Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiru da yayi yana jin yadda ƙwaƙwalwarsa ke faman aiki amma babu abinda yake fahimta dai wani shuuuuuu!! Da yaji batirin kansa nayi,
ga wasu jijiyoyin kansa da suka miƙe sosai suka shiga harbawa da ƙarfi ciki yanayi na sauri kuma,
duk da hakan bai hana zuciyarsa tsananin bugawa da ƙarfi ba, ya rasa dalilin daya sanya sai ya kusanci Parlon yake samun wannan bugawar zuciyarsa wacce take dai-dai da fitar numfashi, har yanzu ya kasa gane meke haifar da hakan.

sanin cewa kuma babu mace tsarinsa ya sanya gaba ɗaya tunaninsu bai kawo cewa kusancin zuciyarsa data Julde ne ke haifar masa da bugawar zuciyar ba,
ƙara matse shoulder ɗinta yayi yana mai sakin wani fitananan numfashi wanda ya kejin tahowarsa tun daga ƙasan zuciyarsa, al'amarin daya ƙara zautar da duniyarsa, da kuma tunaninsa kenan komai nasa ya gushe, jinsa ganinsa haɗi tunanin da yay raguwa a cikin ƙwaƙwalwar tasa, ƙara ware tsumammun idanunsa yayi wanda sukai jajirr tare da janyewa cikin yanayin na ficewar hayyaci da kuma na Zallar maye, ya manna fuskarsa tsakanin wuyan Julde,ya shiga fidda wani emotional sound kana a hankali ya ƙara manna farar fuskarsa wacce zuwa yanzu ta juye zuwa jaaa, sanyin ƙwantaccen sajansa daya mannu da fatarta yasa ta kame Jikinta waje guda tana ƙara narke fuska,
bugun zcyarsa ka ɗai ya shaida mata cewa Ballowo ɗinta ne her Helper,
bata ganin komai cikin ƙwayar idanunta sai duhun hakan yasa bata gane irin halin da yake ciki, amma sosai ta fahimci akwai matsala, mutumin dako inda yake bai raɓa amma mene ya kawo shi Jikinta male male haka,
teeths ɗinta ta sanya tare da datse jajayen laɓɓanta saboda wani irin fitananan numfashi daya sauke mata a tsakanin wuyanta hakan yasa gaba ɗaya tsigar jikinta zubewa suka shiga tashi.

Abu Maleek kam ya daɗe da lulawa duniyar mashaya hakan yasa baya gane fari balle baƙi infact ma bai san cewa Julde ce a wajan ba,
all What his know shine ya rungome Sweet ɗinsa, kwaɓe fuska yay sosai kamar zai tsaki kuka kafin cikin wata iriyar kasalalliyyar murya mai kama da da husky voice ya ware laɓɓansa Murya can ƙasa yace.

"No.. no one's love me, Uhm no one's what i have done to them? Ba'a so na sweet, even my brother Adams baya sona, he hate me, why kowa Jalaluldeen? Me nayi masu sweettttt, i love them I love my family, my Oumuu, my Mumy, Salimerh and my elder brothers, I love them butttt...."

Sai kuma yay shiru yana lumshe idanunsa a hankali kuma wasu siraran hawayen wahala suka sakko daga cikin idanunsa,
yanayin yadda yake sauke numfashi da sauri zai sanya kasan how sad he's,
sosai yake jin zafi da kuma raɗaɗi a cikin zuciyarsa, amma bashi da wanda sharing all his fellings dashi,
hannunsa ya sanya a hankali tare da mannawa a tsakiyar lafaffan cikin Julde, da sauri ta runtse idanunsa duk da cewa till bata Fahimci mene abinda take ji ba,
amma tana jin wani mugun sauyi a Jikinta, Zuciyarta har wani tsalle take a duk sanda yay ƙoƙarin taɓa ta,
A hankali kuma ɗumin Numfashinsa ke sauka a saman wuyanta, Numfashin daya haifar mata da wata muguwar kasala,
a hankali ya Lumshe idanunsa yana jin yadda numfashi ke fita yana shaƙar wani kuma,
cikin wata raunatacciyar murya mai ɗauke da Zallar rauni ya ƙara buɗe bakinsa yace.

"And the frist person daya keso na, he gone, i lose him ya tafi ya barni sweet, And my happiness tayi nisa dani i lose my mother too, sweet babu wanda yake sonaaaaaa, but duk da haka i love my family sune komai ne, tunci kashi na, fitsari, bana da lafiya suna gigicewa, they loving me lokacin da ciwo ya kamani"

Shiru yayi na wani lokaci kafin wata zuciyar tace masa.

"What about your son Maleek???"
Sharrrr hawaye ya sake sakko masa, kamar ba professional footballer ba,
Aremo ɗan sarki wanda yake shirin zama sarki period,
cikin Murya Mafi rauni da sauran yace.

"Maleek? My photocopy serious bana so....."
Sai kuma yay Shiru da sauri kuma ya manna fuskarsa a wuyanta tare da riƙeta sosai,
ya shiga shassheƙar kuka, a hankali ɗumin hawayensa ya shiga sauka a saman fuskarta, cikin irin yanayi mara fasaltuwa Julde ta runtse idanunta,
a zahiri bata Fahimci komai a surutan mayen giyar da yake ba,
kalma "BABU MAI SONA" itace ta samu gurbin zama a cikin ƙwaƙwalwar ta, su waye basu sansa?? Sune tambayar data kewa kanta amma babu amsa, a hankali itama Hawayen dake maƙale a cikin ƙwayar idanunta suka samu damar sakkowa, rauninta ya bayyana ta dalilin sukar hawayensa, sosai ta gigice hakan yasa ta sanya kuka cikin siririyar muryarta tace.

"Ballowo.. Ballowo Yayana!!!! Kuka kake??? Ko damata maa Ballowo??? Kuke kake? Ina ke baka ciwo kalli kana kuka Ballowo"

Ta faɗa a gigice tana ƙoƙarin zamewa amma riƙon da yayi mata ya sanya ko motsi ta kasa, yana fesar da numfashi idanunsa na janye cikin wata very low voice yace.

"Cry??? Why should i? I'm not cry, I'm hero!!!! I can handle everything sweet"
Ya faɗa lokacin da idanunsa suke ƙara janyewa domin yanzu yaje matakin ƙarshe matakin da a ko wanne lokaci bacci zai iya awon gaba dashi.

Ware jajayen laɓɓansa yay wanda hawaye suka jiƙasu, hakan yasa laɓɓansa sukai wani santsi cikin magajin bacci ya ƙara manna laɓɓansa da sauri Julde wacce Jikinta yake rawa tace
"Auchhhiiii heyyyyy Ballowo"
baya gane abinda yake bare ya fahimci ƴar ƙarar da tayi hakan yasa yaji kamar sweet kitty ɗinsa ce tayi kuka da ɗan sauri yace
"heyyyyy you stop shouting, sweet the you love me? Kina so na?"
Jin abinda ya faɗa yasa Julde saurin ware baki domin duk duniya tana bala'in son taji ance ana sonta, hakan yasa da sauri ba tare da wata manufa ba tace.

"Allah Ina sonka Ballowo, nafi kowa masifar sonka a duniya, Amma baka min magana kamar yadda Yaya Adams keyi min"
ta ƙare maganar a shagwaɓe a hankali kuma taji Numfashinsa yana sauka da sauri hakan ya tabbatar mata da cewa bacci ya ɗauke sa, Shiru tayi tana jin yadda ya sauke mata duk nauyinsa ya hanata kata ɓusss,
ga wani fitananan ƙamshinsa dake cika mata hanci, Ajjiyar zuciya ta sauke tana faɗin
"wai badai nauyi ba, yana ta surutu saboda yasan ban iya karatu ba Allah idan naje makaranta nai karatu nima sai na rama" ta faɗa tana turo baki tare da murguɗa bakin.

