Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

BUSA A MUTU!!!
Littafi Na Daya (1)
Part A

Marubucin Littafin
Abdulaziz Sani M/Gini

Marubucin ya fara da cewa...

A YARIN Fatake ne da 'yan gudun hijira daga
wata babbar kasa da ake kira Lairus.
Yawansu ya kai dubu uku, wasu akan
dawakai suke tafiya, wasu a rakuma da alfadarai. A
kalla wadannan mutane sun shafe kwana tara suna
tafiya a cikin daji suna keta kwazazza bai, koramai da
duhuwoyi. A cikinsu akwai zaratan samari majiya
Rarfi, sannan akwai mata, yara da tso fafffi kuma
yawancinsu iyalai ne, wato wani zaka ga tarc yakc da
matarsa da kuma dansa ko 'yarsa ko kuma 'ya'yansa
guda biyu ko uku. Wani kuwa tarc yake da mahaifinsa
ko mahaifiyarsa. Wani yana tare da dan uwa ko 'yar
uwa. Kuma gashi suna daukc da dukiyoyinsu wasu ma
har da dabbobinsu.

Abin tambaya anan shi nc, ina wannan ayari suka
nuta, kuma daga ina suka fito, sannan ina suka dosa?
Ba wani abu banc ya sa wannan ayari suka yi
gudun hijira ba face masifar yaki da ta 6arkc a kasar
tasu ta Lairus wadda ta haddasa asarar miliyoyin
rayuka da dukiya.
Shi dai wannan yaki ya faru nc sakamakon
wadansu 'yan tawaye wadanda suka yiwa Sarki
Muraisu borc domin tabbatar da cewa sun tunkude
mulkinsa da karfin tsiya saboda kawai ganin cewa shi.
mutum ne adali wanda baya zalunckuma bai yarda da zalunci ba
Su dai wadannan 'yan tawaye sai da suka shekara
bakwai suna tanadi na wannan yaki suna tara dakaru a
baye a can wata kasar daban gami da kayan yaki. Sai
da suka tara mayaka miliyan biyu da rabi kuma ya
zamana cewa kullum a cikin basu sabbabbin horon
yaki ake.
Babban abin takaici shi ne ba wani bane ya dauki
nauyin wadanma Dakarun iawayc ba face Yarima
Huraisu kanin Sarki Muraisu wanda suka kasance uwa
daya uba daya.
Tun Muraisu da Huraisu suna yara kanane suka
taso basa jituwa saboda bambancin halaye sa ra'ayi
suka zama tankar abokan gaba, ya zamar.a ccwa basa
yiwa juna ga maciji. Babu abinda ya tsananta gaba a
tsakaninsu face Huraisu ya san ceva idan mahaifinsu
Sarki Salmar ya mutu, Muraisu ne zai hau kan karaga
saboda tuni Sarki Salma ya yi nuni da hakan har ma ya
bar wasiyar hakan.
Halayen Sarki Saimar iri dayane dana Muraisu
wato suna da son taiakawa,tausayi da taimako. Kwata-
kwata abin duniya bai danesu ba. Begu da kari
Muraisu ya kasance saurayin mai farin jini matuka a
wajcn jama ar gari saboda ganin cewa ya taso da
halaye na mahaifinsa. Duk inda ya wuce ma sai dai ka
J1 ana yi masa kirari da Magajin Sarki. Shi kuwa
Huraisu jama'a sun tsaneshi kamar yadda suka tsani
Mutuwarsu saboda bakar zuciyarsa ta zalunci. Ko
kallonsa mutum ya yi ya tsargu Sai ya zare makami
nan take ya sareshi. Idan ya ga budurwa mai kyau ko
'yar gidan uban waye sai ya yi ma ta fyade haka kurma
duk dukiyar da ya gani in dai ya ji yana bukatarta to fa
sai ya kwaccta.
A duk sa'adda Huraisu ya yi irin wannan mugun
aiki baya yarda ya dawo gida sai dai ya shiga daji ya
buya saboda sanin cewa saii Sarki ya sa an yi masa
hukunci mai tsauri dai-dai da laifin da ya aikata.
Sarki ya sha sawa a yiwa Yarima Huraisu bulala
arba'in ko hamsin a farfasa masa jiki har sai ya yi
jinya. Kuma duk sa'adda ya aikata laifin ya gudu daj
babu mai iya zuwa ya kamoshi da karfin tsiya sai dan
uwansa Muraisu.
Muraisu da Huraisu sun kasance gawurattun
Sadaukai na gaban kwatance kuma kwararrun mayaka
wadanda suka yi shuhura a cikin nahiyarsu sai dai
Muraisu ya fi Huraisu karfi, jarumtaka da iya yaki
nesa ba kusa ba.
Wani lokaci idan Muraisu ya tafka laifi sai Sarki
ya sa a daureshi tamau a sama a jikin dirka a gasashi a
cikin rana, ba ci ba sha har tsawon sa'a ashirin da hudu
amma saboda naci da bakin hali idan aka sakeshi gobe
ma sai ya kara aikata wani laifin da ya fi na baya.
Azaba ko bazarana ba ta firgita Huraisu koda
kuwa ya san cewa zai iya rasa rayuwarsa sakamakon
azabar da za a yi masa.
Sarki Samral yana matukar kaunar Yarima
Muraisu saboda ladabinsa da biyayyarsa da kuma
halayensa da ya gado gami da yadda ya ga jama'ar
birnin Lairus ke tsananin kaunarsa suke girmamashi.
Ko kara Sarki Salmar ya ajiye Muraisu ba zai ketarce
ba.
Mahaifiyar Muraisu ta rasu ne a ranar da ta
haifesu suka zo duniya lokaci guda tagwaye. Muraisu
da Huraisu suna matukar kama da junansu tamkar an
tsaga kara.
A wannan rana an cc Sarki Samral ya yi
matsanaicin kuka da bakin ciki. Al'amarin da ya
matukar baiwa mutanen kasar gaba dayansu mamaki
ke nan, domin a tarihin rayuwar Sarki Samral tun daga
kuruciyarsa kawo izuwa girmansa ba a taba ganin
kwalla ba a idanunsa, amma sai gashi an ga ranar da
yake ta kuka kishin6ar! da hawaye daki-daki, wani na
bin wani.
Sarki Samral kasaitaccen sadauki ne kuma
gabjcjen mutum mai kirar mutanen farko, domin duk
sa'adda yaje nahiyar da ba a sanshi ba da zarar mutane
sun ganshi sai su firgice su kama guje-gujc, wasu su ce
sun yi gamo da aljani, wasu kuma su ce ai fatalwa ce.
Komai girman bishiya da hannu daya Sarki
Samral ke hankadeta ta fadi kasa. Komai girman dutse
da nauyinsa idan har ya ritsashi da hannayensa biyu to
fa zai iya rabashi da kasa ya dagashi sama ya yi
doguwar tafiya da shi ba tare da ya gaji ba.. Idan kuwa
zai fita yaki saj dai a tanaji giwaye kamar guda arba in
a matsayin ababcn hawansa, kumna babu wacce za ta
, AA Misau Nake, iya daukarsa sama da tsawon rabin sa'a ba tare da ta
gaji ba ta durkushe kasa saboda tsananin nauyinsa. Kai
idan Sarki Samral ya fusata yana iya daukar ita kanta
giwar ya yi wurgi da ita tamkar ya yi wurgi da hoge.
Labarin Jarumtakar Sarki Samral ya bazu ko ina
a nahiyarsu har ma da sauran nahiyoyin da ba nasu ba.
Kuma ba a ta6a samun GWARZON MAYAKI ba
kamarsa. A tarihin yake-yaken da ya yi a rayuwarsa
tun kafin ya hau karagar mulki har izuwa sa'adda ya
bar duniya ba a taba cinsa da yaki ba, kuma ba a taba
ji masa ciwo ba. Idan yana tsakiyar abokan gaba yana
saransu da sukarsu da takobinsa sai ya shafe sa'a goma
sha biyu bai gaji ba, kuma tsananin zafin namansa da
Rarfin gudunsa ya wuce misali kamar iska ce ke
sarrafa gababen jikinsa.
Da yake mutum ya kan haifi kansa sai gashi
Sarki Samral ya haifo zakwakuran sedaukai da suka
gado wannan girman jiki irin nasa da kuma jarurntaka
tasa sai dai inda aka sami akasi Muraisu ya fi Huraisu
komai ya ma ninkashi.

Lokacin da fitinar Huraisu ta yi yawa kuma ta
damu Sarki Samral ya zamana cewa duk irin azabar da
aka vi masa da irin hukuncin da ake yi masa mai tsauri
a duk sa'adda ya aikata laifi sun zama a banza sai Sarki
ya kafa masa doka ta karshe ya sanar da shi cewa dukLa
ranar da aka sake kamashi da laifin yin fyade ko sata
ko kuma cin zali sai an yanke masa hannayensa biyu
Domin kowa ya huta da fargabarsa saboda ya addabi
Gaba dayan jama'ar birnin da Rauyuka.
Sa'adda mutane suka ji wannan gagarumin
bukunci da aka dauka akan azzalumi Huraisu sai suka
cika da tsananin farin ciki. Tun daga wannan rana
kyawawan 'yan mata suka sami 'yancin yawo a ko ina,
attajirai suka rinka fatauci a ko ina a kasar cikin
kwanciyar hankali, sabanin da can da 'yan fashi suka
yawaita a ko ina a cikin kasar, kuma gaba dayan 'yan
fashin yaran Yarima Huraisu ne.
Lokacin da Yarima Huraisu ya ke kan sharafinsa
na aikata duk irin laifin da ya ga dama ne ya tara yara
a karkashinsa sama da dubu dari, kuma a kowanne
birni da ke cikin kasar yana da wakilai.
Duk sa'adda Fatake za su ratsa wata hanya ko
kuma a duk inda za a yi wani gagarumin kasuwanci da
dukiya mai yawa sai labari ya riskeshi sai dai kawai
aga shi da yaransa sun baiyana a wajen sun tafka
gagarumar 6arna. Ran biladama kuwa sun mai da shi
tamkar na kiyashi.
A wannan lokaci ne Huraisu ya tara dukiya mai
tsananin yawan gaske saboda haka sai ya så aka gina
masa wani tafkcken gida a tsakiyar waii daji da akc
Kira Kirzufa, wanda ke tsakanin iyakar birnin Lairus
da wani birni mai suna Hutaira.
Shi dai wannan daji na Kirzufa dade ana rigima a
Kansa a tsakanin kasashen biyu domin kowacce kasa
kuma sau ashirin da daya ana yaki a zamanin Sarki
Samral akan dajin, amma duk sa'adda aka yi yakin sai
dai ayi ragas, duk da cewa Sarki Samral ya zama
dodon maza kuma gagaraba dau. ba komai ne ya janyo
Madakin Gini
hakan ba face tsananin yawan mnayakan birnin Hutaira
ya wuce misali.
Akwai lokacin da Sarki Samral ya kwana arba'in
Cif yana yaki da su shi kadai amma sai ya kasa karar
da koda rabinsu, suma suka kasa hallakashi ko kaishi
Ras.
Duk sa'adda ya ga ya gaji ainun sai ya falfala da
matsanaicin gudu su kasa cimmasa har yaje wani
wurin ya buya sai ya huta sannan ya dawo a ci gaba da
gumurzu. Gashi dai yana kashesu tamkar ana kakkabe
ganyaycn bishiyoyi a daji, amma sai ka ga kamar
matattu ne suke tashi saboda azabar yawansu. Kai a
wannan zamani sai da masu bincike suka gano cewa
ko mutan cn birnin Sin ba su kai rabin yawan mutancn
birmin Hutaira ba.
A karshe bisa dole Sarki Samral ya janye yakin
da kansa ya koma birninsa ya hakura da mallakar dajin
Kirzufa. Har Sarki Samral ya bar duniya da takaicin
rashin mallakar dajin Kirzufa ya tafi, kuma kafin ya
mutu sai da ya barwa Muraisu wasiyyar cewa duk
yadda zai yi ya tabbatar da cewa ya mallaki dajin
Kirzufa kafin shima ya bar duniya. Muraisu ya dauki
alkawarin cewar koda kuwa zai rasa rayuwarsa a
kokarin mallakar dajin Kirzufa ba zai Gaza ba
Sarkin da ke mulkin birnin Hutaira, wani
gawurtaccen boka ne mai suna Ishmar ibiní Suraifa.
Shima Sarki Ishmar babu abinda bai yi ba akan
ya ga bayan Sarki Salmar domin ya mallaki dajin
Kirzufa amma abu ya gagara.
Abinda yake daurc masa kai shi ne, "Me ya sa
tsafī baya tasiri akan Sarki Samral?
Babu irin binciken da bai yi ba a hallarar tsafi
domin ya gano wannan matsala amma abu ya gagara.
Kawai abin da ya iya ganowa shi ne akwai wani
babban sirri a tarc da Sarki Salmar wanda yasa tsafi
baya tasiri a jikinsa kuma ya ziyarci bokaye da yawa a
duniya wadanda ma suka fi shi karfin sihiri amma
dukkaninsu sun kasa gano wannan sirri. Abinda
bokaye suka gaya masa shi ne duk duniya babu wanda
ya san wannan sirri face shi kansa Sarki Samral kuimna
kafin ya bar duniya sirrin zai koma kan dansa Muraisu,
shima kafin ya mutu dansa zai gaji wannan sirri.
Haka al'arnarin zai ta bibiyar zuri'arsu shckara da
shekaru, zamani bayan zamani. Ba za a taba rabasu da
wannan sirri ba face a ranar da aka kai mai sirrín kas a
filin yaki aka sami nasarar hallakashi. A sannan nc za
a tsaga kirjinsa a ciwo wannan sirri wanda ya kasance
dan siriri tamkar silin gashin da ke wuyan doki guda
daya.
Sa'adda Sarki Ishmar ya ji wannan jawabi sai
hankalinsu ya dugunzuma ainun, domin ya san cewa
, AA misau nake, : shi dai abu ne mawuyaci a zamaninsa ya ga wannan
rana sai dai nan gaba a zamanin 'ya'yansa ko jikokinsa.
Akan haka ne ya rungumi kaddara bisa tunanin
mallakar dajin Kirzufa a wannan lokaci amma sai ya
ayyana a ransa cewa komai darcn dadewa sai an sami
wani daga cikin zuri'arsa ya mallaki wannan sirri.
Shi dai Sarki Ishmar Allah Ya albarkaceshi da
yayye har guda talatin da tara, amma gaba dayansu
mazane babu mace ko guda daya, kuma a binciken da
ya yi zuri'arsa ba za ta taba samun damar mallakar
wannan sirri ba na Sarki Samral face an haifi
gagarumar BASADAUKIYA jininsa wacce za ta
shahara a ko ina cikin duniya.
Wani babban abin
takaici
shi
ne
gaba
daya
'ya'yan
Sarki
Ishmar
manya
wadanda suka yi aure duk
wanda
matarsa
za
ta haihu
sai aga
namiji ta haifa ba a taba samun wacce ta haifi
'ya
mace
ba bare Sarkı
İshmar ya
sa
ran
cewa
ita
ce
za
ta kar6i wannan sirri ga
zuri'ar Sarki Samral.
Saboda wannan dalili. ne duk sa'adda aka yi
haihuwa Sarki Ishmar ya ga namiji aka samu sai ya
kamu da tsananin bakin ciki ya rufe kansa a cikin daki
ya yi ta kuka domin ya san cewa har abada ba zai ga
ranar da zai raba Sarki Samral da wannan suri na sa ba
Wanda zai sami damar cuiar da shi da zuri'arsa da
Carfin sihirin tsafi. Babban abin takaici a gareshi shi ne
lsufa ya riskeshi ya shekara tamanin da hudua dunivai ya
san cewa ajali ko yaushe
ajali zai iya riskarsa
: De jin Kirzufa wani irin sihirtaccen daji ne
wanda sama da shekaru dari baya ba a aba samun
mahaluin da ya shiga cikinsa ya iya dauko wani abu
ba face mutum aya rak, wato Sarki Samral.
a wannan
ikokinsa.
Shi
dai wannan daji na Kirzufa
Allah
Ya
albarkaceshi da tsuntsaye iri-iri gami da dabbobin daji
kala-kala masu yawan tsiya. Wata dabbar ma ko a
labari mutum bai taba jin labarinta ba.
Babban sirrin dajin Kirzufa shi ne, idan mutum
ya shigeshi in dai bai yi ko Rarin đaukar wani abu ba
ko cutar da wata dabba ba to fa zai shiga lafiya kuma
ya fito lafiya, amma da zarar ya yi yunkurin daukar
wani abu ko cutar da wata halitta, to fa sunansa gawa!

Mafarauta da mayaka sun sha hada runduna su
shiga dajin don đebo albarkatun cikinsa, amma
dayansu baya dawowa a raye.
Shi kansa Sarki Samral sau daya ya taba shiga
dajin ya yi farauta inda ya kamo wadansu giwaye guda
shida. Nan take ya kashe guda hudu ya ciro haure
guda biyu kuwa ya sabosu a kafadunsa ya fito da su
daga cikin dajin.

Koda va iso inda ya bar Dakaru hamsin wadanda suka
yi masa rakiya izuwa farautar suka ganshi da
wadenan giwaye da kuma haure sai suka cika da
tsananin mamaki suka rinka shewa suna yi masa
iinjina domin shi ne mutum na farko da ya karya
alkadarin dajin Kirzufa.....

Sbd haka Nima Ku Tafamin😂
Dafatan Kowa yana lafiya
SaikumA Mun sake haduwa a part BBUSA A MUTU!!!
Littafi Na Daya (1)
Part B

Marubucin Littafin
Abdulaziz Sani M/Gino

Marubucin yaci gaba da cewa....

Nan da nan labarin wannan jarumtaka da ya yı ya
bazu a ko ina a nahivar. Wani abin mamaki shi nc,
hauren giwayen da ya farauto a cikin dajin sai da suka
zamo sanadiyar samun dukiyarsa mai tsananin yawa
irin wacce bai taba samu ba a rayuwarsa domin
manya-manyan Sarakunan duniya ne suka rinka yin
tattaki suna zuwa har birnin Lairus suna siyan hauren
giwa daya jal akan miliyoyin dirhami.
Duk wanda ya sayi hauren giwar sai ya kaishi
masarautarsa ya adanashi a gidan tarihi mutane suna
Zuwa suna gani suna biyan kudi. Shima ya sami abin
samun kudi.
Shima Sarki Samral sai da ya ajiye hauren giwar
guda daya jal a tsakiyar fadarsa saboda barin tarihi,
kuma yasa aka sassa ka gunki mai kamanninsa da
girmansa sak! Yana gumurzu da giwaye shida na
gumaka.
Duk mutumin da ya shigo fadar Sarki Samral ya
ga wadannan gumaka na giwaye shi da Sarki Samral
dole ne ya yi sha'awarsu domin sun yi matukar kyau,
kasancewar an yi su ne da zallan zinare, kuma
masassakin ya kwarance ainun, da ka kallesu sai ka ga
kamar za su yi motsi tamkar na gaske ne ba gumaka
ba,
Daga wannan rana da Sarki Samral ya shiga dajin
Kirzufa ya yi wannan farauta ya dawo gida bai sake
sha'awar sake zuwa daji ba Shekara na zagayowa ne ya kamu da cutar ajali.
ya kwanta ciwo. Kuma a wannan lokaci ne Yarima
Huraisu ya yi fishi ya bar birnin Lairus ya koma can
daji inda aka gina masa wannan tafkcken gida ya
zauna tare da yaransa manya-manyan 'yan fashi suka ci
gaba da sharholiyarsu.
A sannan ne labari ya riski Yarima Huraisu
cewar mahaifinsa Sarki Samral ya kwanta cutar ajali.
Koda samun wannan labari sai Huraisu ya cika da
matukar farin ciki ya fara tunanin hanyar da zai tara
mayaka masu yawan gaske wadanda za su zama 'yan
tawaye su je su yaki birnin Lairus su karbi mulki da
Rarfin tsiya tunda Sarki na kwance ba lafiya amma sai
abu daya ya fađo masa a rai wanda ya firgitashi. Ba
komai bane wannan abu ba face dan uwansa Yarima
Muraisu wanda ya tabbatar da cewa ya fishi jarumtaka
nesa ba kusa ba, kuma duk abinda Sarki Samral ya yi
shima zai iya yinsa, don haka Muraisu shi kadai zai
iya tarwatsa mayakan da zai tanada ya hanashi cika
burinsa.
Abu na biyu da ya kara dugaunzuma hankalinsa
ya jefa masa tsananin bakin ciki shi ne, ya san cewa
duk sa'adda Sarki va mutu lallai Muraisu ne zai
gajeshi, kuma hatta wannan sirrin sihiri na shiga dajin
Kirzufa sai ya mallaka masa shi.
Babban burin Yarima Huraisu shi ne bayan ya
Zama Sarkin Lairuf ya shiga dajin Kirzufa ya yi farauta
a cikinsa kamar yadda mabaifinsa ya yi ya shahara
A ko ina a duniya. A takaice dai yanzu burin Yarima
huraisu guda biyu ne. Yana son ya zama Sarkin Lairuf
kuma yana son ya sami daukaka irin wacce mahaifinsa
ya samu a sanadiyar shiga dajin Kirzufa.
Lokacin da tunanin wadannan abubuwa biyu
suka yi tsanani a cikin zuciyar Yarima Huraisu sai
hankalinsa ya dugunzuma ya rasa abinda ke masa dadi
a duniya, ya kasa zaune ko tsaye, ya yi ta zarya a cikin
wannan gida nasa na daji.
A wannan lokaci manyan yaransa na zazAune
sun zuba masa ido kawai an rasa wanda zai
tambayeshi abinda ke damunsa.
Daga cikin yaran nasa akwai wani jajurtacce,
mara tsoro, wanda shi ne shugabansu, kuma ya
kasance gawurtaccen mayaki wanda shi kansa Huraisu
yana ji da shi, yana alfahari da shi, ana kiransa da suna
Busara ibini Kalhur.
Ba tare da fargabar komai ba Busara ya nikc
tsaye ya tari gaban Huraisu ya ce, "Ya shugabana wai
shin mene ne yake damunka ne a yau alhalin a jiya da
daddare mun fita sana'a mun dace tunda mun. samo
dukiya mai yawan gaske...Sannan ga giya ganga-ganga
a gidan nan babu adadi, ga mata nan ba na banza sai
Wacce kake sha'awa, komai na jin dadin duniya
akwaishi a cikin gidan nan".
Sa'adda Yarima Huraisu yajı1 wannan tambaya sai
ya kyalkyale da dariya lookaci guda kuma ya murtuke
fuska ya ce, "ya kai Busara, kayi sani cewa buri baya yankewa a zuciyar dan'Adam. Na sani cewa a halin
yanzu na mallaki komai na jin dadin duniya. Duiciyar
da na tara a yanzu har na bar duniya ban isa na karar
da ita ba! Amma ai har yanzu ban sami mulkin birnin
Lairus ba..AA Misau Nake, Har yanzu ban mallaki sirrin shiga dajin
Kirzufa ba. Ta ya ya zan samu daukaka irin wacce
mahaifina ya samu a duniya?"
Sa'adda Yarima Huraisu ya ZO nan a zanccnsa sai
Busara ya yi murmushi ya ce, "Ya shugabana ai babu
wata cuta a duniya wadda bata da magani. Ina ganin
cewa idan ka jc wajen Sarki Ishmar ibini Suraifa zai
iya sanar da kai hanyar da za ka bi ka sami bivan
bukatunka."
Cikin matukar mamaki Huraisu ya dubi Busara
ya ce, "Ta ya ya kake tsammanin ccwa Sarki Ishmar
zai bani hadin kai alhalin ya kasance babban makiyin
mahaifina. ?" Busara ya sake yin murmushi a karo na
biyu ya ce, "Ai Sarki Ishrnar ya san duk abinda ke
tsakaninka da mahaifinka, kuma ya san baka da wai
buri wanda ya fi ka ga bayan mahaifin naka, don haka
tabbas zai ba ka hadin kai tun da fadnwa ta zo dai-dai
da zamna,"
Ya yiin da Huraisu yaji wannan shawara, sai nan
Take ya cika da farin ciki, ya dubi Busara ya ce, A
shirya mini tafiya izuwa bimin Hutaira gobe da safe
Kuma mu uku ne kacal zanu tafi ni da kai da sadaulki
Rauhaz".
Sadauki Rauhaz shi ne na biyu a cikin manyan
yaran Yarima Huraisu wadanda yake takama da su,
kuma baya shakkar turasu aiki ko ina.
Sadauki Rauhaz jarumi nc na gaske, kuma Allah
Ya horc masa basira da kaifin tunani da hangen ncsa,
don haka in dai ya shirya yadda za a yi sata sai an sami
nasara. Ba a taba samun akasin hakan ba.
Haka kuma idan aka shiga RINTSI ko wani bala'i
da zarar ya bada shawarar abinda za a yi a kubuta, ana
yin amfani da shawarar tasa take ake samun mafita.
Bisa wannan dalili ne Yarima Huraisu in dai zai
yi tafiya sai tare da sadauki Rauhaz, domin ya ri ga ya
camfa cewa in dai suna tare duk abinda zai yi sai ya
sami nasara akansa. Har ma kirari yake masa yana
cewa da shi, "Kai ne mabudin hanya! Kai ne tutar
Nasara Rauhaz!!m
Kashe gari kuwa da sassafe Yarima Huraisu,
Busara da sadauki Rauhaz suka yi shiri suka hau
dawakansu suká durfafi birain Hutaira.
Daga wannan daji wanda Huraisu da yaransa ke
zaune zuwa birnin Hutaira, tafiya ce ta kwanaki ashirin
da biyu. Haka kuwa su Huraisu suka shafe wadannan
kwanaki suna tafiya. Kai tsaye suka rinka ratsa
dazuzzuka ba tarc da fargabar komai ba tamkar a cikin
gari suke tafiya, kuma komai dare ko rana basa jin
tafiyar. Babu abinda yake tsaida su face gajiyar
dawakansu da yankewar ruwan sha. Duk inda suka
riski korama ko kogi sai su yada
Zzango a wajen su huta, idan kuwa dare ya yi sosai sai su kwana a wajen.
Duk lokacin da suka yi gamo da muggan 'yan fashi ko
aljanu da sauran dabbobin daji ababan tsoro, cikin
kankanin lokaci suke ragargajesu, su kashe na
kashewa, na gudu su gudu. A haka suka isa birnin
Hutaira lafiya sumul.
Fadace Rasaitacciya wadda ta kawatu ainun fiye
da tunanin mutum, kai a tsaya yin bayanin abinda ke
cikinta ma kauyanci ne sai abinda mutum ya gani da
idanunsa.
Sarki Ishmar na zaune a bisa karagar mulki,
fadawa sun kewaye shi, ga mutanen gari sun taru da
yawansu, AA Misau Nake, wato dai fadar ta cika ta batse sai tafiyar da
harkokin mulki ake.
Sarki Ishmar ya kasance gajeran mutum mai
katon ciki kuma kakkaura amma kuma kyakkyawane
shi a fuska kuma yana da matukar kwarjini, domin
mutum bai isa ya kura nasa idanu ba.
Wata irin kyakkyawar shiga ya yi ta fararen kaya
da doguwar riga da wando da farin alharini wanda
akayi musu dajiyar baki da zaren lu'u-lu'u, sannan ya
đora bakar alkyabba mai tsananin sheki da walwali. A
kansa ya dora wani dan karamin rawani mai kyau
gwanin ban sha'awa, takalmin kafarsa fari ne sol.
Hakika shigar tayi masa matukar kyau kamar da kavan
aka halecceshi a jikinsa. A hannun sa na hagu kuwa
yana rike da farin kwagiri wanda saman sa sifface ta
Zaki.
Kallo daya mutum zai yiwa Sarki Ishmar a
Wannan lokacin ya fahinmci cewa yana cikin farin ciki
domin fuskarsaa cike take da annuri sai murmushi ya
ke yi kamar wanda aka yiwa busharar samun Sarautar
duniya.
A wannan lokaci wasu Makada ne suka baje
kolinsu a fadar, wadansu kyawawan 'yan mata na ta
faman tika rawa. Babu abin da zai baiwa mutum
mamaki face ganin yadda wadannan 'yan mata su
ashirin da hudu kamanninsu ya zo duk iri daya tamkar
tagwaye. Wani karin abin sha'awa a tare da su shi ne,
dukkaninsu sun yi wata iri shiga co ta Zakara, wato da
siffar Zakara aka dinka tufafin jikinsu.
Duk sa'adda Sarki ishmar ya dubi wadannan
kyawawan 'yan mata suna ta cashe

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

2 Comments On BUSA A MUTU Book 1
avatar
shuraihu-usman-1

1 year ago

Reply

Aha

avatar
bilkisu-adam-yusuf

10 months ago

Reply

Littafin yayai dadi

Please Login or Register in order to submit comment