Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_


*_TABARMAR K'ASHI_*

*SAFIYYA HUGUMA*

_AREWABOOKS:Huguma_
https://arewabooks.com/u/huguma

Page 01


K'awataccen bedroom ne me yalwa,wanda ya wadatu da kyawawan kayan gado da suka kasance cikamakin ado da kyawun dakin,komai dake cikin dakin an hada masa color iri daya CREAMY WHITE da ratsin gold me daukar idanu,ya wadatu da sanyin ac da kuma haske sosai tarwai.

Saidai kuma abinda zai baka mamaki shine,duk da irin kayan ado da qawar da bedroom din ya mallaka,kusan komai na dakin a hargitse yake,hatta da tattausan farin bedsheet din da comforter din dake daga gaban gadon a yamutse suke guri guda,uwa uba kuma dukkansu sunyi staining da wasu abubuwa da bazaka iya tantance meye a jiki ba,illa dai ka ragewa kanka wahala ka kirasu da datti kai tsaye.

Daga can tsakiyar gadon kuwa, matashiya ce zaune sannan a cure waje daya,tamkar wadda ke shirin saka kanta cikin gangar jikinta ta koma abu guda,ta rungume gwiwoyinta sosai a qirjinta. Baka iya hangen fuskarta,amma kana iya hangen sassalkan gashinta me tsaho da santsi daya cukurkude,kwatankwacin yadda zare yake cakudewa guri guda,tsahon sumar ya sanyata barbazuwa har saman qafafunta,ya kuma rufe dogayen fararen singalalin hannunta. Rigar jikinta doguwar riga ce ta wani material ne ruwan madara,kallo daya zakayi masa kasan me tsada ne,saidai shi kansa ya canza yanayi yayi wani irin azababben squeezing.

Idan ka kasa kunne da kyau zaka iya jin sautin kukanta,sautin da bashi da wani qarfi ko karsashi a cikinsa ko misqala zarratin,saboda rashin wadatacciyar garkuwar jiki da zata bata wannan damar,uwa uba kuma.......tayi kukan tayi kukan har batasan adadi ba,ta zubda hawayen har sai data daina sanin lokacin tahowarsu......har sai da idanunta suka fara gani dishi dishi,ta yanke tsammani daga samun dukkan dauki,ta kuma gama sallamawa qaddara rayuwarta.

Duk da cewa a hankali ya bude qofar dakin amma hakan bai hanata jin alamun an bude din ba,a hankali ta daga kanta,ta kuma sauke dubanta ga bakin qofar,duk da mummunar wahala da ibtila'i me gigita hankali da gusar da imanin me raunin tauhidi da take fuskanta,amma har yanzu kyakkyawar fuskar nan tata tana nan yadda take,wani irin kyau na daban me matuqar tasiri da fusgar hankali da ya gagara gushewa shimfide saman fuskar tata,saidai kana kallonta kasan ba haka take ba,abubuwa da yawa sun canza wanna fuskar.

Shi da ita suka zubawa juna ido kamar yau ce ranar farko da suka fara ganin juna,kowannensu da kalar kallon da yakewa dan uwansa. Dariya ya saki ya cire hannuwansa daga aljihun trouser din jikinsa,ya fara takowa zuwa cikin dakin bayan ya sanya hannu ya maida murfin qofar dakin ya rufe. Yana takowa yana tafa hannayensa, idanuwansa kuma a kanta kamar yadda dariyarsa bata yanke ba,ita kuma taci gaba da binsa da kallo,zuciyarta tana la'antarsa,tana sake daukaka qararsa zuwa ga sammai wajen ubangijin al'arshi.

A haka ya qaraso,ya jawo stool zuwa gaban gadon,ya zauna sosai yana fuskantarta hadi da taka gefen gadon da qafarsa guda daya

"Kewai kina tunanin akwai abinda zakiyi da zai warware dukka shirina?,ko kina zaton zaki kubuta da sauqi haka?" Kyawawan idanunta da suka sake zama manya manya ta lumshe,ragowar hawayen da basu samu damar zubowa ba suka gangaro,sannan ta budesu tarwai a kansa

"Bani da tsumi kuma bani da dabara,ban isa na fidda kaina ba,amma na kaiwa me kowa me komai,mai iko akan kowa qararka,koda kayi ajalina.....koda bayan raina ina fatan nutsuwa da salama suyi qaura daga rayuwarka,ka girbe fiye da abinda ka shuka" ido ya runtse ya kuma bude a tare yana sakin qaramin murmushi,sai ya miqe tsaye

"Dadina dake tawakkali....." Yayi furucin yana qara taku biyu zuwa gaban gado,ya haye gefan gadon ya zauna,sai tayi saurin sake tattare qafafunta ta rungumesu da kyau,kamar wanda yake shirin raaba mata maciji a jikinta.

Qafafun nata yabi da kallo har ya zuwa fuskarta,sai ya sake qyalqyalewa da dariya

"Ina sonki.....kuma banajin zan daina sonki,saidai kin shiga hurumin daba naki ba,kin shigar gonar daba taki ba,kin tsallake iyakarki,kuma a yanzu nafi buqatar wadan nan abubuwan fiye dake,ki daukominsu ki damqamin,ke kuma na barki kici gaba da rayuwarki cikin salama" kai take girgizawa tana hawaye,wani irin mamakinsa tana jin kamar zai kasheta, kowacce rana da zata bullo zuwa faduwarta cikin shakka da kokwanto take,anya wannan din ADAM NE?,anya adam dinta ne?,anya musanyensa akayi mata ba?,ko kuma wata rundunar mugayen shaidanun aljanu ta shige jikinsa ne ta samu mafaka?,don abinda yakeyi a yanzun da ainihin wannan suffar tasa ta yanzu.......bata taba ganinta a tattare da adam dinta ba,koda kuwa cikin mafarkan bacci bare a kai ga rayuwa ta zahiri,adam din da ko quda baya qaunar ya sauka a kanta?,adam din dake kuka da idanunsa idan bata da lafiya?,adam din da yake kasa bacci saboda ta shiga damuwa?,adam din da yake kasa sukuni idan tana da buqata har sai ya adar mata?,dole ta shiga shakka.....amma kuma kullum yana qara tabbatar mata da cewa shi dinne fa,bawai kama ko musaye bane,to me yake faruwa?.

"Bazan taba baka ba.....burinka bazai taba cika ba,saidai na rasa rayuwata,kayi duk abinda kaga dama" ta fada tana jin bacin rai yana taso mata,tare da wani irin qwarin gwiwar tunkarar duk nau'in kalar azaba tuggu da makircin daya shirya mata.

Wani murmushi ya kuma saki yana dubanta,da wani irin kallo na qasa qasa mai cike da tarin mugunta

"Ke kike jawa kanki koma meye,tunda ke muguwa ce ba zaki iya sallamamin abinda kikafi qarfinsa ba tako ina,to nima bazan sassauta miki ba har sai sanda kika gasu,kikaji cewa zaki iya sallamawa" daga haka ya miqe,ya fara fidda kayan jikinsa yana zubarwa a wajen.

Idanu ta bude da kyau cikin tsananin tashin hankali tana dubansa,kada dai ace haqqinsa na aure yake shirin karba kamar yadda ya saba?,zallar rashin imanin da yake gwada mata bai sanya ya daga mata qafa ba,yakance

"Har yanzu fa a sunan matata kike,ban saki igiyar ba,wannan abun dake faruwa wani issue ne na daban daya shafi interest dina da kuma naki". A duk lokaci irin wannan idan ya rabeta tana jin inama zata bude idanu taganta kwance cikin ramin qabarinta?,banda addininmu ya haramta kisan kai,naka ko na Wani,tabbas da tuni ta tsufa da kai kanta kiyama.

Da gaske so yake ya kusanceta alhalin yasan cewa cikin jinin al'ada take,rashin imanin nasa qara gaba yake,dole tace rundunar shaidanun aljanu ne suka shigeshi,don lamarinsa yafi qarfin shaidani guda daya.

Kansa tsaye ya nufota gadan gadan,kamar ba adam din nan da abaya a lokutta irin wanann yake sanyata taji babu ya ita cikin 'ya'ya mata ba,ya sanyata taji duk duniya babu macen da tayi sa'ar abokin rayuwa irinta ba,a yanzu ya koma mata wani tsohon annamimin ifritu mashayin jinin bil'adama da ko motsinsa bataso ji bare ya rabeta,bashi da maraba da qaton shaidani a idanuwanta.

Ringing din wayarsa ya dakatar dashi daga sake tunkarota,sai ya koma cikin aljihun wandonsa da ya yasar yana lalubar wayar. Cikin hanzari ya karata a kunnensa,sai kuma yace

"Ok,yanzu yanzu?,tom" ya latse wayar da sauri ya maidata,sannan ya soma mayar da kayan jikin nasa tana daga zaune tana kallonsa.

Ga mamakinta sai taga yana bi yana balle button na rigarsa yana watsarwa,ya kama gaban rigar da qarfin tsiya ya ciccisge,sannan ya tsugunna ya jawo plate din tangaran din dake ajjiye gefe wanda ya kawo mata abincin da bata budawa bare ta taba,ya dagashi har abincin ya tamfatsa shi da qasa ya tarwatse,ya dauki wani yanki daga ciki ya yanki jikinsa ya kuma shashshafe maiqon a jikinsa.

Sake miqewa yayi ya fara fatali da kayan dake saman madubi da duk wani abu na glass dake dakin yana cewa da matuqar daukaka murya

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,ki tsaya......ki tsaya don Allah,ya salam,karki jiwa kanki ciwo, Hasbunallahu wa ni'imal wakeel,ya hayyu ya qayyumu ya baki lafiya" yana fada hawaye na sauka a idanunsa,yana kuma ci gaba da tarwatsa dakin tare da sake hargitsashi,bayan tsaiwa da tayi tayi masa gyara na nutsuwa,waiko hakan zai sanya wani daga cikin ahalin nata su ankara da cewa akwai hankali tattare da ita.

Sanqamewa tayi a zaune,tunaninta ya dinke cifff kan meye manufar adam na aikata haka?,saidai koma meye tasan halinsa,ungulu ne baya jewar banza,ba shakka akwai abinda yake shirin sake qullawa. Kafin takai ga lalubo abinda ke shirin faruwa sai ta tsinci muryoyin mutanen da a kullum take addu'ar isowarsu gareta,qila akwai wani haske da zai risketa,ya kuma zama silar fitarta daga duhu zuwa haske.

Da mugun qarfi ta yunqura zata dira daga gadon,yayi caraf ya tsallako ya damqeta ya cukuikuyeta da kyau yana sake yamutsa rigata da yamutsatsen gashinta.

Ya mata mugun riqon da bazata iya qwacewa ba,saboda banbancin qarfi da kuma qarancin garkuwa jiki dake tare da ita,don haka ta bude baki da zummar kiran daya daga ciki

"Koda kin kirasun ma sun shigo sunanki bazai canza ba a idanunsu,sunanki mahaukaciya har yau har gobe,sai ranar da kika fanshi kanki,ni kuma zan wankeki a idon duniya" daga haka yaci gaba da qaraji da ambaton sunan Allah yana mata kyakkyawan riqo,ita kuma taci gaba da yunqurin qwacewa hawaye na gudu bisa fuskarta, kokawa ta barke a tsakaninsu duk da cewa ba wata nasara a hakan sai azabar riqon da yayi mata da takesha,dai dai sanda aka turo qofar da sauri aka shigo,ya saki wani lafiyayyen murmushi daga can qasan zuciyarsa,burinsa ya cika,plan dinsa ya tafi a dai dai,dama abinda yakeso kenan.


FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*

+22799643131

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥
*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_* 💔
_Arewabooks:Huguma_
https://arewabooks.com/u/huguma

Page 02


*_1988_*

Cikin madaidaicin falon matsakaicin gidan,wanda bai cika da wani kayan ado da qawa na rayuwa ba,saidai tsananin tsaftar data bayyana kanta jikin kowanne loko da saqo na gidan zai matuqar burgeka tare da daukar hankalinka,har kayi sha'awar matsakaicin gidan.

Kyakkyawar macace fara sol,irin farin da zai iya daukan hankalinka,tare da alamta maka cewa lallai mutum yana da nasaba da wani yare cikin yarukan nigeria zuwa afrikaans da kowa yasan fatar duk wani dan yarensu farace,koda akwai baqaqe suna wahala qwarai. Duka duka shekarun haihuwarta a ido ba zasu haura ashirin ba.

A gurguje take sakawa yaron dake tsaye a gabanta uniform dinsa,tana gyara masa kwalar rigar uniform din,lokaci guda kuma tana jijjiga yarinyar dake goye a bayanta daketa faman tsala kuka kamar wadda ake yankar naman jikinta.

Kana kallonta zakasan a rude take,uwa uba kuma alamu sun nuna sauri takeyi sosai,fadi takeyi cikin yanayin damuwar dake shinfide akan fuskarta

"Yi shuru......yi haquri yanzu zamu wuce kyasha iska a hanya" ta fada fana durqusawa tana qoqarin sanyawa kyakkyawan yaron da sumarsa mai yawa da santsi ke sake kwantowa gaban goshinsa saboda duqawar da yayi zai karba safar da take qoqarin saka masa

"Zansa da kaina ummee"

"Bari na dauko maka lunch box dinka da hijabina saimu wuce,kaima ka kusa makara yau" tayi maganar tana miqewa,dai dai lokacin da aka bankada labulen falon aka shigo.

A nutse ta daga kai ta kalli matar,wadda zasuyi kusan sa'anni da ita,idanma ta girme mata duka duka baifi ta bata shekara daya ba. Ita dinma ita ta kalla suka hada ido,saita dauke kai tana yatsine fuska,ta kuma tattara dukka bacin ran duniya ta azawa fuskarta,ba tare data ko kalli sassan da matar gidan take ba,ta wuce kanta tsaye zuwa kitchen din gidan.

Wani abune yazo ya tsaye mata a wuya,duk da cewa idan da sabo yaci ace ta saba da mummunar hali da dabi'ar ta,amma akance,duk mutumin da yasan daraja da martabar kansa baya iya jurewa cin xarafi daga wajen ko waye,tana da dukka hanyoyin da zata cusguna mata ta hanata jin dadin zaman tarensu,to amma wannan ba shine muradinta ba a halin yanzu,don haka tayi qoqarin share wannan daga ranta,ta wuce kitchen din tana dan bubbuga goyon nata data samu ta lafa da kuka zuwa yanzu.

Tsaiwa tayi turus tana dubanta cikin kitchen din,lunch box din yaron da tazo dauka tuni ta budeshi,ta kuma zazzage duka soyayyen chips da indomie din data dafawa yaron,wanda su kenan sukayi saura cikin gidan nasu,sai yau da take sanya ran samun albashi take tunanin ta biya kasuwa ta taho masa dasu.

Ba yau ne karon farko data fara yi mata irin hakan ba,saidai na yau din yafi na ko yaushe bata mata rai da quntata matuqa,idan a baya tanayin hakan ta qyaleta ta debo wani ta dafa masa,yanzun basu da sauran abinda zata dafa masan,don haka cikin muryarta data cika da bacin rai tace

"Wanne irin abune haka?,bakisan abincin waye bane da kika juye kina ci?" Cikin gadara ta waiwayo,ta watsa mata wani banzan kallo da ya sake tunzurata matuqa

"Ko abincin me gidan ne ina da right din naci qarewa ma kenan,tunda dai yaya na ne ya kawo,guminsa ne,saboda haka banga wanda ya isa ya dinga yimin shamaki ba" wani mummunan bacin rai ya yunquro mata,taji ya tsaye mata a wuya,kamar ma da qyar take zuqar numfashi,har batasan sanda ta isa gareta ba ta tankwabe plate din abincin ya warwatse a qasa ba. Itama abun yazo mata a bazata,don bata taba tanka mata ba,duk da ire iren wadan nan abubuwan da take mata masu yawan gaske.

Da yatsa ta nunata tana kafeta da idanunta da suka canza launi

"Wannan abincin dama saurana binciccikan da kike zuba rashin mutunci da rashin tarbiyya a kansu to ba yayan naki bane ya kawosu ba,gumi na ne ke dashi duka kuke ci,kuma daga rana irin ta yau kinci iya rabonki kenan,duk ranar da kika qara saka hannu kika taba min wani abu dana ajiiye cikin kitchen dina,bama kitchen dina ba gidana ma gaba daya sai nayi maganinki naga uban daya tsaya miki" tuni ta miqe tsaye,gabanta yana faduwa saboda ta tsorata da yadda ta ganta,ta jima tana burin wannan ranar dama

"Ni kika zaga?" A fusace ta daga kai daga kwashe lunch box din yaron ta dubeta

"Muddin wannan shine zagi to na zagekin,kiyi duk abinda kika iya"

"Wallahi wallahi sai na sakaki kinyi nadamar wannan abun da kikayimin,zakiga iya matsiyina a wajen dan uwana"

"Na nawa kuma?,annamimiya?,wadda ta sanadinta na rasa duk wani walwala jin dadi da fahimtar junan dake tsakanina da mijina kuma me yayi saura?,ai ba abinda ya rage sai abu daya......"

"Wannan abu dayan shi zan ida" ta fada idanunta carr a tsaye cikin nata. Haka kawai ta samu kanta da faduwar gaban fitar lafazin daga bakin FAUZIYYA,amma saita gyada kai

"Karki fasa shashasha wofi" kai ta jijjiga da qarfi,sanna tabi takan indomie din da tayi kaca kaca a qasan kitchen din ta fice.

Kasa tsayawa ta tsaftace gurin tayi,sai ta juya kawai ta fice ta saka yaron a gaba zasu fita,har taje tsakar gida ta dawo,ta laluba maqulli ta datse qofar falonta ta wuce da key din,abinda bata taba yiba tsahon zamansu da fauziyyan.

Tun daga cikin gidan harta isa titi,bus ta iso suka hau kwanyarta empty take,babu abinda yake mata kai kawo sai zallar illar da zaman fauziyya cikin gidanta tayi mata,ta jima da sanin cewa FAUZIYYA annoba ce cikin gidanta,tun daga randa ta tsoma qafarta cikin gidanta bayan rasuwar mahaifiyarsu......komai ya fara jagule mata,makira hatsabibiya kuma annoba,wadda ta kwashe dukkan wani walwala da jin dadi gami da fahimtar juna dake tsakaninta da mijinta da sukayi auren soyayya.....tayi amfani da matsananciyar qaunar dake tsakaninsu ta jini daya,uwa daya uba daya,take juya akalar gidan,take kuma juya komai yadda taga dama.

Bata taba damuwa da furucinta ba,amma a yau abinda ta fada din ya tsaye mata a rai,har ta sauke yaran bayan ta siya masa biscuit da drink ta hadashi dashi,ta kuma wuce zuwa nata gurin aikin.

Sukuku ta wuni,har zuwa lokacin tashi aiki yayi. Tana tsaka da tattare kayanta kira ya shigo wayarta,a mamakance ta dakata tana duba number,number makarantar yaronta ne,gabanta ya yanke ya fadi,to me ya faru?,saita koma ta zauna tana rungume yarinyarta a qirji ta amsa wayar.

Tayi mamaki sosai jin cewa har yanzu yaron yana makaranta fa ba'a zo an daukeshi ba,mamaki ya cika kwanyarta,ta sani abbansa baya wasa ko jinkirin zuwa daukarsa,to amma a yau din meye ya faru haka?,sai ta katse tunanin ta soma laluben layinsa.

Sau uku tana kira ana rejecting,zuwa sannan mamakin dake qasan zuciyarta ya gaza boyuwa ya bayyana har saman fuskarta

"Anya kuwa lafiya?" Ta yiwa kanta da kanta wannan tambayar,irin hakan bai taba faruwa ba,don haka ta sake gwada kiran nasa a karo na hudu,amma sai take yankewa kafin ma takai ga shigar,alamun dake nuna anyi blocking dinta,ko akwai qaqqarfar matsalar network,don haka ta katse dukka wasu wasi wasi nata,ta hada komai nata a gurguje a jaka,ta dauki yarinyar ta baro office dinsu.

Tana gab da bakin gate taji ana matsa mata hon,a dan hanzarce ta waiwaya,matashiya ce data kusa shekarunta zaune cikin motarta,suka hada idanu saita sakar mata murmushi yadda fuskar waccar din take shinfide da murmushi,duk da bata shiryawa hakan ba.

Abokiyar aikinta ce kuma qawa a gareta,duk da ita din tana dan jan jiki da qawancensu,ganin cewa akwai tazara me yawa a tsakaninsu cikin gidan auren kowaccensu,amma tsananin kirkinta da kulawar da take bata ba zata iya sanya hannu ta tankwabe ba

"Yauma guduwa zakiyi,to Allah ya kamaki,shigo na saukeki" murmushi ta sake sakar mata,duk da cewa ba'a nutse take ba

"Ayyah,ba haka bane wallahi,yau din ba gida na nufa kai tsaye ba,saina tsaya na dauko yaro a makaranta" harara tadan jefa mata

"Shi din ba yarona bane nima?,ki shigo kawai muje"

"Na gode" ta fada tana zagayawa daya side din,batason zancan ya tsawaita,don hankalinta ba'a jikinta yake ba,gaba daya yana kan yaron. Suna hanya tana janta da hira,saidai gaba daya bata da wanna sukunin,lokaci lokaci tana sake gwada number wayar data kira dazu,amma sam taqi shiga ko sau daya ne.

Da gudu ya taho ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya,farar fuskarnan tasa tayi ja,kwantaccen gashinsa duka ya hargitse,bai taba dogon zaman jira irin haka ba,yana cikin sahun daliban da mahaifansu ke fara daukarsu saboda yadda ya damu da al'amuransa.

Har qofar gida ta ajjiyeta,ta fito rungume da babyn,yaron yana dauke da jakarta,ta zagaya ta bakin window tayi mata godiya sosai

"Wai meye a ciki?,ai mun zama daya" qaramin murmushi ta saki tana juyawa zuwa cikin gidan,cikin Zuciyarta cike da mamakin karamcin matar,da yadda take sonta,yaron yana biye da ita yana mata qorarin yunwa yakeji

"Abinci zan fara dafa muku in sha Allah"ta fada tana jin tausayinsa na tsahon zaman da yasha,gashi bai samu tafiya da abinci ba,tasan dole kuwa yasha yunwa.

Zaune yake a tsakar gidan saman kujerar plastic daga dai dai bakin qofar falon,shi din ta fara gani,sai a sannan ta tuna cewa ta kulle falon,bata bar masa key din baa,kuma koda wanne lokaci yana iya dawowa tunda bashi da tartibin lokacin fita ko dawowa,tun bayan da ibtila'i ya fada masa.

"Subhanallah" ta fada a ranta,sai tayi sallama a nutse tana sake qoqarin karantar yanayinsa,kai ya cira a hankali ya sauke kallonsa a kanta.

Mummunar faduwa gabanta yayi,wani irin hargitsatsen kallo daya watsa mata shi ya sanyata cikin rudani,batasan me tayi masa banda kulle qofa da tafiya da key din,kallon daya watsa mata yafi qarfin wannan laifin,kallo ne na zallar qasqanci da kuma tsana,tasan dai ranar yau lafiya qalau suka rabu,ya fita cike da murna zai karbo upper dinsa aiki ya samu,suna ta murna dukkansu tare da saka ran

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment