Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bazan tafiba sai bayan andaura Aurena bayan bikin Aunty Zainab da kwana biyu ko uku saina tafi wallahi Abba inajin dadin zama daku sosai domin da ace bayanzune Auran Aunty Zainab ba banajin zan'iya tafiya nabarta domin munyi sabanda bazan'iya tafiya nabarta ba duk kanninsu sunji dadin abinda tafada Abba sai kallonta yake yana murmushi yace Safna Allah yaimaki albarka Amin Abba shidai Safna tana birgesa tinda jimawa tatashi tana kokarin fita Abba yatambayeta inazata kafin tayi magana Salim yayi murmushi Abba gurin Safwan zata tararrashesa duk kansu sunyi dariya kunya ta kamata tasunkuyar da kai Abba yace Salim kenan ai inaganin tamika tsaye nasan gurin Safwan zata to jeki tayi murmushi tayi tafiyarta har zuwa wannan lokacin Umma bata saki jikiba haryanzu da akwai damuwa sosai aranta Abba yakalleta tare da kiran sunanta Sadiya saida taji faduwar gaba da sauri ta'amsa na'am Abban Safwan yakamata komai yawuce kimanta da komai kikuma manta baya kigyara gaba amma kisani barin damuwa aranki wannan bazai zamemaki mafitaba dafatan kinfahimta ai Abban Safwan abinne da nauyi ga kuma kunya to yazakiyi Allah yakyauta yasa mudace Amin ya Allah

Safna tasami Safwan afalon kasa sai mafan fishi yake tabiyo tabayansa tarofe masa fuska tana murmushi yasa hannunsa yajanyota tagaba domin yasan cewar itace yazaunar da ita yana kallonta yanzu Safna shikenan kinyarda zaki tafi tawani zaro ido da sauri yaushe dan Allah dena wannan zancan to inazani nabarka lokacinma danake shakkar zansameka ko bazansameka ba natsaya atare dakai balantana ayanzu danake da tabbacin cewar kaine mijin da zan'Aura nanda sati daya saidai nakiraka da Angona to taya zantafi nabarka aibazan iyaba inanan daganan sai gidanka da yardar Allah aina fadama Abba cewar niba inda zani inanan tare da kai zama daram batafiya kai kanwata amma wallahi bakaramin dadi najiba Allah yabarmu atare Amin mijina yayi dariya tare dajan hancinta itama dariyar take komai yayi dai-dai sai dare su Mummy suka Tito zasu tafi sunyo masu rakiya harbakin mota duk kanninsu zuciyarsu cike take da farin ciki sunyi masu sallama suntafi Salim ma yamasu sallama yatafi yabi bayansu Mummy sun'iso tare sunshigo yaga gidan yadan jima suna fira sannan yamasu sallama yatafi yadawo gida ransa fari kal baya tare da komai face farin ciki dajin dadin yashigo saidai yasami falo bakowa kasancewar dare yayi yafara zuwa dakin Safna yasameta tana barci ya'isa inda take yasunbaceta tare da sanya mata albarka yamata addu'a sannan yafita

Yashiga dakin Nafisa yasameta kwance tana ganinsa tajuya masa baya tana fishi yayi murmushi yakarasa inda take yazauna kusa da ita sosai yarika hannunta yakira sunanta ssidai bata amsaba balantana ta'iya juyowa yasa hannunsa yajuyu fuskarta sunfuskanci juna yagirgiza mata kai dan Allah Nafisa karki hukuntani da rashinki kiyimin uzuri sannan kisaurari abinda zanfada maki idan yaso daga bisani saikiyimin hukuncin dakikaga yadace dani amma kafinnan dan Allah kiyi hakuri kinji eh naji amma yaya Salim maiyasa neta kiran layinka baka dagaba sannan kuma kai baka kiraniba yanzu kuma dakadawo inajinka kafin kazo inda nake saida kafara zuwa gun Safna hakan yana nufin tafini muhimmanci agurinka haba yaya Salim waimai yasa kakeyimin hakane Safna fa tana kasa dani kuma ita 'yace amma kafi bata girma akaina a'a Nafisa bahaka bane bara kiji mezanci mezaka fadamin ni wallahi jin Safna nake tamkar kishiyata domin kafi bata kulawa akaina tinda nahaifi Safna shikenan saika dena sona kabarni kadauki Safna a'a Nafisa taya zandena sanki kema kinsan fada kawai kike domin bazsiyuwuba ina sanki sosai sanda bazaiyuwu na'iya fadarsaba Nafisa kiyarda dani mana ina taki ssuraransa sai mita take tayimasa yarasa yazaiyi lokaci daya yayi mata kallon tsab yatsaida idansa kan bakinta dayaketa faman mita yajinjina kai bata ankaraba saijin bakinsa tayi cikin nata nanyaci gaba da tsotsar lebenta natsayin wani lokaci sannan yafitar da bakinsa cikin nata yakalleta yana dariya itakuma murmushi take ya'akai kikayi shiru danace kiyi shiru ai bakiyiba tayi ajiyar zuciya tare da fadawa cikin kirjinsa yaya Salim wallahi ins matukar kaunarka fiye da tinaninka ko yanda nakesan kaina Nafisa kenan ainima sanda nakemaki saidai kawai nayi shiru domin bazai faduba yanzu bari kiji dalilina nayin dare da kuma dalilin saka wayata silent lokaci daya yabata labarin duk abinda yafaru Ita kanta mamaki da Ikon Allah sunkamata harta gagara magana sai fari'a kawai take farin cikinta yabaiyana tatayashi murna tare dayimass fatan alkhairi

Zainab na kwance takalli Safna tayi murmushi Safna waibazakizo kikwantaba Aunty Zainab wallahi tinda nake bantaba kassncewa acikin farin cikiba irin nayau Da farin nasami yaya Safwan amatsayin miji abinda najima ina mafarki sai kuma wani farin cikin yakara shigata abinda bantaba tinaniba yaunaga Mummy da Dady gaskiya ina cikin farin ciki kuma wani abin farin cikin shine wanda duk natina dadin kamani yake shine kassncewarmu 'yan Uwa Mummy da Umma Uwa daya Duba daya wallahi wannan abun yamin dadin sosai araina bake dayaba Safna domin natabbata duk kanmu muna cikin wannan farin cikin saidai maki yafi namu yanzudai kizo kikwanta kinsan gobe kina da exam ta'amsa da to tatafi takwanta

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:56] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 3
1⃣8⃣
By

Fauziya Usman

Washe gari Safna nacikin shirinta takalli Zainab Aunty Zainab kinsan wani abu kuwa a'a saikin fada wallahi abinda nayitawa Nasir ne yake dawomin har inajin bankyautaba wallahi Aunty Zainab dazanhadu da Nasir ayau dana basa hakurin abinda nayi masa yanzu bansan ayanayin da yake kallonaba Zainab sai kallonta take Safna kenan wannan shi'ake kira ihu bayan hari ko kina tinanin zaki kara haduwa da Nasir gaskiya bana da wannan tabbacin to amma maiyasa bazaki nemi layinsa ba Aunty Zainab aikema kinsan banda number Nasir to saiki hakura da nemansa domin banajin zaki sake haduwa da Nasir to nidai ina fatan Allah yasake hadani dashi koda saudayane arayuwata domin nabasa hakurin abinda nayi masa takarasa shirinta tafito tagaisa dasu Umma tayi break fast sannan tatafi school

Salim kuwa baitafi office ba bayan sunshirya sunyi break fast zuwa karfe 11:00am yadauki Nafisa da Safna suka tafi gidansu Mummy sunshigo tare dayin sallama saidai bakowa sunzauna kamar na mintuna biyar saiga Mummy tafito daga kicin tagansu azaune tayi murmushi Salim barabanku yanzu kuke tafe eh Mummy ina kwana lafiya qlau Nafisa tagaisheta cikin girmamawa Mummy taji dadi sosai aranta tajanyo hannun Safna tana mata wasa Safna bakisanniba ko Nafisa tace yaya Salim nafa taba ganin Mummy bama saudaya ba yakalleta cike da mamaki a'ina kikaganta a asibiti lokacin da aka kwantar da Safna Mummy tayi murmushi tabbas nima naga fuskar gani Mummy tatashi ina zuwa kunsameni ina aiki aiki kuma Mummy eh aikinme tayi murmushi abincin break fast tanufi kicin Nafisa tabi bayanta tasameta akicin Mummy kibarshi zankarasa maki a'a Nafisa ayihaka daga zuwanki saiki fara da aiki a'a Mummy wallahi bazaiyuwuba ina zaune ina hutawa kekuma kina kicin kina aiki dan Allah kibarni nakarasa maki to nagode Allah yaimaki albarka Amin tafito tabarta takarasa komai tashiryashi kan tebur sannan tadawo tazauna Nafisa sannu da aiki lah bakomai Mummy lokacin Dady yasauko sungaisa sunyi break fast bayan sunkarasa Salim yace Dady zantafi Kano domin nasanar dasu Ummi to Salim Allah yakiyaye Amin Dady Mummy saina dawo Allah yakaika lafiya Yakima dawo dakai lafiya idan kaje kagaishesu Amin Mummy insha Allah zasuji Nafisa tayimasa rakiya harbakin mota tare da Safna yatafi saida suka fice sannan tadawo ciki tagyara gidan tas sannan takoma tadora girki farin ciki yakama Mummy sosai Dady ma yafita zuwa office

Safna ta'isa class ranta fari kal saiji take tamkar tafi kowa farin ciki aduniya Hafsat da Asma'u sai kalonta suke dama sauran yan class Safna farin cikin me kike haka wallahi Hafsat bazai baitanuba domin karamin abu baki yake iya baiyanawa babba kuwa saidai kawai akallesa domin baki yayi kankanta da ya'iya baitanasa to koma miye Allah yasanya alkhairi Amin ya Allah bayan sungama exam kafin afara fita Safna tatashi tafara raba invitation taba kowa dake class din maza da mata duk kanninsu mamaki yakamasu domin banda Asma'u da Hafsat bawanda yasan da zancan Auranta aikuwa yan class sunshiga tsokanarta Amarya-Amarya Bashir yasamesu tsaye suna fira yamasu sallama sun'amsa yace Safna wai da gaske Aure zakiyi Allah yasa ga Bashir ga shaidanan kagani kuwa haba Safna maiyasa zakiyimin haka kokinasan kice dani bakisan cewar inasankiba nasani Bashir domin sanin hakanne yasani nanisanta kaina dakai domin bana bukatar alakar so takullu atsakaninmu kasancewar ni inada wanda nakeso hakama banasan kayi kuka dani wannan dalilinne yasa nadena kulaka sosai tindaga lokacin dana fara fahimtar kana sona Bashir kayi hakuri dominni ayanzu banda banbanci da matar Aure yajuyo gasu Hafsat Asma'u nizan tafi sai gobenku to Allah yakaimu Amin tajuya tayi tafiyarta Bashir yabita da kallo Hafsat tagirgiza kai Bashir karka batawa kanka rai dama lokaci abanza domin Safna tajima dazama matar wani kabar komai yawuce kamanta da komai domin inaga hakan shizaifiyema duk kabsu sunkama hangar gida Safna daga makaranta kaitsaye gidan Salim tanufa saidai tasami gidan arufe lokaci daya tinanin zuwa gidansu Mummy yazomata kaitsaye tanufican ta'isa gidan tashigo tasami Mummy da Nafisa saifira suke tamkar sunjima da sanin juna Mummy tayi murmushi maraba da Safna yauwa Mummy sannunki da zuwa daga ina haka naganki kinada alamar gajiya tayi murmushi daga makaranta nake Allah sarki toya makarantar Alhamdulillah yasu Zainab suna lafiya tana gaisheki duk dacewa batassn nazoba Allah sarki ina ansawa sai lokacin tagaisa da Nafisa Aunty Nafisa ashe kinanan wallahi daga gidanku nake nassmu bakwanan dama gurin Kawata nake yanzu tana ina naga bangantaba tobakizo asa'aba domin kawarki batanan tayi tafiya ita da yaya Salim tafiya kuma inasuka tafi Mummy takalketa Safna ce kawarki eh Mummy tayi dariya lallai Safna akwaiki da shirme kintaba ganin inda da Yakima aboki a'a to taya 'ya zata dawo kawa kemadai Mummy kyafada domin ni da yaya Salim munfada mata yafi akirga amma sam yaki yards kinga Mummy nifa saida nafara saninta amatsayin kawa sannan nasanta amatsayin 'ya dan haka kar awani hanani kawance da ita Mummy taje da kanta takawo mata abinci Nafisa tace Mummy da kanji eh Nafisa habadai Mummy yanzu gani ga Safna amma zakitafi da kanki a'a Nafisa wallahi bakomai aini nasa kaina karfa kimanta Safna ce Auta Yar lele tafada tana dariya kuma Nafisa kiduba kiga aikin dakikai agidannan kuma kawoma Safna abinci saina saki dan Allah kibari haka kihuta Mummy aini bazankawo ma Safna abinciba domin danasan zatazo dabanzanyi girkin da itaba saidai tashiga tagirka Nafisa Auta face tadawo da kallonta ga Safna kinga Safna kici abinci kinji tayi murmushi to Mummy taci abinci bayan takarasa takai kayan abincin kicin tadao suncigaba da firarsu

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:57] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 3
1⃣9⃣
By

Fauziya Usman

Kano

Salim yayi nasarar isowa gidansu Ummi lafiya yashigo tare dayin kyakkyawar sallama Larai ce ta'amsa masa kasancewar itakadaice afalon tashiga yimasa sannu da zuwa tataresa da fari'arta shima fari'ar yake yazauna sungaisa ta tambayesa ya Nafisa tana lafiya to madallah Safna yau bamagana Aunty Larai hala ina Ummi Umminka yanzunnan tashiga daga ciki amma insha Allah bazata jimaba zata fito aikuwa bawani jimawa dayawa tafito mamakin ganin Salim yakamata tayi murmushi Salim kaine eh Ummina maraba sannunku da zuwa yahanya yauwa Ummina hanya Alhandulillah ina Nafisa tana lafiya tace agaisheku Safna tayi gurin Ummi tagaisheta Ummi takalleta tana dariya Safna yan mata ina mamarki tana gida kikazo abinki kikabarta agida eh Ummina ina Abbana Abbanka baidawoba amma nasan insha Allah yana kusa da gida bata karasaba sukaji sallamarsa sun'amsa masa yace Salim cike da mamaki na'am Abba dama yau zakashigo shine Umminka bata fadaminba a'a Abba karkaga laifinta domin itama banfada mataba koda safe damukai waya bansanar da ita zanshigiba to dafatandai lafiya eh lafiya qlau to madallah Safna yau bagaisuwa Salim yakalleta Safna bakigaida Abbana ba tatafi gurinsa tagaishesa yadauketa yadorata kancinyarsa Abba shiga ciki yashirya sannan yafito sunci abinci bayan sunkarasa sundawo falo Salim yace Abba dama nazone domin nasanar daku wani abu to Salim bismillah munajinka nanyabasu labarin komai nagame da iyayensa lokaci daya mamaki da ikon Allah yakamasu suntayashi murna sosai tare dayimasa fatan alkhairi yakuma fada masu zancan Auran Safna sunce aizasu shiga da yardar Allah Ummi tace Salim dafatan bazaka dena kulawa damuba kasancewar kagane iyayenka yayi murmushi tare da girgiza kai haba Ummina nikuwa wane irin mutunne dazanyadaku dan takamar nagane iyayena aikunfi da haka kunfi karfin watsarwa agurina dominku harkullum harkoyaushe iyayena kuke biyayya agareku wajibina ne to Allah yama albarka Amin Ummina sai yamma sosai sannan yafito yayi masu sallama tare dayimasu tini akan bikin Safna karka damu Salim insha Allah zamu shigo to Allah yayarda Amin ya Allah Safna konabarki gurin Ummi tagirgiza kai alamar a'a Safna yaukuma bazaki kwana ananba to Allah yakiyaye kigaida mamarki Salim kagaidasu Mummy kafin mushigo to Abba zasuji insha Allah sunyi sallama yatafi

Kaduna

Safna ganin yamma tayi yasata tashi domin tafiya Mummy nizantafi to Safna sai yaushe tayi murmushi Mummy sai zuwa jibi saboda gobe bazanfito exam ba sai 04:00pm kuma kinga gobe ake sister day shima karfe 04:00pm ne to Allah yabada sa'a Amin Mummy tayi musu sallama tayi tafiyarta bata wani jima da tafiyaba Salim yadawo yashigo tare dayin sallama Safna da gudu tayi gurin mamarta Mummy tayi dariya Safna auni bazakizo gurina ba sunyi dariya Nafisa tadauketa Safna kundawo eh Salim kundawo eh Mummy andawo lafiya yahanya lafiya qlau yasu Ummi duk suna lafiya sunce agaisheku to muna amsawa sannu da zuwa yaya Salim yauwa Nafisa yasu Ummi suna lafiya sunce agaisheki ina amsawa Nafisa tatashi takawo masa abinci da juice tare ruwa yakalleta yana murmushi nagode Nafisa itama murmushin take bayan yakarasa yace Mummy wai ina Dady inajin yau ayuka sukayimasa yawa baidawoba Safna ma batajima da tafiyaba Allah sarki ashe tashigo eh tajima anan batajima da fitaba kashigo ok sundanjima suna fira sannan Abba yadawo sungaisa Salim kadawo lafiya yahanya lafiya qlau hanya Alhamdulillah to yasu Abba da Ummi suna lafiya suna gaisheku muna amsawa aizasu shigo bikinsu Zainab to Allah yanuna mana Amin sunjina suna fira daga bisani su Salim sukayimasu sallama sukatafi bayan sun'isa gida Nafisa taje tashinfide Safna tare dayimata addu'a tafito tanufi dakinta tayishirin kwanciya Salim bayan watsa ruwa yashirya yazo yakwanta suna kwance Nafisa tace yaya Salim natambayeka wani abu eh inajinki waiyasu Ummi sukaji dama fadamasu su Mummy suna araye gaskiya sunyi farin ciki sosai suntayani murna matuka saidai Ummi tanunwmin karna manta dasu domin zuciyarta tana nuna mata cewar zanbarsu tinda yanzu nagane iyayena na aswli nafadamata bazantaba barinsuba har'abada kuma bazandena kulawa dasuba amatsayin iyayena Allah sarki Ummi nikaina nasan dole zataji wani abu aranta

Safna ta'isa gida tashigo taji gidan sai shiru ketashi kaitsare tanufi dakinsu bataga Zainab ba tofa ina Aunty Zainab tadauki wayarta takirata hellow Safna ya'ake cikine qlau Aunty Zainab kina ina kindawone eh nasamu bakyanan eh nafita ne tare da Hafiz nanbada jimawaba zandawo insha Allah to Allah inagaidashi zaiji saina dawo to adawo lafiya Allah yasa Amin ta'ajiye wayar bayan mintuna biyu yashiga kiran layin Safwan ringing biyu yadaga Amincin Allah yatabbata agareka yardar Allah da kariyarsa suka sance atare dakai yayana kuma mijina Amin kanwata kana ina kindawo ne eh nadawo saidai nassmi gidan yayi duhu narashinka kadawo domin gidanmu yahaskaka nikuma nakasance acikin haske Safna kalamanki suna zuzutani wallahi Safna da bansameki amatsayin mataba dana shiga uku nalalace niyakamata nafadi haka bakaiba yanzudai yaushe zaka dawo domin idanuwana Suna bukatar ganinka karki damu yanzunnan zandawo tosaika dawo kafinnan kakulaman da kanka toyayi saikin ganni

Umma tafiro falo tasamu bakowa taduba agogo taya karfe biyar dakusan rabi tace to ina Safna kotana gidan Hajiya ne tabbas akwai yuwuwar haka domin batakaiwa irin haka bata dawoba tana cikin tinani Safwan yayi sallama ta'amsa masa yakalleta Umma tinaninme kike haka tayi ajiyar zuciya dama Safna ce naga tajima bata dawoba shine nake tinanin kotabiya ta gidan Hajiya yayi murmushi Umma ai Safna tana gidannan tinda jimawa Allah sarki aini bansaniba ganin bangantaba nazaci bata dawoba tokirata taci abinci ya'amsa dato yatafi yasameta kwance kan kujera yashigo yana murmushi harya iso kusa da ita tataresa da murmushi sannu da dawowa yayana yauwa kanwata dafatan kina lafiya lafiyata tana tare da taka farin ciki na yacika yakammala tinda nassmeka amatsayin mijin Aurena Safna kenan nikuwa naceme yaya safwn aiki kariga kagama magana tinda harka iyafurta Kalmar so agareni kuma kazabeni amatsayin mata inagodiya abisa hakan sai kallonta kawai yake yana dariya toyanzudai tashi muje kici abinci domin nassn tinda kikadawo baki sakawa cikinki komaiba a'a yayana nakoshi niyanzu banajin yunwa yakalleta dakyau kinfara ko maikoma nayi haba kanwata maiyasa ke akullum saikinyi gardama yayincin abinci kinga tashi mutafi kick abinci ko mubata da sauri tarufe masa baki da hannunta tare da girgiza masa kai dan Allah yayana kadena fadar hakan kaji harzuwa wannan lokacin hannunta yananan kan bakinsa yawani rufe ido tare da sunbatar hannunta da sauri tajanye hannunta tana murmushi shima murmushin yake idan kingama sai mutafi to mutafi ok

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:57] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 3
2⃣0⃣
By

Fauziya Usman

Sunfito sunsami Umma kai afalo Safna tatafi tagaisheta ta'amsa Safna ashe kindawo eh Umma Allah sarki aini bansaniba saida Safwan yake fadamin eh Umma lokacin dana dawo nasami falo bakowane shiyasa shima yaya Safwan yawa nayi dashi toya exam Alhamdulillah to Allah yataimaka yabaki sa'a Amin Umma to atafi taci abinci Allah yaimaki albarka Amin Umma tatashi shikuwa Safwan sai wani dadi yakeji aransa suna cikin cin'abinci Zainab tashigo lokacin Umma tashige ta'isa inda suke sannu da zuwa Aunty Zainab yauwa yaya Safwan ananan tare da Amayar jibi eh Amaryar gobe sunyi dariya Safna na'am Hafiz yana kiranki yana awaje tatashi yayana zantafi nadawo to adawo lafiya tayi murmushi sunfita sunsamesa tsaye ajikin mota yaya Hafiz ina wuni lafiya qlau ya hidima yashirye-shirye da fama da jama'a duka Alhamdulillah to Allah yataimaka Amin Safna kinmin laifi maigirman gaske laifi kuma yaya Hafiz eh nikuwa wane irin laifi na'aikatama yaya Hafiz yayi murmushi Safna laifin dai shine maiyasa bakifadamin cewa kema Amarya bace tayi dariya yaya Hafiz bari nayi Aunty Zainab tafadama aitafadamin zaki Auri yaya Safwan kice yanxu kinzama Auntynmu da sauri tawani zaro ido tana kallansa yaya Hafiz dan Allah rufamin asiri to Allah yasa alkhairi Amin ya Allah sundan jima sannan sukayi sallama yatafi sundawo ciki dawowarsu keda wuya Abba yadawo sunyi masa sannu da zuwa ya'amsa yatafi dakinsa sundan jima suna fira sannan suka tafi suka kwanta

Washe gari da safe suna karasa break fast iya karfe takwas 08:00am suka fita Safna tafita da motarsu ita kuma Zainab Habu yadauketa Zainab gidan Asiya tanufa domin acan zasu hadu da kawayenta domin tafiya gyaran jiki da sauran hidimarsu ita kuma Safna kaitsaye gidan Salim tanufa tasami kofar arufe tabuga kamar sau biyu zuwa uku Nafisa tazo tabude mata tashigo sungaisa Safna yau kuma tafiyar safe ake wallahi kuwa ko school zaki tafi a'a nazone nadauki Kawata mutafi ayimana lalle da gyaran kai zuwa najiki gaba daya kinsan zuwa 02:00pm inada exam shiyasa nayi fitar safe Safna kenan kice kunshirma biki harda wani gyaran jiki to kardai kufi Amarya kyau habadai Aunty Nafisa mu'mun'isa aikema kinsan bazaiyuwu mufi Amarya haduwa ba kokinmanta kyan Aunty Zainab ne a'a kodaya amma naga kedinma kyakkyawa ce sannan kuma gaki Amarya tonaji nakuma yarda yanzudai kiramin Kawata aibatashi daga barciba tanacan tare da yaya Salim suna barci kuma bazaiyarda natashetaba aibasai kinkai garesaba nidinma bazanyarda kitashetaba tofa aikuwa jira yaganki eh nayarda wannan bazai zama damuwaba toshikenan bara nashiga kicin ok bara natayaki tatayata sunyi abincin break fast sunshiryashi kan tebur sundawo falo sunsamisu Safna mamaki Yakama Salim naganin Safna tafahimci hakan daga kallon dataga yana yimata takaraso inda yake inakwana yayana lafiya qlau Safna yau tafiyar safe kike eh wannan tafiyar ta kawatace nazo daukarta mutafi gyaran jikine tofa kice abin na manyane yaya Salim dai kodaya yarama sunayi ire irenmu toyayi yaushe zaku yanzuma zamu iya tafiya bayan tayi break fast damacan ita nake jira toshikenan suntashi sunnufi guri cin'abinci bayan sunkarasa Nafisa tagyarawa Safna sannan suka tafi gidan lalke suka fara zuwa bayan ankarasa masu sukayi gurin gyaran kai dana jiki anyimasu komansu iri daya domin sunmayi tinanin Uwa da 'yane karfe 01:00pm suka dawo tadan zauna kadan zuwa karfe 02:00pm tanufi gida domin shirin zuwa makaranta karfe 03:30pm lokacin da aketa shirin tafiya gurin biki lokacinne Safna tafita zuwa makaranta tanashiga tasamu har'anfara exam abin yabata mamaki sosai domin lokacin baigama cikiba haka tazauna tafara baifi mintuna arba'inba takarasa exam dinta tare tafito dash Asma'u basuyi wani surutuba sabida tana sauri tadai tambayesu kozasu shigo sun'amsa mata da eh insha Allah to saikunzo tayimusu sallama tatafi kaitsaye gurin maidinki tanufa takarbo dinkinta dana Safna tanufi gidan Salim domin tashira atsanake kasancewar gidansu Umma yacika da yan biki tana'isa tasamu su Salim zasu fita Aunty Nafisa sai ina Safna kemadai kinsman gurin sister day zamu tonaji nidai kubarmin Kawata natafi da ita sunbar mata ita sunfito sunyi tafiyarsu sarna tafada babdaki tayo wanka tafito mai kawai tashafa tasaka kayanta tasama Safna dinkin datayi mata irin nata dinkinma iri dayane tadauketa sunyi gurin kwalliya acan gurin bikin kawayen zsinab sai tambayar Safna suke shikansa Hafiz tambayar Zainab yake ya'akai Safna haryanzu batazoba wallahi Hafiz nima bansaniba nadaisan tana da exam to Allah yasa lafiya Amin

Safwan yana tare da Salim amma gabadaya hankalinsa baya jikinsa yana gurin Safna yashiga kiran layinta yana ringing amma ba'adagawa yakira kamar sau biyar amma duk ba'adagaba Salim yalura yanayinsa yadan sauya yashiga tambayarsa Safwan lafiya kuwa to dasauki dai maiyafarune wallahi layin Safna nakira har sau biyar amma bata dagaba shine nake tinanin ko lafiya kaga karwannan yadameka domin Safna tana cikin koshin lafiya kawai hidimace tayimata yawa kasan tayi exam yau tana dama da gajiya to Allah yakawota lafiya Amin bayan ankarasa masubkwalliyar sunyikyau sosai komansu iri daya harjaka da takalmi yankune da sarka Hadi da awarwaro komaidai iri daya hakan tasa sai sukayi yanayi daya da juna tamkar Uwa da 'yarta sunfito sunkama hangar zuwa gurin biki Safna takalli Safna karama takirata Kawata na'am Aunty Aunty kuma eh maiiyasa kikakirani da Aunty Dadyna yace narika kiranki da Aunty dominke Auntyna ce nima kidena kirana da kawa kiika kirana Safna ko Baby tayi murmushi to shikenan zanrika kiranki da baby yamaki eh yamin tokinsan mainakeso dake a'a idan muna is a gurin biki duk abinda nayi toshinakesan kiyi kinji eh kinfahimci mainake nufi eh Aunty yauwa Yar albarka sunkaraso sunshigo tindaga nesa Nafisa tahabgesu tayi murmushi tare da fadar masga Allah ganin yanda taketa murmushi yasa Salim kallon inda take kalla yahangi su Safna sai waya tafiya suke cikin kasaita lokaci daya yanunawa Safwan kallo daya yayi mata tatafi da zuciyarsa saiji yake tamkar yahadiyeta dan so sai wani murmushi yakeyi tamkar dansu ake bikin sunzo sunwuce tagabansu batare da ko kallansu ba balantana su'iyamasu magana Safwan yace a'a Yakoma haka sunwuce tagabanmu basuko kallemuba balabtana su'iyamana magana Safwan kenan wannan kuma wani takune sukazo mana dashi saimusaka ido muyi kallo danganin abinda suke nufi da hakan sun'isa gurinsu Zainab sungaisa kaimasha Allah Aunty zsinab kinshakyau sosai yaya Hafiz inatayaka murnar samun Aunty Zainab amatsayin mata inagodiya Safna Aunty Zainab kema kinyi dace da samun miji irin yaya Hafiz Allah yakara dankon so da kauna Amin Safna ya'akai kikajima bakishigoba mutane da dama

Please Login or Register in order to submit comment