Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Maleek yake sauke numfashi a hankali, da alama ya fara jin sassauci daga ciwon da yake ciki,
Idanunta ta ɗaga ta kalli Adams ganin Gaba ɗaya idanunsa ba akanta yake ba yasa ta juya, sai a lokacin data tuna da Julde na wajan, a ranta tace.

"Shikenan batun ɓoyewa ya ƙare"
Mema ya sanya ta fito da ita ne, yanzu bata da wata mafita wacce zata kare kanta da kuma ƙaryar da zata shimfiɗa akan Julde, cikin basarwa tace.

"Allahamdulillah, naga ciwon ya fara sauka, taimakamin na kaisa Bedroom"
A hankali ya zame idanunsa yana mai dashi akan Abu Maleek, wanda gumi ya shiga feso masa jikinsa kuma duk ya saki,
Shikam tunda ya fara shaƙar Inhaler yaji numfashin nasa ya fara sauka a cikin huhunsa, hakan yasa ya ƙara narkewa jikin Julde yana shaƙar Inhaler yana shaƙar ƙamshin dake fita a ƙirjinta, yayinda har kawo lokacin hawayenta bai tsaya ba.

Miƙewa Oumuu-Ayman tayi tare da ƙoƙarin janye kan Abu Maleek dake ƙirjin Julde, da sauri Julde ta kwaɓe fuska hawaye na sakko mata tace.

"Oumuu zai gudu fa, kice kada ya sauka Kinji"
Ta ƙare maganar tana ƙaryar da wuya like yadda Abu Maleek ɗin keyi,
Ganin haka yasa Oumuu-Ayman faɗin.
"A'a Daughter, ɗaki zan kaisa fa, naga bacci zaiyi"
Girgiza kai Julde tayi tace.
"A'a Oumuu ni kibarsa ba kinci bashi da Lafiya ba?"

Adams dake Kallonta yace
"to ba kya jin nauyi ne? Kalleki ba kuma ki kallesa"
Shiru tayi Saboda jin baƙuwar Murya da tayi sai kuma tace
"waye wannan ɗin? Shima ɗan ki ne?"
Oumuu-Ayman dake janye Abu Maleek tana miƙar dashi zaune tace.
"Eh, yayan Ballowo ki ne"
Washe baki tayi haƙuranta da sukai fari yanzu suka bayyana kafin tace.
"To amma dai kana magana ko? Ba Irin Ballowo ne ba kai? Nama san zakai magana ai ina jin hakan a jikina"

Shiru yayi mata sai fuskarta daya tsorawa idanu, kafin a hankali ya sauke idanunsa zuwa cikin idanunsa da yake masa tsananin kama da dana Abu Maleek har blue ɗin ciki iri guda ne, bambancin kawai nata a ɗan juye suke, sosai surutun ya birge Adams.

Abu Maleek kam cikin dauriya ya ɗan aro jarumta ya sanyawa kansa, duk da cewa har kawo lokacin bai ji dai-dai ba, amma ya ɗan samu relief daga azabar ciwon da yake ciki, bisa taimakon Oumuu-Ayman ya miƙe tsaye gaba ɗaya kuma ya narke a jikin nata, ita dai Oumuu-Ayman bata tsaya biyewa Adams ba taja Abu Maleek zuwa can part ɗin da yake amfani dashi a cikin flat nasa.

Bayan shigewar su ne, kuma Adams ya gyara tsaiwarsa cikin son jin sautin zazzaƙar Muryarta yace.
"Ke kuma magana kike so? Cai cai cai haka?"
Ya faɗa yana kalon tsarin surarta, jerarrun teeths ɗinta ta buɗe tace.
"To ai kurma ne kawai yake shiru da bakinsa ko? To kai yaya sunanka?"
Murmushi yayi sosai yana shafa kai yace.
"You Are beautiful, i mean kina da kyau sosai"
Ya faɗa yana Kallonta kafin kuma ya ware idanunsa saboda abinda yaji tace na.

"Haka a Rugar mu wasu suke faɗa, amma kasan mene?"
Girgiza mata kai yayi domin a tunaninsa tana kallonsa, jin shiru ne yasa Julde tura yatsarta a baki tana fara tsotsa kuma ta zame tace.

"Ayyah! Nikam ai ban taɓa ganin kyau ɗina ba, kai ma kana da kyau ne kamar nawa?"
Ta faɗa lokacin da idanunta yayi rau rau, da mamaki Adams yake Kallonta kafin yace.

"Kamar ya?? Mene yasa baki kallon kyan naki?"
Yarfar da hannayenta tayi Alamar ohhhu!! Sai kuma tace.
"To ai bana gani, nifa Makauniya ce, kai ma bana ganinka, haka ban taɓa ganin Ballowo ba, har muka gama zama a cikin jeji"

Wani irin buɗe ido Adams yayi saboda kaɗuwa da al'ajabi gadai idanunta sosai a buɗe babu wata alama data nuna ita Makauniya ce, cikin mamaki yace.

"Wacece ke? Daga ina kike? Wane ya kawo ki nan ɗin tunda ke Makauniya ce, And wanne jejie kike magana"
Ya jera mata tambayar yana ƙara buɗe ido
Baki Julde za buɗe zatai magana sai kuma Oumuu-Ayman ta katse ta da faɗin.

"Daughter lokacin sallar Isshā yayi maza zo muje kiyi, kici abinci ki kwanta kinji ko"
Da sauri Adams ya juya a zuciyarsa yana faɗin.

"Ƙwarƙwara da ita tafi mutanan gida sakewa, duk laifin Daddy ne daya bata dama mtwss!!!!"
Ya faɗi hakan a ransa yana ɗan jan siririn tsaki gefe guda kuma ya fice daga flat ɗin cike da so da kuma ƙaunar Yarinyar daku sunanta bai sani ba.

Ƙara narkewa jikin duvet ɗinsa Abu Maleek yayi yana jin wani iri sam ɗumin duvet ɗin bai gamsar dashi ba, duk da cewa a cikin halin ciwo yake amma ya fahimci ɗumin jikin Julde daban yake dana duvet ɗin, kuma har A.c Oumuu duk sai wani blue light ta bar masa,
Marai-raice fuska yayi yana taune leɓansa yana jin yadda kuma numfashin sa ke dai-dai-to wa, lumshe idanunsa yayi sai kuma ya saki tsaki saboda abinda yake masa gizo a cikin idanunsa,
A haka bacci ya ɗauke sa.

Washe gari
4:10
Ya shiga motsa idanunsa Wanda sukai masa nauyi sosai, wani numfashi yaja cikin Sa'a kuma yaji Numfashinsa yayi nrml kamar ko yaushe, cukurkuɗewa yayi cikin duvet ɗin kafin ya miƙe zaune a hankali bakinsa ɗauke da addu'a,
Ya motsa fuska yayi jin yadda gaba ɗaya jikinsa yayi weak, lumshe idanunsa yay yana taune leɓansa da sauri kuma ya buɗe tunawa da ko sallar Isshā bai ba, jiki a sanyaye ya miƙe tsaye,
A hankali ya miƙa hannunsa ya kunna light ɗin bedroom ɗin, cikin nutsuwarsa da kamewa irinta masu sarauta ya nufi bathroom,
Ruwa mai ɗan zafi ya sanya rabonsa da ruwan zafi kam har ya manta, bayan yayi wanka yayi brush ya ɗaura alwala, handrayer,
Ya ɗauka sai kuma ya ajjiye yana langwaɓar da kansa gefe saboda gaba ɗaya bashi da wani kuzari.
Jikinsa yaja zuwa bedroom yana zuwa yaja stool ya zauna,
Wani cream ya shafa mai ƙamshi da laushi kana ya shafa wani Ginger Geminal Oil -hair bayan ya shafawa kan nasa mai ne ya ɗauki Luxury Beard Oil ya shafa a sajansa zuwa gemunsa, nan da nan ya ɗauki ƙamshi da kuma ƙyalli.

Wata lallausar White kaftan ya ɗauka mai gajeran hannu ya sanya bayan ya sanya pat da trouser, a hankali ya jawo wata ƙatuwar prayer mat ya shimfiɗa cikin nutsuwa kuma ya tayar da sallah, bayan ya idar ya zauna har lokacin sallar Subhi yayi jiki a matuƙar sayaye ya gabatar da sallar dan bazai iya zuwa Masjid ba, yana idarwa ya zame rigar jikinsa ya zauna da trouser nan na ɗewa yay cikin duvet nan take bacci ya ɗauke sa.

Gaba ɗaya suna zaune saman dinning area kasancewar yau Friday ne, Salimerh dake shan coffee ta kalli Oumuu-Ayman tace.
"Oumuu-Ayman kwana biyu banga Zaki ba, ko kuma miskilanci nasa ne ya motsa a kanmu"

Girgiza kai Oumuu-Ayman tayi tana ajjiye spoon ɗin hannunta tace.
"Kwana biyu baya jin daɗi Asthma ɗinsa ya tashi tun shekaran jiya"
A gigice Salimerh ta miƙe tana faɗin.
"Subuhanallah, amma Oumuu-Ayman mene yasa baki faɗa min na duba shi ba?"
Ta faɗa cikin tausayin yayan nata, Murmushi Mai Babban ɗaki tayi tace.
"Ai da sauƙi nima yanzu naje dubasa yana ma bacci, kuma naga yau ɗin da safe har wajan tsuntsayen sa yaje, ƙila zuwa Yamma ya fito"

Ajjiyar zuciya Salimerh ta sauke sai yanzu hankalin ta ya kwanta, a hankali ta zauna ta fara cin abinci, a ranta kuma tana faɗin.
"Ka ƙara haƙuri, haƙiƙa azzalumai sun Cutar da rayuwarka, Amma komai yazo ƙarshe Lokaci kawai nake jira lokacin da gaskiya zata bayyana kanta"
Ta ƙare maganar zucin tana Miƙewa domin tafiya makaranta.
Queen Ayoola, Bola, Adams, Shakiru ba wanda yayi magana sai Sharefddeen da yace.

"Allah sarki Zakin Oumuu-Ayman our champion har yanzu Asthma bar barshi ba, Allah ya ƙara lafiya zan dubasa zuwa anjima"

Miƙewa Oumuu-Ayman tayi tana faɗin "Ameen ya rabbi, sai kazo"
Ta faɗi hakan ne kuma domin tasan Sharefddeen bashi da Matsala, da wani irin kallo Queen Ayoola tabi bayan Oumuu-Ayman dashi, Bola ce ta numfasa tace.

"Dan Allah Oumuu-Ayman na biyoki na dubasa??"
Ta ƙare maganar Zuciyarta a karye, Allah ya gani tana son mijinta ciwonsa kuma dole ya shafe ta, Kallonta Oumuu-Ayman tayi kafin tace.

"Yana bacci yanzu, amma yana tashi zan nema maki iso wajansa"
Ta faɗa tana yin gaba zuwa fita daga cikin baban flat ɗin family ɗin baki ta isa zuwan cikin asalin harabar Alaafi ɗin, nan da nan Barori da Fadawa suka shiga zubewa suna gaida ita, kasancewar ta ƙwaƙƙwarar late King bai sanya sun hana bata girma ba, domin soyayyarta ƙarara ta bayyana a fuskar Late King Tunde Muhammad Jalal hakan yasa Kowa na Alaafi yake girmama ta fiye da Asalin matarsa Queen Ayoola, Queen Roomana wannan mai gaba ɗaya ce,
So da ƙauna ko ina nuna mata yake.

Kai tsaye wajan Dawakai ta nufa fa, Sarkin Kilisa na ganinta ya miƙe tsaye yana zubewa tare da gaisar da ita, Murmushi tayi sosai kafin tace..
"Ina fatan ana kula da dawakan Jalaluldeen Tunde Muhammad??"
Cikin girmamawa yace.

"In sha Allah, kullum cikin hidimta masu ake sunyi kyau da kuzari sosai ai zaiji daɗin ganinsu"
Juyawa tayi ganin ba kowa yasa tace.
"Yaya Khaleluddeen yake? Fatan yana cikin ƙoshin lafiya?"
Ƙasa yayi da kansa yace.
"Ya shugabanta Khaleluddeen yana cikin ƙoshin lafiya, kamar yadda kika buƙaci na bawa matata ta kula dashi har zuwa lokacin da zaki buƙace sa"
Numfashi ta sauke cikin jin daɗi tace.
"Ma sha Allah, ina godiya kwarai sai na sake dawowa"
Ta faɗi haka tana juyawa, wajan Shanu ta nufa ta amshi Madara mai zafi wacce aka tasu a idanunta kana aka zuba mata zuma akai.

Kai tsaye flat ɗin Abu Maleek ta nufa,
Fitowar sa kenan daga cikin part ɗin da yake kwana, yana sanye cikin wasu Sleeveless jersey tank top wacce take milk sai tracksuit trouser mai kyau shi kuma black, yana tafe a hankali saboda rashin kuzarin da har yanzu bai samu ba, hannunsa riƙe da Inibi yana sha, sai sweet dake hannunsa,
Kai tsaye babban Parlo ya nufa inda yake saka ran ganin Oumuu-Ayman yunwa yake ji sosai,
Yana fitowa ya buɗe baki yana faɗin.

"Oumuu! Oumuu!! Oumuu na fito yunwa ciki na please"
Ya faɗa yana lumshe idanunsa tare da zubewa a saman kujera yana ajjiye sweet, jin zuciyarta ta buga da ƙarfi ne yasa ya ɗan marai-raice fuska tare dasa hannu ya riƙe saitin wajan, mostin da yaji ne ya sanya ya buɗe idanunsa kai tsaye kuma idanunsa ya sauka akan Julde wacce take bacci a saman kujera ta juya tare dayin miƙa, gaba ɗaya tayi baya zata faɗi, hakan yasa ya miƙe yana jan tsaki tare da nufar inda take kafin ya ƙarasa yaji ta saki wata iriyar......


Abu Maleek isn't free contact to subscribe 08119237616
Kiji tsoran Allah🥰





*_45-46_*
Miƙa a hankali kuma ta sauke ajjiyar zuciya tare da mirginawa ta koma baccin ta, tana haɗe Jikinta waje guda saboda sanyin A.c, domin ko sanyin gari babu a flat ɗin na Abu Maleek ko ina a rufe yake.


Ganin ta gyara kwanciyar nata ne ya sanya shi yin baya tare da komawa saman kujera ya zauna, shiru yayi zuciyarsa fal tunani, ganin tunanin na son yi masa yawa ne ya sanya ya ɗauki remote ya kunna t.v, duk channel ɗin da yakai sai yaga suna love serious tsaki yaja murya can ƙasa yace.

"Uhm! Iskanci ko ina ba dole mutum ya lalace ba idan yana kallon wannan shirman"
Ya faɗa yana saurin sauya channel daga telemondo zuwa zee world, lumshe idanunsa yayi a hankali kana ya shiga sauke ajjiyar zuciya, kafin a hankali ya buɗe idanunsa tare da sauke ganinsa akan wani mutum dake fuskar t.v,
Yanayin shigarsa mutumin ya tabbatar da cewa sarki ne, ƙara ware idanunsa yayi sosai, ganin yadda yake zazzaga mazifa, yayinda matansa suke gefe da alama kuma shine da gaskiya.

Idanunsa ya mayar ƙasan t.v haka nan ya samu kansa da duba sunan film ɗin ganin an sanya Johda and akbar yasa ya tabbatar da cewa mijin shine Akbar matar kuma Johda amma sauran matan fa?? Jalaluldeen Muhammad Akbar ne ya zare ta kobin hannunsa lokacin daya samu labarin ɗan gidan Mahmanga wacce ya kewa kallon uwa ya shigo palace ɗin ya kashe masa babban amininsa kuma ɗan uwansa..

Haka Abu Maleek ya wanzu a parlon yana kallon Film ɗin Johda and akbar yana nan zaune har aka gama episode ɗin ranar aka tsaya a wajan da Akbar yake ƙona kujerar Sarauta saboda baƙin ciki da kuma tashin hankali, yace kujerar bata haifar masa da komai ba sai damuwa, ko burinsa yaga ya mallaki kujerar dan haka bata da wani Amfani shine ya sanya ya cilla mata huta.

