Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sakinta gaba ɗaya ta faɗa saman,
Jiƙaƙƙen yashin dake wajan, gani yake kamar tana sani take zare masa ido, a fili kuma ya lumshe idanunsa tare da faɗin.

"Kamar wani tafi ido"
Ya faɗa yana mai ɗaukan babban kifi tare da yin gaba Sweet ma kifi ɗaya ta ɗauka ta biyo bayansa.

Dafe kai Julde tayi abinka da kai babu gashi, Idanunta ne ya cika da hawaye sosai taji zafin faɗuwar da tayi ko kuma tace ya yar da ita,
Baki ta murguɗa a fili tace.
"Wayyoooo kai na"
Ta faɗa tana runtse idanunta, ganin zaman sam ba zai mata ba ya sanya ta miƙe tare yin alwala duk ba wani iyawa tayi ba,
Sallah tayi kana ta zauna a wajan tana mai jin yunwa ga kuma ciwon da ƙirjinta yake mata.

Bayan yayi kyasto, ya haɗa dotsen wuta da wani a saman ɗan busassun itacen daya samu, nan da nan wuta ta tashi,
Faɗaɗa fuskarsa yayi da Murmushi yana bala'in son tsuntsaye da kuma irin wannan halittun, kifin daya suke a cikin wani ƙaton sanda ya ɗauko,
Kana ya ɗura saman wutar ya fara gasawa,
Almost 20minutes kafin kifin ya gasu sai tiriri yake yayi jajir dashi, gashi ƙato mai tsuka da yawa,
A saman wani ƙaton ganye ya ajjiye kifin kana ya fara ci cikin nutsuwa, sweet ma baki ta sanya ta fara yagar wanda ya sanya mata,
Sai da yaci sosai yabar raguwa kafin yaje yasha ruwa,
Gyara tsaiwa yayi tare da ɗaukan sweet ya fara duban hanyar da zaibi domin ya isa cikin Rugar Mahinjo a yau ɗin nan,
Motsin da yaji a bayansa ya sanya ya juya da sauri ganin Julde tsaye fuskarta cike da hawaye,
Ya sanya ya ɗauke idanunsa da sauri yana mai taɓe bakinsa,
Julde kowa ƙara banza hanci tayi saboda ƙamshin data ji ya sanya cikin siririyar muryarta tace.

"Zanci kifi, zaka sammin ko?"
Zare ido yayi yana mamakin yadda take iya fahimtar wani abun Kamar ba Makauniya ba, tsaki yaja yana Lumshe idanunsa kafin a ransa yace.
"Witch"
Ya faɗa a taushashe cike kuma da gajiya, ganyen ya ɗauka ta cilla mata saman ƙirjinta, da sauri ta ɗauka tana sauke numfashi da kuma Murmushin jin daɗi,
Zama tayi tare da tanƙwashe ƙafafuwanta, ta fara yagar tsukar kifin tana kaiwa ɗan ƙaramin bakinta,
Janye idanunsa daga kan guntun bakin nata, wata dabara ce ta faɗo masa, a hankali yayi baya yana mai shafa ƙirjinsa magana yake sunyi amma sam ya gaji da surutun wannan mai bakin akun,
Yana lumshe idanunsa tare da motsa bakinsa da ƙyar yace.
"Heyyy blind ina ne Mahinjo!!!?"
Ya faɗa yana mai ɗan ɗaga Murya tare da lumshe idanunsa,
Ambaton sunan Mahinjo da yayi ne ya sanya ta tsaya da cin kifin Jikinta ya ɗan ɗauki rawa,
Sai kuma a lokacin ta tuna da shanun da aka bata kiwo,
Cikin sauri ta miƙe tana jujjuya Idanunta kafin a hankali ta sulale ƙasa cikin Muryar kuka kuma tace.
"Na buni, dan Allah ba kaga shanuwa ba? Wayyoooo Madibbo shikenan zasu kashe ni an kwashe masu shanu"
Da mamaki yake binta da kallo ko kalma guda na maganarta bai fahimta ba,
Tsaki Yana cikin ɗaga murya haɗi da tsayawa ya koma Abu Maleek ɗinsa wanda yake na asali bawai yanzu da aka sanya ya zama mahaukaci ba yace.
"Noi inde wuroman?" (Ya sunan garin ku).
Ya faɗa in a serious tone.
Cikin firgici ta tarin tsoro tace "Rugar Mahinjo"
Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ya sauke yana mai ɗan jin daɗi dan ko babu komai sai ta rama masa taimakon da yayi mata cikin haɗe fuska kamar tana kallonsa yace.
"Let's go"
Ya faɗa yana yin gaba, dafe ƙirji tayi tana sakin kuka kafin tace.
"Dan Allah ka barni a nan wallahi kashe ni Arɗo zaiyi"
Haɗe fuska ya ƙarayi saboda yarinyar ta fara bashi ciwon kai, haushi da kuma takaicin tsayawa inda take ma yake,
Gyara tsaiwa yay kafin cikin kakai murya yace.
"Su kashe ki mana, ni dai ba ruwana saikin raima min abinda nayi maki dan kiji"
Kuka ta sanya masa shi kam ko a jikinsa juyawa yayi ya ɗauki sweet kana kamar mai raɗa yace.
"Muje"
Bata taɓa tunanin bashi da kirki ba sai yanzu, da alama shima daga rugar yake saboda taji yayi fulatanci,
Kanta ta sunkuyar ƙasa kafin tace "bani da sanda ai, bazan iya tafiya ba"
Ta ƙare maganar Idanunta na zubar da hawaye,
Ba tare daya kalleta ba domin shi ya ƙosama yabar inda mayatacciyar yarinyar take, wata igiya ya ɗauka tare da cilla mata yana ɗan yatsuna fuskarsa yace.
"Tied your hand"
Sharrr hawaye ya ƙara sakko mata ta ɗaure hannu kuma? Dabba ce ita da zata ɗaure hannayenta, ganin tana ɓata masa Lokaci ne yasa ya ɗan ƙara daka mata tsayawa wanda shima da kansa sai daya dafe kansa sabida tsorata da tsawar da yayi,
Da sauri ta riƙe igiyar duk Jikinta rawa yake kana ta naɗa a hannunta idanunta na zubar da waye,
Shima yayi hakan ne sabida bai tsayawa kusa da ita bare har ya yi tunanin riƙe mata hannu,
Tana gama ɗaura igiyar ne shi kuma ya riƙe bakin igiyar tare da fara tafiya da sauri yana janta da sabida igiyar dake ɗaure a hannunta.
A haka suka fara tafiya domine isa Rugar Mahinjo.

A can cikin rugar kowa Arɗo ne da Barkido sai kuma Lamiɗo zaune, suna tattaunawa gyara zama Lamiɗo yayi kafin Yace.
"Na aikata da mutane a sirrince domin su duba min abinda ke faruwa a sakamakonsa harbin da mukaji, sai dai abin mamaki gaba ɗaya Shanuwanmu suna nan amma an nemi Julde an rasa"
Da sauri Barkido ya kalli Lamiɗo tare da faɗin.
"Kamarya an nemeta an rasa? Kana nufin ba'a ganta ba ko mene? Tayaya za'a ga Nagge amma ba'a ga mutum ba"
Kallon Barkido arɗo yayi sabida ya gama fahimtar ɗan nasa cewa ya faɗa tafkin soyayyar Julde, shi kam rashin Julden ba ƙaramin daɗi yayi masa ba,
Rashin nata kuma ya ƙara tabbatar masa da cewa Tabbas burinsa zai cika koma yace ya cika, dan matsalar sa ɗaya Madibbo do ya gama da Yakumbo ya gama da Madibbo mai uwa a gindin murhun ma ya gana da shafin ta,
Gyaran murya yayi kaɗan kafin ya kai dubansa ga Barkido yace.
"Meye damuwarka? Mene tsakaninka da ita, daman ai burinmu ace yau babu ita, domin idan har tana raye Tabbas burinmu bazai taɓa cika ba, kafi kowa sanin yadda muka sha wahala kafin mu kawo iya zo, dan haka ina gargaɗinka idan ma wani abu zuciyarka take kissima ta daina, Aradon Allah ina ci maka mutunci"
Arɗo ya faɗa yana nuna Barkido da hannunsa, kafin kuma ya fuskanci Lamiɗo yace.
"Wane mahaukacin daya Shigo cikin jejin?"
Lamiɗo ya kalli Arɗo kana yace "Barkido babu waje"
Tashi yayi zuciyarsa cike fal da tarin baƙin ciki, tattaunawa sukai kafin ko ya tashi ya nufi makwancinsa sabida dare yayi, gari yayi tsitt.

Ganin duhu yayi sosai ya sanya Julde zamewa a hankali ta kwanta tana sauke numfashin wahala,
Shi kansa Abu Maleek ya gaji tunda suka taho babu abinda yake tsayar da su sai sallah, gashi dare yayi duhu ba zai sanya suci gaba da tafiya ba,
Bisa Dole shima ya nemi waje ya kwanta yana sauke ajjiyar zuciya tare da rufe idanunsa,
Julde numfashi ta ƙara ja da ƙyar tana riƙe da saitin zuciyarta dake wani irin harbawa sabida tsananin ciwon da ƙirjinta yake,
Cikin fidda sauti da kuma da kuma tarin wahala da kuma ciwon dake ƙirjinta ta cije bakinta, tana murje ƙirjinta dake mata wani iri zafi da raɗaɗi,
Zame idanunsa yayi daga kanta yana jan tsaki a ransa yake faɗin.
"Guntuwar Yarinya sai ƙaton nono mtwss!!!"
Ya faɗa yana mai kwanciya a saman wata ciyawa dake jiƙe da ruwa.

Washe gari da sassafe sukaci gaba da tafiya ba tare da sunci komai ba,
Tunda suka tafi babu wanda yace komai, yana janye da ita da igiya wajan sallar Zhur sukaiwa Rugar Mahinjo tsinke,
Lokacin gaba ɗaya kowa yana cikin Rugar ana hutawa tare kuma da tarin Alhinin rashin ganin Julde wanda tsirari daga cikinsu suke.
Cikin rugar Abu Maleek yabi da kallo yana kalla kuma yaji kansa ya sara da ƙarfin gaske, zuciyarsa ta harba da ƙarfi,
Hakan nan ya samu kansa cikin tarin fargaba kasancewar sa ba komai ne kai bayyana a fuskarsa ba ya sanya ko alamun tsoro bai nuna ba,
Fitowar Lamiɗo kenan daga cikin bukka idanunsa ya sauka akan Julde da sauri yace.
"Arɗo!! Arɗo!! War, War Arɗo"
Jin Muryar Lamiɗo ne ya sanya Jikinta ya shiga rawa nan da nan idanunta ya fara zubar da hawaye shkknan yanzu zasu kasheta, abinda take rayawa a zuciyarta kenan,
Yana yana cikin bukka hannunsa riƙe da wata paper wacce babu wanda yasan da ita wajansa, sabida babu wanda ya iya karatu bare rubutu a cikin Rugar.
Yana tsaka da duba paper ne yaji Muryar Lamiɗo yana kwala masa kira da dukkan muryarsa, da sauri ya ɓoye paper kana ya fito,
Abinda idanunsa suka gani ne ya sanya shi zare ido,
Julde a hankali tayi bayan Abu Maleek tana ɓoye fuskarta domin a yanzu shi kawai take tunanin zai taimaka mata,
Gyara Arɗo yayi kafin yace.
"Ardon Allah ƙarya kake, shaiii kaci Ubanka ka biya mu Naggen mu, Lamiɗo kawo mana ita nan ka tara mana jama'ar gari"
Jin haka ya sanya Julde sanya ihu a gigice kuma ta sanya dukkan hannayenta a saman ququn Abu Maleek tare da ɗura fuskarta a tsakiyar bayansa ta ƙanƙamesa, da sauri ya runtse idanunsa sabida sarawar da kansa yayi masa ga wata halbawa da zuciyarsa tayi masa,
Kasa motsawa yayi da sauri kuma yasa hannunsa ya dafe kansa saboda yadda yaji Julde ta ƙara....


*ABU_MALEEK NA KUƊI NE KIJI TSORAN ALLAH KADA KI TAFI LAHIRA DA ABINDA BA NAKI BA, IT'S 500 VIA 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK 08119237616*





*_Nimcyluv 25-26_*


Manne Jikinta a bayansa, tare da ƙanƙamesa sa sosai, hawaye na zuba daga cikin Idanunta, yayinda dukkan Jikinta ya ɗauki rawa tamkar mazari,
Abu Maleek kam abun ne yazo masa a bazata, jin yadda Julde ta rungomesa tana manna fuskarta a bayansa ne ya sanya shi janye idanunsa a hankali tare da rufe su ruff, ya shiga sauke numfashi a hankali yana mai ɗan taune jajayen laɓɓansa,
Arɗo dake tsaye ya ƙara duban Lamiɗo yace.
"Maza ka ɗauka shi ka kawo min shi nan"
Ya faɗa yana mai kallon Abu Maleek kafin Lamiɗo yayi magana Arɗo ya ƙara cewa.
"Kai mahaukaci mene ya kawo ka rugar Mahinjo, me kazo yi a wannan rugar, ko kuma kasan wannan yaron Julde ne?",
"JULDE!!!?"
Sunan da Abu Maleek ya ƙara maimaita wa a cikin zuciyarsa kenan, to mene ma'anar wani suna Julde ne?
A zahiri kuma raunatattun idanunsa ya buɗe tare da saukesu akan Arɗo, ƙara ware idanunsa ya yi akan Arɗo fari ne tass ɗan shawalwali dashi, baya da wani jikin arziƙi sai dugun wuya,
A ƙallah zai iya kaiwa Shekaru arba'in, janye idanunsa yayi ba tare kuma da yace komai ba, domin shi ba wannan yake buƙata ba,
All abinda yake buƙata shine hanyar da zata sada shi da Birnin Bera wannan shi ne,
Lamiɗo ne kai tsaye ya nufi inda Julde take manne a bayan Abu Maleek tare da rufe fuskarta da tsakiyar bayansa, sai tsuma Jikinta yake,
Yana zuwa ya miƙa hannu zai jawo ta tare da rabata da jikin Abu Maleek ance.
"Wait"
Jin sautin zazzaƙar Muryar mai cike da ilhama da kuma tarin nutsuwa da kamewa ya sanya, Lamiɗo tsayawa cak, sosai Muryar ta dakar masa zuciya ta sanya shi tuna wata makamanciyar Murya data huce a shekarun baya,
Da sauri Lamiɗo na ya ɗaga idanunsa ya kalli Abu Maleek cikin azama kuma ya janye idanunsa dan baya jin zai iya, ci gaba da kallon ƙwayar idanunsa sai zuciyarsa ta buga,
Ya kuma janye idanun ne dalilin wani tarin nutsuwa da kuma kwarjinin daya hango a cikinsu,
Tsoro da fargaba duk ya cika zuciyarsa, saukar Muryar Abu Maleek kuma ya haddasa masa wani irin faɗuwar gaba, sosai Muryar tayi masa kama data wani can a shekarun baya,
Cikin son dakewa da kuma mazewa Arɗo yace.
"Haii yaron arziƙi wasa ina maka, Hai ka fito daga Bayan wannan Mutumin"
Ya faɗa yana sakin Murmushin takaici, domin ba ƙaramin cika masa ido Abu Maleek yayi ba, baya jin zai iya yiwa Julde wani abu akan idanunsa,
Jin abinda Arɗo ya faɗa ya sanya ta sakin ajjiyar zuciya a hankali ta shiga zare Jikinta daga bayan Abu Maleek idanunsa a Lumshe tana shaƙar wani fitananan ƙamshi daya kawowa hancinta ziyara,
Kallon Arɗo Lamiɗo yayi da alamar "ya haka?" Girgiza kai Arɗo yayi kafin ya juya da baya yana faɗin.
"Noi indema?" (Ya sunanka)"
Sarai Abu Maleek ya fahimci maganar kuma ya san dashi ake, sabida yana ɗan jin fulatanci ba tare da kowa ya sani ba ake koya masa,
Na zai manta sanda Hamida Zubaida take koya masa ba, akwai sanda Oumuu-Ayman ta koya masa,
Lamiɗo ne yayi murmushi yana kallon Abu Maleek cike da mamaki gashi dai sak mahaukaci amma sam muryarsa ba tayi kama data mahaukaci ba,
"Muje daga ciki"
Lamiɗo ya faɗa yana mai ɗan dai-dai-ta Hausar sa, yadda Abu Maleek zai fahimta, jinjina kai yayi tare dabin bayan Lamiɗo jin haka ya sanya Julde ɗan miƙa hannu zata riƙesa da sauri yayi gaba yana mai harɗe hannayensa a ƙirjinsa,
Tsaya tayi cak jin ance.
"Ko damata maa?" (Meke damunki?)
Zare idanu tayi waje tana dafe ƙirjinta saboda jin Muryar Barkido,
Murmushi Barkido ya saki yana ƙarewa Julde kallo, yana jin wata zallar soyayyarta a zuciyarsa,
Wanda bai san lokacin daya fara ba haka kuma bai san lokacin da zai goshe ba,
Ja baya tayi tana ɗan girgiza kai ganin tsoransa ta keji ya sanya cikin ƙasa da murya yace.
"Babu abinda zan maki Julde kiyi haƙuri dana baya ma"
Ya faɗa yana juyawa sabida baya sun Arɗo ya fito ya samesa a wajan, shiru tayi ba tare da tace komai ba,
Kamar zai kuka Barkido ya ƙara buɗe baki yace.
"Julde kiyi haƙuri jin? Zaki haƙura ko, bana ƙara yi maki komai"
Ya faɗa idanunsa na ciccikowa da hawayen so da kuma ƙaunar ta, ƙasa tayi da kanta a hankali cikin ƙaramar muryarta tace.
"To na haƙura"
Ajjiyar zuciya ya sauke kafin yace "Nagode, muje ciki na baki kindirmo mai zafi"
Farin ciki ne ya kamata hakan ya sanya ta fara bin sahun tafiyarsa har suka isa wata bukka, ciki ta shiga tana zaune ya je ya kawo mata kindirmo mai yawa a ƙwarya, kana ya sake fita babu jimawa ya dawo hannunsa ɗauke da wasu kayan Fulani masu ɗan haske ya bata tasa.

Arɗo ne a gaba Abu Maleek na bin bayansa a hankali cike da Zallar nutsuwarsa irin ta ƴar ƴan sarakai, wanda jinin sarauta ya gama ratsa su,
Wata bukka mai kyau wacce aka cikata da kayan ado irin nasu na Fulani, Arɗo ya sanya kansa cikin Bukkar, Abu Maleek kam tsayawa yayi cak,yana mamakin ta inda zai shiga bukkar gaba ɗaya bukkar a tsakiyar cikinsa ta tsaya, baya tunanin cikin bukkar ma zai Wada cesa, waro manyan gajiyayyun idanunsa yayi waje ganin yadda Arɗo ya sunkuya sosai kamar zai dafa ƙasa kafin ya samu ya shiga cikin bukkar, cije lips ɗinsa yayi yana fesar da iska daga cikin bakinsa, a hankali cikin kuma ƙasaitacciyar muryarsa mai cike da kamala ya ware softness lips ɗinsa masu taushi da ɗan kauri cikin ƙasa da murya very slow yace.
"Goodness"
Ya faɗa yana janye idanunsa daga kan Bukkar, Arɗo dake ciki ne yaji Shiru baƙon mahaukacin nasu bai shigo ba, ya sanya shi leƙo dakai ganin Abu Maleek yayi a tsaya hakan ya sanya yace.
"Ai shaii ka rarrafa ka shigo"
Arɗo ya faɗa yana mai tsare ƙirjin Abu Maleek da kallo saboda wani baƙin zane daya hango, kwance a saman faffaɗan ƙirjin nasa,
Ganin hakan ya sanya Abu Maleek haɗe rai kafin ya ɗauke idanunsa yana faɗin.
"Wicked and stringy man"
Ya faɗa a fili amma Murya ƙasa, Murmushi kawai Arɗo yayi ba tare da yace komai ba,
A hankali ya sunkuya sosai, cikin rashin Sa'a kansa ya bugu da gefen bukkar, kwaɓe fuska yay sosai kamar zai sanya kuka, a hankali cikin Muryar taɓa ra yace.
"Auchhhiii! Daman salon mugunta akai wannan guntuwar abar, an san ai baƙi zasu iya zuwa, mtwss!"
Ya faɗa yana ƙarasa shiga cikin Bukkar duk ya marai-raice fuska kamar zai kuka, ganin ya shigo yasa Arɗo fita tare da ƙwarya a hanunsa, Not too long ya dawo da ƙwaryar cike da kindirmo mai kyau, wanda yake zalla babu algus,
Kindirmon yabi da kallo kafin a hankali ya haɗe ƙafafuwansa waje guda, bai son Kindirmon sabida sam bai yarda da tsaftar mutanan garin ba,
Amma idan yaƙi sha bai san abinda zai samu nan gaba yaci ba.

Zama Abu Maleek ya gyara tare da ɗaukan ludayin Dumar ya sanya cikin ƙwayar kindirmon da aka kawo masa, ganin yadda Kindirmon yake da haske sosai ga wani irin kyau da yayi masa a idanu, ya sanya a hankali cike da nutsuwa ya ƙara naɗe ƙafarsa kana ya ɗebi Kindirmon yakai bakinsa, da sauri ya ja idanunsa ya rufe saboda wani daɗi da kuma garɗi daya ratsa cikin kunnuwansa, shan Kindirmon kuma ya taso mata da duka yunwar daya keji a haka yaci gaba da sha, sai da yasha fiye da rabi kana ya ajjiye,
Murmushi Arɗo yayi yace.
"Birnin Bera kace ko, haii daga wannan rugar sai Birnin Bera tafiyar kwana guda ce rakk, amma haɗarin tafiyar yafi na shekara guda"
Kallonsa Abu Maleek yayi sai kuma ya ɗan taɓe baki, yana tsotse laɓɓansa wanda har yanzu daɗin Kindirmon yaƙi barin saman harshansa,
Lumshe idanunsa yayi harga Allah matsu ya samu maganin ya koma Benin kana ya ga King Tunde Muhammad Jalal ya samu lafiya daga nan kuma sai koma Madrid baki ɗaya, ya samu ya huce dukkan gajiyarsa a can!.

Kai tsaye waje Arɗo yayi yana zuwa ya nufi wajan Lamiɗo ba tare da yayi magana ba, yaja hannun Lamiɗo zuwa wata bukka,
"Meka fahimta dan gane da wannan baƙon?"
Arɗo ya tambayi Lamiɗo yana share zufar data karyo masa,
Gaba ɗaya Abu Maleek ya gama firgita Arɗo da kwarjininsa, har baya iya tsayawa inda yake saboda tsoro,
Lamiɗo ne yaja numfashi kafin yace.
"Ban fahimci komai ba, amma dai kamar bashi da lafiyar ƙwaƙwalwa, duba da yanayinsa da kuma shigarsa, ga kuma yadda kansa gaba ɗaya yaƙi tsayawa waje guda"
Jinjina kai Arɗo yayi kafin yace.
"Haka ne,amma akwai lauje cikin naɗi, mene ya kawo sa wannan garin? A cewar sa dai wai Birnin Bera zashi, amsar magani kuma babu wani magani da ake bayarwa, uhm! Kasan babu wanda ya taɓa shiga Birnin ya fito da ransa, saboda haɗarin da mutanan garin suke da shi, kasan mutanan tamkar kuraye haka suke, su kuma kalar tasu maitar a fili suke cin shan jinin Mutum, kuma da sun cijeka shikenan kai ma harbo wannan maitar"
Cike da gamsuwa Lamiɗo ya jinjina kansa kafin yace "haka ne, amma wannan mutumin kamar da sammu a jikinsa, ina kallonsa naji hankali na yaƙi kwanciya, ina ganin mu taimaka masa mu faɗa masa gaskiya zaifi"
Murmushi Arɗo yayi domin shi ya gama tsara Abinda zaiyi,
Juyawa yayi tare da nufar bukkar da Julde ke kwance har zai shiga sai kuma ya fasa ya juya yana mai sakin murmushi.

Cikin dare Abu Maleek yana kwance tunani fal ransa, idan ka ganshi zaka ɗauka da gaske bacci yake amma idanunsa biyu,
Ƙara yaji kamar na ringing ɗin waya daga bakin bukkar, mamaki ne ya cika masa zuciya domin yasan babu yadda za'ai a samu waya a wannan garin, garin da ku service bashi dashi, gashi ya lura ko addini basu iya ba,
Ware fararan idanunsa yay yana da ɗan kasa kunne muryar Arɗo yaji yana faɗin.
"Sir trying to remembered it, nayi ƙoƙarin ganin na aikata hakan but it's difficult to me, gaskiya i can't do that I'm sorry!"
Shiru yayi yana mai ƙara juya gudun kada wani yazo ya riskesa a haka, jinjina kai yay kafin yace.
"That's great job, any way duk yadda mukai I'll get back to you"
Ya faɗa yana mai kashe wayar tare zuge ta zugen wandonsa, a cikin aljihun 3gauther ya sanya wayar kana ya shigo cikin bukkar,
Da sauri Abu Maleek yaja idanunsa ya rufe mamaki ya hanasa tunanin komai bare ya fahimta, Tabbas akwai abinda yake faruwa a wannan Rugar mene shi, yaya akai Shugaban Rugar Mahinjo ya iya sarrafa harshe haka? Da wannan tunanin bacci ya ɗauke sa.

Washe gari waje ya samu mai kyau ya ɗan watsa ruwa a tsaye gudun infection,
Bayan ya shirya cikin wasu fararan kayan Fulani masu kyau, ya fito daga cikin Bukkar yana mai ɗan fesar da huci daga cikin bakinsa,
Arɗo dake gefe yace.
"Har ka fito?"
Kallon Mutumin yayi a ransa yace "munafuki"
A zahiri kuma idanunsa kawai ya lumshe tare da buɗe su,
Gyara tsaiwa Arɗo yayi kafin ya kalli Abu Maleek yace.
"Haii ka buɗe kunne da kyau kaji baƙo, babu wani magani da ake bayarwa a Birnin Bera, gaba ɗaya mutanan garin masu shan jini ne, a tarihi ma babu wanda ya taɓa zuwa koda ƙofar garin ne balle ya shiga, duk wanda yace kazo garin to bayanka ya keson gani Aradon Allah"
Kallonsa A.m yake domin yana son ya fahimci asalin Maganar, babu Abinda Ya gani a idanun Arɗo sai zallar tarin gaskiya tsagwaronta,
Juya idanunsa yayi kana ya mirgina kansa gefe yace.
"Are you sure?"
Ya faɗa yana cije bakinsa dan nan da nan yani kansa ya fara sarawa, sosai maganar ta dakesa, mene ya sanya akai hakan? Wane ya sanya Malamin Alaafin ya faɗi haka, lallai Tabbas biri yayi kama da mutum dalilin daya sanya kenan suka hana ya duba King Tunde Muhammad Jalal sabida suna tunanin zai iya fahimtar wani abu, Tabbas dole ya koma Benin ba tare da ɓata wani lokaci ba.

A can Alaafi Kanzaf kowa, tsaro aka ƙara mai tsananin gaske, cikin Alaafin yayi shiru baka ganin komai, ko jin motsin wani face na securities, tsaron da aka ƙara yafi na kullum, babu mai shiga babu mai fita, Al'amarin daya tayarwa da jama'ar Kanzaf hankali kenan,
Kana kuma ya sanya masu tsoro da tarin zullumi a cikin zuƙatansu,
Yau wajan sati guda kenan da tafiyar Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal kenan, tafiyarsa kuma ta haifar da tarin matsaloli wanda ba'a san ta inda suke kunna kai ba.
Salimerh ce zaune a saman bed ɗin ta tana sanye da kayan bacci dark brown panjamas, masu kyau,
Waya ce maƙale a kunanta tana sauraran abinda Junaid yake faɗa mata,
Daga can ɓangaren Junaid gyara kwanciyar sa yayi a hankali cikin ƙasa da murya yace.
"My princess kina son zuciyata ta buga saboda soyayyyar ki da tayi min yawa ko? I can't control my self idan ina wajanki ko su kike ba aikata abinda ba Shikenan ba?"
Ya faɗa yana jan numfashi, girgiza kai Salimerh tayi kafin tace.
"Ba haka bane, ni aure a yanzu ta kurani zai, ina karatu akwai tarin abubuwan da yake gabana masu muhimmanci"
Uhm kawai ya iya cewa kafin yace.
"Kenan baki sona?"
Girgiza kai tayi tace "i love You, ina sonka Junaid but...,"
Ka tseta yayi da "if you really love me, then marry me"
"I'll" da sauri yace "then when? Kinga stop pretending gobe zanwa Otun magana ya nemi Agba Akin (CHIROMA)domin a nema min Auranki, I'm tried My princess ki shirya zama matar Junaid soon"
Bai jira tayi magana ba, ya katse kiran yana mai mamakin yadda sam bata fahimtar son da yake mata,
Ajjiye wayar tayi domin ita sam babu maganar aure a tsarinta yanzu, tana big issues dalilin daya ta zaɓi karanta Law kuma ɓangaren criminology justice.

Washe gari da yamma Adams ya fito daga shashinsa cikin shigarsa ta ƙasaita, yana sanye cikin wani tattausan farin yadi mai manyan zane, anyi masa ɗinkin half body sai shot hand, yayi masu kyau sosai, ya ɗura wata hula mai gashi sai manyan murjani daya sanya a wuyansa,
Yana tafe a hankali a haka ya isa dinning room ɗin, Oumuu-Ayman ce zaune sai Mai Babban ɗaki da kuma Queen Ayoola, kana Bola lunch suke ga Cook yana serving kowa, lafiyayyan Moi-moi ne wanda yaji bushasshen kifi da kwai, kana da curry da kayan magi, ga wani ƙamshi da yake fitarwa musamman da aka samu wanke mai kyau..
Sai vegetable soup wacce tasha carot da beans sai zallar hanta wacce aka yanka manya,
Kujera yaja ya zauna, yana mai ɗan cilla idanunsa ganin babu Shakiru babu SHAREFUDDEEN, motsawa yayi kafin yace.
"Barka da rana Granny Oumuu, Mumy"
Duk suka amsa da "yawwa" a hankali ya fara yin lunch kafin ya kalli Mai Babban ɗaki yace "yau zan tafi Cairo"
Da mamaki ta kallesa kafin tace.
"Daman akwai tafiyar ne ko yanzu ka shirya?"
Kallon Salimerh yayi dake fitowa cikin shirin ta mai ɗaukan hankali, tana riƙe da hand bag sai kuma school bag ɗinta, da sauri ta zauna ta fara luch ɗin,
Ɗauke idanunsa yayi yace.
"Na daɗe shirya tafiyar sai yanzu komai ya dai-dai-ta, zuwa dare jirgin mu zai tashi"
Kallonsa Oumuu-Ayman tayi tana jin sam bata yarda da tafiyar amma bata ce komai ba.
"Da ka haƙura zuwa lokacin da ɗan uwanka zai dawo, muga jikin Mahaifin ku

Please Login or Register in order to submit comment