa mami tai ta nufi dakinsu ,À kwance ta tadda ita ,tayi ruf da ciki akan gado tana rusar kuka ,

Mami tace "maheer yace ke yake so ,nikuma naga maheer bai dace da mara ASALI ba irinki ,dan haka nace ansaka miki rana ,dan muddun maheer bai auri meimah ba ,baxai aureki ba ,dan haka n'a takareki ,in kika sake kikace maganar danai ba haka take ba ,ko kika biyewa maheer kukai soyayya ,to ina mai sanar miki saidai ki dawo ,titi da kwana ,dan xan koreki daga gidana ,sannan kuma xansa à koreki daga Aiki ,ina dai dada tuna miki baki da ASALI ,daga haka ta fice daga dakin ,
Wani sabon kukan meimei ta kara fashewa dashi ,kusan kwana tai à ranar tana kuka ,gashi ita kadaice à dakin mami ta hana meimah xuwa ,



Bangaren maheer kuwa ,byan dad Sun gama waya da mami ,ya sanarwa maheer Yadda sukai ,
Maheer yace ,gaskiya dad ,banjin maganar bada ita gaskiya ne ,dan haka baxan cire rai daita ba ,har sai nayi bincike n'a gano gaskiyar lamarin ,

dad yace ,nima dai wani tunani yaxomun xuciya ,dan haka baxan hanaka ba ,duk abinda kake so ,nima shi nake so ,Allah yashi maka albarka,
yace Ameen dad ,sannan suka fita xuwa masallaci danyin sallar isha ,





****
washe gari da meimei ta tashi ,idanuwanta sunyi luhu-luhu sbda kukan da tasha ,ga kanta da yake mata matukar ciwo ,gidan gaba daya yaimata xafi ,gashi yau ba ranar Aiki ba ,bare ta fita ko taji sanyi à xuciyarta ,

À haka take à limke a kan gado ,ita kadai cikin dakin ,inma mutuwa xatai babu wanda yasani ,

Muhseen da ya fito break ,yaga baiga meimei ba ,kuma byan ba haka suka saba ba ,Mikewa yai yanufi dakinta ,

rudewa yai gaba daya da yaga yananyin da take ,cikin rudewa yake tambayarta ,meimei lfya me ya sameki ?

fashe masa tai da kuka ,yace look meimei kinsan kukanki n'a tadamin da hankali ,ki shiru ki sanar dani abinda ke faruwa ,

cikin kuka meimei ta sanar dashi abinda ke faruwa ,harda abinda ya wakana tsakaninsu da maheer ,da kuma soyayyar da takewa maheer ,


gaba daya xuface ta rufe muhseen ,tashin hankali ya bayyana gareshi ,jin cewa meimeinshi ta fada soyayya da waninsa ,baiga laifinta ba ,laifinshi ya gani ,da ya kasa furta mata yana santa ,baiga Amfanin BOYEYYEN SO ba ,da XURFIN CIKI dan su suka kaishi ga wannan halin ,tabbas yana son meimei ,irin sonnan da xai iya sadaukar mata da komai ,yana San farin cikinta ,baisan bacin ranta ko kadan ,dan haka dolene yayi kokarin samawa meimeinshi farin ciki ,yana so yaga wallwala à fuskarta ,yana so yaga FARIN CIKI ya dore a rayuwar meimeinshi ,

share kwallar idonshi yai ,yashiga lallashinta da kwantar mata da hankali ,yace ta tashi ta shiga wanka ta shirya su fita ,ko ta rage damuwa ,shima ya fita domin ya shirya ,

tashi tai tashiga toilet ,cikin Jin dadi ,domin xaman gidan ya isheta ,sosai da sosai,


suna cikin tafiya a mota ,suna dan taba hira jefi-jefi ,traffic light ta tsaidasu ,

Maheer dake cikin tasa motar ,ya tafi duniyar tunanin ta ina ,xai fara binciken nan,kamar ance ya kalli gefensa ,yai toxali da SANYIN IDANIYARSA,tana sakarwa Muhseen murmushin da yake tafi dashi,wani irin daci yaji à xuciyarshi ,wanda bai taba jin irinsa ba ,rintse idonsa yai wanda à lokaci daya ya canja coulor,yana cikin wannan halin aka basu hannu ,da gudu yabi bayan motarsu ,

gidan abokinshi mustapha, Muhseen yakai meimei ,da fara'à da komai matarshi mumtax,ta tari meimei ,kasancewar tasan Muhseen sosai ,

nan ta taresu ,da kayan break ,sbda basu dade da kammalawa ba ,mustapha ya fita ,

