Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*'YAR kwalliya* β€πŸ’‹



WhatsApp numberπŸ“± 07036891952




πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 
πŸ’„πŸ’… *HEEDAYA* πŸ’…πŸ’„
*(l KIRARI)*
πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 








Written by *husba'ahfama*


*Instagram @officiall_husba'ahfama*
Facebook *Real husba'ahfama*





Follow me on wattpad *@Real husba'ahfama*






30-35

"eh mana dake a Banza kike tinani ze hado kaya irin wannan

Yasmeen ta tafi tinani shaheeda ta dafata

"Yasmeen ba lokacin tinani bane yanzu aikin gama yariga ya gama kiyi musu fatan alkhairi nizan shiga daki kaina yadauke na shiga duhu Bari nadan kurba idanna hau online zanfi kawo wuta

Ta mike ta shiga daki Yasmeen ta bita da kallo hajiya naja'atu na shiga ta fara masifa ta inda take shiga ba tanan take fita ba Alhaji Ibrahim gadara yana zaune yana binta da kallo da kanta ta gaji ta zauna Kasa tayi da murya tana tambayar shi

Alhaji Bazaka kula niba da kai nake fa

murmusawa Yayi "nasani

"Alhaji kayan daka kawo na meye shikawai nakeso nasani

"kayan dai Na fadar kishiya ne gaba daya nakine Na amarya kuma ankai gidan su jibi zata tare

hajiya naja'atu tamike tsaye tacire dan kwalinta ta jefar bakinta se motsi yake alamun tanada abin cewa

Gaskiya ba a kyauta minba arasa lokacin da za amin kishiya se wannan lokacin haba Alhaji kayiwa Allah ka fasa auren nan kadubi Manya 'ya'yan da muka tara Alhaji

"ba yanda zanyi naja'atu nikaina banida niyar kara aure dana dawo segashi Allah ya hadani da ita Ashe matarda zan aura ce kiyi hakuri kuzauna lpy naja'atu kece babba

ya isa babu wani sauran mutunci tsaka nina dakai tin da har kasan kanemi aure bada izininaba harta kusa Tarawa ban saniba kamuna furceni Alhaji Allah ze saka min insha Allah ita kuma matsiya ciyar da zaka auro ka sanar mata cewa takawo kanta inda zata mutu harlahira dan gidana kabarini ga duk wacca ta shigo da sunan kishiya

"fada kikeyi naja'atu bazaki iyaba da kunya tsaka ninku baki tambayeni waceceba

"kai ka sani wannan kaita shafa nidai inaso ka sani bakai ba zaman lpy a gidan nan har abada

murmusawa yayi "naja'atu kishine irin naku na mata ya motsa nasani toni bari na fada miki a bagas Kareemace yar gidan hauwa'u

kim kakeji hajiya naja'atu ta zube kasa bata numfashi Alhaji ya tebo ruwa ya zuba mata tai hajiyar zuciya

"wlh Alhaji se Allah ya gaggauta saka min kacuceni ka Gama dani yar Kawar tawa Zaka auro dan cin fuska harka zauna Kana fada min daga kai har ita na shirya muku Allah ya kawo ta lpy

"Ameen

"Au hakama zakace

kai ba dankwali tayi waje duk ta fita haiyacinta waya ta dauko ta shiga kiran hajiya saude harya katse bata dauka ba seda ta sake kira sannan ta daga

"Assalama'alaikum hajiya y kike

"Wa'alaikumus salam hajiya saude ba lpy gida ya hargitse zata shigo zekawo ta wlh yauya gaya min

"karki tada hankalinki hajiya naja'atu kimai da komai ba komai ba kinji zan shigo gidan se mu bazama duk abin da suke takama dashi nima na fisu

"niko abinci bazan iya ciba dan tashin hankali kira wanda mukaje gurinshi ki tambaye shi wana aiki Yayi

to jirani bari na kira shi naji
Ta kashe wayar bayan wasu yan mintuna hajiya saude ta sake kira naja'atu ta daga Cikin kaguwa naja'atu

tace meyace miki

"eh to cewa yayi ya maida shi ruwan sanyi se yanda kikayi dashi

"kai rowan sanyi kuma nina shiga uku dawannan ruwan sanyi dashi wanda yayi aikin Allah Ya

kul-kul karki fara taya kina nema a gurinsu zaki la ancesu ki iya bakinki ta haka kike so kisamu nasara kinga bazaki gane aikin da amfanin hakaba se a gaba ki huta sena zo

" to Allah ya kawo ki

duk wayanda sukeyi Yasmeen na jinta kusa da ita ta zauna

"Yasmeen Alhaji ze kara aure

"nagani

"shine baki damu ba

"eh bazan da muba Saboda aure sunnar annabi Muhammad (S.A.W)

kanta kai aya hajiya naja'atu ta rufeta da duka

"ja ira base kinyi haka zansan kina farin ciki da haka ba bakinku daya waya sani kuke kika zaba mai ita

kamar daga sama shaheeda take jiyo shashekar kuka dukda a bige take haka ta taso tana hada hanya tana fitowa taga hajiya naja'atu ta daga hannu zata daki Yasmeen ta rike hannun tana layi cikin muryar maye

tace karki fara wlh kina tabata ina rama mata meta miki mutum kamar Yasmeen zaki daka ki shiga hankalinki

a tsaye take amma ta kasa tsayuwa se layi shaheeda takeyi

Me zan gani haka shaheeda wannan wana irin mafarkine kinga jeki kwanta ba a mafarki a tsaye se a kwance kina magagin bacci kika fito jeki kwanta

"Niba bacci nake jiba ras nake karkiji dawai ina shiga naji kukan ta wlh zan fito kuma zakiji ba dadi Yasmeen ki dena kuka dena mana kidena nace ko

kai Yasmeen ta iya daga wa

"meyasa kika daketa na fasa hakura rama mata zanyi tinda taki yin shiru fada min

"Nidai na kasa gaskata a duniyar da nake yau kodai ninake mafarki ba ita ba shaheeda gaba daya kin canza ki kula karki fado min aka

"ras nake na fada miki metayi

"Kishiya za a min amma makirar yarin yar nan na farin ciki da haka ita daya dace ta tayani kishi

"shine kika daketa me kikeso tayi kuka hakan zesa a fasa auren to wlh kinci bashi yanzu zaki biya dan zaneki zanyi a gidan nan tinda ke bakisan raya sunna bane aure

zare ido hajiya naja'atu tayi shaheeda ta daga hannu zata kai mata hajiya ta kauce shaheeda ta bita tanaso ta daka

"hajiya hutu shine kizo na rama mata tanan dai zaki wuce ko to wuce na gani Yasmeen temakamin da madoki nan kusa koki bani faran tin can juye abinciki

"Idan kika sake kika bata Yasmeen idan na kamaki sena karya miki kafa da hannu

"Au to shikenan shawara me kyau zan karya miki abinda kika fada

"Yasmeen ki hanata mana ki bata hakuri

Mommy ya kamata kisan matar da kika zabawa danki lokaci yayi Yasmeen ta fada a hankali ta yanda ba wanda zeji

"Nakula ba bani zakiyi ba Yasmeen

shaheeda ta dauki farantin da kanta ta dinga jifan hajiya besa metaba ta koma daukar duk abinda ta samu kofin data jefo segashi a goshin ta se jini hajiya ta gigice tafara neman hanyar da zata fita da kyar hajiya tasamu ta bar folon bayan tasha wuya a hanun shaheeda dakinda Alhaji yake nanta shiga ta doko kofa a kasa ta zauna jikin kofar tana maida numfashi gano Alhaji Ibrahim gadara tayi yana ta sharar bacci harda munshari

"kayi bacci mana bayan ni ka tada min hankali oohni naja'atu meke faruwa dani yau nice nasha da kyar a gorin shaheeda Tab

A bangare guda kuma Najib ne a hakimce a Kofar gidansu heedaya ya kasa ya tsare setura yara yake akan tazo amma taki zuwa se da mami ta gaji ta tirsasa ta taje taji a binda yasa yeke nemanta badan taso ba ta tashi zata fita a bangare daya kuma bakin umma da lubabatu yaki rufuwa ganin irin kayanda Alhaji Ibrahim gadara ya kawo wa Kareema seda lubabatu ta dai daici fitowar heedaya seta daga labile

tace su oo ko boka Za a bi baza a hado mata irin kayan nanba Saboda tsabar bakin jini irin nasu wanda aka gada kaka da kakanni bakinciki yahana a zo a gani nan aka baje kayan a tsakar gida kan ashigo dashi ciki bakeyar wanda muka gani ba uwaba ba yarba Allah Ya kyauta boka be bada iziniba koda kunzo daga baya bazaku Ganiba dan bamusan dame aka zoba ehhhe

heedaya tayi murmushi ta fita cak ta taya a gabanshi taki cewa komai a gogo ta same shi yana sawa sewani goge shi yake daga shi har agogo taimusu kallon sama da kasa ta zubar

"Baki ga agogo naba kyauta aka kawo min kena fara sawa danki gani idan kin gani daga yau har kullun idan zanzo wajanki shizan dinga sawa

yafada yana nuna mata a gogon jin batace komai ba ya cigaba da

cewa heedaya Dan Allah ki tausaya min kigane inda na dosa qaunarki zemin lahani

"Wa'alaikumus salam

"Yi hakuri kingani ko namanta Banyi salamaba duk a dalilin qaunarki heedaya karki sani cikin wani hali Assalama'alaikum

"hmm iska na wahalar dame kayan kara wannan wana irin nacine kake dashi haka Najib bakai kake *I KIRARI* zaka sace niba idan ban sokaba ka bude kunnanka kaji da kyau Najib bana sanka bansan me Sanka bazan taba sankaba

Jingina Yayi a jikin motar a gogon dabe karasa sawaba kenan jiyayi kamar anrabashi da wani abu a jikin shi kasa ce mata komai yayi yana kallonta ta koma gida tashi yayi jiki ba kwari ya bude mota a gogon hannun shi ya fadi besan ma ya fadi kasa ba yashiga ya yaja mota ya tafi a guje ya debi motar

Umma na kallon dawo War heedaya tayi dariya ta dawo ta zauna kan kujera ta kalli Kareema

"jeki dora mana ruwan girki muyiwa bakin da zasu zo dan Kinsan anjima gidannan cika zeyi

to umma Kareema

ta tashi ta fita tana fita umma ta kira lubabatu

"lubabatu zokiji

lubabatu ta zauna kusa da ita

"Wani Shiri nayi zuba ido ki gani

"Umma dadai zaki fada min dana so

"kawo kunnenki ke ai ta gurinace

Tana gama fada mata

lubabatu tace kinyi dai dai Allah y kara ba sira umma amma ita Kareema ta sani

"ban fada mata ba Saboda batamana shiri zatayi

"ehhto hakane kuma bari musha kallo

Kareema na tsugunne tana wanke tukunya ta kuna fanfo zata zuba ruwa taji an danki rigarta ta baya an janyo
ta seda rigar tayi karar yagewa dasauri ta juya zaki ta gani ta zare ido

"hahhh kada kiyi mamaki baby wannan sumin tabine kafin ranar ya fisge zanin Kareema tasa ihu jan kayan Jikinta yake da karfin gaske yana niya Danne ta Kareema ihu take da karfin gaske mami da heedaya ne suka fito da gudu abinda suka ganine yasa mami yin salati Kareema hannu take mikowa mami ta temake mata mami taje ta tureshi amma ina hankadata yayi tafadi kasa heedaya ta dauki ice tana buga mishi itama hadata yayi da bango mami ta mike kuma ta janye Kareema yakara hankadata umma taga abin yana Nema ya wuce gona da iri yasa ta fito tana kokarin kwatar 'yarta itama da taje marinta yayi ya watsata gefe lubabatu ta dinga dukanshi gashin kanta ya kama ya hadata da bango

a kunnen Kareema yake fada mata danginki sunsa ni jin yunwa naki yau zan anshi hakkina a gurinki bazan hanuba da mahaifiyarki tasan abinda ke taska nina dake bazata kawo aikin nan guri naba Kareema ta kara saka ihu yarufe mata baki

"shiru bana san ihu inba hakaba sena ninka hukunci kina ihune saboda zakiyi aure jibi baki fada mishi kinadaniba eh ya kara fusgar rigarta gaba dayan su suka hadu kan shi suna duka amma yaki sakin Kareema idan shi yarufe niyar aikata abinda ya kawo shi yakeyi Allah ya shigo da mazan gidan gaba daya abinda malam nazifi ya gani yasa shi mutuwar tsaye Mansir, Ali da Adam susuka rufeshi da duka baji ba gani shima yana ramawa Kareema taja jikin ta daya gaggun kayanta kamar ta fito daga bakin kura lubabatu ta dauko hijabi ta sa mata Kareema kuka kawai ta keyi Allah ya bawa su mansir nasara a kan zaki sukai mishi jina-jina komotsi baya yi sai dai yana numfashi a lamar yanada rai

Adam ya dan koshi Cikin bacinrai da tsawa yake Tan bayanshi "waya aiko ka me kazo yi anan

Yaki bashi amsa adam yasake dukan shi dan kanshi ya daga mishi hannu
Adam yasunkuya ya sake maimaita tambayar daya masa

zaki ya kalli umma umma ta boye bayan lubabatu saitin da umma take ya nuna sedai tuni umma tabar gurin heedaya ce a kusa da ita sai ya zamana heedaya yake nunawa kowa ya maida kallon shi gareta

"zaki yace ita ta aikoni gurinta nazo daban same taba sena samu dayar

"karya kakeyi adam yasake rufeshi da duka

"Adam karka karyatashi bakasan komai ba nina sani malam nazifi ya kalli heedaya

Abba wlh ban san shiba nibani na aiko shi ba meyasa zan tsaya idan nina aiko shi cewar heedaya

"kodan ki wanke kanki zaki Tsaya mana wannan tabbacine nace bayan tafiyar Kareema gidan nan zezama sansanin maza kukanku baku wuce abinda ya samu Kareema ba hankalinku ze kwantane kadai idan heedaya tabar Gidan cewar lubabatu

Ya isa lubabatu tsaya a ma tsayinki karkisa baki a binda ba rowan ki wanna maganar muce besha fekiba cewar mansir

"yasha feta tinda kawar tace dole abin ya mata zafi kufita dashi kukuma saurari hukuncina cewar malam nazifi

Kama zaki sukayi suka fita dashi yan sanda suka gani a kofar gidan su yasa suka danka zaki hannunsu tareda sanar dasu abinda yayi umma naso ta hana seta kasa magana dan kar su tuhumeta kwari da yaran zakine cikin shiga irin na yan sanda sai sunkuyar dakai suke ta yanda ba zasu gane suba zare ido kwari Yayi

"zaki kaine haka garin yayi Ka bari haka ya faru haba kamar ba kaiba

wani yaron zakine yace mu gaggauta daukeshi daga nan kansu baro mu a mota suka sashi suka bar Gurin

Kowa yaji auren da za a daura jiba harda heedaya nida kaina zan zaba miki miji kuma duk wanda yayi yunkurin hanani zanbata mishirai Matuka wannan ba shine na farko ba heedaya kekin sani ko Hafsat kufara shirye-shiryen biki cewar malam nazifi

yana gama fada yabar wajan umma da lubabatu suka kama Kareema suka shiga da ita

heedaya ta fashe da kuka da kyar Adam ya rarrasheta ta hakura ta shiga daki suna zaune a falo sunyi jugum-jugum sautin kukan heedaya ne kadai yake tashi a gurin

Ali yace mami meyasa abba ya yarda kuma naji yace ba shine na farko ba

"eh bashine kazafi na farkoba wanda aka yiwa heedaya kiyi hakuri ki auri wanda abbanki ya zaba miki Allah yasa shine mafi alkhairi a gareki

Adam yace heedaya kiyi hakuri mana kinji kiyi shiru ba abin da hakan ze canza mana

mami tace mansir bayan tafiyarka Abuja abubuwa da yawa Sun faru a kwai Allah

Cikin muryar kuka heedaya take magana "Kowa yaji bazan taba auran wanda abba ya Zaba minba *guduwa* zanyi nabar gidan bayan komai ya lafa zan dawo ya zanyi da karatuna idan nayi aure seda aski yazo gaban goshi za a katseni a'a baze yiyuba *guduwa* zanyi *guduwa* zanyi

Mansir yace heedaya kidawo cikin hanka linki karki kara futa kalmar guduwa kina jiko

yaya mansir babu abinda ze hanani *guduwa* daga gidan nan kamar na barta na gama ni za a yiwa auren dole kayi hakuri

Adam ne ya zare ido ya mike tsaye Ali ma zare ido yayi yamike haka mami da mansir heedaya na juyawa ya dauketa da mari ya kuma dauketa ta wani takara fashewa da kuka

"ki gudu karki fasa na godewa Allah dayasa naji wanna *I KIRARI* naki a kunnena idan kin gudu karki dawo min gida na salla maki baki a cikin yarana bani da heedaya zan dauka cewa heedaya ta mutu har a bada bazata dawo ba malam nazifi na Gama fada ya fita daga dakin

"Umma kinji abinda abba yace

Dauketa itama tayi da mari takuma sakar mata wani

"Nima haka nace kiji da kyau nidai ba wannan tarbiyar nayi mikiba a gabanmu a kunnen mahaifinki kike *I KIRARI* guduwa Allah ya baki sa a ki jeki tambaya kiji duk wanda ya gudu saboda auren wana hali yake fadawa waya gaya miki dadi sukeji kidaiji abinda mahaifinki yace ko to masha Allah

Tana Gama fada ta shiga daki mansir ya dinga mata fada


"umma gaskiya zaki mahaukacine haka akeyi daga sashi aiki seya wuce gona da iri cewa lubabatu

"kibari kawai lubabatu abin ya bata min rai sannu Kareema

"menakejine haka umma kekika aiko shi ya keta min mutun cina a gabanki

"Rufemin baki kinsan dalilina na yin haka kuma ki rufe bakinki karki bari wani ya sani

kwari kai tsaye asibiti suka wuce da zaki aka dubashi harda mishi karin ruwa suna zaune a gaban shi sai jin-jina dukan da aka mishi sukeyi tinda aka mishi allura ya samu bacci be bude ido ba ga jiya sukayi da zama

kwari yace nifa tashin shi zanyi na gaji da zama gashi ba wani dan abu da mutum zesha kanshi ya dawo dai dai

yashiga tashin zaki yana bude ido

yace yauwa bayan uban dukan da kaci mun godewa Allah da yasa Kana raye tashi mu tafi nizan rike rowan muna tafiya harya kare

"Bazan iya tafiya ba kwari ka Bari na danji normal zuwa anjima se mu tafi

"Bazan iya jira bane zaki bazan iya ba

"Kaden kara hakuri

"To naji

Agogo ya gani a hannun zaki yanata sheki hannun ya rike yana karewa agogon kallo

"Zaki a ina ka samo wannan

"a kofar gidan su heedaya na samu

"yayi kyau sosai ma kuwa muna barin nan zamu kaiwa dillaliya ta siya ta bamu kudinmu

"bazan siyar ba ina san abuna sannan ka sanar da yaran ka gobe zasu min wani aikin sirri

"ba Matsala indai wannan ne nidai kawai ka amince a siyar mu dafe abinda zamu dafe

"Karka kara min maganar sayar da agogon nan bazan tsiyar ba na fada maka ko

"Shi kenan toh nayi shiru

Tin ranar da aka kawo kayan fatar kishiya takuma jiwace kishiyarta Bacci ya gagari hajiya naja'atu duk ta tada hankalinta a kunnen ta akaikiran sallar asiba har Wayanda zasu gyara dakin Amarya sukazo namma hankalinta ya Dada tashi takasa zaune ta kasa tsaye sai kiran hajiya saude take a waya amma taki dagawa zama tayi ta zuba uban ta gumi hannun taji an Tan kwabe daga kai tayi taga waye hajiya saude ta gani zama tayi kusa da ita

"haba hajiya naja'atu meye haka karki bada mata mana wannan dan abinne ya daga miki hankali

"ya bazan daga hankalina ba abuya kankama dakinfa ake gyarawa yanzu haka shine bazan daga hankalina ba

"ehto da wannan kuma nidai abinda zan fada miki shine kizuba ido kiga dame tazo nikuma zan miki sauran aiki ga wannan

kullin magani ta mika mata ta ansa

Shikuma hayakine kece zakiyi wannan kuma rubu tune sau biyu akeso kisha harya kare wannan kuma kwalline a idanki zaki sa indai kikayi wannan karyane ta mulkaki wlh sedai ki mulkata dagidan gaba daya

"yauwa harnaji dadi hajiya saude na gode sosai Allah yabar zumunci

"Ameen nizan koma dan akwai inda zanje miki yanzu haka au harna manta ga wannan shikuma na Alhaji ne abinci da wanda zesha zakisa mishi zaki sha mamaki

"to zanyi insha Allah bari na kira miki shaheeda

"a'a ki barta mungaisa da zan shigo wannan zuwan nakine ba nata ba

"OK muje na rakaki tai mata rakiya ta koma gida

Gidan su heedaya cike yake da mutane sai aiki ake tayi fuskokin su fal farin ciki banda na heedaya daketa aikin kuka fuskarta ta kumbura idonta yayi ja Kareema ce ta leko

tace heedaya zomuje anso dinki abba ne yace muje tare mu dawo tare

zatayi magana mami ta gargadeta

"tashi ki bita

"toh inazuwa kije waje yanzu zanzo

heedaya ta shirya tsaf zata tafi

"mami zan tafi

"sekin dawo amma ki dena kukan kinji

"hartasa kafa waje ta kara juyowa ta kalli mami tana hawaye jikin mami ya mutu tarasa dalilin haka dagudu heedaya ta dawo ta rungume ta tana kuka mami ma kukan takeyi

"heedaya kodai fasa zuwa zakiyi asa wani ya anso miki

"a'a mami zanje da kaina hannayen mami tarike duka 2 ta sunkuya kasa mami kisani duk inda zani a duk inda nake bazan taba canza wa daga heedaya da kika sanni ba kiya femin abisa *I KIRARI* da nayi jiya mami bazan karaba ki yafeni mami kiyafemin kirokar min abba kice ya yafeni natuba na yarda zanyi biyayya takarasa maganarta da kuka

Dagata Mami Tayi "heedaya na yafemiki kuma abban Kuma ze yafe miki Allah y miki albarka

"Ameen Zantafi mami

"se kin dawo heedaya

Jiki a Mace heedaya take tafiya ta waigo ta kalli mami sekuma ta juya kai tana kuma

"Tsaya heedaya bari na rakaki waje

umma ta rike mata hannu tayi mata rakiya har jikin adai-daita sahun da zasu hau heedaya ta rungumeta tana kuka

"heedaya idan kina min haka jikina mutuwa yakeyi Allah y dawo dake lpy

"Ameen nagode mami ina kaunarku kuma kuna cikin raina kuyafemin

umma tasa heedaya A adai-dai sahu sekun dawo yaja suka tafi mami na komawa gida a daki ta zauna tana kuka da batasan dalilin yiba motar su heedaya na tafiya wani mota na binsu a baya a tare suka shiga gurin dinkin motar dake binsu ya parking fuskokin su a rufe da bakin abu matukin motar

yace gasu nan zan nuna muku ita kukamo ta

dinkin suka anso suka fito wayar Kareema ne ya shiga Kara ta daga bayan tayi sallama

"to ina zuwa heedaya ki hau wata motar ki koma gida lubabatu ce ta kirani nizan tafi

Harzata shiga mota ta dawo ta riketa "heedaya ki kula da kanki

kai kawai ta daga mata ba tare da tace komai ba

Matukin motar yace gata can ya nuna Kareema suka bude suka fito kansuzo tuni ta hau mota ta tafi se heedaya suka rufe mata baki da kyalle suka daukota suka sa a mota suka tafi wani gida suka kaita ba kowa a ciki duk tarkace ne a dakin suka daureta jikin kujera suka kulle mata baki kafa da hannu suka barta a ciki ita kadai suka tafi Sai da yamma Kareema ta koma gida mami na ganinta ta tambayeta ina heedaya

"bata dawo bane mun rabu akan ta tari mota ta dawo gida zanje kiranda lubabatu take min

"waiyoo Allah shikenan Kareema ina kika kai heedaya meyasa baki sata a mota ba kafin ki tafi

Umma ce tataso rai a hade "heedaya yarin yace da har za awani sata a mota ta dawo gida tatafi yawon bariki kirubuta ki ajiye

Mansir na jinsu"lpy meyake faruwa a nanne

"mansir heedaya bata dawoba tin dazu da suka fita da Kareema

"ke Kareema ina kika Kai heedaya kifadi gaskiya tin muna kallon juna da mutunci

"yaya mansir inako zankai heedaya duk da abinda ke tsaka nina da ita bazan iya cutar da ita ba wlh

"ina kukaje

"anso dinki

"Su Adam na waje zandau kesu muje gurin tarekuma zamu duba duk inda mukasan tana zuwa Abba ya sani

Mami ta girgiza kai tana kuka

Mansir ya fita ya sanar da su abinda yake faru hankalin su ya tashi Sosai malam nazifi ya bazama neman heedaya sukuma gurin dinkin sukaje akace bata nan sukaje makarantar su nanma aka sheda musu bata nan basu suka dawo ba se karfe 10 nadare a tsakar gida suka Tsaya suna jiran dawo warsu mami na ganinsu

tace mansir an dace

mansar yayi shiru Adam yace munduba duk inda mukasan tana zuwa bata can kuma har yanzu bata dawo gida ba ina taje haka

*I KIRARIn* da heedaya tayine ya dawo WA malam nazifi "Kin gudun kenan ko heedaya da kyau ya fada a hankali saikuma ya daga murya yace ku saurareni kuji bazata dawo ba kowa yaje ya kwanta heedaya tayi *I KIRARIn* guduwa kuma tagudu inaso kowannanku ya sani ni malam nazifi bani da 'ya *HEEDAYA* ta mutu kowa ya sani yafa yana karasa maganar da tari yana rike kirji

*I KIRARIn* da tayine ya dawowa kowannan su Adam ya dafe kai Ali yarike baki mansir kasa magana yayi mami ta kara fashewa da kuka umma baki har keya Kareema jiki a Mace tarasa abinda zata ce ta gigice damuwa karara a fuskarta

"Allah ya kyauta yanzu wana mataki auren nasu yake ciki cewar umma

"za a daura auren Kareema a ranar zata tare kowa yaje ya kwanta daga yau karwanda yasake tada maganar nan a binne ta anan duk wanda ya karya min doka zegamu da fishina cewar malam nazifi

haka kowa ya tafi makwancin shi jiki a mace banda umma dake ji kamar ta zuba ruwa a kasa tasha malam nazifi na zaune a daki

Please Login or Register in order to submit comment