Sauya channel yayi zuwa International channel wato (Aljazeera) Ajjiyar zuciya ya sauke tare dayin baya ya lafe saman kujerar tare da lumshe idanunsa,
Tunani ne fal ransa, haka nan kuma tunaninsa ya ƙara ta'azzara tunda ya kalli Johda and akbar, wato sarauta banzar abace, musamman yadda yaga palace ɗin su Akbar take, Masarauta iya Masarauta, amma kowa son zuciyarsa yake bi, mutane kaɗan ne masu tsoran Allah,
Ƙara fesar da iska yayi daga cikin bakinsa, wato zafin mulki sai ya sanya ka kashe ɗan uwanka?? wannan tunanin Shine a ransa kafin ya ja table ya ɗura fararan ƙafafuwansa yana jan tsaki a cikin ransa yace.

"Shima Akbar yayi haɗa ma, mata uku kamar wani maye, Queen Johda, Queen Rukayyah, Queen Salima"
Ya faɗa yana sanya hannunsa tare da shafa sajan fuskarsa yana ɗan fidda numfashi kaɗan.

Oumuu-Ayman ce ta shigo cikin Babban Parlon hannunta riƙe da wata ƙwarya mai kyau anyi mata zanan tambarin sarautar, tunda ta shigo idanunta ya sauka a kansa yana zaune ya lumshe idanunsa tare miƙar da ƙafafuwansa a saman table,
Wajansa ta nufa tana sakin Murmushi tana zuwa ta ajjiye ƙwaryar hannun nata a saman wani table ɗin daban, kafin ta juya ta nufi cikin wani wanda da alama kitchen ne, plate ta ɗauka ta zuba masa alkali da bakilawa, sai kuma wani da zuba masa tarkacan fruits domin yau abincin Masarauta take son yaci.

Bayan ta gama jera masa komai a table ɗin ne ta nemi waje kusa dashi ta zauna tare da faɗin.
"Zaki your breakfast is ready"
Idanunsa ya buɗe a hankali ya kalleta sai kuma ya ɗauke idanunsa tare da kawar da abinda yake ransa, table ɗin ya tsorawa idanu kafin da sauri ya kalli Oumuu-Ayman tare da faɗin.

"Oumuu what is this??? Nifa ba wannan ba"
Ya faɗa yana marai-raice fuska tare da langwaɓar da kansa gefe guda alamar shi ba'ai masa dai-dai ba,
Idanunta ta ɗauke daga garesa bayan tayi masa wani irin kallo sai kuma tace.
"Abinda za kaci yau kenan, na tsara maka time table na duk abincin daza kaci, Breakfast, lunch, dinner, bayansu duk abinda aka baka ban yarda kaci ba"
Ware idanunsa yayi sosai kamar bazai magana ba sai kuma yayi baya yana faɗin..

"Gaskiya Ni bazan iya cin wannan abun ba, mene wannan abun a duƙunƙune kuma??"
Sosai abin ba ƙaramin mmki ya bata ba, musamman yadda taga yana narke fuska hakan ya tabbatar mata da gaskiyar abinda zuciyarsa yake faɗa,
Tana jin yadda yake mita tai masa banza haka ta bashi Alkalin tauna ɗaya yayi yace shifa sam bazai ci ba,
Sai ma ya motsa fuska yayi tare da Miƙewa tsaye yana faɗin.

"Oumuu wannan ai a ciki zai tsaya kawai aiyi wani kamar maciji, uhm"
Ya faɗa yana shigewa cikin part ɗinsa kai tsaye kuma bathroom ya huce ya ɗaura alwala jin ana kiran sallar zhur, bayan ya fito ne ya samu Oumuu zaune da Julde tana bata Abinci,
daga kallo ɗaya da yayi musu bai sake ba ya nufi ƙofar baya kai tsaye ya shige masjid.

Julde ta ɗan kwaɓe fuska tare da faɗin
"Oumuu to baya magana ne wai shi??"

Ta faɗa tana shagwaɓe wa, kamar zatai kuka.
Murmushin kawai Oumuu tayi domin ta daɗe da fahimtar Julde matan nan masu surutu, gashi kuma Ubangiji na neman haɗata da miskilanci miji wanda gane masa sai addu'a.
Fresh milk ta bata tana faɗin.
"Yana magana mana,ba kiji muna hira dashi ba"
Rau rau haka idanunta suka kawi ruwa kafin ta tura baki gaba tace.

"Oumuu to ni mene yasa ba yayi min? Ko dan yaga bana gani ne, Allah Oumuu yanzu ji nake dama iduna zai buɗe naga Ballowo nasan ba wani kyau ne dashi ba"
Wani irin Murmushi Oumuu-Ayman tayi kafin ta ɗaga Idanunta a sanyaye ta kalli bakin ƙofa,
haɗa ido sukai da Abu Maleek wanda yake tsaye jinjine da ƙofa ya a harɗe hannayensa waje guda,
Kallon yadda ya haɗe fuska tayi waje guda kafin ta ɗauke idanunta tana danne dariyar dake shirin kwace mata tace.

"Eh gaskiya bai cika wani kyau ba, gashi nan da manyan idanu,
da gashi har wuya kamar wani buzu,
sai tsayi da faɗi kamar basamude,
kai abinda zai wanda ya gani"
Oumuu-Ayman ta faɗa tana sakin wata lafiyayyiyar dariya mai ban sha'awa,
Abu Maleek kam cika yayi fam sai bakin yarinyar daya tsorawa idanu ko yawo bata haɗiya sai ɗan ban zan surutu kamar ako.

Julde dake sauraran abinda Oumuu-Ayman take faɗa ne yasa ta karyar da wuya tace.
"Ayyah, kenan shi yasa baya magana? Oumuu Kice yana kulani mana"
Ta faɗa kamar zatai kuka,
Daga bayansu sukaji ance.
"Ni zan kulaki idan shi yaƙi, har labarai zanna baki ai"
Washe baki tayi fararan haƙuranta suka bayyana har wani haske suke fiddawa kafin tace.
"La!! Yayan Ranar ko Oumuu, shi kam yana da kirki"
Da mamaki Oumuu-Ayman ta juya tana kallon Adams mene ya sanya masu tsaron flat ɗin Abu Maleek suka basshi ya shigo? Idanunta ta ɗauke daga kallon Adams kana ta miƙe tsaye tare da shigewa bedroom ɗin da Julde take kwana,
Tayi hakan ne kuma domin ta haɗawa Julde ruwan haka, dalilin kuma hakan zai sanya ta janyeta daga wajan Adams.

Da idanu kawai Abu Maleek yake kallon ɗan uwansa Adams da ita kanta Julde mamaki ya kamasa, ganin yadda Adams ɗin yake ta jan Julde ta surutu,
Hakan nan yaji zuciyarsa babu daɗi ransa ya ɓaci ga wani mugun haushin yarinyar daya cika masa zuciya,
Mai makon ya shigo sai kawai ya fice tare da nufar Lambu.

Adams kam duk abinda Abu Maleek yana sane dashi, yana son ya Fahimci mene halaƙarsa da Yarinyar amma ya kasa fahimtar hakan, saboda yadda fuskar Abu Maleek take a ɗaure hakan yasa bai fahimci komai ba.

Gyara zama yayi idanunsa akan Julde yace.
"Uhm what's your name? I mean menene sunanki beauty?"
Shiru tayi sai kuma tace "Naji ƙamshin turaren Ballowo shi ne ya shigo?"
Ta faɗa tana narkar da fuska, da rashin fahimta yace.
"Ballowo?? Waye haka kuma?"
Cikin siririyar muryarta tace "Oumuu tace sunansa Jalaluldeen amma ana ce masa Abu Maleek to Shine Ballowo ai"
Shiru yayi yana nazari kafin ya ɗan cije baki yace.
"Nagane, ba shi bane ƙamshin turarena kikaji"
Girgiza kai tayi Idanunta na kawo ruwa tace.
"Allah shi ne gashi nan naji zuciyata yana harbawa, kuma sai yazo waje kawai na kejin hakan"
Ta faɗa Idanunta cike da hawaye, wani abu mai ɗaci Adams ya haɗiye domin jiya kawai da yaga yarinyar tayiwa zuciyarsa mugun kamo, da ƙyar ya iya bacci daya rufe idanunsa ita yake kallo.

Ajjiyar zuciya ya sauke tare da faɗin "Ok Amma kina son idanunki su buɗe ko?"
Da sauri ta ɗaga kai tace "Eh ko dan naga Ballowo ai"
Jinjina kai yayi yace "Ok zanwa Oumuu-Ayman magana za'a fita dake waje ayi maki aiki idanunki su buɗe"
Wani daɗi ne ya lulluɓe zuciyar Julde wanda ya sanya tayi ɗan tsalle a saman kujera hakan yasa brest ɗinta juyawa wanda suke a tsaye ƙam,
Cikin farin ciki tace "Dan Allah da gaske kake? Idanuna zai buɗe?"
Murmushi yayi mai sauti domin komai na Julde birgeshi suke kafin yace.
"Eh mana, amma kiyi min al'ƙawari"
Da sauri ta ɗaga kanta tace "Nayi maka Allah tunda idanuna zasu buɗe"
Ɗan juya yayi sai kuma ya sauke numfashi ganin babu kowa ne yasa shi faɗin "Kimin Al'ƙawarin ba zaki taɓa auran Ballowo ɗinki ba?? Kimin Al'ƙawarin ba zaki taɓa son sa ba"
Shiru tayi a zahiri tasan kalmar Aure kuma tasan daman ai Ballowo ɗinta bazai ce zai aureta ba, sannan bata san soyayya ba tana jinta dai a baki,
Ya take? Ya daɗin ta take duk bata sani ba, ganin tayi shiru yasa Adams faɗin.
"Ko baki son idanun naki ya buɗe ki fara gani kamar kowa beauty?"
A sanyaye tace "A'a ina so, kuma na baka al'ƙawari"
Wata lafiyayyiyar ajjiyar zuciya Adams ya sauke yana jin wani daɗi na ratsa masa zuciya kafin ya ɗan ware idanunsa yace.
"Ok Yaya sunanki, Nima gaya min tunda Oumuu-Ayman ta faɗa maki nawa ko?"
Ji tayi Jikinta duk yayi sanyi ba tare da sanin dalilin faruwar hakan ba tace.
"Hawwa'u Julde"
Lumshe idanunsa yayi yana jin daɗin sunan nayi masa yawo a cikin ƙwaƙwalwarsa.

Oumuu-Ayman ce ta fito fuska a sake tace "Zo Daughter kiyi wanka ki Sallah ki kwanta ki huta"
Hannu Julde ta miƙawa Oumuu-Ayman haka ta miƙar da ita suka nufi ciki,
Gyara zama Adams yayi domin ya ɗauki alwashin bazai bar gurin nan ba sai an faɗa masa Matsayin Julde a cikin Alaafi.

A hankali yake tafiya cike da nutsuwa da kamewa ga wata haiba da kwarjini daya mamaye ilahirin saman fuskarsa,
Yana tafe yana sauke numfashi tare da Ajjiyar zuciya a jajjere yana jin ransa na ƙara ɓaci,
Ga kuma gudun da zuciyarsa ta ƙara, a haka ya isa haɗaɗɗan Lambun nasa mai ɗauke da shukoki da furanni dabam dabam,
Ga kukan wasu tsuntsaye dake tashi a hankali yake saukar da nutsuwa kuma a zuciya,
Gusa da ƙoramar dage gudana a wajan ya ƙarasa, tare da zama a wajan wata duguwar kujera ta hutawa,
Jikin kujerar yabi ya ɗan kishin giɗa yana sauke ajjiyar zuciya tare da lumshe idanunsa, a hankali kuma ya zura ƙafafuwansa cikin ƙoramar,
Ya shiga wasa da ƙafafuwansa nasa yana jin daɗin sanyin ruwan nayi masa daɗi,
Wayarsa dake aljihu ce ta fara ƙara yana ji amma bai ko motsa ba, sai da akai wajan 5 miss call kafin ya zaro haɗaɗɗiyar wayar tasa,
Ganin sunan Salimerh yasa yayi answering call tare da sawa a speaker.

Daga can ɓangaren kowa Salimerh ce, zaune a cikin mota Dawowar ta daga makaranta kenan, har zata shiga ciki sai kuma ta tsaya tare da ɗaukan waya ta kira Abu Maleek ajjiyar zuciya ta sauke lokacin da taji ya ɗaga kiran.
Kafin a hankali ciki ƙasa da Murya yadda ba zata damesa ba tace.
"Fatan zaki yana cikin koshin lafiya?"
Ta faɗa tana ƙara gyara zama, sanin ba lallai yayi magana bane yasa ta faɗin.
"Zaki dan Allah dukkan abinda zai fito a hannun Mumy kada kaci, ko ruwa ta baka kada kasha"
Ta faɗa cikin raunin Murya.

Abu Maleek dake sauraranta ya ɗan gyara kwanciyar sa yana ware idanunsa tare saukar da idanunsa a saman nunannun gauva wacce sukai manya gwanin sha'awa,
Kafin ya Fito da tongue ɗinsa ya shiga taune leɓansa tare da sauke ajjiyar zuciya yace.
"Uhm"
Ya faɗa cikin wani Emotional sound domin tun ɗazo ya kejin jikinsa duk yayi weak.

Jin "Uhm" ɗin da yace ne yasa Salimerh fahimtar cewa ƙarin bayani ya keso cikin nutsuwa da kuma dadɗan kalami tace.
"I don't means anything Zaki, kowa da kalar zuciyarsa, Mumy mahaifiyata ce, amma kwanan na fahimci wasu muna nan abu a tare da ita, to dan Allah ka tayani tseratar da rayuwarka, idan kayi hakan zaka taimake ni ƙwarai wajan ganin nayi aikina ba tare da wani matsala ta faru ba, a yanzu hana da shaidar da zan nuna maka amma Tabbas ina zargin mahaifiyata akan abubuwan da suke faruwa a cikin Alaafin, Dan Allah Zaki daga nan har abada kada ka sake bawa Mumy dama a kanka, Kada ka sakar mata fuskar da zata baka wani abu tace kaci"

Ta ƙare maganar Muryarta na rawa kamar zatai kuka,
Tunda ta fara maganar yake sauraranta yake kuma fahimtar kalaman nata, amma tayaya Mumy zata cutar dashi? Baya tana bashi maganin damuwa a lokacin da zuciyarsa take masa ciwo? Wannan maganar ma ta sanya yaji yana ƙaunar zuwa wajan Mumy yaji idan zai samu abinda take basa.

Jin yayi shiru ne Kamar baya fahimta yasa Salimerh faɗin.
"Please Zaki saboda Allah ba danni ba"
Ganin tana shirin sauya masa lissafi yasa a ɗan kasalance ya buɗe baki yace.
"Ok!"
Ya faɗi hakan yana kashe kiran nata,
Kafin a hankali ya miƙe jin ana sallar Asar, ko flat ɗin bai koma ba ya nufi Masjid.

Oumuu-Ayman ce ta kalli Adams tace.
"Me kace?"
Ta faɗa like batai understanding maganar tasa ba, bai damu ba domin shike nema a wajanta dan haka ya gyara zama yace.
"Wacece wannan Julden? Mene haɗin ta da Alaafi??"
Murmushi Oumuu-Ayman tayi tace.
"Ba kowa bace ita ɗin face sabuwar Hadima wacce ake sanya ran zata zama Amintacciyar Hadimar sabon King"
Jinjina kai yayi cike da gamsuwa kafin yace.

"Zan ƴantar da ita, domin naji kamar ina sonta Oumuu-Ayman, kuma zan fita da ita waje domin a gyara mata idanunta"
Kallonsa kawai Oumuu-Ayman tayi tana Miƙewa tsaye tace "To babu matsala za muyi magana da Mai Babban ɗaki, batun ƴantar da ita kuma

Please Login or Register in order to submit comment