Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kama sukayi waje suna fita megadi na budewa hajiya saude get tana shigowa da mota

" wanake gani kamar Yasmeen

"ba kamar bane itace

Ohh nanma biyoni tayi yarinyar nan tasamin ido fiye da yanda bakya zato yi parking din motar naji dame tazo

hajiya saude ta parking motar hajiya naja'atu ta fita tana kiran sunan Yasmeen Yasmeen ta jegurinta da gudu tarungumeta

"mommy nayi missing dinki ina kwana

"lpy klau biyoni kikayi kenan

" bazan iya jure rashinkiba mommy muje gida ko

"eh muje shaheeda meyake damunki idanki yayi ja jikinki na rawa gashi kamar kina jin sanyi

shaheeda tafara in'ina tarasa abin da zata ce

Yasmeen tace batada lpy kantane yake ciwo amma tasha magani

"Allah ya kara sauki mu zamu tafi hajiya saude sena jiki

"to bari nasa a kaiki iro iro

"na'am hajiya da gudu yazo

"gashi mukullin mota ka maida su gida

iro yace to hajiya hajiya shaheeda tin dazu nake nenanki gashi inji kwaro wai a baki kuma yana jiran kudin shi

ya mika mata leda shake da kwalaben magani Yasmeen tabi ledar da kallo sai da tagano meye a ciki sannan ta dauke kai kamar bata ganiba shaheeda tasa hannu ta ansa

" to naji zamuyi waya dashi

Mommy muje ko shaheeda muntafi

Toh Yasmeen ina jiranki kinsanke zaki min babbar kwa

"nasani karki damu zaki ganni


Suka shiga mota suka tafi suna tafe a hanya Yasmeen ta dora kanta akan mahaifiyar ta

"mommy hakika ni yarin yace nayi laifi kiyafe min bansan dalilin hada auren yaya Najib da shaheeda ba saidai yanzu na gane Sun dace da juna

hajiya naja'atu tadan murmusa "nina sani nasan wata rana zaki gane abin da nake gani babu wacca ta dace da Najib se shaheeda yarinya irin arziki

Yasmeen tayi dariyar keta har iro ya saukeso a gida ya Koma hajiya naja'atu bata dena bada lbrin shaheeda ba

Agefe daya kuma Alhaji Ibrahim gadara ne ya hakimce a kofar gidan su Kareema ya tura yaro ya Kira mishi Kareema tana Jin kiran tasan shine sai da ta tirara jinkinta da hayakin Data saba sannan ta fito tana tafiya dai-dai harya isa wajan shi

"Alhaji inawuni

"lpy klau y kike ya yan gidan

"lpy klau y aiki

"to Alhamdulillah zance ina Baba yake

"yana ciki

"zanso ace na fara magana dashi tukunna

"Ba komai bari na maka Sallama dashin

tanayi tana rufe fuska

tashiga gida ta mishi sallama dashi malam nazifi yasa ta shinfida tabarma data Gama ta shiga gida shikuma ya fito sukayi musa biha malam nazifi yace su zauna bayan Sun gama gaisawa Alhaji Ibrahim gadara ya sanar dashi abinda ya kawo shi malam nazifi yayi shiru nawasu yan mintuna sai kuma

yace to Allah yasa haka shiyafi alkhairi nidai bazance komai yanzuba harse naji daga bakinta idan tana sanka shikenan ai ba abinda ze gagara

umma da Kareema na labe suna jinsu dadi kamar ya kashe su jin amsar da ya bayar murya kasa-kasa umma

tace Kareema kinada mugun sa'a wlh daya gadama hanawa zeyi zece wannan cin amanar bada shiba badan karyace kinyi rashin kunyaba dasenace kije kice Kin amince

Kareema tayi murmushi

"Zomukoma ciki munji me mahimmanci ai

haka suka koma ciki malam nazifi da Alhaji sukayi sallama ya dawo ciki ya tura mishi Kareema

suka sha hira abinsu sannan sukayi Sallama ya bata kudi ya shiga mota ya tafi tana shigowa taci karo da umma a bakin kofa

Kareema ta zare ido umma me kikeyi a nan labe kanta karasa

umma ta rufemata baki tana mata magana kasa-kasa"ke abu na shirya banaso ya ritsa dake shiyasa nake leke idan mun hada ido nace ki dawo gida zomuje ki zuba ido Kiga abinda na shirya

Kareema bata yarda kwata-kwata gani take Umma ta fadane dan kartace takamata tana musu labe

Motar data saba kowa heedaya na zuwa umma tayi dariya "yanzu za a fara heedaya

Kareema takalleta kawai a zuciyarta tace borin kunya

kansu ankara kareema taji karar wukake kamar ana fada a waje anata zage zage suna niyar jiwa juna ciwo Kareema tayi waje da gudu umma taki fita tayi zamanta a daki malam nazifi da mami sukabi bayan Kareema

Kareema na fita aka kusa sara mata adda bashiri ta dawo gida heedaya na tsakiyar su malam nazifi ya bi ya rude Kareema

tace abba heedaya na waje tana waje

Umma daga daki ranta ya baci ganin yanda Kareema take kiran sunan heedaya

malam nazifi yasa waya ya kira yan sanda suka shedamai cewa gasunan zuwa

lokacin kofar ya kara zama sansani yan dabane kungiya-kungiya suke zuwa fada na Dada baci sunata jiwa junan su ciwo





























New writer's

Hakan Take
*husba'ahfama* 😍❀🀩
*'YAR kwalliya* β€πŸ’‹


WhatsApp number πŸ“± 07036891952




πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 
πŸ’„πŸ’… *HEEDAYA* πŸ’…πŸ’„
*(I KIRARI)*
πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 






Writing by *husba'ahfama*




Instagram *@officiall_ husba'ahfama*
Facebook *Real husba'ahfama*







21-23

Baajimaba yan sanda suka zo alokacin sun Gama jiwa junan su ciwo harda wayanda basu jiba basu ganiba akahada sai da yan sanda sukayi da gaske sannan suka raba suka kada kansu zuwa police station suka bukaci malam Nazifi ya biyo su kasa hakura su mami da Kareema sukayi suka dage sesunje malam nazifi badan yaso ba yace su taho harda heedaya aka wuce police station sai zubar jini wayanda sukai fadan sukeyi

DPO na Zaune yana binsu da kallo daya bayan daya yasa kowa ya fadi sunan shi da inda yake da zama bayan Sun gama fada ya gyara zama ya kalli zaki dake ta motsa baki da alama gun-guni yakeyi

Dpo yace Ali meya haddasa fadan da kukayi gashi duk kunjiwa junan ku ciwo

Zaki yace oga abin dai ba a cewa komai kwari da yaransa Sun hana karena sakat basu isa suzo kiwo wajan da sukeba sesu bisu da duka a haka suka kashe the boy yau kwana 3 kenan dama inada burin daukar fansa dan nayi I KIRARI nan yau ina zaune shine yaro na yace min ba lpy gari ya hargishe inzo muje kwari da kanshi ne yake neman budurwar shi muna zuwa muka samesu a kofar gidan muka afka musu abinda ya faru Kenan dama da jikakkiya

"idan na fuskanta fadan yafarane saboda kare naji kace the boy shikuma waye shi yaron naka wana irin halakane tsaka ninshi da budurwar ambashi itane ko ba a bashiba

"The boy shine sunan karen da suka kashe min ga yaron nawa shine ze iya amsa wannan tambayar Mage kayi bayani

Mage ya kalli Dpo yace ba a bani ita ba bakuma auranta zanyi ba mun hadune a bariki acan muke sheke aya da ita munyi akan zanzo na dauketa har gida mu tafi se ga kwari na dade da samun lbr cewa yana cusa kanshi gurinta harta amince mishi su hadu nibana san cin amana heedaya tawace ni Kadai Bani na kawota bariki ba amma Tare zamu fita bana kula kowace mace saboda ita tana min duk wani abu daze dauke min hankali daga kallon wata Mace ninasan dadinta ta san nawa

heedaya ta zare ido Jikinta yadau zafi lokaci daya kafarta ya fara rawa malam Nazifi ya rintse ido dajin abinda mage yake fada idan shi yayi ja Kareema ta gigece dajin tuggun umma mami tayi mutuwar tsaye

muryar heedaya na rawa tace kaji tsoran Allah Mage kasanni ka taba ganina in banda yau kaji tsoran Allah ka tina Zaka mutu ka tarar da Allah mutuwa gaskiya ne

rai a bace malam nazifi ya daka mata tsawar da ya gigi tata tabbas yau ransa yayi matukar baci fiye da misali "kiyi shiru bansan jin komai daga bakinki heedaya ko Kalama daya karki furta harmu barnan kinji na fada miki

heedaya ta fashe da kuka me tsuma zuciya

Mage ya mike tsaye "heedaya karkimin haka karki bari kwari ya shiga tsaka nina dake idan kudinki da ban bakijiya bane yasa kikace baki sanniba zan baki indan muka jame a daki karki damu har kari zan miki

Dpo ya daka mishi tsawa "kayi shiru wannan tsaka ninkune inkun hadu a duk inda zaku hadu kwayi magana kwari

"na'am oga

kaji abimda Ali zaki da idris wanda kukafi sani da Mage ya fada mezakace akan haka

"Karyane kawai oga heedaya tawace ni kadai heedaya tasice kowa kwasarta yake ita tasan da haka meye dan yana binta nima nabi sahu abinda yake nema nima shinaje nema tomeye abariki ba a kishi kanka santa wani ya santa batun Kare kuma bamu muka kashe shiba yan adawane gawar karan muka gani a kangon da muke zama

Dpo yayi shiru yana nazarin maganar su"zaki dakai da kwari yadace ku hada kanku kare meye kare da zaku hada fada a kofar gidan mutane saboda kare da budurwa zamu hada wayanda kuka jiwa ciwo basu jiba basu ganiba mukai asibiti kudin da ake bukata zaku biya idan suka dawo zamu yanke muku hukunci dai-dai da abinda kuka aikata daga yanzu har mukaisu asibiti mudawo zaku shiga sel copra

"Yes sir

"sasu a sel gaba dayansu wayannan masu zubar jini kuma kuwuce asi biti dasu malam nazifi kanada abincewa

yana duniyar tinani bemasan ana magana da shiba sai da yasa aka taboshi azabire yace na'am

Dpo yace magana nake nace kanada abincewa

"eh niko keda abincewa ka shiga tsaka ninsu da Gidana da 'yata basu ba 'yata da kofar gidanama karsu kara zuwa indan kazafi kukaiwa 'yata kuje kuda Allah inba nan akwai can duk wanda aka cuta Allah ya saka mishi

To insha Allah sunji kuma bazasu sakeba idan Suka sake Ka sanar damu zamudau mummunar mataki a kansu malama nazifi zaku iya tafiya copra kayi kamar yanda nace

"Ok sir

Aka kada kan zaki da kwari harma da yaran su aka sasu a sel wayanda sukaji rauni aka garzaya dasu asibiti malam nazifi yayi waje Kareema mami da heedaya suka bi bayan shi har suka shiga gida bece komai ba a tsakar gida ya zauna ya dafe girji heedaya ta sugunna a gaban shi tana kuka

"abba dan Allah kayi hakuri wlh ban aikata abinda suka fada ba sharri sukai min ina kan tarbiyar da kuka bani abba ban canza haliba ka yarda dani mami wlh bana sabawa Allah adawa kawai sukeyi da karatun da nakeyi Abba ku fuskan ceni

Hannu ya daga mata"heedaya bazan ce miki komai ba se godiya kirjina ciwo yakemin ga kaina kibarni da wannan ma haka muryarki kara bakan tamin yakeyi ina miki magana ne yanzu cikin limana kitashi kibar nan idan kikaki kome nai miki ke kika ja

heedaya takara rusakuka ta tashi jiki ba kwari ta shiga daki mami tabi bayan ta

umma na cikin daki tana jin su farin ciki ya rufeta fitowa tayi tana mika alamar daga bacci ta tashi "malam lpy yaka zauna anan

Da kyar ya samu ya bude ido ya kalleta Kareema ta shiga daki dataga Bashida niyar kulata ta hakura ta koma daki ta rufe Kofa ta fisgo Kareema

"ke Kareema meyasa kike abu kamar mara hankali newai meye naki na binsu harda wani rudewa kina abba heedaya a waje ina ruwanki tinkafi musa Kafar wando daya dake ki ciresu a ranki kinji na fada miki kina sane dacewa mansir yana abuja kudin kayan dakinki na turashi ya anso idan ya tashi dawowa zasu dawo tare da adam da dan yarin yarcan Ali ranar alhamis zasu dawo saura kwana4 kenan karna sake naji wannan maganar a bakinsu inba hakaba sena nunamiki waccece hauwa'u


Kareema rai beso ba tace toh

Bayan kwana 4

malam nazifi na zaune a tirakarsa ya ya kira Kareema heedaya umma da mami dasuzo yana san ganin su sukazo kamar yanda ya umar cesu

"yau zan kawo karshen abubuwan da suke faruwa a gidan nan Kareema Alhaji Ibrahim gadara yazo neman izini gurina Akan ya turo iya Yansa bance komaiba senaji daga bakinki kina sanshi ko a'a

Kareema ta sunkuyar dakai tana murmushi

"Yasake cewa Kibani amsa da bakinki eh ko a'a

"eh abba ina sanshi

"Alhamdulillah amna kina sane dacewa mijin Kawar hauwa'u ne ko kuma kunsan yanda kuke da ita kanya karasa umma tatari numfa shinshi

"Eh ahaka take sanshi haka Allah ya rubuta Kareema matar sace ba haramun bane dan ta auri mijin kawata babatun cin amana dan Nasan haka zakace arziki na kiranmu ana yimana bakin ciki Allah yafi duk wani me ciki baki da auren nan

"Hauwa'u dake nake kena tambaya kona kira sunanki wannan maganar da kike fada dawa kike kinsan Allah hauwa'u idan baki shiga hankalinkiba sena dauki mummunan mataki a kanki Kareema ina jinki

"Eh abba nasani na amince zan aureshi a haka

"ah hap nina sani yarinya taji ta gani se wani dukunkuna magana akeyi akwai auredai a tsaka ninsu aure dai se anyi korai be soba umma take fada cikin gun-guni

"Ke kuma heedaya cikin sama rinki masu zuwa wakika tsayar daga ciki tare nakeso na aurar daku inkuma baki dashi zan baki wanda nakeso nagaji da kalamai marasa dadi da nakeji a kanki karatu ba dole se a gidanku zakiyi ba zaki iya yi a gidan mijinki

heedaya tazere ido ta dafe kirji "aure

"eh aure mun gaji da tazubar da ake mana a gida idan ba auren aka mikiba gobe dan shege zaki zo mana dashi tinkafin ranartazo gwara a dauki mataki cewar umma

Nidai na gama magana Kareema kicewa Alhaji Ibrahim gadara ya turo iya yansa banaso adau lokaci me tsawo duk agida jen maza janku nakeson ganinku

Mami tace malam banki taka ba yakamata a duba bantaba rokar wani abu a gurinkaba amma zan roki wannan alfarmar da kajanye maganar hadata da wani kabari ta fito da wanda takeso Wata kila lokacinta beyiba mazan yan zu kosun kashe kudi sun auri mata suna wula kantasu inaga wanda akaba kyau ta malam kaduba dan Allah kajanye

Umma ta harareta "inafa Zakiso a mata aure bayan ketake kawo wa kudin inta samu kuma kema kina kanta karasa ya daka mata tsawa

Hauwa'u bakijiba ko to shi kenan Allah ya baki sa'a Hafsat kindai ji komai da kunnan ki ranar da mukaje police station ko to Zan miki wannan alfarmar na yarda na janye amma da sharadi 1 heedaya bude kunnanki kiji dakyau idan har nasake ji magana makaMancin wannan wlh sena miki aure kuma duk wanda raina ya rayamin shizan baki indai taji shikenan nina gama magana

cikin muryar kuka heedaya take magana "naji abba insha Allah haka baze sake faruwa ba

Umma tana dariyar mugunta azuciyarta tace tukunna heedaya karyane Kareema ta tafi ke ki zauna sekin bita wlh dake za a daura aure sekin bar karatu kokinki kokinso

"kuje shikenan dama abinda zan fada muku Kenan

suna fita Kareema tace oyoyo oyoyo Yaya mansir Ali Adam sannunku da zuwa sannu da zuwa

Bashiri heedaya ta goge hawa yan fuskarta Tana musu sannu da zuwa falon mami suka shiga gaba dayan su umma ranta ya baci heedaya ta kawo ruwa da lemo kareema ta kawo abinci Kareema bata shiga dakin mami saboda su yau ta shiga abin ya bata mamaki seda sukaci suka koshi Kareema ta kwashe kayan sannan suka shiga gaisawa da juna sunata hira

Kareema tace Adam yanzu kumzama manyan yara an Gama secondary school yanzu Admission kuke jira ko

Ali yace eh da tini mun dawo gida asonmu muyi komai a nan yaya usman ne ya hana seda mukayi jamb sakamako ya fito sannan ya barmu muka dawo albarkacin yaya mansir

amma dai sakamakon yayi kyau ko cewar heedaya

Adam yace eh yayi kyau sosai sister heedaya kin rame meya Faru ko bakida lpy


Kai heedaya ta rike "kainane yake ciwo

Bari muje dakin umma cewar mansir

sister heedaya zanzo muyi magana akwai lbr masu zafi

heedaya tayi murmushi tana son Ali da Adam suzo hutu koba komai suna sata farin ciki

Suna rungume da juna sukaje suka gaida umma tasaki fuska kamar ba komai

bayan sallar magariba Ali da Adam suka je gurin HEEDAYA tinkafin su shiga falo Adam yaketa kiran ta

"sister heedaya gani nazo dama na fada miki zanzo

Tana jinshi ta sauko daga kangado ta fito falo "gani kai nake jira

yana kujera me kallon kujerar da heedaya ta zauna

Adam yace sister yaushe zakije abuja suna san ganinki karma i'heesan taji lbr tace idan baki jeba zata zo da kanta koda kwatan cene

"karatune ya hanani zuwa daga nasa rana se wani abin ya daso yasu yaya usman da matar sa

"lpy klau Albishirin ki yaya mansir yayi babban kamu shima aure koyau ko gobe

"Dan Allah amma na mishi murna

"tsaya aku me bakin magana nidai Bari naje ciki gurin mami na barku lpy tana ciki Cewar Ali

"Eh tana ciki

dakin ya shiga

Adam Suka ci gaba da magana da HEEDAYA

I'heesanfa ze aura

"waiyoo dadi a kano zasu zauna

"eh toh bansaniba komai zan gaya miki

"Adam Kaifa katada maganar dakayi shiru ni bazanma san anyi ba

"au haka zakice sister bazan fada miki me mahimmancinba

"fada min Mana dan uwa

"Sister meyasa kika rame ba haka kikeba kinga kanki a madubi kuwa

"Dan'uwa bakomai kamar yanda na fada maka hawaye ya biyo kuncinta

inda take zaune yazo "sister boyemin zakiyi Ashe bankai matsayin da zaki fada min damuwar kiba

" ba haka bane heedaya ta fada cikin muryar kuka

"to meye

heedaya ta fada mishi abinda yake faruwa daga farko har karshe mami da Ali suka fito daga daki akujera suka zauna sukai jugum jugum Adam ya dafe kai

"waiyo umma kece kadai zaki iya shirya komai dama baki yada maka mankiba yana wannan tinani yaji

Heedaya na cewa Adam dan Allah karka sanar da yaya mansir basan mezan cemai ba idan yaji

"heedaya Ashe zaki iya boyemin magana irin wannan ni mansir

"ba haka bane banaso kajine wannan ba abinji bane ko kadan

Adam yace injiwa yanzu ya akai da zaki da Kwari

"ban Saniba amma haryanzu suna sel

Agurin suka samawa kansu mafita tareda yiwa heedaya nasiha sosai umma kasa zaune tayi ta dinga labe amma bataji abinda suke yiba


gidan Alhaji Ibrahim gadara cike yake da mutane sai aiki a keyi an sauya komai na gidan gawani kyau daya kara basiru sanye da farar Shadda da malin-malin Najib ma Haka fuskar basiru yafi na Najib annuri Kana ganin Basiru kasan yana cikin farin ciki Najib kuwa ba yabo ba fallasa tsaf suka shirya sukaje gurin daurin aure aka daura auren

basiru da maryam
Najib da shaheeda

Suka dawo gida dare nayi aka kai amare gidajensu fur Najib yaki yarda akai shaheeda gidan shi daya gida yace sedai ta tare a gidan su hajiya naja'atu tafi kowa farin ciki da haka idan aka cire Yasmeen da take tausayawa mommynta maryam kai tsaye gidan ta aka Kaita hajiya naja'atu se zakewa tskeyi koda Najib ya dawo beje dakin Shiba dan yasan shaheeda nacan shaheeda nata zuba ido kozata ganshi amma shiru bezoba data gaji ta kwanta bacci a falo Najib ya kwana hajiya naja'atu ta fito da asiba ta sameshi yana sharar bacci dafda za a kira sallar asiba wutar falon ta kunna danta tabbatar da abinda ta gani shidinne kuwa a zuciye tadebo ruwa me sanyi ta kwara mishi



























New writer's


Hakan Take
*husba'ahfama* 😍❀🀩
*'YAR kwalliya* β€πŸ’‹



WhatsApp number πŸ“± 07036891952



πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 
πŸ’„πŸ’… *HEEDAYA* πŸ’…πŸ’„
*(I KIRARI)*
πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 





😑😑 *Gargadi ban yarda wani ko wata ya Dora min novel dina a kowana social media bada izinina ba idan haka ya faru ban yafe ba har'abada hakan baya nufin bayanda zanyi da mutum Niko nakeda yanda zanyiβš–πŸ‘¨β€βš–magwaji kuma ya gwada*





Written by *husba'ahfama*








*IG @Officiall_husba'ahfama*
Facebook *Real husba'ahfama*







24-25

"Najib mezan gani haka dakin matar Taka kabaro kazo falo ka kwanta ita kuma ka barta da filo meye amfanin auren eh fada min Najib

"Mommy sallane ya fito dani

"Ban son karya najib tashi kaje taganka tasan tayi aure idan na kara gani da matarka da komai kozo falo da sunan bacci zan saba maka tashi mana

Najib ya mike yana tafiya a hankali

"Au bazakai sauriba naji aunaga ikon Allah kokai ka kakeso nayi

Najib y girgiza kai

"A'a idan kaika kakeso nayi jirani aiba laifi bane danna rakaka

Ganin najib bashida niyar tafiya yasa ta kama hanun shi tanata masifa ta kaishi kofar dakin

" shiga ina gani idan cikin ma nizan kaika to anya najib kanada lpy kuwa mata aka kawo maka fa

Sai mommy ta rage murya kodai akwai ma tsala daga canne najib fadamin munema maka magani da wuri akwai ko babu

"Mommy lpy ta kalau fa

"Toh shiga

Yabude zeshiga kenan akakira sallar Asiba

"mommy kinji ko kibari naje masallaci na dawo Sena Shiga

Kaje ka dawo ina nan ina jiranka ba inda zani har ka dawo

Ya tafi masallaci itama ta dauro alwala tayi salla sebaza ido take taga shigoWar shi amma be dawo ba saida gari yayi haske sosai wajan karfe 7 sannan ya dawo ya sunkuya a gabanta

"mommy ina kwana

"kalau nake Najib haka mukai dakai yanzu aka idar da sallah

"a'a mommy karatu na tsaya yi

"Kasan Allah najib idan kace Zaka batawa shaheeda rai zamusa kafar wando daya dakai tashi kaje gurinta

yatashi yatafi dakin Yasmeen kuma ta zo falon

"mommy ina kwana

"lpy klau nake jekicewa habiba Ta gaggauta gama girki saboda yar mutane

"toh mommy bari naje na fada mata

Najib ya sameta a kwance tana bacci dakin ya shiga dubawa kozega wani alama daze nuna mishi Cewa tayi sallar asiba amma be ganiba hannu ya daga sama ya kai mata Dukan daya gigitata ta tashi tsaye kwalbar maganin mura ya fado daga jikinta yasun kuya ze dauka tarigashi kai hannu rai a hade ya hada kwarbar da hannunta ya matse kara ta kwalla ba shirr taSaki kwalbar ya daga yana kalla

"me kikeyi da wannan

"me a keyi da shi dama

ya matso inda take ya kama hannunta ya murda saitin kunnenta yasamu yake cemata

Ba a amsamin magana ta cikin raini bazan dauki haka daga gurin kiba ki Tsaya a matsayinki karki zaci kinzo jindadi a gidannanne Kinzo shan bakar wuya da azabane a gurina me kikeyi da wannan

taki cewa komai ya kara murda hannun da karfi saida ta kwalla kara hadida hawaye

"shanayi ina mura shiyasa

"tin yaushe kika fara sha

"jiya

"shine ya kare gaba daya wana likitane yabaki kuma shiyace ki shanye gaba daya

"a'a bajiya na fara shaba

Ya'isa tsaya kiji shaheeda idan har na gaskata abin da nake tinani a gurinki hmm kitabbatar aurenki ya mutu kinyi sallah

"eh nayi

Yakara murda hannun yanzu kam hannun yake yunkurin cirewa shaheeda ta Saki kara me rikitarwa hajiya naja'atu naji tasan i ta da najib ne ta kuma shirya fito warshi danta wankeshi da masifa

"a karo na 2 shaheeda kinyi sallah ko bakiyiba

"ban yiba wlh banyiba

Shaheeda bazan dauki wannan rashin yin sallar nakiba idan kikace haka zakiyi zakisha wuya a gurina jekiyi alwala Kizo kiyi Salla ya hankadata saura kiris tabige da bango

Fuska gaje gaje da kuka a zatona zata cigaba da kuka da mamakina senaga murmushi takeyi tana shafa hannun da Najib ya murda mata ta shiga bandaki da niyar yin alwala zata fara yin alwala seta tino da maganar da mommyta tafada mata cewa

"shaheeda indai kinaso ki mallake Najib da yan gidan su bazakiyi alwalaba balle salla inji boka harna tsawan kwana Arba'in indai kikai haka shikenan se yanda kikayi

Kuma tayiwa mommy nata alkawarin bazatayi sallaba

tashiga kaiwa da kawowa "yazanyi da Najib daya kasa ya tsare

madubin dake cikin bandakin ta kalla inda take gano kanta

"Najib nicefa shaheeda problem hmm kome zakayi kayi lokacin kane ina samun abin da ya kawo ni gidan nan duk zaku gane kuranku nice fa

ta bude kofar ta fita tana gwale kafa "Najib naga wata Ashe jini ya batani ta ciki ban saniba

Najib yayi kwafa ya tashi yabar

Please Login or Register in order to submit comment