Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sharad’i
da Aliyu Misiriyi sai ya soma tafiya Misira ya
samu iyalin Alin a cikin fatara da yunwa da
tsiraici, sai ya d’auke su ya tafi da su Yaman
ya ba su tufafin alfarma daga dukiyar nan
suka sanya sannan ya taho da su nan. Yayin
da Ali ya ji maganar zuwan iyalinsa sai ya
tashi ya tafi wurin attajirai ya fad’a musu
labarin zuwan kayansa yana cewa, “ku zo ku
raka ni wajen taren kayana, kuma ku taimaka
da iyalanku domin su tarbi nawa iyalin domin
na san yanzu a gajiye suke.” Suka ce, “mun
ji, mun bi.” Suka fita gaba d’aya zuwa bayan
gari suka zauna suna hira suna tattaunawa
sai ga k’ura ta turnuk’e sararin samaniya.
Kowa ya maida hankalinsa zuwa ga wannan
k’ura, yayin da ta yaye jama’a suka ga abin
da ke musabbabin k’urar. Alfadarai ne da
rak’uma birjik da dawaki da mahaya da ‘yan
mata suna ta wak’a har suka iso kusa da
jama’ar nan. Shugabansu ya matso kusa da
Ali ya sumbaci hannunsa ya ce, “ya
shugabana mun samu jinkirin isowa domin
jiya muka so mu shigo amma saboda tsoron
‘yan fashi muka jira sai yau, shi ya sa muka
yi kwana hud’u bayan shigowar ka, Allah ya
kiyaye mu da su.” Daga nan attajirai suka
hau alfadaransu suka yi gaba, karauka na
biye da su sai kuma tawagar mata da yara
da masu tsaronsu na biye da su. Matar Ali da
‘ya’yansa na cikin su suna sanye da kayan
masu daraja na alfarma. Mata na kallon su
suna sha’awar kayan, suna cewa, ‘hak’ik’a
wad’annan kayan ko ga sarakunan
Bagadaza ba za su samu ba balle wani wuri
daban. Attajirai kuma suna ta mamakin irin
wad’annan alfadarai da dawaki fird’a – fird’a.
Haka suka yi ta tafiya, Ali na cikin jerin
manyan attajirai, matarsa da ‘ya’yansa na
cikin manyan matan attajirai har suka isa
masaukinsa.

Zanci gaba05 HIKAYAR ALIYYUL MASIRIYI DAN HASANUL

suka yi ta tafiya, Ali na cikin jerin manyan attajirai, matarsa da ‘ya’yansa na cikin manyan matan attajirai
har suka isa masaukinsa, suka sauka
Shiga cikin gidan har zuwa tsakiyarsa aka
sauke labtu tare da dukkan abubuwan da ke
d’auke da dabbobin nan. Matan fatake suka
tafi tare da matarsa da ‘ya’yansa zuwa wajen
wanka, wajen ya kasance mai yawan itatuwa
da shimfid’u masu kyawun launi da
tsuntsaye na ta kuka mai dad’in saurare.
Yayin da ta fito sai wajen duk ya haskake ta
zama ita kad’ai ake kallo. Suka zauna suna
cin abinci suna hira tsakaninsu ana ta dariya
da shewa. Bayan nan suka dawo zuwa gidan
mijinsu sannan da attajirai suka bar wajensa
sai suka aiko masa da kyautuka da yawa,
matayensu ma suka aikawa da matarsa irin
tasu kyautar abin da ya danganci gari, da
sukari da ruwan wardi da turare da sauransu
masu yawa da suka fi gaban k’idayawa. Ali
ya zauna tare da attajiri mai masaukinsa
suka yi ta hira suna tattaunawa game da
harkar ciniki da sauransu. Attajiri ya ce masa,
“ka bar bayi da hadimai da babanni da
sauran dabbobi su je gidana da ke bayan gari
su huta anan. Ali ya ce, “yau za su tafi domin
na aike su zuwa wani wuri.” Suka tafi zuwa
bayan gari, bayan sun b’ace daga idanun
mutane sai duk suka b’ace zuwa wurin
sabgoginsu. Su ba su kasance sun yarda an
sallame su ba, sai da suka tabbatar sun yi
nisa tukunna suka cika da murna da farin
ciki. Ali da mai masaukinsa suka yi ta hira
har zuwa sulusin dare sannan suka yi
sallama da juna, Ali ya shiga wajen matarsa
suka dasa wata sabuwar hira. Ya tambaye ta
game da halin kasancewarsu tun lokacin da
ya tafi ya bar ta shekaru masu yawa. Ta
fad’a masa irin wahalun da suka shiga na
k’uncin rayuwa da talauci da fatara da
yunwa da tsiraici har sai da ta kai kowa ya
guje su. Ya ce, “godiya ta tabbata ga Allah da
ya kub’utar da ku. Fad’a min yadda kuka zo
nan wurina.” Ta ce, “muna kwance ni da
yarana sai kwatsam muka ji an yi sama da
mu muna tafiya tsakanin sararin samaniya,
ya kai mu wani waje inda muka ga tawagar
larabawa ya sauke mu ba tare da wani lahani
ba. Bayan ya sauke mu muka ga gungun
alfadarai da bayi maza da mata yara da
manya da yara. Na ce da su, “su wanene ku,
kayan wanene wannan kuma ina za ku da
mu?” suka amsa suka ce, “mu bayin Aliyul
Misiriyi ne d’an Hasan mai jauhari na
Bagadaza, ya aiko mu domin mu d’auke ku
zuwa gare shi a Bagadaza.” Na ce da su, “ku
fad’a min daga nan zuwa Bagadaza kwanaki
nawa ne?” Suka ce, “ranki ya dad’e
tsakaninki da birnin Bagadaza tafiya ce
kurum cikin duhun wannnan daren.” Daga
nan suka shigar da mu cikin darbuka muka ci
gaba da tafiya. Da gari ya waye muka tsinci
kanmu anan wajen babu ciwo babu lahani.”
Ya ce, “to wa ya baku wad’annan kayan
alfarmar?” Ta ce, “madugun fataken ne ya ba
ni, ya bud’e d’aya daga akwatin da ke bisa
alfadari ya fito daga wad’annan tufafi ya ba
mu ni da yarana muka sanya, sannan ya
kulle ya bani mukullai ya ce ki kula da su
idan kin sadu da mijinki ki ba shi.’ To ga
mukullan a hannuna.” Ya ce, “za ki iya gane
akwatin daga ciki?” Ta ce, “eh zan gane shi.”
Ya kai ta zuwa taskar nan ta k’ark’ashin
k’asa, ta duba akwatunan nan ta gane
wanda aka fito da shi daga ciki. Ya sa
mukullin ya bud’e ya ga yana d’auke da
mukullan ragowar akwatunan. Ya rik’a bud’e
akwatunan ya tarar da tufafin alfarma masu
daraja da wasu nau’in zinariya da jauharai
da lu’ulu’ wad’ana ba a samun tamkar su sai
wajen sarakuna, ya kwashe dukkan
wad’annan ya kai waccan taskar ya had’a da
wad’ancan na farko. Ya ce da ita, “kin ga
wannan falala ce daga ubangiji mai girma!”
Ya fad
d’imbin dukiya haka.
“wannan falala ce daga ubangiji mai girma mad’aukakin sarki.” Ta ce, “ya shugabana wannan duka ya kasance daga addu’ar da
mahaifinka ya yi maka gabanin mutuwarsa
inda yake cewa, “Ya Allah kada ka sa d’ana
ya abku cikin wahala, ka riskar da shi cikin
sauk’i a kusa.” Na godewa Allah da ya
k’addara kub’utar ka daga mawuyacin hali
kuma ya yi maka sakayya mafificiya tun
daga nan duniya. Na rok’e ka don girman
Allah kada ka sake komawa cikin halinka na
baya inda ka ke mu’amala da miyagu. Ka ji
tsoron Allah bisa dukkan abin da za ka
aiwatar a fili ko a b’oye.” Ta ci gaba yi masa
nasiha tana tausasar zuciyarsa. Tana jan
hankalinsa kan ya bi sunnar ma’aiki mai tsira
da aminci su tabbata a gare shi. Ali da
matarsa da ‘ya’yansa suka cigaba da
rayuwa cikin yalwar arziki da wadata. An ba
shi rumfa cikin kasuwa inda ya jera kayan
jauhari da lu’ulu’u masu tsada, ‘ya’yansa da
bayinsa da barorinsa na taimakonsa wajen
saye da sayarwa. Ana nan sarkin Bagadaza
ya samu labarinsa ya aika masa da ya je
fada domin ya ganshi. Ya d’auki manyan
farantai na jan zinare ya cika su da
kyautauka na daga dukiya mai daraja da
tsada ya tafi wajen sarki. Ya fad’i gabansa
yana mai gaisuwa. Sarki ya ce, “ya kai tajiri
hak’ik’a mun yi murna da zuwanka wannan
gari namu.” Ali ya rusuna cikin girmamawa ya
ce, “Allah ya taimaki sarki, ga wata ‘yar
kyauta daga bawanka na kawo maka
gaisuwa.” Sarki ya karb’i farantan ya duba ya
ga dukiya mai tsadar gaske wadda biyanta
zai kwashe adadin kud’in da ke babbar taska
guda. Sarki ya cika da mamaki, domin irin
wannan dukiya ko wajen sarakuna ba wurin
kowa za a samu ba. Sarki ya ce, “mun karb’i
gaisuwarka, kuma za mu sakanta maka da
misalinta da yardar Allah.” Ali ya sake
rusunawa ya yi gaisuwa ya tafi. Sarki ya tara
manyan majalisarsa ya ce da su, “sarakuna
nawa ne daga sarakunan duniya suka nemi
auren d’iyata?” Suka ce, “suna da yawa
k’warai.”
“To a cikinsu wanene ya kawo min kyauta
kamar wannan?”
Suka ce, “babu ko d’aya, domin babu ya
mallaki kwatankwacinta!”
“To zan rok’i Allah mad’aukakin sarki domin
neman dacewarsa na aurar da d’iyata ga
wannan attajirin. Me kuka gani game da
haka?” Suka ce, “wannan al’amari daidai ne
kamar yadda ka yi nufi.” Ya sa bayi suka
shiga da farantan dukiyar cikin gida aka
nunawa matarsa. Ta duba su d’aya bayan
d’aya ta ga ba ta tab’a ganin abu mai kyau
da daraja irin su ba. Ta ce “daga wanne sarki
wannan abu yake? Da fatan yana d’aya daga
cikin manema ‘yata.” Sarki ya ce ba ya ciki
amma saboda ganin irin wannan kyautar mai
girma gare mu na ga dacewar na aura masa
ita. Kuma na shawarci mutanen fada sun
lamunce min. Yanzu kuma ina son ji daga
gare ki. Yaya kika gani?” Matar ta ce,
“wannan kam babu laifi, domin ya cancanci
fiye da haka ma.” Ta k’ara da cewa, “wannan
al’amari ne daga wajen Allah, idan ya
k’addara haka babu mai ikon hanawa.” Sarki
ya ce, “idan haka ne kuwa babu wanda zan
aurawa d’iyata sai wannan saurayin.” Da gari
ya waye ya aika aka kirawo Ali tare da
dukkan fatake suka hallara gaba gare shi
yana kishingid’e bisa kujerar sarauta. Suka
kwashi gaisuwa sannan ya umarce su da su
zauna, ya sa aka hallara da alk’ali da shaidu.
Ya ce da alk’ali, “ka rubuta cewa na aurarwa
da d’iyata Ali Misiriyi.” Ali ya yi farat ya ce,
“ya sarki ina neman afuwarka, kama ta da
bai wuce bafatake ba, na yi kad’an ya had’a
surutaka da kai.” Sarki ya ce, “nufina ne na yi
maka ni’ima kuma na jawo ka jikina, don
haka na nad’a ka sarautar wazirina.” Ya sa
aka kawo kayan sarauta ya sanya masa
sannan aka rubuta masa takardar nad’i aka
ba shi. Sarki ya yi umarnin ya zauna akan
kujerar wazirci, bayan ya zauna ya godewa
sarki bisa wannan nad’i sannan ya ce, “ya
sarkin zamani, ina mai matuk’ar jinjina da
godiya gare ka bisa wannan karamci da ka yi
min, amma ina da magana d’aya da nake so
ka ji.” Sarki ya ce, ‘fad’i maganar ka kada ka ji
shakkar komai.”
“Ran sarki ya dad’e, tunda mai martaba ya yi
nufin aurar min da d’iyarsa tun farko, ina
rok’on wannan karimci ya karkata zuwa ga
d’ana a d’aura masa ita aure.” Sarki ya ce,
“kana da babban d’a ne?” Ya amsa, “eh ina
da shi.”
“A kawo shi mu ganshi.” Ya sa aka kirawo
d’ansa wanda a lokacin ya kai shekaru goma
sha hud’u. Sarki ya dube shi ya gan shi
cikakke ne wajen kyau da nishad’i da ban
sha’awa. Babu makusa a tare da shi, har ya
fi ‘yarsa kyawu ma. Yaro ya durkusa cikin
ladabi da biyayya da harshe mai fasaha.
Sarki ya gamsu da nutsuwarsa da
hankalinsa. Ya ce masa, “d’ana yaya
sunanka?” “Sunana Hasan.” Alk’ali ya juya
wajen alk’ali ya ce, “ka rubuta takardar aure
tsakanin Hasan d’an Aliyu Misriyi da ‘yata
Husunul Wujud.” Aka rubuta takardar aure
tsakaninsu, daga nan fada ta watse kowa na
cike da farin ciki saboda alherin da sarki da
waziri suka yi musu. Waziri ya samu rakiyar
manyan fadawa da sauran jama’a har zuwa
gidansa. Sannan duk suka watse kowa ya
shiga sha’anin gabansa. Ya shiga wajen
matarsa ta ganshi cikin tufafi irin na wazirai
ta tambaye shi yadda abin yake ya bayyana
mata komai, ta yi farin ciki mai yawa. Aliyu ya
kwanta barci har zuwa wayewar gari sannan
ya kintsa ya tafi fada. Ya durk’usa gaban
sarki ya kwashi gaisuwa. Sarki ya karb’e shi
da murna ya jawo shi kusa da shi domin su
k’ulla shawara. Ya ce da shi, “ya waziri, ina
so a shirya bikin yaran nan da wuri domin su
tare mu huta.” Waziri ya ce, “haka nan ne
Allah ya baka nasara.” Sarki ya sa aka rubuta
wasiku zuwa k’asashe sarakuna, ya sa aka
k’awata gari aka shiga shagali har kwana
talatin cif sannan aka daina. Hasan ya shiga
wajen amaryarsa. Yayin da ‘yar sarki ta
ganshi da irin kyawunsa sai ta cika da
tsananin begensa, ta so shi fiye da yadda
yake sonta. Kamar haka kuma mahaifiyarsa
ta nunawa amarya k’auna. Sarki ya sa aka
gina turaka nan kusa da turakarsa, aka
kammala aikin cikin hanzari da gaggawa. Ya
sa ango da amarya ciki bayan an k’awata
gidan da kayan alatu. Mahaifiyarsa ta
kasance kullum tana gidan tare da d’anta da
surukarta. Idan ta yi ‘yan kwanaki sai ta
koma wajen mijinta. Saboda haka matar sarki
ta ce masa, “Ya sarkin zamani, matar Waziri
Aliyu kuma uwar mijin ‘yar mu ba za ta iya
barin d’anta ba kuma ba zata iya barin
mijinta ba. Ta kasance kullum tana zirga –
zirga, a san abin da ya kamata a yi.” Sarki ya
ce, ‘wannan zancen gaskiya ne.” Ya sa aka
d’ebi wani babban fili a kusa da shi aka gina
turaka ta uku cikin hanzari. Ya umarci waziri
Aliyu ya dawo nan gidan ya zauna. Wajen ya
kasance da turaka uku kenan. Duk lokacin da
sarki ke son hira da waziri sai ya taso ya zo
wajensa su yi ta hira abinsu, ko kuwa ya aika
a kirawo shi wajensa. Wani lokaci kuma ya
kana tara dukkan iyali a zauna ana ta hira.
Da haka suka zauna cikin farin ciki da jin
dad’in rayuwa.

GOBE ZAMU KARASA SANNAN MUSHIGA WATA SABUWAR HIKAYAR06 HIKAYAR ALIYYUL MASIRIYYI DAN HASANUL GADADIYU

Sarki da Waziri
suka zauna cikin farin ciki da jin dad’in
rayuwa har zuwa lokacin da Sarki ya kwanta
rashin lafiya, kullum ciwo ya zamana ya
hauhawa. Da ya ga haka sai ya aika aka
kirawo masa manya fada tare da sauran
masu fad’a a ji duka suka hallara gabansa.
Ya ce musu, “kun ga yadda cuta ta k’i
warkewa, na hak’ik’ance wannan ciwon ba
mai warkewa ba ne, domin duk d’an Adam
sai ya d’and’ani mutuwa. Don haka na kira
ku a kan sha’anin sarauta bayan na mutu,
ina so ku duba lamarin da kyau.” Suka ce,
“wacce nasiha za ka yi mana game da haka
ya Sarki?” Ya ce, “ni yanzu na tsufa, ga ba ni
da lafiya. Ina tsoron bayan mutuwata
wannan masarauta ta fad’a hannun
mak’iyanta ko kuwa ku yi ta fad’a a kan
sarautar har abokan gaba su rinjaye ku. Don
haka nake so ku zab’i wanda zai gaje ni a
cikin raina domin zan fi samun nutsuwa.”
Suka ce gaba d’ayansu, “mun zab’i mijin
matarka, Hassan d’an Waziri Aliyu Misiriyi.
Domin kuwa mun yaba da hankalinsa gami
da hangensa nesansa da ladabinsa ga
manya. Sannan yana girmama dukkan babba
da k’arami a cikin mutane.” Sarki ya ce, “kun
amince da hakan ku da kanku?” Suka ce,
“k’warai da gaske mun amince.” Ya ce, “ta
yiwu kun fad’i haka ne a gabana domin ku
faranta mini rai. Ku je ku yi tunani kada kuma
daga baya ku sauya ra’ayi.” Jama’a suka ce,
“wallahi ba da gangan muke ba, shi ne
zab’inmu a fili da b’oye, mun amince da shi
da zuciya d’aya da iya kk ya wa ur niyya.” Sarki
ya ce, “tunda kun amince da haka, ina so ku
kirawo alk’ali tare da ragowar dukkan
manyan fadawa da masu sarauta wad’anda
ba su hallara nan ba, domin a tabbatar da
wannan shawara.”
Mutane suka tafi suka hallara da dukkan
malamai da masana da sauran sarakuna
duka suka hallara washegari a k’ofar fada.
Bayan sun samu iznin shiga wajen Sarki
suka gaishe shi sannan suka ce, “ga mu
gaba d’aya a gabanka domin cika
umarninka.” Ya d’aga kai ya dube su sannan
ya ce, “ya ku sarakunan Bagadaza, wa kuka
zab’a a cikinku domin ya sarauce ku bayan
raina.” Suka ce gaba d’ayansu, “mun zab’i
Hassan d’an Waziri Aliyu surukinka.” Ya ce,
“tunda gaba d’ayanku kun amince bisa
wanan matsaya, to a je a kirawo shi nan
gabanmu.”
Aka tafi zuwa gidansa aka kirawo shi. Ya zo
gaban Sarki ya fad’i yana mai gaisuwa. Sarki
ya ce masa, “zauna nan kusa da ni ya
d’ana.” Ya matsa kusa ya zauna, Sarki ya
cigaba da magana yana cewa, “ya kai
Hassan, sarakunan wannan daula tamu sun
amince gaba d’aya da kasancewar ka Sarki
bayana. Saboda haka na yi nufin na tabbatar
da wannan al’amari a lokacin rayuwata,
domin zance ya zo k’arshe tun yanzu.”
Hassan ya mik’e ya sumbaci k’asa gaban
Sarki sannan ya ce, “ya Sarki babana, ka sani
a cikin sarakunan nan akwai wad’anda ya fi
ni cancanta da dacewar ya zama Sarki fiye
da ni.” Dukkan sarakunan suka ce, “mu ba
mu da wani zab’i sai kai. Mun amince ka
sarauce mu.” Hassan ya ce, “to ga mahaifina
nan a ba shi a maimakon ni.” Waziri Ali ya ce,
“a’a, wallahi ba za a yi haka ba, dukkan abin
da ‘yan uwana suka amince da shi ni ma na
amince da haka. Kada ka sab’a umarnin
Sarki da na iyayenka.” Hassan ya sunkuyar
da kansa saboda jin kunyar Sarki da
mahaifinsa.
Sarki ya dubi jama’a duka ya ce, “kun amince
da ya zama sarkinku?” Suka amsa gaba
d’aya, “mun amince bisa ga ya zama
sarkinmu!” ya dubi alk’ali ya ce, “ya alk’ali a
rubuta takarda cewa dukkan sarakuna sun
amince da Hassan d’an Waziri Aliyu Misriyi
ya zama sarkinsu bayan raina.” Alk’ali ya
rubuta haka, kowa ya rattaba hannu, ya
zama doka. Daga nan Hassan ya shimfid’a
hannunsa, dukkan sarakuna suka yi masa
mubayi’a, Sarki ma ya yi masa haka. Ya
umarce shi da ya zauna a kan karagar mulki.
Gaba d’aya sarakuna suka mik’e suka yi
gaisuwar ban girma gare shi, suka sumbaci
hannunsa. Sannan suka yi rantsuwar biyayya
a gare shi. Sabon Sarki ya yi mulki a tsakanin
mutane a wannan yinin, ya ba da umarni, ya
yi hani ya yi ta kyauta da sadaka ga mutane
daidai gwargwadon ikonsa.
Da yamma da fada ta watse ya je gaban
surukinsa ya gaishe shi sannan ya sumbaci
hannunsa. Tsohon Sarki ya ce masa, “ya
d’ana, ina maka nasihar ka ji tsoron Allah a
zuci da bayyane. Ya amsa ya ce, “ya babana, da
addu’arka gami da fatan alherinka gare ni
zan samu cimma dukkan abin da nake
buk’ata.” Ya yi masa sallama ya shiga
turakarsa, ya tarar da matarsa da
mahaifiyarta, suka tashi suka tarbe shi da
murna da farin ciki. Suka sumbaci
hannayensa. Sannan ya shige wajen
iyayensa su ma suka yi masa addu’a da fatar
alheri. Mahaifinsa ya yi masa nasihar ya ji
tsoron Allah wajen tafiyar da mulkinsa kuma
ya yi adalci tsakanin talakawa. Ya kwana a
wannan daren cikin farin ciki da godiya ga
Allah.
Yayin da gari ya waye ya yi sallar asuba sai
ya tafi wajen surukinsa ya gaishe shi, sannan
ya dawo wurin iyayensa ya gaishe su. Daga
nan ya kintsa ya tafi fada. Ya wuni a wannan
ranar yana hukunci tsakanin jama’a cikin
adalci, kowa yana farin ciki da wannan
sarautar tasa. Da yamma bayan tashin fada
ya shiga wajen surukinsa ya same shi
ciwonsa ya sake tsananta, ya durk’usa yana
masa addu’ar samun sauk’i. Sarki ya bud’e
ido ya kira sunansa, “Hassan!”
“Labbaika ya sayyadi.” Hassan ya amsa cikin
girmamawa.
“Ka sani ni lokacina ya k’arato, na hore ka da
ka zama mai adalci ga matarka da
mahaifiyarta da kuma iyayenka. Ka ji tsoron
Allah bisa dukkan abin da za ka aiwatar a
rayuwarka. Ka zama mai adalci a cikin
mulkinka kada ka zalunci mara k’arfi ko ka
hana talakawa zuwa kusa da kai.” Hassan
ya ce, “na ji wannan nasiha kuma zan yi aiki
da ita da yardar Allah.” Daga nan Sarki ya
cigaba da jinya tsawon kwana uku ya ce, ‘ga
garinku nan.’ Aka yi masa lifafa aka yi masa
sallah sannan aka binne shi. Aka samu wasu
suka tsaya akan kabarinsa suna karanta
Alk’ur’ani mai girma. A gida ma aka cigaba
da addu’oi gare shi har kwana arba’in.
Sarki Hassan d’an Waziri Aliyu ya cigaba da
mulki a madadinsa. Ya shimfid’a adalci
tsakanin talakawa na birni da na k’auye,
ko’ina aka rik’a sonsa. Mahaifinsa ya zama
babban wazirinsa na hannun dama sannan
aka nad’a wani wazirin na hannun hagu.
Mulkinsa ya zamana mai cike da adalci a duk
tsawon zamaninsa cikin Bagadaza. Allah ya
azurta shi da haihuwar ‘ya’ya uku duka maza
tare da ‘yar Sarki wad’anda suka gaje shi.
Haka suka cigaba da zama cikin farin ciki da
annashuwa har mai rusa jin dad’i, mai
rarraba jama’a ta zaike musu. Tsarki ya
tabbata ga wanzajje wanda ba ya mutuwa
har abada.

INSHA ALLAH GOBE ZAMU SHIGA WATA SABUWAR HIKAYAR

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment