Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan ya kawo min fuskar Hadima Zubaida akan yana son na dinga shiga ina jiyo masa komai dake faruwa, a nan naji labarin cewa wai za'a ce Maleek ya mutu saboda masu san ganin bayansa, wanda nima ban san su ba, Ni da kai na na ɗauki waya mai vedio da fuskar Hadima Zubaida sannan na kawo nace gayamin akai, dalilin daya sanya aka kulle Hadima Zubaida kenan, dab da Abu Maleek zai dawo kuma Sharefddeen ya kawo garin meriz yace aiki zai dashi, a cikin Abincin da Hadima Zubaida take kaiwa King Tunde Muhammad Jalal aka zuba Garin meriz ɗin, hakan yasa ya fara jinya sosai, batun auran Zaki da Kubraahh kuma dalilin rashin kasancewa da Abu Maleek ba yayi dani sai ake tunanin idan har aka aura masa mace mai ilimi zata iya janye hankalinsa, hakan yasa aka aura masa Kubraahh without his permission, ban san yaushe ne Abu Maleek ya samu ciwon juyewar tunani ba, amma ina da tabbacin dukan da akai masa aka shine ya jawo faruwar hakan, Soyayyar Abu Maleek ta fara a Zuciyata tun lokacin daya kira Oumuu-Ayman a waya na ɗauka naji muryarsa yadda yake zuba mata shagwaɓa, lokacin Oumuu na wajan Queen Roomana wacce aka bawa wani abu abinci Allah dai ya rufa asiri bata mutu ba, na samu Sharefddeen akan zan faɗi gaskiya saboda yace lokacin yay da zance wannan ɗan bana Abu Maleek bane, dalilin da yasa ya caka min wuƙa kenan"
Wani sabon kuka ne ya kwance mata bayan ta gama bayanin, Shakiru ne ya jinjina kai kafin yace "Ikon Allah! To yaya akai kika kasance a raye?" Kafin tayi magana Adams yace "Akan ido na Sharefddeen ya ɗauke ta zuwa Cikin ƙarshen Alaafi, jinin dana gani kuma ya ɗaga min hankali sosai matuƙa, a hankali a ɓoye nake binsa har ya ajjiye ta, yana barin wajan naje na ɗauke ta na kaita asibiti a nan take zama ana kula da ita kullum kuma ina zuwa wajanta, yau kuma bayan munshirya zamu taho nan naga ya dace azo da ita duk da bata gama warkewa ba"
Shiru kawai wajan ya ɗauka kafin aji kuma Bola ta saki ƙara tare da faɗin "Wayyoooo Abu Maleek bayanka" da wani irin sauri Shakiru ya riƙe hannun Sharefddeen mai ɗauke da wuƙa yana niyyar cakawa Abu Maleek a tsakiyar kansa.
Murɗe hannunsa Shakiru yay nan suka fara kokawa cikin rashin Sa'a kuma wuƙar ta goce tare da shigewa Marar Sharefddeen,wata iriyar Razananiyyar ƙara ya saki yana dafe mara saboda wuƙar akan J ɗinsa ta sauka.
Kuka Queen Ayoola ta sauke tana yadda zani tare da ɗura hannu a ka.
Dai-dai lokacin ne kuma Junaid ya ƙarasu wajan ɗauke ta Julde wacce take a sume saboda gigita.
Da sauri Abu Maleek ya miƙe tare da nufar Junaid yana zuwa ya karɓe ta tare da rungome ta a jikinsa, kai tsaye wajan wata ciyawa ya nufa da sauri kuma Jon wuro yay wajan Abu Maleek yana zuwa ya kwantar da ita ya shiga shafa mata ruwan yana faɗin.
"Wake up Queen Hawwa'u, open your eyes buɗe idanunki nine your Cucuu, Ɓallowaaaaa ɗinki Open your eyes"
Ajjiyar zuciya mai ƙarfi ta sauke dalilin ruwan sanyin daya shafa mata a fuska, tana Ganin ta faɗa jikinsa tare da rungumesa tana sakin kuka tare da shiɗewa.
Bayanta ya shiga bugawa a hankali kafin cikin ƙasa da murya yace.
"Am sorry na kasa kulawa take kiyi hqr kinji ko?" Ajjiyar zuciya ta ƙara saukewa wata masifaffiyar yunwa ta keji a hankali tace.
"Cucuu" fuskarta ya tallafo baki ɗaya ya manna a fuskarsa yana sauke wani wahalallan numfashi, cikin natsuwa da kuma daɗin da yake ratsa shi ya manna bakinsa a saman goshinta ya mana mata halattacciyar sumbata a tsakiyar goshin yana shafa kanta a hankali kuma yake sauke ajjiyar zuciya, cikin nutsuwa yayi ƙasa da hannunsa zuwa ƙasan rigarta tafin hannunsa ya kifa a saman lafaffan cikinta ya murza kaɗan yana shafawa dai-dai kunanta yana wura mata wata dadɗar iska yace.
"Wunya ko My Queen?"
Idanunta ta Lumshe kafin a hankali ta sanya hannunta a fuskarsa tana shafawa zuwa saman ƙwantaccen sajansa cikin ƙasa da murya irinta wanda suka sha wahala tace.
"Cikina juyawa yake, wunya na keji sosai" juyawa yay a hankali ganin babu kowa Jon wuro ya tafi yasa cikin sauri ya manna bakinsa a nata, ta sauri tana sauke ajjiyar zuciya taja tongue ɗinsa ta shiga kissing nasa tana sauke numfashi, kwana biyun da ba tayi da mijinta ba yasa tasha wahala bata bacci sam, zare bakinsa yay wani irin kwaɓe fuska tayi tare na shagwaɓe masa, wani irin Murmushi Yay mata mai tsayawa a zuciya yace.
"Sorry My Queen bana son zurmewa na sakar maki ragama ta matsala za'a samu"
Murmushi tai masa tace "Ina sonka, Ana Uhibbukaaaaaa, I love You" wani irin lumshe idanunsa yay yana jin wani daɗi na musamman yana ratsa shi, ɓata fuska tayi tare dasa hannu ta daki ƙirjinsa riƙe hannunta yay yana Rungome ta yace.
"Auchhhiiii zaki fasa min ƙirjin rungome ki fa"
Hawaye ne ya zuba mata da sauri ya haɗiye dariyarsa saboda jin kukanta cikin kulawa ya ɗura fuskarsa a nata, bakinsa dai-dai nata, hancinsa a kan nata suna shaƙar ƙamshin junansu yace "ohh! Stop cry nine ko?" Turo baki tayi wanda ya samu shigewa cikin nasa da sauri kuma ta zare tace "Uhm! Uhm to bakai bane ba kace kana so na ba, har yanzu babu soyayya ta a ranka" tsora mata idanunsa yay yana ganin yadda duk ta shagwaɓe masa kamar ƙaramin yarinya, a hankali ya ƙara shigar da ita cikin jikinsa yana wata nutsuwa na shigarsa cikin wata kamilalliyar Muryarsa mai matuƙar daɗi da kwantar da hankali yace.
"Da Jalaluldeen da dukkan abinda ya mallaka aka naki ne Mrs Jalaluldeen, bare kuma wata zuciya Ni ƙaunar nake ba sonki ba, don mind me kinji" baki ta tura gaba tana lumshe idanunta wanda suke cike da bacci da gajiya tace "to ai ba kace i love You ba" gira ya ɗaga mata yana lumshe idanunsa just like she did yace "to a special place nake faɗa, kina ganin nan sai ihu kowa masifa na cinsa" zamewa tayi daga cikinsa zata fara buga ƙafa da birgima da sauri ya ɗauke ta tare da yin sama da ita tace.
_"Mi yidi ma (Fulatanci) Nya Raina (Barbanci) Mo nife re (Yarbanci) A hurum gi n'anya (Inyamuranci) I love you Hawwa'u! Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal loves you Naa...nahh, Abu Maleek na Sonki, Zakin Oumuu-Ayman na ƙaunar ki, Ƙaunar ɗan gidan Mami never end, I promised to protect you till my last breath Naa.. nahhhh, I promise to stand by you ina sonki ki daina tunani ok"_ wani irin kalar numfashi tayi tana rungomesa sosai kafin a hankali ta zame daga jikinsa tana riƙe ciki.

A can cikin Bukkar kuwa Arɗo na shiga ya fara zarya a ciki, da sauri kuma yaje ya zaro paper da yake ɓoyewa tsayin shekaru masu yawa, a hankali ya fara bin rubutun da kallo kamar haka..
_Ban san ko ina raye ba, ban sani ba ko bana raye, nayi tunanin yin Wannan rubutun ne saboda halin rayuwa da kuma yadda ake ta kaiwa rugar mu hari, gaba ɗaya Nagge da sukai saura mallakin yarinya ta ne, dukkan yawan Nagge nan mallakin JULDE MUIDO a duk sanda ta girma wannan wasikar nata ne,amma a yanzu na baka wannan riƙon wasiyyar ɗan uwa na MODIBBO_

Ajjiyar zuciya ya sauke bayan ya gama karantawa gaba ɗaya tunaninsa ya tsaya, jin kansa na juya masa ne ya nemi waje ya kwanta, kwanciyar keda wahala bacci ya ɗauke sa.
A cikin baccinsa ya fara ganin wani abu mai kama da reflection, a hankali wata mata mai tsarin halitta tazo gabansa ta tsaya, tana ɗauke da yaro sai Murmushi take masa, kama ta yay tare dayin kissing nata, ya shafa kan yaron kana yay mata addu'a, juna suka tsaya suna kallon kamar ba zasu rabu ba, can kuma ya shiga mota yana shiga motar, tafiya sukai mai nisa yana tafe yana waya idanunsa na cika da hawaye bayan ya gama wayar ne kuma kamar daka sama suka ci karo da wata ƙatuwar mota gefe guda kuma ga wata ƙaramar mota, nan da nan dukkan motocin suka huta, murfin motar da yake ciki ne ya buɗe ya fito da sauri tare da nausawa cikin daji, yana tafe kansa ya daki wata ƙatuwar bishiya kafin a hankali ya faɗi ya gangara can yana zuwa kansa ya ƙara dukan wani ƙaton Dutse nan take ya saki ƙara Numfashinsa ya ɗauke.
Kamar a lokacin abin yake faruwa haka ya tashi yana sakin salati gumi duk ya wanke sa, Wayarsa ce ta fara ƙara da sauri ya ɗauka yana picking yace.
"Okey! Sir" fitowa yay da sauri ganin hakan yasa sauran ƴan rugar suka nufi inda yake banda Jon wuro dake kallon Hadima Zubaida, a hankali itama take kwallon sa, Cikin umarni Arɗo yace.
"Yanzu Oga zai sauka ɗaukan wannan mutumin wanda aka amshe sa madadin matarsa, Ina Barkido Lamiɗo?"
Girgiza kai Lamiɗo yay alamar bai sani ba.
Julde kam tuni ta gigice ta riƙe Abu Maleek sosai ta fashe da kuka tana girgiza masa kanta, Queen Ayoola kuwa tana kusa Sharefddeen dake cikin maqiya hali an ɗaure masa wajan saboda babu wani hospital, Queen Roomana tana zaune har lokacin hawaye take tana kallon Arɗo, yayinda Hadima Zubaida take kusa dasu Mai Babban ɗaki da Bola, Adams da Shakiru da Junaid suna tsaye, haka ma su Otun da Agba Akin.
Kamar daga sama suka fara jin saukar jirgin sama, a hankali duk suka ɗaga kansu har jirgin ya gama sauka ƙofar jirgin ta buɗe, gaba ɗaya suka zare idanu ganin Malamin Alaafin ya fito cikin wata kalar shiga wacce basu san sa da ita ba, fuskarsa a haɗe ya shiga sakkowa, mamaki duk ya hanasu magana ba, Queen Roomana sam ba tayi wani mamaki ba, kallon Arɗo yay yace.
"Ina aikin namu?"
Shiru kawai Arɗo yay yana kallon Mutumin wanda akace shi ne Oga, to shi kuma waye ogan nasa? Da yake cewa hajiya? "Muna son jira ga kuɗin ku nan" a hankali Arɗo ya sauke Ajjiyar zuciya kafin kuma ya juya suka haɗa idanu da Abu Maleek da sauri Abu Maleek ya ɗauke saboda wani irin kwarjini da Arɗo yay masa a cikin idanunsa a karo na biyu, jikin Arɗo a sanyaye yace "gashi can" ya faɗa yana nuna Abu Maleek miƙewa Abu Maleek yay yana gyara tsaiwarsa, da sauri Julde ta miƙe tana faɗin "No! Don't leave me Kada kaje ka bari naje" wani kallo yay mata yace "Ni idan naje ko kashe ni akai ni ɗaya ne, ke kuma bayan rayuwarki akwai na jinina a jikinki, ko cikin jikinki yafi rayuwarta muhimmanci bare kuma ke" kuka ta sanya masa tace "a'a Kada kaje dan Allah ka bari muje tare bazan jure rashinka ba, na kasa bacci na kasa cikin komai na wani sati, yaya kake tunanin rayuwata zata kasance idan akace babu kai gaba ɗaya?" Daga saman jirgin su kaji wata Murya tace.
"Wow! Sai ku tafi lahira lokaci ɗaya soyayyar tafi daɗi" a wannan karan hatta Sharefddeen dake kwance sai da ya zabura da ganin wacce take magana.
Salimerh ce take sakkowa daga strains ɗin benen cikin wata haɗaɗɗiyar shiga, fuskarta babu walwala ta faɗa sosai, da sauri Malamin Alaafin yace "Hajiya ai zan ƙarasa komai ba sai kin fito ba" wani irin yatsuna fuska tayi a hankali ta ƙarasa sakkowa, Queen Ayoola ce ta kasa jurewa tace "Salimerh" wani irin killer smile tayi tace "Yes Mom!" Ta faɗa tana ɗan ya motsa fuska, kallon kowa tayi na wajan kafin tace.
"Ban so fitowa ba, naga dai ya dace daga ƙarshe na bayyana maku kai na, Wheel Tun lokacin dana fahimci cewa niɗin Agola ce acik Alaafi na fara shirin yadda zan samu komai na dukiyar Alaafin, nasan za kuyi mamaki amma tunina duk ya shallake naku, Nice na ɗauke Queen Roomana" da sauri Adams ya kalli Queen Roomana sai kuma ya janye idanunsa jin tace "Ni kuma na kashe Oumuu-Ayman, lokacin dana fahimci cewa itace uwar Abu Maleek ba Queen Roomana ba, sun raina min hankali sun juyar min da tunani, wannan dalilin yasa na kawar da ita, amma zahiri ba ita nai niyyar kashe wa, Abu Maleek nasu kashewa nasan cewa Oumuu-Ayman ita take shirya maka abinci, wannan dalilin yasa tana fita nasa Hadima Akin ta zuba mata gubar da take kashe Mutum a lokacin acikin abincin data haɗawa Abu Maleek, nayi rashin Sa'a fa domin a lokacin tuni ta kaiwa Zaki abincinsa wanda aka zuba maganin shine wanda za taci, hakan yasa tana zuwa ta fara cin abincin na shiga tashin hankali sosai lokacin da naji tana faɗin _S...K...K_ wannna harafan sun tsaya min a rai sosai, amma dana suna cewa kalmar S zata ɗauki Sharefddeen, zata ɗauki Shakiru sai abin bai ɗaga min hankali ba, nice kuma na ɗauke dukkan wata dukiya dake cikin Alaafin kuma Allahamdulillah yanzu komai nawa ya cika, duk da cewa yanzu Zanan Taswira kawai ya rage min, Ɗauko min Akwatin nan suga Zahiri Maganar Gobar dana zuba acikin Abinci kuma har Queen Roomana taci ban so al'amari ya tsaya ba, amma shigowar Julde cikin Alaafin ya ruguza min komai ma rayuwa, wani abun idan zanyi sai na kasa tana zuwa cikin bacci na muyi ta faɗa da ita sosai" Malamin Alaafin ne ya kawo Akwatin da ƙyar wani irin Murmushi Hadima Zubaida tayi ita da Julde domin sun san cewa wannan ba itace Akwatin ba.
Murmushi Queen Roomana tayi kafin tace "A ina kika san Arɗo?" Malamin Alaafin ne yace "wannan ni zaki tambaya" gyara tsaiwa yay yace "Munje wata ruga yin kwacan shanu bayan mun dawo a hanya kawai naci karo dashi kwance cikin jini, kallo guda nai masa nasan wanene shi domin rayuwata kakaff a Alaafi ta fara, sosai nai mamakin ganinsa domin a lokacin tuni an shaida mutuwarsa, ɗaukan sa nai kana na koma Rugar a lokacin na samu gawar wanda muka kashe da yawa daga ciki akwai ta Arɗon rugar, kai tsaye na ɗauke su, su biyun na nufi asibiti dasu, tashin farko akace ya samu juyewar ƙwaƙwalwarsa ma'ana yay losing memory ɗinsa, ya manta komai da komai na rayuwarsa na baya, Yayinda kuma Arɗon rugar ya mutu a wannan lokacin, wani tunani ne yazo kai na, ta yadda zan samu jagora a cikin Fulani ba tare da wani tashin hankali ba komai nace za'ai min a wannan lokacin za'ai min, sai kawai na kwashe su nai ƙasar waje dasu na nemi a sauyawa King Muhammad Jalal fuskarsa ta koma irinta Arɗo sak, a nan manyan likitocin suka ce min har safarar tunanin Arɗo za'a iya yi zuwa cikin ƙwaƙwalwar King Muhammad Jalal, sannu a hankali zai mance komai ya fara abubuwa irin na Arɗo, cikin sauri na amince aka sauya fuska akai masa safarar tunani, na sha wahala sosai, idan ya fara tunaninsa na baya yayta kiran Jalaluldeen My Queen, i don't understand anything da yake faɗa, idan kuma tunaninsa ya fara dawowa na Arɗo sai ya juye zuwa fulatanci yayta magana akan cewa duk shanunsa an kashe raguwar Hannun MUIDO ya rage, a haka na mai dashi Rugar sosai mutanan rugar suka ji daɗi daga nan ban ƙara waiwayar su ba, sai bayan wasu shekaru ina zuwa naga Rugar babu kowa a haka na samu labarin sun koma GUINEA da zama a can na samu labarin Birnin bera, lokacin da Salimerh take faɗa min cewa tana da tabbacin Jalaluldeen ba ɗan King Tunde Muhammad Jalal bane yasa na fara sauya shiri, akan tura Jalaluldeen Birnin bera domin ya haɗu da mayo su cinye sa, a wannan lokacin banyi tunanin cewa Jalaluldeen zai haɗu da Arɗo ba, sai gashi ya dawo tare da ƴar gidan Hadima Zubaida"
Da wani irin sauri Julde da Hadima suka kalli juna Jon wuro kam mamaki yay kafin Malamin Alaafin yace.
"Kina tunanin ban sa me nake ba ko? Bayan kin cilla Yarinyar ki cikin kogi ke kuma an harbeki, bayan duk sun tafi na dawo wajan duba yarinya ban same ta ba, har zan tafi sai naga kina motsi da sauri na ɗauke ki zuwa asibiti akai Maki aiki, kai tsaye na kaiki cikin Alaafin akan Sabuwar Hadima, cikin Sa'a kuma late King Tunde Muhammad Jalal ya mayar dake Amintacciyar Hadimar sa, nasu na janye tunaninki domin kina yimin aiki, sai na kasa saboda tsarin dake jikinki, sosai na fahimci akwai abinda kike ɓoyewa sai ban fahimci komai ba, dole na rabu dake, wannan Yarinyar kuma bayan naje Rugar Mahinjo naga Yarinyar hannun wata tsohuwa a nan wani Madibbo yake shida min cewa ƴar gidan MUIDO ce, ya tsince ta a ruwa dalilin daɗewar da tayi a ruwa kuma idanunta sun samu matsala, har wasiyyar da Mahaifin ta ya bayar ya nuna min, Ni kuma na samu Arɗo na faɗa masa akan duk yadda za'ai yaga bayan Madibbo Sannan ya ɗauke wasiyyar daga wajansa"
Wani irin daɗi ne ya ziyarci zuciyar Hadima Zubaida tace "tun kallon farko da nayi wa Julde nasan tabbas ita ɗin ɗiyata ce, Allahamdulillah" kuka ne ya kwance wa Julde ta faɗa jikin Abu Maleek tana kuka.
Queen Roomana ce tace "kamar yadda wasu suka sani wasu basu sani ba, nidai ban haifi Jalaluldeen ba, ban kuma haifi Khaleluddeen ba, Adams shine ɗana, wanda na haifa da ciki na, ina tare da Oumuu-Ayman tun ina budurwar inda na kasance kuma ƙwarƙwara ga King Muhammad Jalal, ranar da Akace ya rasu ranar ta same ni, nida Mai Babban ɗaki take faɗa min cewa zan zama madadinta na kuma Queen Roomana madadin ƙwarƙwara, shiru nayi domin bana jin zan iya wannan aikin,amma da tace akan rayuwar Jalaluldeen ne da sai na kasa yi mata mosu, a wannan lokacin daman Tunde ba'a ƙasar yake da zama ba shi da matarsa Queen Ayoola, hakan yasa tun a can aka haɗa plan dashi cewa idan yazo zan zama Queen Roomana amma dai a ɓoye ni ɗin zan zama ƙwarƙwararsa kamar yadda nake ƙwarƙwarar Muhammad Jalal, a zahiri kuma Oumuu-Ayman itace ƙwarƙwarar anyi haka ne kuma saboda fahimtar cewa akwai munafukai, aka sauya komai na Alaafi a wannan lokacin ma hadda Otun da Agba Akin aka shirya, amma dake suma butulu ne suka fara cin dudduniyar mu, duk da cewa babu wanda suka faɗawa, lokacin Jalaluldeen yana Ƙarami ni kuma ina tare da Adams ya ɗan fara wayo, saboda shima ɗan King Muhammad Jalal ne amma kasancewar ni ƙwarƙwarar ce yasa bashi da ikon gadar sarauta, lokacin da Late King Tunde Muhammad Jalal ya dawo Alaafi aka bashi sarauta ya fara bincike akan komai, lokacin yaransa biyu Shakiru Sharefddeen, bayan Queen Ayoola ta haife su sai suka samu Matsala ta fita ta auri wani a nan ta haifi Salimerh mutumin ya mutu sai aka mayar da Auran su da Tunde Muhammad Jalal, komai Oumuu-Ayman ke yiwa Jalaluldeen yayinda ni kuma aka sanya min idanu domin tunanin duk na kowa ni matar King Tunde Muhammad Jalal ce saboda ya faɗawa Queen Ayoola yana da mata a Nigeria da yara biyu, Adams da Jalaluldeen, ansha kawo min hari za'a kashe ni kowa yana zaton nice uwar Jamaluddin amma rashin sani duk yasa suke haka, asalin mahaifiyar Jalaluldeen itace Oumuu-Ayman, soyayya mai zafi ce tsakanin Oumuu-Ayman da Abu Maleek, wanda duk mai hankali idan ya duba yasan cewa ba iya shaƙuwa ce zallar so da ƙauna ne da jini dake yawo a cikin ko wannan su, kwanci tashi tafiya tayi nisa Oumuu-Ayman ta fahimci tana da ciki, ashe tun baya akwai cikin amma kwanciya yay, sai na rufe kace Oumuu-Ayman babu lafiya a bata hutu, dake kowa ba sonta yake ba, saboda tsananin girmamawar da King Tunde Muhammad Jalal yake mata, a haka ciki ya tsufa tana haihuwa aka bawa Hadima Zubaida rainon yaron mai suna Khaleluddeen, bayan suna shima aka zana masa Taswirar Alaafi, ban san wanda ya sace ni ba, saboda kullum fuska a rufe ake zuwar mu, dani da Oumuu-Ayman mu kaje aka cirewa Abu Maleek sha'awarsa ya zamana baya son ko wacce mace, dalilin dukan kuma da akai masa ya samu matsala wanda yanzu Allhamdulillah ya dawo dai-dai"
Shiru kuwa yay yana tunani yayinda Salimerh kuma tace.
"Uhm Ƙarasa aikin ka" gyara tsaiwa Malamin yay yace "babu abinda zan maka kawai Taswirar jikinka muke son ɗauka" wani irin mugun kallo Abu Maleek yaywa Malamin yace "idan kana da ƙarfi kazo ka ɗauka" Murmushi Salimerh tayi tace "haka kace?" Wani banzan kallo yay mata dan shi a tsarin shi baya sanya mata, musamman da yaji wai itace ta kashe mata Maaamahh ɗin sa, "Uhm shut him" Malamin ya faɗa yana bawa Arɗo bindiga cikin bada umarni, amsa Arɗo yay yana nuna Abu Maleek da bindiga kafin kuma da sauri ya ɗura bindigar akan Malamin yace "Muhammad Jalal my name not Arɗo, na dawo hankali na yau ɗin nan bayan komai daya dawo cikin bacci na, idan Taswirar kake so gata har biyu zaɓi wacce kake so, da sauri Julde ta zare rigar jikin Cucuu, cikin sauri Arɗo ya zare rigarsa nan take Zanan Taswirar ya bayyana a ƙirjin ko wannan su, da wani irin sauri Salimerh ta.....



Allah Ubangiji ya nuna mana Monday lafiya😍🤝🏻 idan nai kuskure feel free bawai ka zagen ba dan Allah, ɗan Adam ajizi ne,a kullum muna yiwa Ubangiji laifi bare ɗan Adam😭



*SARAUTAR MARUBUTA*




*_95-96_*
Tai baya luuu zata faɗi Junaid yay saurin tare ta, da wani irin hargitsastsan kallo take bin kirjin ko Wannan su, a hankali kuma cikin ruɗu ta fara bin zanan Taswirar dake ƙirjin ko wannan su,sosai tai mamakin ganin zanan Taswirar yana da bambanci da wacce take jikin Arɗo da kuma wacce take jikin Abu Maleek, Murmushi Muhammad Jalal yay yana wani ɗan lumshe idanunsa kamar yadda Abu Maleek keyi Salimerh ya kalla yace.
"Mamaki ko? Ban san ki ba, i have no idea akan who are you, amma ke har kin samu damar farautar abinda yake ba naki ba? Kin samu damar da zaki kwashe dukiyar da ko mahaifiyar ki bata da iko a kanta balle kuma ke? Uhm kamar nasan da haka, hanyar fitar da kaya ta ƙarƙashin ƙasa a Alaafi guda biyu ce, ko kin samu Taswirar jikine Abu Maleek akwai inda zaki ɓata a hanya, domin an cire zanan ƙofa biyu na ƙarƙashin ƙasa, kina tafiya hanyar zata bauɗe maki, Wow! The you know what? Zaki koma hanyar Zanan Taswirar jikina, ita kuma bakinsa yadda zata fitar dake waje ba, hakan yasa zaki ɓata ɓatt, ki ƙasa dawowa Alaafi kuma ki ƙasa fita wajan gari, hakan na nufin zaki ƙare rayuwarki ne a cikin ƙarƙashin ƙasa" Shiru yay yana sauke numfashi yana jin yadda kansa ke masa ciwo kafin a hankali ya dawo da dubansa ga Malamin Alaafin yace.
"Ka sauya min fuska, kasa anyi min juyan tunanin Mutumin da bashi da imani ko ɗaya a ransa, ko iya haka na Barka Ubangiji zaimin sakayya dakai, na amince maka na yarda da kai na baka dukkan amanata amma kai watsi da hakan ka ruguza farin ciki na, bana ƙaunar fuskar daka sanya aka samin Kamilalliyar fuskata tafi wannan da take jikina, kamar yadda ka sani mu biyu mahaifin mu Jalal ya haifa, da Tunde da kuma ni Muhammad, nine babba amma ko da nayi aure ban samu haihuwa da wuri ba, sai ya zamana Tunde ya rigani haihuwa ya haifi Sharefddeen, Tunde ba yaji he's very stubborn wannan dalilin tun kafin yay aure yabar ƙasar, sai da yay auran muka samu labari, lokacin Mahaifin mu ya rasu, Ni kuma naci gaba za riƙe kujerar sarautar Kanzaf, bisa taimakon Otun da Agba Akin, da Mai Babban ɗaki, sai kuma Ƙwarƙwara ta Roomana" shiru yay yana jin wani hawaye na kawowa fuskarsa cikin dauriya ya kalli Salimerh yace.
"You killed my wife, me tayi maki? Akan kawai biyan buƙatar ki? She's so nice, friendly Educated ina da tabbacin komai kika ce kina so zata baki, kin kashe min matata ba tare da laifin komai ba, ƙilan abinda take gudu kenan shi ne yasa ta maida kanta matsayin ƙwarƙwara, akwai ƙyakkyawar fahimta tsakanin matata da brother na, akwai wasan ƙanin miji yana girmama ta sosai, shiyasa take kula da shi amma kalli yadda kika kasheta,ta hanya mai muni you killed my wife Salimerh" ya faɗa yana zubewa a wajan tare da

Please Login or Register in order to submit comment