Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

๏ปฟ[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž


*YESMEEN*

๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž


*WRITEN BY:*
*UMMYN YSRH*



*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
*(P.M.L)*




_MASOYA NA KWARAI HAR ILAYAU BAKI BAZAI IYA FURTA KALAMAN GODIYA DA ADDU'A AGAREKUBA DA BAZARKU NAKE RAWA๐Ÿ’ƒ๐Ÿป_

*MERMUE* *(MRS JABO)*

*YESMEEN TAFEESU*

*QUEEN MIEEMIE*

*RASH KARDAM*

_Fatan alkhairi agareku_
_Allah k'ara d'aukaka_
_Allah k'ara nisan kwana da tsawon rai mai amfani_
_Ina godiya Allah yabar zumunci_

_DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN K'AI TSIRA DA AMINCI SU TABBATA GA FIYAYYEN HALITTA ANNABI MUHAMMADU (S.A.W)_


*1~5*

Babbar motoce d'auke da d'alibai,kowacce kaganta cikin farin ciki take na murnar kammala makarantarsu ta secondary,motar d'auke da tambarin Gov't Girls College Bauchi (G.G.C.B).

D'alibaine da yawa wanda suka fito daga garuruwa da yawa ko wacce za'a kaita har garinsu.

Garin Jos suka dosa,duk d'aliban garin basu wuce mutum bakwai ba,kowa murnar komawa gida yake,daga gefe na wango wata y'ar budurwa zaune duk wake_waken da d'aliban suke bata sauraransu tunda suka d'auko hanyar garin nasu taji duk jikinta yayi sanyi ga kuma fad'uwar gaba da takeji,sun kuyarda kanta tayi jikin seat d'in moton.

Tunda suka shigo garin ba wani hayaniyar mutane wasu guraren ga k'onannun motoci,kwata_kwata ba wani alamar mutane sosai agarin sai d'aid'aikun mutane dakuma jami'an tsaro,tasha aka sauk'esu motar ta k'ara lulawa gaba don kai sauran d'aliban garu_ruwansu.


Sunfi awa guda suna zaman jiran abun hawa don kaisu gidajensu amma ba kowa duk shagunan kasuwar arufe suke ba mutane masu d'oki da wak'ok'i duk jiki yayi sanyi.
Gajiya sukayi da jira kowacce ta d'aura d'amarar da'bawa ak'ar don tafiya gida.

Haka suka rabu daga wajen *Yesmeen* datun amoto batada wani kuzari haka ta kwashi kayanta tayi gaba itama,ahanya tahad'u da wani take tambayarshi meke faruwa agarin nan yake shaida mata fad'ane ya kaure kwana uku dasukawuce,cikin dare aka rink'a bankama gidajen musulmai wuta musamman unguwar rogo anyi ta'adi sosai,jin an ambaci unguwarsu yasa tad'au hanya bataredata tsayajin k'arshen zancenba.


Sauri take batamasan inda take jefa k'afartaba, burinta kawai Allah kaita gida lafiya.

Abunda tagani ya mugun firgitata,gaba d'aya gidansu ya k'one ba alamar wani abun amfani ko rai mai motsi awaje duk da gidan nasu tamkar unguwace guda don duk danginsu na cikin gidan sai k'alilan da suke wani garin,don mafi yawansu auren dangi suke kuma duk wanda zaiyi aure cikin gidan yake zama.

Salallami kawai takena

_INNALILLAHIWA'INNA'ILAIHIRRAJU'UN_

nima dake gefe tayata nake had'e da kwalla๐Ÿ˜ฅ




~UMMYN YSRH~
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž

*YESMEEN*
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

*WRITEN BY:*
*UMMYN YSRH*


*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
*(P.M.L)*


*6~10*


Salati kawai take tare da tafiya da baya da baya,ji tayi tayi karo da wani abu juyawar da zatayi taga k'onannen motar mahaifinta,ga mashind'in yayan babanta shima yasha wuta duk ya k'one,wani sabon hawaye takumaji ya kuma gangaromata,kamar wacce aka tsikara ta zura aguje tayi cikin gidan ba komai ciki sai gayyar toka da k'onannun k'asusuwar mutane da kuma gawayi.


Sassa kusan gomane cikin gidan amma duk angama dasu,wasu sassanda wuta bai kamasuba jinine kwance awajen tamkar kwata mayankar dabbobi,da gudu tajuya tabar wajen gefensu tashiga ba wani abu cukinshi komai ya k'one wajen ajiye Qur'anansu ta nufa mamakune ya kamata ganin duk wani abu dake cikin lokar ya k'one amma wuta bai tab'a Qur'ananba sai d'an gefe_gefe wajen daba rubutu tace "ALLAHU AKBAR."
saikuma tasake rushewa da kuka,wajen ta d'urk'ushe rungumeda Qur'anan.

Jitake kawai inama azo asake cinnama gidan wuta ko itama suyi gunduwa_gunduwa da ita kozata huta,don ayanzu bataga amfanin cigaba da rayuwartaba.

"Wai yaushe garinsu zai sami zaman lafiya?"

"yaushe za'a daina irin wannan kashe_kashen?"

"yaushe za'adaina maida mata zaurawa?"

"yaushe za'a daina maida yara marayu?"

"marasa yanci,galihu,bamai kuladasu,saidai ad'ebesu akaisu gidan marayu a jibgesu bamai kuma waiwayensu,bamai basu wadataccen ci,sha,sutura,uwa uba Ilmi."

"Wai ina masu kud'inmu shuwagabanninmu?"


"Yaushe garinmu zata sami tsaro adainawannan tashin hakula?"
Maganganu kawai take ita kad'anta tare da tambayoyon dabasuda wani amfani balle amsa.


Lokaci maitsawo ta d'auka durk'ushe awajen,tana tunanin wani irin rayuwa zatayi ayanzun idan tace Bauchi zata koma wajen k'anwar babanta wazai bata kud'in moto?,ina zata sami moton ta shiga? don daga dukkan alamu garin bashiga ba fitane,yanzu ya zatayi?kodai tazaunanan ko cikin dare itama zatasami masu k'arasata.

Zamatayi tareda dura kanta cikin cinyoyinta,tacigabada kukanta,chan nesa takejin maganganun mutane,ji take kamar cikin gidan suke shigowa yadda takejin tafiyar manyan takalma tasan masu k'arasatane duk jikinta ya k'ara d'aukar sanyi,ko yatsar hannunta bata fatan ya motsa balle har tajega d'aga kanta taga yanayin halittar makasanta, chan taji wani daga cikinsu yana "gatacen"
cikin wani irin gurb'atacciyar turanci.


K'ara tura kanta tayi cikin cinyoyinta tareda k'ara rungume Qur'anan dake hannunta bisa k'irjinta mai barazanar rusowa.

Jitayi andafata tareda rungumata lokaci guda kuma sai kuka,ahankali take d'ago kanta saidai har yanzu idonta rufe yake,harta gama d'agokan bata bud'e idonba illa hawaye dake gangarowa bisa k'uncinta,wacce ta rungumata tace
" *YESMEEN*bud'e idonki nice."

Ahankali take bud'e idon har tawaresu kan fuskan k'anwar mahaifinta da sauri itama ta rungumeta tana kuka tana fad'in
" *UMMAH HABIBAH* sun kashesu,sunkashemana kowa,sunmaidamu marayu."

"kishiru akwai Allah,kitamusu addu'a"

"Taya zan daina kuka?"

"yaushe ruwan idona zaidana zuba bisa zaluncin da cin zalin da akamana?"

"har abada bazan dainaba,zan rayuwa inama duk wanda akama danginshi irin wannan cin zalin addu'ar Allah mana sakayya Allah yasa suyi k'ask'antacciyar rayuwa,sannan suyi mutuwar wulak'anci."

"naji kima me kitashi mutafi don yanzu unguwar ba kowa don ko jiya saida akasake kahomusu wani harin."

"kije kawai nizan zauna gara nima suzo su kasheni don ayanzu rayuwata batadawani amfani."

"bazan iya barinki ananba,yanzu duk danginmu mu uku kawai muka rage,kitashi muje yanzuma da taimakon sojojinnan nasamu nashigo garinnan."

Batakuma cewa komaiba tamik'e suka yi waje,wani harara take zubama sojojin don aganinta basuda wani amfani tunda har za'ayi wannan ta'asar basuyi yunk'urin hanawaba.


Fita sukayi daga konannen gidan suka nufi wajen motocinsu,kayanta data dawo dasu tahau d'iba suka sa cikin moton,kallon gidan kawai take tana k'ara rushewada kuka shikenan tagama rayuwarta agida?
Shikenan yanzu rayuwarta ya koma wani garin?

Meyasa basuyi jinkiri harsai ta dawo suhad'a da ita sukasheba?

Meyasa sukabarta araye?

Runtse idonta tayi yayindataji direban *UMMAH HABIBAH*
Ya tada motor, har sukabar garin jos bata bud'e idontaba,saida sojojin suka fiddasu garin kafin suka juya.




โœ๐Ÿป ~UMMYN YSRH~
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž
*YESMEEN*
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž



*WRITEN BY:*
*UMMYN YSRH*



*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*


*21~25*

Yau satinsu d'aya da dawowa,saidai sam batajin dad'in abin da ake ma Umman nata,yadda dangin mijinta da Uwargidan ta ke mata na gorin rashin haihuwa.


Shekarar ta goma da aure Allah bai bata haihuwa ba kullum cikin gori da bak'ak'en maganganu take sha,wajen mijinta kawai take samun sauk'i.

Wai da wanne za taji ne? yanzun da rashin dangin ta ko da matsalar kishiya da dangin miji na rashin haihuwa?.

Me yasa mutane suke manta cewar Allah shi ke bada haihuwa ba wayon ka ko dabarar ka ba?.

Wa za ta kai ma kukan ta a yanzu don ya sharemata hawayenta?

Y'ar uwarta da ta ke gadara da ita ko kad'an basu gaban ta a yanzu giyar kud'i na d'ibanta ta manta da su tayi watsi dasu ta samu sabin dangi, su d'in ba kowa bane a gare ta.

Zata ci gaba da kaima Allah kukan ta,shi zai mata maganin matsalolinta.


Haka rayuwars u ta kasance cikin gidan,duk da ba wani shahararren arziki ga mijin Ummah ba,yana da rufin asirin shi daidai gwargwado, yana kuma iya bakin k'ok'arin shi kan iyalan shi.


*YESMEEN* ta ware sosai sai dai ko da yaushe tunanin ta yana wajen y'an'uwan ta marayu,ko suna cikin wani hali?duk sanda zata wurga loman abinci bakin ta sai ta tuno dasu ko sun samu sunci?,idan sabon sutura zata sa sai tayi tunanin ko suma sun samu sun sa?


Da sauri ta shiga gida kamar zata tashi sama, ko sallama babu ta nufi falon gidan daidai zata wucesu taji ance.

"Toh jikan marasa kunya iyalan kalan dangi da chusa kai,kin shigomana gida ba sallama balle gaisuwa."

Juyowa tayi tana kallon mai maganar ji take duk sanda taga matar kamar ta dab'a mata wuk'a don tsanar DA ta ke mata.

Amsa tayi niyyar bata sai kuma ta fasa tace

"Sannun ku masu gida."

Wata daga gefe tace

"fad'i ki k'ara fad'i yarinya,gida namu ne sai dai mutum yazo yaci arzik'i ya k'ara gaba."

dariya tayi sannan tace
"Ruky kike kowa?
Kalleni tsaf kin san nafi k'arfin shigowa gidan nan inci arzik'i,ke kanki kinsani."

Umma Habiba ce ta fito daga kitchen tace

"ke Hanifa sa'i'on ki ne su da zaki rink'a musu magana haka?kul ko da wasa bana son hakan,wuce ciki k'awarki na d'aki."

Wucewa tayi tana watsa musu harara
Kishiyar Umma Hajiya Talatu tace

"ai dole ki korata tunda kin sa ta gama yi mana rashin kunya,haka dai zaki k'are akwashe_kwashen y'ay'an mutane da cika mana gida da manyan kashi."

Juyawa tayi ba tare da ta kuma tanka su ba. Zuciyarta sai k'una yake kamar ta Ciro shi waje ta huta don azabar zafin da ke mata.

Ihu yaran suka sa lokacin da ta juya suna ma Uwar tasu kirari da Sai Mama uwar masu gida.


D'aki Hanifa ta shiga tana kwalama Yesmeen Kira.

"Ke wallahi kin fiya Kira kamar makauniya,ki k'araso gani ciki guga nakeyi."

"Dallah ki tashi ki shirya anjima zamu unguwa."

"Unguwa kuma? Wacce iri,kuma ina?"

"Ohho! nidai ki tashi ki shirya zuwa k'arfe biyu zamu tafi."

"Idan nayi niyar zuwa ko ban yiba zaki sani dole kenan?"

"Malaman su aima dole kije Wallahi,bari ma ki gani b'ata lokacina nake gurin ki idan na had'aki da Ummah dole kije Baby."

Fita tayi tana mitar mutum kullum sunk'ume a gida kamar wani mummunan amarya.

"Me kikecewa?"

"Nace Allah barmu da wannan k'awa tawa y'ar ra'ayi da jan aji."

"zaki sani idan na rik'eki zaki gayan wace mummunar amaryar".

"Au! ashe kin jinine."

"A'ah kinsan na zama kurma."

K'arasa ficewa tayi tana dariya.

Kitchen ta nufa gunda Ummah keta k'okarin had'a abincin rana tace

"Ummah dama nazo tambayar ki ne don Allah Yesmeen ta shirya muje wajen hidimar bikin d'iyar k'awar Hajiyata."

"shine sai kin tambayeni? ai an zama d'aya."

"ai nace ta shirya muje wai ba za ta ba."

Tak'arasa maganar tamkar mai shirin kuka.

"tsokanarki take,jeki shirin ki zan mata magana."






โœ๐Ÿป *~UMMYN YSRH~*
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž

*YESMEEN*
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž


*WRITEN BY:*
*UMMYN YSRH*



*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
*(P.M.L)*

_THIS PAGE IS 4 U MY CHUCHU๐Ÿ˜_

_ALLAH YABAR ZUMUMCI SO DA K'AUNAR JUNA_


*11~20*


Saida sukayi nisa da tafiya kafin ta bud'e idon da taji *Ummah Habibah* nacewa

"ohh! wato nan akazo aka zubara mutanenmu?"

Kallon wajen nayi asannan na gane wani gari muke, *TILDEN FULANI* mutanene birjik awajen mafiya yawansu matane da k'ananan yara sai maza y'an tsiraru,kowanne ka kalleshi kasan fitowan rashin shiri yayi.

Tsayawa moton tayi muka fita don duba y'an gudun hijiran ko Allah zaisa muga wasu daga cikin y'an'uwanmu.

Makarantar bokoce aka ba y'an'gudun hiriran da suka haura sama da mutane dubu uku,ajujuwa shine wajen kwanansu,rijiya guda d'aya tak shine wajen d'iban ruwa domin yin ibadansu da kuma girki ahakan wasu daga cikin y'an garin suna d'iban ruwan cikin gara kuna suna kaiwa gari domin samun taro sisi.

Kan sumintin da duk ya farfashe yayi rami shine makwansu,
Babu tabarma balle kuma katifa, ga buhun shinkafa uku da garin masara biyu da gwamnati ta aiko musu dashi don girkawa.

Jefe chan ga yara birjik sai kuka suke ba iyaye ba y'an'uwa,ankashe kowa nasu.

Shin wazai tallafi rayuwar wad'annan yaran?

Suwa zasu mayemusu gurbin iyayensu?

Wani irin rayuwa zasu fuskanta?

Wazai tallafi rayuwarsu ya basu ingantattaciyar kulawa?

Ahaka rayuwarsu zata k'are ko kuma zasu sami masu tallafamusu domin zama manyan gobene da ake ikirari?

Daga jefe nace mata babu mai iya baki amsar tambayarki,ki musu addu'ah kawai,Allah shine gatansu shine kuma jagoransu.
Allah ya rayasu bisa turba madaidaciya.


Juyawa tayi ta kuma ganin yadda yaran ke kuka da kiran iyayensu,juyawa tayi da gudu tana wani irin kuka mai tsuma zuciya,jitake kamar zuciyarta zai fito ya tarwatse.


Tunda ta shiga moton ta duk'ar da kanta k'asa ta runtse idanuwanta bata kuma bud'ewaba tanaji Umman nata suka shigo direba yaja ahankali tace

"Allah kawo muku sauyi cikin gaggawa."

"Allah kawo masu tallafawa rayuwarku"

"Allah bi mana hakkinmu,ya mana sakayya."

*AMEEEEEEN*

Ba wanda ya kuma magana har suka iso cikin garin Bauchi,unguwar Fedral low_cots suka nufa gidan Umman.


Suna isa ta wuce d'akin Ummah Habiba,ta ajiye kayanta bayan gida kawai ta wuce alokacin shida harda wani abu,gashi ko sallar azahar bataiba,tun d'azu neman gafarar ubangiji kawai takeyi na had'a sallolin da tayi,tana watsa ruwa ta d'auro alola ta sunkuya bada farali.





โœ๐Ÿป *~Ummeen yusrah~*
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž

*YESMEEN*
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž



*BY:*
*UMMYN YSRH*


*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*



*26~30*

Haniface ta shigo cikin shirin tafiya,sanye take da riga da wando duk sun d'ameta sai after dress data d'aura,gawani takalmi mai uban tsini kamar kifiya.

Haka ta shige d'akin Umma ba tare datama kowa maganaba.

Tana shiga tasamu Yesmeen tagama shiri itama,atamfa tasa da gyalanta mai d'an girma da d'an flat shoe nata ba laifi tayi kyau.

Kallo Hanifa ta bita dashi tace

"ke wallahi har yanzu baki wayeba,saikace ba girman Jos ba."

"wacce irin wayewa kikeso inyi?"

"chasufa za'ayi, amma kin wani d'au atamfa kin saka habba! aisaikiban kunya."

"Tooow! Shigar tawace bataiba kome?"

"Eh."

"Don Allah muje gida inbaki wasu irin nawa kisa."

"Allah sauwak'emin."

"Waiku me kuka baku fito kuntafiba,idan kun had'u sai kuntab'a hali."

"gamu fitowa."

Fitowa sukayi suna hira suna dariya kamar ba yanzu suka gama rigimaba.

Y'an gidan sai binsu suke da kallo ana maganganu k'asa_k'asa.

Suna fitowa Hanifa tace

"d'an jira inshiga gida in d'auko aika saimu wuce."

"ki sauri karki dad'e."

Fitowa tayi hannunta d'auke da wani d'an madaidaicin jaka.

"mujeko baby."

Adaidaita suka shiga Hanifa tace

"Malam Fadamar mada zaka kaimu d'angaba da asibitin Alwadata."

Ciniki sukai ya kwashesu,lokacin da sukazo wucewa wajen Makarantar kwana ta G.G.BAUCHI Yesmeen jitayi kamar ta shiga,amma haka aka wuce.

Shiga sukayi da sallama wata y'ar matashiyar budurwata ta lek'o da fara'arta tace

"sannunku da zuwa kushigo."

Falo suka shiga suka zauna,wata budurwa tafito da gani tad'an girmesu

"sannunku da zuwa manyan bak'i."

"yawwa sannu. kina lafiya?"

Gaisawa sukayi,akata shigo musu da abinci da abunsha,gawani girmamawa da ake musu, itadai Yesmeen tazama y'ar kallo su Hany kuwa an sake sai hira ake.

Itadai Yesmeen abun ya d'aure mata kai tunda sukazo bataga matan gidanba sai gayyar yaran gida masu kama d'aya,takuma rasa ina tasan mai wannan kamannin.


Wajen k'arfe uku da rabi budurwar maisuna Salma tace

"nakai muku ruwan wanka, kushirya zuwa k'arfe hud'u za'a tafi."

Yesmeen tace

"wanka kuma? ai munriga munyi wanka tun kafin muzo."

Hanifa tace

"Mungode Aunty Salma."

Mik'ewa tayi taje tai wankarta ta dawo d'akin su Salma,nidai shiga nayi na gyara kaina dayake lokacin period d'inane.

Ina fitowa naga Hanifa ta d'au kwalliya sanye da wasu riga da wandon,kawai baki nasaki ina kallonta.

"Gashi kisanya tunda kink'i ki wankan."

Dubawar dazanyi naga wasu riga da wando da kad'an zai wuce gwiwata idan nasa,wurgamata nayi nace

"Bana buk'ata kema kinsan ida nayi niyar sawa tun agida gaban iyayena zansa ba abayan idonsuba,abunda banyi agaban idonsubako bazanyi abayan idonsuba,idansu basa ganina ALLAH yana ganina."

Kwashe kayan tayi batace komaiba,kiransu akayi su fito ana jiransu waje.

Godiya sosai sukayi suka fice,motar da Yesmeen tagani shiyasata fad'uwar gaba,motar abokin saurayin Hanifane.

Sai yanzu ta gane 'yan gidan da abokin saurayin suke kama.

Tik'ashi! dama gidan saurayi ta kawosu?
ranta inyayi dubu ya b'aci,motar kawai suka shiga ba tare datace komaiba.

Basu zame ko inaba sai School of armour, tundaga k'ofar hall d'in kid'a ke tashi fita sukayi daga cikin motan suna fita Hafiz juya abunshi,Hanifa da saurayinta Adam rik'e da hannun juna biye nake dasu har cikin wajen.

Lokacin da mukashiga wajen cike yake da mata da maza,musulmai da chirista saidai ko kad'an bazaka tab'a iya banbance wace Saratu wace Sarah ba,duk shigar d'ayane sai rungememeniya ake tareda taka rawa wasu agefe sai shaye_shayen kayan maye suke

Subhanallah!

Mezamucewa ubangijinmu kan kiwon daya bamu.

Kana iya k'ok'arinka wajen ba y'ay'anka tarbiya wasu b'ata gari suna warwarema.

Allah kar kabarmu da iyawarmu kamana jagora wajen ba y'ay'ayenmu tarbiya.

Fitowa kawai nayi daga cikin hall d'in don idona bazai iya jurar kallon wannan iya shegenba.

Nafi awa tsaye awaje ina tunani yadda zan koma gida ga wajen da d'an karan nisa.

Jinayi an rik'emin k'ugu tare da fad'in

"fine baby ke bazaki shiga ayi rawar dake bane?"

Juyowa naye da sauri na tureshi tare da kwad'a mashi mari cikin b'acin rai.






โœ๐Ÿป *~UMMYN YSRH~*
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž

*YESMEEN*

๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž


*STORY & WRITEN BY:*
*UMMYN YSRH*


*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*


_KINCHANCHANCI YABO TA KO'INA DOLE IN YABA KUMA IN GODIYA DA FATAN ALKHAIRI AGAREKI_

*SIST HALIEYMERH AMEEN*
_ALLAH JA KWANA DA LFY MAI AMFANI ALLAH K'ARA D'AUKAKA YABAR ZUMUNCI_๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜


*inaba masoya wanna novel hak'uri na rashin jina da sukayi na kwana da yawa amin afwa kunsan jiki da jini๐Ÿ˜ฅ*



*35~40*

Fitowa tayi da sauri da nufin shiga kitchen don taji kamar miyarta na kamawa,bata kulaba ji tayi ta buge mutum,juyowa tayi don bata hak'uri,saidai kafintayi magana Hajiya Talatu ta rigata,
cikin masifa tace

"Tooow! Muguwa,y'ar bak'in ciki.shine kika taho aguje don ki bangajeni?
Kina bak'in cikin cikin jikina ko? Burinki ya zube muzama d'aya ,toh ta Allah ba takiba,keda haihuwa saidai kiga munayi,mun ajiye biyar gana shida yana hanya."

Ummah Habiba tace

"don Allah ki hak'uri bada niyya na buge kiba,miyace naji tana kamawa na shiga sallah shine na fito da sauri,amma ki hak'uri."

Sallama sukaji daga k'ofar falon da sauri Hajiya Talatu ta durk'ushe gurin tana rik'e ciki,tare da bubbuga y'ar yatsarta kamar mai nak'uda,lokaci guda ta fita hayyacinta.

Umma Habiba ta amsa sallamar tareda yima mai sallamar barka da zuwa saidai ko kad'an batabi ta kantaba,

"Subhanallah! Talatu meke faruwane?"

Cikin muryar wahala tace

"ina d'aki naji miya na kamawa a kitchen shine na duba na fito zan koma d'aki, shine Habiba ta fito ta nufoni gadan _gadan ya gulleni a cikina."

"ita Habiban!!?"

"eh,wai don meyasa zan tab'amata girki alhalin nasan baran girkina bane."

"toh!muguwa mai bak'in hali,y'ar bak'in ciki,duk tsiyarki sai jikana na fito duniya,idanma burinki cikin ya zube toh k'aryarki munafuka,duk abunda yasami cikinnan k'arshen zamanki kenan agidannan wallahi."

"wallahi bada sani na bugetaba Haj......."


"rufemun baki,tunda tasamu cikinnan kike bak'in ciki,zamuje asibiti yanzu adubata kuma Wallahi ina k'ara gaya miki akasami wani abu ya tab'ata abakin aurenki."

Kama Talatun tayi ta zaunarta kan kujera taje ta d'auko mata hijabi a d'aki sukayi gaba,juyawar da Umma Habiba tayi zatayi kitchen wani jiri ya d'ebeta ta zube k'asa.

Tana kaiwa k'asa

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment