Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaifi"
Miƙewa yayi yace "nasu yin hakan, amma tafiyar ta zama dole but ba daɗewa zanyi ba"
Jinjina kai tayi tace "Allah ya bada Sa'a"
Queen Ayoola ma Miƙewa tayi tace "za muyi missed babu kai babu Shakiru balle Sharefddeen, ga kuma tashin hankalin da muke ciki na rashin lafiyar King"
Kallonta kawai yayi ba tare da yace komai ba, tafiya yayi kai tsaye zuwa sashin King Tunde Muhammad Jalal domin dubasa, Salimerh ma makaranta ta nufa.
A daran jirgin Adams ya ɗaga zuwa Cairo.

Washe gari Otun ya samu Agba Akin da maganar Auran Junaid da Salimerh, suna cikin maganar ne kuma saƙo ya riskesu jikin King Tunde Muhammad Jalal ya tashi,
A ranar babu wanda ya runtsa dan yin Bacci fargaba da cika zuciyar kowa,
Banda sunan JALALULDEEN TUNDE MUHAMMAD JALAL babu sunan wanda yake kira sai sunan Little wanda ba'a san ko sunan waye ba, kawai sun ɗauka zafin ciwo ne, a haka gari ya waye masu suna tare da shi sai kumfa yake fitarwa ta cikin bakinsa, ga wani irin zafi da jikinsa ya ɗauka jikin yayi jajurr dashi.

Kimanin kwana uku kenan da zuwan Abu Maleek Rugar Mahinjo, rabonsa da Julde tun ranar da suka shigo garin gaba ɗaya, ya manta da babin rayuwarta, shirin komawa ƙasar sa yake,
Domin kwana biyun nan hankalinsa sam yaƙi kwanciya,
Yanzu ma fitowar sa kenan daga cikin Bukkar da yake kwana, a hankali yaja idanunsa ya rufe yana shaƙar iskar dake Kaɗawa,
Cikin Rugar yayi tsitt duk sun tafi kiwo,
Walking slowly hannayenta a saman ququnsa yake tafiya yana ɗan sauke ajjiyar zuciya,
A haka ya isa can gefen wata bishiryar mango wanda sukai manya sunyi jawurr dasu,
Daga can gefe kowa Labbo ne tsaye a gaban Arɗo yana faɗin "Da gaske ina sonta kuma na shirya auranta" ƙirjin Arɗo ne ya buga da ƙarfi, yana shirin yin magana kenan sai Barkido yace.
"Nima ina son Julde kuma auranta na ke sonyi"
Da wani irin sauri Arɗo ya kalli ɗan nasa yana zufa na yanko masa, Lamiɗo ne yayi murmushi yace.
"Kenan Shaɗi ya wajaba a cikin wannan Rugar ta Mahinjo, ga Labbo ga Barkido mazaje a motsa"
Arɗo kasa magana yayi sosai tashin hankali ya wanzu a saman fuskarsa, Tayaya Barkido zai ce zai auri Julde bayan yasan burinsu? Kuma yana da tabbacin Barkido zai iya shanye dukkan bulalar da Za'ai masa.

Hannunsa ya miƙa ya ciri Mango tare da cillawa sweet ɗinsa, tsalle tayi tare da buɗe baki Mangon ya faɗa bakinta,
Lumshe idanunsa yay a hankali kuma ya ware bakinsa yace "O'ohhhh" yayi hakan ne saboda zuciyarsa da yaji ta tsananta bugu kwanan nan, musamman yanzu da yaji ta wani harba masa, mango ya cira manya guda biyu kana ya ɗauki Sweet domin komawa cikin bukka, a hankali yake tafiya cike da tarin nutsuwa kamar ance ya kalli gefensa da sauri ya runtse idanunsa kafin ya buɗe idanunsa a hankali, tana zaune hannunta riƙe da sanda ta tura ƙaramar yatsarta a cikin baki tana tsotsa,
Taɓe baki yayi ganin ta ɗan sauya kaya kanne dai yana nan kamar na namiji, gajeren tsaki yaja cikin ransa yace.
"Empty head"
Har ya tafi sai kuma ya tsaya a fili yace "Allah sai na rama tsoran da kika ban, ina sane ai"
Sweet ɗinsa ya cilla mata da ƙarfi kuma yace....



*ABU MALEEK NA KUƊI NE, BOOK 1 2 3 SHINE 500 VIA 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616*



*BY*
*SARAUTAR MARUBUTA*





*_Nimcyluv 27-28_*



"Ga maciji nan"
ya faɗa cikin ɗan ɗaga Murya yadda za taji abinda yace, kai tsaye kuma magen ta sauka saman kanta,jelar magen tayi kwance a wuyanta,
Wani kalar numfashi Julde taja saboda laushi da kuma sanyin jikin magen daya ratsa fatar Jikinta,
Tsoran da yayiwa Julde yawa ne ya sanya ta fita cikin hayyacinta tun daga wannan Numfashin data ja bata sake motsawa ba, balle taja wani Numfashin,
Sosai take da jin tsoro abu kaɗan ke firgitar da ita, sweet da itama ta firgita, da sauri ta sauka a jikin Julde ta buɗe baki tare dayin ƙara kana ta nufi wajan Abu Maleek da gudu, tana zuwa ya durƙosa ya ɗauke ta tare da rungome ta, yana shafa bayanta a hankali, kana cikin ransa yace.
"Bana faɗa maki ba? Gashi nan tsoro ya hanaki magana"
Ya faɗa yana shigewa cikin bukkar gaba ɗaya bai lura da halin suman da Julde ta shiga ba.
Barkido dake can tsaye yayi saurin ƙarasawa inda dake tare da durƙosawa, inda take ganin bata numfashi ya sanya ya ɗan firgita, da sauri kuma ya miƙe babu jimawa ya dawo ɗauke da ruwa a hannunsa,
Yayyafa mata ruwa yayi, cikin Sa'a kuma ta sauke ajjiyar zuciya tare da sanya kuka ta ƙoƙarin Miƙewa tsaye Jikinta sai rawa yake.
"Julde, nine Barkidon ki"
Ya faɗa yana yana ƙoƙarin riƙe hannunta, zamewa tayi ba tare data bashi damar riƙe hannun nata ba, cikin shagwaɓa fuska tace.
"Shine ya tsorata ni yayi tafiyarsa ko?"
Barkido da bai fahimci maganar taba yace.
"Waye kuma? Me yayi maki?"
Ya tambaye ta, yana mai ɗan juya sai dai baiga kowa ba, turo baki tayi tana sakin ajjiyar zuciya kafin a hankali cikin Muryar rauni tace.
"Wannan baƙon mutumin, Allah bashi da kirki gashi da miskilanci"
Cike da tausayawa Barkido yake kallonta ganin duk ta tsorata har bata iya ɓoye tsoran dake zuciyarta, gashi nan ya fito ya bayyana sosai a saman fuskarta,
Ƙasa yayi da murya yace "Ayyah kiyi haƙuri kinji? Ƙilan bai sani ba"
kwaɓe fuska tayi tace "Allah nima sai na rama, nasan ramawa yayi"
Jimm Barkido yayi zuciyar nayi masa zafi sosai, kafin ya haɗiye abinda ya keji yace.
"Kin san shi ne? Me kikai masa da har zai rama yanzu?"
Ya tambaye domin zuciyarsa bata aminta da maganar ta ba,
Hannayenta ta watsa masa irin ohuu ɗin nan sai kuma tace.
"Ihu nayi masa akai fa, kuma ai tsolo ruwa inaji"
Jinjina kai yayi alamar gamsuwa, kafin ya gyara zamansa sosai yace.
"Julde ina son muyi magana, nasan ba lallai ki fahimta ba, amma dole zan faɗa maki, kafin nan ina ƙara baki hqr akan abinda nai maki, nasan Ubangiji ne ya rama maki, ta hanyar sanya mini soyayyyar ki mai tsanani a Zuciyata, wallahi Aradon Allah ina sonki kuma Auranki na kayi"
Maganar taji kamar ba zata, tasan cewa bata ilimin soyayyya bata san yaya take ba, dan haka bata kawo wannan tsarin rayuwarta, ita idan aka barta da ranta da lafiyarta da kuma abinda lafiyarta zata samu, ya wadatar da ita, sai kuma ilimi bata ƙaunar zamanta a cikin jahilci,tana buƙatar samun ƴanci kamar kowa, duk ta san abune mai wahala ta samu wannan saboda lalurar rashin ganinta.
Ganin tayi shiru ne kuma ya sanya Barkido yaji zuciyarsa ta buga baya fatan yayiwa Julde dole akan ta susa, yasan Tabbas zai sameta saboda shi ɗin jarumi ne zai iya jure dukkan wata bulala da Za'ai masa a wajan shaɗi.
"Kina jin tsoro na ko? Saboda abinda muka aikata a gareki? Ban san komai ba Julde duk abinda nayi sanyani akai, ban kuma san dalilin daya sanya Arɗo yace nayi hakan ba, kiyi hqr ina ƙara baki hqr amma ina sonki da gaske, zan baki farin ciki bazan taɓa bari wani ya cutar dake ba"
Shiru tayi tana nazarin kalaman sa saboda Allah ya bata ƙwaƙwalwa duk da cewa bata gani amma tana iya fahimtar kalaman mutum har ta fahimci inda zan can ya dusa,
Ajjiyar zuciya ta sauke kafin tace "zaka sani makaranta? Ina sonyi karatu sosai domin na samu hanya mafi sauƙi wajan kare rayukan jama'a da kuma gano inda mugwayen mutane suke"
Abu Maleek dake can bayansu yana ɗan shan mango a hankali yana jin gaba ɗaya zaman garin ya ishesa, ya ɗan taɓe bakinsa saboda yana jin abinda suke faɗa kasancewar yana da saurin ji kamar maciji, cikin ransa yace.
"Daman kalar zaran dole sai kalar yadin, kayan Shirme sai shirmammu"
Ya faɗa yana jan tsaki tare da juya zuwa cikin bukkar,
Barkido ƙara kallon Julde yayi sosai kafin yace.
"Karatu kikeso?"
Da sauri ta ɗaga masa kanta tana zare yatsarta daga cikin baki, Murmushi yayi yace.
"Na maki al'ƙawarin indai kika aure ni ko mene kikeso zan maki, wannan al'ƙawarin na ɗauka"
Washe ƙana nan jerarrun dafaffun haƙuronta tayi cikin sanyin murya da kuma ɗan farin cikin daya shigeta tace.
"To Shikenan"
"Kin Aminci zaki auran?"
Ya faɗa yana mai kallon saman ƙirjinta tare da sauke ajjiyar zuciya, kafin tayi magana yaji daga bayansa ance.
"Jarumtar ka itace zata tabbatar cewa ka dace da auranta ko kuma a'a, ka daina saye zuciyarta domin zaka cutar da ita, saboda ba kai ka ɗai kake sonta ba ka mari ƙarfinka ya baka ita"

Labbo ya faɗa yana dire sandar hannunsa, Miƙewa Barkido yayi kafin ya fuskanci Labbo yace.
"Idan batu kake na Jarumtar ka ɗauka Julde ta zama tawa, idan kana magana ƙarfi ne kasan cewa wajan ka tarar, idan maganar saye zuciya kake wannan saƙo ne daga zuciyar da take so zuwa zuciyar da akeso ina fatan ka fahimta?"

"Aradon Allah ƙarya kake, Julde Matana ce nine zan aureta, idan baka shirya ba ka shirya shaɗi Arado jikinka zai faɗa maka"
Juyawa yayi ya kalli Julde saboda yaga yaya yanayin ta yake, tana nan zaune ta cure waje guda sai faman juya idanu take da dukkan alamu fata fahimci inda zan can yake ba,
Ɗauke idanunsa yay kafin ya juya ya kalli Labbo yace.
"Na daɗe da shiryawa, ina maka fatan samun nasara"
Yana faɗin hakan ya juya zuwa cikin wata bukka, bin bayansa Labbo yayi da kallo, kafin ya maida idanunsa zuwa ga Julde dake zaune tana aikin tsotsar yatsarta,
Kamar zai mata magana sai kuma kawai ya juya tare da nufar bukkar Mahaifiyar sa.

Abu Maleek na shiga cikin bukkar kowa zamewa yayi tare da cire rigar jikinsa, Lumshe idanunsa yayi yana daɓe baki kafin ya ware laɓɓanta cikin gajiyawa yace.
"Kaya duk wari, Uhmmm"
Ya faɗa yana cilli da rigar tare da sanya hannunsa ya saman ƙirjinsa ya shiga shafa ƙwantaccen gashin ƙirjinsa, tunani ne fal zuciyarsa a yanzu kuma tunanin Mami Shine yafi damun zuciyarsa, ina take? Wane ya ɗauke ta? Mene ya sanya Adams cewa shi ne ya ɗauke mahaifiyar su? Mene ya sanya yake zarginsa? Wannan tambayoyin sune suka tare a cikin zuciyar Abu Maleek, amma sam bashi da amsar su, gaba ɗaya yaushe ya dawo garin ma? Tafin hannunsa ya sanya a saman goshinsa ya shiga ɗan murza goshinsa a hankali yana sauke numfashi, taune leɓansa yayi yana zuciyarsa na tsananta bugu, a hankali ya sauke wata wahalalliyar ajjiyar zuciya tare da sanya hannunsa a dai-dai tsakiyar ƙirjinsa ya ɗan matse wajan,
Idanunsa ne ya sauka a saman zanan dake ƙirjinsa har zuwa ƙasan cibiyar sa, lumshe idanunsa yay a hankali ya furta.
"Where are you Mami? Ina nothing without you, ya rabbi! Come to our family Mami"
Ya ƙare zan can yana ɗan runtse idanunsa da wannan tunanin kuma bacci ya ɗauke sa.

A can wajan ruga kowa tuni Arɗo ya sanya aka buga tambura na sanarwar, kafin kace me dukkan jama'ar dake cikin Rugar maza da mata yara da manya sun halarci kiran Arɗo,
Bayan kowa yazo ne Arɗo ya gyara zamansa tare da fuskarta jama'ar Rugar yace.
"Kamar yadda muka sani a al'adance idan mane ma sukaiwa yarinya yawa, akwai wata hanya domin kawo mafita da kuma samun sauƙi wajan ware mutum guda wanda ya amsa sunan Jarumi da zai zama miji ga wannan Yarinyar haka ne?"
Gaba ɗaya suka amsa da
"Eh"
Gyara zama yayi yace "akan maganar Julde ne, Yaro Labbo yaga Julde yana so, ga wannan yaro nawa Barkido yaga Julde yana so, kowa kuma ya cancanci a bashi a auranta, bisa wannan dalilin ya sanya za muyi abinda muka saba a al'adance, ma'ana zamu gabatar da SHAƊI tsakanin ma nema biyun, wanda ya samu nasara shikenan ya zamu auran wannan yarinya"
Gaba ɗaya sukai na'am da zan can Arɗo kafin ɗaya daga cikinsu yace
"Yau she ne za'a gabatar da SHAƊIN?"
Arɗo na Miƙewa tsaye yace.
"Babu jira ai, dukkan mane man su shirya gobe za'a gabatar da komai"
Wani Murmushin jin daɗi Barkido yayi yana mai Miƙewa tsaye tare da shigewa bukkar Adda Manga (Senior sister) domin ta fara shigarsa daman ya daɗe da shiri saboda zuwan irin wannan ranar, shima Labbo wajan iyayensa suka nufa nan kowa ya fara shiri,
Abu Maleek kam dake bacci mai san meke faruwa ba, yana jiyo hayaniya sama² dai amma baya fahimtar komai,
A wannan ranar babu wanda ya kwanta bacci gaba aka fara shirin shaɗi sai tsuma samari biyun ake wanda suka kasance ma nema aure ga Julde wacce itama bata san abinda ke faruwa ba, ta bukka tana bacci yatsarta sanye cikin bakinta.

A can Alaafi kowa yammaci ne mai ɗauke da wata sassanyar iskar dake Kaɗawa, alamu ne dake nuna cewa yanayin damuna zai fara, duba da yanayin yadda samaniya ta cika da gajimare mai duhu da kuma jaa, gaba ɗaya weather ta sauya sai iska ake garin yayi kyau sosai ga wasu kukan tsuntsaye dake tashi a hankali.

Junaid ke tafiya cikin kuzari da kuma izza, yana sanye da black ɗin shadda mai kyau,
Sosai fuskarsa ta faɗaɗa da Murmushi tunda yaji saƙon cewa an bashi auran Salimerh duk sanda ya shirya ya fito, dalilin fitowar sa ma tun jiya yake kiran Number bata answering shiyasa ya yanke shawarar zuwa ya sameta.
Yan tafe bayi da barori na gaishesa, a haka ya isa cikin sashin Queen Ayoola tana zaune saman wata lallausar kujera mai kyau, ga hadinkai sai fifita suke mata duk da uban sanyin dake tashi a parlon nata,
Ga wasu kuma na matsa mata ƙafafuwansa ta, wasu kuma ma jera mata kayan motsa baki,
A bakin ƙofar parlon ya tsaya tare da neman iso, wajan Queen Ayoola,
Ba jima aka bashi damar shiga, bakinsa ɗauke da sallama ya shiga,ganin mai shigowar ne ya sanya Queen Ayoola yin wani ƙawataccen Murmushi tare da bawa Junaid umarnin shiga, bayan sun gaisa ne Junaid yace.
"Mai Kanzaf da Alaafi baki ɗaya Salimerh fa?"
Cikin jin daɗi maganar ta Junaid tace.
"Tana sashin Bola, kaje mana"
Miƙewa yayi yana faɗin "godiya nake, na barki lafiya Jagorar Alaafi"
Da Murmushi tabi bayansa da kallo, kai tsaye kuma shashin Bola ya nufa, bayan anyi masa iso ne ya shiga,
Suna zaune a parlo suna cin abinci idar da sallar su kenan ya shiga,
MALEEK dake zaune saman sofa yayi saurin tashi yana sakin kuka tare da nufar inda Bola take zaune,
Murmushi yayi yace.
"Maleek ka girma till now bak daina gudun mutane ba?"
Bola da ajjiye spoon ɗin hannunta tare da Miƙewa bayan tasha ruwa tace.
"Ai na rasa irin Maleek, bashi da yarda gaba ɗaya"
Ta ƙare maganar ta kama hannunsa tare da nufar side ɗin ta,
Salimerh abinci ta keci a hankali ganin bata da niyyar yi masa magana yasa shi miƙewa tare da jan kujera ya zauna yana mai kallon fuskarta yace.
"Congratulations Madam!"
Juya idanunta tayi tace
"For???"
Murmushi yayi tare da fara cin abincin plate ɗinta yace "uhm soon zamu zama miji da mata"
Daga yaci gaba da janta da Shira.
Washe gari bayan tayi shirin tafiya Makaranta ta nufi Sashin King Tunde Muhammad Jalal, tana zuwa ta samu Oumuu-Ayman zaune a gefe tana masa sannu, zama tayi cikin damuwa tace.
"Yaya jikin nasa yanzu Oumuu-Ayman?"
"Jiki Allahamdulillah Salimerh"
Ta faɗa a hankali gudun kada hayaniya ta damesa, Shiru tayi tana kallon Mahaifin nata, kafin tace.
"Wai wanne irin ciwo ne haka? Ace har yanzu babu sauƙi"
Ajjiyar zuciya Oumuu-Ayman ta sauke tace
"to yaya za'ai da ikon Ubangiji Auta? Muci gaba da addu'a Allah ya dawo da Zaki lafiya"
"Ameen" tace Idanunta na sauka a bakin King Tunde Muhammad Jalal ganin wani farin yawo na fita daga cikin bakinsa yasa a hankali ta sanya yatsarta ta shafo yawon ganinsa yana yauƙi ne ya sanya tai saurin kai yatsar bakinta, wani ɗaci taji ya game bakinta da sauri ta Miƙe tsaye tana faɗin "Garin meriz??? Innalillahi wa'inna ilaihir Arjun gubar ƙune jini"

Rugar Mahinjo
A hankali yake buɗe idanunsa wanda sukai masa nauyi, bakinsa ɗauke da addu'a,
A hankali kuma ya yunƙura tare da tashi zaune,
Hakan nan yay yake jinsa wani iri jikinsa yayi masa nauyi yana buƙatar motsa jiki sosai,
Idanunsa ya ɗaga ganin Arɗo ya shigo ga kuma kiɗa dake tashi a Rugar, tun kallon farko da yayiwa Arɗo bai sake kallonsa ba.
"Kamar dai julal ya bayyana, what the fork" ya faɗa yana jan numfashi duk abi an cika mutane da ihu, Kallonsa Arɗo yayi kafin yace.
"Wasan motsa jiki ne"
Da sauri ya buɗe idanunsa kamar bazai magana ba sai kuma yace.
"Uhm ball or what?"
Ya faɗa yana Miƙewa tsaye tare da yin waje domin jikinsa duk ciwo yake masa, yana fita kowa ya mutane da yawa sai kiɗe-kiɗe ake.
Bayansa Arɗo ya biyo yace "ko kana so ne?"
Lumshe idanunsa yay tare da buɗewa Arɗo yace.
"To muje na gabatar dakai"
Gently yabi Arɗo jiki babu ƙwari, Barkido ne da Labbo a tsakiyar filin kowa jikinsa da guro jikinsu sai rawa yake, ga wata zabgegiyyar bulala a hannun Barkido da alama shine zai fara dukan Labbo, kana ganin bulalar kasan tayi shekaru a jiƙe saboda yadda ta kumbura,
Arɗo ne yace.
"An samu ƙarin ma nemi, yanzu jaruman namu guda uku ne"
Jin haka yasa Labbo tsorata da kuma firgita, a hankali ya dinga janye jikinsa kafin kace me ya nausa cikin jeji domin tsira da ransa, domin labari yazo masa hadda kitsan kibari aka saka wa bulalar Barkido,
A hankali Abu Maleek ya dawo tsakiyar filin a ransa yace "bana faɗawa Oumuu na girma ba, bari naiwa wannan duka zan bata labari"
Ya faɗa yana cije baki, Barkido ne yace "kai baka san komai akan wannan abun ba, kada kayi a sarar ranka, ka janye ka bar min kamar yadda ɗayan ya gudu"
Abu Maleek damai san kan abun ba ya kalli Barkido yana mai ɗan tsotsar laɓɓansa kafin yace.
"Uhm ba'a sauya min ra'ayi, idan nace zan yi to zanyi kada ka cikani da ihu kayi abinda ya dace"
Ran Barkido ne ya ɓaci a ransa yace "za kaci Ubanka yanzu mahaukacin banza kawai"
Ya ƙare maganar yana fincike rigar jikin Abu Maleek nan da nan surar jikinsa ta bayyana mai cike da haiba, ga zanan ya fito raɗau gwanin sha'awa, ƙuri Arɗo yayi masa da ido, a na haka aka bawa Barkido umarni,
Gyara tsaiwa yayi sosai tare riƙe bulala hannunsa da kyau, babu zato babu tsammani Abu Maleek yaji an zabga masa bulalar a tsakiyar bayansa, runtse idanunsa yayi saboda tsananin azaba da kuma raɗaɗin daya shige sa a lokacin guda,
Kafin ya dawo daga gigin dukan Barkido ya ƙara shimfiɗa masa wata bulala a tsakiyar bayansa zuwa tsakiyar kansa, dunƙule hannu Abu Maleek yayi tare da langwaɓar da kansa gefe guda cikin a zababban zafin daya ratsa masa jijiyar kansa ya buɗe bakinsa yace.
"O'ohhhh"



*Abu Maleek na kuɗi kada ki karanta bada izini na ba, kiji tsoran Allah idan kina buƙata kiyiwa wannan number mgn 08119237616*




*_Nimcyluv


29-30_*



Ajjiyar zuciya Abu Maleek ya sauke, tare da runtsa idanunsa saboda wani azaba da yaji ya ratsa saman fatarsa, yana neman gigita masa lissafi.
A hankali kuma wata zufa ta fara yanko masa, yadda jikinsa ke rawa kaɗai zai fahimtar dakai Tabbas bulalar ba ƙaramin shigarsa tayi ba.

Jikinsa ya cure waje guda, yana jin yadda naman jikinsa yake rawa tamkar zai ciro daga jikin ƙashin sa ya faɗo ƙasa.
A hankali ya fesar da numfashi daga cikin bakinsa yana mai jan numfashi tare da gyara tsaiwarsa,
Yana mai shigar da lip's ɗinsa cikin bakinsa yana tsotsa.
Sweet dage can gefe ta shiga tsalle tana sakine ƙara, tare da ɗaga jela, ƙurie yayi mata da idanunsa,
Kafin yaga wasu ruwa na taruwa a cikin Idanunta, ƙara runtse idanunsa yayi a hankali kuma jikinsa yaci gaba da ɓari, yana mai ɗan taune leɓansa.

A karo na uku kuma Barkido ya ƙara saita bulalar hannunsa tare da sakarwa Abu Maleek a tsakiyar bayansa,
"Uhmmmmm"
Shine kawai abinda bakinsa ya iya faɗa,domin azabar da yaji ta huce ya buɗe bakinsa yayi ihu,
Gaba ɗaya tsukar jikinsa rawa take,
Bai taɓa samun kansa cikin a azaba mai raɗaɗi a jikin irin yau ba.

Wata kyakkyawar ajjiyar zuciya ya sauke, tare da taune leɓansa gumi ya shiga tsastsafo wa a tsakiyar goshinsa lokacin,
Da Barkido ya sakar masa bulala ta biyar.

Cikin jin daɗi da kuma farin cikin samun nasara kuma Barkido ya ƙara sakarwa Abu Maleek bulala ta goma a gefen hannunsa,
Yana tsaye cirr daga inda yake ko motsi ba yayi, kansa a ƙasa ilahirin jikinsa kowa rawa yake,
Ga wata zufa dake yanko masa,
A dukkan kofufin gashin jikinsa, laɓɓansa sai rawa suke saboda tsananin a zaba, da kuma raɗaɗi haɗi da zugin dake gigita masa fatar jikinsa.

Gefe kowa Arɗo ne da Lamiɗo zaune suka kallo mamaki duk ya cika su, ganin ko wani ƙyakƙyawan motsi Abu Maleek bai ba, bare a sanya ran cewa zai sanya kuka kana ya gudu daga cikin rugar baki ɗaya.

Lamiɗo ne ya gyara zamansa tare da sakin murmushi kana ya fuskanci Arɗo yace.
"Da kasantuwar Baƙon Mutumin nan zai shanye dukkan bulalar da Za'ai masa, yanzu ana bulala ta ashirin da biyu ne bulala takwas kawai ta rage masa, amma ko motsi bai ba, bare kasa ran cewa hawaye zai zuba daga cikin idanunsa, na tsorata da al'amarin sosai"

Murmushi Arɗo yayi kafin ya juya ya sauke idanunsa akan fuskar Barkido wanda shima tashin hankali ya bayyana ƙarara saboda ganin ya yi bulala ta wajan ashirin da biyar amma babu alamar Abu Maleek zai kuka ko kuma ya gudu daga cikin filin baki ɗaya,
Idanunsa ya ɗauke daga kallon Barkido kafin ya juya ya kalli Lamiɗo yace .

"Burina daman Wannan mahaukacin ya shanye wannan bulalar nan, domin ba ƙaunar Barkido ya auri wannan Yarinyar, kasan abinda yake gabanmu, kasan kuma dalilin daya sanya na raba Madibbo da ransa, wannan dalilin ya sanya itama nake son ganin bayanta amma Allah bai ba, nayi amfani da wannan damar ne wajan ganin tayi nesa damu baki ɗaya, yadda zata mance data taɓa rayuwa cikin Fulani balle kuma ta tuna sunayen mu, jin daɗin kuma duk inda ta ganmu ba zata taɓa fahimtar su waye ba, balle kuma ta kama sunayen mu a baki,
Zanyi farin ciki sosai ace wannan Mahaukacin ya samu na sara yaje can su ƙarata shi da ita"

Cike da gamsuwa Lamiɗo ya jinjina kansa, kafin ya juya ya kalli Abu Maleek a dai-dai lokacin da Barkido yake sauke masa bulala ta talati cifff,
Juyawa yayi ya kalli Arɗo yace.

"Tayaya kake tunanin bulalar da akai masa zata damesa? Kallesa da kyau, wanne bashi kaɗai bane akwai tsari mai yau gaske a jikinsa wanda shi kansa bai san dasu ba, hatta wannan magen da yake tare da ita rai da rai ban amince da ita ba,
Tabbas akwai wani Ɓoyayyan al'amari da yake tare da shi Tabbas, akwai kuma tarin ƙaddarori a cikin rayuwarsa"

Miƙewa tsaye Arɗo yayi kafin yace.
"Ba wannan ke ban mamaki, tsarin kyahun halittarsa, haibarsa da zallar isa ƙasaita, zanan ƙirjinta yana fisgata sosai, kana ganinsa kaga babban mutum Wanda rayuwa cikin talakawa sam bai saba da ita ba, sauƙin kansa kuma abin burgewa ne,yana rayuwa damu babu ƙyamata, abu ɗaya na lura baya son ihu a saman kansa, raɗashi yake, tambayar a nan mene ya sanya ya zama mahaukaci? Mahaukacin gaske ne ko kuma na ƙarya? Wanne dalili ya sanya ƴan uwansa turosa cikin Birnin Bera ko ƙaunarsa ne ba sayi?"

Shiru gaba ɗaya sukai, tare da nufar inda Abu Maleek yake, Barkido kam baya yayi tare da neman waje ya zauna, shi kansa da yayi dokan jikinsa mugun ciwo yake sosai, amma al'amarin Abu Maleek ya firgita sa sosai, yana danne wa saboda kada mutane su Fahimci halin da yake ciki.

Abu Maleek kam gaba ɗaya baya gane abinda yake faruwa ya daɗe da shiga ɗaya duniyar tasa, tun lokacin da yace "O'ohhh" hannunsa gaba ya dunƙule waje guda jikinsa duk ɓari yake,
Yayinda jijiyoyin kansa suka fito sukai raɗa raɗa a saman goshinsa,
Jin alamar tafiya ne kuma ya sanya ya juya ya kalli gefensa, Ganin Arɗo da Lamiɗo na nufu inda yake tsaye ne ya sanya da wani irin sauri ya juya ya nufi wata bukka dake kusa dashi, ko kallon gabansa baya iyawa,
Sweet na ganin haka ta rufa masa baya, jikinsa na wani irin ɓari na azaba ya faɗa cikin Bukkar tare da faɗawa saman wata tabarma kaba daya gani.

A hankali ya ɗaga hannunsa da niyyar ya jawo sweet jikinsa, jin babu sweet kusa sai kamar mutun a kusan shi, ya sanya bai jira tsayawa komai ya sanya tattausan hannunsa wanda yake fidda wani irin gumi mai zafi ya jawo wanda kusa dashi jikinsa,
Cikin bacci Julde taji an matse ta sosai, kamar za'a rabata gida biyu, a hankali ta motsa domin

Please Login or Register in order to submit comment