Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma d'ayar cikin murmushi ta amsa tana bin Mawahib da kallo harta shige part dinsu, saida taga shigewar Mawahib sannan ta maida kallonta wajan Hajiya kilishi tace"Matar Alqali,Ina kuka samo 'yar kyakykywar yarinya haka?"

Hajiya kilishi tace"Hajiya Mariya baki ganeta bane?"

Wadda aka kira da Hajiya Mariya tace"ina zansan wannan yarinyar? duk zuwan danake bana ganinta,anya anan gidan take kuwa? Kina ganin yarinya jajir da'ita kamar wankan inji? Kiduba kiga wannan uban diri kamar ita tayi kanta,badan da 'yanbiyun samarinki a gidan ba aida nayiwa Farouq d'ina kamu..."

Hajiya kilishi tace" 'yar wajan Maryam cefa,da wanne samarin zaki had'ata?,inaaa! bade 'yanbiyu naba,har abada babu had'i, yanda kika gantannan kullum haka take yawo tana nunawa mutane jiki,ita ga tantiriya,kuma uwarta ce take koya mata komai,idan na kuskura nabari yarinyar nan ta auri d'ana aina kashe kaina, tun yanzu ma kafin ayi mata aure bad'ala iri-iri uwarta take koya mata,to inaga anyi aure? tana saka irin wannan kayan yanzu,idan tayi aure kuma wanne iri kike tunanin zata saka?kinsan 'yar maiduguri ce uwar, idan 'yarta ta auri dana kuma ai shikkenan sai yanda aka min dashi, kiduba kigani de yanda tashiga tafita a wajan malamai da bokaye saida tarabani da 'yanbiyu nah,basu Isa suzo gidan nanba saide kiga sunje part dinta sun tare,Ashraf ma dayazo shekaran jiya danyaga na tsaye masa ne, na Kuma saka masa ido,amma da abinci ma Infad'a miki saide yaci awajanta, to inda nakejin dad'i sauqina d'aya,yarinyar bata gabansu duka su biyun, musanman ma ARYAN...."


Cikin sauri Hajiya Mariya ta katse ta" ke dakata matar Alqali,wai kina nufin yarinyar nan ce 'yar wajan Maryam tagirma haka?"

Hajiya kilishi tace"hmm ai Ina ganin ikon Allah Hajiya Mariya,itace wallahi,ai kallon tsoro kikai mata,bakiga uban nonuwan taba"


Hajiya Mariya tayi ajiyar zuciya tace"to aikuwa matar Alqali tun wuri kitashi tsaye,inba hakaba kiyiwa kanki sakiyar daba ruwa..."

Cikin sauri Hajiya kilishi tace "wa?, Allah yatsare ni,ai har abada babu alkhairi a tsakanin ta da 'yanbiyu na,to Ina alkhairi ga yarinyar da batayi gadon haihuwa ba? Ita kad'ai uwarta tahaifa daga ita babu qari, ita kuwa bana tunanin ma idan tayi auren zata haihu, tunda batayi gadon haihuwa ba,to waima INA UBANTA?, har zuwa yanzu mude bamu ganshi da idonmu ba"(๐Ÿ˜ณ๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€๏ธtofa)

Hajiya Mariya tayi ajiyar zuciya tace"tabdi, aikuwa matar Alqali saiki dage,kuma kisawa 'ya'yanki ido sosai, kinsan maza da jarabar tsiya,da gane-gane, suna qyalla ido idan suka ganta shikkenan,musanman idan wannan dirin nata ya rud'esu,kina zaune saide kiji Ashraf yana cewa shizai aure ta shima Aryan yana fad'in shi zai aure ta...."(๐Ÿ˜‚)

Hajiya kilishi tayi ajiyar zuciya tace"kada ubangiji ya nunamin wannan baqar rana....to Hajiya Mariya ai bakisan wani abuba,gaba d'ayansu su biyun fa har yanzu basuda tsayaiyar budurwa,abun har tsoro yake bani, shekaru sunata tafiya sunqi aure, musanman Aryan, shi bashida magana, bansan yaya zaiyi yasamu mace ba"

Hajiya Mariya tace"tokode baqar aljana ce ta aure shi?"

Cikin sauri Hajiya kilishi tace"aiko farar aljana ce dole zaiyi aure shima ya ajiye zuri'ah"

"wannan gaskiya ne" cewar Hajiya Mariya, daga nan tarakota get dinsu na farko, sannan tadawo.


******


Da daddare Mamy tagama cin abinci suna zaune afalo gaba d'ayansu, yayanta dake maiduguri Alhaji Mustapha yakira wayarta, bayan sun gaisa yace"Maryam yaronki ne yasani wannan waya, kinganshi nan zaune tun yamma yazo yasani agaba lalle saina kiraki nafada miki shifa yanason Mawahib,yace nafada miki yanason ayi masa izni yafara zuwa wajanta zance "

Mamy tayi murmushi,tasan cewa yayan nata bashida wani da namiji Sai guda daya, sauran duka mata ne, cikin Jin dadi tace"Nabil kenan,yanzu nice nazama haka awajansa? bazai Iya kirana yafadamin da kansa yanason Mawahib ba saide yasaka kakirani kaida kanka Yaya?"

Gaban Mawahib ne yayi wata irin faduwa Jin maganar akanta akeyi,dama Yaya Nabil sonta yake shiyasa taga kwana biyu yana matsa mata da magana idan tahadu dashi a chat?
Bata gama tunanin datake ba taji Mamy tana cewa"a a, batada kowa Yaya, amma Nabil aina gida ne,Allah yasanya Alkhairi, Allah yasa rabon sa ce"

Bayan sungama wayar,cikin jin dadi Mamy ta Kalli Alhaji Isah tace"Abban Mawahib kaji wai Nabil din Yaya Mustapha ne yace afada mana yanason Mawahib"

Abba yayi murmushi ya Kalli gefenda Mawahib take zaune kamar ruwa ya cinyeta,cikin tsokana yace"yanmatana wai zaki aure shi kigudu kibarmu?"

Cikin kunya tatashi da sauri tafice daga part din nasu, tatafi wajan Nabiha.

Alhaji Isah yayi murmushi yace" To Alhamdulillah, gaskiya naji dadi sosai, Nabil ai yanada hankali,zansamu su Yaya inyi musu maganar,shima saiki fada masa yazo suyi magana shida Mawahib din,idan sun sasanta kansu shikkenan, idan Allah yayi auren dashi,saita qarasa karatunta adakin mijinta"

Mamy tayi murmushi tace"hakane,amma gaskiya ni naso ace saita kammala karatunta sannan zatayi aure,banason irin neman aure da wurin nan,duka-duka ma nawa Mawahib din take?shekara goma sha takwas Alhaji wanne irin aure ne wannan zasuyi?"

Abba yayi murmushi yace"wanne karatu Maryam?yaushe tafara karatun? ko level two bata shiga bafa yanzu tasa qafa a karatun,kicire wannan tunanin aranki inde harshi Nabil din zai barta tayi karatunta ai Alhamdulillah, batun shekaru kuma bawata matsala bane,tawani fannin ma gara hakan, mijinta zai koya mata soyaiya da kansa, sannan kuma kinsan abinda mu iyaye mukeso akan yayanmu qaddara tana zuwa ta sauya shi,kiga abinda mukeso din bai faruba, ke kinaso ace tagama karatu, taqara shekaru, sannan tayi aure,nikuma abinda yake Raina shine naso ace ta auri Yayanta CAPTAIN ARYAN,dukansu dagashi har ita Ina musu sha'awar junansu"

Gaban Mamy ya yanke yafadi,cikin sauri tace"Alhaji kadena wannan maganar Dan Allah, Allah yasa Nabil din yazame mata mafi Alkhairi"

Cikin Sanyin jiki Abba ya amsa mata da "Amin"


******


Tana zuwa dakin Nabiha tace"Nabiha nadena zuwa wajanki daga yau, ke bakida aiki saiki ki shige daki ki dauki wayarki,gaba daya kin manta dani"

Cikin murmushi Nabiha tace"to yi haquri,nadena, shikkenan? meyake faruwa naganki yanzu goma saura?"

Saida ta yatsina fuskarta sannan tace"kinsan me?wai Yaya Nabil ne yasa kawu Mustapha yayiwa Mamy magana wai yana sona"

Nabiha tanajin haka tagyara zama tace"ke dan Allah?"

Mawahib tace"wallahi,Nina rasa yanda zanyi,gaskiya ni bana sonshi,amma zan aure shi kodan Momy kilishi, idan tadena ganina ai shikkenan, bazata sake fada mana magana nida Mamy naba"

Nabiha tayi ajiyar zuciya tace"hakane kam, amma gaskiya nide Mawahib nafi miki sha'awar Yaya Ashraf,saboda naga kamar yana ra'ayinki"

Cikin sauri Mawahib tazaro idonta(๐Ÿ˜ณ) tace"Rufamin asiri Nabiha,inani Ina 'ya'yan Momy kilishi?,sannan kuma yamin girma,banason tsoho, gara yaro dan ashirin dawani abu"

Nabiha tayi murmushi tace"lalle yarinyar nan, Yaya Ashraf ne tsoho? to bari Kiji wallahi irinsu akeso,sunfi yaran Iya soyayya....wallahi innice ke ko,yanda Yaya Ashraf dinnan yake kulaki,wallahi sainayi soyayya dashi Inga Yaya Momy kilishi zatayi,Yaya Captain nede dama bamu Isa mugwada hakan ba" (๐Ÿ˜‚)

Mawahib tace"Nabiha ko amafarki bana fatan nayi soyaiya da 'ya'yanta, zama lafiya aiyafi zama dan sarki"

Haka suka dinga tattauna zancen har shadaya nadare,sannan Nabiha tarakota, sukai sallama

******

Washegari tun kafin tatashi daga bacci Nabil yakira ta yakai sau biyar tana bacci bata dauka ba,kuma wayar tana silent, saida tatashi taga messages dinsa dayawa,kusan guda hudu, duka babu wanda bai zuba mata kalaman soyaiya ba,kasancewar ta farin shigan soyaiya tafi minti ashirin tana daga kwance tanata aikin karanta saqonnin nasa,daga baya kuma tatashi tayi wanka ta shirya ta futo ta gyara musu gidan,bata dade da gama aikin ba Mamy tadawo kasancewar yau juma'ah da wuri take dawowa,sai bayan ansauko daga sallar juma'ah sannan Nabil yakira ta,sun dade suna waya tun Mamy tana mamakin Mawahib harta dawo ta daina ganin yanda take magana qasa qasa ita Ala dole da saurayi take waya, da abun ya isheta saita Kalle ta tace"Mawahib kije daki kiyi wayar mana"(๐Ÿ˜‚)

Babu musu tawuce dakinta,saida sukazo sallama dashi ne sannan yake fada mata zaizo gobe,me takeso yataho mata dashi, ta nuna masa batason komai, daga qarshe sukai sallama.

Saida daddare take fadawa Mamy Yaya Nabil zaizo gobe,Mamy tayi murmushi tace"Allah yakawo shi lafiya"

Washegari da sassafe taje tatashi Nabiha daga bacci,cikin Jin dadin bacci Nabiha tace"dan Allah Mawahib ki barni nayi bacci na"

Mawahib tace"kitashi dan Allah Yaya Nabil ne zaizo anjima, yamin waya yana hanya wallahi"

Cikin sauri Nabiha tatashi zaune tace"wai daga maidugurin zaizo?"

Tace"eh,bansan me zanyi masa ba,nahada masa drinks kawai yayi?"

Nabiha tace"haba Mawahib,ya mutum zaizo tundaga maiduguri amma mu bashi lemo, kinsan me? fita zamuyi muyo cefane muyi masa girki mai dadi, kinsan yau momy kilishi ce zatayi girki ba Mamy ba bare muce zamu bashi abincin gida,kuma wallahi momy kilishi abincin gargajiya takeyi, kawai kije kifuto muje driver yakaimu kasuwa muyo cefane mudawo"

Mawahib ta jinjina kanta tace"eh hakane kuma,to bari inje in shirya, kema kitashi dan Allah"

Cikin sauri suka shirya suka fita,driver yakaisu suka siyo abinda suke so, sannan suka dawo gida, suna dawowa ko zama ba suyi ba suka fada kitchen, kasancewar kayan maqulashe suka hada masa nan da nan suka gama kafin ma ace Hajiya Kilishi ta shigo kitchen din, Mamy de taga anata jera girke girke afalo cikin ranta tace"ikon Allah,zamani kenan"

Sai wajan qarfe uku na yamma yazo,kasancewar sa ba baqo ba a gidan yasa kai tsaye Mawahib ta shigo dashi falo,saurayi ne matashi bazai wuce shekara ashirin da bakwai ba.

batayi kwalliya mai yawa ba,kawai light makeup tayi,tasaka riga da siket na leshi,tayafa mayafi dan madaidaici mai kyau, bayan sun gaisa ta gabatar masa da kayan ciye ciye, babu kunya yaci abunsa sosai, sannan takira masa Mamy suka gaisa, Mamy tadan dade a zaune tana tambayarsa 'yan'uwanta mutanan maiduguri, sannan ta koma daki tabarsu shida Mawahib din.

Cikin nutsuwa yafara yiwa Mawahib magana cikin sigar jan hankali domin kuwa ya lura bata taba soyaiya ba,a hankali a hankali harya dinga janta da zance harta sake dashi,nan da nan ya dinga sakata dariya sai gashi tun kafin yatafi taji ya kwanta mata arai kasancewar sa mutum mai barkwanci, maisata nishadi.
bai dade sosai ba yace zai tafi, kasancewar tafiyar akwai nisa,sai a lokacin takira masa Nabiha suka gaisa,dazata tafi yadauki 5k yabata, Nabiha tayi masa godia sosai, sannan tatafi, ita kuma Mawahib suka qarasa tattauna wa sannan ta futo zata rakashi,sunzo get nafarko ya kalleta yace"to Amarya ta,zan tafi,sai yaushe kenan?"

Kalmar daya fada ta amarya ta, itace tasa Mawahib dariya,har dimples dinta suna futowa, adede lokacin musa megadi ya budewa Ashraf get yasako hancin motarsa ciki,dasu yafara cin karo,tun daga nesa ya hangota tana yiwa wani qato murmushi, lokaci daya yanemi annurin fuskarsa yarasa,ko gama daidaita parking baiyi ba yafuto daga cikin motar ya nufi get na biyu,fuskar nan tasa a murtuke, Mawahib data dago daga dariyar datake lokaci daya tayi ido biyu dashi, mamaki ya kamata,kode Yaya Captain ne yadawo? to ai kuma idan shine yadawo dole zata sani,da tuni qofar gidansu ma yacika da jama'ah, to meyasamu Yaya Ashraf yayi irin wannan daure fuskar?gaba daya saiya koma mata Yaya Captain sak.

Koda wasa baima kalli inda suke ba yabude get din zai shige,Nabil ya kalle shi cikin mutuntawa yace"barka da shigowa Ina wuni?"

Ba tareda ya kallesu ba yace"lafiya"
kamar anyi masa dole, yana shigewa ciki Nabil ya Kalli Mawahib yace"Sojan gidanku yadawo ne? naga shine baya fara'ah, kinsan niba ganesu nakeba"

Mawahib tayi wata dariya Mai kamada yaqe, tace"shine...,"

Saide cikin ranta tana mamakin sauya war Yaya Ashraf zuwa fishi, idan ta cewa Yaya Nabil bashi bane zai Iya tunanin wani abu, shiyasa tayi masa qarya cewa Yaya Captain ne.

Nabil yayi ajiyar zuciya yace"rannan naga bbc sunyi posting din karramawar da'aka musu,naga photon sa shida shugaban qasa, Allah yasanya Alkhairi"

Kanta aqasa tace masa "Amin ya Allah"

Motarsa yabude yadauko mata wata babbar leda fara, yabata yace "ki shiga da wannan ciki,babu yawa yar qaramar kyautata ce izuwa gareki"

Cikin sauri ta girgiza masa kai tace"A a,Mamy zatamin fada,babu ruwana ka barshi"

Murmushi yayi yace"naji, to ki kar6a zankirata awaya inyi mata magana"

Saida taji haka sannan ta kar6a tayi masa godia,yace zaije suyi sallama dasu Alqali sannan yawuce,tayi masa Addu'ah,sannan tajuyo zuwa cikin gida.



Tana shiga part dinsu, ta tsinci muryar Yaya Ashraf cikin fishi yana fadin"Amma Anty Mamy yaushe tafara karatu da zaku barta tafara sauraron samari yanzu? waye yabata damar kula samari haka anyhow....?"

baima tsaya jin amsar da Mamyn zata bashi ba yajuya cikin 6acin rai zai fice daga part din,yana ganin Mawahib abakin qofa a tsaye da
uwar leda a hannunta yazo wucewa ta gefenta qiris yarage ya bigeta, cikin sauri ta matsa gefe, tsananin mamaki ya cikata dama shima yana fishi haka?(๐Ÿค”)

Mamy takasa magana tabi Ashraf da kallon mamaki harya fice daga part din,a hankali tasaki murmushi ganin wannan qarfin hali nasa, gaba daya tagama gane inda yadosa,kuma hakan bazai ta6a iyuwa ba,koda ace Mawahib din tana sonshi dole zata haqura dashi, haka inma mazan gidan sukace zasu qullah to bazata yarda ba,saide wannan karon a saketa har abada tafice tabar familyn Alqali.






(wata sabuwa๐Ÿฅบ๐Ÿ˜ฑ)













Amnah El Yaqoubโœ๐Ÿป

๐Ÿ’—MAWAHIB๐Ÿ’—


Writing By Amnah El Yaqoub


7&8




Cikin sanyin jiki ta qarasa shigowa falon,tazauna kusa da Mamy tace"Mamy me a kayiwa Yaya Ashraf tunda yashigo naga kamar yana fishi"

Cikin basarwa Mamy tayi murmushi tace"Fada yake saboda kinfara tsayawa da saurayi, baisan su Alhaji ne suka bawa Nabil damar zuwaba,tun ranar da mukai waya da Yaya Mustapha Abbanki yaje yasamu Yaya Alqali yafada masa komai"

Ahankali Mawahib tasaki ajiyar zuciya tazauna,tabawa Mamy ledar hannunta cikin dari-dari tana tsoron kartayi mata fad'a,cikin murmushi Mamy ta kar6i ledar tace"Kawo miki yayi?"

Tace"eh, saida nace yabarshi shine yace zai fad'a miki"

Mamy tace"to inbanda shirme menene naqin kar6a? koba maganar soyaiya Nabil ai yayanki ne,dani da mahaifinsa uwarmu daya ubanmu daya,bazanyi fad'aba danya baki wani abu,bari mugani menene aciki"

Tafadi hakan tana bude ledar,kayan kwalliya ne aciki masu tsada harda turarukan da chocolate dayawa,sai wata 'yar qaramar Envelope da dubu goma aciki,cikin murna Mamy tace"lalle Nabil,wannan uban kaya haka ai kinci qarfin albashin nasa,Allah yasanya Alkhairi,amma ya kikagan shi? ya miki?"

Cikin tsananin kunya taturo dan qaramin bakinta gaba tace"kai Mamy dan Allah....nide kidena min wannan maganar"
cikin sauri tamiqe zatabar wajan, Mamy tana dariya tace"dawo ki dauke kayan ki,kije kikaiwa 'yar'uwar taki itama"

Cikin shagwa6a tadawo tabude kayan tadibawa Nabiha komai,sannan tatafi zatakai mata.


Nabiha tagama dudduba kayan da Mawahib takawo mata, cikin mamaki tace"Gaskiya kinyi sa'ah Mawahib,yaya Nabil da qarfin sa yafuto,kuma da alama da gaske yake tunda gashi ta wajan iyaye yafara neman,kuma daga gani bashida rowa,gashida fara'ah masha Allah, kinsan wannan kayanfa tsada ne dasu"

Mawahib tayi murmushi tace"nima shiyasa naji yafara birgeni,tunda yazo yaketa bani dariya,gashi bashida shekaru sosai irin mijinda nakeso,ke kinsan meyafaru dazu da yamma kuwa?Yaya Ashraf yadinga yiwa Mamy fad'a saboda na saurari Yaya Nabil,kuma fa Abbana yasan da zuwan nasa"

Nabiha tayi shiru tana sauraron Mawahib,tunda Mawahib d'in tafara magana dayake ita tafita shekaru da wayo, nan da nan ta dauki haske akan dalilin fadan Yaya Ashraf din, tayi shiru saida tagama jin qarshan zancen sannan tayi ajiyar zuciya tace"kinsan abinda nake tunani? Yaya Ashraf fa Ina zargin sonki yake"

gaban Mawahib yayi wata irin faduwa,cikin tashin hankali ta zaro idonta tace"dan Allah Nabiha? Innalillahi...naga takaina"

Nabiha tace"menene abun wani innalillahi...? kinsan Allah sonki yake,kuma zakice nafada miki"

Mawahib tace"ai yanzu yaga Yaya Nabil,nikam babu ruwana, bazai ma fadamin ba, babu ruwana da Momy kilishi"

Cikin bada qwarin gwiwa Nabiha tace"kinsan Allah,ki ajiye wannan haqurin naki irinna Mamy agefe ki fuskanci rayuwa, wani lokacin idan biyaiya tayi yawa anfi yima is'kanci,kina mata biyaiya kamar itace takawo ki duniya,ni bakiga idan tana sababin tama wayata nake dauka ba?"

Cikin rawar murya Mawahib tace"bazan iyaba Nabiha,itama kamar uwa ce awajanmu, watarana ai sai labari,nan gaba kadan ma zanbar mata gidan har abada inkoma wajan Yaya Nabil maiduguri"

Nabiha tace"to ai shikkenan,saiki daina rawar jikin"
Sai a lokacin Mawahib ta Lura jikinta rawa yake tunda Nabiha tace mata Yaya Ashraf yana sonta, sun dade suna fira daga baya tayi mata sallama tatafi.

Washegari da safe takama weekend ne, Mamy tana gida bataje ko'inaba,itama Mawahib tun safe data gyara musu part din nasu takoma dakinta tagyara shi,tarasa meyasa tun safe gabanta yaketa faduwa,sai Addu'ah taketa maimaitawa aranta, tana gama gyara dakin Yaya Nabil yakira wayarta,tayi zamanta adakin suna wayarsu,
Mamy ce taqwala mata kira cikin sauri tayi sallama dashi tafuto,ganin Mamy tayi dauke da wani yaro yana kuka kad'an-kad'an, ita kuma Mamy sai jijjigashi take,Mamy ta kalle ta tace"d'auko hijabin ki kikai wannan yaron gidan Maman Fati,yanzu ta aiko shi nayi masa allura kuma naga yaron daya kawo shi kamar bazai riqe shi dakyau ba,nace yaje yaturo babba adaukeshi,kuma kinji shiru babu wanda yazo"

Tace"to Mamy"

Sannan tajuya dakinta tadauko hijabi tafuto,hayaniyar datake ji a waje ne yabata mamaki tarasa me'akeyi haka,Mamy ta nufo bayanta da yaron tace"yi sauri ki goyashi kikai matashi yaro yanata kuka tun dazu"

tafad'i hakan tana dora matashi abayanta, Mawahib tasa zanin goyon tana kokarin goya yaron, tace"Mamy wai hayaniyar menake ji a waje? kosu Daddy ne suke rabon zakka?"

Cikin sauri Mamy tace"riqeshi ki goyashi ni,kin dameni da tambaya sauri nake,CAPTAIN ne yazo, inaso inyi sauri inyi masa ferfesu med'an sauqi"

tana fad'ar haka tayi d'akinta tabar Mawahib atsaye a wajan

Haushi yakama Mawahib,tabi bayan Mamy da kallo gabanta yana dukan uku uku,cikin ranta tace"mukam yau munshiga uku, bala'i yadawo"

tajuya ta kalli yaron dayake goye abayanta yana qishin-qishin din yin kuka,cikin haushi kuma a fili tace"Yanzu fisabilillah Mamy saboda wannan mutumin jikinta yake rawa haka? saikace wani mutumin kirki za'a je anayi masa wani farfesu? wahalalle yanzu haka da wannan uniform din nasa na kullum-kullum yazo"(๐Ÿ˜ฑ)

tasake juyawa ta kalli yaron dayake goye abayanta,tatuna maganar qawayenta 'yan makarantar su dasuke cewa goyo yana zubar da Nono, cikin fad'a tafara qoqarin sauke yaron daga bayanta tareda fadin"kaikuma sauko,wallahi bazan goyaka ba"
tasake rage muryarta taci gaba da fadin"Salon d'an nonon nawa duk su zube mijina yarasa na kamawa...."(๐Ÿ™Š)

Qamshin turaren daya bugi hancinta,wanda bata gama tantancewa nawaye ba yasa tajuya bayanta dasauri....,lokaci d'aya idonsu yahad'u dana juna,gabanta yayi wata irin fad'uwa,atake gumi yafara rufe mata fuska,idonta yayi tsilli-tsilli qarara tsoro ya baiyana a cikinsu,Addu'ah take aranta Allah yasa baiji maganganun datayi ba, kallonta yake fuskar nan tasa murtuk babu alamun fara'ah,amma hakan bai hana kyawunsa baiyana ba,kyakykywane ajin farko,kamar kullum yana sanye cikin kakinsa na Soja,kayan yayi mutuqar yimasa kyau,farar fatar jikinsa tabada hadin kai wajan qawata uniform din a jikinsa,agaban rigar bangaren hannun dama an rubuta CAPTAIN ARYAN,gefen hannun hagu kuma an rubuta NIGERIAN ARMY.


Jikinta ne yadauki rawa,cikin sauri tacire idonta daga nashi,gani take kamar wani abu ne yake futowa daga cikin nasa idon yana shigewa cikin nata idon,da sauri ta matsa ta bashi hanya, tayi wuf tafice daga part din nasu,saura qiris ta doka tuntu6e takayarda yaron hannunta,kai tsaye ta nufi get tafice daga gidan, saida taje bakin get din nasu sannan taga sauran mutane sunata daukar kayan abinci kama daga shinkafa har zuwa taliya da macaroni,gakuma wasu sojoji a tsaye agefe kowanne hannunsa daukeda bindiga, cikin sauri ta wuce kai tsaye taje takai yaron gidansu, sannan tadawo gida,tanaji tana gani part dinsu ya gagareta shiga,sai part dinsu Nabiha ta wuce.

Duk yanda sanyin esi ya ratsa dakin Nabiha, hakan bai hana Mawahib cire hijabin jikinta tana sake firfita dashi ba,Nabiha tace"meyake faruwa ne Mawahib naga sai gumi kike hadawa?"

Cikin rawar murya tace"nida Yaya Captain ne...,maganganu nasaki baki inata fada,bansan yana bayana ba,bansani ba yaji abinda nake fada ko baiji ba,amma kunya ta kamani, na aikata abinda ba halina bane Nabiha"

Cikin sauri Nabiha tace"innalillah....Yaya Captain kuma?to me kikace? wacce maganar kikayi?"

Mawahib tayi shiru tana tunanin me zata cewa Nabiha? nayi maganar nono kuma Yaya Captain yajini?kokuma nagama zaginsa tsaf kuma yajini?

Cikin sauri ta girgiza kanta tace"kede abar kaza cikin gashinta,amma na tabbatar inde yaji abinda nafada,babu abinda zai hanashi dukana"

Nabiha tace"to yau kin janyo mana ruwa, kinganni nan? tunda naji hayaniya a waje nasan cewa shine yazo,shiyasa naqi fita ko nan da can"

Mawahib tace"to yanzu yaya zanyi Nabiha?"

Nabiha tace"wai akenki yayi kikaqi zuwa ne?"

Cikin rawar murya Mawahib tace"nace miki kidena tambayata abar kaza cikin gashin ta,ni wallahi yau babu inda zanje daga nan"

Tana fadar haka ta kwanta a gadon Nabiha tareda shigewa cikin bargo,gaba daya sai taji zazza6i yana neman rufeta.

Ba'ita ce tabar part dinsu Nabiha ba, saida aka kira sallar magrib, taji gidan shiru alamun duka mazan gidan suntafi masallaci, sannan ta lalla6o ta wuce part dinsu da gudu.

da daddare suna zaune afalo da Mawahib da Abba dakuma Mamy suna kallo, Mawahib tana sanye cikin doguwar riga ta bacci amma mai kauri, su Mamy suna kallo suna fira kad'an kad'an, amma Mawahib gaba daya tunaninta baya kansu, shawara tagama yankewa aranta gara tahada kayanta tatafi maiduguri idan taji labari Yaya Captain yatafi, saita dawo, kokad'an bataji dadin zuwansa ba, ga kuma rashin kunyar data gama yimasa wanda bata saniba yaji ko baiji ba.

Abbanta yayi magana yaji shiru bata saka baki, a hankali yajuya ya kalle ta yace"yanmatan Abba, babu matsala deko?"

Kallansa tayi cikin ladabi tace" Abba babu matsala,amma inaso idan ka amince zanje maiduguri"

Abba Yajuya ya Kalli Mamy yace "lafiya zata tafi?"

Mamy tace"Alhaji nima sai yanzu naji zancen tafiyar"

Cikin mamaki yace"meyafaru zaki tafi,kuma tafiya babu shiri baki sanarda mahaifiyar kiba?"

Wani irin murmushin qarfin hali tayi sannan tace"Abba dama inaso naje hutu ne kafin hutun mu yaqare"

Abba yace"A a Ruqayya,yaushe kukai hutun ai baki gama hutawa ba,sannan ga yayanku yazo d'azu da yamma, kowa yana gida,bai kamata kitafi ba,ni kinyi masa murna ne akan karramawar daya samu?"

Wani irin qullutun taqaici ne yakama Mawahib,yanzu saboda Allah dan Yaya Captain yazo sai ahanata tafiya hutu maiduguri?
Cikin kwanciyar hankali ta shimfidawa Abbannata qarya tace"eh dazu mungaisa nayi masa ala sanya Alkhairi"

Tana rufe baki, aka turo qofar part din nasu aka shigo,wani irin qamshi mai dadi yadaki hancin Mawahib,sanin datayi cewa irin qamshin dazu ne, hakanne ya tabbatar mata da cewa Yaya Captain ne, hakanne yasa koda wasa batayi kuskuren dago kanta ba,cikin sallama suka shigo falon,dukansu su biyun sanye sukeda wando three quarter, da riga marar hannu alamun kayan shan is'ka ne a jikinsu tunna yamma,gaba daya sai suka saje suka zama abu d'aya,saide fuskar mutum daya data kasance babu wasa akanta.

Mawahib tayi mutuwar zaune kamar ruwa ya cinyeta,saika rantse bata cikin falon.
Cikin farinciki Mamy tace"yan samari"

Captain yad'ora hannunsa akan daya daga cikin kujerun falon yace"Anty Ma-my...."

yakira sunanta a rarrabe,cikin murmushi tace"Captain"

Yaya Ashraf yace"Anty Mamy akwai sauran kunun madarar nan na dazu?"

Mamy tace"akwai, yana dinning bari in dauko muku"
Tafadi hakan tana kokarin tashi, Abba ya Kalle ta yace"yakamata kiyiwa 'ya'yanki fad'an ajiye iyali Maryam"

Mamy takawo musu kunun madarar wanda yaji kwakwa aciki har lokacin da zafinsa,tazuba musu a cup tabawa kowa,ta zauna a kujera tana fadin"to gasunan de Alhaji,inajin saimun fara tallarsu a yanar gizo"

Adede lokacin Yaya Nabil yakira wayar Mawahib,a hankali tasaki wata irin ajiyar zuciya,dama atakure take a wajan,idan tatuna maganar Nabiha datake cewa Yaya Ashraf yana sonta, tasake tunawa da kato6arar datayiwa Yaya Captain dazu, gaba daya saitajita atakure, a hankali tamiqe tanufi hanyar dakinta,Captain Aryan yana shan kunun madara yad'ago da manyan idonsa a hankali yabita da kallo,karaf idonsa ya sauka akan hips dinta,cikin sauri yad'auke kansa.

Shikuwa Yaya Ashraf kasa daina kallonta yayi, har saida yaga ta shige dakinta tareda rufowa.

Mamy tayi ajiyar zuciya ganin Mawahib tabar wajan,gaba dayansu tana lura dasu yanda suka bi yarinyar da kallo, musanman Ashraf da tun shigowar su ya kafeta dawani irin kallo,to shikuma Captain Aryan kallon na menene? a hankali gabanta yafara faduwa,amma data tuna da maganar Nabil, saitaji hankalin ta ya kwanta harta sake sukaita firarsu.



Sun dade a part din Mamy sannan suka tafi dakin su,Ashraf yafara gyara musu lafiyaiyen gadon su,Captain yana danna wayarsa,d'ayar wayar tasa ce tayi qara, yadauka yana magana a hankali kamar da mace yake magana,Ashraf yayi tunanin Captain din yayi sabuwar budurwa ne, a hankali yadago yana kallon sa saiyaji yana cewa"A a bamu da irin wannan bindigar,idan zaka shigar da bayanan ka rubuta muna buqatar irinta,musanman saboda sababbin ma'aikata wanda zasu kar6i horo ok?"

Daga dayan 6angaren aka amsa masa, sannan ya ajiye wayar.
Ashraf yace"bansan yau zaka shigo gari ba, da nasa yaran nan sun gyara mana dakin,duk yayi datti wallahi"

Hankalinsa yana kan waya yace"nima bansan zan taho ba,kawai nagaji ne,kuma inason ganinka kaida Momy, shiyasa kawai nataho,toko muje gidanka mu kwana tareda wad'ancen sojojin?"

Ashraf yace"Rigima boy kenan....babu matsala mu kwanta kawai gobe saisu gyara mana,wai kasan yarinyar nan Zulaihat kuwa har yanzu tana nan tanata nacin kirana?"

Captain ya ajiye wayar hannunsa yace"karabu da'ita kawai,dan nima ganin farko danayi mata naji tamin..."(๐Ÿ˜ฒ)

Ashraf yace"but... tabani tausayi, tana kuka tana tambayata meyasa zan yaudareta?"

Cikin rashin damuwa Captain yace"toya zatayi? Kashareta kawai kanemi wata"

Ashraf ya zauna abakin gadon ya kalli Captain yace"amma kasan idan nasake yin wata budurwar kace kana sonta saika raina kanka?"

Captain yace"to idan aka dace Ina sonta ya zakayi? zamu auri mace d'aya ne?"

Ashraf yadauki fillo yadora a cinyarsa sannan yace"wai kai baka ga Mawahib bane?"

Saida ya yatsina fuskarsa sannan

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment