Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin sauri kuma ya nufi inda take yana zuwa yasa hannunsa yay cilli da sandar haɗe Jikinta tayi waje guda hawaye ya shiga sakko bata,
Kafin tayi wani motsi taji ya sanya hannunsa ya ɗauke ta cak tare da sanyata a tsakiyar bayansa kana ya goyata a faffaɗan bayan nasa....



Sai mun haɗu a book 2
Gobe akwai tattaunawa akan book 1 kowa yayi joining na comment section.

*Abu Maleek na kuɗi ne, biya 500 domin yin karatu cikin nutsuwa 08119237616*


*BY*
*SARAUTA*









*HADEEYATULLAH*

BONUS kuma kuji ɗan abinda ƴan PAID suka gani😆


*LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI🤷🏻‍♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822



*Page 33-34*

Sai da mu sha hira sosai sannan Abbas ya baiwa Haidar biscuit da chocolat da ya sawo mashi,haka kawai naji kamar nayi zamana a can tare da ɗan uwana.

Kallona Abbas yayi yace "ko ke ma a mayar da ke boarding ɗin ba ki san je ka ka dawo?"baki na turo na girgiza kaina,stop yayi gun mai gasa masara ya na mai fiddo waya ya kira Alhaji amman sam layin yaƙi shiga.

Kuɗi ya miƙa a zuba mashi masarar a leda,miƙo min ɗaya nayi da murna na karɓa na fara ci ina mamakin yadda aka yi su ke sayar da masara kamar wasu Hausawa.


Mu na shigowa gida na tsinkayi Raliya zaune kusan flowers ta na sunsunar su,baki na ɗan taɓe haka kawai naji matar ta fita raina sai ma haushinta da ni ke ji.


Fita nayi na kama hanyar da za ta sada ni da ƙofar shiga falo yayinda shi kuma Abbas ya zarce gun sanyin idaniyar shi,a Shagwaɓe ta faɗa jikin shi ta na shafar gemun shi "miss You dear"sai da yayi mata kiss a lips sannan "moi aussi tu me manques"masarar da ya sawo mata ya miƙa mata ta karɓa haɗi da komawa ta zauna.


Abbas na ƙoƙarin shiga falo appel d'urgence ya shigo mashi,a kiɗime ya nufi mota yayi mata key mai gadi ya buɗe mashi ko da ya hau titi gudu ya kawai ya ke shararawa.
Zuwan shi asibiti sai da ya girgiza,aiki suka fara yi mata sai dai abu ya cuttura doli ya fito ya kira number Noor ta Niger sai da ta kusa tsinkewa ya ɗaga bai bashi damar yin magana ya shiga ce mashi "urgence dan Allah in akwai jirgi mai zuwa ka dawo Innalillahi wa'inna iley raji'un Noor marâtre ce...."sai kuma ya kasa ƙarasawa saboda kuka a doli ya yanke kiran.



Ana shirin kiran sallah jirgin su Noor ya sauka ,direct asibitin ya wuce shi ma sai da ya girgiza yadda ya ga lokaci ɗaya yadda marâtre (uwar rainon su Abbas a gidan marayu)ta koma lokaci guda rabin fuskarta ya yashe yayinda ƙashin ƙafarta ya tsage zafin ciwon kuma ya so taɓa zuciyarta.


Cike da ƙwarewa Noor ya shiga yi mata aiki yayinda a doli aka canzawa fuskarta fasali,naman kanta kuma da ya fita a cinyar ta aka yanka aka yi ma dashe.




Ƙarfe biyun dare har da wasu mintinan sannan aka kammala yi mata aiki duka,cike da gajiya Noor ya shiga ɗakin da aka kwantar da Abbas tausayin abokin na shi ne ya ɗarsa ma shi doli ne ya girgiza domin marâtre tamkar uwa ta ke gare su tun tasowar su ba su san kowa ba sai ita.


Wanka yayi a nan cikin asibitin sannan ya samu tea ya sha,zugum yayi ya na tunanin Tirday irin borin da ta hau a kan zai tawo haka kawai yaji kukanta ya tsaya masa rai.


Ƙoƙarin hakiceta ya ke amman ina tayi katutu cikin zuciyar shi da kwanyar shi, da wannan tunanin barci ya ɗauke shi.
Washegari bayan ya dawo daga sallah asuba ya shiga ya duba Abbas ,jikin nashi kuwa yayi garas dama fargaba ce ta haifar mashi da ciwon.

Har ɗakin da aka kwantar da marâtre Noor ya kai shi,sharrr sai hawaye ganin yadda duk rabin jikinta ya ke naɗe da bandeji.
Ko da suka fito kallon shi Noor yayi yace "please kar ku bari Raliya ta san da haka saboda cikin jikinta"kai Abbas ɗin ya girgiza yace "in shaa Allah ba zan sanar da ita ba kuma zan gayawa abokanan ta kar su sanar da ita"


Wuraren tara na safe asibiti ta cika da marayu wai sun zo ganin marâtre ,haƙuri Abbas ya fara basu sannan ya kwantar masu da hankali,sauran marâtres ɗin ne kawai aka bari suka shiga su ma ta glass ne suka hangeta na'ura sai aiki ta ke a jikinta doli suka zubar da ƙwalla.


Abbas kuwa ya na zuwa gida ya tarar da Raliya na sharɓar barci a falo yayinda Hadeeyatullah ke kitchen ta na girki, murmurshi yayi lokacin da ya leƙa ya ga ta dafe ƙugu ta na kallon yadda wanke ke tsuuu cikin mai.

Jin kamar mutum a kaina yasa na waigo, murmurshi nayi tare da yi mashi alama da ya shigo ya gani.Ƙarasawa yayi wanken da cikin mai na nuna mashi wani ƙato nayi mashi alama da shi ne sai wani ɗan matashi na mashi alama da falo wato Raliya ce sai wasu ƴan ƙanana kusan biyar na taɓa cikina haɗi da nuna falo alamun yaran da Raliya za ta haifa ne.


Dariya yayi jin shirme na,sai yace min "to ke ki na ina?"shiru nayi can sai na maƙe kafaɗa na girgiza mashi kai dungure ni yayi da goshi yace "to ke yara dozin za ki haifa min"cike da Shagwaɓa na shiga bubuga ƙafafu shi kuma ya na dariyaya ta.


***Bayan wata biyu

Sosai jikin marâtre yayi sauƙi sai dai har yanzu ba'a cire bandejen ba,a lokacin kuma tuni Raliya ta sani dan dubiya mu ka tai.
Yunwa ni ke ji amman sam Abbas ya hana ni cin abinci kuma ban san dalili ba,baki kawai ni ke turowa shi kuma ya zuba min ido ya na kallo.
Mu na nan zaune Raliya ta fito ita ma cikin shirinta,mota mu ka nufa ga mamakina sai na ga Raliya ta shiga seat ɗin baya ni kuwa na shige gaba.
Ba mu zarce ko ina ba sai asibitin su,a cikin harabar asibitin na tsinkayi Dr Noor ya na saffa da marwa ya kasa zama ya kasa tsaye sai zagaye ya ke.

Tsayuwar motar mu ne ya sa shi yin tsaye cak ya ƙurawa Hadeeyatullah ido,wani irin tausayinta ya ke ji tun ɗaga ƙasan zuciyar shi.
Fuska Abbas ya tamke dan ya san dama za'a rina wai an saci zanen mahaukaciya,bai baiwa Noor damar tambaya ba gaisuwar da Raliya ta yiwa Noor ƙememe ya ƙi amsawa sai ni da ya kafe da ido.


Ciki mu ka shiga,gabana ne ya shiga bugawa da ƙarfi ganin Abbas ya fara cire min kaya yayinda Raliya ke gefe tayi zir haihuwar uwa ta ko pant babu a jikinta.


Ina ji ina gani Abbas ya cire min kaya,wani ƙyalle ya luluɓa min haka ma Raliya.
Wani ɗan matashin saurayi ya shigo ina kallo lokacin da ya yiwa Raliya allura da ƙashin baya,cikin kunne na Abbas ya raɗa min "ki kwantar da hankalin ki riga-kafi ne za'a yi maku yanzu zan maida ku gida kin ji ko?"kai na ɗaga dan har ga Allah maganar shi ta samu karɓuwa dan ba ƙaramin kwantawa hankalina yayi ba.

Ya na gama yi min allurar Abbas ya kwantar da ni sai a lokacin Noor ya shigo, dishidishi na fara gani ina jin lokacin da Noor ke cewa Raliya ta ɗaga hannunta ita kuma ta na cewa ta kasa ba ta iyawa to fah shikenan ban ƙara sanin abinda ke faruwa ba saboda barci mai kama da mutuwar da ya ɗauke ni.


Cikin ƙwarewa Noor ya fasa cikin Raliya daidai marar ta ya ciro baby ɗan wata uku da ƴan kwanaki tare da ɗaukar sa ya dasa shi cikin marar *HADEEYATULLAH*😭

Cikin mintinan da ba su wuce sha biyar ba aka gama komi tare da ɗinke cikin aka naɗe shi da bandeji,ɗankin hutu duk aka kai su.
Noor ya dubi Abbas yace "yanzu hakan da kukayi kun yi adalci ne?ta yaya yarinya ƙarama za ta iya ɗaukar cikin da ba nata ba?"shiru Abbas yayi bai ce komi ba Allah na gani wannan ce kawai hanyar da zai sa su ma su ga ɗan cikin su.

Ko kafin Sallah azahar Raliya ta farka dan allurar da aka yi mata ba ta mutuwar jiki ba ce duka, Hadeeyatullah kuwa sai washegari.
Yunƙurawa nayi in tashi sai dai mi?azaba naji ga cikina doli na koma na kwanta ina hawaye nurs ce ta fita sai ga ta sun dawo ita da Abbas ....



*_35-36_*
Wani mutumi daya kafa bakinsa a hannun Julde, bayan ya finciki naman hannunta ne kuma ya kafa bakinsa ya shiga zuƙar jinin dake zuba ta jikin wajan daya cire naman wajan.

Zuciyar A.m ce ta buga da ƙarfi tare da wani irin harbawar daya sanya shi sanya hannunsa ya dafe tsakiyar goshinsa, tashin hankali ƙarara ya bayyana a saman fuskarsa.

"Innalillahi wa'inna ilaihir Arjun!" Shine kawa abinda yake fita daga ƙasan zuciyarsa tare da fitowa ta cikin bakinsa, yayinda wata ƙyakƙyawan zufa ta shiga yanko masa, jijiyoyin kansa suka shiga Miƙewa.

A hankali ya dinga jaa da baya, sai sauke Ajjiyar zuciya ya kamar wanda yayi tsere, bai taɓa ganin mutanan da suke cin naman mutum ko susha jinin mutum ƙarara a zahiri ra'ayin aini ba, sai yau, wanne kalar abu ne haka? Mene Amfanin shan jinin mutum? Waye wannan ɗin? Sune abubuwan da yake ta tunani a ransa amma babu amsa.

Wata kalar zabura yayi saboda tunawa da mutanan Birnin Bera, ƙara mai da idanunsa yayi kan mutumin daya dage yana shan jinin Julde, ba wasu sutturar arziƙi ne a jikinsa ba, sai wani jan bante daya sanya ya rufe al'aurar jikinsa, yayinda jikinsa yake baƙiƙirin.

A hankali ya juya ya shiga duba wajan, ga mamakin sa sai yaga babu kowa na dangane da mutanan Birnin Bera sai wannan mutumin hakan ya tabbatar masa cewa ƙwace wa yayi daga cikin Birnin Bera ya fasu jikin gari!.

Julde dake fidda wani kalar numfashi bakinta ya shiga fidda wata kalar Kumfa, mai yauƙi ga kuma yadda Jikinta ke ɓari kamar wacce take jijjiga, azabar data keji a cikin jijiyoyin dake Jikinta wacce jini ke gudana a cikinsu ɓata Lokaci ne, zuwa yanzu kam gaba ɗaya tunaninta ya fara sauyawa yayinda hancinta ya fara ɗauko mata wani kalar ƙamshi wanda bata taɓa jin maka mancin sa ba.

A sannu a hankali kuma ƙamshin data keji ya fara juyewa yana dawowa ƙarnin jini, da sauri kuma ta zabura tana ɗan buɗe bakinta yayinda ta ware idanunta akan A.m dake tsaye dukkan jikinsa yana ɓari tamkar wanda ake buga masa gangi.

Kwaɓe fuska yayi tare da marai-raice wa, ya ɗan langwaɓar da kansa gefe guda, saboda wani Irin kallo da yaga Julde ta nayi masa, wanda a zahiri shike Ganin hakan amma sam bata ganin komai kawai Ubangiji ne ya nufe ta da kallon saitin da yake tsaye.

Shiru Julde tayi saboda wani irin baƙon yanayi daya fara shigarta, yayinda gaba ɗaya ta kasa fahimtar komai, sosai taji zuciyarta na buƙatar wani abu, yayinda hancinta ke jiyo mata ƙamshin wani abu, wanda yake gigita mata lissafi,
A hankali kuma jijiyoyin jikinta suka fara saki, yayinda dukkan wani kuzarinta ta neme sa ta rasa, wani kalar numfashi take fesar wa yayinda take jan numfashi kuma da ƙyar.

A gigice Mutumin kuma ya cire bakinsa daga hannun Julde, yana wani irin gurnani, gaba ɗaya bakinsa ɗigar da jini yake,
Yana layi kuma ya janye jikinsa zuwa baya tare da Miƙewa tsaye, juyawar kuma da zaiyi ne idanunsa ya sauka akan Abu Maleek dake tsaye ya sunkuyar da kansa zuwa ƙasa.
Hangame bakinsa Mutumin yayi wanda zai iya bashi sunan (Arnan daji).
Kai tsaye kuma yana tan gaɗi da wata iriyar tafiya mai kama data ƴan shaye-shaye,
Gaba ɗaya bashi da kuzari saboda ya sha jini yayi bankas.

A.m kowa tuni jikinsa ya fara rawa, jijiyoyin kansa sun fito sunyi raɗa raɗa, yayinda gargasar jikinsa ta shiga mimmiƙewa, yana jin kansa na wani irin harba masa tamkar zai tsage gida biyu.

A hankali mutumin yake nufar A.m yana tafe yana buɗe bakinsa, alamar a wannan karan jinin Abu Maleek yake nema, kai tsaye kuma yana zuwa ya fara ƙoƙarin kaiwa A.m cafka.

Karyar da wuya Abu Maleek yayi kafin ya ɗan buɗe bakinsa Murya can ƙasa bata fita sosai yace.
"O'ohhhh"
A dai-dai lokacin ne kuma Mutumin ya ƙara buɗe bakinsa tare da kusanto A.m kafin ya ida sauke bakinsa a damtsan A.m,
Tuni Abu Maleek yayi ƙasa tare da ɗaukan wani ƙaton Dutse ya miƙe a hanzarce kai tsaye kuma ya sauke dotsen akan Mutumin,
Nan take ya tsulale a wajan jini na zuba ta tsakiyar kansa,
A hankali shima Abu Maleek ya sulale a wajan, wanda tuni ya manta da shiga ɗaya duniyar tasa, hakan yasa gaba ɗaya yaga samaniya na juya masa,
Yana ganin taurari na sakkowa zuwa dab da idanunsa,
Idanunsa a shiga Lumshe yayinda fatar jikinsa ta ɗauki rawa sanadiyyar rawar da naman jikinsa yake,
Cikin rashin makama da kuma rashin sanin abinyi ya sanya tafin hannunsa dake fidda wani gumi ya manna a tsakiyar goshinsa, wanda ya kejin kamar zai rabe masa gida biyu, kunnuwansa kowa wani irin numfashi yake jiyowa wanda ya kasa tantance wanne kalar numfashi ne wannan ɗin.

Ƙara cure jikinsa waje guda yayi tare fesar da numfashi, ya shiga taune leɓansa, yana jin wata azaba na fincikar jijiyar kansa, kafin a hankali ya fara saki wani sound mai kama da gurnani, gaba ɗaya jikinsa ɓari yake, sanyi da kuma iskar wajan haɗi da haraɓar dake kwance a wajan bai hana,
Wata wahalalliyar zufa keto masa ba, sosai ya keji samun kansa a cikin a zaba muddin juyewar tunaninsa ya tashi.
Zuro sweet tayi da idanunta, yayinda ta rakuɓe waje guda.

1hour left
Ya shiga sauke wani Numfashin wahala yana ɗan jujjuya kansa, dake sara Masa, duk da cewa yaji ciwon yayi ƙasa, amma hakan bai yana yaji kansa yayi masa nauyi sosai ba.

Bakinsa ɗauke kuma da salati ya shiga buɗe narkakkun gajiyayyun idanunsa, wanda sukai masa nauyi, kafin a hankali ya yunƙura ya miƙe tsaye baki ɗaya,
Sweet dake gefe na ganin hakan ta fara tsalle tana kaɗa jela, a sanyaye fuska a narke ya kalli sweet suna haɗa idanu ya kwaɓe mata fuska, irin I'm tired ɗin nan, a hankali ya sunkuya zai ɗauki sweet domin suci gaba da tafiya domin Allah yana kallo ya mance da batun Julde, baya Sweet tayi tare da juyawa ta kalli Inda Julde ke yashe, slowly ya juya idanunsa zuwa ga direction ɗin da Sweet take kallo.

Idanunsa ne suka sauka akan Julde wacce take kwace, farar fuskarta ya tsorawa idanu ganin yadda ta ƙara wani mugun haske, tai fari fatt da ita,
Langwaɓar da kansa gefe guda yayi yana ya mutsa fuska tare da marai-raice wa baki ɗaya kafin ya juya ya kalli sweet yace.

"Kin gani ko? I can't Sweet ni bazan iya ba gaskiya aita wahalar da mutum, ko uban me take a kwance kuma ohhhhoo??"

Ya ƙare maganar yana ƙara mirgina kansa gefe guda, tare da ƙoƙarin juyawa, cak kuma ya tsaya, saboda kansa da yaji ya sara take kuma ya fara tuna abinda ya faru, cikin sauri ya juya kanta tare da cilla idanunsa akan Julde wacce take fidda numfashin wahala,
"Yasubuhanallah!"
Shine abinda ya zo bakinsa, Shikenan ta harbu yaya zai yi kenan? Anya bazai barta a nan ba, tunda daman neman kai yake da ita?
Wata zuciyar kuma tace.

"A'a Jalaluldeen, wannan dukkan haƙƙin ta yana wuyanka, kula da lafiyarta, cinta, shanta, sutturar ta, Wheel ba ita tace tana sonka ba,
Sanda za'ai auran itama bata sani ba a yanzu dukkan abinda ya sameta you're the reason behind, dan haka ya zama dole ka kula da ita, domin ita ɗin KYAUTAR ALLAH ce, KYAUTA CE DAGA ALLAH kare ranta kuma na nufin kare rayuka da dama wanda suke gab da salwanta"

Zuciyar ta ƙare maganar tana harba masa, tare da ƙara bashi umarnin zuwa ya taimake ta.

Kwaɓe fuska yay yana jan tsaki kafin ya kalli sweet yace.
"Sweet naje? I'm scared kada ta cijan na zama maye"
Karkaɗa jela sweet tayi, kafin tayi gaba zuwa wajan Julde taɓe baki Abu Maleek yayi yace.
"Uhm! Allah za muyi faɗa sweet, i don't know why kike son Fulani girl ɗin nan"
Ya ƙare maganar yana riƙe ququnsa da dukkan hannayensa, kafin kuma walking slowly ya marawa sweet ɗin baya, yana zuwa ya durƙosa dai-dai kanta ya kallo ƙyakkyawar fuskarta mai kyau wacce ta kasance zagayayyiya (Oval shape).

Wani irin fisgar numfashi Julde taja lokacin taji ƙamshin mutum kusa da ita, a hankali kuma Jikinta ya fara rawa ta shiga ƙoƙarin tashi zaune tana buɗe baki,
Zare ido A.m yayi a ransa yake faɗin "Mayya!!" Zanyi maganinki yasin,ji yadda take buɗe mitsitsin baki ko small yatsana bai shiga"
Ya ƙare maganar yana sanya duguwar yatsarsa ya dungure mata kai.

Julde bata san mene yake ba, burinta kawai ta samu abinda hancinta yake jiyo masa ƙamshin sa,gane abinda take so ne yasa ya ɗan saki Murmushi ƙiri-ƙiri an mayar da ita mayyar ƙarfi da yaji.

Idanunsa ya juya kaɗan cikin Sa'a idanunsa ya sauka akan wani yadi, kafin yayi magana sweet ta ɗauko yadin da bakinta ta kawo masa, kanta ya shafa cikin ƙaunar magen tasa yace.
"Love You!"
Zama yayi sosai yana mai ya tsuna fuska shi gaba ɗaya tsantsamin Julde yake,
bisa dole ya tattausan hannunsa ya ɗan jawota gefensa tare da ɗura kanta a cinya,
idanunsa kuma ya mayar wajan ciwon ganin yadda yake zubar da jini,
wani irin zabura Julde tayi tayo kan Abu Maleek duk da bata gani,
unexpected abun ya zuwa A.m hakan yasa yayi baya tare da faɗuwa Julde kuma tabi jikinsa ta kwanta tana buɗe baki tare da neman inda zata ciza,
ganin hakan yasa Abu Maleek neman yadda zai ƙwaci kansa dan muddin ya bari ta cijesa ya gama aiki,
hannunsa ya buɗe baki kasancewar mai faffaɗan ƙirji yasa gaba ɗaya ta rufta cikin ƙirjin nata,
da sauri kuma ya sanya hannayensa yayi mata rumfa dasu,
Kokawa suka fara inda take ƙoƙarin ganin ta kama hannunsa yayinda yake sun ganin ya riƙe fuskarta baki ɗaya, shi Abin dry ya basa,
Ganin kuma tana ɓata masa Lokaci ne yasa ya ɗan haɗe fuska sosai tare dasa hannunsa a saman karan hancinta ya ja,
Wata ƙara ta saki saboda zafin da taji sai kuma ta kwaɓe fuska ba tare kuma da tace komai ba kamar wacce aka bawa umarnin tayi ƙasa da kanta zuwa ƙirjinsa, tare da sauke ajjiyar zuciya,
Tana mai ƙara mannewa a jikin nasa ba tare kuma data kai masa cizon ba.
Lumshe idanunsa yayi sosai yana jin yadda take saukar masa da gajiya, kafin kuma
Ya ɗauki yadin ya shiga naɗe mata baki dashi, yana gamawa ya sauke numfashi tare faɗin.
"Ya Allahu Ya Rahamu"
Kana ya miƙe tsaye da ita a jikinsa tare da ɗan taɓe baki yana faɗin.

"Kawai aita wahalar dani, yarinya wallahi sai na rama, ƙwaffff"
Ya faɗa yana jan ƙwafa, kana ya cilla ta bayansa ya ɗauki sweet a hannunsa,
Ko takan nono da ruwan bai bi ba, ya kama hanya tare da suma tafiya, yayinda kuma Julde tai lubb a bayansa tana sauke ajjiyar zuciya da ƙarfi.

Yau ta kasance ranar juma'a, ranar da dukkan wanda yake Kanzaf bazai taɓa mancewa da ita ba, ranar data shiga tarin daga cikin ranakun tarihi, ranar da mutanan Kanzaf da mutanan da suke cikin Alaafi suka shiga cikin tashin hankali, tashin hankali mara fasaltuwa, ranar da Kanzaf ta zama kamar wani sansani na maƙabarta saboda Shiru da garin yayi baka jin motsin komai, Hatta tsuntsayen da suke shawagi kullum daga Cikin bishiyoyin Alaafin zuwa bishiyoyin Kanzaf yau babu su,
Sai wata dadɗar iska mai daɗi da kuma ratsa zuciya dake tashi, cikin ƙaramin lokaci kuma garin yayi duhu saboda tasuwar hadari daya haɗa da wata gagarumar iska mai ƙarfi.

Oumuu-Ayman ce tafe ita da Salimerh sun sanya Mai Babban ɗaki a tsakiya wacce Idanunta yayi jajurr, ga wani irin rawa da Jikinta yake, a haka suka nufi sashin King Tunde suna zuwa suka samu Queen Ayoola a kusa dashi riƙe da hannunsa sai kuka take, gefe guda kuma Otun da Agba Akin ne zaune suna masara addu'a tare dayi masa fifirta,
Daga can gefe guda sautin kukan Bola ne tashi a hankali, Zama Mai Babban ɗaki tayi tare da kallon ɗan nata, a hankali ta sanya dai-dai kunansa ta shiga karanta masa addu'a, ta nayi tana kalmar shadda,
Jin yadda Mai Babban ɗaki take nanata Kalmar Shahada ne ya sanya Salimerh gigice wa, tare da sanya kuka tana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir Arjun, Dad!! Dad!!"
Ganin yadda Salimerh ta gigice take neman ruɗa MALEEK dake kusa da King Tunde Muhammad Jalal daya riƙe hannunsa sosai yana jin tamkar Zakinsa ne kusa dashi,
Ya sanya Oumuu-Ayman ta riƙe Salimerh tare da rungome ta sosai, tana faɗin.
"Just pray for him, ita yake buƙata Salimerh"
Kuka Salimerh tasa tana rungome Oumuu-Ayman tare da faɗin.
"Oumuu!! Oumuu Dad!! I'm going to lose my Dad Oumuu, Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
Sosai Oumuu-Ayman ta rungome Salimerh a jikinta, ganin tana neman ficewa daga cikin hayyacinta.
"In sha Allah, noting will happen to him sai abinda Ubangiji ya tsara Salimerh, just pray kiyi masa addu'a"
Ta ƙare maganar tana juyar da idanunta saboda hawayen daya cika mata idanu,
Da sauri Salimerh ta miƙe tana faɗin "Oumuu Zaki?? Shakiru, Sharefddeen, babu kowa Oumuu yaya za mu yi?"
Sai kuma ta juya da sauri ko ganin gabanta ba tayi yana fita, taci karo da Junaid tana ganin ta nufi inda yake, runtse idanunsa yayi saboda wani mugun mugun! Tausayinta da yaji, tana zuwa ta faɗa jikinsa tare da riƙesa sosai tana faɗin.
"Junaid, My Dad! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un zan rasa farin ciki na Junaid yaya zanyi? Yaya Zaki zaiji idan ya dawo ya samu babu Dad? Wayyoooo Allah, Ubangiji ya dube mu, ka kawo mana sauƙi akan abinda yake shirin samu mun ba, Ubangiji ka dubi idanun mu ka tausaya mana ka barmu da mahaifin mu, shine jin daɗin mu, shine farin cikin mu, shine garkuwan mutanan Kanzaf, La'ilahaillahu Muhammadur Rasulullah S.A.W"
Ta ƙare maganar tana sakin kuka sosai, tare da riƙe Junaid, idanun Junaid yayi jaa sosai, a hankali ya sa hannunsa ya rungome ta a jikinsa yana so da ƙaunar ta na ƙara nunkuwa a zucyarsa, ga kuma wani tausayinta daya gama mamaye zucyarsa, a hankali ya shiga bubbuga bayanta tare da faɗin.
"It's okay My princess, In sha Allah Dad zai miƙe zaici gaba da zama damu, Kiyi masa addu'a please wifyna"
Ya ƙare maganar yana ɗan bubbuga bayanta, kafin ya janye ta daga Jikinsa, yana kama hannunta tsayawa tayi tana girgiza masa kai alamar ba zata shiga ciki ba.

Girgiza kai kawai yayi kana ya shiga ciki, yana barin wajan Salimerh ta nufi Part ɗin ta, tana zuwa ta samu wayarta na ringing da sauri tai answering daga cikin wayar akace.
"We are on our way Ranki ya daɗe?"
Wasu zafafan hawaye ne suka sakkowa Salimerh kafin tace.
"Ina Zaki na?"
Daga cikin wayar akace "we're all together Maaahh!"
Jinjina kai tayi cikin tsananin farin ciki da kuma jin daɗin Dawowar JULALUDEEN TUNDE MUHAMMAD JALAL, kafin tace.
"Ka shigo ta ƙofar baya"
Daga cikin wayar aka amsa mata da "In sha Allah" kashe wayar tayi a sanyaye kuma tace "Allahamdulillah"

Oumuu-Ayman ce tsaye da Salimerh suna nan tsaye kuma suka hango motar na shigowa ta can ƙofar baya, wata Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Oumuu-Ayman ta sauke, yayinda wata nutsuwa ta sauka a zcyarta, tun bayan tafiyarsa bata da wata nutsuwa kullum cikin damuwa take,
A hankali motar take tafiya harta iso inda suke Oumuu-Ayman suke, a hankali kuma Oumuu-Ayman ta nufi back seat tare da sanya hannunta ta buɗe motar, Idanunsa dake lumshe ya ware a hankali tare da sauke su akan Oumuu, tashin hankali daya a cikin ƙwayar idanun ta ya sanya ya tsorawa mata narkakkun idanunsa,
Zame idanun ta tayi daga cikin idanunsa saboda kallon da taga yana bata, a hankali kuma idanun ta ya sauka akan Julde wacce take kwance bakinta a ɗaure tana bacci juyawa tayi ta kalli Salimerh tace.
"Shiga ciki ina zuwa"
Tayi hakan ne kuma saboda bata son Kowa yaga Julde, hannunta ta miƙa wa Jalaluddeen alamar ya kama,
Ƙara ware idanunsa yayi a kanta kamar bazai magana ba dai kuma yace.
"Dad????"
Ya tambaya kai tsaye domin

Please Login or Register in order to submit comment