Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake sauraran dukkan abinda take faɗa masa, mai kama da tatsuniya, she never understand his fellings, ballai tasan abinda yake ransa kuma yake damunsa ba.

Shi kansa baya jin cewa akwai wata rana daza tazo ya amince da mace, komai na rayuwarsa yana tafiya ne bisa umarnin zuciyarsa, bai taɓa yin abu ance ba dai-dai bane, hakan yasa baya gane dai-dai da kuma ba dai-dai ba,
Rayuwa yake ta kaɗai ce wacce kuma yake jin daɗin ta a yadda yake!

Ajjiyar zuciya ya sauke yana mai ɗan Lumshe idanunsa dan baya jin zai amsa maganar ta Oumuu-Ayman dan bata da wani muhimmanci a garesa, rayuwarsa shi kaɗai mugun daɗi take masa.

Kallon yadda ya rufe idanunsa tayi a hankali kuma numfashin sa ya fara sauka,
wanda yake fita da wani irin zafi,
Gane cewa ballai yayi magana ba domin duk abinda bashi da muhimmanci a garesa baya damun kansa dashi.

A hankali ta shafa lallausar sumar kansa tana jin so da kuma ƙaunar Jalaluldeen na ratsa zuciyarta,
yayinda tausayin rayuwarsa ya mamaye dukkan Zuciyarta,
lumshe idanunta tayi a hankali ta sauke ajjiyar zuciya yayinda wani kalar rauni ya cika mata zuciya, cikin tausasa murya mai ɗauke da su da kuma kewa yace.

"Ya Allah! Ka bawanka ka kula dashi, ka sanya albarka a cikin rayuwarsa, Ya Rabbi ka kare rayuwarsa daga magauta, Allah ka sanya masa tawakkali a cikin zuciyarsa, Ubangiji ka sanya kada rauninsa ya bayyana ga maƙiyansa, Allah ka karesa daga cikin kariyarka, Allah ka bashi lafiya ka cire masa tsoron da mata suka dasawa zuciyarsa, Ya Allah ga bawanka Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal ka kula dashiiiii"

Ta ƙare maganar a raunace yayinda idanunta ya cika da hawaye, bata san mene zai je ya dawo ba, amma Tabbas Zuciyarta ta fara samun nutsuwa da kuma gamsu wa wacce bata san dalilin faruwar hakan ba.

Yadda Numfashinsa ke fita a hankali ne ya ɗan cure waje guda, tare da narke jikinsa a jikin Oumuu-Ayman yasa Oumuu fahimtar kewa da kuma ɗumin jikin uwa da yayi, Tabbas Abu Maleek yana buƙatar kulawa yana son kasancewa da Uwa mahaifiya wacce bai daɗe a wajanta.

Hannunta tasa a hankali ta shiga shafa sumar sa yayinda bakinta ke motsawa tana yin addu'a tare da tofa masa a tsakiyar kansa.

Duk da cewa bacci yake amma sosai yake jin daɗi da kuma sanyi a ransa sanadiyar addu'a da Oumuu take masa, wani irin kuzari da kuma ƙarfi ne suka sauka a saman gangar jikinsa, a haka yaci gaba da baccin daya daɗe bai ba, sai Ajjiyar zuciya yake saukewa akai akai!

Ganin yadda yake jin daɗin baccin ne yasa Oumuu gyara masa kwanciya tare da riƙe tafukan hannayensa, a haka suka kasance tare Abu Maleek sai sharar bacci yake.

Adams ne yake tafiya a hankali kansa a ƙasa, cikin nutsuwa da kamala kai tsaye sashin Mai Babban ɗaki ya nufa, bai shiga ba sai da Mai Babban ɗaki ta bada umarnin ya shiga.

Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga yana ɗan cilla idanunsa, a can ya hangota saman Ladduma hannunta riƙe da casbawa tana jaa.

Kallonsa tayi kafin tace.
"Lale! Da zuwa mijin tun shekaran jiya ban sanyaka a idanuna ba, lafiya dai?"

Kwallon e kawai yayi ba tare da yace koma ya nemi waje kusa da Mai Babban ɗaki ya zauna, kafin a hankali ya dumeta da kyau yace.

"Matar irin wannan kyau haka, ko ni akaiwa??"
Ya faɗa yana sanya hannunsa tare da ɗaukan Apple ɗin dake gabanta a saman plate ɗin dake ɗauke da nau'in kayan lambu kala-kala.

A hankali yasa Apple ɗin a bakinsa tare da gutsira kafin yace.
"Nikam Ina Oumuu ne?? 2days ban ganta ba"
Ya faɗa yana ƙara gutsirar Apple ɗin.

Jinjina kai Mai Babban ɗaki tayi kafin tace.
"Kasan shalelenta ya dawo, tana can wajanta hala shine ya tsare ta ta son jikin nan nasa, kamar wannan magen tasa wacce yana nan tare da ita rai da rai kamar wata uwarsa"

Shiru Adams yayi bai ƙara magana ba, sai Apple ɗin da yake sha, ganin hakan yasa Mai Babban ɗaki sanya hannunta ta ajjiye plate ɗin fruits ɗin tana faɗin.

"A'a ya haka kuma?? Wannan sata ne ko kuma fashi?"
Kallonta yayi ya ɗan sakin murmushi kafin yace.

"Da bindiga kika ganni hala? Sata kuma ai ba sata nayi ba, Allah ki ban ko naje na kwashe waccar zumar da kike masifar so"

Zare ido Mai Babban ɗaki tayi kafin tace.

"Yau na kejin sabuwar masifa? A'a wallahi babu ruwan maza fice min, kada na sake ganin shuɗaɗɗiyar ƙafar nan taka"

Miƙewa tsaye Adams yayi kafin ya faki idanunta ya kwashe Apple ɗin gaba ɗaya na plate ɗin.
Yana ɗauka Otun na shigowa ganin haka yasa Mai Babban ɗaki sakin kuka tare da faɗin.

" Yawwa Otun tunda kai Ubansa ne ƙilan yaji maganarka, wallahi ko dai ya biyani ko kuma na kira masa Police, dan Allah wannan ba fashi bane, yanzu kai magana ace rikicin tsufa bane, gaba ɗaya kuɗaɗe ba shine yake kwashe su, to Fisabilillahi wannan ba sata bace? A'a wallahi bazan iya zama da ɓaruwa ba"

Ta ƙare maganar tana sakin kuka tare da ɗaukan wayarta tace.

"Wallahi babu ruwana da cewa kai jikana ne, yanzu zan sa akai ka bayan kanta"

Ta ƙare maganar tana danna wayarta, Otun dake tsaye ya nemi waje ya zauna kafin ya kalli Adams dake tsaye yana ɗan sakin murmushi yace.
"Aremo mai kai mata ne? Matar da ba lafiya ba....."

Da sauri Mai Babban ɗaki ta katse Otun da faɗin.
"Muhammadur Rasulullah S.a.w na shiga Aljanna naƙi fitowa masifar da kake jawo min kenan? To wallahi sai dai kaga Junaidu a gadon Asibiti ba dai ni ba"
Ta ƙare maganar tana sakin kuka, Murmushi kawai Otun yayi domin ya fahimci tun lokacin rasuwar late King Tunde Muhammad Jalal Mai Babban ɗaki ta ƙara riki cewa, ga kuma shekaru dake a kanta kullum,
Gyara zama yayi yana faɗin.

"Kai Adams mene kayi mata ne har haka? Ko kuma kana son kwanan kanta ne?"
Ka faɗa Adams ya ɗaga tare da watsar da hannu alamar "Ohhhhoo!!"
Kafin ya juya cikin izza yabar musu wajan yana sakin Murmushi.

Bayan fitarsa ne kuma Otun ya gyara zama sosai, cikin nutsuwa tare dayin ƙasa da murya yadda Mai Babban y zata fahimci abinda zai faɗa yace.

"Mai Babban ɗaki daman magana nazo muyi ne, naga kuma dake kaɗai ya dace nayi maganar shine ya sanya nace bari nazo wajanki"

Kallonsa Mai Babban ɗaki tayi, kafin ta ɗauke idanunta tana ɗan jan casbahar hannunta, gane cewa ba zatai magana bane yasa Otun ƙara yin ƙasa da murya yace.

"Kin san cewa sarauta bata jira..."
Da sauri ta katse sa da faɗin "Ai haba dai, bani da labari ai"
Ta faɗa tana ɗan yi masa kallon gefe, jinjina kai kawai Otun yayi yana danne abinda yake ransa kafin ya ɗura da faɗin.

"Eh! Haka ne, Sarauta bata jira, koda ba za'a naɗa wani ba, ya dace a bawa wani riƙon ƙwarya domin hakan zai sanya Mutunan Kanzaf suji daɗi a ransu su gane cewa ko babu King Tunde Muhammad Jalal akwai wanda zai iya mulkarsu kuma yayi mulki irin na Murgayi"

Jinjina kai Mai Babban ɗaki tayi tare da ɗaukan glass ɗin ta, ta sanya kamar ba zatai magana ba sai kuma tace.

"Au too! Yanzu na gane yanzu mene kake so ayi sarautar za'a naɗa ko kuma riƙon ƙwaryar??"
Ta faɗa tana ɗaukan sandar ta, tare da Miƙewa tsaye hakan ya sanya Otun sauke numfashi kana cikin jin daɗin fahimtar maganarsa da Mai Babban ɗaki tayi yace.

"A'a ko riƙon ƙwaryar ne sai a fara, kafin a duba wanda ya dace ya hau kan wannan kujerar, daman ko Agba Akin ko kuma ni naga duk mu manya ne zamu iya komai"

A hankali Mai Babban ɗaki ta fara tafiya zuwa cikin bathroom ɗin wanda aka ƙawata da kayan mure rayuwa, sai da taje bakin ƙofar shiga bedroom ɗin ta tsaya tace.

"Babu maganar riƙon ƙwarya, Sarauta za'a naɗa ana yin 40days ba kowa bane kuma King ɗin sai Zakina Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal, idan ka fita ka jamin ƙofar"

Tana faɗin hakan tayi cikin ɗaki tana surutu ƙasa ƙasa,
Wata harbawa zuciyar Otun tayi yana jin wani irin mai kama da damuwa ko kuma baƙin ciki yana mamaye dukkan kofufin zuciyarsa,
Cikin rashin kuzari da kuma juyawar da kansa yake ya miƙe tsaye tare da ficewa daga cikin sashin na Mai Babban ɗaki.

Mai Babban ɗaki kowa na shiga Bedroom ladduma ta sanya tare da tayar da sallar zhur saboda jin masallacin Alaafi na tayar da sallah.

A hankali Abu Maleek yake taka ƙafafuwansa, fitowar sa kenan daga cikin Masjid, idanunsa ya lumshe yana sauraran abinda da Shakiru yake faɗa,
Kasancewar duk tare suka fito daga cikin Masjid ɗin, Yana tsakiya Yayinda Shakiru ke gefensa sai kuma Sharefddeen dake gaba yayinda Adams yake baya.
Shakiru ne ya ƙara duban Adams dake baya yace
"Big bro Company's takalan man nan yana buƙatar sabbin ma'aikata, kuma ƙwararro duba da yadda muka samu sabbin disygner masu kyau da kuma ƙayatarwa"
Jinjina kai Adams yayi kafin yace.

"Kuyi magana da P.a mana Shakiru ka faɗa masa abinda ake buƙata, and why kake tambaya ma? Bayan kai ne Manager na Companyn"
Ya faɗa yana gyarawa zaman agogon hannunsa , Murmushi Shakiru yay kafin yace.
"Haka ne big bro daman na faɗa maka gane kada kazo kaga baƙin fuskoki a companyn, amma zanyi komai dani da P.a"

Ya faɗa yana duban Abu Maleek dake tafe a hankali yana sauraran dukkan abinda suke faɗa, bai san komai na daga kasuwanni ba, shiyasa bai fiya gane dukkan zan can da suke faɗa ba, ƙara Lumshe idanunsa yayi yana taune leɓansa saboda bugawar da zuciyarsa tayi,
Wani Murmushi Shakiru ya yi kafin ya dubi Adams yace.

"Ga Abu Maleek ko za'a fara ta kansa ne, domin ya rage zaman gidan hakan zai sa ya daina zama cikin kaɗai ci da kuma samu kansa cikin damuwa"
Ya faɗa yana kallon Abu Maleek Sharefddeen dake gaba juyawa yayi ya kalli Jalaluldeen ganin yadda ya marai-raice fuska ne kuma tare da taɓe baki yasa kawai ya ɗauke kansa tare da shigewa cikin sashinsa, domin tuni sun Shigo cikin Makaken babban side ɗin Family na Alaafin.

Adams ya ɗaga kansa a hankali kuma ya sauke idanunsa akan bayan Abu Maleek dake tafiya kamar bai so, tafiya kuma mai cike da nutsuwa da kamala, sosai Abu Maleek ya kere su a girman jiki tsayi faɗi, uwa ba tarin haiba da kwarjini ga wani sahihin kyau mai ɗaukan hankali,babu abinda yafi ɗaukan hankali a jikin Abu Maleek sai jajayen laɓɓansa da kuma blue eyes ball ɗinsa, sai kuma ƙwantaccen gashin bayansa Wanda yake ɗaure da ribbon.

Ɗauke idanunsa yay ba tare daya ƙara kallon Abu Maleek ba ya dubi Shakiru da yake ƙare masu kallo yana son ya fahimci wani abu yaji Adams yace.

"Shakiru kayi abinda yake gabanka kawai, duk abinda kukai da P.a let me know!"
Ya faɗa yana ɗan tsayawa ganin hakan yasa Shakiru tsayawa yace.
"In sha Allah big bro komai zai tafi cikin tsari"
Yana faɗin haka ya dubi Abu Maleek daya ɗan tsaya shima yana kallon sararin samaniya a hankali kuma yake tsotsar laɓɓansa da suke ɗauke da danshin ruwa yace.

"Our footballer ko magana babu yau?"
Abu Maleek yi yayi kamar baiji abinda Shakiru ya faɗa, yayi hakan ne e saboda baya son takura ko kaɗan, wajansa Shakiru ya ƙarasa yana faɗin.
"Ina fatan gwarzon mu yana lafiya, ya kuma ƙarin haƙurin mu?"

Gently Abu Maleek ya juyo tare da sauke tsumammun idanunsa akan Shakiru kafin ya ɗan sauke ajjiyar zuciya yana dai-dai-ta tsaiwarsa, bakinsa ya shiga motsawa yana son dai-dai-ta kalaman da zai faɗawa Shakiru can kuma ya numfasa yace.

"Allahamdulillah bro"
Ya faɗa yana Lumshe idanunsa wanda suke nuna gajiyawa da maganar da yayi ga kuma tarin baccin dake idanunsa, domin har yanzu gajiya bata gama sakinsa, uwa ba kewa da rashin Dad ɗinsa dake damun zuciyarsa.

Murmushin Shakiru yay yana yin gaba tare da faɗin.
"Allah ya ƙara mana haƙuri da juriya"
Ya ƙare zan can yana shigewa cikin sashinsa shima, wajan ya rage daga Adams sai Jalaluldeen, cikin nutsuwa Abu Maleek ya ɗaga idanunsa tare da sauke kallonsa akan Yayan nasa, wanda ganinsa yake haifar masa da nutsuwa yake jin kamar Maminsa ya gani,
Shima Adams ɗin kallonsa yayi sosai, kallon da yake nuna zallar tsana da kuma ƙyamata,
Zuciyar Abu Maleek tayi rauni sosai a hankali ya langwaɓar da kansa gefe guda cikin nutsuwa kuma ya nufi wajan Adams yana zuwa ya faɗa jikinsa tare da ruggumesa yana sakin ajjiyar zuciya mai nauyi yayinda farin ciki ya lulluɓe zuciyarsa, muryarsa na rawa yace.

"I miss You so much Lovely bro"
Ya faɗa yana sakin tagwayen ajjiyar zuciya mai ɗan ƙarfi, Rungumesa Adams yayi kafin ya ɗura bakinsa akan kunnan Abu Maleek yace.

"Uhm ya tabbata kai ne ka sace Mami, duba da yadda baka damuwa da rashinta, na tsaneka Jalaluldeen tsana mai yawa, tsanar da ban taɓa yiwa wani ɗan adam ba, wallahi muddin baka dawo min da mahaifiya ta ba, uhm!!!!"
Ya ƙare maganar yana janye jikinsa daga jikin Abu Maleek kai tsaye shima ya nufi sashinsa

Runtse idanunsa Abu Maleek yayi yana jin tsallan da zuciyarsa tayi sosai kalaman Adams suka tsaya masa tashin hankali, tsoro da fargaba suka ratsa masa zuciya, lumshe idanunsa ya ƙarayi yana shaƙar iskar dake Kaɗawa a wajan, kafin yaja ƙafafuwansa ya nufi sashinsa, yana shiga kai tsaye bedroom ɗin sa ya shiga tare da murza key yama mance da batun wata Julde.

Kai tsaye Art room ɗinsa ya shiga ya ɗauki pencil da colours masu yawa, wani madaidaicin ɗaki ne, mai masifar kyau, wanda yake ɗauke da wasu ƙawatattun kujeru masu kyau wanda suka kasance na ƙarfe, sai wasu Flowers masu kyau wanda suke fidda wani dadɗan ƙamshi mai sanya nutsuwa da kasala a jiki.

Sai wata A.c mai bala'in bada sanyi a wajan, ka wani lallausan green ɗin carpet dake shimfiɗe a ƙaramin parlon dake cikin bedroom art ɗin, ga deep freezer dake gefe guda, sai ƙaramar plasma, ga wata ƙatuwar kwalba wanda aka cikata da kifaye masu kyau wanda kai tsaye ruwa yake saukar masu daga lambu.

Wani table ya jawo ya zuba pencil da colours ɗin a ciki, kafin a hankali ya nufi wata loker ya zaro wata farar carbon paper a ciki, yana ɗaukowa ya mannata a jikin wani ƙarfe da yake zanan jiki, kafin ya nufi deep freezer ɗin ya ɗauki fresh milk da lemon power horse energy masu sanyi ya ajjiye saman table ɗin, wata ƙaramar kujera ya ɗauko tare da zama kai ya ɗauki pencil ɗin bayan ya ɓalle murfin fresh milk ɗin ne ya ɗan kafa a bakinsa, saboda sanyin daya jine yasa ya lumshe idanunsa a hankali kuma ya manne hannunsa a saman paper ya fara zanan idanunsa a lumshe.

Wajan 20 minutes ya ɗauka yana zaman still kuma idanunsa suna rufe, sanssanyar ajjiyar zuciya ya sauke bayan ya furzar da iska daga cikin bakinsa, slowly ya buɗe idanunsa tare da saukewa akan art ɗin da yayi,
Da sauri yaja idanunsa ya Lumshe saboda zanan da yayi arba dashi, cije lips ɗinsa yay zuciyarsa cike da mamaki why kullum idan yayi zanan idanunta a rufe? Mene ya sanya kuma har yanzu ya kasa tantance photon Namiji ne ko kuma na mace? A kullum yayi zanan sai yaga kai babu gashi idanu a rufe, kirji kuma fal da brest kamar zasu tsaga ƙirjin su fito,
Ajjiyar zuciya ya sauke yana ƙara ware idanunsa akan laɓɓan wacce ya zana, kawo yanzu ya fara tunanin macace, duba da yadda laɓɓanta suke jajir gwanin sha'awa, amma irin laɓɓan tsiwa ne.

Lumshe idanunsa e a hankali ya ware laɓɓansa tare da cizon lips ɗinsa na ƙasa kamar zai kuka Murya a narke yace.

"Fitananniyyaaaa!!!"
Ya ƙare maganar yana jan harafin Yaaaa!!! Yana nan zaune har aka kira sallar Asar, gaba ɗaya baya jin daɗin fresh milk ɗin babu abinda yake son sha yanzu wanda ya huce Alcohol, Abar da aka sabar masa sa shanta tun yana Ƙarami.

A sanyaye ya miƙe ya koma bedroom ɗinsa yana zuwa ya samu sweet na shan madara kanta ya shafa yana faɗin "Sweet my love, my best friend"
Ya faɗa yana shigewa bathroom ya ɗaura alwala kai tsaye yabi ta ƙofar baya kasancewar yana sahun gaba yasa bai haɗu da ƴan uwansa ba, bayan an idar da sallah kuma zama yayi tare da lumshe idanunsa yana sauraran bugawar zuciyarsa.

Haka sallar magrib da Isshā duk haka yayi bai ƙara haɗuwa da kowa ba,
Ko Abinci bai tsaya ci ba ya shige cikin bedroom ɗinsa tare dayin wanka ya sanya wasu haɗaɗɗun nightwear Panjams masu santsi da taushi ya sanya bayan ya fesa parfume ne ya kwanta tare da jawo sweet ya rungome ya lulluɓe su da duvet mai laushi bayan ya ƙure gudun a.cn bedroom ɗin.

Washe gari
Tun 4:05 ya tashi saboda sautin kiran sallar farko na Subhi da yaji, jiki a sanyaye jike da kasala ya ware duvet ɗin jikinsa kai tsaye bathroom ya nufa,
Yayi wanka ya wanke bakinsa tare da ɗaura alwala,
Shirya kansa yayi cikin wata farar tattausan Male La Doublej Jallabiya mai gajeren Hannu, wata farar hula ya ɗauka wacce ake cewa tashi kafiya naci irinta larabawa, a saman sumar kansa ya sanya hular wacce ta rufe masa sumar kan sauran gashin kansa kuma suka sauka saman wuyansa, kai tsaye masjid ya nufa bai dawo ba sai wajan 7:00

Yana dawowa ya shirya kansa cikin ƙana nan kaya masu kyau, wandon ya tsaya masa iya laps ɗinsa kamar dai kayan spots wear, gorar ruwa ya ɗauka mai sanyi kai tsaye gym part ɗinsa ya nufa, yana zuwa ya fara motsa jikinsa domin idan yace zai zauna haka tabbas damuwa da kuma rashin mahaifinsa sai iya tarwatsa zuciyarsa, haka ya dinga motsa jiki har wajan 10:30 sai zufa ce take karyo masa.

Tura ƙofar side ɗinsa yayi a hankali bakinsa ɗauke da gorar ruwa yana shan yayinda gumi ke yanko masa, ganin Oumuu-Ayman ne yasa ya ɗan ware idanunsa tare da kwaɓe fuska a sanyaye ya ƙarasa saman kujera yana sauke numfashi.

Murmushi Oumuu-Ayman tayi kafin tace.
"Wlcm Zaki"
Jinjina kai Abu Maleek yayi kafin yace.
"Barka da safiya Oumuu na"
Kallonsa tayi sosai ajjiyar zuciya ta sauke ganin babu abinda Abu Maleek ya bari na dan gane da kamannin Murgayi King Tunde Muhammad Jalal.

"Zaki Ya mai jiki?"
Zare idanunsa yayi kafin ya langwaɓar da kansa gefe guda cikin gajiyawa yace.
"Ayyah! Baga irinta ba, wallahi Oumuu na manta da ita tun shekaran jiya"

Murmushi kawai Oumuu-Ayman tayi kafin tace "Ni ina sane da ita, domin duk bayan wasu awanni sai nazu na gyara mata Jikinta na shafa mata mai a kanta, Allahamdulillah naga gashi ya lulluɓe kan nata, gwanin sha'awa wallahi"

Taɓe baki yayi ba tare da yace komai ba, gani yau bai tashi da ƴan son magana da ita bane yasa Oumuu bashi breakfast Pancakes and Syrup sai haɗin salad Wanda yaji da faffan ƙwai, da Tomato's With Onion kana masan Salad da caroot.
Yana gama ci ya shige bedroom ɗinsa, Miƙewa Oumuu tayi ta nufi bedroom ɗin da Julde ke ciki, tana kwance tana sauke numfashi goge mata Jikinta tayi ta bata madara tare da gyara mata sumar kanta daya feso da yawa Lokaci guda.
Kwaɓe fuska Julde tayi a hankali ta shiga motsa bakinta cikin Murya mai rauni tace.
"Ballowo!!"
Shiru Oumuu-Ayman tayi domin ta fahimci Julde Makauniya ce, amma sam bata Fahimci sunan "Ballowo" da take yawan faɗa.

After 7days
Bayan anyi sadakar bakwai ne aka fara shirin yin naɗi, gefen Abu Maleek kowa ya manta da batun Julde rabonsa da ita tun ranar daya bata jininsa tasha wajan kwana shida ko biyar kenan.
Yayinda kullume sai Oumuu ta gyarata kuma sosai Jikinta ya murje saboda zama waje guda, cima mai kyau ga kulawa, har lokacin kuma babu wanda yasan da zamanta a cikin Alaafi!.

4:40 dawowarsa kenan daga masjid yana sanye da wata Blue ɗin Armless mai kyau, wacce ta ɗan kamasa yayinda ya ɗan zuge gaban rigar bayan shigowar sa cikin side ɗin nasa,
Walking slowly yake shigowa cikin side ɗin nasa, yayinda yake tafe yana ɗan sauke ajjiyar zuciya saboda bugawar zuciyarsa take masa, wacce lokaci zuwa lokaci take masa,
Ya iso dab da bedroom ɗin da Julde ke ciki yaji Zuciyarsa ta harba da ƙarfin gaske da sauri ya runtse idanunsa tare da saurin faɗin.
"hasbunallah!"
Ya faɗa yana dafe ƙirjinsa, har ya ɗaga ƙafa sai huce kunnuwansa suka jiyo masa sautin Muryar ta, tare da buge bugen da take,
Golden eyes ɗinsa wanda suke fidda wani ruwa ruwa saboda tsabar farinsu,
Kamar zai tafi sai kuma ya nufi bedroom a ransa yana faɗin "O'ohhhh This Fulani girl..."
Hanunsa ya ɗura saman wajan passward ɗin yana rubutawa ƙofar ta buɗe, a hankali ya sanya ƙafarsa ciki yanayin kusantar ɗakin yanayin ƙaruwar bugun zcyarsa, can ya tsaya lokaci guda kuma yaja baya da sauri yana dafe ƙirjinsa saboda idanunsa da suka sauka akan......



Abu Maleek isn't free contact to subscribe 08119237616





*_41-42_*
Dugwayen ƙafafuwan ta, wanda suke farare tass har wani yellow suke saboda wani fari da tayi fatar ƙafafuwanta sunyi fresh, sunyi ɓulo ɓulo.

Ga wasu gargasa da sukai kwance a saman farar fatar jikin ƙafafuwan nata, sai ƙyalli suke saboda tsanani kulawar da Oumuu-Ayman take bawa Julde,
Sauyawa ta musamman tayi saboda zama waje guda, da kuma kulawar da Oumuu-Ayman take bata akai akai.

Ajjiyar zuciya ya sauke a hankali ya jingina bayansa da jikin door, yana ɗan sauke numfashin tare da jan Maraitattun idanunsa ya rufe su, a hankali yake fidda numfashi kuma yake shaƙa, almost 30seconds kafin cikin nutsuwa ya shiga ɗaga zara-zaran eyes lashes ɗinsa wanda suke kwance saman fatar idanunsa.

Kai tsaye kuma ya sauke idanunsa a saman fararan farcen yatsun ƙafafuwan ta, wanda akaiwa ado da wani red ɗin jan farce, hakan ya ƙara bayyanar da Zallar kyau da kuma tsarin kyawun yatsun nata.

Ƙuri yaywa yatsun ƙafar nata kamar mai Shirin neman wani abu, some seconds kuma ya shiga zame idanunsa yana ɗan taɓe bakinsa kamar wanda yaga kashi,
Teeths ɗinsa yasa ya datse jajayen laɓɓansa tare da fara tauna su, saboda wani irin harbawa da zucyarsa tayi masa da ƙarfi, al'amarin daya haddasa masa saurin runtse idanunsa yana furzar da iska daga cikin bakinsa.

A hankali kuma ya sanya tafin hannunsa da a kullum baya rabuwa da gumi ya manna a saitin wajan da yaji yafi harba masa a cikin ƙirjin nasa, kwaɓe fuska yay tare da langwaɓar da kansa gefe guda,
Cikin wata kasalalliyyar murya mai matuƙar sanyi ya ware laɓɓansa tare da faɗin.

"Uhm! Ya Hakkamu!!!"
Ya faɗa yana ɗan juya da sauri zai bar cikin bedroom, domin ji yake idan yaci gaba da tsaiwa Tabbas zuciyarsa zata iya fitowa saboda a zabar bugawar da take masa.

Kamar daga sama yaji sautin Amon muryarta wacce take fita a hankali, Muryar da Amonta kawai zai sanya ka fahimci rauni da kuma halin buƙatuwa da mai muryar take ciki tana faɗin.

"Ballowo!!"
Shine abinda ta faɗa yayinda sautine Amon muryarta wajan faɗin wo!!!!! Ya ƙare a raunace kamar mai shirin fashewa da kuka.

Julde kam tun kafin ya shigo taji, Zuciyarta tayi sanyi a hankali kuma ta shiga bada sautin dib! dib!! dib!!! Sakamakon kusanta zuciyarta data Abu Maleek, shiru tayi kamar mai nazari a hankali kuma ta tsaya da buge bugen da take, yanayin yadda Jikinta ke ɓari da kuma bugawar zcyarta daya tsananta yasa ta fahimci Kallonta yake.

Ajjiyar zuciya ta sauke, a hankali kuma kunanta yaji sautin mutsawar gangar jikinsa alamar fita zai wannan dalili ya sanya ta kwaɓe fuska a hankali wasu sila sila hawaye suka ganganro daga cikin idanunta zuwa gefen fuskarta, kafin cikin muryarta mai ɗauke da zallar shagwaɓa ta ambaci sunan nasa.

Wannan dalili ya sanya Abu Maleek tsayawa ba tare daya juyawa ba, shi kam shagwaɓe fuska yayi kamar zai kuka,
Jin shiru yasa Julde fara sakin shassheƙar kuka yayinda da Jikinta yaci gaba da bugawa, tana shirin yin magana taji Muryar sa wacce ta sanya tayi saurin yin shiru da bakinta sai Ajjiyar zuciya take saukewa amma still Jikinta bai bar rawa ba.

Walking slowly ya fara taka ƙafafuwan sa a saman lallausan carpet ɗin bedroom ɗin, hannunsa duk biyun zube cikin aljihun wandon sa, cak ya tsaya saman kanta, Jin numfashinta a kusa da ita ne yasa,
Ta ƙara marai-raice fuska ta shiga ƙoƙarin Miƙewa zaune,
Ganin abinda take ne yasa ya ɗaga ƙafarsa guda ɗaya, tare da ɗurawa a saman hannunta ya danne.

Ƴar ƙara ta saki tana turo bakinta gaba kafin tace.
"Bafiiii fa Ballowo"
Juya idanunsa yayi sosai a ransa yake faɗin "wato Yarinyar nan komai nawa take kwaikwayo Uhm, Witch!"
Ya faɗa a ransa yana ƙara danna ƙafarsa dake saman hannunta.

Oumuu-Ayman ce ta turo ƙofar a hankali tare da shigowa bakinta ɗauke da sallama, tun kafin ta shigo ta san cewa

Please Login or Register in order to submit comment