Muhseen yace ,Aikwa kamar kinsan batai break ba muka fito ,ga tanan Amana ki kulamin ita ,kisata dariya ,xanje ni naga mustapha ,xuwa yamma insha Allah xanxo na dauketa ,

Murmushi ,mumtax tai ,tace insha Allah xa'ai mata duka abinda ,inma taki cin abincin xan mata dura ,shikuma yasa kai ya fice ,


yana fita ,yatadda maheer à tsaye à jikin mota ,karasowa inda yake maheer yai ,ya bashi hannu suka gaisah ,maheer yace, im maheer mahmud ,Muhseen ma yace ,cwt name ,im Muhseen ,ya ganeshi shine maheer din da ya dauke masa xuciyar meimeinshi à take yaji kishinshi ya kamashi ,Amma ya kanne,

Maheer yace ,Nice name ,dan Allah ko xansan meye tsakaninku da meimei?

Murmushi Muhseen yai ,yace ni yayanta ne ,mai kaunarta ,mai san farin cikinta ,mai kuma gaba da bakin cikinta ,dama xan nemeka ko baka nemeniba ,sbda samawa kanwata farin ciki ,domin farin cikinta shine nawa ,xanso mu shiga ciki ,xan sanar maka abinda kake son ji ,

kulle motarshi maheer yai ,yabi bayan Muhseen xuwa ciki ,
À falon kasa suka xauna ,nan muhseen ya warwarewa maheer komai ,da labarinta iya wanda yasani ,Amma ya boye mishi San da yakewa meimei,ya dora da cewa ,ni xan tsayawa kanwata sai ta samu farin cikinta ,

Abinda xakamin shine ,ka rikemun ita Amana ,ka kaunaceta ,ka kulamin daita ,kai yaki da dukkan mai takura mata ,in kamin wannan ka gama mun komai ,yakai karshen maganar cikin xubda hawaye ,

Maheer fuskarshi ta jike jagab da hawaye ,kuka yake harda shashsheka ,yaje suka rungume juna ,suna kuka ,kowa da kalar wanda yake ,maheer yace "n'a maka alkawarin xan rike meimei Amana ,xan jiyar daita ,dadin mahaifanta da ta rasa ,xan bata dukkanin kulawa ,xan ji daita fiye da kaina ,Muhseen ina San meimei tunkan n'a ganta ido da ido ,ina matukar santa ,wanda bansan iya kacinsaba ,kaunarta A JININA TAKE da itta xan koma ga mahalliccina ,dan banga ranar fitarta ba ,

sai da sukai kukansu mai isarsu kana suka lallashi kansu ,

Muhseen ya dauki wayarshi ,ya kira meimei yace taxo ta sameshi à kasa ,kana ya mike yacewa maheer bari shi ya tafi ,

maheer yadingai masa godiya ,shikuma yasa kai ya fice cikin KUNAR XUCI,

tana sakkowa idonta yai toxali da SANYIN IDANIYARTA ,mikewa yai yana kallanta ,sabon tausayinta ,soyayyarta ,kaunarta,muradinta ,à lokaci 1suka mishi rubdugu a XUCIYA DA RUHI ,

ta cage daga gurin da take à tsaye ta kasa motsi ,

cikin wata iriyar murya da take nuna yana cikin shaukin SO yace meimei kece farin cikina kece rayuwata ,meimei ban taba furtawa wata mace kalmar so ba ,Amma yau xan furta miki ,meimei ina sanki ,ina kaunarki ,sanki da kaunarki yashiga jinina ya ratsa shi ,meime i love u with all my heart

You are my always on my mind and in mu heart.
You are every thing i've ever wanted you présence in my life ,complètes me .

You are every thing to me ,i'm lost with out you.

You are my beautiful angel in disguis .

You are my angel,my princess,my baby doll,no one can take your place in my heart.


you are my joy.

🤣maheer fa ya haukace a love ,sai fayyace mata sirrin xuciyarsa yake ,lol,

Tunda ya fara maganar ta kumshe baki take kuka ,ya dago idanuwansa da suka rine à soyayya ,yace meimei ,me yasa kike kuka ,keda xaki farin ciki ?

cikin kuka tace "bana sanka maheer dan Allah ka nisanta dani ,ni An riga an bada ni ,ya kake neman tarwatsamun xuciyane?

Jin kalmar bata sanshi ,ba karamin raxanashi tai ba ,gun da take à tsaye ya nufa à xuciye,

tana ja da baya yana binta ,har suka kai bango,rintse idonta tai tana xubda hawaye ,shima hawayen yake ,yana kallan fuskarta,,yace wlh meimei karya kike kina sona ni nasan da haka,durkusawa tai kasa ta kife kantaa guiwa ,tace "nace maka bana sanka leave me a lone pls nd pls ,ka fita rayuwata,ta fashe da matsanancin kuka ,

Rintse idonshi yai ,ya fesar da wani abu mai xafi ,ya juya ya fice daga falon ,

Muhseen da ke cikin mota ,tun bayan fitowarshi kuka yake ya kasa tabuka komai,yaga fitowar maheer yana matsar kwalla ,yashiga mota ya jata à xuciye ,

Fitowa yai daga motar Yai cikin gidan .......







E.W.F
[11:16pm, 9/11/2017] YAR GATAN HUDAH: ♠♣🖤♣♠♣
*BABBAR CUTA*
♠♣🖤♣♠♣

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM♻

( *GORON SALLAH*)



Writing by ;♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*

*91-95*

pls meimei kukan yaisa haka ,ki dago ki bani amsar me ya faru ,naga shima ya fita yana hawaye ,

dago kanta meimei ,tai tana kallanshi ,tace "me yasa xaka saurareshi ,me yasa kake San karasa min damuwa ,kasan kana sane da abinda mami tace muddun n'a amince da soyayyarshi ?

to mami Allah ce ,ni ba burina n'a sa miki damuwa ba ,burina n'a samo miki farin ciki ,aduk inda yake ,ki ture maganar mami gefe ,ki kau da tsoro ,bata isa ta miki abinda Allah bai miki ba ,mutum ce kamar ke ,dan haka ki Amince da maheer ,yana MASIFAR SONKI ,ni nagani à kwayar idonsa ,ina da tabbacin xai rike ki amana meimei karki bari maheer ya kubce miki ,domin samun irinshi sai AN TONAH,
Nandai yadinga lallashinta ,da kalamai masu dadi ,wanda à xahiri tajishi ,Amma à xuci ba hakan bane ,


*****

washe gari ta kama monday ,meimei tayi shirinta tsaf ,cikin doguwar riga ,Ash coulor ,tayi kyau sosai ,ta dan goge kwallarta ,da tuni tare da meima suke yin shirinnan ,su fita tare ,Amma kalli kan DA NAMIJI Sun raba makwanci da komaima ,tasan yanxu ma Sun dade da barin gidan ,
Key din motarta ta dauka ta fita ,



tana xaune cikin offis inta ,tana yan rubuce -rubuce ,wasu dattijai suka shigo ,biyu maxa daya mace ,guri suka samu suka xauna ,gaishe dasu meimei tai ,suka Amsa ,

daya daga cikin dattijan ,mai suna malam sunusi ,ya daukko wani frame in hoto ya ajiye gabanta ,

daukar hoton tai ,tana gani ,wasu kyawawane à jiki ,mace da namiji ,da yar karamar yarinya à tsakiyarsu ,yar kyakkyawa kawa baturiya ,

dago kai tai tana kallanshi domin karin bayani ,
yace ,"yarinya wanda kike gani à jikin hotannan yarona ne ,dayar kuma yarinyar wayannance ,ya nuna sauran dattijan ,dayar kuma jikar muce ,

Shekaru da dama ,da suka wuce ,sukai mna sallama domin xai kawota ganin gida nan garin ,kuma dama anan garin yake kasuwancinsa ,tun daga wannan rana bamu sake sakasu à idonmu ba ,ni da mahaifiyarshi kullum cikin tashin hankali muke n'a rashinsu ,da mukaji shirun yai yawa ,sai muka taho garinnan domin bincikawa ,mu kaje gidan marayu inda yarinyar take ,sai suke cemana tabbas sunxo ,Amma kuma byan Sun gaisa ,sukai musu sallama suka tafi ,haka muka dawo gida cikin rashin samun labarinsu ,hka muka mika lamarin ga Allah ,kullum cikin Addu'ar Allah bayyanasu ,Amma kullum shiru kake ji ,basu ba labarinsu ,


Tom Rannan saiga wayannan bâyin Allahn ,ya nuna wayannan dattijan ,suka xo gurinmu tare da ma'aikaciyar gidan marayu ,suna neman yarinyarsu da danmu ya aura ,Amma sai n'a taresu da wannan mummunan labarin ,hankalinsu ya tashi sosai ,nima à lokacin tabon dake damuna ya famu ,muka hadu muka taya juna jimami ,sannan muka nemawa kanmu mafita ,kan fara bincike ko Allah xaisa mu dace ,

byan xuwanmu nan garin aka bamu labarinki ,yadda kike aikinki ,aka bamu yakinin in muka kawo kukanmu gunki ,xaki taimakemu ,domin kin iya aikinki sosai da sosai ,

dattijuwar ta amshe da cewa ,ki

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment