Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba gaba daya baya cikin nutsuwarshi ,Khadijah sai magana take masa ,tana tambayarshi ,Amma ya kasa magana illah harisah da bakinshi yake furtawa ,bai aune ba stiaring din motar ya kubce masa ,motar tasu ta gangara tadinga juyi dasu ,daga bisani ta watsar dasu akan titi ,ita kuma ta kama da wuta ,

Yayin da mimi ke gefe tana ta tsala kuka ,abin al'ajabi ko kwarxane Mimi bataiba ,

daga Hashim har Khadijahn kwa basusan inda kansu yake ba ,


dai dai karasowar harisah ,ganin abinda yafaru ya karawa kukanta kaimi,


Kan kuce kwabo an kwashe Su Hashim an nufi hospital dasu ,nan danan likitoci suka dungumu a kansu ,


Bincike ya nuna musu Khadijah ta dade da cikawa ,Hashim ne dai ke numfashi kadan labbanshi na furta harisah ,ganin haka likitoci suka kira masa harisah ,


Ki yafeni alkawarin da na daukar miki ban cika ba ,Abinda Hashim yaiya furtawa kenan shima yacika da kalmar shahada ,



Kifewa harisah tai akanshi tana kuka ,na yafema shine abinda take fada tana rusar kuka,



Mimi sai kuka take tsalawa tana fadar mama cikin gwarancinta ,Umman Su harisah ce da basu jima da xuwa ba ta dauketa tana jijjigata har tasamu tai bacci,




Ankai gawarsu gidansu na gaskiya ,An musu sitira,



Harisah sai kuka take sheka kamar ranta xai fita ,

Inda Allah ya taimaka Mimi koda da ran mahaifiyarta xa'a iya yayeta ,sbda ta shekara da yan watanni ,kuma dama khadija na hada Mata da abincin gwangwani............






E.W.F
[9:45pm, 8/6/2017] YAR GATAN HUDAH: ♠♣🖤♣♠♣
*BABBAR CUTA*
♠♣🖤♣♠♣

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM♻

( *GORON SALLAH*)



Writing by ;♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*

*61-65*
meima tunda suka koma gida ,taishi Su meimei da xancen maheer ,

Meimei tace "Wai ke kin damu dashi ,kin ishemu da xancensa ,shi baima san da xamanki a garin Kano ba ,"

wa yagaya miki ,shikwa yasanni ,saidai ya mantani ,dan sanda Muna yara ,in mami taje dani gun Aiki tare muke huni dashi ,

tabe baki mimi tai ,tace kin birge Toh,

meima tace "wlh yarinya dan baki ganshi bane ,ya hadu iya haduwa ,Yadda kikasan black America ,fatarshi ta ratsu da hutu ,

Meimei tace Hmmmm ke shi ya dameki ,ni maxa Sam basa gabana ,Ki barni da Aikin da yatararmun ,

Meimah tace "kyace haka man ,yar rainin hankali ,Amma Ai Muhseen yana gabanki ko?"

Muhseen Ai ba soyayya muke ba ,kawai shakuwace ,


To Ai shakuwama na kawo soyayya ,ko mai kaucen da xakimin na Dade da ganoku soyayya kuke ,

murmushi meimei tai ,tace sai kuma kiyi ,baki da Aikin yine shiyasa kika xo kina takuran ,

bari na barmiki dakin ,na tafi dakin ya Muhseen ,nafi samun nutsuwa acan ,takai karshen xancen hade da nufar bakin kofa ,

Meimah tace ,kedai fadi gaskiya ,kin tafi xance dai ,dan ba wani Aiki da xaki acan ,saidai soyayya ,

Meimei tace "naji dai ,kedai kiji da dafin da yasareki a xuciya ,ta fita tana mata dariya ,

lumshe idonta meimah tai ,tabbas maheer yasa mata dafi a xuciya,






****
Maheer yagama bincikensa sosai ,ya hada evidence inshi guri guda, kawai ranar da xa'a shiga courtu yake jira,


23\8 /2017
Aka shiga court ,an fafata sosai ,maheer yai nasara ,bisa evidenc in da ya gabatar gaban courtu,Alkali ya yanke hukunci ,courtu ta tashi ,

bakin courtu ,cike take da yan jaridu ,kowa so yake ya dauka ,Su meimei ma sunxo daukar rahoto ,Amma ita tana gefe jikin motarta ,fahad ne (abokin Aikinta ) yashiga turmutsutsun mutanen ,domin daukko musu rahoto ,

Barr Maheer da barr faruoq suna tsaye ,sun bada baya ,mahaifin yarinyar da mahaifiyarta suna tamusu godiya ,sai aka kira maheer a waya ,ya matsa gefe yana amsawa ,A daidai lokacin yan sandan suka fito da kungurmun mai laifin,bindigar dake kunxugun shi ya fito daita ,yana saitin maheer ,

Kamar a idon meimei ,ta nufi gurin da gudu ,ta hankada maheer ya fadi kasa ,itama tabi bayanshi ,bullet din ya hucesu ,sai a kafadar Barr da ya kareshi ,

yayin da yan sanda suka kwace bindigar ,suka tisa keyarshi gaba ,cike da bakin cikin burinshi bai cika ba ,dan yaso ya Aika barr maheer lahira ,Allah bai nufa ba kuma ,

tashi meimei tai ,tana gyara mayafin rigarta da ya cire ,maheer sai sannu yake mata ,badai kiji ciwo ba ko ?

Kai ta daga masa ,dai dai lokacin fahad yaxo gurinta ,yace "ina kika shigene ,tun daxu ina ta nemanki ,kuma naga motarki ,batai magana ba ,kawai ta shige gaba ,yabi bayanta ,

Maheer yace "kinga"
ta juyo tana kallanshi ,yace "nagode fah "
Murmushi kawai tai ta juya suka tafi ,

Murmushi shima yayi , yaso yaji muryarta ,Amma takiyin magana, ya nufi gun motarshi ,byan sunyi sallama da barr faruoq ,yana tuki yana murmushi ,har ya karasa gida ,

wanka ya fara yi,ya kuma hadewa cikin sabon dresing ,ya fito falonshi sai xuba kanshi yake ,fuskarshi cike da annuri,

Nana ya tarar a xaune ,da tiren abinci a gabanta ,

Mur yasha ,yadauki mukullin motarsa da ke kan kujera xai fita ,
tace masa ,abinci fah?
Yace Ki ajiye kije ,sai na dawo xanci ,bai jira me xatace ba ,yafice daga dakin .....





E.W.F
[1:00pm, 8/15/2017] YAR GATAN HUDAH: ♠♣🖤♣♠♣
*BABBAR CUTA*
♠♣🖤♣♠♣

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM♻

( *GORON SALLAH*)



Writing by ;♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*


~muna masu bawa ma'abota wanga littafi hakuri ,bisa jinmu na kwanaki masu yawa da kikai ,wanda mu kanmu ba haka muka soba ,saidai ba Yadda xamui ,saidai~ ~muna masu muku albishir da cewa ,yanxu xaku fara samunsa~
~aka akai ,har xuwa karshensa ,short novel ne 👌🏽,mai matukar amfani~


*31-35*
Aduk sanda harisah ta bude Ido ta kalli MIMI sai taji wani Kululun bakin ciki na xiyartar mata xuciya ,idonta na hango mata sanda taga Hashim dinta da wata mace ,hadda ya rinya kamar turawa,
Hakan na damunta sosai
Har ta kudur tarwa ranta cewar baxa ta rike MIMI ba saidai takaita gidan marayu ,domin Santa ta kalleta takaici ne ke damunta,



Bayan an share makokin Hashim da Khadija ,harisah ke xuwa ta samu mahaifiyarta da xancen kai Mimi gidan marayu ,Momy tace

"Ina sam ,mai rabata da mimi sai mutuwa ,dan Yadda Allah ya Dora mata kaunar mimi ji take kamar diyarta tsoka daya a miya "

Takaici yaishi harisah ta rasa bakin magana ,sai gata ta fito da kayanta ,ta riko hannun mima ,Wai gidan ta xata koma,

Momy tace
"Kome xaki kiyi ,nidai baki isa Ki hanani Aikin alkairi ba ,in banda hauka irin naki ,ina aka taba kishi bayan rai ,Su wanda kikeyi dansu ma sun manta sunyi rayuwa a duniyar ,tasu ta kare yanxu tamu ce abin dube ,in xakki ajjiye kishhi Ki rungumi marainiyar Allah ta SILAR ta kila takaiki Aljannah"


Kishi ya rufewa harisah Ido,xunburar baki kawai tai ,tai gaba ,

Yayin da momy ta bita da neman shiriiya,......




*****
Malam da inna sunji shiru ,suna ta xuba idon ganin Hashim da Khadijah ,Amma sunji shiru ,Abin ya damu xukatansu Ainun,
Amma ya xasuyi ,haka suka xubawa sarautar Allah ido,




Mimi sosai take samun kulawa gurin Momy da dad,suna matukar kaunarta ,Allah ya xubawa mimi masoya birni da kauye ,
A jininta yake,.......







*****


*After 8yrs only*

Harisah tayi aure ,tare da Angonta Umar ,Umar matarshi mutuwa tayi ,yana da da daya mai suna muhseen ,ba wani yaro ne karami ba ,sbda ya mallakki hankalinsa,....



Mimi da mima suna prmry 2,class insu daya ,sam Basa jituwa ,harisah ta dora mima Akan nuna kiyayya ga mimi ,

dadin dadawa ma ,duk malaman da ke koyar dasu ,da kuma yan ajin nasu ,suna matukar kaunar mimi suna ji daita ,duk da ba wani kokari ne daita sosai ba ,tana dai fahimtar karatu sosai ,dan mima tafi ta kokari,

Junior dinsu da senior dinsu ma suna kaunar mimi ,Tom hakan ne ke karawa mima jin haushin yar uwar tata



****

Mimi ce sanye da uniform na schl jikinta ,Sun matukar amsar fatar ta ,so beautiful baby ,saima da tanawa hamxa magana ,dake tsaye yana kade mota ,

Hannuwanta duka biyu a kugu ,dan Allah baba hamxa kai sauri kaga exam muke ga 8 ta kusa yi ,hade da kallan agogon dake tsintsiyar hannunta. ,kamar wata babba ,

Hakan ba karamin kyau yaimata ba ,

da sarsarfa hamxa ya bude motar ,xo Ki shiga yar baba ,yau dole nai gudu dan kar ki makara ,

Murmmushi tai har saida dimpe inta dake bari daya ya lotsa kana tashiga motar ,Aikwa hamxa yajata da gudun tsiya,


sanda suka isa , bakin get din schl din A lokacin ake sauke mimah ,harara mimah ta gallawa mimi ,

Inda sabo mimi ta saba da hararar ,A tare suka shiga class tunda dama ajinsu daya ,

Tuni class ya Rüde ,kowa fadi yake mimi ga guri taho Ki xauna ,yayin da mimah tai sororo ,takaici ya isheta,

Murmushi mimi tai siraran hakoranta suka bayyana ,kana taje ta sami guri ta xauna ,

Koda aka tashesu ,Sun taho suna tafiya ko wacce da kawayenta ,saiga xainab ,(A junior take ,tana kaunar mimi kullum da abinda xataxo ta kawomata ,)

Mimi na hangota ta tafi da gudu ta dafeta tana dariya ,xainab ta dagata sama ta dire ,tace mimina yau da safe ban ganki ba ,ina ta sauri kar naje an tasheku ,

Hope kina lpya ,ba wanda ya tabamin ke ko ?

Cikin muryarta ta yara mai dadi ta furta ,lpy qalau aunty na ,babu wanda ya taba miki ni ,

tace "yauwa mimina ,ungo "ta Mika mata Leda cike da chaculate lala2,Ki gaidamun da Momy ,da malami a class inmu bari na koma ,

tace "Tom Aunty na gode ,ta daga mata hannu itama tana daga mata ,


tana fitowa bakin get ,mima na tsaye ,Itama har lokacin ba'axo daukanta ba ,

Mima tana ganinta da ledar chaculate a hannu taje ta fisge,mimi ta fadi a gurin tana birgima tana ihu ,mima ta dauki guda Uku ta cilla mata ledar ,tai tafiyarta ,

dai2 lokacin baba hamxa yaxo daukar mimi ,yaganta tana ta kuka tai face2 da hawaye ,Rarrashinta yashiga yi ,dakyar ya samu tai shiru ta tashi suka tafi............














E..w.f
[10pm, 8/15/2017] YAR GATAN HUDAH: ♠♣🖤♣♠♣
*BABBAR CUTA*
♠♣🖤♣♠♣

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM♻

( *GORON SALLAH*)



Writing by ;♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*




*36-40*

yana perking din motar ta fita da gudu ,ta Dora kukanta daga inda ta tsaya ,

tana shiga dakin ,bata kula da Yadda momyn Tata take ba ,ta fada kanta tana kuka ,

dagota Momy tai ,ta tashi daga kwancen da take ,kana tace "mimi ke dawa ?"

cikin kuka mimi tace "ba mima bace Aunty xainab ta bani chaculat ta kwace ta diba"

Momy cikin dauriya tace "yi shiru Ki rabu daita jeki gun hinduwa tai miki wanka , kici abinci,sai kixo Ki anshi wata chaculate in ,"

tsayawa tai da kukan ,kana ta Mike ta fita daga dakin ,

Momy ta rike kanta dake sara mata sbda axabar ciwo ,lokaci daya kuma ciwon ya saukar mata ,bin mimi tai da Ido bayan ta fita ,tausayin yarinyar ya baibaye Xuciyarta ,tana tausayawa rayuwarta ,

tana nan xaune tana ta sake2 har mimi ta dawo ,tace "wlh Allah Momy naci abinci ,kibani chaculate in "

duk da halin da Momy ke ciki saida ta murmusa ,dan tasan bata ci abincinba ,dan kar ta hanata chachulate in shine har da rantsuwa ,

Inda chaculate din take ta gaya mata ,ta tafi da gudu ta daukko ,kana ta dawo ta xauna kusa da momyn tana barewa ,saida ta fara shan chachulate din kana ta lura da halin da Momyn ke ciki ,

Cikin damuwa tace "momyna baki da lafiya ?"

Eh kaina kemun ciwo ,

sannu momyna Kinji ,duk San shan chachulat din da mimi take ,kasa sha tai ,ta ajiyeta a gefe ,taxubawa Momyn nata ido duk bayan sakan daya xatace "sannu Momyna ,


Tun Momy na karfin hali ,har ciwon yaso yaci karfinta ,mimi ta sakata gaba sai kuka take ,kukan nata kuma na dagawa Momyn hankali ,dakyar tace mata taje ta kira mata baba hamxa ,ta fita kiransa ,saiga harisah taxo gidan ,

A hargitse ta sakawa mahaifiyar tata hijabi ta kamota suka fito ,ko takan baba hamxa bata biba ta sakata a mota ,kana ta xaga tashiga taja motar ta figi motar da gudu,

A gurin mimi ta tsuguna tana ta kukah,



basu karasa Asibitin ba ,Momy tadinga ruwa2 ,Tsai da motar harisah tayi ,ta fito ta xaga Barin da take ,ta tallafo Kanta ta bata ruwan rabi ya tafi rabi kuma ya jika mata gaban hijabinta,


Rike hannunta Momy tai ,tace mata " ga mimi nan Amana ce a gurinki ,Ki kula daita ,marainiya ce Ki tausaya ko kya rabauta ,manxan Allah yace
"duk wanda yajikan maraya ,kafada da kafada xasu shiga gidan aljanna"

Allah ya albarkaci rayuwarku ,

Karshen maganarta kenan ,tai kalmar shahada ta cika ,

Rungumeta harisah tai ,ta saki kuka iya karfinta ,abin tausayi ,

saida taci kukanta sosai ,kana tadau Waya ta kira dad ta gaya mishi har gurin da suke ,dan A halin da take ciki baxata iya driving ba ,






Allahu Akbar mutane da yawa sunji mutuwar baiwar Allah nan ,dama addu'arta kullum ,Allah yadau ranta ba tare da ya Dora mata jinya mai tsahoba wacce xata wahalar da mutane ,sai gashi kuma Allah ya Amshi addu'arta ,Allah ya rahamsheta ,,Ameen,


An mata wanka akai mata sitira ,kana Akai mata sallah ,wanda dubban jama'a sukai ,kana suka tafi rakata gidanta na gaskiya ,



Mimi bayan tafiyarsu Asibiti ,bayan ta gama shan kukanta ,ta tafi daki ta kwanta ,sai bacci ya dauketa ,sai yanxu ta farka ,

Mikewa tai ta fito ,taga gidan a cike,
Can ta hango harisah a xaune tana ta xubar hawaye ,
Karasawa gabanta tai tace "Mami ina momy?" banxa harisah tai mata ,ganin haka mimi ta fashe da kuka ,

Tsawa harisah ta daka mata ,bani guri ,da kukanki xanji ko da rashin mahaifiyata danai,

Juyawa harisah tai jikin ta na makyarkyta tabar dakin ,dan ta tsorata sosai ,tunda aka haifeta ba'a taba mata tsawa ba ,,,

Guri ta samu ta takure tana risgar kuka ,saiga mima nan taxo kanta ta tsaya ,taja tsaki ,ke sai wani kuka kike sai kace kakar kice ta mutu,Ai mami tace ba kakarki bace kuma ba Momynki bace,



Karawa kukanta kaimi tayi ,jin mima tace momynta mutuwa tayi ,duk da a shekarunsu bawai sanin me ake nufi da mutuwar ba ,

Kuka take sosai hadda shashsheka ,daga bisani bacci ya dauketa ,hinduwa ce ta kula daita ,taxo ta dauketa ,ta nufi daki ta kwantar daita ,tana kwantar daita ta bude ido ,tace aunty hinduwa Wai da gaske Momy ce ta mutu?"


Eh mimi na ,itace ta mutu ,ta share kwallar da ta tarar mata a ido ,

Tom sai yaushe xata dawo?

Ai baxata dawo ba mimi ,tariga ta tafi kenan ,duk wanda ya mutu baya dawowa


Xabura mimi tai ,ta kuma fashewa da kuka ,hinduwa ta rungumeta tana rarrashinta ,dago da kanta tai ,ta share hawayen idonta tace "wai aunty hinduwa Momy ba momyna bace ?"

Wa yagaya miki?

Inji mima ,

Karya take miki ,dan kawai ta sakaki kukane ,share hawayenki Ki manta da xancenta ,

Lallashinta tashiga yi ,har ta samu ta koma baccin ,




*******
Bayan an share bakwan Momy ,daddy yadauki Amanar mimi yabawa harisah ,yai mata nasiha sosai ,hade da kawo mata faidoji na rikon maraya .......











E.w.f
[2:54pm, 8/20/2017] YAR GATAN HUDAH: ♠♣🖤♣♠♣
*BABBAR CUTA*
♠♣🖤♣♠♣

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM♻

( *GORON SALLAH*)



Writing by ;♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*


*41-45*

ba laifi nasihar mahaifinta ta dan doketa ,jikinta yai sanyi ,

haka mimi take rayuwa a gidan halisah ,babu tsangwama bare kyara ,saidai dan banbancin da dole dama sai ta hadu dashi ,dan ko rikicine ya hada mimi da mima byan mima take bi ,koda mimi ce da gaskiya,


***
Kamar kullum mero mai aikin harisah ,ta gama kimtsa mimi da mima cikin uniform insu na makaranta ,

Ta daukko flask insu ta ajiye musu,xaraf sai mima ta dauke na mimi ,sbda neman tsokana ,Aikwa mimi tace sai ta bata flask inta ,ita Kuma ta hanata ,

Aikwa mimi ta bare baki tahau kuka ,mero tadinga lallaba Mima ta bata flask inta ,,Amm ta hana ,Ana cikin haka saiga harisah (Mami)ta fito ,tsawa ta dakawa mimi da tasa ta dinke bakinta ,ta makale a bayan mero tana makyarkyata ,

Mami ta tambayi mero abinda ke faruwa ,nan ta xayyane mata ,tsaki Mami tayi tsaki ,To shine abin kuka xaki bare baki uwa baure kina disturb in mutane ,


dauki kema nata Ku shige Ku tafi ,mimi Kin daukar flask in tai ,tai ficewarta ,Mami sai Ca tai "Au ke xuciya ko baxaki dauka ba ,Tom yunwar ta kasheki ,gadon tsiya "

Muhseen dake tsaye ,duk yana ganin abinda ya faru ,sai yaxo yadauki flask in yabi bayansu ,


Hannunta ya kamo yajata gefe ,,yana goge mata hawaye ,rada naga yaimata a kunne ,ta saki kyakkyawan murmushi ,ya Mika mata flask in ta Ansa ,ta juya tana daga mishi hannu shima yana daga mata hannu,

Har saida yaga. fitarsu daga get din gidan ,kna ya juya yashiga ciki ,


Harara Mami ta galla mishi ,gami da jifanshi da kalmar munafiki ,ko a jikinshi yai shigewarsa daki ,



**

da daddare suna xaune a falo ,muhseen nawa mimi lesson,saiga mima da gudunta ,

yarinya kinga Abba ya siyomin yar tsana,mimi ta dago idonta tana kallon yar tsanar ,

Wata katuwar yar tsanace da kadan miman ta fita tsawo ,

Rangwadar da kanta mimi tai ,tace Kin caba ,tamai da hankalinta ga littafinta ,

ba karamin bürge muhseen taiba ,tausayinta ,ya darsu a xuciyarshi ,tabbas mahaifinshi yana nuna banbanci tsakanin mimi da mima ,kuma duk Mami ce ta Bada kofar hakan ,

Ya dago yana kallan mima dake ta tsokanar mimi wooo wullu😛ba'a Santa ,ba'a siyo mata ba ,Anfi sona😜,


Tsawa muhseen ya daka mata ,da gudu tabar falon tana kuka ,


Janyo mimi jikinshi yai yana share mata kwallar idonta da ta taru ,yace "karki bata hawayenki a banxa ,gobe in Allah yakaimu kema xan siyo miki ,Kinji "

daga kai tayi ,yace yauwa mimina saki ranki muci gaba da karatunmu ,

Mami ce ta katsesu da cewar ,kai muhseen Kaxo inji Abbanka ,tana fadar haka tai juyawarta ,

sakin mimi yai ya mike ,ya harhada mata littattafan ,ya Mika mata ,maxa jeki baba mero tai miki shirin bacci ,saida safe ko ,

daga mishi kai tayi ,ta Amshi jakar ta tafi ,shima ya mike domin Amsa kiran Abbanshi ,



da sallama yashiga falon,yatadda mima kan cinyar abban sai xuba shagwaba take ,


yace "Abba Barka da dare "

yace "yauwa ,barkanka dai muhseen ,me kuma ya hadaka da kanwarka ,taxo ta kawomun kararka ?"


Mami tace "mekwa ya hadasu ,ya tsaneta ne kawai ,yafi kaunar wancen iblishiyar ,duk wata kulawa ita yake bawa ,dan tsabar munafunci ma kullum da daddare ita kadai yakema lesson"


Muhseen yace " Abba wlh ba haka bane ,dukkaninsu ina kaunarsu ,kuma a matsayin kannena na daukesu ,Abinda yasa nafi nuna kulawata ga mimi ,sbda na lura bata samun kulawa a gurinku ,kunfi nuna kulawa ga mima ,kuma kullum da daddare tana gurinku ,har sai tayi bacci ,ni kuma ganin hakan yasa nake Jan Mimi nake mata lesson ,har sai ta soma jin bacci "


shi kanshi Abban yasan abinnda Muhseen ya fada gaskiyane ,,Amma ya xxaiyi abinda matarshi ke so ,shi xaiso ,dan haka sai yahaushi da fada ,

Wannan banxan dalilin naka ka rike xaka dinga musgunawa mima ,kafi mu sanin dai dai ne ?To wlh ahir dinka duk randa ka kuskura ka kara mata tsawa saiga ka bacin raina ,ina ruwanka da shiga shirginsu ,dan haka ka fita daga lamuransu ,takaddunka ma su fito nan da sati mai xuwa xaka tafi "


Yace "Tom Abba Insh Allah hakan baxai kuma faruwa ba ,Allah yakaimu ranar ,Allah kuma ya kara girma ,kana ya mike yai musu saida safe ,ya fice daga dakin xuciyarshi a matukar bace ,






****
A yau aka bawa Su mimi hutun xango na uku , wanda A Daren jiya Muhseen ya tafi misrah domin cigaban karatunshi,yana Karantar Hadith,

An babbasu result insu a hannunsu ,mima ce tai First Position ,mimi tai na 3 ,dukkaninsu sai murna suke ,Sun dokantu da Axo daukansu ,suje Su nuna a gida ,,


Aikwa sai gashi Anxo daukansu ,da gudu suka tafi suka shige motar ,

Suna isa gidan mima ta fita da gudu ,tana shiga ta tadda Mami a falo,ganin diyarta da gudu ,yasanya ta tasowa ta tareta da gudu ,ta dauketa tana juyi, daita suna kyalkyala dariya ,kana ta direta ,ta Anshi result in nata tana dubawa ,Ai tana gani ta bata Kiss a goshi Gami da cewa "dole nabawa diyata mai kwaxo gift"

Mimi da ke tsaye tana kallansu ,ko Su kalli inda take ,ta share hawayen idonta ,ta rungume result in nata a kirji tana hawayen tunowa da Muhseen da tunni shi xai tareta ya Bude ya gani ,


ganin Mami taja diyarta sunyi ciki ,yasa Itama tashiga ciki gurin baba mer tana hawaye..........








E.W.F
[12:02am, 8/24/2017] YAR GATAN HUDAH: ♠♣🖤♣♠♣
*BABBAR CUTA*
♠♣🖤♣♠♣

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM♻

( *GORON SALLAH*)



Writing by ;♻ *EXCLUSIVE WRTERS FORUM*


*46-50*
_sosai mimi tayi Kewar Muhseen ,yaxamana kullum cikin kadaici take ,babu mai share mata hawaye ,babu maijin damuwarta ,babu mai lallashinta ,babu wanda yadamu da damuwarta ,haka Allah ya tsara mata rayuwarta_,



_mami ta shirya meimah cikin pink in t-shirt hade da blue in jeans ,tai mata two babeis da pink in riborm,tasanya mata pink in combos mai kyau ,_

_Meimei na xaune a falo tana kallo ,dan shine mahaifiyarta, shine Mahaifinta,shine kuma abokinta ,dan uwanta ,shi xata kalla tayi nishadi tayi dariya ,_
_Mami taxo ta shige ,hannunta rike da na meima sai xuba kamshi suke ,_

_Binsu da kallo Meimei tai ,kwalla ta tarar mata a Ido ,tana tausayin kanta ,dan bata da wanda xai dingai Mata irin abinda akewa meima,_


_ofis inta mami take tafiya da meimah ,tana xaune tana ta Ayyukanta ,sbda sun tarar mata ,meimah kuma na gefe tana ta wasanta ,_

_wayar tace tai ringing ,da hanxari ta dauka ta amsa kiran da ake mata ,_

_ba komai Ake sanar daita ba illah kiranta da ake meeting na gaggawa da Alhaji mamuda mai company kenan yakira ,_

_cikin hanxari ta tashi ta harhada komai ,kana taja hannun meimah suka fita ,_

_Anan gurin PA dinta take barin meimah ,ta shiga dakin meeting in ,_

_Meimah tana ta wasanta ,saiga maheer nan dan gidan Alh mamuda ,dan da yake matukar ji dashi ,shekarunsa basu wuce 18 ba ,_


_Meimah da ya hanga yarinyar taimasa kyau ,gurinta ya nufa ,ya daukko chaculate ya Mika mata ,Aikwa ta bangala mishi dariya ,ta Ansa ta bare ta tana sha ,nanfa ta fara xuba mishi surutun da bai tambayeta ba ,wani yayi dariya ,wani kuma ya tsaya yana kallanta kawai ,A haka iyayan nasu suka fito suka taddasu ,wanda hakan yaiwa mami dadi sosai ,_

_to fah tun daga wannan rana kullum mami meimah take xuwa ofis ,Indai kuma maheer yaje ,tare xasu huni tana xuba mai shirme ,wanda hakan yasa shakuwa tashiga tsakaninsu sosai_ ,



Alhaji mamudah
Allah yaimishi Arxiki mai tarin yawa da Albarka ,domin dukiyace da yake amfani daita ta hanyar Allah ,dukiyace da xata kaishi ga aljannah ba wacce xata halakar dashi ba ,(Allah ubangiji ka axurtamu da irin wannan dukiya ,Alfarmar Annabi Muhammad (S.A.W)Ameen ya Allah)
hajiya Asiya itace matarshi ta fari ,haihuwarta daya ,Allah ya kaddara rabuwa tsakaninsu ,A lokacin Maheer yana shekara 6 ,

Bayan rabuwarsu hjya Asiya ta koma garinsu italy , ta tafi tare da maheer dan tace baxata bar mishi shi ba ,
duk kaunar maheer da mamuda yake ,haka yabar mata shi suka tafi ,sbda shi Allah yayishi ba maisan rigima ne da tashin hankaliba , kasancewar mahaifin Asiya mai tarin dukiyane ,maheer yaga gata sosai ,ga mahaifinshi na xiyartarshi Akai- Akai ,

bayan rabuwarshi da Hjy Asiya sai yake auran xuwaira ,inda A yanxu xuwaira tana da yaya 3 duk mata ,fahima ,farha,fauxah,
Xuwaira duk ta Tara kannanta a gidan ,duk wacce auranta yaxo Alhj mamuda ke aurar daita ba tare da damuwaba ,

Kaunar da Alhj ke nunawa maheer ,da kuma ranshi da ya kwallafa Akan maheer ,da kuma dukkan burinshi da ya Dora Akansa , hakan na damun xuwairah ,har taji ta tsani yaron tsana mai tsanani ,hakan yasa koda Alhj ya dakkoshi domin yaimasa Hutu ,bai samun kulawa gurin xuwaira ,saidai mahaifinshi dake kulawa dashi sosai ,domin kaunar maheer A jininsa take ,babu wanda yaisa ya gusar daita ,sai wanda ya dasa mai ita ,

Har xuwa wannan lokacin hjy Asiya batai aureba ,tamai da hankalinta kan Aikinta ,domin cikakkiyar likita ce ,da kuma rainon tilan danta maheer ,wanda bata hada soyayyarshi da ta kowa ba ,

A yanxu ma Alhj mamuda ne yaje ya dakkoshi domin yamishi hutu ,wanda da kyar Hjy Asiya ta yarda

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment