Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sukayi dakin da sukajiyo ihun shaheeda suna shiga nanma sukayi mutuwar tsaye dakyar suka Hana najip dukansu anahaka

Amjad yashigo da yan sanda yace yihakuri Yaya najip ga yansanda Nan zasubima hakkinka


gaba dayansu akahada kansu da sauran abokan holewar tasu lokacin da zaashige dasu

alhaji yace kutsaya yadaga Kai yakalli karima yacemata nasakeki saki uku abin da kikaimin Allah yasakamin yabimin hakki

karima tadada sakin wanni kukan tace Dan Allah kayi hakuri karkamin haka

Alhaji yace Daman Ni narasa tayaya na aureki yarcikina dake kinzo kin koranmin uwar yarana kinrabani da ita


najip shima yakalli shaheeda yace kema nasakeki saki uku ga takardar results dinku da Dr yakawo dukanku kuna da ciki muna tayaku murna ke shaheeda kema kinsani zamana dake baabin da yataba shiga tsakanina dake Kuma da macan bani na aurokiba mummy ce yau naso ace tananan tagani da idanta abin da yafaru kekuma karima aje akaiwa hauwa'u jika gida tayi raino danwannan batarbiyar malam bace kinzubar da tarbiyir gidanku da mutuncin gidanku


yansanda sukaja mota sukatafi dasu jiki amace suka dawo gida yasimee kuka kawai take se rarrashinta sukeyi

Su najib atare sukace daddy yaushe zamuje wajan mommy mudau kota

yace yanzu yamma tayi mubari gobe da safe dukanmu semu tafi sukace Allah yakaimu


alhaji yace nifa mamakin tafiyar hajiya naja'atu kyauye nake Kuma kunce dakaina nakaita


sukace eh daddy nansaka bashi labarin yanda akayi


Alhaji hawaye kawai yakeyi daki alhaji yashege yakulle kansa yazauna Yana ta kuka


WASHE GARI DA SASSAFe

Alhaji da yaransa gaba daya sukadau hanyar zuwa grin bawo sun Isa lafiya sunkusa zuwa gidan su hajiya naja'atu sukaga wata Mata zani daban Riga daban mayafima haka takalmin yatsinke andaureshi da leda da kara akanta tana tafiya dakyar


yasimee tace Allah sarki su Yaya kuga wata Mata dakara akanta


mansur yace kyauye kenan inaga kobata da yarane take daukowa da kanta


sukace Allah sarki


Alhaji najinsu bece komaiba shi damuwa tayimasa yawa azuciya suna garasawa kofar gidan suka finfito zasu shiga kenan sukaga wannan matar da suka shige da Kara akai tazo itama zatashiga gidan


Amjad yace lah kunga matar da muka shige ahanya itama Ashe Nan zatazo



sukace waya gayamaka


yace gatanan tataho zata shiga kubari tafara shiga tukunna semu shiga

tazo shiga tana daga Kai takallesu kawai seji sukayi takira sunansu cikin kuka tayar da Karan dake kanta baki suka saki suna kallan ikwan Allah atare sukace wacece wannan kamar mommy

tace nice Baku ganeniba ko tadada fashewa da kuka

dagudu suka rungumeta Alhaji shima kukan yakeyi suna shiga cikin gida marka tajiyo kokekoke dagudu tafito daga daki tana tambayar lafiya dantajiyo Harda kukan hajiya tsayawa tayi cikin jinkunya yauga ga mijin hajiya naja'atu da yaranta sunzo wajanta


hajiya cikin kukan murna takalli Marka tace matar baba Kinga ikwan Allah miji yau yazo wajan matarsa gayara suma sunzo ganin mahaifiyarsu

marka takasa magana sabo da kunyar da takamata


Hajiya tajasu tace kozo muje dakina

sunashiga darawar jiki takade musu tabarmar da take kwana akai

tace kuzauna cikin mamaki suka hada baki sukace mommy dagaske kike nanne dakinki dakike kwana


tace eh menene

sukace to Ina katifar da kike kwanciya akai cikin hawaye tanuna musu tabarmar da ta shinfida musu basusan lokacin da suka dada fashewa da kukaba sabo da tausayin mahaifiyarsu da sukeji aransu

alhaji kuka shima kawai yakeyi dukunyar kanshi yakeji yau matarsace uwar yaransa abar kaunarsa itace cikin wannan halin adalilinsa sanadiyar auran da yakara

Hajiya tace ku zauna fari a i ebo muku ruwa

sukace aa mommy zauna kihuta atare su najip suka gaisheta cikin farin ciki taamsa

tadaga Kai takalli alhaji tace sannu da zuwa Ina wuni kanshi asunkuye yakasa amsawa shikunyarta yakeji

dasukaga haka mansir yaimusu Ido sutashi sufita suka tashi suka ce mubari muleka waje muga ko tsohunnan yadawo mugaisa semu shigo dashi tare sukai sauri suka fice

Ita hajiya azuciyarta tinani takeyi ko haryanzu kamar Dane tace dama danake fes yakini bare yanzu kanta asunkuye se hawaye takeyi sejitai

alhaji ya rungumeta yace naja'atu kiyafemin Dan Allah duni najamiki halin da kike ciki

tace bakomai alhaji Ni alheri hakan ya zamemin karka damu Nima kayafemin kusan nice silar komai


Sallamar babanta dasu yasimee sukaji dasauri alhaji ya amsa harkasa alhaji ya gaisheshi cikin fara'a yaamsa

su Amjad se tsokanar kakansu sukeyi

Malam bukar baban hajiya yace jikokina sungirma naji dadin ganinsu nayi mamaki dasuka ganeni

Atare su najip sukace haba tsoho Kuna kama da mommy fa aidole muganeka


Nan alhaji yaimasa bayanin

Sunzo tafiya da hajiya naja'atu

baban hajiya
yace to dama tini tagama karbar maganinta tawarke tinda tazo basu tashiba yace Amma kwana zakuyi


alhaji yace yau zamu tafi baba ai zamudawo kwana zamuyi inmunzo yace ga yaranan yanzu sunsan garin ,zakaringa ganinsu akai akai

marka tinda tashige daki Bata Kara fitowaba sabo da kunya dakansa malam yace Wai inana markane

Hajiya tace tana daki

yakwalla Mata Kira tafito Kai asukunye Nan su yasimee suka hau tsokanarta haba tsohuwa daga ganinmu seki shige daki kobakiyi murnar ganin jikokinkin nakiba

tace haba aa nayi murna Daman yanzu zanfito mugaisa .

itadai hajiya dariya kawai takeyi

Hajiya tace Bari naje nashirya naimaza naje nai sallama da malamarmu

dasauri yaran sukace mamala Kuma

taidariya tace eh

Se yamma suka taho bayan alhaji yacikasu da abin arziki marka dukunya takama ta su najip da zasu taho sukabata kudi sukace tsohuwa gashi ajajari bakihar kunne se murna take akunyace

take nunawa hajiya tai dariya tace inaruwana keda jikokinkiki

nansuka rabu cikin farin ciki suka dawo gida



Bayan sundawo da kwana biyu hajiya naja'atu tahuta suke mata bayanin abin da yafaru bakaramin tashin hankali tashigaba da Al ajabin abin da su shaheeda sukayi Nan take cewa

najip yayafe Mata yaje yanemo Yar gidan mutunci a auramasa baruwanta da arziki tace yanzu nagane meye duniya nagane da rajar Dan adan badan komaiba wannan abin da yafaru Dani yazamemin alheri arayuwata Nan take fada musu rayuwar da tayi akyauye sunji tausayina sosai Harda kuka

Tace yanzu inasu karima suke Nan suke fada Mata haryanzu suna wajan yan sanda

Hajiya tace Amjad kar ayihaka asakesu sukoma wajan iyayansu shaheeda da karima iyayansu koba komai kawayenane itakuma karima kodan mutuncin mahaifinta


Nan Amjad yakira abokinsa dansandan da maganar take ahannunsa yace yasakesu sutafi gida zasuje gida ayimaganar yacemasa to


Alhaji da lokacin yafito daga daki duyanajin hirar da sukeyi yace hajiya kishirke keda najip muje gidan su karima

Hajiya tace to

sukafito zuwa gidan su karima lokacin karima tadawo gida agala baice seda tazo gida takarbi kudi gurin malam tabame motar da yakawota lokacin malam nakofar gida shima yatsorata dayaga karima tambayarta yake meyafaru sekuka take taki magana anahaka


sega motar su hajiya naja'atu tatsaya akofar gidan dagudu karima tashiga cikin gida tana kuka lokacin yan gidan duka sunanan sunata Hira atsakar gida sukaga karima tashigo da gudu tana kuka atare sukahau tambayarta meyake faruwa se sallamar hajiya naja'atu sukaji


umma da tafito daga daki nantarude tana rawar baki tana nuna hajiya naja'atu da hannu tace naja'atu kece


hajiya tai dariya tace hauwa'u kenan nice


umma tayi mutuwar tsaye

Mami tacemata hajiya karaso sannu da zuwa


malam da su alhaji atare suka shigo suma Nan umma da karima suka Kara rudewa umma tarasa meyake faruwa


malam yace alhaji kuzauna gawaje


bayan sunzauna su Adam suka gaigaishesu


Nan malam yafara magana yace alhaji abin da yasa nacema mushigo cikin gida sabo da iyalina duka sunanan Kuma inaso kaimin bayanin meyake faruwa agabansu

Nan alhaji yayiwa su malam bayanin abin da yafaru tindaga farko harkarshe karima nagefe tamakure waje daya sekuka take bakaramin tashin hankali suka shigaba gaba dayansu sunkasa cewa komai kowa ya girgiza da maganar


Nan alhaji yakecewa ga takardar sakinta tin alokacin nasaketa saki uku


umma jiki yamutu sezarzare Ido take

Alhaji yace malam muzamu koma sewani lokacin

akunyace malam yafito yaraka su alhaji malam yaitaba alhaji hakuri

Bayan suntafi malam yashigo gida Yana shigowa yanemi waje yazauna yafashe da kuka hauwa'u kuncuceni keda karima

Malam yadafe kirjinshi Yana tatari yakasa karasa maganar da yakeyi nanan su Mami suka rude suka yokansa dagudu suna Kiran sunanshi




















New writer's


Hakan Take
*Husba'ahfama* 😍❀🀩
*'YAR kwalliya*β€πŸ’‹



πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 
πŸ’„πŸ’… *HEEDAYA* πŸ’…πŸ’„
*( I KIRARI)*
πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 







Written by *husba'ahfama*






*IG officiall_husba'ahfama*
Facebook *Real Husba'ahfama*


Follow me on Wattpad *@Real Husba'ahfama*













60-61

Sunakiran sunanshi malam lokaci guda yafita haiyacinsa dagudu suka daukeshi zuwa asibiti likitoci suntaru akansan danceto rayuwarshi


Lokacin da malam ya farfado sesannu iyalinsa sukemasa idanshi arufe hawayene kawai yakefita a idanunshi yaki yaimusu magana Nan Dr yashigo yace yana bukatar hutu abarshi yahuta kowa yafita abar mutum daya awajansa


Umma da kareema sunkasa binsu asibiti agida akabarsu suna fita umma tayo kan kareema tarufeta da duka dukanta take idanta yarufe


kareema kincuceni kingama dani nashiga uku Ni hauwa'u yazanyi dakaina da wannan abin kunyar da kikajamin dawana idan zankalli yan gidannan musamman hafsa da heedaya uwa uba Kuma mahaifinki kinsan in yawarke bazamuji tadadiba agidannan narufamiki asiri nanemomiki gidan da Zaki huta gashi kinjawa kanki kinfito daga gidan


tadada fashewa da kuka tace oni hauwa'u yaunice akakawowa cikin shege gida wlh kozaki mutu se anzubar da cikinnan Dan wannan abin kunyar yamin yawa heedaya da itace yadace tashigo da cikin shege gida Bata shigo da shiba seke da kike da aure waiyo Allah Ni hauwa'u kareema kincuceni kingama dani du gatan da na nunamiki abinda Zaki sakamin dashi kenan


Kareema nishi kawai takeyi tana fitar da numfashi dakyar kukanma takasa damuwa da danasani sunmata yawa azuciya ga azaba da jikinta yakemata



Atsakargida umma tabar kareema tashiga daki kuka kawai take rusawa tarasa tinanin da zatayi



Lokacin Mami da heedaya suka shigo sunbar mazan a asibiti sunyi sallama bawanda ya amsa nansukaga kareema akwance da sauri sukayo kanta


heedaya nakuka tace anty kareema mekike anan kishiga daki kowankama bakiyiba Bari nadora Miki ruwan
wanka


heedaya ce tahada Mata ruwan wanka takaimata tayi wankan

Nan heedaya tace anty kareema meyasa kika jamana abin kunya Kika zubarmana da mutuncin gidanmu kinjamana taban da bazetaba gogewaba a idan mutane kinjefa Abba awani hali yanzu kinsan halin da mukataho muka barshi a asibiti kinsanme likitoci sukace akanshi


Kareema tace kuyi hakuri heedaya wlh shirrin shedanne niyanzu bansan dawana idan zankalli Abba ba Dan Allah heedaya karkubari Abba yakoreni Dan Allah kutayani bashi hakuri tadada fashewa da kuka


Mami najinsu itama hawaye take tayi azuciya Mami tace Allah kenan danhaka bakyau kanajawa danwani alkaba i inkayi kanka yake dawowa hauwa'u baabin da bakiceba akan heedaya gashi Allah yakareta seakan yarki abin yakoma Allah kadada shiryamana zuria karabasu da shirrin zamani



Heedaya takalli Mami tace Mami tinani. Mekikeyi


Mami take bakomai heedaya kamata kirakata daki Wai kareema Ina hauwa'u


tace tana daki

Mami tace au dama tananan tabarki atsakargida awannan halin



Heedaya da kareema nashiga dakin umma ta dakamusu muguwar tsawa


Umma take kebakar muna fuka karnaga kafarku anan hardawani rikota burunku keda uwarki yacika kunmata asiri tadauko abin kunya kekuma kareema wawuya harkinmanta suwaye heedaya da hafsa kika saki jiki dasu to in bakisaniba murnasuke azuciyarsu danhaka kikoma wajansu bazaki kwanarmi adakiba nabarwa hafsa me



Kareema tace Dan Allah umma kiyi hakuri karkimin haka karki gujeni awannan halin da nakeciki koma meye dasu umma susuka temakamin daki fa kikashige gashi kogurin Abba kinki zuwa Kuma kojikinsa kinki tambaya Kuma mumuka jamasa halin da yakeciki ayanzu



Umma tace shikenan wlh dagaskene sun aikaceki sun juyarmiki da kwakwalwa toseki koma wajansu barikuga mezanmuku karku fitarmin daga daki


da sauri heedaya tadada kama kareema takaita dakin Mami sunashiga kareema tanemi waje takwanta tarasa meyake Mata Dadi

du maganar da umma takeyi Mami najinta taimata shuru itama daki tashige tasamu kareema nata kuka heedaya na rarrashinta



Nan Mami tahau yimata nasiha har hankalinta yakwanta taishuru



Su alhaji da sukabar gidansu kareema katsaye gidansu shaheeda suka wuce sukasamu manaifan shaheeda suka yimusu bayanin abin da yafaru Nan Babar shaheeda tahau borin kunya tana cewa bahalin yarta bane

Nan baban shaheeda yadaka Mata tsawa yace nasan zaarina yanda Kika Bata tarbiyaarta kituna komainisan jifa kasa zedawo kisani Allah yakubutar Dani daga sihirinki nayi shurune kawai nabarki azaman azirin dakikemin Yana tasiri ajikina koke hajiya naja'atu kinsan komai wani lokacinma har nasiha kike Mata yan uwana nane sukadage da addu'a da magani


Nan alhaji ibirahim gadara yabashi hakuri suka yimusu sallama baban shaheeda yaba najip hakuri akan abin da yafaru Nan yarakasu har mota

Baban shaheeda nakomawa gida

Yace shaheeda banga lefinki sosaiba kowana hali Kika shiga mahaifiyarki ce taja miki

Nan ya daga Kai yace asabe
asirin da kikaimin yakarye Kuma yanzu kullin inacikin azikar danhaka kokinyi wani sihirin baabin da zesameni insha Allah danhaka zanmiki albishir nafarko nadade da Kara aure harta haihu yanzu Haka dawani tsohon cikin ajikinta jikinta

Sekuma albishir na karshe kije nasakeki saki daya Kuma adalci daya zanmiki kizauna agidannan keda yarki bazan korekiba darajar haihuwar da mukai dake nabarki agidana tintini duwani abunawa me mahimmanci nadaukeshi nakaishi gidan da matata take aciki Dan Haka Kinga tafiyata


Sabo da tsabar rudanin da hajiya asabe Babar shaheeda take ciki yanke jiki tayi tafadi ko motsi batayi


shaheeda batasan lokacin data kwalla ihuba mommy kitashi Dan Allah daddy kayi hakuri kar kaimana Haka daddy


Kojuyowa beyiba yana kuka azuciyarshi yace zandawo wajanki shaheeda sekingane menene duniya tukunna se babarki tayi nadamar abinda take aikatawa yashiga mota yai tafiyarshi



BAYAN kWANA UKU


Ansallami malam daga asibiti alhamdulillah yasamu sauki tinda akakai malam asibiti umma da kareema basujeba su Mami ne suke tazarya haryau da aka sallameshi umma nadaki sejitayi ana sallama Harda muryar malam


Nan umma tadora hannu aka tace nashiga uku shikenan malam yadawo yasamu sauki wlh yau baze barmuba seyadau mataki akanmu



Malam Yana shiga dakinsa bayan yahuta yakira iyalinsa duka kowa yazo Amma Ban da umma da kareema


Nan malam yace su hauwa'u basa nanne


Adam yace sunan Abba


Malam yace jeka Kirasu Kuma kagaya musu karsu Dade inba hakaba ransu zebaci


Adam nashiga cikin umma yafara Kara Nan Adam ya gayamata sakwan malam


yaleka dakin Mami yakira kareema tinda

malam yadawo umma take zaryar bandaki gudawa takeyi Kiran da malam yaimusa yanzu cikin yadada rudewa

jiki amace umma tashiga da sallama abakinta kowa yaamsa Mata Amma ban da malam


kareema da tashigo kanta asunkuye tamakure guri daya


Nan malam yaigaran muyar kowa yaishuru Yana sauraran mezece






















New writer's

Hakan take
*Husba'ahfama* 😍❀🀩
*'YAR kwalliya* β€πŸ’‹



πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 
πŸ’„πŸ’… *HEEDAYA* πŸ’…πŸ’„
*(I KIRARI)*
πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 







Written by *husba'ahfama*




*IG officiall_husba'ahfama*
Facebook *Real Husba'ahfama*


Follow me on Wattpad *@Real Husba'ahfama*







GABADAi GABADAI
GIDAN BARDEπŸ‘πŸ‘Œ
Allah🀲 yakareku
Allah 🀲yadada daukakaku anakinku Allah nasanku🀣kunza ciwan Ido sehakuri🀣bayanda zaaidaku hm Dan adanπŸ€”abin tsoro Allah 🀲kadada karemu daga sharrin masu sharri
Ameeen summa ameeen

WANNAN SHAFIN NAKUNE GIDAN BARDE

Nasadaukar da shi gareku Ina kaunarku sosaiβ€πŸ˜πŸ˜˜πŸ‘Œda sosai Allah ya kareminku 😘❀









62-63





Malam yace bakomai bane yasa nataraku anan se akan abin da kareema tajawa gidannan tazubar Mana da kimar gidannan da mutuncina dakomai Ni yau Yar Dana Haifa ta aikata wannan badalar balefin kowa bane hauwa'u lefinkine danhaka tare Zan hukuntaku Kinga ikwan Allah hauwa'u ba abin da bakiceba akan heedaya Amma segashi duabin da kikafada Akan kareema ya faru ita heedaya Allah yakareta Danhaka seyazama darasi awajanki Yar makaranta budurwa batadauko cikin shegeba takawo gidan ubanta se Wanda Bata zuwa Kuma matar sure ita tadauko cikin shege takawo gida doka tafarko banyarda kodawasa kokuma kinasane kiyi yunkuri zubarwa da kareema cikin jikinta wlh wlh inhar haka tafaru hukuncin da zan yanke Miki konace muku bazakuji da dadiba Dan wlh hardaureku senayi dasauri umma da kareema suka daga Kai suka kalli malam sukaga bawasa afuskarshi maganar da yake fada dagaske yake zeaikata dasauri suka sunkuyar da kansu




Malam yacigaba da cewa sedoka tabiyu kafinnan kafin dare kugaugauta barmin gida duwani Abu da kukasan nakune kukwashe inhar kukakai dare agidannan zanmuku korar wulakanci Wanda Baku taba zatan zanmukuba


umma tafashe da kuka shikenan malam inka koremu inazamu kasan komai wajanwa zandosa adangi Dan Allah Dan annabi malam kayi hakuri kayafe Mana sharrin shedanne kusa baki su Adam kunaji zaakori uwarku kunki magana Dan ubanki kareema kibashi hakuri tadada fashewa dakuka



su Adam zasu bawa malam hakuri yaimaza yadaga musu hannu yace baruwanki duwanda yai magana ranshi zemugun baci


kareema in Banda kuka baabin da take tace Dan Allah Abba kayi hakuri nagane kuskurena kayafemin Dan Allah karka koremu wlh bazan karaba


yadaka Mata tsawa yace karna karaJin muryarki bazanmiki bakiba Allah yashiryeki kutashi kubani waje wannan shine hukuncin da nayanke Kuma kisani hauwa'u wannan lokacin kowa kikakira bazantaba saurararshiba yakalli su heedaya yace kutashi kotafi Allah yaimuku albarka


dujikinsu amace sukatashi sukabar dakin se Mami datakasa tashi


umma nagefe tana ta kuka tadaga Kai takalli Mami tace kinkisa baki sabo da kinamurna zanbarmiki gidan ko


Mami tace nibana murna Dan zakibar gidannan insha allahu bainda zaku


malam yace hauwa'u kitashi kibarmin gidana kafin raina yakara baci


dasauri tatashi tabar dakin tana kuka


Mami takalli malam tace haba malam inrai yabaci hankali ake nemowa Dan Allah kayi hakuri yanzu inka koresu inazasu da wannan cikin kaga mundada tonawa kanmu asiri insukabar gidan hannunka baya rubewa kayanke kayar kayi hakuri Dan girman Allah kayafe musu kabarsu da wannan kaddarar da tasamesu


yace hafsa bazaki ganeba kema kinsan nadade inahakuri da hauwa'u dufitinar da takeyi agidannan nasani kawai inashurune kozata gane gaskiya tinda taki ganewa Dole tabarmin gidana sujecan suraini cikin Amma baanan gidanba kema karna batamiki ranki kitashi kibani waje zanhuta



Dole Mami tabashi waje takoma daki tasamu su Adam jiki mace tashiga ta zauna


su heedaya sukace Mami yanzu meye abinyi ran Abba yabaci sosai wlh baze sauraremuba munsan kema kinbashi hakuri yakiyarda


Mami tace mubari yahuce kafin dare semu dada bashi hakuri

Sukace to Allah yasa yasauraremu


Umma da kareema Banda kuka baabin da sukeyi adaki

umma tace shikenan kareema Kinga abin da kikija Mana yanzu wajanwa zamudosa dawannan abin kunyar Koda danatafi lokacin Yana rashin lafiyarnan dannasan kina gidan alhaji zakisa yasayamin gidan da,zan zauna shiyasa Amma yanzufa wanake dashi bani dakowa mahaifana sunrasu saura yan uwana sumakuma bawani shirimuke dasuba kiga abin kurya da Kika jamana gaban su hafsa Kuma kinsan makiyanmune su basa kaunarmu gasharadin da yakafa karna kiramasa kowa yanzu yazanyi sekitashi muhada Kaya yanzu ko yankunne da sarkarki na daham zamu Saida baze sayamana gidaba sedai mukama haya


ita kareema taki cewa komai hawayene kefita daga idanta


Mami ce takira aminin malam awaya Dan Allah yazo wata matsalace take faruwa dasauri malam lawan yazo gidan bayan sungaigaisa yake tambayar Ina umma

Nan Mami tace Daman akantane muka kiraka katayamu bawa malam hakuri


malam lawan yace meyake faruwa Kuma

Nan Mami tafada Masa hukuncin da malam ya yanke Amma Bata fadamasa abin da kareema taaikataba


Aminin malam yace haba habakaikuwa Dan uwana aminina wannan hukuncin da kayanke yayi tsauri da yawa yanzu insuntafi Ina kakeso suje Dan Allah kayi hakuri kabasu dama takarshe nanemi wannan alfarmar takarshe akansu yace Wai Ina hauwa'u ne tazo itama


Mami ce taje takirata tazo Nan yadada mata.fada yace tadada bawa malam hakuri Kuma Dan Allah kartakuma

dakyar malam ya hakura bayan malam lawan yatafi


Nan malam yace dokar da zandada samuku nafarko maganar zubar da ciki korashin lfy kareema tayi akaje asibiti akaduba akace waniabu Tasha daniyar zubar da ciki nariga nafada Miki abin da zanmuku Kuma daga yau bani bake ki harkarki naitawa kina zaunane darajar yaranki da aminina dawasa naji wata fitina tatashi agidannan niji da sahannunki wlh sekin barmin gidana har abada


Nan tadaga Kai tana kallan malam taga tsanarta karara a idansa batasan lokacin da tadada fashewa da kukaba tace insha Allah baabin da zefaru nagode


yace Kuma naji korar da kikayiwa kareema daga dakinki baki isaba dolane takoma dakinki tinda yarkice kije kitayata rainan cikin Kuma tahaifo kiraini jikanki seyanzu Zaki sakarwa hafsa ita yanzu tinda tadauko abin kunya keinkina da kunya Zaki kora kareema dakin hafsa keda kike da tarbiya Kika iya koyarda ita ai bakyakaita dakin da zata lalaceba tinda baabin da baki fadaba akan hafsa da yaranta musamman heedaya yanzu Dan Allah bakiji kunyarsuba


jiki amace tatashi tatafi daki tanafitar da hawaye




Bikin heedaya nata matsowa su Mami se shiryeshirye akeyi Wanda zaabawa heedaya koyazo bawata hirar arziki bace take shiga tsakaninsu kawai tana fitane danbiyaiyar mahaifinta Amma bawai Dan tana sansaba tana fitane Danta farantawa mahaifinta Rai




SAURA sATI DAYA BIKIN HEEDAYA




Sukawayi gari da rasuwar mijin da zata aura sanadiyar ciwanciki lokaci daya kafin akaishi asibiti Allah yakarbi ransa bakaramin tashin hankali mahaifan yaran sukashigaba da labarin rasuwar yazowa su heedaya da mahaifanta bakaramin tashan hankali suma suka shigaba hankalinsu yatashi sosai ko heedaya mutuwar ta girgizata



Mami tace kekuma heedaya kandarar da tasameki kenan in har lokacin auranki yazo sewata kandarar dazo tashige taciki Allah ya jikan yaran kekuma Allah yaimiki zabin alheri tace ameeen Mami


Ali dasu Adam adakin Mami suna hira heedaya sukaga tadaga Kai sama tana ta murmushi


Adam yace ikwan Allah heedaya tinanin mekike Haka Harda murmushi


tace wlh Yaya waniabu natuna

yace meneneshi

tace tinani nayi tinda Wanda Zan aura yarasu shikenan yanzu Abba zekyaleni nacigaba da karatuna kaga daganan har Allah ya kawomin Wanda nakeso


yace hm heedaya kenan waiharkin manta Abba baya magana biyu inyafadi Abu seyacika to wlh kidena murna dakuma wannan tinanin tinda kikaga haryanzu bece komaiba kumayau saura kwana uku bikin da Allah yanufa yaran nadarai wani ikwan Allah ranar sadakar bakwansa shine ranar daurin auranku dayana raye kijira kiga me Abba zeyi ranar kedai kawai muyita addu'a Allah yaimiki zabin alheri allah yafimu sanin meyake faruwa


Nan jikin heedaya yamutu gaba daya

ali yace wlh Yaya dazu Abba yana waya damasu yimata Kayan daki suna fadamasa sungama

dasauri heedaya tace Dan Allah mekaji yace Kuma

Yace aa nibangama jinsuba nashigo gida



Rana Bata karya sedai uwar Diya taji kunya yaune sadakar bakwan yaran da zaa aurawa heedaya akofar gidansu heedaya akayi sadakar bakwan mutane suntaro sosai bayan angama addu'a gawanda yarasu har mutane sunfara tashi akai sanarwa kowa yakoma yazauna akwai daurin aure

Andaura auran heedaya Akan sadaki nera dubu dari buyu dakyar malam yayarda da sadakin da akawo cewa yayi kudin sunyi yawa mahaifin yaran ne yace kudin basuyi yawaba ayi hakuri akarba Haka sukainiyar bayarwa su aganinsuma yayi kadan Dan karsu bada dayawane ace yayi yawa shine sukaba da dubu dari buyu


Su mami dasu heedaya suna daga cikin gida sukajiyo sanarwar daurin auran heedaya kowa yayi mamakin sunan angwan da akakira da sunan mijin heedaya bakaramin kaduwa su Mami sukayiba harta kareema da umma dasukaji sunan angwan Dana mahaifin angwan sungirgiza dajin sunan


Heedaya tadada kasa kunne taji sunan Wanda akekira taji shidinne mijin da aka auramata Nan kunnanta yajiyo Mata hakane wani irin ihu heedaya ta kurma tafadi kasa sumarmami






















New writer's

Hakan Take
*Husba'ahfama*😍❀🀩
*'YAR kwalliya*β€πŸ’‹

πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 
πŸ’„πŸ’… *HEEDAYA* πŸ’…πŸ’„
*(I KIRARI)*
πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 






*IG officiall_husba'ahfama*
Facebook *Real Husba'ahfama*


Follow me on Wattpad *@Real Husba'ahfama*














64-65







Dagudu su Mami sukayo kanta arude

Mami tace kubani ruwa anabata tayaiyafamata taja dogon numfashi tabude Ido ahankali takalli Mami

tace

Please Login or Register in order to submit comment