Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata macan da tayi katarin gani,
Tsadaddan Murmushi wanda kafin a gani sai an sha wahala.

Murmushi daya haifar da bayyanar wasu irin kyawawa kuma jerarrun teeths ɗinsa, haɗi da wani teeths gave na gefe,
Ga wani haɗaɗɗan dimple wanda yake a iya ɓangaren kumatun sa na dama.
Faɗin kyan da Murmushin yay masa ɓata baki ne.

Hannunsa ya sanya ya tallafa ta sosai, kafin a hankali yay ƙasa da bakinsa saman kunanta yace.
"Su Kululuuu manya, kina son jikin mijinki ko?"
Da wani sauri ta ɗago da jikinsa tace.
"Ni ba mijina bane, bayan Oumuu tace kai Hamma na ne"
Ƙuri yay mata kafin yace.
"Meye Hamma?"
Turo bakinta tayi gaba kafin tace "Yayana mana, ai kai kayi ƙato da zama mijina ko Ballowo"
Kallonta yay Yana jin wani abu mai kama da fargaba na riskarsa.

Bai ce komai ba sai fuskarta da yake kallo, jin hakan yasa ta miƙa hannunta cikin Sa'a kowa hannunta ya sauka akan fuskarsa, wajan ƙwantaccen sajansa wani irin shafa sajan tayi kafin tace.

"Ballowo wannan abun naka yana daɗin taɓa wa"
Ta faɗa tana shafa laɓɓansa kafin kuma ta tura yatsarta cikin madaidaicin bakinsa, ajjiyar zuciya ya sauke yana matse ta sosai a jikinsa yana jin yadda wani sanya yake masa yawo a jiki,
Da sauri kuma tace.
"Wayyoooo Hancina yaji ka cire min"
Idanunsa ya buɗe ile kowa abin yajin ne manne a tsinin hancinta, baya jin zai iya ɗaga hannunsa.

Hakan ya sanya ya ɗan matsar da fuskarsa sosai wajan fuskar ta,
Kana ya manna laɓɓansa a tsinin hancin nata,
Wani irin maraitaccen numfashi mai kama da ƙara suka sauke a tare,
Wani irin kyarma da ɓari jikin Julde ya fara lokacin da laɓɓan Abu Maleek suka sauka fatar hancinta.
Kafin da ƙarfi taja numfashi tana jin yadda numafashi yake gab da barin gangar Jikinta,
Abu Maleek kam lumshe idanunsa yay kafin ya ƙara sauke numfashi, wani irine Amintaccen siɗa yaywa tsinin hancin nata, kafin a hankali ya ɗura da wani lamintaccen tsotsa inda ya tsotse abin yajin kana ya ɗiye zuwa cikinsa.

Kauda fuskarsa yay kafin ya ɓalle medicine ɗinta yace "uhm haaaa" maƙale kafaɗa tayi kafin cikin muryar shagwaɓa tace.
"Ni ban son magani Allah amai nake"
Kallonta kawai yay a zuciyarsa yace "Uhm akwai aiki, mitsitsiya da ita sai salo, fitinanniya kawai"
A fili kuma ya ɗan ya motsa fuska yace.
"Chocolate ne ohyyyah buɗe muga"
Jin ya ambaci chocolate yasa ta buɗe bakinta da sauri ya watsa mata maganin kafin ya manna mata gorar ruwan a bakinta, cikin sauri ta shanye maganin tana kuka,
Miƙewa yay kana ya kama hannunta har yay gaba sai kuma ya tsaya yana kallon kayan jikinta, bai ce komai ba ya juya not too long ya dawo riƙe da wata abaya mai tsayi.

Ba tare da yace komai ba, ya matsa kusa da ita ya kama hannunta tare da yin sama dasu kana ya zura mata rigar idanunsa ƙuri a tsakiyar cibinta, da sauri kuma ya zura mata abayar ba tare daya kalli jikinta ba.

Kai tsaye sashin Mai Babban ɗaki ya nufa da ita,
Tana jin wani daɗi na ratsa mata zuciya jin iska na shigarta tako ina,
Suna shiga kallo ya dawo gare su,
Bola kam idanu kawai ta tsorawa Julde wai wannan za'a ce itace Amintacciyar Hadimar Abu Maleek? Ta ina bayan wannan ƙyakkyawar yarinyar ko matar shugaban ƙasa sai haka,
Ƙwafa tayi lokacin da Oumuu-Ayman tace.
"Zonan Hawwa'u"
Ta faɗa tana riƙe hannunta, Abu Maleek gefen Mai Babban ɗaki yaje ya zauna yana ɗan lumshe idanunsa.

Gyaran murya Mai Babban ɗaki tayi kafin tace.
"Nasan da yawa ko baku tambaya ba, nasan dole a ranku za kuce Wacece Hawwa'u, to Allahamdulillah Hawwa'u Abu Maleek ne ya tsince ta, a hanyarsa ta dawowa nan gida, a rugar Mahinjo, hakan yasa ya taho da ita domin Taimakon rayuwarta,
Daga baya kuma na yanke shawarar zata zama Amintacciyar Hadimar sa, kamar yadda shima ya zaɓa, to zuwa jibi in sha Allah za'ai mata aikin ido, gata kuma za'a naɗa tsarki"

Da sauri Shakiru yace.
"Waye Sarkin?"
Kallonsa tayi cike da nutsuwa da kuma karantar yanayinsa kafin tace.
"Zaka gani ranar"
Bola wacce take cike fam tace.
"Oumuu-Ayman na yiwa Abu Maleek komai da yake so, mene ya sanya kuma a wannan karan zai zaɓi wannan budurwar matsayin Hadimarsa? Gaskiya ni ban amince ba"
Ta faɗa Idanunta na aikawa da Julde harara wacce take raɓe jikin Oumuu-Ayman.

Murmushi Mai Babban ɗaki tayi kafin tace.
"Daman ba amincewar ki ake buƙata ba, an faɗa maku ne domin ku sani"
Cikin wani irin yanayi Bola tace.
"Na amince ni ya mayar dani Hadimarsa zan iya yi masa komai ma dadin makauniyar nan kuma TSINTACCIYA"

Gyara zama Mai Babban ɗaki tayi kafin ta juya ta kalli Julde,kana ta kalli Abu Maleek a nutse ta mayar da Idanunta kan Bola tace.
"Ina tunanin kamar nace Jalaluldeen shine ya zaɓi Hawwa'u matsayin Hadimarsa, kenan wannan ƙorafin mijinki za kiyiwa"
Ta faɗa tana nuna Abu Maleek, tsaye ya miƙe cikin takunsa mai matukar ɗaukan hankali yay waje hannayensa zube cikin aljihun.

Kuka Bola ta sanya tana faɗin.
"Rayuwata da Abu Maleek bata da amfani, rayuwar aure muke ko kuma rayuwar gaba da juna? Bafa ni na tilasta masa zama dani ba, mene ya sanya ya mayar dani abin wulaƙantawa? Baya tunanin akwai sanda haƙƙina zai kamasa ne Eheee? Baya so na fine amma a kullum ya tuna ina rayuwa a Alaafi ne dalilinsa, i have my own family ina da gata da duk abinda yake tunanin yana dashi, if baya ƙaunar aure na he can divorce me, ba zan magana ba yana da right nayin hakan,
Ko cewa akwai ni dutse ne Eheee?? Ban san daɗin jikina bane ko menene? Akwai haƙƙina a kansa na auratayya,
Ko kuma gantali zan fara ina neman mazan wasu?"
Miƙewa tsaye tayi tana sakin kuka kafin tai waje da sauri.

Da idanu gaba ɗaya suka bita, Julde wacce tausayin Bola ya mamaye zcyrta tace "Oumuu to mene yasa take kuka? Ko akan Ballowo ne"
Shiru Oumuu-Ayman tayi ba tare da tace komai ba, Mai Babban ɗaki kam miƙewa tsaye tayi ganin lokacin Sallah yayi kafin tace.
"Zaku iya tafiya, Oumuu-Ayman kibar Hawwa'u nan"
Tana faɗin hakan tai bedroom ɗinta.

A hankali suka shiga ficewa, banda Adams da yake zaune yan manna idanunsa akan Julde,
Oumuu-Ayman ce ta kalli Julde kafin tace.
"Daughter ki zauna yanzu Hadima Akin zata kaiki bathroom kiyi alwala ki Sallah"
Da sauri Julde tace.
"Oumuu Ballowo fa, ni bana son zama nan kaina ciwo yake"
Kallon Julde Oumuu-Ayman tayi sosai kafin tace.
"Yanzu zai dawo nan Sallah ya tafi kinji ko"
Kai kawai ta ɗaga ita kuma Oumuu-Ayman tai waje zuwa nata sashin ta.
Tana barin parlo ya sauke Ajjiyar zuciya yana faɗin "Munafuka!"
A hankali kuma ya dawo kusa da Julde yana kallonta yana jin kamar ya jata ya rungome ko ya samu sassaucin abinda ya keji a ransa cikin so da kuma ƙaunarta yace.

"Cute nayi missed naki sosai kamar zuciyata zata tarwatse"
Ya ƙare maganar cikin rausayar da kansa gefe,
Baki Julde ta washe kafin tace.
"Hamma Adams"
Murmushi Yay mata kafin ya miƙa yatsarsa ya taɓa dimple ɗinta na gefensa,
Ji yake tamakar ya taɓa ganin mai irin wannan dimple ɗin dama fuskar amma ina? A ina? Yaushe? Bai sani ba.
"Kina da kyau sosai cute na, ina sonki da yawa zaki Auran?"
Shiru tayi kafin kuma tace.
"Ba kace zaka kaini asibiti idanuna ya buɗe ba? Kuma zaka kaini makaranta ko?"
Murmushi Yay mata kafin ya juya yaga babu kowa cikin ƙasa da murya yace.
"Yeah sure! Aiki yay min yawa shi ne yasa ranar nan nace Ballowo ɗinki ya kaiki asibitin"
Da sauri ta sauke ajjiyar zuciya jin ya ambaci sunan Ballowo sai kuma tace.
"Laa kaini kasa shi ya kaini, Amma mene ya sanya ya dake ka?"
Rasa me zai ce mata yay kafin kuma yace.
"Cos he hate me, ya tsane ni baya so na"
Ya ƙare maganar tamkar zai saki kuka,
Baki ta buɗe zatai magana taji anyi saurin riƙe hannunta,
Kai Adams ya ɗaga tare da sauke idanunsa akan Abu Maleek wanda yake tsaye hannunsa riƙe dana Julde,
Cikin tarin jin haushin Abu Maleek Adams yace.
"I'm glad to hear that, Zama Hadimarka doesn't means she's your wife Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal, bana tunanin akwai wata mace da zakai mafarkin kasancewa da ita? And babu wata mace da zata iya zama da nakashasshe kamarka, Idan kaga ban auri Julde ba ka ɗauka ni Adams Tunde Muhammad Jalal bana raye"
Lumshe ido Abu Maleek yana taune leɓansa tare ƙara matse hannunsa dake cikin na Julde

Cikin nutsuwa da kuma isa haɗi da Zallar izza wacce ta gama zama a jikinsa tace.
"All the best Adams Tunde Muhammad Jalal"
Yana faɗin hakan yaja Hannun Julde zuwa flat ɗinsa.

Washe gari
Ya kama Monday tun safe Abu Maleek ya shirya cikin kamilalliyar shigarsa, bayan yay breakfast ya bawa Julde maganinta ya nufi company sa.

Julde kam yana fita Oumuu-Ayman ta shiga bata labarin a nutse akan abubuwan cikin Alaafi,
Har ɓatan Queen Roomana sai da Oumuu-Ayman ta
Faɗawa Julde
Hakan kai taji ta samu nutsuwa da Julde shiyasa ta faɗa mata komai!
Kuka Julde ta sanya lokacin da Oumuu-Ayman take faɗin.
"Rayuwar Ballowo ɗinki tana jin tsaka mai wahala, Daughter kowa burinsa bai huce yaga ya kashe Abu Maleek yaga bayansa ba, a kullum a ko wanne lokaci maƙiyi zasu iya kaiwa Abu Maleek hari wannan yasa muke cikin tashin,
Hawwa'u ita fatan zaki zama haske a rayuwar Abu Maleek, ina fatan zaki bashi farin ciki, Jalal yana buƙatar nutsuwa,
Ba zai taɓa samun nutsuwa ba idan ba'a wajanki ba, Maganar naɗin sarauta Abu Maleek shi ne zai zama Sarkin Kanzaf, I'm scared ban san yadda zai ɗauki abun ban,
Ina so ki tayani tausasa zuciyarsa, I'm happy time ɗin kin samu idanunki ki taimaka mana Hawwa'u ki taimaki rayuwar Abu Maleek"
Oumuu-Ayman ta ƙare maganar hawaye na sakko mata,
Domin tasan duk sanda Abu Maleek ya tabbata a matsayin sarkin Kanzaf shike an bawa maƙiya ƙofa.
Da ƙyar Julde tai shiru domin gani take kamar an kashe mata Ballowo ɗinta ne.

Wajan shida na yamma Julde na zaune sanye
Da farar atamfa wacce akaiwa ɗinkin duguwar riga mai faɗi,
Ga wasu pink flowers da suke jikin atamfar,
Tai kyau sosai kamar ka ɗauke domin wannan shine karo na farko data sanya kayan hausawa,
Ita kaɗai ce zaune a Parlo tai shiru tana jin karatun da Oumuu-Ayman ta sanya mata,
Kamar daga sama taji an jawo ta tare da ɗauke ta da gigitattun maruka guda biyu,
Kafin a hankaɗa ta jikin table kanta ya bugu da jikin ƙarfe,
Wani razanan nan ihu Julde ta sanya lokacin da kanta ya dakin bango nan take kuma,
Jini ya fara zuba,
Cikin ɓacin rai da gushe War tunani Bola ta sanya takalmin ƙafarta mai tsini ta dake mata ƙafa,
Subuhanallah wani ihu ta Julde ta sanya mai kama dana ɗaurewar rai saboda tsananin azaba,
Ko kuka ta kasa sai gumi dake yanko mata,
Jikinta sai ɓari yake
A hargitse Bola tace.
"Shegiya munafuka, wallahi Mijina yafi ƙarfin ki, da na zauna ina kallonki ki ƙwace min miji wallahi gwamma na kashe ki, Nima a kashe Ni kowa ya rasa, akan Abu Maleek babu abinda ba zan iya ba, i love him.... I love my husband zan zauna dashi har abada"
Ta ƙare maganar tana ƙara gwara kan Julde ta ƙarfe a wannan karan ko baki Julde bata iya buɗewa ba,
Gaba ɗaya jinta ya ɗauke jini ne kawai ke zuba a goshinta.

Ƙafa Bola ta ƙara ɗagawa da niyyar ƙara dukan Julde taji an sanya ƙafa anyi ball da ita,
Baya tayi tare da faɗawa saman kujera tana sakin ihun,
Kafin ta miƙe taji an sanya hannu an fincikota tare da ɗauke ta da wasu kyawawan maruka, a gigice ta buɗe idanunta ta sauke akan fuskar Abu Maleek,
Ba ƙaramin gigita tayi da ganin yadda fuskarsa ta sauya ba, fuskarsa tayi jajirrr idanunsa har wani ruwa yake,
Abu Maleek kam tashin hankalin daya shiga ba'a magana cikin wata kakkausar murya yace.
"You're mad? Ashe baki da hankali? Kisa za kiyi? Uban me tayi maki ko saboda Ni bazan daku ba?"
Murmushin takaici Bola tayi tace.
"Wow! So akan wannan makauniyar kake mari na? Don't forget I'm your wife, ka fifita wata akan matarka"
Cikin ko in kula yace.
"Wata? Idan akwai wata kece, Jidderhhh tafi ƙarfin wata get lost you stupid"
Dariya Bola ta sanya tana faɗin.
"Thank God sai ka kalleta da ido, domin har bada baza ka ji daɗin ta ba, yadda ban taɓa kasance wa dake matsayin miji a kuma kan gadon ka ba, to itama haka, domin ta haɗu da lusarin miji wanda bashi da abinda zai tsinana mata, ta haɗu da mata maza"
Abu Maleek daya tallafo Julde zuwa jikinsa ya runtse idanunsa domin sosai maganarta ta daki ƙahon zuciyarsa "mata maza" shine za'a kira da mata maza kallon Bola yay yace.
"Ke ba tsari na mace, ko zan kasance da mace baki da abinda zan so a jikinki"
Dry tai idanunta na zubar da hawaye tace.
"Mu gani a ƙasa, ai sai dai kaci kasha amma babu kayan kula da mace domin da ace kana dasu da tuni Maleek ya samu ƙani"
Idanunsa ya ƙara birkicewa kafin ya manna Julde a jikinsa yace "haka kike gani?"
Cikin rashin damuwa tace "haka ne ma, bawai nake gani ba, lusari mata maza kawai"
Wani Murmushin takaicih yay kafin yace "just warch and see"
Ya faɗa yana sauke numfashi tare gyara zamansa sosai,
Idanunsa a saman fuskar Julde, wacce bata da mara ba da sumammiya, ya ƙara haɗata da jikinsa tare da tattare da sumar kanta yay baya da ita,
Sam bai damu da jinin dake fuskarta ba, ya manna fuskarsa a saman ta, tsoro da fargaba suka dirar masa,
Yayinda kuma zuciyarsa ke harbawa da ƙarfin gaske, jikinsa na rawa ya manna jajayen laɓɓansa a saman laɓɓan Julde yasubuhanallah, ji yay kamar an zuba masa narkakkiyar dalma a tsakiyar kansa,
Wani wahaltaccen numafashi ya sauke lokacin daya ware laɓɓansa, lips ɗin Julde ya faɗa cikin bakinsa, wani irin harbawa jijiyoyin kansa sukai yayinda tsigar jikinsa ta miƙe baki ɗaya,

A kusan tare suka sauke wata zazzafar ajjiyar zuciya, da wani irin ƙarfi kuma ya ƙara rungome ta sosai a jikinsa kafin ya ƙara manne laɓɓansa a mata, wata Amintacciyar tsotsa yay wa laɓɓanta, cikin ikon Allah hakan yay dai-dai da harbawar J......



🤸🏽‍♀️🤸🏽‍♀️😍🤝🏻






*_61-62_*
Wata kasalalliyyar ajjiyar zuciya ya sauke yana mai matse idanunsa da suke a lumshe,
Tsananin mamaki da kuma tarin Al'ajabi ya sanya Abu Maleek fesar da wata zazzafar iska, yayinda da ya kejin wasu masifaffun abubuwa nayi masa yawo a saman jijiyoyin kansa, abinda bai taɓa tunin faruwa ba kenan dashi ba,
Ya riga daya sallama akan wannan murɗaɗɗan yanayin abun, sai gashi a lokacin da bai taɓa tunanin faruwar hakan ba, babu zato bare tsammani yaji J ɗinsa tayi harbawa wanda ya kusa tafiya da mutuwarsa.

Ƙara lumshe idanunsa yay, wanda suka tashi daga launin farare suka koma jaa, saboda tsananin azabar ciwon da kansa yake masa,
A tare suka fitar da wani irin wahalallan numfashi,
Yadda gangar jikinsu da ƙirjinsu ke haɗewa waje guda,
Haka ma zuciyoyinsu suke manne, yayinda numfashin ko wanansu yake fita tare dana juna.

Julde duk halin data shiga bai hanata jin wani irin sabon yanayi ba,
Sai dai duk yadda tasu da buɗe baki ta ambaci kalmar "Ballowo" al'amarin ya ta'azzara a gareta,
Wani fitananan ƙamshin strowbeery ne ke mata zirya a cikin hancinta.

Lokacin da Abu Maleek ya samu damar riƙe tongue ɗinta a bakinsa,
Ji yay gaba ɗaya gidan nasa na bala'in juya masa,
Tamakar zai faɗo kansa, azabar da yake ji ne kuma yasa idanunsa cika da wani irin ruwa wanda kai tsaye baka isa ka fasalta yanayi ko kuma launin ruwan ba,
Kifa ƙyakkyawar fuskarsa yay mai cike da nutsuwa da kuma tarin haiba a saman fuskarta,
Yayinda zuciyarsa taci gaba da bada wani irin sauti dib! dib!! dib!!.

Cikin nutsuwa a hankali ba tare da yin wani ƙwaƙƙwaran motsi ba ya zame lip's ɗinsa daga cikin bakinsa,
Yana mai fitar da wani emotional sound!

Wani ihun Bola ta sanya kafin cikin wani irin tashin hankali tace.
"What? Kissing nata kake? Da gaske rungome ta kayi? Akan wannan Makauniya za kaci zarafi na Jalaluldeen??? The you know how much i love You????? Na kasa bacci saboda soyayyyar ka? Ka tsallake ka barni for some years, and u came back duk da hakan ka share ni kama manta ina zaune cikin Alaafi just because of you??? What exactly wrong with you? Eh?? Mena aikata gareka? What i have done to you Abu Maleek? U hate me, even your son ka tsana sa baka son ganin sa?
Kana tunanin Ubangiji zai Barka ne??? Eh? To wallahi idan uwa da ubane sukai cikina bisa sunna suka haifan kamar yadda ban samu damar shiga zuciyarka ba, ban kasance dakai a matsayin sunna ta aure ba, wlh billahi i promise to you Sai na lalata Rayuwar wannan Yarinyar,
Zaka gane cewa ni ma ina da haƙƙi a kan ka, wallahi i Will do anything akan dawo da mutun cin aure na just watch and see Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal"

Tana faɗin hakan tai waje tana sakin kuka, tare da ɗaukan alwashi mai girma akan Julde, tsayin shekara da shekaru ta ɓata akan dawowar Abu Maleek, amma bai ga karamcin zaman jiran da tayi akan sa ba,
Yake shirin zaɓar wata ya barta a matsayinta Na uwar ɗan sa!

Ajjiyar zuciya Abu Maleek ya sauke, kana cikin wata kasalalliyyar murya wacce take bayyana mood ɗin da yake ciki yace.
"Jidderh??"
Ya faɗa yana fesar da numfashi yana jin fitananan yanayi na ratsa dukkan gaɓoɓin jikinsa, a yanzu bashi da nutsuwar da zai tantance maganganun da Bola take faɗi,
Abu guda kowa zucyarsa take iya saurara shine bugun zuciyar Julde dake fita da sauri.

Gently ya miƙe da ita a jikinsa tare da nufar part ɗinsa yana rungome da ita tsam bisa ƙirjinsa,
Duk da yadda zuciyarsa ke tsananin bugawa yana jin kamar zata faso ƙirjinsa ta fito bai hana shi taka ƙafafuwansa bisa kan haɗaɗɗan carpet ɗin daya wanzo a cikin sashin nasa ba.

Kai tsaye kuma bedroom ɗinsa ya nufa yana zuwa ya shimfiɗe ta saman makeken royal bed ɗin sa mai kyau da kuma tsari,
Julde wacce take sauke numafashi da ƙyar ga wani bala'in ciwo da kanta yake mata sanadiyyar ciwon da taci,
Ƙuri Abu Maleek yay mata da idanu kafin a hankali ya sauke numfashi yana ɗan lumshe idanunsa,
Wanda suke jajirrr har wani zubewa tsigar jikinsa keyi saboda jinin dake ɗan zuba bisa goshin Julde!

A hankali ya miƙe yana ɗan taune bakinsa cak ya tsaya jin ta riƙe masa tsakiyar tafin hannunsa, juyawa yay a hankali tare da sauke ganinsa a saman fuskarta.

Julde dake kwance jin alamar zai tafi ya barta ne ga matsanancin ciwon data keji yasa cikin wata raunatacciyar murya tace.
"Ballowo"
Ta faɗa a wahalarce cikin karyar da kanta gefe, domin a yanzu shi kawai take son ji kusa da ita, dukan da Bola tai mata ba ƙaramin zautar da ita yay ba!
Saukar Muryarta cikin kunansa ya haifar masa da wani kasala, yasa shi jin wani abu na sauka a jikinsu mai kama da kiyashi, lumshe idanunsa kafin a nutse ya ɗan yi gaba zuwa,
Kanta idanunsa akan fararan yatsun hannunta masu kyau ya ɗan zauna tare da durƙosa dai-dai kanta yana sauke mata wani zazzafan numafashi.

Hannunta dake cikin nasa ta riƙe idanunta na zubar da hawaye cikin wata Murya mai ɗauke da amon! Kuka tace.
"Ballowo kai na, bafiiii kada ka barni a nan tsolo ina ji kaji"
Ta faɗa ƙwallar idanunta na zirarowa zuwa saman fuskarta.
Idanunsa ya ɗaga kaɗan tare da sauke ganinsa akan jajayen laɓɓanta masu masifar kyau,
Wanda yake ganin kamar jambaki ake sanya masu,
Karo na farko kenan a rayuwa da yaji wani matsanancin tausayinta ya kama shi, a sai kuma a lokacin ya tuna da dukkan abinda Jon wuro ya faɗa masa, tiryan tiryan kuma yaji maganganun na dawowa masa kunne kamar haka.

_"Zuwa yanzu dai Julde_ _amana take a wajanka,_
_Kasan duk wanda yaci_ amana Shida Ubanginsa,
_Bazan maka dole akan ka sota ba,Saboda so halitta ne_
_Amma ina fatan wata rana ka zame mata Garkuwa, bangon da zata jingina taji daɗi, duk abinda_
_Ya samu da rayuwarta a yanzu kuma KAI NE SANADI, kayi haƙuri ka zame mata Hasken da zai haskaka rayuwarta, ko ba zaka so ta ba, ka kula da rayuwarta"_

Lumshe idanunsa yay yana jin kamar yay wasa da amanar Ubangiji, idan ya san bazai iya menene ya sanya tun farko ya amsa? Tabbas a yanzu yana son sanin Wacece Julde? Yana buƙatar komawa Rugar Mahinjo koda hakan zai zama sanadiyyar mutuwar sa.

"Kar ka barni Ballowo dan Allah"
Ya ƙara jin saukar Muryarta cikin kunansa, da ɗan sauri ya buɗe gajiyayyun idanunsa, kafin a hankali ya Lumshe idanunsa saboda wani fitananan ƙamshin ta daya ratsa cikin hancinsa,
Yake haifar da nutsuwa kuma a cikin zuciyarsa,
Hannunta dake cikin nata ya matse tare da ƙara manne su yana jin wani mugun mugun tausayinta,
Meye laifinta akan ya zaɓe ta matsayin Amintacciyar Hadimar sa? Mene yasa Bola take tunanin wani abu a tsakaninsa da Julde? Bayan har yanzu kallo ƙanwa yake mata.

Hannunsa na hago ya sanya kamar mai tsoro ya kifashi a saman fuskarta kafin a hankali,
Ya ƙara ranƙwafawa a kanta, yana jin yadda numafshinta ke fita da sauri,
Innocent face ɗinta ya kalla, kafin Murya can ƙasa kuma yace.
"I'll stay with you Kuluuu, for rever and ever, don't cry okay ban barin ki"
Ya faɗa yana shafa sumar kanta, ajjiyar zuciya ta sauke kafin tai shiru tana jin yadda bugun Zuciyarta ke dai-dai-ta,
A hankali ya miƙe tare da juya cikin zallar kamewarsa ne kuma ya nufi wata ƙofa yana zuwa ya shiga cikin wani bedroom.

First-aid box ya ɗauka, kafin ya dawo cikin bedroom ɗin nasa, ka ya nufi bathroom ya haɗa warm water a bowl ya dawo ɗauke da ƙaramin towel,
Baya jin zai iya jawota jikinsa a yanzu, domin bambancin ne ƙarara da abinda ya keji game da ita ada,
Yana da ita yake ya ɗan matsa sosai gareta, kafin ya sanya fararan hannunsa cikin bowl ɗin ruwan zafin,
Ƙara ta sanya tare da yunƙura wa zata tashi, saboda wani a zababban zafi daya ratsa ta, dalilin saukar towel ɗin a goshinta,
Hannunsa ya sanya cikin rashin Sa'a kuma Hannun ya sauka akan ƙirjinta, yana jin lokacin da tafin hannunsa ya gogi nipples ɗinta.
A ɗan tsorace ya zame hannunsa, yana jin wani abu kamar shouk na jansa, nan da nan kuma yaji tsigar jikinsa na zubewa tare da tashi,
Wani irin runtse idanunsa Yay da ƙarfi a hankali kuma jikinsa ya ɗan ɗauki rawa, kafin gently ya sauke fitanan nishii a kunanta wanda ya sanya tari saurin juyawa tare da faɗawa jikinsa tana faɗin.

"Auchhhiiii Ballowo"
Ta faɗa tana ɗan riƙe gaban rigansa, nishin daya sakar mata a cikin kunanta ya sanya tayi saurin Lumshe idanunta,
Tana jin wani sanyi a jikinta, ga wani nutsuwa da nishin daya saukar mata.
Idanunsa ya buɗe ya shiga Kallonta, wani irin Murmushi ne ya ɗan sauka a fuskarsa, bayyanar dimple ɗinsa ne kuma zai tabbatar maka da cewa Murmushi Yay.
Hannunta ya ware gaba ɗaya, ya sanya su tsakanin hannayensa ya shigar da ita jikinsa, kafin a hankali ya ƙara ɗaukan towel ɗin dake cikin bowl ya ɗan manna mata a goshinta, ƙara ta saki tana sakar masa kuka tare da suma ƙoƙarin kwancewa,
Tana kuka tana cizon sa a haka ya gasa mata wajan ya sanya mata magani, kafin ya gama tuni bacci ya ɗauke ta,
Sai saukar numfashinta da yaji yana sauka a kunansa.
Ƙyakkyawar fuskarta ya shiga kallo, bai tsaya kallon a salin kyanta ba sai yau Tabbas Julde tana da mugun kyau, bai taɓa ganin zallar kyau mara algus irin mata ba.
Hannunsa ya sanya a sanyaye ya shafa sumar kanta wacce take ta tsayi har ya huce shoulder ɗinta.
Cikin wani irin husky voice yace.
"You're my sister _Jidderhhh_, I'll take good care of you, as so much as i can, I'll make you happy, ko dani ban shiga farin ciki ba, ke amanata ce Fulani gal, zan kula dake ƴar filllooo na"
Ya faɗa yana wani irin sauke numfashi kafin gently ya miƙe yana gyara mata kwanciya ya nufi waje.
Gaba ɗaya wannan tashin hankalin yasa ya manta da babban abinda yake damunsa, wanda ya sanya shi baro company ya dawo gida!

Washe gari
Cikin nutsuwa ya fito daga cikin part ɗinsa, yana sanye da wani cotton ɗin dark Maroon na yard, yay masifar kyau sai zabga ƙamshi yake,
Yana tafe hannunsa cikin aljihun wandon sa,
Tunda ya kawo kai cikin parlon idanunsa ya sauka akan ta,
Bai taɓa ganin kyanta irin na yau ba, cikin 10 seconds ya gama ƙare mata kallo,
Kafin ya ɗan taɓe bakinsa kana ya nemi waje ya zauna yana faɗin.
"Mrng Oumuu"
Kallonsa Oumuu-Ayman tayi kafin tace.
"Ya mai jiki?"
Kallon ban gane ba yay mata,ba tare da yace komai ba, kuma ya ɗauke idanunsa yana latsa Wayarsa.
Julde wacce tun shigowar sa ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana mai haɗa numafashi kafin kuma bakinta ya shiga rawa cikin rashin sani kuma taji bakinta

Please Login or Register in order to submit comment