Almost 30minutes a haka kafin Oumuu-Ayman ta turo ƙofar babban Parlon ta shigo, zuwa lokacin tuni ya zame daga jikin Julde ya kwanta amma yana riƙe da hannunta gam, Itama Julde a nan kusa dashi bacci ya ɗauke ta, kusan lokaci kowan nan su yake sauke Ajjiyar zuciya,
hakan yasa gaba ɗaya Numfashin su haɗewa waje guda, cike da Mamaki Oumuu-Ayman take kallonsu domin harta kwanta bacci ya fara ɗaukan ta, sai kuma ta tuna da Julde tasan cewa ba lallai bane Abu Maleek ya kaita bedroom ɗinta wannan dalilin ya sanya ta tashi tayo nan kai tsaye, to abinda ya gani kuma yanzu yayi matuƙar bata mamaki, ganin babu inda tunanin zai kai tane yasa a hankali ta shiga tashin Julde.

a firgice ta tashi saboda daman a ɗan tsoran cen ta kwanta, ba tare da Oumuu-Ayman tayi magana ba, taja hannunta a hankali zuwa bedroom ɗin ta, har tsakiyar bed ɗin ta kwantar da ita, tare da lulluɓe ta da duvet,
gorar ruwa ta ɗauka ta ajjiye mata a gefenta inda take tunanin zata iya ɗauka kafin a hankali ta zauna gefenta tace.

"Daughter ga ruwa nan ko zaki nema cikin dare"
Kai kawai Julde ta ɗaga tana ƙara sauke ajjiyar zuciya,
girgiza kai kawai Oumuu-Ayman tare da fita taja mata ƙofar, tana zuwa Parlo ta zauna kusa da Abu Maleek idanunta ta lumshe tana jin matsanancin tausayin zakin nata, magauta sunyi masa yawa, Ubangiji ne kawai ke karesa,
idanunta ta buɗe a hankali ta sauke ganinta a saman ƙirjinsa, ƙuri tayiwa wajan, kafin ta ja numfashi tana ƙara matsawa kusan sa,a hankali ta miƙa hannu da nufin ganin zanan gaba ɗaya domin iya na saman ƙirjinsa kawai tayi, wata kalar zabura Abu Maleek yay tare da kifawa yay rufda ciki.

Murmushi kawai tayi tare da buɗe tafukan hannunta ta shiga karanto addu'a tana tofawa, kafin ta gama ta shafe masa fuskar zuwa bayan wuyansa,
tana jin lokacin daya jan wani wahalallan numfashi saboda sanyin tafin hannunta daya sauka a jikinsa,
Miƙewa tayi tare da gyara masa kwanciya tasan sanyi bai fiya damunsa ba, hakan yasa hasken parlon kawai ta rage masa kana tai waje,
tana fita taga masu tsaron ƙofar Abu Maleek cikin nutsuwa ta kallesu kafin tace.

"Ko kula da kyau, domin yau Abu Maleek a babban parlo zai kwana, idan kuka bari wani ko wata suka shiga ciki, duk abinda ya samu zaki kuyi kuka da kanku"

Zubewa sukai suna mata kirki tare da al'ƙawarin babu abinda zai faru, gaba tayi ta barsu a nan.

4:14
Agogon Nigeria ya buga, wanda yay dai-dai da fara kiran sallan farko da Subhi, a hankali ya juya daga rufda cikin da yay, tun kafin ya buɗe idanunsa yaji gaba ɗaya kwanciyar ba tayi masa daɗi ba.

Ga yadda wuyansa ya ƙage, ya motsa fuska Yay bakinsa ɗauke da addu'a ya shiga ware gajiyayyun idanunsa wanda suka janye kawo lokacin kuma gaba ɗaya jan da sukai ya ye.

A mamagance ya shiga ware gajiyayyun idanunsa saboda ganinsa da yayi a parlo ya matuƙar bashi mamaki, a hankali ya furta "Astagafirullah!!" Domin sai a lokacin ya tuna da abinda ya faru, bai san mene ya sanya har yanzu ya kasa daina shan Alcohol ba, yasan is totally haram in Islam, amma what should i do? Ya tambayi kansa, ya buɗe idanu da Alcohol wanda tun yana ɗan shekara 5 ya fara shanta musamman idan yana jin zucyarsa babu daɗi, runtse idanunsa Yay sosai yana jin wani irin abu mai ɗaci nayi masa yawo a cikin maƙoshinsa.

A hankali ya fesar da iska daga cikin bakinsa kafin gently ya miƙe tare da zuba hannayensa a cikin aljanu ya nufi part ɗinsa, yana shiga ya hangi sweet akan bed ta naɗe Jikinta da duvet, kansa kawai ya girgiza yana mai kwaɓe fuska.

Yana shiga ya sakarwa kansa shower wanka yay sosai, kafin ya wanke bakinsa da sumar kansa, tun a bathroom ya busar da sumar kansa.

Yana fitowa ya shiga shirya kansa bayan ya shafa lallausan cream ɗinsa ne, ya shafa man gashinsa dana gemu ya fesa body spray.

Wata lallausar Embrodiery islam jallabiya ash color ya sanya mai ƙaramin hannu, prayer mat ya ɗauka ya tayar da sallar raka'atul fijir, zama yayi ya fara addu'a da neman yafiyar Ubangiji, miƙewa yayi tare da sanya Scuff faux-shearling slippers kai tsaye ya nufi Masjid yana fidda wani ƙamshi mai daɗi.

Bai dawo gida ba sai wajan 7:15 yana dawowa ya shirya kansa cikin three-piece dinner suit, wacce take dark Maroon, Wayarsa ya ɗauka da briefcase ɗin sa, sosai yay masifar kyau shi kansa yasan kyansa daban yake dana sauran mutane, a haka kai tsaye ya nufi babban Parlo yana zuwa ya samu Oumuu-Ayman da Julde a zaune wacce take sanye cikin Halter top bayan t.shirt ɗin Jikinta, sai black trouser mai kyau, an sanya mata hula mai butterfly, a cikin seconds yay mata kallon siririn tsaki yaja tare da neman wajan zama a gefen Oumuu yace.

"Mrng Oumuu"
Ya faɗa yana lumshe idanunsa wanda sukai masa ɗan nauyi domin har yanzu bacci bai sake sa ba, wani Murmushin jin daɗi Oumuu-Ayman tayi ganin yadda Abu Maleek ya fara sanya kansa busy wannan lokacin tunanin da zaman kaɗai cin duk babu, cike da kulawa tace.
"Mrng, how was your night Zaki?"
"Allahamdulillah" Shine abinda ya faɗa yana ɗan taune leɓansa tare da ƙara Lumshe idanunsa.

Julde dake zaune tun fitowar sa tasan cewa shi ne, saboda yanayin yadda bugawar zcyarta ya sauya, haɗe Jikinta tayi waje guda ta kasa ci gaba da shan tea ɗin dake hannunta, a hankali ta shiga motsa jajayen laɓɓanta Wanda suka ƙara wani irin jaa kamar ana shafa masu jambaki, bakinta na rawa tana ƙara riƙe rigar jikinta da ƙarfi cikin runtsewar idanun cikin wata raunatacciyar murya tace.

"Goo... Good morning Ballowo"
Ta faɗa lokacin da hawaye yake ciki idanunta, sosai yaji saukar sautin Muryarta a cikin kunansa amma ko motsawa bai ba, bare a sanya ran zai amsa, jin Shiru ne ya sanya Julde sakin Kuka tare da kwaɓe fuska kamar Yarinyar tace.

"Oumuu kinga bazai amsa ba ko? daman nace baki ni baya so na, Nima zan daina son shi Allah"
Ta faɗa tana ƙara sakin kukan shagwaɓa wanda kana ganin kukan kasan cewa Zallar taɓa ra ke damunta, Cikin lallashi Oumuu-Ayman tace "A'a ya amsa ba kiji bane Daughter"
Oumuu-Ayman ta faɗa tana share mata hawaye cikin rashin yadda tace "Allah Oumuu bai amsa ba"
Ta faɗa lokacin da take sakin wani sabon kukan, juyawa Oumuu tayi da nufin cewa Abu Maleek ya amsa amma ko inuwarsa bata gani ba, tuni ta fice daga cikin parlon kamar walƙiya.

Abu Maleek kam tun lokacin da yaji saukar Muryarta ya miƙe cike da nutsuwa da kamala haɗi da kamewarsa cike da kwarjini da haiba yay waje, kai tsaye kuma sashin Mai Babban ɗaki ya nufa.

Masu tsaron ƙofar na ganinsa suka shiga yi masa kirari, ko takan su bai bi, kai tsaye ya shiga Parlo Mai Babban ɗaki a can saman wata haɗaɗɗiyar ladduma ya sameta.

Amintacciyar Hadimar ta wato Hadima Akin ta shirya mata breakfast, zamewa yay tare da zama a gefen ta, kafin ya ɗan narke fuska ba tare da yace mata ya sanya hannunsa a saman plate ɗin dake shaƙe da kayan marmari ya ɗauki Apple wacce aka yayyanka.

Cikin nutsuwa ya sanya yankakkiyar Apple ɗin a bakinsa, zaki da kuma sanyin Apple ɗin ya haddasa lumshewar idanunsa ba tare daya shirya ba, Murmushi Mai Babban ɗaki tayi kafin tace.

"Yau Mijina na gaban goshi ya tuna dani kenan, anya wannan auran zai yiwu kowa Zaki?"
Ta faɗa tana ƙara tura masa plate ɗin fruits ɗin, idanunsa a lumshe cikin nutsuwa kuma yake tauna Apple ɗin sa, kafin ya ware idanuna a kanta cikin kamala da kamewa yace.

"Barka da safiya Granny"
Ya faɗa lokacin da yake kai ɓararan tanjirin bakinsa, Mai Babban ɗaki da farin ciki ya cika mata zuciya tace.

"Sai naji abin farin ciki wajan Oumuu-Ayman, tace ka buɗe Company ko? Toh toh ma sha Allah, Allah ya taimaka ya shige maka gaba"

Idanuna a Lumshe yana shafa cikinsa da yaji yayi ɗan nauyin kafin a hankali ya kama lip's ɗinsa ya shiga taunawa kamar bazai magana ba sai kuma yace.

"Ameen Granny, uhm Ina son ganin Hadima Zubaida"
Shiru tayi tana kallonsa kafin ta ɗan jinjina kai tace "You have to do that kana da ikon yin haka baka da shamaki"
Sauke numfashi yay tare da ƙara gyara zama cikin ƙasa da murya ya buɗe baki zai magana yaji saukar muryarta, da sauri ya haɗe fuska tare da juyawa ya fuskanci Granny ɗinsa, Maleek dake Hannun Bola ya zame da sauri tare da nufar wajan Abu Maleek cikin farin ciki yake faɗin.

"Bàami! Bàami!! Bàami na"
Ya faɗa lokacin da yake faɗawa kan Abu Maleek da sauri Abu Maleek ya runtse idanunsa saboda wani kalar bugawa da zuciyarsa tayi masa.

A sanyaye Bola ta shigo ciki tana ɗan sauke wata Ɓoyayyiyar ajjiyar, ganin Abu Maleek a yanzu ba ƙaramin sanya mata nutsuwa da farin ciki yay ba,daman tazo da niyyar gaishe da Mai Babban ɗaki ne.

Zama tayi kanta a ƙasa tana ɗan satar kallon dugun wuyansa wanda gashi ya kwanta a kai, ba ƙaramin kyau yay mata duk da cewa bata kalli fuskarsa ba, cikin ƙasa da Murya tace.

"Barka da safiya Mai Babban ɗaki"
Jinjina kai Mai Babban ɗaki tayi kafin tace "Ya Maleek ya kwana da jiki?" Cikin damuwa tace "Allahamdulillah, amma zazzaɓin ya takurasa jiya kwana yay yana kiran Bàami da ƙyar yay bacci"

A hankali Abu Maleek yakai dubansa zuwa ga Maleek wanda yake kwance a jikinsa, sai a lokacin ya lura da ramewar da yaron yay ga wani hucin zafi da yake fitarwa, a hankali cike da tsoro kamar mai shirin taɓa wuta ya shafa wuyan Maleek, zafin da yaji ne ya sanya shi lumshe idanunsa lokaci guda kuma tausayin ɗan nasa ya ratsa masa zuciya, a hankali ya shafa kansa ba tare da yace komai ba.

Ba jimawa kuma ya miƙe yana jin lokacin da Bola tace "Mrng Abu Maleek ya jiki?"
Banza yay mata a hankali yaci gaba da tafiya da sauri Maleek ya riƙe hannunsa yana faɗin.
"Bàami zan bika"
Narkakkun idanunsa ya zubawa yaron wanda yake tsananin kama dashi, domin kamannin sa da Maleek har makaki yake basa, ba tare daya hana Maleek ba sanya hannunsa tare da ɗaukan sa cak ya rungome sa, kana ya juya cike da nutsuwa yabar flat ɗin.

Yana fita ya haɗu da Salimerh da Sharefddeen, Murmushi Sharefddeen yay yace "A'a yau kai da Maleek, like father like son"
Salimerh dake tsaye cikin shirin makaranta tace "Zaki Allah komai naka my son ya kwashe ina ga saura kaɗan ya fara buga ball a gidan nan"
Ta faɗa tana kama hannun Maleek da sauri ya kasance hannunsa yana Rungome Mahaifin sa da kyau, saboda gani yake yana sauka zai gudu ya barsa.

A sanyaye Abu Maleek ya sauke numfashi tare ware idanunsa cikin kasala ya kalli Sharefddeen yace "Bro" ya faɗa a hankali Sharefddeen yace "Munji abin Alkairi Allah ya sanya alkairi Congratulations once again Bro"
Salimerh dake yiwu Abu Maleek da Maleek photo a iphone ɗin ta tace "wlh I'm so much happy Zaki, ba kaji daɗin da naji ba, sai nazo siyan Shoes da jersey masu kyau na Companyn J&J ART SHOE AND JERSEY DESIGNER.

Wani sangartaccen Murmushi gefen baki Abu Maleek yayi wanda kai tsaye ba zaka kirasa da Murmushi ba, saboda rashin sabo dayin Murmushi kafin ya ɗanyi gaba yana faɗin.

"Thank you Bro/Sis"
Ya faɗa yana yin Gaba yana jin yadda Maleek yake sauke numfashi mai zafi alamar tuni bacci ya ɗauke sa, kai tsaye mota ya nufa inda ya samu p.a Sameer na jiransa, karɓar kayan hannunsa yay shi kuma ya shiga mota yana ɗauke da Maleek.

Kamar kullum sai bayan sallar Isshā ya dawo gidan saboda aikin da yayi masa yawa, ganin dare yayi ne ya sanya ya nufi sashinsa da Maleek a nan ya barsa ya kwanta shi kuma ya shiga wani bedroom ɗin ya kwanta Shida sweet.

Washe gari
Wajan 11 na safe Oumuu-Ayman ta shigo sashin na Abu Maleek yau gaba ɗaya makara tayi, kai tsaye bedroom ɗin Julde ta nufa tana zuwa taga babu kowa ciki, da mamaki ta shiga Bathroom tasan cewa ballai tana ciki ba,ga tunaninta kowa bata ciki, da sauri ta nufi part ɗin Abu Maleek tana zuwa ta samu Maleek zaune da Sweet suna wasan ball, tashin hankali ya bayyana a fuskar Oumuu-Ayman, ina Julde zata da wanne idon zata fita? Babu inda bata shiga a cikin flat ɗin Abu Maleek ba amma babu ita, cikin kiɗima da kuma tashin hankali ta shiga kiran Number Abu Maleek sai da tayi kira wajan uku kafin ya ɗaga, lokacin yana tsaka da drawing na wata sabuwar jersey a hankali ya sauke numfashi tare dayin baya yana ɗan tsotsar laɓɓansa cikin wata husky voice yace.
"Oumuu!!"
Jin Muryar Abu Maleek yasa Oumuu faɗin "Zaki Banga Julde ba"
Cikin rashin fahimta ya ɗan saki laɓɓansa kafin yace "wace haka?" Wani haushi ne ya kama Oumuu-Ayman cikin ɗan faɗa tace.
"Ohh! Saboda ina rabuwa dakai ko? Matarka ce baka sani ba? To ka sani duk abinda ya sameta wallahi laifin ka ne"
Taɓe baki yay kafin cikin nutsuwa yace "to ban gan ta ba" ya faɗi hakan ya kashe kira a hankali kuma cikin wani irin sabon yanayi juyar da kansa tare da sauke ganinsa akan Jul....


Abu Maleek na kuɗi ne, kiji tsoran Allah ki daina karanta abinda ba naki ba, ko banyi Allah ya isa ba nasan Ubangiji zai isar min domin baya barin haƙƙin wani akan wani ki biya 500 ki karanta cikin nutsuwa 0116886423 sulaiman Naima s union bank 08119237616



*_51-52_*


Julde wacce take kwance saman sofar office ɗinsa tana bacci, sai sauke Ajjiyar zuciya take saboda kukan da tayi.

Domin har ya janyeta daga cikin Bedroom ɗin ta ya kawota office ɗinsa bata san ko wanene ba, hakan yasa ta tsorata, tsoron da yayi mata yawa ne kuma yasa gaba ɗaya ta kasa fahimtar yanayin sauyin bugawar zcyarta.

A hankali ya zame idanunsa daga kanta, tare da maida kallonsa ga zanan da yake, cikin nutsuwa yaci gaba da zana sabbin Desgner na jersey masu kyau da tsari.

Yana nan zaune har lokacin sallar zhur tayi, A hankali ya miƙe yana tattare hannun rigarsa, cikin nutsuwa ya nufi bathroom ɗinsa, alwala ya ɗaura, bayan ya fito kai tsaye ya bar office ɗin ya nufi Masjid ɗin dake cikin babban Company nasa.

A hankali Julde ta shiga motsawa tare daya motsa fuskarta, har lokacin kuma ajjiyar zuciya take saukewa, domin duk a firgice take, kwaɓe fuska tayi tana cinno bakinta gaba kamar ƙaramar kafin a hankali cikin ƙunƙuni tace.

"Uhm, ko waye ya satoni ma ohhhu, Allah sai na faɗawa Ballowo na, dan anga bana gani ko?"
Ta faɗa tana narke fuska, kafin a hankali ta miƙe tana mimmiƙa hannunta gaba domin samawa kanta hanya.

Slowly ta Fara tafiya tana bin bango, tana a haka ne kuma cikin rashin sani goshinta ya daki bango, wata gigitacciyyar ƙara ta saki tare da zubewa a wajan tana yarfe hannu nan da nan kuma wajan ya kumbura jini ya taro cikinsa.

Wata a zaba ce ta shiga ratsa dukkan jijiyoyin jikinta, yayinda Jikinta ya ɗauki rawa da kyarma, gaba ɗaya ta firgice ta shiga rera kuka tana yarfe hannunta.

Abu Maleek dake tsaye shida P.a yana sauraran abinda p.a yake faɗa masa, a hankali ya sauke numfashi tana ɗan Lumshe idanunsa kafin ya ware idanunsa da suke ɗauke da gajiya akan P.c cikin ƙasa da murya yace.
"Wane date aka sanya?"
Rusunawa p.a yay cikin girmamawa yace.
"Sir, till now ba'a sanya date na ƙaddamar da sabbin kayan namu ba, amma mun gama komai kai kawai muke jira, domin a lokacin za'a haɗa da bikin buɗe Company baki ɗaya ne, to the choice is yours"

Hannayensa duk biyun ya zuba a wandon suit ɗin jikinsa, kafin ya ɗan taune leɓansa yana furzar da iska daga cikin bakinsa kana a hankali kamar mai raɗa yace.

"Kayi komai p.a"
Ya faɗa a taƙaice tare da juyawa ya fara tafiya, da idanu p.a ya bisa, sosai yake mamakin Abu Maleek gashi dai company nasa ne, amma yana abu like an masa dole, ɗauke wannan tunanin yayi a ransa kafin yace.

"Sirr!"
Cak Abu Maleek ya tsaya a hankali ya juya ya kalli p.a da wannan narkakkun idanunsa masu ɗauke da wasu ninadari mai karyar da zuciyar mai kallonsa, ware idanunta yay sosai, hakan yasa P.a fahimtar yanayin kafin yace.

"Sir wasu sun buƙaci ganinka, saboda suna buƙatar kayan wannan company, nace zan shirya masu appointment dakai, hakan yasa nake gaya maka Yanzu domin naji wacce rana kake free sai nayi masu magana ta Gmail ɗinsu"

P.a ya faɗa yana yin ƙasa da kansa domin sam bazai jure ganin ƙwayar idanun Abu Maleek ba, Abu Maleek kam ƙuri yaywa P.a da gajiyayyun idanunsa kafin a hankali ya janye idanunsa ba tare da yace komai ba, domin baya jin zai iya magana a wannan lokacin.

Juyawa yay yaci gaba da tafiya yana shirin ɗura hannunsa a saman handle ɗin ƙofar p.a ya ƙara faɗin.
"Sirr"
Da wani sauri ya juya ya kalli P.a cikin yanayin damuwa da kuma zafin zuciya ya buɗe baki da niyyar yin magana, sai ya fasa saboda wani gigitaccen ihu daya jiyo daga cikin office ɗin sa, da sauri ya juya yana mamakin ihun mene haka??? Domin serious yana manta da batun Julde, yana ƙoƙarin juyawa ga P.a ya ƙara jin ihun a karo na biyu, da sauri ya murɗa handle ɗin tare da ɗan tura kansa ciki.

Idanunsa ya shiga rarraba wa, sosai ihunta ya sanya kansa sarawa, a hankali ya ƙara tura kansa ciki can ya hangeta ta durƙoshe sai kuka take tana yarfe hannu, idanunsa ya ƙura mata, ganin yadda take acting like baby girl, gaba ɗaya kuma ƴar duguwar rigar Jikinta ta tattare daga ƙasa fara manyan cinyoyinta sun bayyana sai glowing suke.

P.a dake bayan Abu Maleek wanda shima ya kasa tafiya saboda ihun da yaji, da ɗan sauri cikin yanayi na kulawa yace.

"Sir what happened?"
P.a ya tambaya yana ƙoƙarin tura kansa cikin office domin ganin abinda yake

Please Login or Register in order to submit comment