Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta bashi BOY din nata (sunan da take kiranshi dashi kenan tun yana yaro.........



Wannan kenan👌🏽










E.W.F
[4:29pm, 8/26/2017] YAR GATAN HUDAH: ♠♣🖤♣♠♣
*BABBAR CUTA*
♠♣🖤♣♠♣

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM♻

( *GORON SALLAH*)



Writing by ;♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*

*56-60*
08:00Am jigin Su maheer ya sauka A Nigeria ,garin Kano mai tarin albarka da ni'imah ,

cike da farin ciki ,Alhj mamuda ya tari yaron nasa ,suka hau mota suka nufi gidah,


dan neman fada xuwaira tasaka kanwar ta nana ta shiryawa maheer kayan tarba na ban mamaki ,

cike da farin ciki suka tari maheer ,nana sai kallanshi take ,Yadda take xatonshi ya huce nan,

gun deining suka kaishi ,nana ce ke saving inshi ,Su farha sun xagayeshi sai xuba mai surutu suke ,

xuwaira ce taja hannunsu ciki dan Su barshi yaci abincin ,

daddyn nasa ma tashi yai yashiga ciki ,Aka barshi daga shi sai nana ,sai sakar mishi murmushi take ,

shikwa gaba daya ,ya hade mata fuska ,dan baida wannan lokacin ,

cin abincinsa yake ,itakwa ta xuba mishi ido tana kallanshi ,kamar ta cinyeshi danye ,

dagowa yai suka hada Ido ,yaja tsaki ,malama Wai so kike sai na kware ne ,kin xuba Min ido ,dan Allah Ki dan bani guri mana,

Mikewa tai jiki a sanyaye ,ta koma falo ta xauna,

yana kammala cin abincin nashi ,ya tashi ya nufi sashin shi ,

komai na cikin gurin an canja mishi shi ,ya dawo sabo fil ,bed room yashiga ,ya haye luntsumeman gadonshi ,mai laushi ,dan ya rama baccin da bai samu yayi ba jiya ,

Aikwa bai wani jima da kwanciya ba ,bacci yai gaba dashi ,




Bashi ya farka ba sai misalin 12:pm ,toilet ya fada ,ya watso ruwa ,ya fito sai xuba kamshin sabulun Himalaya yake ,ya daukko man shima na Himalaya ya shafa ,ya hade cikin kananu kaya ,black in jus da whight t-shirt ta dan kama jikinshi ,sai ta kara fito da xatinsa ,

turaruka ya fesa ,ya kwashi wayoyinsa ya fito ,dakin dad inshi yaje ya daukko key din mota ya fito ,
domin yabishi company nasa ,dan yasan Acan xaya sameshi ,

har yashiga motar xai tayar ,wayarshi tai ringing ,
ganin kiran babban abokinshi ne ,Barr farouq ,yasa nan danan yai peaking ,
Hello br ya akai?

Wlh Alhmdllh ,

Fine , ina San mu hadu ,ya xa'ai ,

Yanxu dai ,da ofis in daddy xani ,
Ok tom mu hadu a can ,nima ganinan tahowa ,

yace ," ok tom sai ka karaso ,kana suka katse wayar ,yaja motarshi yai gaba ,


yana traffic light ta tsaidasu ,ita Kuma meimei ta huce ta daya barin ,byan ta baro ofis in meima ,sbda xasu shiga metting ,sai sannan ita kuma ta nufi gurin aikinsu ,

Binta yai da kallo ,har ta huce ,aranshi yana cewa tama fi kyau a fili ,

yana can tunani har aka basu hannu bai saniba ,sai da yaji na bayanshi suna mishi horn kana ya farga ,


dirrect gun da suke metting din ya nufa ,byan da an sanar masa ,
yana shiga ,mahaifin nashi ya washe hakora ,xuciyarshi ta sanyaya na ganin yaron nashi ,

ya shafa kanshi ,yarona ka tashi ,Ykk to ,
lfy kalau daddy ,sai kewarka da ta damen shiyasa na taho ,

yace tom nemi guri ka xauna ,kan mugama metting in ,

A'a daddy bani key in ofis inka ,xanyi bakone ,

Toh Toh gashi ,ya mika masa ,shikuma ya Amsa ,ya fice,

Meima da mami suka bishi da Ido ,har ya fice,


Bai jima da xama a ofis inba ,faruoq ya iso ,
Hannu ya mika masa suka gaisa ,kana ya nemi guri ya xauna ,

Wlh Barr wata Shari'ah ce ke neman Shan kanmu ,Anyi xama na biyar kenan ,wannan xaman da xa'ai shine na karshe ,kuma suna kokarin yin nasara ,sbda Akwai sa hannun manya A ciki ,

shiyasa kaga na kagu Kaxo 9gria ,na kuma nemeka dan kai kadai xaka iya yin nasara a kansu ,sbd na yarda dakai ,

Barr maheer yace "tom ina jinka Akan me ake Shari'ar ?"

Wani kungurmun dan fashine ,suka shiga gidan wani bawan Allah ,suka mai fashi sannan yaiwa yarinnyarshi fyade ,

Nandai ya fayyace masa dukkan abinda ke faruwa ,

Barr Maheer yai mishi alkawarin xai fara binkice sosai ,xai taimaka in sha Allah .....








E.W.F
[6:17pm, 8/26/2017] YAR GATAN HUDAH: ♠♣🖤♣♠♣
*BABBAR CUTA*
♠♣🖤♣♠♣

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM♻

( *GORON SALLAH*)



Writing by ;♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*


*51-55*

*AFTER 13YEARS*

_Abubuwa da dama sun faru ,harda haihuwar mami twince Ainah da Aimah ,da karamin kaninsu Ahseep,sai kuma candy da Su meimei sukai ,da kuma shakuwa dake shiga tsakanin meimei da meima ,dan tunda meima ta lura ,farin jini A jinin meimei yake babu wanda yaisa ya futar dashi sai wanda ya halitta mata shi ,dan duk inda xasu shiga kowa kaunar meimei yake ,ba ga maxa ba ,baga mata ba ,hakanne yasa meima tai yaki da *BABBAR CUTAR* dake damunta a xuci ,ta jaho yar uwarta jikinta ,ta kuma nemi yafiyar abubuwan da tayi mata a baya ,dan tasan kuruciya ce ta kawo hakan ,_

_ga mami kwa salon bai canja ba ,domin har yanxu tana jin xafi a kirjinta in ta kalli meimei ,shiyasa har yanxu banbancin da take nuna musu yana nan ,bai ragu ba ,saidai meima dake san nusar da mahaifiyar tata ,_

_bayan Su meimei sunyi candy aka samarwa meimah jami'ar dake Florida ,meima ta kafe Indai bada meimei xasu tafi ba ,itama ta fasa xuwa ,ganin hakanne yasa aka hada harda meimei aka tafi ,_
_Meima na Karantar harkar business ,kamar Yadda mahaifiyarta tayi ,yayin da meimei ke Karantar mass com ,burinta kenan tun tana yarinya_

_A yanxu dai dukkaninsu sun kammala karatunsu ,ko wacce ta kama Aikinta ,meima A company da mami ke Aiki Anan itama takeyi ,itace ta gaje kujerar da mami ta bari bayan an karawa mami matsayi_


_Muhseen ya kammala karatunshi ya dawo ,yaxama lecturer a jami'ar bayaro ,da jamiar Akcils ,shakuwarshi da meimei har yanxu tana nan ,yai matukar farin ciki da yaga meimei da meima sun hade kansu_

_maheer kwa yaxama barrister ,domin abinda yake karanta kenan ,rabanshi da 9gria tun xuwan dayai yana dan 18 year ,saidai mahaifinshi na yawan xuwa_

To masu karatu kunji takaitaccen abinda ya faru a cikin wayannan shekaru da suka gabata ,da fatan kuma xakuci gaba da binmu dan jin me xai faru nan gaba ,

Kananan marubutankune ,kuma yan autan marubuta ke muku fatan Alkairi
♻E.W.F







*******
Meimei ce ke taiwa meima mitar tai sauri ta kammala shirinta ,Su tafi ,
ba mota 1 xasu shiga ba ,kowa da tashi ,ba kuma gun Aikinsu 1 ba Amma ya xame musu ka'Ida saisun fita tare,


dan Allah meima Ki sauri ,kinga yau xamuje gurare da dama daukar rahotanni ,nasan kilama Su hudah suna can suna jirana ,

Meima tace "Ai ke kikaga xaki iya yin wannan Aikin mai xirga -xirga da wahalarwa "

Hmmmm kuma kar kiso kiji dadin Aikinnan da nakeji wlh sosai ,burina ne tun ina yarinya kuma Allah yacika mini shi"

Muhseen ne yace "kinga meimei taho mu tafi Ki rabu daita ,ta tsaya kyale kyalen da ko farcenki baxata Kamo a kyau ba "


Kanta ta dago daga daurin da take ,ta galla mishi hararar wasa ,kana tace "dadinta dai ,Nima ko Banyi kwalliya ba da kyauna ,kuma in kana da kyau ka kara da wanka ehe "ta durkusar da kanta taci gaba da daurinta ,

Jerowa sukai Su uku ,meimei da meima sunsha anko cikin material mai dan karan kyau , perpul colour ya Amshesu sosai fuskarsu sai Annuri take bayarwa ,

kowa motarshi ya nufa yashiga ,motocin sunsha wanki ,sai kyalli suke ,kana sukaja ,suka fice daga harabar gidan A jere.







*****
barrister maherr ,yana kwance kan luntsumemiyar kujerar dake hadadden falonshi ,ya kurawa TV Ido ,gaba daya nutsuwarshi yabata ita ,
ganin hakane yasa na kalli TV domin na gano muku abinda ya daukewa wannan shalelen saurayin hankali,


Meimei ce sanye da duguwar Riga red colour ,mai duwatsuna masu kyau ,kanta ba dan kwali ,sai mayafin rigar da ta yafa ,gashinta ya kwanta a gaban goshinta yai luf-luf ,
tana magana cikin siriyar muryarta mai dadin sauraro ,

_masu sauraro ,yau mun tashi ,da tashin hankali a garin namu na Kano ,sakamakon jirgi da yai hatsari ,bayan tasowarshi daga Lagos ,dukkanin mutanen dake cikin wannan jirgi Allah ya Amshi rayukansu ,saidai Allah al hakimu ,Allah mai iko Allah gagara misali ,Allah gatan kowa,wannan yarinya da kuke gani ,aka nuno photon wata yarinya ,itace koda kwarxane bata samu ba ,dan haka Ana neman yan uwan wannan yarinya ,in labari ya samu yan uwanta sa iya tuntubar wannan numb , 080........_
Tana yin maganarne cikin kwarewa Akan Aikinta ,da kuma salo da sarrafa harshe ,Abinda ke kara tafiyar da maheer Akanta ,barin kumatunta dayake lobawa ,wanda yakara mata sirrin kyau ,

Lumshe idonsa yai ,bayan yagama sauraranta ,yana jinta har cikin jinin jikinshi ,xakin muryarta tashiga yimasa amsa kuwa a kunne ,

Mikewa yai yanufi sashen momynsa ,tana xaune a kasa Akan kafet ,bayan ta gama sauraran meimei ,itama tana kaunar yarinyar har jinin jikinta ,kwanciya yai Akan cinyar mahaifiyar tasa ,tasaka hannunta tana shafa kansa kana tace ,"my boy me yafaru"

Momy ina san xuwa gun daddy ne

Murmushi mommy tayi ,tace "yaushe kake ganin xaka tafi ?"

gobe nakesan tafiya ,

Momy tace "Allah yakaimu goben ,mahaifinka yamun kara akanka sosai ,sbda ya lura bansan abinda xai nisanta ni dakai ,shima kuma gareshi hakanne ,Amma yakemun kawaici"

Ai mommy daddy mutumne mai karamci da kuma kara da kawaici ,shiyasa nake kaunarsa har bargon jikina.....









E.w.f
[7:25pm, 9/7/2017] YAR GATAN HUDAH: ♠♣🖤♣♠♣
*BABBAR CUTA*
♠♣🖤♣♠♣

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM♻

( *GORON SALLAH*)



Writing by ;♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*


*66-70*

yauma kaya iri daya meimei da meimah suka saka ,sunyi kyau sosai ,cikin Jan less mai adon baki ,suka sanya farin hijabi ,iya guiwarsu mai hannu ,
Hannun mai roba ,sunyi kyau Ainun ,suka fito a tare ,gun motar meimah suka nufa ,kasancewar yau meimei baxata gun Aiki ba ,xata bi meima ofis dinta ,ta dan rage mata Aiki ,

Meimei ce ke tukin a hankula,suna hirarsu ,har suka karasa ,ma'aikatar tasu ,

sunxo bakin kofar shiga meimei bata kula da wani turkeken kare a kwance ba ,gashi masifaffe ,jikinsa duk gashi ,ta taka mishi kafa ,yasaka ihu ,ya biyota yana haushi ,Aikwa kafa me naci ban baki ba ,ta kwasa a guje ,ta nufi ciki ,

gudu take tika ,ko waiwayen bayanta batai ,taga wata kofa a bude ,ta afka ciki ,ta kulle ,ta jingina bayanta jikin kofar ta lumshe idonta tana maida numfashi ,sai haki take ,

Maheer da ke xaune ,yana Aiki tukuru cikin computer,ya dago dan ganin wanda yashigo ofis in ,sai yai toxali daita ,

Kallanta yakeyi ,yana kallan Yadda take sauke ajiyar xuciya a hankula ,Mikewa yai yanufi gurin da take ,idonshi a kanta ,

Jin alamun tafiya datai ,yasata bude idonta ,idanuwansu suka gauraya ,cikin dabarbarcewa ,sbda irin kallan da yake jifanta dashi ,tace ,"I'm sorry "ta fara kokarin bude kofar ta fita ,

ya kasa ce mata komai ,sbda dadin muryarta da ta ratsa kunnanshi ,Aranshi yace "a tv Ana rage mata dadin murya,

Tana bude kofar ,A lokacin meimah ta iso ,me meimah xatai inba dariya ba ,tadinga kyalkyala mata dariya ,
futowar maheer ce ta tsaida ita daga dariyar da take ,
Ya tsaya yana kallansu ganin kayansu iri 1 ,cikin muryarshi mai dadin sauraro ya tambayesu abinda ke faruwa ,
Meimah ce ta sanar masa ,karene ya biyota ,xunburar baki meimei tai ,tace xakisan ni kikema dariya ,nama fasa tayaki aikin ,tai tafiyarta ,
Meima tace "yi hkri my sis karki tafi baxan kuma ba ,bata sailurareta ba ,taci gaba da tafiyarta ,
ita kuma ta tsaya gun maheer dake tambayarta ?

Anan kike Aiki ne ?
tace masa eh ,

Yace ,waccenfa kanwar kice,ko kuma yan biyune ku ?

tace mishi ,eh ,Amma ita ba anan take Aiki ba ,

fitowar mami daga ofis inta kenan ,taxo hucewa ,taga maheer da meimah ,a tsaye ,wani dadine ya ratsa xuciyarta ,ta fara Addu'ar Allah yasa soyayya suke ,

meimah tace ,Wai baka ganeni ba ,kaga mami na can ,lokacin da ina yarinya ,in mami taxo dani tare muke wuni ,

Yace "ikon Allah gashi kuma kema kin girma ,kina kawo kanki ,Ai saida kikamun bayani na ganeki ,Muje naga ofis din naki "

cikin nishadi meimah tace tom Muje ,suka jera suka nufi ofis din ,
suna shiga suka tadda meimei a ciki ,tana waya ,kalmar da ta fara shiga kunnansu ,itace
Hmmmm Allah sarki yayana ,yau banje Aiki ba ,ina gun aikin Su meimah ,


tsayawa sukai ,suna kallanta ,byan ta kammala wayar ta dago ,tana kallansu ,ta murgudawa meimah baki ,tace "to sa'idunawa ,meye kika tsatstareni da na mujiya ,

ba dole ba ,naji kina jiransa,naga
Kuma ba soyayya kika xo yiba ,Aiki kikaxo tayani ,

Murmushi meimei tai ,tace Banda abinki ,in yana kusa dani ,ai nafi saurin yimiki aikin ,

jin alamun bude kofa ,yasasu kallan bakin kofa ,sukaga maheer ne ya fice ,yana fita ,Muhseen ya shigo ,meimei tace Yauwwa dan halak ,gatanan ,ta Nuna meimah Wai baxaka xo mata ofis ba ,

harara ,Muhseen ya jefa ma meimah ,yace "kyalata yar bakin ciki ce ,meye amfanin xaman meimei a ofis inki ,byan ba Muhseen a ciki "

meimei tace "Nima dai haka na gaya mata ,murmushi meimah tai ,ta karasa kan kujerarta ta xauna ,dan yanxu dai batajin xata biye musu ,


Maheer yana barin ofis in ,mota ya nufa ,yai gida ,
Yana tuki yana tunani ,shidai yarinyar nan aduk sanda yaganta ,yana jin dadi a Xuciyarshi ,idanuwansa suna san kallanta kunnuwansa na muradin jin muryarta ,bai taba jin haka ga wata mace ba ,sai ita kadai ,tabbas ta fita xarra cikin mataye ,

Yana isa ya tadda Atakura ,sunan da ya rada mata kenan ,tana ta gyara masa daki ,
Tsawa maheer ya daka mata ,yahauta da fada ,Akanme xaki shigomun daki kihaumun gyara sai kace wata matata,na sakakine ,ni banasan shishshigi cikin lamurana ,in ina bukata ,ai xan saka amun ,
Kixo kibarmun daki ,duk randa na kuma ganin gotatciyar kafarki a dakina ,sai na karyata ,

ficewa tai sim -sim tabar dakin ,tajewa xuwaira harda yar kwallarta ,nanma din xuwaira fada tabita dashi ,kece baki iya karairaya da rangwada ba ,da su kashe ido ,da kinai masa wannan da tuni ya bada kai bori ya hau ,Yadda kike da kyau dinnan ,

dan haka ,Ki kara xage damtse ,wajen karkato da hankalinsa gareki Insha Allah sai mun nasara ,maheer mijin nanah ne ,

Murmushi nana tai ,sbda jin dadin lafaxin yayar tata ...









E.W.F
[9:43pm, 9/8/2017] YAR GATAN HUDAH: ♠♣🖤♣♠♣
*BABBAR CUTA*
♠♣🖤♣♠♣

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM♻

( *GORON SALLAH*)



Writing by ;♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*

*Muna neman Addu'arku ,biyu daga cikinmu basu da lafiya ,ummee xeey &sardy bash ,Allah ubangiji yabasu lafiya ,yasa kaffarane ,yabawa dukkanin al'ummar musulmai lafiya ,Ameen summa Ameen*

*71-75*
Maheer kwance ,bisa kan luntsumemiyar kujerarsa ,ya lumshe idonsa ,yana tunanin masoyiyarshi abar kaunarshi ,yau wajen kimanin sati biyu rabanshi daita kenan ,kullum sai yaje ofis in meima ,dan yaga taxo ,Amma sai yatarar da sabanin haka ,xuciya da ruhinshi suna muradin ganinta ,

yayin da meimah ke jin dadin xuwansa dan a tunaninta ,gurinsa yake xuwa ,dadi yabi ya mamaye xuciya da ruhinta ,a a tunaninta shima dafin da ya sareta ya sareshi ,hakama maminta ta sakankance maheer san diyarta yake ,Abbanshima kan yabar kasar ,yai tunanin haka ,dan ganin Yadda yaron nashi yake sintiri offis din meima ,yaji dadin hakan ,dan yana san yarinyar jininsu ya hadu ,idan har maheer na santa ,ba abinda xai hanashi daura musu aure ,


Wayarshi ce tai ringing ,yana can tunani bai samu kuxarin yin peaking ba ,har ta katse ,tana katsewa wani ya biyo baya ,cikin mutuwar jiki ya dauki wayar ,

Hello mom ,
Hello boy ,Ykk me ke damunka naji muryarka silently ,
Mom bkmi ,daga bacci na tashine ,
Oh my boy ,ka kulamun da kanka ,ya daddyn naka ?
bayanan mom yabar kasar ,shiyasa kika jini shiru ban dawo ba ,duka harkokinshi na nan ,ni yabarma ,
Ai ba komai boy ,kaci gaba da biyayya ga mahaifinka ,ka wahalta mishi kamar Yadda ya wahalta maka ,ka tashi ka tafi offis Tara har ta kusa me kake a gida ?
Mom yanxu xan fita ,
Tom yarona ,Allah baka sa'a a rayuwarka ,yayi maka albarka ,
Ameen mom ,ngd da addu'arki ,shiyasa nake sanki ako dayaushe ,Allah yabarmun ke ,
cikin jin dadi ,tace "Ameen "ta kashe wayar ,


cikin mintin da bai wuce 15 yagama kimtsawa cikin black court ,yayi matukar kyau ,ya fito a cikakken barrister inshi ,sai xuba kamshi yake mai sanyi ,

farar mota ya dauka mai sheki ,ya nufi companny nasu ,ofis din meima ya nufa ,dan ganin ko SANYIN IDANIYARSA taxo ,Amma kash yana shiga ya tadda meimah ita kadai ,tana xaune bisa kan kujerarta ,ta dukufa da Aiki cikin computer tukuru ,

dago idonta tai tana kallanshi ,yayin da sanyin turaranshi yabi kofofin hancinta ,lumshe idonta tai kana tace "barrister barka da isowa "
barkanki dai ya Aiki ?

tace "Alhamdlillah ,cikin jin dadin muryarsa ,

Meimei ce ta bude kofar ta shigo ,
faduwar gaban da ke xiyartarsu a duk sanda suka hadu ,ita ta samesu ,
cikin gwanancewa yake kallanta ,ba tare da sun Ankare ba ,
Meimah tace "sis lfya na ganki a rude haka ?

Ajiyar xuciya ta saki ,tace "kedai bari sis ,Karen rannan na gani ,Aikwa na kwasa da gudu ,ban tsayaba sai anan ,nidai muddun Akwai karennan anan xan daina xuwa ,ta karasa maganar cikin shagwaba ,
Maheer sakin Baki da ido yai yana kallanta ,xuciya da ruhinsa na bugawa da sauri cikin kaunarta ,

Murmushi yayi ,cikin muryarshi mai dadi ,yace "sorry meimei ,ba'ayi haka ba ,yaushe xamuso Ki daina xuwar mana nan ,bayan xuwanki albarka yake kawo mana ,kisha kuruminki baxaki kara ganin kare anan ba "
bai jira me xatace ba ,ya fice daga offis in ,

Meimei ta fada cikin wani yanayi ,sbda yadda yai amfani da muryarshi mai dadi ya kira sunanta ,

saiji tai meimah na meimei Ki karaso ciki Ki xauna mana ,

ba xama xanba sis ,Su fahad na waje suna jirana ,kumbotso xamu ,shine na biyo na gayamiki ,yau baxan dawo da wuri ba ,

Ok tom sis ,sai kun dawo ,Allah ya kiyaye ,yakaiku lfy ,

tace "Ameen meimah ta ,sai na dawo ,kana ta fice ,

Maheer na barin offis in ,oder yaje ya bada ,A fice da karennan ,kar ya kara ganinshi a kewayen nan ,ya dawo sukai karo xata fita ,

A tare suka sakarwa juna murmushin da basusan sunyi ba ,
har ta huce ,ya kirata meimei ,juyowa tai ,tana kallanshi ,yace "har xaki tafi daga xuwa ?

ta bashi Amsa da xamuje unguwane ,Ana jirana a waje ,

Ok ,tom ,Sai kun dawo ,ina sa ranki gobe ,bai jira me xatace ba ,yai gaba Abinshi ,


A mota suna tafiya ,meimei xuciya da ruhinta sun tafi ,tunanin maheer ,tana jin abubuwa da dama akanshi ,wanda bata jinsu ga wasu maxajen ,ko Muhseen bata jin haka game dashi ,shida take ganin soyayyarta cikin idaniyansa ,furta mata ne kawai bai ba sai alamu da yake Nuna mata ,

tuni ta fara yaki da xuciyarta ,dan karta cusa mata abinda xaixo yafi karfinta ,
dan taga soyayyar maheer a xuciyar meimah ,kuma tasha gaya mata ,in.hakane kuwa ,indai xuciyarta ta fada kaunar maheer ,bataiwa kanta da meima adalci ba ,
A cikin wannan tunani meimei ta kasance a tafiyarsu,



sai yamma Lilis meimei ta dawo gida a gajiye ,bandaki ta fada ,tai wanka da ruwa mai xafi ,dan ware gajiya ,tana fitowa ,bayan ta goge jikinta ta ,ta daukko sleeping dress inta ta saka ,bata bukatar mai sbda yanayin xafin garin ,ta fada gado ,ta janyo wayarta tahau danne -danne ,bcs tana fashin sallah ,


Sai lokacin bacci meimah ta shigo dakin ,tana can suna hira da mamin ta,kan gadon ta fada ,tace yar uwa ,yau nayi miss inki da yawa da yawa ,murmushi meimei tai ,tace Nima haka wlh yar uwa me ya faru ne ?naganki cikin farin ciki ,

Meima tace "hmmm yar uwa yanxu xan sanar dake ,Ki tayani farin ciki ,maheer na sona ,kamar Yadda na mato a kaunarshi "

Meimei jitai gabanta ya fadi ,tayi wani luuu kamar ta suma ,saida meima tasa hannu tana jijjigata ,meimei lafiya?cikin basarwa da dauriya,meimei tace farin cikine yamin yawa ,ba son maso wani yar uwata take ba
meimah tace,kedai bari ,yanxu muka gama hirar da mami ,Ashe duk suna lura damu ,harda mahaifinshi ,Ammafa har yanxu bai sanarmin ba ,saidai Alamu ,

Murmushi meimei tai tace "tom Allah yasa xaton ku yaxama gaskiya ,

meimah tace "Ameen ,ta tashi ta fada toilet ,yayin da meimei tai juyi cikin KUNAR RAI........











E.W.F
[2:15pm, 9/9/2017] YAR GATAN HUDAH: ♠♣🖤♣♠♣
*BABBAR CUTA*
♠♣🖤♣♠♣

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM♻

( *GORON SALLAH*)



Writing by ;♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*

*76-80*
A wannan dare meimei tayi kwanan KUNAR XUCI ,

da safe tana kwance ,tana kallan meimah sai shirin offis take ,sai maganar maheer ta fado mata ,da yace ina sa ranki gobe ,ko me xai mata ?sai kawai taji tana san xuwa ,kasancewar yau su suna Hutu ,

meimah xaki jirani na shirya mu tafi ?kokwa na taho ,bansan xaman gida ,

meimah tace "tashi Ki shirya mu tafi ,kya tayani hira ,dan ni yau Banda Aiki sosai ,

Mikewa meimah tai tace tom ,ta fada toilet ,

cikin 20minut sun kammala shirunsu ,cikin black after mai kyawun gaske ,suka yafa mayafinta black mai stone ,

suna falo ,suna xuba salfei ,mami ta fito ta taddasu,cikin shirinta na offis itama ,tsugunawa meimei tai tana gaida mami ,yayin da mami ta bude ma meimah hannu ta tafi da gudu ta fada jikinta ,

Mamina an tashi lfy?
lfya lau daughter na , taja hannunta suka fice ,

Meimei na tsaye na goge kwalla a idonta da ta tarar mata ,ta rasa me yasa mami take mata haka tun tana yarinya ,Anya kwa mami ce ta haifeta ,har yanxu tana san jin amsarnan ,Amma ta gaxa gun wanda xata samu Amsar nan ,meimah taki ta bata fuskar hakan ,in tai mata xancen sai tadinga kauce mata ,

Abubuwan da mami ke mata ,duk uwa baxa taiwa Yarta ba ,
tana cikin wannan tunanin Muhseen ya fito ya tadda ita tanai ,
Ya Dade a tsaye yana kallanta bata saniba ,hawayen da yaga na xirara a idonta ne ya tada hankalinshi ,handkchif inshi yasa yana share mata hawayen ,

dagowa tai tana kallanshi ,ya girgixa mata kai ,me yasa ki xubda hawaye cikin kyawawan idanunki ,kinsan na tsani ganin hawayenki ,
byan kin Riga kin Saba da halin mami ,Ki daina damuwa ,Allah xai kawo miki mafita ,Insha Allah,

Murmushi ta dan kago ,tace yayana ko wata xuciya na son kulawar mahaifiyarta ,ni abinda ke damuna ,Anya kwa mami mahaifiyata ce ?

Ki daina fadin haka kanwata ,mami mahaifiyar kice mana ,Addu'a xamu cigaba da yimata ,Allah ya daidaita ku ,yasa ta gane gaskiya ,

text ne yashigo wayar meimei ,ganin meimah ce yasata budewa da sauri ta karanta ,

_yar uwa nayi gaba kya tawo ,mami ce tasani a gaba ,kiyi hakuri ,ina jiranki pls kar Ki Ki xuwa_
*meimah*


murmushi kawai tayi ,byan ta gama karantawa ,
Muhseen yace "kanwata murmushi yana miki kyau wlh ,gashi yau kinyi kyau ,kamar kar na daina kallanki"

murmushi tai tace "yayana kenan ,ngd ,Muje karmu makara "

yace "tom kanwata "kana suka jera suka fita ,


Byan tai perking ,ta Dade cikin motar kan ta fito ,tana kukan da yaciyota ,saida tai mai isarta ,kana ta gyara fuskarta ,ta saka glass ta fito ,

fitowarta a idon maheer dake saman bene ,cikin ratsatstsan offis in da yaxama mallakinshi ,yana tsaye jikin window yaga fitowarta ,

sanyayyar ajiyar xuciya ya saki ,kana ya rufe window in ,ya koma kan kujera ya xauna ,ya lumshe idonsa ,


da sallama ta shiga offis din ,ta tadda meima a xaune idonta a rufe ,byan ta amsa sallamar Tata ,meimei tace yar uwa lfy?
lfy qalau yar uwa ,kawaidai yau banga maheer ba ,
Rufe bakinta kenan ,ya turo kofa ya shigo ,saida aka danyi kallon kallo ,kana dukkaninsu suka ajiye ajiyayyar xuciya ,

Meimah tace "Barr barka da isowa "

yace "barkanki dai meimah ,An tashi lfya ?

lfya qalau ,ta bashi Amsa ,

Yamaida kallanshi ga meimei ,yace meimei ba gaisuwa ?

sai da ta fara lumshe idonta ,cikin sanyin murya tace "da

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment